Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 56
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 56: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 56. Kafin ƙarfe takwas sun gama shirinsu na zuwa asibiti,…
3,338 words
Kafin ƙarfe takwas sun gama shirinsu na zuwa asibiti, asibitin su Dr husnah zai kaita yama kirata tace yazo asibitin ya sameta, yau banyi musun zuwa asibitin ba, danni kaɗai nasan me nake ji a jikina, yau ko aikin gida ban iya yi ba, shi yayi komai, ya sakamun hijabina ya kama hannuna muka tafi, part ɗin Ammi muka nufa, tana kitchen suna aiki, zama nayi akan kujera dan bazan juri tsaiwaba, Ammi ta fito jin sallamar su, kallo ɗaya tayiwa Maryam tasan ba lafiya ba, Mustapha ya gaisheta nima na zamo daga kan kujerar na gaisheta, ammi ta amsamun ta ƙara da faɗin "ɗiyata lafiya kike kuwa?" Mustapha ne ya bata amsa da faɗin "bata jin daɗi ne, yanzuma asibiti zamu na shigo na faɗa miki" Ammi cikin tausayawa tace "Ayya, Allah ya ƙara sauƙi, wanne asibitin zaku kuma?" yace "Asibitin su Dr, husnah dannama kirata tace insame ta ƙarfe 8" Ammi tace "kasan asibitinne?" Yace "A'a driver'n kune ze kaimu, aishi ya sani ko?" Ammi tace "ehh yasani sosaima" Mustapha ya duba tsadadden agogon hannunsa yace "zamu wuce 8 ɗin ta kusa" Ammi tace "saikun dawo, Allah yakiyaye" muka amsa da Ameen, na tashi ina taune lips ɗina, Ammi tace "sannu kinji ɗiyata, Allah ya baki lafiya" na amsa cikin sanyin murya tare da ficewa, yaya ya biyo bayana. ya kama hannuna cikin tausayawa yace "sannu baby" na gyada masa kai kawai yace "har yanzu cikin na murda miki?" nace "a'a bakina ne kawai kemun ɗaci, sai jikina da babu kwari" yace "sorry zai dena insha Allah, ko in d'aukeki nace "a'a, zan iya tafiya" muka ƙarasa parking space yana zubamun sannu, bayan ya kira direban ammi muka shiga motar, muka shiga baya nida yaya ina kwance a jikinsa. Ba nisa asibitin sosai cikin wasu yan mintuna muka ƙarasa, kiran Dr husnah Mustapha yayi ta masa kwatancen office dinta, da tambaya suka gane gurin, sai da muka ɗan jirata ta ƙaraso, dan sanda mukaje bata zoba, bayanta muka bi kamar yadda tace har cikin office dinta muka zauna a kujerun gaban table ɗinta. Dr husnah na duban Maryam tace "amarya ya jikinnaki?" kaina a ƙasa na amsa mata, suka gaisa da Mustapha nima na gaisheta, ta dube ni da kyau tace "me yake damun kine ko kuma ince ya kike jin jikinki?" a hankali nace mata "ina jin jikina babu kwari ga jiri dake damuna, sai kuma zazzaɓi kaɗan_kaɗan, jiya kuma harda amai. Mustapha kallon Maryam kawai yake, yadda take faɗar abunda ke damunta amma shi ko sau ɗaya be taɓa sani ba, kullum sai ta dinga lafiyar ƙalau take. Dr husnah yace "yaushe rabon da kiyi period ɗinki" nayi shiru dannama manta da wani abu period, batare da tunanin komai ba nace "tun azumi" Dr husnah tayi murmushi tana duban Mustapha tace "zamu ɗauki jininta da kuma sauran gwaje_gwaje sai mu gano abinda ke damunta." yace "ok badamuwa."
Anyiwa Maryam duk abunda ya dace, inda sakamako ya bayyana tana da shigar ciki na sati 8, Mustapha jin abun yayi tamkar a mafarki ya rungume Maryam ɗinsa cikin tsananin farin ciki da murna, yayiwa Allah godiya babu a daɗi, alheri mai yawa ya cika Dr husnah dashi sannan suka dawo gida, suna dawowa gida ya bata abinci taci tana gama ci sai bacci, su ammi duk sun shigo sun dubata. Tattalin Maryam sosai Mustapha yakeyi baya barinta tayi komai na aiki, shi yakeyin komai duk da ita batasan hakan tafiso tayi aikinta amma yaƙi barinta, ko Part ɗin Ammi baya barinta zuwa saboda wai idan taje zata iya yin aiki a can, sai dai inya fita ta samu taje. Yau juma'a wanda ya kama babbar Sallah saura sati ɗaya, yau kuma k'anin Ammi da iyalansa da mahaifiyarsu zasu zo, dama suna Dubai yana harkar kasuwancinsa kusan watansu guda kenan a can, yau kuma zasu iso naija da yardar Allah........✍️ Meson complete Whatsapp 08166674823
*ABIN DA KA SHUKA....!*
*8️⃣1️⃣*
.........Kwance nake a k'irjin yaya nayi shiru ina jin yanda bugun zuciyata yake k'aruwa, tun jiya da daddare gabana yake ta fad'uwa wanda bansan dalilin hakan ba. Shafa kanta Mustapha yayi cikin tsananin tausayinta, jikinta yayi zafi zau alamar zazzaɓi, cikin tsantsar kulawa yace "princess d'ita" na dan d'ago na kalleshi amma bance komai ba, fuskarta tayi fayau ga damuwa ƙarara akan fuskartata, yace "Please tell me, what happened to you?" cikin sanyin murya ina ƙoƙarin b'oye damuwata nace "babu komai yaya, ka yarda dani" yayi shiru kawai yana kallonta, tun jiya yaga yanayinta gabad'aya ya sauya, ga damuwa a tattare da ita, ƴar girimar da take masa ma jiyan batayiba, tambayar duniya ya mata meke damunta ko inane yake mata ciwo amma tace babu, yayi fushi ya kyaleta tasa masa kuka tace ita dai kawai ya tofa mata addu'a, batajin daɗi ne, yau kuma tunda safe data tashi yaji jikinta da zazzaɓi, yace suje asibiti a dubata taƙi, wai ita kar a mata allura. Na shafi gefen fuskarshi ganin yanda yake kallona, ajiyar zuciya ya sauke ya kai hannunsa ya shafi cikina yace "baby'nmu na wahalar dake ko, sorry" nayi murmushi ganin yanda yayi maganar nace "um, um yaya baya wahalar dani" yace "Allah yasa" na marairaice nace "yaya dan Allah ka barni naje na taya su ammi aiki, ko zanji k'warin jikina" yace "A'a, ki barsu suyi ai suna da yawa, yanzuma kuma sun kusa gamawa, koma ba hakaba keba cikakkiyar lafiya ba inake ina aiki" na turo baki gaba nace "wai yaya ni haka zanta zama bazan dinga aiki ba" yace "a'a amma dai sai baby'nmu yayi k'wari zaki cigaba" nace "haka akeyi dama?" Yace "mu haka zamuyi" nayi shiru ina tunanin wai nice yau da ciki, nice zan haihu nanda wasu watanni, zan zama uwa nima, wata irin soyayyar cikin da kaunarsa ce take ƙara cikamun zuciya. Bayan sallar azhar Dr husnah ta ƙaraso gidan, tun safe mustapha ya kirata akan rashin lafiyar Maryam, tace idan ta taso daga aiki zata biyo ta dubata. Ina d'akin yaya a kwance shi kuma yana falo, ya shigo yana dubana yace "bacci kike ne?" na girgiza masa kai alamar a'a, ya ƙaraso kan gadon ya zauna a baki yana faɗin "ga Doctor nan tazo zata dubaki" na tashi zaune ina kwabe fuska nace "yaya dan Allah kace mata karta mun allura, wlh tanada zafin hannu" ya shafa fuskarta yana murmushi yana tuno darun da'aka sha da ita a asibiti time ɗin da za'a dibi jininta da yi mata allura, cikin kwantar da murya yace "dubaki kawai zatayi ta baki magani" na turo baki gaba nace "nifa lafiyata k'alau" becemun komai ba ya tashi ya fita, two minutes suka dawo ɗakin tare da Dr husnah da sallamarsu, bayan na amsa musu ta dubeni tana murmushi tace "maman biyu, me raki" nayi murmushi kaina a ƙasa nace "ina yini" tace "lafiya ƙalau, ya jiki_jiki?" cike da kunya nace "da sauƙi" ta ƙaraso kan gadon ta buɗe jakar ta ta fara dubani, bayan ta gama ta dubi Mustapha tace "zazzaɓi ke damunta, amma bayan shi babu matsalar komai, yanzu zan rubuta mata magani sai ka siyo mata tasha, tunda batason allura" Mustapha yace "ai gwara ayi mata allurar, dan maganin ma basha zatayiba" na marairaice nace "nidai nafison maganin kuma zansha" yace "shima basha zakiyiba na sani" ya maida dubansa ga Dr husnah yace "kimata allurar kawai" Dr tayi murmushi ta shiga haɗa allurar, na kalli yaya kamar zanyi kuka, ya ɗauke kanshi, bayan tagama haɗa allurar tace "saifa ka riketa" ya tako ya hawo kan gadon ya janyoni jikinsa, na riƙe shi gam dan har na fara jin kamar antsikaramun allurar ajikina, jin hannun Doctor a jikina tana ɗan yin ƙasa da skirt d'in jikina na runtse idona ina ƙara ruk'unk'ume yaya, tana tsikaramun nayi wani zillo hawaye na kwaranyomun, sosai naji zafin allurar gashi dama duk a tsorace nake, yaya ya shiga mulmulamun gurin yana hura mun iska a cikin kunnena, na cizeshi a gefen wuyansa, ya shafa gashin kanta a hankali yace "sorry baby nah" nayi masa shiru ina sauke numfashi tare da ƙara lumshe idona, wani irin bacci na fizgata, cikin abun da baifi 5 minutes ba bacci ya ɗaukeni, Mustapha ya kwantar da ita a hankali jin tayi bacci ya fita falo inda Doctor take jiransa, suka ɗan ƙara tattaunawa akan jikin Maryam ɗin, tace masa babu matsalar komai sannan sukayi sallama ta tafi.
Misalin ƙarfe uku da 'yan mintuna uncle ɗin Mustapha suka ƙaraso gidan su Ammi cikin k'oshin lafiya. Ammi tana harabar gidan tana jiransu, ganinsu yasa ta nufesu da sauri tana ƙara faɗaɗa fara'a akan fuskarta, mahaifiyarta ta fara rungumewa tana mata sannu da zuwa, sannan k'aninta MUHAMMAD mai tsananin kama da ita, sai matarsa kyakkyawa da ita da yaranta twins mace da namiji. Aunty ta jasu zuwa part d'in baƙi na gidan, wanda yasha gyara saboda zuwansu, bayan sun zauna aka ƙara gaggaisawa, Mama, Zuhura, mama Nafisa da Umaimah suma sun ƙaraso falon dan tarbarsu, UNCLE MUHAMMAD wanda yaranshi suke kiranshi da ABBU, sai baza ido yake yana son ganin ta inda d'anshi Mustapha zai ɓullo, mahaifiyarsu su ammi wadda suke kira da HAJJA itama haka dan dama ganin ɗan jikallennata ne ya kawo ta Nigeria. Da sallama ya shigo falon gabad'aya suka zubo masa ido zuciyoyinsu cike da d'okin ganinsa, shi kanshi a nashi a ɓangaren haka ne, fuskarsa ɗauke da murmushi ya ƙarasa ya rungume UNCLE d'insa, wanda ya k'ura masa Ido, cikin Muryar mai cike da zallar farin ciki yace, "welcome my dearest uncle" Abbu ya shafa kansa fuskarsa ɗauke da yalwataccen murmushi yace "welcome Son like no other, nice to meet you" cikin tsananin kaunar uncle d'innasa yace "me too" tare da sakinshi ya nufi gurin wadda yake da tabbacing itace grandmother d'insa saboda yadda take kama da Amminsa duk da ta manyanta, Hajja wadda ta saki baki da hanci tana kallonsa cike da tsananin mamaki ta fashe da kuka cikin hausarta da bata fita sosai "Allah k'adiran, mai girma da juya al'amari a duk yadda yaso, tabbas wannan babu tantama jininmune kuma jinin modibbo, lallai ikon Allah ya wuce gaban komai, yaro mai tsananin kama da ubansa, yanda kasan modibbo haka nake ganinsa" mustapha ya ƙarasa gareta ya rungumeta, ta rungumeshi itama tana cigaba da kuka tana faɗin "ashe da rabon zaka dawo garemu, Allah ya jikan mahaifinka adalin mutum mai farar zuciya wadda ke cike da alheri" Mustapha ya amsa da "ameen" tare da sakinta ya shiga share mata hawaye, yanajin wata irin kaunarta na ratsa masa zuciya, Ammi tayi ƙasa da kanta tana ƙoƙarin maida kwallar data taron mata a ido saboda tuno mata da mutumin da bata da kamarsa a duniya, Hajja ta ƙara ruk'unk'ume Mustapha a jikinta tana kuka, ya samu ya lallasheta tayi shiru, amma fa duk inda yayi idanta na kansa, gurin matar UNCLE d'insa wadda yaranta suke kiranta da Ummee yaje ya gaisheta, twins suka taho jikinsa gabad'aya suna gaisheshi, yara kyawawa 'yan kimanin shekara 7, sai larabci suke zuba masa, Mustapha ya ƙurawa macen ido saboda yadda take acting ɗinta sai yaga kamar Maryam ɗinsa, musamman idan ta waro manyan fararen idanunta ko kuma ta turo ɗan ƙaramin bakinta gaba idan, ya rungume yaran a jikinsa cikin kaunarsu. Su ammi suka cikawa su Hajja gabansu da lemuka nasha kala_kala da ruwa, Abbu kuma sanin da Ammi ta masa baya shan abu mai sanyi, sai ta kawo masa had'add'en shayin data masa na musamman. Ammi ta dubi Mustapha tace "ina ɗiyata kuwa, ko batasan sun ƙaraso bane" Mustapha ya ɗan shafi kansa yace "tana bacci ne, amma bari na taso ta" Hajja ta amshe zancen da faɗin "a'a, karka tasota barta tayi baccinta, abunda muna gidan ba yau zamu tafi ba, idan ta tashi ma gaisa" Mustapha yace "ai lokacin Sallah ma yayi kuma ta jima tana baccin" Ammi tace "katasota toh tunda ko abincin rana bata ciba" ya amsa tare da miƙewa, Umaimah ta bishi da kallo cike da kaunarsa, twins suka ce zasu bisa, umminsu ta hanasu.
Na farka daga baccin tun ɗazu amma ban tashi ba, ina kwance akan gadon jikina yayi wani irin sanyi sai faduwar gaba da nake tayi, addu'a na shiga yi a cikin raina kona samu sauƙin abunda yake damuna, idona a lumshe yaya ya shigo ɗakin, gadon ya hawo ya janye blanket d'in dana lullube jikina, ya shafa fuskata tare da faɗin "princess har kin tashi?" na buɗe idona a hankali na sauke su akan kyakkyawar fuskarsa, kai na gyada masa alamar eh. Ya janyoni jikinsa yana faɗin "time ɗin Sallah yayi, muje muyi alwala" bance komai ba, ban kuma yi yunkurin motsawa da niyyar tashi ba, sai kwanciya da nayi a jikinsa nayi lamo, ya d'ago fuskata fuskarsa na nuna damuwa yace "Princess me yake damunkine wai, ko jikinne?" na girgiza masa kai alamar a'a, ya taɓa wuyana yaji zafin jikina ya ragu sai gumi dake tsatstsafomun alamun zazzaɓin ya tafi. Bai ƙara cemun komai ba, ya ɗauke ni ya kaini toilet, shap_shap yamun wanka nayi brush, muka dauro alwala sannan muka fito. Yana ƙoƙarin fita yace "kiyi sauri ki shirya kije part d'in baƙi su uncle sun ƙaraso tun ɗazu, bai jira amsataba ya fice jin antada sallah a masallaci. Shiryawar na shiga yi cikin sauri kamar yadda yace, sai dai bansan Meyasa ba nakejin zuciyata na wani irin bugu tun ɗazu, yanzu kuma daya sanarmun da zuwansu uncle sai bugun zuciyar ya k'aru. Bayan na idar da Sallah na nufi part d'in baƙin, da sallama na shiga falon kyakkyawar matar dake zaune wadda bazata wuce shekara 38 ta amsamun tare da bina da kallo, na ƙarasa gabanta na durkusa har ƙasa na gaisheta domin nafahimci itace matar uncle, ta amsamun da fara'a a fuskarta ta ƙara da faɗin "kece sirikartamu kenan" nayi murmushi tare dayin ƙasa da kaina cikin jin kunya, Hajja ta fito daga d'akin da tayi Sallah Hanifa na biye da ita a baya, haka kawai Hajja taji gabanta yayanke ya fad'i, ummee ta dubeta tace "Hajja ga kishiyar taki fa, kyakkyawa da ita kamar mijinta" Hajja ta zauna akan kujera tana bin Maryam da kanta ke ƙasa da kallo tace "to sannunta, amma dai nasan duk kyanta na fita shiyasa ta kasa d'ago kai ta kalleni" nayi murmushi tare da tashi na nufi gurinta muna haɗa ido gabana ya faɗi sosai, _hasbunallu....._ na shiga karantawa a raina saboda faduwar gaban ta isheni, itama Hajja anata ɓangaren haka, kafe Maryam da ido tayi ko kiftawa babu, na daure duk da abunda nakeji a raina na gaisheta cikin girmamawa, tsohuwar mata ce amma hutu da jin daɗi ya boye tsufanta, tana kama da Ammi sosai, ta amsamun gaisuwata tare da cigaba da tsokanata. Haneefah ta matso jikina tana mun murmushi tare da mun magana cikin harshen larabci, na shafa kanta inajin wata kaunar yarinyar lokaci ɗaya ta shigemun zuciya, itama kuma lokacin dana kalleta sai da gabana ya faɗi, surutu take tamun, cikin abunda na fuskanta ta faɗamun sunanta Haneefah, tana da ɗan'uwa Haneef yabi Abbunsu masallaci, ummee tacemun nayiwa Haneefah turanci tana ji. Muna zaune muna shan hirarmu da Haneefah ammi ta dawo ɗakin, Hajja da Ummee kuwa kallonmu kawai suke kamar sun samu TV, Ammi ma data shigo sai da ta kalli Maryam ta kalli Haneefah, ta ƙara kallousu, tayi haka ya kai sau uku, sannan ta sauke numfashi ta amsa sannu da zuwan da Maryam ta mata, tare da tambayarta ya jiki, dan Dr husnah, ta biya sun gaisa ɗazu tace Maryam tazo dubawa. Haneef na gaba Abbu na binshi a baya suka shigo falon, Hannef ganin yar'uwarsa gurin Maryam shima ya nufi gurinta ya zauna a jikinta yana gaisheta, amsawar da Maryam tayi yasa Abbu wata irin juyowa yana kallon Maryam a wani irin yanayi na rud'ewa, dan jin Muryar da tayi kama data wadda bazai taɓa iya mantawa da ita ba a rayuwarsa, a hankali na d'ago kaina jin wanin yanayi na baƙuntar zuciya da gangar jikina, na kalli mutumin da Haneefah take nunanmu tana faɗin "ga Abbunta ya dawo" cikin harshen turanci, wani abu da bansan ya zan misalta muku shiba ya ziyarci zuciya, kasa gaisheshi nayi Saboda wani nauyi da harshe na yamun, Abbu dayake ganin tamkar Maryam ɗin shi daya bari tsawon shekaru masu yawa yace "Maryam!" cikin ƙaraji, Ammi ta dubeshi da tsantsar mamaki tace "kasanta ne ɗan'uwa?" Bai iya bata amsa ba sai jikinshi daya ɗauki wani irin rawa nuna Maryam yake da hannunshi amma ya kasa magana, ƙasa yayi luuu zai fadi Mustapha da shigowarsa kenan ya tafi da sauri ya riƙeshi, zaunar dashi yayi akan kujera gabad'aya su Ammi suka yo kansa suna masa sannu cikin tsananin al'ajabin abinda yasashi a cikin wannan hali lokaci ɗaya. Hajja ta dafa kafadarsa cikin yarensu na buzaye a ɗan ruɗe take faɗin "Muhammad meyafaru?" Abbu ya sauke wani gwauron Numfashi yana fitar da numfashi da k'yar yace "Hajja gamo nayi, naga wata kamar matata Maryam danake baku labarinta kuma tayi magana har muryarsu iri ɗaya" Ammi ta juya da sauri jin abinda yace ta kalli Maryam data kasa koda motsi, idanunta a lumshe hannunta dafe da kanta, Ummee ta mik'o masa ruwa mai sanyi wanda ta tsiyayo masa a cikin wanda ammi ta kawo musu, ya karba yayi bismillah ya fara sha, ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama shan ruwan ya dafe kansa daya fara sara masa. Mustapha kallonsa kawai yake bece komai ba zuciyarsa na bugawa shima, Ammi ta tattaro dauriyarta dan itama a ruɗe take tace "Muhammad ba gamo kayi ba, wadda kagani akwaita a zahiri kuma itace matar NOOR kuma itama sunanta Maryam, amma nasan ba ita bace wadda kake nufiba" Abbu ya mike da sauri yana faɗin "ina take?" Ammi ta nuna masa Maryam dake zaune kamar mutum mutumi, ƙarasawa yayi gurin Maryam da sauri ya rungumeta a jikinsa cikin tsananin zak'uwa yace "dan Allah wacece ke? ya akai kike tsananin kama da Maryam d'ita? dan Allah ki faɗamun ko kin santa ki kaini inda take dan Allah" Maryam tayi tsit tana jin wani irin abu na ratsa jikinta a sanadiyyar jinta a jikin Abbu, Abbu ya saki Maryam ya dubi Ammi a ruɗe yace "ƴar'uwa ki mata magana ta faɗamun dan Allah, inason ganin Maryam d'ita kullum da tunaninta nake kwana nake tashi a raina ita da cikina dana tafi na barshi a jikinta" Ammi ta kama hannunsa ta zaunar dashi cikin kwantar da murya tace "ka nutsu Muhammad ka mana bayanin waccen Maryam kake nufi" yace "Matata! Matatace, itace matata ta farko wadda mak'iya suka shiga tsakaninmu suka rabani da ita da garin Kanon gabad'aya shekara kusan 20 kenan yanzu" Ammi ta zauna dab'as a kusa dashi dan ita bata taɓa sanin da batun wata matarsa Maryam ba, Hajja ta zauna a ɗaya gefennashi tana faɗin "wai kana nufin matar Muhammad itace kagani kamar Maryam ɗin da kake bamu labarinta?" Ya gyad'awa Hajja kai idanunsa a kan Maryam, da kanta ke ƙasa har lokacin, Mustapha ma kallonta kawai yake. Ummee ta ƙarasa ta zauna a kusa da Maryam ta rungumeta a jikinta tana addu'ar fatanta ya zama gaskiya akan Maryam, ko dan ta samu nutsuwar mijinta da kwanciyar hankalinsa gami da farincikinsa ya dawo, dan yasha faɗa mata bazai taɓa samun hakan ba, harsai yaga Maryam d'insa ya nemi yafiyarta akan tafiya da yayi ya barta. Ammi ta dubi Hajja so surprise tace "kema kinsan Maryam ɗin dayake magana akanta ne?" Hajja tace "eh matarsa ce daya aura a Kano tun bayan barowarsa daga nijer" ammi tace "to me ya rabasu, kuma a yanda na fuskanta tunda ya barta bai waiwayetaba" Hajja tace "shi zaki yiwa wannan tambayar" Ammi ta maida dubanta ga Abbu tace "Please Muhammad ka fitar dani daga cikin duhu, I want know alot about what you said" Abbu yaja wani gwauran numfashi yace "labari ne mai tsayi ya Maryam, amma zanyi ƙoƙari na tak'aita miki, amma kafinnan inason nasan wacece ita wannan Maryam ɗin" Ammi tace "forget about this bro, ka fara bamu labarin taka Maryam ɗin, zakasan ko ita wace daga baya" ganin yanda Ammi ta damu Abbu basan ransa ya fara basu labarin kamar haka.