Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 1
Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 1: Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 1. ƘADDARAR RAMLAH
4,452 words
ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ƊAYA
Tsaye nake a farfajiyar gidan mu, littafi a hannuna, ina kokarin kammala wani assignment kamar yadda na saba. Har na fara jin bacci yana mamaye ni, sai naji murya daga cikin kicin.
"Wai Ramlah! Aikin naki ne har yanzu ba zaki zo ki karasa mana abincin ba? Kinsan Baba Zuwaira batanan fa!"
Cikin ɓacin rai na lumshe idona, na rufe littafina ina turo baki waje.
"Mumy wallahi nagaji da kama mata aiki. Ki samo wata yar aikin mana." Na fada cikin raina, abace.
Tana jiyo shigowata sai kawai tayi dariya, tana fadin,
"Allah ya shiryamin ke yanzu Ramlah. Zo kishige, abbanku zai shigo yanzu. Kuma kin san kamain yayanki su dawo su damemu da tambayoyi. Ina abincin?"
Na kame kaina. Na san dai wannan itace rayuwata. Amma yau ita ce kishiyar mahaifiyata da na koma ƙarƙashinta... Kuma komai take so, to dole ne in bi.
A wannan lokacin ban san cewa wannan karamin gajiya da kuka nake yi yau, shine mafari na babban juyin rayuwa da zai sauya duk wata mafarkina ba.
A dakin girki na shige ina jan hijab dina, na tashi girki kamar wacce ta saba da wannan rayuwar tun daga haihuwa.
"Ramlah ki wanke kayan kubewa nan, sannan ki niƙa tumatir din. Idan kika gama ki daka garin yaji, amma ki tsame rabin, kin san Abban ku baya cin mai yaji sosai,"
Wannan kalaman nata sun fi sau goma a kullum, haka kuma yadda take kokarin nuna kamar kulawa take yi, alhali dai ni na fi kowa sanin cewa ina da matsayi na daban a zuciyarta.
Ban gama daka garin ba sai naji sallamar Abba, wato mahaifina. Da sauri ta fito daga kicin tana dariya,
"To Alhaji, sannu da zuwa! Yauwa gwara ka iso da wuri, dama muna shirin kammala abinci." "Sannu da zauwa abba." Kallona yayi yana dan nazari sai naji yace " Allah yayi Albarka Ramlatu."
Ina jin umma tana amsawa. Na juya daga mashin na daka yajin, na cigaba da aikina.
"Wai Ramlah, ba zaki yi sauri ba?!"
Muryarta ta cika gidan gaba ɗaya. "Ni wallahi idan nasakaki aiki kamar ina miki dole, narasa dalilin da yasa ki ke ta bata rai! Ranar da babu raina zaki tabbatar gata nake miki!"
Kaina na sunkuyar, jikina yana rawa. Ina jin har kalmarta ta sare zuciyata, amma ban iya ce mata komai ba.
Sai jin muryar Abba nayi, ya shigo cikin ɗakin girki da sauri kamar wanda ya jima da sauraron rikici.
"Me kuma ke faruwa ne?! Wai Ramlatu har yanzu kina ta nuna rashin jin daɗi akan ayyukan gidan? Nasan tayi hakan ne dan Abba yaji!"
Yana ɗaga murya sosai, fuskar sa cike da ɓacin rai.
"Aikuwa sai na ɗauki mataki. Yarinya shekara goma sha biyar idan ba ta iya girki ba, me zatayi? Duk irin yadda Zainab ke sangarta ki, amma ke kullum sai kin nuna mata kamar ba diyarta kike ba. Wallahi banason haka Ramlatu, zamusa kafar wando ɗaya dake."
Cikin rawar murya da kuka nace,
"Abba kayi hakuri... Mumy kema kiyi hakuri... bari na karasa."
Abba yana tsaye yana cigaba da yi min faɗa, kamar zan zubar masa da mutunci a ido. Kowane kalma nashi kamar ƙaya ce a kunnena, zuciyata kuwa kamar ana murƙushe ta da hannu.
Cikin gaggawa Mumy ta katse shi, tana cewa da ƙarfi
"Haba Abban Ramlah! Ka daina yi mata faɗa haka. Wallahi Ramlah diyata ce kuma ba ta taɓa nuna min bambanci ba. Yarinyace fa! Waye bai yi kuskure a ƙuruciya ba?"
Tana karasawa da hawaye a idonta, sai ta juya gareni.
"Allah ya shirya min ke Ramlah... Allah ya sa ki yi albarka. Amma meye na kuka ke kuma?"
Na saki hawayena a hankali, ban iya ce mata komai ba. Kalmar "diyata ce" kawai ke yawo a kunne na kamar mafarki, kamar ƙarya.
Sai Abba ya ja wani mugun tsaki ya ce,
"Dama ai ke kike sangarta. To ku cigaba. Kuyi dai tayi. Ku kawo min abinci kawai, ni zan sake fita."
A gaggauce na kammala duk aikace-aikacen gidan na jera abinci a dining kamar yadda aka saba, na share ƙasa, na yi wanke-wanke. Jikina duk ya gaji. Test ce dani gobe a makaranta, amma karatu ya zama abu na ƙarshe a raina yau.
Ina kwance a ɗakina, lokacin ya kusa ƙarfe goma na dare. Na jingina da gado, ina shirin rufe idona sai na ji ƙofar ɗakin ta ɗan buɗe.
Mumy ce. Ta shigo da fara'a a fuska tana cewa
"Ramlah, ba zaki je kici abinci ba? Yanzu Ramlah, damuwa kike son saka min ne? Ba kya so na ji daɗi kuwa?"
Ta karaso kusa da ni tana bubbuga cinyata cikin tausayi.
"Haba diyata, ai aikin ya ƙare. Gobe Babah zai dawo, kuma kinsan yadda nake son komai ya kasance lafiya. Taso yar albarka, mu ci abinci."
Cikin shiru na dago idona, zuciyata na yi min yawo. Idan ta nuna ƙauna irin wannan, sai in manta cewa ita ce take kallona kamar ba kowa ba da safe. Sai in ce "ko da gaske take?" ko kuma "haka kawai take so in ji daɗi yanzu ne?"
Kafin in ce komai, sai na ji muryar Abba daga tsakar gida
"Takawo min ruwa! Ina jin kishirwa."
Na fito falon gidanmu cikin gajiya, na zuba abinci akan tebur. Ina cikin aikin naji muryar Abba da Mumy daga ɗaki suna hira akan dawowar Yaya Billy. Ita ce babbar yayata kuma ni ce auta a gidanmu. Mu huɗu ne yaran gidan:
Yaya Abbas shine babba. Yana da shekara talatin da biyar (35). Shi yana da aure da yara biyu, yana zaune lafiya da iyalinsa.
Sai Yaya Usman, wanda bai daɗe da yin aure ba. Shekararsa talatin (30). Shi kuma yana sona sosai, har nakan ji kamar ciki ɗaya muka fito dashi saboda yadda yake kula da ni.
Sai Yaya Billy, wacce suke magana kanta yanzu. Ita tana da shekara ashirin (20). Tana karatu ne a Abuja a gidan abokin mahaifina, wanda ake kira As'ad. Wannan As'ad babban mutum ne kuma ɗan gidan Sarki ne, saboda haka kowa yana girmama shi sosai.
Ni kuma ni ce ƙaramar gidan. Ni kaɗai mahaifiyata ta haifa, kuma ta rasu tun ina shekara biyu da haihuwa. Na taso a hannun Mumy, wacce take rike ni tamkar ita ce ta haifeni. Duk da cewa tana sakani aiki sosai wani lokacin har da fada, amma gaskiya tana sona kamar yar da ta haifa.
Sai dai Yaya Billy akwai matsala da ita. Tana sona, amma tana da girman kai sosai, kuma tana da rashin haƙuri. Wani lokaci idan na yi mata wani abu sai ta nuna fushinta. Gaskiya tana bani haushi sosai, amma ba zan iya faɗa mata ba saboda girma da take min.
Mahaifinmu kuma mutum ne mai tsauri da ƙa'idoji. Shi baya son wasa a cikin gidan, saboda haka kowa yana bin dokokinsa. Wannan ne yasa muka tashi cikin nutsuwa da hankali.
A haka rayuwata take tafiya, amma duk wahalar da nake sha, ina godewa Allah domin ban rasa gata ba.
Ina zaune a gefen kujera har yanzu, gajiya ta lullube ni amma ban da niyyar kwanciya ba. Sai na ji Mumy ta ce da fara'a,
"Ramlah, tashi ki je ki kwanta mana."
Abba yana kallona daga gefe ya karɓa,
"Haka ne, tashi ki huta."
Sai na zaro ido kadan nace,
"Abba, ai banason kwanciya yanzu saboda ban daɗe da cin abinci ba."
Mumy ta dariya tace,
"Sannu uwar mata! Idan kina magana sai a rantse babbar mace ce. Abban Ramlah, ka daina bamu dariya fa. Kada muyi tumbi ko auta."
Sai muka fashe da dariya gaba ɗaya. Cikin shagwaɓa nace,
"Mumyta, Allah ya ƙara miki lafiya. Abba, good night."
Na mike na shige ɗaki da murmushi.
Ina shirin rufe ƙofa sai na jiyo Abba yana cewa da Mumy
"To ai dole tayi iyayi, rainon Zainab ce fa... uwar magana."
Mumy ta daga hijab dinta tana bin shi da dariya,
"Au! Sharri zaka min kenan, Abban Ramlah? To bari in biyo ka zuwa sama!"
Washegari tun da na idar da sallar asuba, na kama aikin gida kamar yadda na saba. Daman doya da kwai nayi niyya a yi, don haka na fara da gyara gidan, sannan na dafa tea cikin sauri. Na diba nawa na kai dining, sannan na dafa koko saboda nasan Abba ya fi son koko fiye da shayi.
Kuna ganina kamar ƙarama, ko? Abba kullum yana cewa shekaruna ba su fi goma sha biyar ba, amma ni yanzu Allah ya kai ni 16 years. Kuma gaskiya, duk aikin gidan nan babu wanda ban iya ba - daga girki, tsafta, har ma da kula da kowa.
A haka ma ina SS2 yanzu a makaranta. Mumy kuwa, gimbiya ce ta gaske. Wayayyiyar mace ce wadda idan kana tare da ita, sai ka rinka dariya da mamaki. Wayo da iya magana? Ai daga gareta na koya. Ni da Anty Billy, wallahi ba za a iya kayar damu da magana ba.
Da na ga karfe 7 na kusa, sai na kunna turaren wuta a gidan domin kamshi. Na huce da wanka, na fito na shirya cikin uniform dina.
Ni ba fara bace sosai ba, amma fatar jikina na da haske. Ina da kyau irin wanda ba sai a ƙyale ba. Ina da hanci mai kyau, idanuwa da kyau, ga baki ƙarami, mashaa Allah. Jikina kuwa? Ai ko bra bana sawa. Tunda Yaya Billy ta fara siyamun kayayyakin da masu tsada ke amfani da su, jikina ya canza - ya yi kyau, ya yi laushi, ya kara "fresh".
Na shirya lunch box dina, na haɗa komai, sai na haura sama inda na tarar da Abba yana lazumi kamar kullum. Mumy kuwa, ai bata tashi da wuri - sai 9.
Na gaishe shi, ya amsa da fara'a. Ya bani 500, sannan ya dubeni da murmushi yace:
"Ramlah, ki rike mutuncinki. Ki yi karatu sosai. Ki zamo mace mai daraja."
Ina fita harabar gidanmu da jakata a hannu, sai na tarar da Malam Idi, direban gidanmu, yana gyara motar. Na gaishe shi cikin fara'a:
"Ina kwana Malam Idi."
Yace, "Lafiya lau Ramlah. Ya gida?"
"Alhamdulillah," nace, "don Allah ka wuce da ni gidan Babah kafin makaranta."
Yace, "Ba damuwa," sai muka tafi cikin sauƙi.
Cikin kankanin lokaci muka isa. Da na sauka, sai na hanzarta shiga gidan. Babah, matar da ke aiki a gidanmu da daddare, tana zaune akan tabarma. Na gaisheta cikin nutsuwa:
"Babah, lafiya kuwa? Me yasa baki dawo aiki ba ne?"
Sai ta dubeni da hankali tace,
"Ai Mumy ce tace na huta, tunda ga Ramlah a gida zata rinka taimakawa."
Na yi shiru. Ban ce komai ba.
"Mumy ce tace haka?" Sai na sake tambaya a raina. Na tuna yadda jiya da dare ta ce min "ki je ki kwanta, kin gaji," amma yau ga Babah a gida tana hutu ni kuma zan rika ɗaukar nauyin komai.
Babah tayi murmushi, irin nasu na manya, ta ce:
"Eh to hakanne, ai yanzu kin girma."
Na danyi murmushi shima, amma zuciyata cike take da tambayoyi da ban da amsarsu.
"Me Mumy take nufi da haka? Me yasa komai sai ni?"
Ban jima ba, sai muka yi sallama. Na koma mota muka wuce makaranta. A cikin motar nayi shiru. Zuciyata cike da kokonto. Ban gane kan Mumy ba, wallahi.
Wasu lokuta tana nuna ƙauna kamar uwa, wasu lokuta kuma kamar ba ta so na huta ko na numfasa.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA BIYU
Yau kam wallahi na gaji sosai a makaranta. Test ɗin da muka yi ban tsammanin zan ci ko rabi, domin kuwa ko kaɗan ban samu na yi karatun ba saboda ayyukan gida da suka jibge min jiya. Makarantar da nake zuwa ba ƙarama ba ce, makaranta ce ta 'ya ƴan masu kuɗi da yara masu ji da ji da kansu da fahimtar zamani. A cikin ajinmu ma, zan iya ce muku ni kaɗai ce mai sauƙin kai da rashin damuwa.
Yanzu haka ma ina tsaye a gefen kujerun da muke zama bayan an tashi daga makaranta, ina jiran Malam Idi, direban gidanmu, ya zo ya ɗauke ni. Kawayena suna gefe suna hira suna dariya, ɗaya daga cikinsu mai suna Fatima ta matso kusa da ni tana bani labarin saurayinta. Ban ce mata komai ba, na dai yi murmushi kawai ina jin mamakin yadda ita Fatima ke ta ɓata bakinta a banza akan saurayi tun yanzu.
Can sai ga Malam Idi ya iso cikin harabar makarantar, ya shigo ciki yana faɗin,
"Auta, nazo fa, muje gida."
Sai na yi sallama da su Fatima na shiga mota, muka kama hanyar gida. Yayin da muka hau hanya ne tunanina ya tafi wajen kakata, mahaifiyar mahaifiyata.
Da can idan aka tashi daga makaranta kakata tana zuwa ta ganni, amma yanzu bata zuwa. Shin, na ba ku labari kuwa? To, bari ku ji.
Tun bayan haihuwata, kakata ta roƙi mahaifina ya bata ni ta raineni a wurinta, amma sam-sam ya ƙi. Ya ce bazai iya rabuwa da ni ba. Wannan batu har ya jawo rigima mai zafi tsakanin kakata da Mumy. Mumy dai ta tsaya kai da fata cewa ni diyarta ce ita zata riƙe ni. Abba kuwa ya ce idan kakata tana son ganin jikarta, to a kawo ni wajenta, amma ba za ta zo gidanmu ba. Wannan abu ya taɓa zuciyar kakata sosai.
Amma saboda ni kaɗai ce jikarta daga mahaifiyata, sai ya sanya ta yi ƙoƙarin bibiyar karatuna da rayuwata ta kowace hanya. Tun ina jin kunyarta har muka zama aminai. Yanzu ina matuƙar ƙaunar kakata, kuma duk lokacin da na tuna wannan lamarin, sai na ji zuciyata ta yi rauni.
Mun kusa isa gida, zuciyata cike da tunani daban-daban. Wannan rayuwa dai, duk yadda mutum ya so ta, ba dole ne ta so shi ba.
Muna karasowa gida, na sauka daga mota, sannan na yi wa Malam Idi godiya tare da yi masa sallama cikin girmamawa.
Ina shiga babbar harabar gidanmu, na tsaya na kalli kicin ɗinmu. Abin takaici sai na ga duk an yi kaca-kaca da shi. Kawai sai na ji zuciyata ta baɗe. Na tuna dai da safe na bar ko'ina tsaf, amma yanzu kamar ba gidan da na bar ba ne. Sai kuma na juya na duba falonmu, nan ma abin sai dai ku gani da idanunku, kamar an yi fadan duniya. Wannan ba aikin wani bane sai aikin Mumy, gimbiyar Abba. Ai dama gimbiyoyi ba sa aikin wahala!
Wannan gimbiya ta gidanmu kuwa akwai mulki da izzah. In dai ba don Abba ba ya cin abincin 'yan aiki ba, da sai dai a ɗauko mata masu aiki su yi mana girki. Amma duk wannan mulki da izzar tata, ita ce kawai take girkin Abba, kuma bata barin kowa ya yi masa abinci.
Mumy kyakkyawar mace ce, mai kyau sosai, gata fara tas! Allah ya albarkace ta da cikar jiki da kyan fuska. Amma fa, bata da wani tsayi sosai. Wani lokacin ma idan tana magana, sai na ji kamar muryarta ce kawai ke isa mutum, saboda tsarinta da iya zance. Abin burgewa da shi a wurinta shi ne, ban taɓa ganin tayi faɗa da Abba ba, ko da kuwa shi ne yayi mata laifi. Idan ma faɗa take mana , to tana hadawa addu'a , musamman ni. Wani lokaci idan ba ka san halinta ba, sai ka ɗauka cewa matan Aljannah ce gaba ɗaya!
Amma bari dai na yi shiru kawai, domin idan kuka ga abin da na gani yanzu, sai kun tausayamun. Yanzu da na shiga cikin kicin ɗin nan, wallahi babu wani abincin da aka shirya. Da alama dama tana jira ne har na dawo daga makaranta sai na zo na yi girki!
Sai na girgiza kai kawai, na buɗe fridge, na ɗauko fura da nonon da na dama tun jiya, na ɗauki biscuits, na saka a cikin jakata a hankali, don kada Mumy ta ji motsina.
Sannan na shiga ɗakina na shirya cikin kayana na islamiya. Na san tana can sama kwance, tana ta juye-juye da dannawa waya kawai. Dama ta kore mai aikinta, wai yanzu Na isa aiki!
Ina fitowa da jakar islamiya ta, lokacin har ƙarfe biyu saura kaɗan. Na yi sallar azahar, sannan na ce da Malam Idi
"Mu je kawai malam Idi, makaranta zamu koma."
Na san dai cewa idan na dawo gida daga makarantar islamiya, dole akwai wani sabon shirin Mumy yana jira na. Amma dai yanzu bari in yi tafiya ta. Na dai san tabbas, Amma yanzu dai na fita da dariya kawai muka wuce makaranta.
Tun lokacin da Mumy ta sauko ƙasa wajen ƙarfe huɗu na yamma take ta kwalamin kira, har ta gaji. Ta yi tunanin ko na dawo daga islamiya, ina ɗakina ina hutu, ko kuma na ɓoye ne saboda aiki ya ishe ni. Ta jira na yi mata sannu da gida kamar yadda na saba, amma shiru kake ji, babu amo babu labari.
Ganin ban fito ba ne yasa ta tashi cikin ɗan hanzari ta shiga ɗakina don ta duba. Sai dai tana shiga taga ɗakin babu kowa, wayam! Nan take zuciyarta ta ɗan tsinke, hankalinta ya tashi kaɗan, domin ko kadan bata saba ganina bana nan ba lokacin da take bukata ta.
Da sauri ta ɗauki wayarta, ta kira Malam Idi direba.
"Malam Idi, ina Ramlah take? Ko akwai inda kuka tsaya ne bayan kun dawo daga makaranta?" Ta tambaye shi cikin ɗan ɓacin rai.
"A'a Hajiya, ai Ramlah tana islamiya yanzu. Tun ƙarfe biyu na kai ta makarantar islamiya," Malam Idi ya amsa mata cikin girmamawa.
Mumy ta ji zuciyarta ta tashi, har tana shirin yi masa faɗa akan me zai kai ni makaranta ba tare da ta sani ba. Amma sai ta danne zuciyarta, ta ja numfashi cikin natsuwa tace
"Allah ya tsare min ita, Malam Idi. Ya dawo min da ita lafiya."
Malam Idi ya amsa mata da amin, ta kashe wayar, zuciyarta cike da takaici. A zuciyarta tace, "Yau kam Ramlah kin wuce gona da iri. Dole akwai maganar da zan yi dake idan kin dawo."
Ta dube agogo, sai ta ji yunwa tana neman cin cikinta. Ga kuma takaicin babu abinci a gida. Dole ta mike cikin nutsuwa ta shiga kicin da kanta, ta ɗora ruwa akan gas cikin fushi amma babu yadda za tayi. Duk tana masifa a zuciyarta amma tana ƙara tabbatar wa kanta cewa ni kaɗai ne 'yar aikinta da babu na biyu.
Cikin lokaci kaɗan ta gama girkin jallof din shinkafa mai daɗi, ta haɗa shi da coslaw mai kyau. Ta zuba cikin flask ɗin abinci ta shirya akan dining, dai-dai adadin mutanen gidan. Bayan ta gama komai, ta yi sama kawai cikin yanayi na sarauta irin nata, zuciyarta kuma tana cike da tunanin yadda zata nuna min cewa tayi fushi da abinda na yi.
Ni dai a wannan lokacin, ina can ina koyon karatu a makarantar islamiya, ban san abin da ke jirana ba a gida.
Ƙarfe biyar na yamma daidai, Abba ya shigo gida yana cike da gajiya bayan dawowa daga wurin aikinsa. Bai ƙarasa shiga cikin falon gidan ba, ya tsaya daga bakin ƙofa yana kallon ko'ina da mamaki. Gidan nan fa kamar ba gidanmu ba, ko'ina kaca-kaca! Kicin, falo, komai ya hargitse babu alamun cewa akwai wani mai aikin tsafta a nan gidan.
"Subhanallah! Me yake faruwa a gidan nan yau ne? Ina mutanen gidan suke haka?" Abba ya tambaya cikin ɗaga murya, fuskarsa cike da ɓacin rai.
Mumy ta ji muryarsa daga sama, sai ta fito a hankali tana ɗan dafe kanta kamar mai ciwon gaske.
"Abban Ramlah, sannu da zuwa," tace cikin murya ƙasa-ƙasa kamar ba ta da lafiya.
"Meke faruwa ne a gidan nan Zainab? Ina Ramlah take da gidan nan yake haka?" Abba ya tambayeta da damuwa.
"Ai wallahi Abban Ramlah, ni kaina ciwo yake min sosai tun safe. Ga shi kuma Ramlah tace min ita fa ta gaji da aikin gidan nan, bazata iya ba. Shine fa gidan nan ya zama haka. Ni kuma ka ga ban da lafiya sosai," Mumy ta faɗi hakan da muryar tausayi, tana nuna kamar tana kare ni.
Abba ya fusata sosai jin wannan magana. "Ramlah tace maka ta gaji da aiki? Wannan wani irin shiririta ne haka? Yarinya ƙarama da ba ta da wani aiki sai karatu da kula da gida, amma yanzu zata ce ta gaji? Ai wallahi ba zan ɗauki wannan halin ba!"
Mumy ta matso kusa da shi da sauri, cikin hikimar kissa tace masa:
"Abban Ramlah, ka yi hakuri da ita, yarinya ce fa. Ko da yake ni ban ji daɗin maganarta ba, amma kasan dole mu riƙa yi mata haƙuri. Amma da ka bari idan ta dawo sai ka yi mata nasiha a hankali, kada zuciyarka ta ɓaci sosai, ni kaina na san ba halinta ba ne."
Abba ya ja tsaki yana girgiza kai cikin takaici, zuciyarsa cike da ɓacin rai. "Zan nuna mata wannan halin ba zai yiwu ba a gidana. Ina ƙoƙarin ganin komai yana tafiya daidai, amma ita kuma sai ta ce ba zata iya aikin ba. Wani irin abu ne wannan?"
Mumy tana tsaye tana murmushi a zuciyarta, ta san cewa wannan labarin da ta kirkira zai ɗora min aiki da yawa da kuma faɗa. Amma daga waje ta cigaba da nuna kamar tana tausaya mini tana kare min martaba.
Ni kuwa ina can a makaranta ban san cewa akwai wani babban matsala da ke jirana a gida ba.
Na dawo daga makaranta cike da farin ciki, babu abin da ke raina sai in je gida in huta. Ban san cewa wani babban abin mamaki ne yake jirana ba a gidan yau.
Ina shigowa cikin gidan na tarar da Abba tsaye a falon gidanmu, fuskar nan tasa babu walwala ko kaɗan. Nan take gabana ya faɗi, zuciyata kuma ta fara bugawa da sauri.
"Sannu da gida Abba," na faɗa cikin sanyin murya, amma kafin in gama gaisuwar ya ɗaga min hannu cikin ɓacin rai ya ce,
"Ramlah, wannan wani irin halin banza kika ɗauko ne wai? Yaushe kika girma har zaki ce kin gaji da aikin gida? Shi aikin gidan nan wani nauyi ne a gare ki har ba zaki iya ba?"
Na ji numfashina ya ɗauke, kalmomin nan sun shige ni sosai. Na dubi gefena sai na ga Mumy tsaye tana nuna kamar tana tausayina, har tana riƙe da kafadata.
"Abban Ramlah, ka yi hakuri mana, yarinyar nan fa ƙarama ce. Ba zata iya komai ita kaɗai ba," Mumy tace cikin murya mai sanyi kamar mai tausayawa.
"Ban yarda ba! Ai wannan raini ne da rashin tarbiyya. Wani aikin ne ma Ramlah take da shi sai karatu da aikin gidan nan? To, wallahi ki gyara halinki. Ba zan lamunci wannan halin ba a cikin gidana!" Abba ya sake faɗa cikin muryar faɗa.
Hawaye suka fara zubowa daga idona, na kasa magana. Ina ji a raina cewa Mumy ce ta tsara wannan ƙarya domin ta ɗora min aiki da yawa.
A wannan lokacin ne sai ga babban yayana, Abbas ya shigo gidan yana sallama.
"Assalamu alaikum! Me ke faruwa ne, Abba?" Abbas ya tambaya cikin damuwa ganin yadda Abba ya fusata, ni kuma ina kuka.
"Abbas, duba wannan yarinyar taka! Wai tace ta gaji da aikin gida, ba zata iya ba," Abba ya sake maimaita maganar cikin ɓacin rai.
Abbas ya matso kusa da ni cikin tausayawa, ya ɗaura hannunsa akan kafadata yana cewa,
"Abba ka yi hakuri. Ai Ramlah ƙarama ce sosai, wannan aikin gidan gaskiya yayi mata yawa. Mumy, ki nema mata wata mai aiki mana, ina auta ina wannan aikin mai yawa haka?"
Nan take Mumy ta girgiza kai cikin ƙissa tace,
"Ai wallahi Abbas na bada cigiyar mai aiki sosai, amma har yanzu ba a samu ba. Kuma Baba Zuwaira ba ta da lafiya ne shiyasa ta daina zuwa yanzu."
Abbas ya dubi Abba cikin nutsuwa yace,
"Abba ka yi hakuri da ita. Ka daina yi mata faɗa haka. Ni da kaina zan taimaka a nema wata mai aiki daga yanzu. Ki yi hakuri Ramlah, kin ji?"
Ya ɗan bubbuga kafadata cikin rarrashi, nan take naji zuciyata ta ɗan yi sanyi kaɗan. Na ji kamar na samu wanda zai kare ni a wannan lokacin da babu mai jin ƙorafina.
Na share hawayena a hankali, ina godewa Allah da ya bani yaya mai tausayi kamar Abbas.
Ina tsaye, hawaye na bin fuskata a hankali, zuciyata cike da baƙin ciki da takaici. Sai kawai naji Abba ya yi min wata irin tsawa mai tsoratarwa da girgiza zuciyata.
"Ke Ramlah! Ki hanzarta ki cire uniform ɗinki yanzu ki gyara gidan nan tass! Idan da mahaifiyarki ce da rai ai nasan ba za ta taɓa barin gidanta haka ba!"
Wannan kalma ta shiga cikin zuciyata har ta ƙona ni. Numfashina ya ɗauke na tsaya cak kamar an dasa ni a wurin. Amma kafin in ce komai, Yaya Abbas ya yi sauri ya tare shi yana cewa,
"Haba Abba! Wannan magana tayi tsauri. Ka yi mata faɗa, amma ba haka ba."
Mumy ta yi saurin katse zancen da ta ga yana neman rikicewa tace,
"Tsakani da Allah, Abban Ramlah, menene ma dalilin wannan magana? Ai Ramlah cikakkiyar 'yata ce. Kowa ya san haka, kuma tana ƙoƙarin iyawarta."
Ni dai ban iya cewa komai ba. Cikin sanyin jiki na juya na fita zuwa ɗakina, na cire uniform ɗina na sanya wata tsohuwar riga. Sai na ɗauki bokiti da abin goge-goge na fara aikin share gidan.
Wallahi idan kuka ga yadda kicin ɗinmu ya koma sai kun tausayamin. Amma haka na dage ina sharewa, ina wankewa, har na tabbatar ko'ina yayi fes kamar yadda nake so kullum. Na yi wannan aikin cikin gajiya da damuwa.
Ina gamawa wata irin yunwa ce ta bugi cikina. Na nufi wajen dining, amma da na isa sai na tarar babu abinci kwata-kwata. Nan da nan zuciyata ta sake cika da takaici. Na koma sama wajen Mumy domin na yi mata sannu da hutawa.
"Mumy, sannu da hutawa. Don Allah ina abincina?" Na tambayeta cikin sanyin murya.
Tace min, "Ban duba dining ba ne? Ai na aje abincin can."
Na ce mata, "Babu komai a dining, Mumy."
Sai tayi murmushi kadan tace, "Oh, Abbas kenan! Ashe ya kwashe duk abincin nan, ban sani ba wallahi."
A cikin ranta kuwa daman ta san cewa babu abin da ta bar min, kuma ta riga ta yanke shawarar cewa ba zan ci ba.
Sai kawai ta sake ce min, "Amma bari na dafa miki indomie ko taliyar da kike so."
Abba wanda ke gefe yana sauraronmu, sai ya dubi Mumy da faɗa yace, "Ita ba za ta dafa ba sai ke uwarta?
Ina jin wannan kalma daga bakin Abba, zuciyata ta ƙara cika da baƙin ciki. Na koma kicin a hankali, amma da na shiga ciki sai kawai na fashe da kuka mai tsanani. Kuka na takaici, kuka na rashin uwa, kuka na rashin gata.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA UKU