Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 11

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 11

Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 11: Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 11. Ya matso kusa da ita cikin salo, yana cewa da murya mai laushi

4,472 words

Ya matso kusa da ita cikin salo, yana cewa da murya mai laushi

"Haneefah, nadanyi bacci ne Ki yi hakuri."

Ta ɗan yamutsa fuska tana tsaki a hankali, tana cewa

"Ni kam ba matsala, ai dama haka kake. Kaga yadda ka barni Ni ɗaya Tun safe?"

Ya ja numfashi cikin sanyi, sannan ya durƙusa a gabanta, ya ɗauki hannunta cikin natsuwa.

"Ki yi hakuri. Ban yi nufin takura ki ba. Ki gafarce ni."

Tana jin murya mai laushi daga bakinsa, sai tsananin so ya mamaye zuciyarta. Ta ɗan yi murmushi, ta ce

"Yanzu na yafe maka, amma fa ka yi min alkawari cewa ba za ka sake ba."

As'ad ya kalle ta, yana ganin yadda kyanta ke ƙara bayyana a ƙarƙashin hasken fitila. Bai jira amsar ta ba, ya matso kusa da ita, yana kamo hannunta da salo, ya ja ta ta zauna a kan cinyarsa.

Ta ɗan yi dariya mai laushi, tana ƙara matse jikinta a jikin sa. As'ad ya rungume ta, yana jin yadda numfashinta ke tsananta. Haneefah ta sa hannunta a wuyansa, tana zagaye masa gashinsa cikin natsuwa.

Ya dube ta da ido mai cike da soyayya, yana cewa da murya mai laushi

"Kin san kina da kyau, ko?"

Ta lumshe idanu, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa. Ta matsa da fuskarta kusa da shi, tana jin kamshin turaren sa yana narkar da zuciyarta. Hannunta ya gangaro zuwa ƙirjinsa, tana shafar jikinsa da laushi, tana jin yadda sanyin fatar sa ke tsuma zuciyarta.

A hankali ya sa hannu a cikin gashinta mai laushi, yana ɗan ja da salo, sannan ya sumbaci goshinta cikin tsananin nutsuwa. Tana jin yadda hakan ya shiga jikinta, ta rungume shi sosai, tana jin tamkar ta narkar da kanta cikin jikin sa.

Ya ɗaga fuskarta da hannu biyu, yana kallon idanunta masu kyalli, sannan ya ce cikin murmushi

"Kin san ke ce farin cikina? Babu wata mace da zata iya shiga tsakanina da ke."

Ta yi murmushi mai cike da jin dadi, tana lumshe idanu, sannan ta kai bakinta zuwa nasa, suna jin yadda zuciyoyinsu ke bugu da sauri.

Ya sauke numfashi mai nauyi, yana jin wani irin farin ciki na musamman ya lullube shi.

"Ni fa, Haneefah, ban taba jin irin wannan soyayya ba. Kina da wani irin salo da ke sa na kasa jurewa," ya furta da gaske.

Hankalin As'ad gaba daya ya fita daga hayyacinsa, yana jin yadda Haneefah ke sarrafa shi da salo mai dadi da soyayya.

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA ASHIRIN DA BIYU.

Arewabook @nanadiso10

Kusan mako biyu kenan babu wanda ke iya samun As'ad. Tun lokacin da ya koma Abuja tare da Haneefah, babu wani labari daga wurinsa. Abin mamaki shi ne, ko Mai Martaba Sarki ya kira wayarsa, ba ya amsawa. As'ad, wanda aka sani da biyayya da mutuntawa, yanzu tamkar ya bar duniya, ya koma bangaren Haneefah kacokan.

Hajja tana zaune cikin falonta mai yalwa, cikin damuwa da tunani. Ta kishinƙide cikin riga mai launin ruwan toka, tana fuskantar Abba, kanin As'ad, wanda ke tsaye a gefenta, cike da damuwa.

"Hajja, wallahi na kira shi sau da dama, amma ba ya ɗauka. Har P.A dinsa ma na kira, ya ce yanzu As'ad ba ya sauraron kiran kowa sai dai abinda Madam Haneefah ta fada."

Hajja ta sauke numfashi mai nauyi, tana jin yadda zuciyarta ke kuna. Ta girgiza kai cikin takaici

"Abba, akwai babbar matsala akan wannan lamari. Ni kam na kasa gane abin da ke faruwa. Ashe Fulany Maryam ta ci nasara akan As'ad? Na ce tun farko kada ku yi wasa da addu'a. Yanzu da alama ta mallake shi, ba kawai zuciyarsa ba, har da hankalinsa gaba ɗaya."

Abba ya tsaya yana nazari, yana jin yadda wannan magana ke tayar masa da hankali. Yana kallon yadda Haneefah ta yi nasarar canza As'ad cikin lokaci kadan.

"Hajja," Abba ya yi ƙasa da murya, "Mamy ta je gidan As'ad a Abuja domin ganinsa, amma aka ce mata ba za ta shiga ba saboda Madam Haneefah bata bada izini ba. Ta dawo gida cike da takaici. Wallahi, na fara jin tsoro, Hajja."

Hajja ta rike kai tana jin yadda lamarin ke kara dagulewa. Ta sauke numfashi mai nauyi, tana jin zafi a zuciyarta. Ta kalli Abba da ido cike da damuwa

Na roƙi Mai Martaba amma Sarki yace kada a takura masa tunda zaman lafiya suke yi."

"Zaman lafiya?" Abba ya ja numfashi cikin takaici,

"Hajja, wallahi wannan ba zaman lafiya ba ne. Fulany Maryam ta yi nasara. Ba ki ji ba? Jikarta da take a Asubuti ta rasu, amma ko ajikinta ba ta je ba. Idan mace ta iya haka, me zai hana ta kwace zuciyar As'ad gaba ɗaya?"

"Wallahi kuwa," Hajja ta amsa tana girgiza kai,

"ina cikin tsananin damuwa. Na san As'ad da kasuwanci da aiki tukuru, amma yanzu bai kira ni ba, bai nemi shawara ba, ba ya ko amsa waya. Wannan ai ba halinsa bane."

Abba ya rage murya, yana kallon yadda Hajja ke nuna tsananin damuwa

"Hajja, ko dai ayi masa ruƙiya ne? Ni kam na fara jin tsoron Haneefah."

Hajja ta zura ido cikin tunani, ta ja numfashi da kyar

"Ruƙiya kuma? amma fa tayaya za a yi masa ita idan Haneefah ce ke iko da shi gaba ɗaya? Wallahi, ba ni da wani iko a yanzu. Za mu cigaba da addu'a, Abba. Na san cewa babu wani abu da ya fi addu’a ƙarfi. Amma a wannan lokaci, ku ma ku tsananta addu'a a ko da yaushe. Kada ku yi sakaci. Domin idan da gaske Fulany Maryam ta yi nasara, to kuwa As'ad zai iya rasa dukiyarsa da hankalinsa gaba ɗaya."

Abba ya amsa cikin jin ƙwarin guiwa

"Toh, Hajja. Zamu yi duk mai yiwuwa. Allah ya bamu damar ceto shi daga wannan kunci."

Hajja ta kalli Abba da idanu masu cike da damuwa, sannan ta ce

"Allah ya sa haka. Yanzu dai zan tsananta addu’a, ko Allah ya warware wannan asiri da aka yi masa."

******

Fulany Maryam tana zaune a falonta tana hutawa sai ga wayarta tana kara. Ta duba sunan mai kira, ta ga Haneefah ce. Ta ja tsaki, sannan ta dauki wayar cikin bacin rai

"Dan ubanki! Ina ce kwanciya da namiji na turaki? Na ce, kwanciya da saduwa na turaki! Sha sha sha! Ke kuwa wacce irin macce ce wacce batasan me ke mata ciwo ba! Kin zuba masa maganin a abinci kuwa?"

Haneefah ta tsaya daga gyaran kanta a madubi, ta turo baki kamar wata yarinya tace

"Mama, wallahi na manta ne."

Fulany Maryam ta sake jan tsaki

"Lallai kin manta! Yanzu kina son ya dawo hayyacinsa ya kore ki kenan? Kin san wannan aure na ikon asiri ne. Ko kallo wallahi baki ishesa ba idan babu magani. Ke kuma sai ki tsaya soyayya? Babu abinda ya dame ni da soyayya!"

Haneefah ta sauke numfashi mai nauyi, ta yi kasa da murya

"Mama, zan gyara. Wallahi, ba zan sake sakaci ba."

"To ki tabbatar da haka! Kada ki sake sakaci. Idan ba haka ba, wallahi zaki rasa komai. Ba soyayya ake ba, iko da mulki ake yi. Da an barki da soyayya, da tuni kin koma gida kina kuka."

"Na gane Mama, zan kula sosai," Haneefah ta amsa cikin ladabi, sannan ta kashe wayar.

Bayan ta kashe wayar, Haneefah ta mike da sauri, zuciyarta na harbawa. Ta nufi wardrobe dinta, ta bude drawer, ta dauki maganin sannan ta nufi dining. Ta bude abincin da ta shirya masa, ta zuba maganin cikin miyar, sannan ta gyara teburin cikin tsari.

Bayan ta gama, ta shiga wanka, ta feshe jikinta da turaren Gucci Bloom, sannan ta zabi wani leshi mai launin ruwan madara mai laushi wanda ya matseta sosai.

***

As'ad ya shigo bangaren nata cikin gajiya, yana jin kansa yana sara masa. Duk da haka, ya yi murmushi da kyar lokacin da ya ga yadda ta nannade kanta da gyale mai kyau.

"Sannu da zuwa, Ya As'ad," ta furta cikin shagwaba, tana matsowa kusa da shi. "Na shirya maka abinci na musamman."

Ya zauna a kan kujerar falo, yana kallonta da kyar. Haneefah ta zuba masa abinci cikin kulawa, tana masa shagwaba, tana taba hannunsa a hankali.

Yana ci, wani irin dadi da sanyi yana ratsa jikinsa. Amma daga bisani ya fara jin nauyi da sara-saran kai. Ya dubi Haneefah da alamar tambaya

"Kaina na ciwo... Bari na je na kwanta can na huta."

Haneefah ta dan ja hannunsa tana murmushi

"Ya As'ad, ka huta a nan mana. Banson naganka nisa dani.."

Ya girgiza kai da kyar

"Babu komai... kawai kaina ne ke ciwo sosai."

Duk yadda ta so ya tsaya, sai ya dage cewa zai koma bangarensa. Ya bar dakin yana jin kamar kansa zai tsage. Haneefah ta dan tsaki cikin takaici, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da karfi.

Bayan ya fita, sai ta kira P.A dinsa

"Kawo min takardun gidansa na Abuja da ya mallaka mata . Ajiye su nan." Tafada tana binsa da harara..

P.A din ya kawo takardun cikin natsuwa, ya miƙa mata, sannan ya fita. Haneefah ta duba takardun cikin natsuwa, ta nannade su a cikin wata jaka ta boye su a cikin drawer.

Yana kwance a daki, wayarsa ta fara kara. P.A din ya kawo masa wayar yace

"Ranka yadade hajja Nason magana dakai tace Na nema mata izini yafaɗa yana dan miƙa masa wayar tasa.

Da kyar ya iya daga wayar, yana jin muryar Hajja cikin damuwa

"As'ad, me ke faruwa da kai ne? Na kira baka dauka. Ka dage da addu’a, kaji? Ga kuma maganin nan da na turo, ka sha yanzu."

"To, Hajja," ya amsa da rauni, yana jin yadda kansa ke sara masa.

P.A din ya zuba maganin a cikin ruwa, ya miƙa masa, sannan As'ad ya sha. Bayan ya gama, bacci mai nauyi ya dauke shi.

Bayan bacci mai nauyi, As'ad ya farka da tari mai karfi, yana jin yadda hayaki ke cika dakin. Ya rike kansa, yana jin amai na taso masa.

Sautin karatun Al-Qur’ani ya fara tashi daga pop speaker. As'ad ya rike kansa, yana jin yadda wannan karatu ke ratsa zuciyarsa. Bai ga remote din ba, kuma ya rasa yadda zai kashe sautin.

"Me ke faruwa da ni?" Ya furta cikin rawar murya.

Ya kira P.A dinsa Amma Baya kusa kwatakwata wayar tashi ma akashe take

"Wannan abu ya yi yawa," ya furta da kyar, yana jin zuciyarsa tana tafarfasa.

*****

Baba Asabe tana zaune a tsakiyar dakin tsafe-tsafe, wuta tana ci a tsakiyar ɗakin, hayaki mai kauri na tashi sama yana cike da ɗakin. Hotunan tsafe-tsafe sun zagaye bangon, yayin da ƙamshi mai ɗaci ke ratsa hancin Ayshatu. Ta tsaya a gaban Baba Asabe, tana jin zuciyarta na bugawa da tsanani.

Baba Asabe ta daga murya da ƙarfi, tana cewa

"Yau kwanaki uku kenan da kamala aikinmu. Aysha, kin yi nasara! Sadaukarwa ta yi aiki! Zaki kasance sama da duk wata mace. As'ad Mallakin ki ne babu aure da wata mace. Iyayensa ma ba zasu kara yi masa maganar aure ba. Mulkin gidan As'ad yana hannunki."

Ayshatu ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, amma duk da haka, wani abu na damunta. Baba Asabe ta lura da yanayinta, ta ce

"Amma fa, Aysha, na gano wata cakwakiya. Ba mu iya magance ta ba."

Ayshatu ta rike hannunta cikin damuwa

"Baba Asabe, wace cakwakiya ce wannan?"

Baba Asabe ta yi dariya mai mugunta:

"Ba wata matsala mai girma ba ce. Amma fa akwai ɗan cikas. Idan har kina son As'ad sosai, zaki yi biyayya ga umarni. Wannan layar zata tabbatar da nasararki."

Ta zaro wata layar daga cikin kwando, ta mika mata

"Idan kin shiga bangaren As'ad, ki jefa layar a kasa. Haka kuma, idan zaki shiga bangaren amaryar, ki jefa ta kusa da sashjnts. Da zarar kin yi hakan, zamansu ya kare!"

Ayshatu ta dauki layar, tana jin tsoro

"Idan aka gani fa, Baba Asabe?"

Baba Asabe ta dara

"Ki kwantar da hankali. Duk lokacin da kika ajiye layar, zata bace kamar iska."

Ayshatu ta yi shiru, zuciyarta cike da fargaba. Baba Asabe ta ci gaba

"Ki tabbata kin yi yanka ranar Lahadi da Laraba. Kada ki Sallah da Asubahi ko La’asar. Idan kika saba, duk abinda kika yi zai lalace."

Ayshatu ta gyada kai, tana jin nauyin alhakin da ta ɗauka. Amma a zuciyarta, ta sha alwashin yin komai don ta mallaki As'ad.

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA ASHIRIN DA UKU

Arewabook @nanadiso10

Kullum cikin kuka nake, zuciyata cike da baƙin ciki da gajiya. Yanzu haka, ba ni jin daɗin komai a rayuwa. Wani lokacin ina ji kamar mutuwa ce kadai mafita. In bi mamata in huta da wannan wahala da azabar da nake ciki kullum.

Na zama kamar baiwa a gidanmu. Aiki kawai nake kamar wadda ba ta da wani amfani sai gyara da kwashe-kwashe. Momy na nuna min tsana sosai fiye da yadda zuciya zata iya ɗauka.

Mun gama jarabawar WAEC, yau kusan makonni uku kenan. Amma rayuwa ta ƙara tsananta. Abba kullum cikin zargi da tuhumata yake, ko motsi kawai na yi, sai Momy ta ga laifi a cikinsa.

A cikin waɗannan makonnin, na zama kamar jaka, babu kima. Na rasa komai tun da Abba ya kwace wayata. Wayar ce kaɗai nake amfani da ita don in ɗan ji daɗi a lokacin da muke jiran sakamakon jarabawar. Yanzu komai ya lalace.

Gaba ɗaya na cika da damuwa, ba kudi, ba walwala. Abokiyata Fatima ce kadai take ban 'yar tallafi ta bani kuɗin makaranta da sauransu. Amma yanzu itama ta tafi ƙasar waje gurin yayarta. Na zauna ni kaɗai, hawaye na gangarowa ba tare da ya tsaya ba...

Yaya Billy Kuwa Tsuntsuwar ƙiyayya da take ɗawainiya da zuciyar ta a kaina ta kai matakin da kalmomi ba za su iya warwarewa ba. Sau da dama na gane ta na ƙoƙarin zubamin wani abu cikin shayi ko lemo, amma Allah ya tsare ni. Duk lokacin da na lura da wani abu ba daidai ba, sai kawai na daina sha cikin hikima. Na gane cewa a hannunta babu amincewa, zuciyarta cike take da wata irin ƙiyayya mai zafi.

Ranar Juma’ar nan, ta zo da wani sabon sharri. Tace wai na satar mata dubu ɗari. Kafin a ce kwabo, gida ya rikide hayaniya ta cika ko ina! Aka nemi kuɗin nan har ƙasa, aka rasa. Duk da nasan ƙarya take, hakan bai hana Abba zafafa fushinsa akaina ba. Ya zarge ni da sata. Na tsaya gefe, zuciyata na rawar jiki, na rasa kalmar kare kaina daga abin da ban aikata ba.

Rayuwata ta cushe da ƙunci. Bana da ko sisin kwabo da zan iya siyan pant ko mai da zan shafawa jikina. Ranar da na nemi Momy tabani kudi, sai ta kalleni da raini, ta ce: “Je gurin ‘yan bariki, su ne zasu baki.” Wannan magana ta fasa zuciyata ƙiririƙi. Wace irin uwa ce ke fadi wa ‘yarta haka?

Abba kuwa sai ya mara mata baya. Ya ce tunda na fara sata, to ko naira biyar ba zai sake bani ba. Na shanye ƙuncina. Na fi kowa jin zafin yadda ya yarda da duk wata magana da ta fito daga bakin Momy. Shi kuwa bai san Momy ba kamar yadda na santa mace ce da ta kware wajen ƙirƙira da tsara sharri.

A cikin wannan duhu da zuciyata ke ciki, akwai fitila guda ɗaya da ke haskaka Shamsiyya, makociyarmu. Ita kadai ce take nuna min dan tausayawa. Watarana tana taimaka min da aikace-aikace, tana bani kwarin gwiwa. Ita ce kadai ta tabbatar min cewa har yanzu akwai wanda zuciyarsa ke da laushi a duniyar nan.

*****

Ina zaune yanzu haka cikin ɗaki, nayi tagumi kai na lulluɓe da zullumi. Gajiyata ta zarce ta jiki har cikin ƙashi na nake jin nauyi. Na gama tuka tuwo da rana, na gyara falo, na wanke kayan girki, amma har yanzu babu wani abu da ya sanya zuciyata farin ciki. Na yi iya ƙoƙarina, amma kamar ruwa ne nake shanya a dutse.

Ba komai nake nema ba ɗan nishadi kaɗan ne kawai. Ko fim ɗin Korea da na saba kallo, wanda ke saka ni dariya, ya ɗan mantar da ni da damuwa. Amma yanzu, ko ₦100 da zan biya na kalla bani da shi.

Rayuwata ta dame ni. Gidan da nake ciki kamar gidan da aka kulle albarkacin zuciya. Ina aiki kamar baiwa, amma kamar ina hasken rana a idon makaho. Na rasa wani da zan bude masa zuciyata na faɗa masa haƙiƙanin abin da ke ci min rai, abin da ke rarrafe a cikin dare yana hana ni barci.

Na tuna da Fatima. Da na saurare ta, da na rungumi salon da ta bi Na kula samari don ɗan kuɗi. Watakila da yanzu ina da ɗan abu da zan biya matsalata da shi. Amma ban iya haka ba. Na tsaya da mutunci.

Yanzu ma wani kaikayi ke damuna, wani irin zafi kamar ana cizon wuta ne a gabana. Amma bana da kuɗin shaver, ko man cream, balle in iya zuwa asibiti. Na gwada shiga ɗakin Momy jiya na zaci zan ɗauki ɗan abu, amma gashi ita ke kallona kamar baiwa da aka aje a gaba marar daraja, marar murya.

Na miƙe a hankali daga inda nake zaune, na ɗauki laptop dina, sannan na fice zuwa harabar gidanmu. Iska mai laushi na busawa fuskata, tana ɗan shafa gajiyata da salama. Idona ya sauka a kan Musa, mai aikin gidanmu, yana share ƙasa a ƙasan bishiyar mangwaro. Na nufe shi da fara’a mai launin ɗaci.

“Ina wuni Musa,” na ce masa da ƙanƙanin murya, kamar wadda ke boye wani sirri a zuciya. “Don Allah, idan zaka iya, ka taimaka ka turomin wasu fina-finan Korea masu kyau. Amma dan Allah, kada kowa ya sani. Ni da kai ne kawai.”

Musa ya tsaya, ya ɗago da murmushi mai sanyi, ya ce, “Haba Hajiya Ramlah, ba matsala kwata-kwata. Abokina ne mai turawa, ai ni ma fina-finai kawai nake karɓa, ba sai kin bada ko sisi ba.”

Na ji wata ƙara mai sanyi ta zuba a zuciyata. Na miƙa masa laptop ɗin da hannayena biyu, cikin ladabi da godiya.

Na murmusa, zuciyata ta ɗan lafa. “Nagode sosai,” na faɗa a nutse, sannan na juya na koma cikin gida, kamar wata baiwar da aka samu nata ƙaramin nishaɗin da zai dan shafe gajiyar zuciya.

A yau ba zan ji kunya ba, na faɗa wa kaina. Ko 10,000 ce, zan tambayi Momy. Komai za ta ce, ko yaya za ta yi, in har ba zan mutu ba, zan fuskance ta.

Na ɗaura ɗankwali da hanzari, Na hau saman bene kamar wadda zuciyarta ke harbawa da fatan samun ƙanƙanin jin ƙai.

Tun kafin na karasa palon, idanuwanta ta zuba min. Tana zaune kan kujera kamar sarauniyar da aka gaji da mulkinta, tana kallon tashar da babu sauti.

Lafiya? Me kike nema da rana tsaka zaki hau min sama haka?

Na tsugunna a gabanta kamar wadda ake shirin yanke wa hukunci.

“Momy…” Na daɗe kafin na iya ci gaba. Muryata na rawa kamar tana kokarin fita ba tare da izini ba. “Dan Allah, ko 10k ce kibani. Akwai kayan gyara da nake so nasiya. Wallahi gaba ɗaya jikina wari nake ji. Ga gashi...”

Sai na ji saukar wani abu mai zafi. Hannunta ya buge min baki kamar ana yanka tunani a idanuwa. Na lumshe ido da sauri, hawaye suka taru amma suka tsaya gefe da gefe.

Ubanki ya bani kudi nace? Bazan bayar ba! Ina mazan da kike bi? Je ki su baki mana! Ni bana son damuwa fa Ramlah. Kada kiga ina yi wa Bilkisu komai, ita cikakkiyar ‘yata ce. Ke kuwa? Ke ‘yar kishiya ce. Kishiya dai dai da aƙalla? Ki tashi ki farka, kin ji? Wani sai kin bi hanya irin ta Fatima sai kuɗi da ake nema cikin sharri!”

Tana magana, zuciyata na fashewa a ciki kamar madubi mai tsufa da aka jefa a ƙasa. Kowace kalma kamar tabarya ce aka zuba min a rai.

Tashi ki bani guri! Wata shegiya! Sai kiba kikeyi kin sha ne har kin manta me kika zo nema? Ko maganin ƙarin kiba kika kara siya?

Zan iya jure yunwa, zan iya jure gajiya. Amma wannan kalmomi? Su ne suka fi komai fasani.

Na daure fuska cikin kwanciyar hankali da hawaye ke bijiro min daga zuciya ba daga ido ba. Na ce

“Mama… A’a..” Na sauka da ƙasa da murya, na durƙusa na juya kamar wadda ke ficewa daga duniyar da ba ta ƙara yi mata amfani ba.

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA ASHIRIN DA HUDU

Arewabook @nanadiso10

Tsaye yake a gaban madubi mai fadi wanda aka shigo da shi daga Italiya. Madubin yana ɗaukar hotonsa Fuskarsa cike da kwarjini, idanuwansa masu haske da zurfin hankali na kallon kansa da nutsuwa.

A jikinsa rigar siliki ce ta musamman, farar fata mai laushi, alamar LV a gefe, da turaren oud daga Dubai da ke zubda ƙamshi a cikin iska.

Tsaye yake yana kallon kansa, sannan ya sauke numfashi a hankali. Ya ɗaura hannu a goshinsa, yana jin ciwon kan da ke damunsa tun jiya ya rage, amma nauyin da ke zuciyarsa bai sauka ba.

“Ya Allah, ka bani nutsuwa,” ya faɗa a hankali, yana mai rusunawa da yin istigfari.

Ya mike, ya ɗauki wayarsa daga mirrored table. Ya shiga lambobin wayarsa, ya kira Ayshatu. Sau ɗaya. Sau biyu. Har sau hudu. Shiru.

Ya dafe goshi. Wani irin bugun zuciya ya taso masa.

“Why aren’t you picking up, Ayshatu?”

Ya jingina da bango, yana kallon sararin samaniya ta cikin tagar gilashi. Hankalinsa yana juyawa. Ya fitar da numfashi mai nauyi, sannan ya kira diyarsa, Aminatu.

Tana ɗagawa cikin sauri da ladabi.

“Assalamu Alaikum, Daddy.”

“Wa alaikumus salam. Yaya gida? You and Abubakar, hope everyone is okay?”

“Alhamdulillah dady, we're all fine. Yaya kai, Dady? Your head?”

“Still heavy. I’ve been trying to reach your mother, but she hasn’t picked up.”

Aminatu ta yi shiru na sakanni kafin tace

“Wallahi Dady, rabona da ita kusan kwana goma. Tace min tana Paris. Ni ma nayi ƙoƙarin kiranta amma bata sake ɗauka ba.”

“Paris?” ya maimaita da mamaki.

“She didn’t say anything to me.” “Tace zata kirani daga baya. Amma har yanzu bata kira ba.”

As’ad ya jingina da kujera ya dafe kansa a hankali. Zuciyarsa cike da tambaya Ina Ayshatu ta tsaya?.

“It’s alright. I’ll try again. Send my regards to Abubakar.”

“I will Dady. Please don’t stress yourself too much.”

“Thank you, sweetheart. Take care.”

Ya kashe wayar, yana jin sanyi ya ratsa jikinsa.

Cikin daƙiƙu kaɗan bayan kammala tattaunawa da diyarsa, Ya danna bell din kofar. Bai ce komai ba PA ɗinsa ne, Mustapha, wanda ke aiki da shi fiye da shekara goma, yana da Amana da sirri sosai da shi.

“Come in,” As’ad ya furta cikin nutsuwa.

Mustapha ya buɗe ƙofar cikin ladabi, yana sanye da farin suit da takalma masu sheƙi. Ya shiga, yana ɗan sunkuyar da kai. “Sir, good morning. Are you available now? You requested to see me urgently.”

As’ad ya ɗaga kai daga littafin da ke gabansa, yana kallon Mustapha da nutsuwa. “Yes, Mustapha. Do I have any meetings today?”

Mustapha ya ɗauko small tablet daga hannunsa, ya duba calendar dashboard ɗin As’ad. “Yes sir. You have four scheduled meetings today one with the Turkish investor at 10AM, a Zoom board update at 11:30, Nigerian Royal Council engagement by 2PM, and a dinner strategy with the EU delegation at 6.”

As’ad ya gyara zama. “That’s a full plate. Alright, ganinan fitowa in few minutes. Make sure the team is ready, the car set, and my private suite at the downtown tower ready for the Turkish guy.”

“Yes sir. Everything is already in motion.”

As’ad ya miƙe tsaye daga kujerarsa ya nufi mirrored hallway wanda ke kaiwa dressing chamber dinsa. Tufafin da ke rataye a cikin ɗakin kayan shiryawa Armani, Tom Ford, da YSL.

Ya zabi baƙar suit mai launin toka a jikin collar, ya ɗaura cufflinks ɗinsa masu logo na family crest ɗin su. Yana gama shiryawa, ya danna intercom

“Mustapha, let’s go.”

“Yes sir,” aka amsa nan take.

Ya fito daga ɗakin cikin ƙamshi na musamman na Oud Wood, yana tafiya kamar sarkin zamani. Ko wanda bai san shi ba idan ya ganshi a haka, sai ya kalli cikakken namiji mai daraja da kamala. Bodyguards biyu suka buɗe masa ƙofa, suka rakashi har zuwa motar Maybach da ke jiransa.

Yana zama, PA ɗinsa da direba suka shiga sannan suka wuce cikin tsari.

*******

Taron ya cigaba da tafiya cikin tsari, kalmomin da ke fitowa daga bakin As’ad na ɗauke da hikima, bayanin kasuwanci, da jagoranci mai zurfi. A matsayin babban attajiri da shugaban kamfani mai haɗin guiwa da ƙasashe sama da ashirin, ya san yadda ake gudanar da taro da ƙwarewa kallon kowa yana kansa, maganarsa ana rubutawa.

Yayin da yake sauraron bayanin Oğuzhan kan yanda za a kafa data-driven smart energy grids, zuciyarsa na tafiya da kallon window da ke nuna masa hasken rana yana saukowa a kan ginin villa dinsa da ke can nesa. Duk da cewa yana gab da yanke shawarar dala biliyan, zuciyarsa na bugewa da tambayoyi “Ayshatu… me kike yi a Paris har yanzu? Kina lafiya? Me yasa ba kya kira? Kuma Haneefa, me yasa take ƙoƙarin shigowa bangarena?”

“Sir? Sir...?” Muryar Mr. Oğuzhan ta dawo da shi daga tafarkin zuciya.

“Yes, I’m here,” ya ce da kwarewa, yana ɗaga ido. “I like your pitch. I’ll have my legal and finance team review this thoroughly and we’ll schedule a signing week after next. Mustapha, make the arrangements.”

“Yes sir,” PA ɗinsa ya amsa da girmamawa, yana zazzage bayanai cikin iPad ɗinsa.

Daga nan, suka tsaya don dan hutu. As’ad ya ja numfashi, ya tashi zuwa wani keɓaɓɓen balcony. Wuri ne mai fuskantar babbar hanyar, ya na kallon motoci da gine-gine masu ɗaukaka.

Ya jingina da katanga, ya ciro wayarsa, ya sake danna lambar Ayshatu.

Tuut... tuuut... Still, no response.

“Subhanallah...” ya furta, yana lumshe ido, yana jin cewa akwai abu mai zurfi da ke gudana. A cikin zuciyarsa ya ɗaura niyya “I will find out what’s going on. I’ll go to Paris myself, but I’ll finish these business duties first.”

A lokaci guda, Mustapha ya ƙaraso.

“Sir,” ya ce da girmamawa, “Your next Zoom conference with the EU delegate is in 20 minutes.”

As’ad ya juyo da murmushi, ya gyara suit ɗinsa.

“Very well. Let’s make it quick and sharp.”

Amma a yayin da suke komawa ciki, ya buɗe Text, ya aika sako ga Haneefa

“We’ll talk soon. I’ve just been under pressure. I see your calls. Be patient.”

*****

Haneefa ta fito daga ɗakin wanka cikin farin doguwar riga mai laushi. Fuskarta na ɗauke da kwalliya, jikinta na ƙamshi da turare Masu dadi. Ta kalli kanta a madubi, ta ga yadda take cikin kyau sosai. Amma duk da wannan kyau, zuciyarta cike take da damuwa da bakin ciki.

Tun jiya mijinta As’ad bai shigo bangarenta ba. Bai kira ta ba. Bai aika mata da sako ba. Wannan abu ya ɗaga mata hankali.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull