Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 12
Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 12: Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 12. Ta tafi bangarensa har sau uku, tana fatan ko zai fito ya ganta.…
4,488 words
Ta tafi bangarensa har sau uku, tana fatan ko zai fito ya ganta. Amma duk lokacin da ta je, masu gadin ƙofar suna gaya mata cewa ba za ta iya shiga ba.
“Hajiya kiyi hakuri, amma ba’a barin kowa ya shiga bangaren oga sai da izini. Wannan shine doka,” daya daga cikin masu tsaro ya ce mata cikin ladabi.
Wannan maganar ta ci mata rai. “To ni fa matar shi ce? Me yasa zan bukaci izini kafin in ga mijina?” ta tambaya cikin da damuwa.
Amma duk da haka, ba su bar ta ta shiga ba. Daga karshe sai dai ta juya da zuciya mai nauyi, ta koma bangarenta.
Tana shiga ɗaki, ta cire mayafinta ta wurgar, ta ɗauki wayarta. Ta kira Fulani Maryam.
“Mama,” ta fara da kuka, “tun jiya As’ad bai zo bangarena ba. Na najei har sau uku suka ce ba zan shiga ba. Wallahi bazan iya rabuwa da shi ba.”
Fulani Maryam ta ce , “Ke dai ki nutsu. Ba na gaya miki ba ki kula da magungunan da na ba ki? Ko dai baki bashi sosai ba?”
“Wallahi mama duk na bashi. Amma dai wulakanci ne kawai nake fuskanta.”
“Matsalar As’ad tuni zan maganinta. Idan kin tabbatar ya sha magungunan, to ki bar komai a hannuna. Ki nutsu kawai,” Fulany Maryam ta ce da kwarin gwiwa.
Haneefa ta ajiye wayarta, ta zauna kan gado. Duk da cewa ɗakin nata na cike da kayan alatu kujerun , labule masu ƙyau, ga kamshi mai daɗi amma babu farin ciki a zuciyarta. Dukiya ba ta kwantar mata da hankali ita tun asalinta shiyasa bata iya zaman auren.
Ta nufi bar counter din ɗakin, ta ɗauki kankana, habbatussauda, madara, kantu da zuma ta hada hadin da ke ƙara sha’awa. Tasha a hankali tana fatan zai ratsata
Gashi har yanzu tana cikin tsananin sha’awa da kishi. Tana tunanin As’ad. “Da ace yana nan kusa dani. Da ace zai riko hannuna... ya kalle ni a ido... ya ce min, ‘Haneefa na, I’m here.’”
Tana cikin wannan tunani, idonta ya rufe. Bacci ya dauketa.
Nana hadiza
09030569336
**************
*IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Paid book N500 naira only
5044109936
Bilkisu Sani Kaura
Shaidar biya
07040402435
Page 1
Idanuwansa ya ɗago ya zuba akan Kyakkyawan matashin dake tsaye acikin paloun riƙe da wuƙa a hannunsa duk jini, fuskar nan tasa a haɗe babu alamun tsoro ko kuma shiga tashin hankali na riskarsa da akayi cikin wannan yanayi balle kuma nadama, a gefensa kuma wata budurwa ce duƙe tasa hannayenta ta toshe bakinta dasu tana kuka, kukan da gaba-daya kana kallon ta zaka fahimci yadda ya sauya mata kamanni ta hanyar sauya kalar fatar fuskarta izuwa ja, yayin da launin idanuwanta dake farare tas suka yi jajir suna cigaba da tsiyayar da ƙwalla. A gaban su kuma babbar macece ta rungume wani matashi ajikinta dake kwance cikin jini ko motsi bayayi tana kuka tana girgiza sa haɗe da sabbatun ya tashi. Ganin da tayi tabbas bazai tashi ba ya sa ta miƙewa cikin wani irin fushi da zafin rai ta nufo wajen saurayin dake tsaye riƙe da wuƙar da kana gani kasan da ita akayi amfani wajen illata wanda ke kwance cikin jinin babu lumfashi a jikinsa, tana zuwa ta ɗauke sa kyakkyawan mari har guda biyu saboda tabbacin da take dashi akan ko shakka babu shine ya yi wannan aika aikan, cikin zaro idanuwa da ƙaraji take cewa "Kai ɗan gidan uban waye? Me ye ya kawo ka cikin gidan nan? Waye ya aiko ka aikata masa haka? Me yarona ya yi maka ne?". Ta jero masa tambayoyin tana shaƙo wuyan rigar sa kafin ta fashe da wani irin kuka tana zubewa ƙasa, saurayin kuwa kasa amsa mata yayi sai ma ƙasa da ya yi da kansa don har lokacin babu alamun nadamar abinda ya faru ko tsoro a tattare dashi, banda zallar masifa da jin kai babu abinda ke cikin idanuwa da suka yi jajir tamkar an watsa barkono.
Kukan da matar keyi ya maido da mutumen cikin hayyacinsa yana faɗin. "Innalillahi wainna ilaihirrajiun". Kalmar daya iya faɗa kenan haɗe da ciro wayarsa, bugu ɗaya ya yiwa wata lamba aka ɗaga, cikin wata irin murya dake nuni da cike yake da damuwa yace. "Commissioner ina so ka turo mani da yaranka anan gidana, Please ranka shi daɗe". A ta ɗayan ɓangaren commissioner of Police ya amsa masa da, "Yanzun nan amma yallaɓai ina fatan dai lafiya ko?" "Ba lafiya ba.." nan ya kwashe duk abinda ke faruwa da suka isko ya sanar dashi yana jin idanuwansa na kokarin kawo ƙwalla yana ji duniyar nayi masa wani irin juyi, gaba-daya ya gama ruɗewar da bai san me zai yi ba banda ya kira hukuma.
Bayan mintuna goma sha takwas da kiransa sai ga motar police har guda biyu ta iso gidan, Nan ya basu izinin shigowa tare da nuna masu wanda zasu yi arresting da suna shigowa su da kansu suka fahimci shine mai kaifin ganin wuƙa da jini a hannunsa, a take suka zagayesa tare da saita bindigogin su akansa saboda kar ya gudu, ɗaya daga cikin yan sandan ne ya fiddo ankwa zai saka mashi a hannu da sauri matashiyar budurwar dake gefe tana kuka ta miƙe tsaye ta nufo wajen, ganin zatayi magana saurayin ya nunata da wuƙa yana cewa. "Wlh kalma ɗaya idan kika faɗa zan kasheki kema sannan na kashe kaina nim.." Bai ƙarasa ba ya ji saukar kan bindiga saman kansa ya saki wata irin ƙara tare da zubewa akan guiwoyinsa saboda tsananin azabar da yaji, baya ta ja tana sake toshe bakinta saboda gargaɗin da yayi mata da take da tabbacin zai iya aikata abinda ya faɗa, "Inspector kuje dashi ayi bincike a gano waye ya turosa har cikin gida yazo ya aikata haka ga ɗana! Bana so ku sassauta masa har sai kun tabbatar daya faɗa maku gaskiya, ku gana masa azabar da zata sa da bakinsa ya faɗi ko waye ya aikosa, ni kuma zan ga wanda zai tsaya masa akaf faɗin ƙasar nan, sai naga wanda ya ɗaure masa gindi da zai hana nayi Shari'a dashi ko da duka abinda na mallaka zai ƙare". Wani dukan suka sake kaiwa saurayin a karo na biyu a saman kafaɗa bayan sun saka mashi ankwa kafin su ɗaga shi suka nufi hanyar fita dashi, suna kaiwa bakin ƙofa ya juyo yana ma yarinyar wani kallo mai cike da gargaɗi, ɗan sandan dake riƙe dashi ya hankaɗasa yana tura ƙeyarsa waje yake cewa, "wuce muje, zakayi bayani". Suka turasa cikin motarsu ta yan sanda bayan sun fito tare da tayar da motar suka fice daga gidan, ɗaya motar ta yan sanda kuma suka ɗauki wanda ke kwance cikin jini aka nufi asibiti dashi, kallon budurwar mutumen ya yi da sautin kukanta ya ƙaru yace, "Ya isa haka ki tashi ki tafi gida, idan ma ya hanaki magana yanzu lokaci zai zo da gaskiya zata bayyana idan aka zo bincike, ina fatan zaki faɗi abinda kika sani don bima yarima da jininsa hakkinsa". Jiki ba ƙwari ta miƙe zata fita matar tace.
"Ki sani ke kadai ce zaki iya bada tabbacin abinda ya faru, idan har kika ɓoye kuma bazan taɓa yafe maki ba". Bata iya cewa komai ba tana kuka ta fice daga gidan, yara yan mata biyu suka zo suka rungume matar suna kuka, shi kuma mutumen ya fice yabi bayan yan sandan zuciyarsa cike da damuwa, driven yake amma tunani yake yi yaushe ɗansa ya dawo ƙasar nan ba tare da saninsa ba? Me yakawo wancan saurayin acikin gidansa har hakan ta faru? Waye shi meye alakarsa da ɗansa da zai shigo har cikin gidansa yayi masa wannan mummunan aika-aika. Ji yai zuciyarsa ta bushe ta cika da wutar son ɗaukarwa ɗan nasa ƙwaya tilo da yake matuƙar ƙauna fansa, a take ya ɗauki alwashin ko waye yaron kuma ko dan gidan waye shi sai an hukunta sa shima dai-dai da laifinsa don bazai yafe ba, bazai taɓa bari jinin ɗansa ya tafi a banza ba.ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ASHIRIN DA BIYAR
Arewabook @nanadiso10
Wajen ƙarfe ɗaya da rabi na dare As’ad ya dawo gida. Ya shigo cikin motarsa mai tsada, wata sabuwar Maybach mai glass roof, fitilarta tana kyalli kamar rana a cikin dare. Ya fita daga mota, masu tsaro suka gaishe shi da girmamawa. Yana tafiya cikin dogon hallway mai fale-falen zinariya da bango mai hoto, sai ya shiga ɗakin sa. A ƙofar dakinsa, wani kamshi mai sanyi daga turaren wuta na larabawa ya bugi hancinsa.
Ya cire takalmi, ya nufi bandaki. Yayi wanka mai kyau, sannan ya ɗaura rigar bacci da aka yi masa a ƙasar Italy. Ya yi sallar dare shafa’i da witr kamar yadda ya saba, sannan ya kira kitchen
“Ku aiko min da dan abinci mai sauƙi, da ruwa mai sanyi,” ya ce.
Ba da jimawa ba aka kawo masa abinci. Tuwo ne da miya mai ƙamshi daga bangaren Haneefa. Yana zaune yana ci, amma cikin cin abincin sai ya fara jin kansa na sarawa. Duk da haka ya daure, ya cinye, sannan ya sha magani ya kwanta.
Zuciyarsa ba ta da kwanciyar hankali. Sai ya juya a gadon, yana jin kamar zuciyarsa tana kiransa zuwa ɗakin Haneefa. Yana jin yana buƙatar ta sosai.
Yayi shiru na ɗan lokaci, sannan ya tashi. Ya buɗe wani ƙofa na sirri da ke haɗa dakinsa da nata. Wannan ƙofa ba kowa ke san da ita ba. Ya shiga cikin nutsuwa.
Yana shiga nata bangaren, fitilar ɗakin nata duk Akunne. Kamshi ne ke yawo mai dadi adaƙin. Ya buɗe ƙofar ɗakinta a hankali, sai ya hangota tana kwance akan gado, rigar bacci a jikinta tana lulluɓe, jikinta bararraje kamar wata sarauniya da bacci ya ɗauke.
Ya ƙarasa kusa da ita, yana kallonta. “Subhanallah...” ya furta a hankali.
Yayi kusanto, ya kamo hannunta. Cikin bacci ta furta, “As’ad...”
“I’m here,” ya ce da kasalalliyar murya.
Ta buɗe ido da kyar. Ta gan shi, tayi dariya mai cike da hawaye. Ta rungume shi da ƙarfi.
“Me yasa ka barni? Ka watsar dani... As’ad...”
“Ki yi hakuri, Haneefa. Na gaji sosai ne. Ina aiki tun safe,” ya ce yana rarrashinta.
Suka rungume juna. Amma sai ya lura da abu guda gabansa bai tashi ba ko irin ya motsa din nan baiyiba. Ya yi kokarin matsawa, amma jikinsa bai amsa ba.
Haneefa ta lura. Ta ja baya, ta dubeshi da mamaki.
“As’ad… me ke damunka? Wannan ba kai bane. Gabanka ba haka yake ba...”
Zuciyarsa ta fara bugawa. Ya zauna da hannu a goshinsa. “Ban san me ke faruwa da ni ba…”
Daren yau ba kamar kowanne dare ba ne. Zuciyar Haneefah ta kumbura da ɗacin rai kamar an watsa mata gishiri cikin rauni. Da ya fice daga dakin da dare, zuciyarta ta bushe, tana ta tunani iri-iri kamar guguwar da ke neman karyar bishiya.
“Wallahi tallahi... bazan zauna da wannan mutumin ba,” ta fara magana da kanta kamar wacce ke tsaka da sihiri. “Idan bazai iya cika hakkin aure ba, me zanyi da shi? Sai dai ya sakeni kawai. Ni mace ce da take da buƙata! Allah ya kiyaye!”
Surutan ta suka cika falon nata falo mai ban sha’awa,Duk irin hakurin da As’ad ya barta da shi da ladabi da tausayi yana faɗin zai je yaga likita gobe, amma hakan bai hana ta zazzaga masa magana ba kafin ta buge da bacci cikin takaici.
A bangaren As’ad kuwa, fitowarsa daga gadon ya kasance cikin natsuwa da shiru. Wanka kawai yayi a cikin babban jacuzzi.Bayan ya gama, ya saka wata rigar alfarma ta Versace silk robe, ya ɗauki wayarsa ya kira
“Umar, get me an urgent appointment with Dr. Khalid private check, no delays,” yace cikin murya mai sanyi da kwarjini.
Ko mintuna biyar ba su shige ba, an shirya masa zuwa babban asibitin lafiya na masu kudi a Asokoro, Al-Burhan Executive Medical Centre. Wannan asibiti ne da ba kowa ke samun damar shiga ba sai masu kasaitacciyar rayuwa, inda kowanne dan kwastoma ke da sirrin daki da likita nasa na kai tsaye.
Ya shiga cikin mota Rolls Royce Phantom dinsa mai launin black onyx. Driver dinsa ya buɗe masa kofa yayin da ya zauna yana shaƙar turarensa na musamman “Creed Aventus”. Kallo ɗaya zaka yi masa ka san Yana cikin damuwa babba.
A lokacin da ya isa asibitin, Dr. Khalid ya karɓe shi da hannu bibbiyu. Tare suka shiga ofishinsa na sirri wanda aka tsara da kayan mahogany da kayan kwalliya na marmara daga Dubai.
“Dr. Khalid, I need your help. I’ve been experiencing some difficulty… with performance. Nothing works,” As’ad ya faɗa da murya mai cike da damuwa.
Dr. Khalid ya gyara zamansa. “You mean erectile dysfunction?” ya tambaya a nutse.
As’ad ya gyada kai.
“Toh, wannan matsala ce da ake kira da Erectile Dysfunction (ED) inda namiji ke kasa samun ko kula da tashi mai ɗorewa yayin saduwa. Saboda rashin motsin jiki, matsin lamba, diabetes, ko stress, wannan abu yana iya faruwa. Bari mu yi gwaje-gwaje daki-daki.”
Aka shigar da As’ad dakin gwaji, inda aka duba jinin sa, testosterone level, cardiac health, da kuma yawan cholesterol dinsa. Aka kwashe awa biyu ana duba shi da cikakken ladabi kamar shugaba.
A ƙarshe, likita ya dawo da sakamakon “There’s no infection, no chronic illness your blood work is clean. This seems like a psychological or emotional trigger. But let’s try a clinical remedy first. I’ll prescribe Tadalafil 10mg, once daily. It enhances blood flow and may improve your performance. But please relax and trust the process.”
As’ad ya karɓi magungunan cikin kwali mai kyau. Baiyi magana ba, amma tunaninsa ya cika. Zuciyarsa bata kwanta da yadda matarsa Haneefah ke kallonsa yanzu ba ba kamar yadda ta fara da shi da soyayya, biyayya da nutsuwa ba.
A daren nan da ya dawo daga asibiti, shiru ya mamaye gidan. Ya shige cikin sashen Haneefah cikin nutsuwa, ya tsugunna kusa da ita yana kallon idonta.
“Haneefah, ki gafarta min. Zuciyata ba dadi. Na dauki matakin da ya dace yanzu. Muna bukatar hadin kai. Magunguna na nan, lokaci zai nuna ko zasu yi tasiri. Let’s be patient.”
Ta kalle shi da idanu masu cike da damuwa, ta furta cikin daci, “Toh, amma wallahi... zuciyata bata ji daɗi ba. Ina jin kamar na rasa kwanciyar hankali na.”
Ya ɗauki hannunta yana shafa shi, sannan ya fice.
Da safe, lokacin da rana ta fara hango cikin tagogin gilashi masu kyau a cikin gidan As’ad, dakin Haneefah ya kasance shiru kamar ba kowa.
Cikin wannan yanayi, As’ad ya turo kofar cikin salo. Ya shigo sashen nata yana sanye da kaya masu kyan gaske white designer kaftan da takalmin “Tom Ford” slippers masu laushi. Fuskarsa a sake, ya matso kusa da ita.
“Haneefah, ya kika tashi?”
Ta ɗan ɗaga kai. “Alhamdulillah...”
Ya zauna a gefenta, Yana riko hannunta “Na fara amfani da magungunan. Wannan satin mu gani. Ina so ki taimaka min da kwanciyar hankalinki. Don Allah.”
Haneefah ta yi shiru. Sannan ta ce, “Ni fa, As’ad, ban ce bana sonka ba. Amma ni mace ce. Ma bukaciya abun da kowace mace ke bukata a zaman aure. Idan hakan ba zai samuwa ba, sai kace min me yasa nake tare da kai?”
Zuciyar As’ad ta ɗan murɗa. Wannan kalmomi sun sosa masa rai sosai. Amma ya lumshe ido, ya ce “Kina da gaskiya. Amma dole ne mu zama masu haƙuri. Likita ya ce a ba maganin lokaci.”
Yana fitar da wannan zancen, sai PA dinsa ya kira ta wayar sirri. Ya dan kauce gefe, ya karɓa.
“Yes, Umar? Oh really? The delegates from Morocco have landed? Ok... get the Rolls ready.”
Yana kashe wayar, ya dawo wurin Haneefah. “Zan je in karɓi wasu baki daga Morocco.
Kafin ya tashi, ya saka hannu cikin aljihu, ya fidda wata karamar kwalba. “Wannan Tadalafil ne. Na fara shan shi jiya. Let’s see what happens by the weekend.”
Ya fice daga dakin, yayin da Haneefah ta bishi da kallo mai cike da ruɗani da fatan alheri. Duk da zafin da take ji, tana fatan soyayya da mutunci za su warkar da komai.
*******
Kwana bakwai kenan tun lokacin da As’ad ya fara amfani da magungunan da Dr. Khalid ya bashi—Tadalafil 10mg, wanda ake amfani da shi domin magance matsalar rashin tashi (erectile dysfunction). Amma ko da yake yana shan maganin kullum, sai dai gaban nasa tamkar ya mutu gaba ɗaya. Baya motsawa, baya tashi. Ko a hankali bai nuna alamar sauyi ba. Wannan abu ya sake dagula masa tunani fiye da komai.
Gashi wayar Ayshatu, ta Paris, bata shiga kwata-kwata. Yana kiranta a waya, babu response, sai “The number you are trying to reach is currently switched off.” Wannan rashin samunta ya ƙara tayar masa da hankali. A kullum, tunaninta yana yawo a zuciyarsa kamar wani sihiri. Zuciyarsa na ƙaunarta fiye da kima, amma matsalolin gidan sun hana shi nutsuwa.
A wasu lokuta ma, in suna tare da Haneefah a cikin ɗaki, sai ta ji yana furta “Ayshatu… Aysha…” yana wata irin numfashi mai sanyi kamar wanda ke mafarki. Idan tayi magana sai ya ce da ita, “Yi hakuri, ban gane ba.” Kafin ya shafa bayanta da salo, yana ƙoƙarin sanya ta cikin jin daɗi. Yana amfani da salo kala-kalamassage, da kalmomi masu ratsa zuciya, da turare masu daɗin ƙamshi. Amma Haneefah tana jin tamkar ana cutarta. Bata gamsuwa da komai. Duk ƙoƙarin sa ya fadi ƙasa.
“Wallahi tallahi, As’ad... ka sakeni kawai!” ta faɗa da murya mai girgiza gidan. “Ni mace ce da nake da bukatu! Idan gaban ka baya aiki, bazan zauna ba... ni fa ba fatalwa bace! Ni mutum ce!”
As’ad ya tsaya kallonta da shiru. Fuskar sa ya ɗan ɗaure, wannan karon ba ladabi ya zo da shi ba. Ya ɗaga murya kaɗan, wanda ba kasafai yake yi ba. “To me kike so nayi?! Ban zabi wannan matsalar ba. Ina kokari. Ina biye da likita, ina shan magani. Me kike so nayi da zuciyarki Haneefah?!”
“Ka sakeni!” ta kara nanatawa cikin kuka. “Ni da kai ba zamu iya zaman aure ba. Ni ina bukata, kai kuma kana da matsala. Ni bana jin daɗin zaman nan!”
Cikin ɓacin rai, Haneefah ta juya, ta fice daga falon. Tana sharar hawaye, ta bar sa tsaye cikin dakini, wanda aka ƙawata da kayan Brazil, Dakin da aka kashe miliyoyin Naira akansa, amma zuciyar mutum ɗaya ta fi mahimmanci.
As’ad ya tsaya a tsaye, hannunsa a kugu, zuciyarsa kamar zata fashe. Shi wanda ake girmama a duniya, wanda ke da matsayi a kasa da ƙasashen waje, yanzu yana jin kansa babu amfani. Babu wata magana da zata iya kwantar masa da hankali a wannan lokacin.
Ya saka hannunsa a kai, ya furta da murya kasa, “Why me? Why now?”
Ya fice daga dakin ba tare da ya sanar da kowa ba. Ya shige cikin motarsa, ya bar gidan, babu inda ya nufa. Zuciyarsa ta cika da tunani. Shin ya rasa Haneefah? Shin Ayshatu ma ta juya masa baya? Shin matsalarsa zata gyaru?
Gaban sa kwance, zuciyarsa a ruɗe.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ASHIRIN DA SHIDA
Arewabook @nanadiso10
Murtala Muhammed International Airport (MMIA), Ikeja – Lagos.
Filin jirgin cike yake da hayaniya da cunkoso. Mutane na shige da fice, wasu na dawowa daga tafiya, wasu kuma na kan hanyarsu.
A tsakiyar wannan cunkoso, Ayshatu na tsaye mace ce da kallon farko ka san ba talakawa bace. Tsarinta da shigar da ta yi sun isa su ja hankali. Rigar Bubu Kaftan ce ja tsantsa, ɗinke da zaren silk. Takalmin kafarta Valentino heels ne, jakar hannunta kuma Chanel Classic Flap Bag. Gilashin idonta kuwa, mai kyau da tsari ne na zamani.
A bayanta, wata ƙaramar budurwa tana ja mata trolley bag tana faɗin:
“Ma, your assistant just called from Abuja.”
Ayshatu ta jinjina kai cikin natsuwa, bata ce komai ba. Matar da bata cika magana ba, amma tana da iko da izza.
Ko da take tafe cikin layin economy class saboda bata samu private jet ba wannan tafiyar, shigarta da kamalarta sun wuce matakin da take ciki. Idanun mutane na biye da ita, wasu na kallo, wasu na lekenta daga gefe.
Wayarta na hannunta. Tana danna lambobi tana bada umarni
“Habib, ku tabbatar an gyara gadona. Ku sauya duk bedsheets. Ene ta shirya dining area. Zan sauka Abuja nan da awa ɗaya. And don’t forget the scented candles lavender and white vanilla, as usual.”
Sai ga kira yana shigowa
"As’ad Habibie – Calling..."
Ayshatu ta tsaya cak. Idonta na kallon sunan da ya bayyana a screen, kamar yana magana da ita. Hannunta na shirin danna Answer, amma sai ta janye. Ta danna Mute, ta ci gaba da kallon tagar jirgi.
“Now you remember me? Sai na kusan kona maka zuciya da ƙaunata, wannan shine aurenka? Na shiga da zuciya ɗaya, amma ka wulakantani saboda wata mace. Sai ka yi dana-sani...”
Ta furta hakan cikin sanyi da tauri. Tana runtsa ido, ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi.
Flight: Air Peace P47216
Landing Time 10:10 AM
Destination Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja.
Da jirgin ya sauka, wata SUV kirar Mercedes-Benz Maybach GLS 600 na tsaye a bakin filin jirgi. Gaban motar an rufe da tinted, number plate ɗinta kuwa customized AS’AD01.
Direban ta, Nura, ya buɗe ƙofa cikin girmamawa yana murmushi
“Sannu da sauka Hajia. An shirya komai yadda kika tsara.”
Ayshatu ta zauna a kujerar baya cikin nutsuwa. Tana kallon waje ba tare da ta ce komai ba. Bayan mintuna uku, sai ta furta a hankali
“Nura... sai gida. Ban buƙatar magana a yanzu.”
***
As’ad na tsaye a cikin katafaren gym ɗinsa na gida. Tiles ɗin kasa marble ne, bangon gilashi yana barin hasken rana ya ratsa, LED lights na canza launi suna bada yanayi na jin daɗi da ƙarfin hali.
Yana sanye da Adidas Black-on-Gold Edition – rigar ta manne jikinsa, tana bayyana lafiyayyun tsokarsa. Yana ɗagawa da dumbbells masu nauyi, jikinsa na gumi, amma zuciyarsa ba a nan take ba.
“Ni da irin wannan jiki… irin wannan lafiya... gaban nawa ya kasa aiki? Why?”
Ya furta hakan a ƙasa, cikin takaici. Ya saki dumbbell ɗin da ƙarfi, yana takawa zuwa treadmill. Daidai lokacin, wayarsa ta fara ƙara. Idonsa ya sauka akan sunan da ya bayyana:
"Hajja - Calling"
Yayi murmushi mai ɗan sanyi, ya share gumi kafin ya ɗaga
“Assalamu Alaikum, Hajja.”
“Wa’alaikum Salam, ɗana. Ina ka shige? Na kira ka jiya baka ɗaga ba.”
Ya zauna a kan bench mai ƙarfe, yana jin sanyi na karfe a fatarsa.
“Hajja, a gafarce ni. Aikine ya ɗan shagaltar da ni.”
“Na kira ne in tunatar da kai. Kada ka yi wasa da addu’a. Duk da kai ba yaro bane, amma a gurina yaro ne. Ka dage da karatun Alkur’ani da azkar. Ka fahimta?”
As’ad ya share gumi daga goshinsa. Kalaman mahaifiyarsa na kara masa nauyi a zuciya.
“Na fahimta, Hajja. Zan dage.”
“Wallahi ka dage da alwala da addu’a. Ka kira sunayen Allah Ya Hayyu, Ya Qayyum, Ya Fattah, Ya Latif. Ka ga yadda Allah zai yaye maka damuwa. Ka koma ga mahalicci, ɗana.”
Zuciyarsa na nauyi. Ya amsa da salo mai tausayi
“Insha Allah, Hajja. Na gode.”
Tun safe, Haneefah ta tashi ranta ba daɗi. Da As’ad ya shigo falon da niyyar gaisheta kafin fita, sai ta tare shi da murya mai ƙarfi:
“Ni wallahi ba zan iya zaman aure da kai ba!”
Kallon da ta masa cike yake da bacin rai, idanunta sun nuna zuciyarta cike take da ciwo.
“Ka daina wasa da hankali na. Gaban ka kwance, ya daina aiki, amma kana so in zauna kamar ba komai. Ka sakeni kawai, As’ad!”
As’ad ya tsaya, ya lumshe idanu, zuciyarsa na bugawa
“Haneefah... kina ganin ban damu bane? Ko ba na ƙoƙari?”
“Ban ga wani ƙoƙari ba! Duk maganin da kake sha ba ya aiki. Kai yanzu ma kamar baka damu da jinina ba! Ni na gaji! Idan baka iya ba – to, zan fita, zan bar gidan nan. Zan nemi wanda zai iya rike ni da gaskiya!”
Ta juya da ƙarfi, ta buɗe ƙofa, ta fice da ƙyamar zuciya. As’ad ya tsaya a tsaye kamar gunki, zufa ya kwanta masa har gaban goshinsa.
Bai san wane mataki zai ɗauka ba.
Ya janyo wayarsa cikin rawar hannuwa. Ya kira abokinsa mafi kusa – Alhaji Farouq – wanda yake ganin tamkar dan uwansa ne.
“Farouq, ina buƙatar magana da kai sosai. Zuciyata tana neman fashewa.”
“Ka iso, ɗan’uwa. Zan jira ka a gidan yanzu.”
Bayan mintuna ashirin, As’ad ya iso gidan Alhaji Farouq da ke Maitama. Farouq na zaune a cikin garden ɗinsa an shimfiɗa kujeru masu laushi da teburin lemo da ruwa a kai, sai ganye da iska ke zagaye da su.
As’ad ya zauna, yana fitar da numfashi mai nauyi. Idonsa a kasa, kamar yana guje wa kallon duniya.
Farouq ya ɗan matsa kusa, yana kallonsa da damuwa:
“Lafiya dai?”
As’ad ya girgiza kai, muryarsa na rawa:
“Babu lafiya, Farouq. Gaba na... gaba na bai tashi. Na sha magani iri-iri, amma har yanzu babu canji. Yau kuma Haneefah ta ce in saketa. Ta ce zata nemi wani.”
Farouq ya gyara zama. Hankalinsa ya tashi sosai. “Subhanallah. Wannan abu ba mai sauƙi bane. Amma ka kwantar da hankalinka, dan’uwa. Aure yana da jarabawa iri-iri. Amma idan da gaske ka na lafiya kamar yadda likitoci suka ce, to akwai sauran mafita.”
As’ad ya lumshe idanu, yana jin hawaye sun kusa zubo masa:
“Na rasa yadda zan yi.”
“Za mu magance, in sha Allah. Sai da addu’a sosai da taimakon Allah. Wannan jarabawa ce, amma Allah ba ya jarraba bawan da ba zai iya ba.”
As’ad ya gyara zama, kamar mai karbar sabon ƙarfin zuciya. Farouq ya ce masa:
“Ka tafi gida. Ka neme ta da lallashi. Mace tana da rauni a jiki – ba a baki kaɗai ba. Ko da fushi take, ka biya mata bukata. Idan zaka faranta mata jiki, komai zai lafa.”
Tafiyar As’ad daga gidan Farouq ba kamar kowanne ba. Ya fito daga motarsa kamar jarumi mai sulhu da zuciyarsa. Sanye yake da kaftan fari, takalmi kirar Louboutin, da agogon Richard Mille.
Kafin ya shiga sashen Haneefah, ya tsaya a bakin ƙofa. Ya fitar da numfashi mai nauyi, ya yi shiru na dan lokaci. Sai ya taɓa handle ɗin ƙofar da sauƙi, ya tura ta a hankali.
A ciki, Haneefah na tsaye a gaban madubi. Sanye take da vest mai manne jiki da doguwar rigar barci mai laushi. Gashinta a waje, fuskarta cikin haske. Tana waya da wata kawarta da murya ƙasa-ƙasa.
As’ad bai tsaya neman izini ba. Ya matso da sauri, ya rungumeta daga baya. Hannunsa ya lallaɓeta a hankali, bakinsa yana sauka a wuyanta cikin zafi da ƙauna.
Haneefah ta yanke wayar da sauri. Numfashinta ya rikice:
“As’ad… me kake...?”
Shiru ne ya zame mata amsa. Bakinsa ya koma kan lebenta, hannunsa na cikin lallashi da sarrafa jikinta da natsuwa. Yana ƙoƙarin cike gibin da ke tsakaninsu ba kawai na jiki ba, har na zuciya.
“Biya mata bukatarta,” kalmar Farouq na sake karanto masa a zuciya. “Ko da tana fushi ne. Mace tana da rauni a jiki...”