Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 13

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 13

Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 13: Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 13. Haneefah ta birkice . Kalaman ta suka koma dirty talk, tana furta…

4,499 words

Haneefah ta birkice . Kalaman ta suka koma dirty talk, tana furta zafafan zance da murya mai raɗa. Hannunta yana kan kirjinsa, tana murza shi da ƙwarewa.

As’ad ya karɓi ikon da ta bari, yana sarrafa ta da cikakken hankali. No hesitation. No apology.

A daidai lokacin...

Ƙofar falon ta buɗe da ƙarfi.

Ayshatu ta shigo.

Ta tsaya cak.

Shikenan, anan muka dakata da FREE PAGES!

Kina/Kana son sanin yadda wannan labarin zai ci gaba da rikicewa, taɓa zuciya da yanke hukunci mai zafi?

To kada ka bari a barka a baya!

Domin samun cikakken littafin daga wannan wuri zuwa gaba:

Ku shiga Group ɗin Karatu ₦700 kacal!

Tura kuɗin zuwa

Account Name: Bilkisu Sani Kaura

Account Number: 7040402435 (OPAY)

Shaidar Biya?

Tura screenshot zuwa 09079274454 ko 07040402435 (WhatsApp)

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA ASHIRIN DA BAKWAI

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

******

Ayshatu ta tsaya a bakin ƙofar shashen Haneefah, cikin nutsuwa da izza. Kallon da ta yi musu ya nuna cewa ta fahimci komai.

As’ad da Haneefah suna manne da juna. Fuskar As’ad na kwance a wuyan Haneefah, bakinsa na goge fatarta. Hannuwansa biyu a bayanta, kamar yana riƙe da wani sirri. Amma da Ayshatu ta shigo, dakin ya yi shiru. Idanunsu suka haɗu da nata cikin razana da rikicewa.

Ayshatu ta tsaya da kafafunta cikin takalman Louis Vuitton stilettos. Rigar jikinta siliki ce, tana ɗauke da ƙamshi. Idanunta na cikin gilashin baki, amma kallon da ke cikinsu ya bayyana komai.

Murmushi ta saki – ba na farin ciki ba, murmushi ne mai ciwo, irin wanda ke ƙone zuciya amma ba ya hura hayaki.

Ta ce da laushi, amma da ƙarfi a sautin kalmarta

“Na zo ne mu gaisa da amarya. Ashe kuwa na yi kuskuren shigowa ba knocking. I’m sorry... ku ci gaba da soyayya lafiya.”

Ta juya, da siririyar dariya a laɓɓanta.

Haneefah ta bita da harara, cike da zafin rai. Ta juya ta kalli As’ad, ta sa hannu cikin wandonsa tana neman jin wani motsi daga jikinsa. Sai kawai ta janye hannunta da sauri, ta ja tsaki.

Ta fara magana cikin murya mai zafi

“Tunda ba zaka iya ba, wallahi ni zan bar maka gidan nan. Ni fa ba zan zauna da namiji da ba zai iya gamsar da ni ba! Ba dai dabino mara ƙwari ba!”

As’ad ya tsaya da ido biyu, ya lumshe su. Bai ce komai ba.

Da Ayshatu ta fita daga falon Haneefah, ba ta ce komai ba. Amma jikinta ya nuna komai. Tafiyarta ta nuna izza da ƙarfin hali. Ko da kuwa zuciyarta na tafasa, ba ta bari wani ya gane. Idanunta sun cika da hawaye.

Tana shiga bangarenta, ta rufe ƙofa a hankali. Ba ta zauna ba; ta tsaya a gaban madubi, ta cire rigar jikinta, ta zuba wa kanta ido.

“How did I get here?”

ta furta cikin sanyi. Wani azababben kuka ya cika mata idanu. A hankali ta zauna a gefen gadonta mai santsi. Ta cire takalmin kafarta mai tsayi, ta ɗora kafafunta kan benci. Ta ɗauki wayarta, sai kuma ta ajiye, ta ja wani azababben kuka.

“I saw what I saw. You made your choice. I’m not a woman you play with, As’ad. Wallahi kai da mace, har abada.”

Ta faɗa, tana buga wayarta gefe. Tana kara rushewa da kuka mai tsanani.

****

As’ad ya juya ya fice daga dakin cikin shiru, zuciyarsa tana cike da rikicewa da nauyin damuwa.

Ya wuce sashensa kai tsaye. Ya cire kayan jikinsa, ya sa farar riga da navy blue suit. Ya gyara agogon hannunsa, ya shafa turare mai ƙamshi. Amma saboda yadda zuciyarsa ke masa zafi, sai kawai ya tsaya yana duban kansa a madubi. Fuskarsa na nuna rauni da rudani.

Ya sake juyowa, ya koma sashen Ayshatu.

Yana shiga, dakin ya cika da ƙamshi mai laushi – kamshin lavender da vanilla. Falonta na da tsari da tsafta. Fitilun dakin suna haskaka komai cikin kwanciyar hankali. Yana takawa cikin nutsuwa har ya isa bakin dakinta.

Ayshatu ta fito daga toilet sanye da tawul ɗaya. Ruwa yana gangarowa daga fatarta mai sheƙi. Ganinta ya tada masa wani abu a cikin zuciyarsa, kamar an ɗauke masa wani dutse daga kirji.

Bai ce komai ba. Ya rungumeta kai tsaye. Ya lumshe ido, yana zura kansa a gefen wuyanta, yana sauke numfashi kamar wanda ya dawo daga tafiya mai nisa.

“Aysha... na yi kewarki. Kin tafi, kin barni ni kaɗai. Kin bar zuciyata a cikin duhu.”

Ayshatu ta tsaya a rungumarsa, ba ta motsa ba. Sai kawai ta dan saki murmushi – murmushi mai laushi da sanyin zuciya. Ta kalle shi cikin ido.

Ya ce da murya mai rauni

“Ke ce kaɗai nake da kwanciyar hankali tare da ke. Don’t let go. I’m losing myself.”

Ya shafa wuyanta da hannunsa. Yaji wani mugun sanyi a ransa. Ya rasa wacce kalar so yake yi mata.

Ta dafa kafadarsa, ta ce a hankali

“Ka ce ka yi kewata? To ka tabbatar. Ba da magana ba, da aiki.”

As’ad ya sauke ajiyar zuciya. A hankali, jikinsa ya motsa kadan. Ya saki murmushi yana kallonta cikin ido.

“Har yanzu fishi kikeyi dani akan abin da banda ikon canzawa, Ayshatu? Kin fi kowa sanin idan tanine to tabbas mu mutu mu biyu. Idan dan nene, Ayshatu, ba zan tsaya ga kowacce diya mace ba. Ke kadai nake gani mace ta kwarai, mai kaunata, mai kuma girmama ni. Don Allah.”

Wani kallo ta juyo tana yi masa, mai cike da takaici, ta ce

“Habibie, shikenan! Kullum iyayenka cikin yimaka aure. Kullum kawai dan a kuntatamun. Ina kai, ina Haneefah – yarinyar da ta gama raba jikinta ga maza? A cikin masu daraja, ba za a taba ambatarta ba! Ita ce za a baka?! Ina kishinka, ina kaunarka. Duk waɗanda ake aura maka, ban taɓa tofa komai ba. Amma Haneefah – bata cancanci tsaftataccen mijina ba, wallahi.”

Tsayawa yayi yana mata kallon kauna. Sai ya ɗago fuskarta, ya aza bakinsa a kanta, ya ɗan ɗauki lokaci yana kissing nata. Bayan ya janye, ya ce

“Allah ya yi miki albarka. Amma umarnin iyayena ba zan iya ja ba, Ayshatu. Ki yi haƙuri, kin ji? Matar Habibie... Zan je meeting yanzu. Amma idan na dawo, sai mu yi magana.”

Ayshatu ta ce da laushi

“Allah ya dawo min da kai lafiya. Duk abinda ka je nema, Ubangiji Allah ya baka, Habibie. Ya kula min da kai...”

Wani sanyi ya ji a ransa sosai. Ya sumbaci gefen kumatunta, sannan ya fita.

Wani zafi mai raɗaɗi ne yake fita daga cikin kirjinta. Ta tuna yadda ya rungumo Haneefah jin hakan ya ɓarke mata da wani hukuncin zuciya cewa rabuwarsu ba ta isa ba. Ya kamata ta ƙara ɗaukar mataki, dan kwanciya da mijinta ba za ta bari kowace mace ta yi ba.

Wani irin ciwon ƙishi take ji, amma kasancewarta mace mai tabbataccen tunani, ta san cewa rabuwarsu tuni ta kammala. Wannan ya sa wani sanyi ya fara shiga ranta sanyi mai haɗe da tsananin raɗaɗi.

***

Da zarar As’ad ya fice daga shashen, Haneefah ta birkice. Masifa ta ko’ina. Tana yawo cikin ɗaki kamar wacce aka watsa wa ruwan zafi.

Zuciyarta na tafasa da ƙiyayya, kamar an zuba mata toka a rana. Tana jin kamar ta fashe da kuka, amma ta fi zaɓar zagi.

“To wai waccan ita ce Ayshatu yanzu?! Na yi mamaki wallahi! Ashe dama haka ta koma? ‘Yar gayu ce? Kyakkyawa?!”

Ta ja dogon tsaki mai cin rai, ta nufi gaban wardrobe. Tana buɗewa da hanzari, ta ciro trolley. Ta zazzage kayanta mafi muhimmanci passport, kaya masu tsada, da 'yan kayan shafe-shafe – tana ajiye su a ciki.

Ta ɗauki wayarta, ta kira ɗaya daga cikin direbobin gidan.

“Ka shirya mota. Zan je filin jirgin sama yanzu.”

Ba ta tsaya jiran amsa ba. Cikin gaggawa, ta fara yin online booking na jirgi, ba tare da wata tantama ba. Zuciyarta tana bugawa da wani nau’in ƙiyayya da ba ta saba da shi ba. Ji take kamar ta yi ihu, ko ta mare iska.

“Wallahi ba zan zauna da namiji mai kama da mata ba!”

A cikin kasa da awa biyu, tana tsaye a layin shiga jirgi. Ba ta wa kowa sallama ba. Ba ta waiwaye gidan ba. A zuciyarta, ta rufe shafin As’ad har abada.

Da ta sauka a garinsu, ta kira gida

“A aiko min da direba yanzu-nan. Ina filin jirgi.”

Lokacin da ta isa gidan sarki, ta nufi dakin Hajja kai tsaye. Da ta shiga, sai ta faɗa kan Hajja da kuka sosai.

Hajja, Fiddausi, da Abba suna zaune suna hira. Cikin sauri suka juyo da mamaki. Sai dai Fiddausi ta yi murmushi ƙasa-ƙasa, kamar wadda ta san abin da ke faruwa. A ranta, tana fadin “Ai duk fitinar uwarki ba ta kai matar yaya ba. Ita fa bata taɓa bari ki zauna.”

Hajja ta ɗaga murya

“Haneefah, Subhanallah! Lafiya? Me ya faru haka da daddare? Kodai tare kuke da shi ne?”

Haneefah na kuka sosai, tana girgiza kai cikin rashin iya magana. “Ni ba zan iya zama da losarin namiji ba, wallahi! Ni dai ya sake ni! Na gaji da shi. Ko ya haƙura, ko kada ya haƙura wallahi Allah, na gama! Namiji ne, Hajja mai kama da mata!”

Ta fashe da kuka mai ƙarfi, kamar zuciyarta na ƙoƙarin fasa ƙirji ta fito.

Abba ya miƙe a hankali, yana kallon Hajja da damuwa a fuskar sa. Kamar yadda sauran matan 'yan uwansa suke zuwa suna cewa ya sakesu, wannan kuma ita ce ke ambatar asaketa. Wannan ya sa ya kulle zuciyarsa.

Hajja ta yi masa alama da yaje ya sanar da Mai Martaba. Ya jinjina kai cikin ladabi, ya tafi.

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA ASHIRIN DA TAKWAS

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

******

Wajen ƙarfe tara na dare, ina zaune a dakina lokacin da na jiyo muryar Abba daga cikin falo. Yana cin abinci yana magana da Mumy cikin lallashi da salo mai sauƙin kai.

“Ina ganin lokaci yayi da zan fitar da Ramlah waje... ko India ma ne inda Yaya Usman ke zaune. Na san zai kula da ita sosai, kuma zata iya cigaba da karatunta cikin kwanciyar hankali.”

Ya ɗan yi shiru sannan ya kara da cewa,

“Kinsan Usman da Auta, sai Allah zaiji dadi sosai idan Ramlah taje can.”

Sai da Mumy ta ja lokaci sosai tana gyara zancen kafin ta buɗe baki tace,

“Abban Ramlah… ban ce Auta kada ta tafi ba. Amma danAllah, kada ka dauke min Ramlah. Wallahi zan shiga damuwa. Ka samo mata makaranta anan kusa da mu, ko babbar jami’a ce, zan fi jin daɗi. Ita kadai nake da ita yanzu da ke bani nutsuwa.”

Na ji Abba yayi shiru na ɗan lokaci, kafin ya ce da ƙasa da murya,

“Kai Zainab… Allah ya zuba miki son yara. Allah ya saka da alheri.”

Na ji Mumy tana sauke ajiyar zuciya tana cewa,

“Bazaka gane ba, Abban Ramlah. Wallahi yadda nake jin Ramlah... haihuwarta ce kaɗai ban yi ba. Allah ubangiji ya raya ta.

Daga can, sai na kuma jin Abba ya tambaya da damuwa,

“Kin basu kuɗin kula da kansu kuwa? Naga kan Ramlah ya tsufa kamar bata je wankin kai ba.”

Mumy ta amsa da sauri, tana cewa,

“Ni wallahi so nake ka yimata faɗa akan rashin tsafta. Jiya babu yadda ban yi da ita ba, tabi Billy ta wanke kai, amma sai ta nace wai ba yau ba.”

Abba bai ce komai ba, sai kawai ya ɗaga kansa yace

“Allah ya kyauta.

Ina zaune a ɗaki na, shiru kake ji sai hucin numfashina. Cikin yanayi na baƙin ciki da ɓacin rai, na ji hawaye sun cika min ido. Na turo su a hankali suka fara malala kan kumatuna kamar ruwan sama a gaban tagar dare.

“Wanne irin makirci ne haka Mumy ke min?” Na tambayi zuciyata. Ni ina fama da kuraje a gabana, kurajen da ke sa min zafi, wari, da kunya. Duk yadda nake jurewa, babu abun da nake iya faɗa mata, domin kowane yunkuri na zama magana sai ya koma masifa daga gareta.

Yanzu ma, na tara ruwan zafi da gishiri, ina shirin gwada wanke gaban nawa, ko Allah zai bani sauƙi. Amma ita can tana cikin dakin falo tana ɗora wa Abba karya akan gaskiya, tana ɓata mini suna a idanunsa.

Wallahi ranar… ranar da zazzabi ya rufeni sosai, har jikina ya kasa, shine da asubah Abba ya tashe ni wai in masa koko kafin tafiyarsa. Duk da cewa jikina babu ƙwari, na nace na tashi. Na gyara masa wajen, na dafa masa koko, nahada masa harda kosai, sannan nagyara gidan a daddafe tunda Mumy ba za ta karɓi uzurina ba.

Yayin da Abba zai fita nace masa

“Abba... inason zuwa asibiti...”

Yace da mamaki,

“Me ke damunki?”

Na ɗan duburburce cikin ruɗani, nace,

“Zazzabi...”

Caraf! Sai naji muryar Mumy daga falo kamar tana jirana

“Yanzu dan zazzabi ne zaki tafi asibiti? Ko kinsanar da? Yanzu auta ina gidan nan amma baki samuna kisanar dani? ni inada maganin zazzabi Zan dakko miki.”

Na kalle ta, na lumshe ido, nace,

“To Mumy…”

Na mike jiki a sanyaye, ina jin ciwon wannan yaudarar datakeyiwa abba Nabar gurin cikin kamewa da shiru. Zuciyata kamar tana ƙuna. Amma ban ce uffan ba. Saboda nasan komai zan faɗa, cikin tsautsayin zuciyarta, bazata taɓa fahimtata ba.

Kwanaki uku kenan ina cikin rashin daɗin jiki. Ba kamar da ba, duk motsina sai da wahala. Amma Mumy, kamar ta fahimci cewa ina cikin buƙata musamman buƙatar kuɗi sai ta fara saka ido kan duk wani motsi na. Ta hana ni kusantar dakinta. Ko da canjin aike ne, sai ta duba ni da idanu masu cike da tambaya, ta ce sai na ba ta kudinta. A wasu lokutan har matsawa take yi akan nadaina ɓoye mata kudinta bata son sata.

A yanzu haka, Islamiyya kaɗai ce mafakata. Na saba fita da safe, na je Makaranta amma yanzu munyi candy muna ma jiran result dinmu ne wannan satin sai dai dayake ina zuwa Islamiyya, daga nan na dawo gida cikin shiru da kadaici tunda banda iko yanzu ko zaman palon danakeyi ina kallo shima sai yazamana laifi tace Indaina samata ido a falonta.

Yau ma dai, na tashi da niyyar karɓar system ɗina daga inda na ɓoye shi. dayake musa idan yakawomun sai yasanya acikin fulawowi na gidan mu Na lallaba naje na dakkona saka shi cikin kayana yadda babu wanda zai sani nasan da momy tasan da system din da tuni tasanya abba ya kwaceta amma kasancewa ta manta inada ita yasanya bata Sanyashi ya ƙarba ba. Na gyara gidan nakuma dora spaghetti da miya da salad dana gama sannan nagyara gurin sannan na nufi Islamiyya kamar yadda nake yi kullum.

A hanya, zuciyata na cike da tunani abaya momy tazama tamkar uwata Ayanzu kuwa duk duniya nice makiyarta ko kallona bataso tayi. Amma da na isa Islamiyya, sai Shamsiyya ta karɓe ni da murmushi. Ta dubeni da kulawa, ta ce “Lafiya kuwa? Naganki wani iri yau badai mumy bace ba?” Na ɗan yi shiru, sannan na ce, “Lafiya lau kawai yau ne banajin dadi.” A zahiri dai ita ce kaɗai nake iya faɗa wa damuwata saboda ta fi kowa fahimtata sannan tana bani shawara Kuma tana cewa in dage da Addu'a.

Na nemi alfarma a wurinta. Na ce mata, “Dan Allah, idan mun gama, ki raka ni gidan Kakata.” Ta ce, “To, ba damuwa.” Har ma ta ara mini kuɗin mota ba tare da wata gardama ba. Wannan abin ne ya taɓa zuciyata irin kulawa da fahimtar da ban saba samu ba.

Da ƙarfe huɗu, muka nemi uzuri a wurin malam ɗinmu, muka fice. Mun isa gidan Kakata cike da fatan samun nutsuwa ko mafita, amma muka tarar kofar a kulle. Wani makwabci ne ya bayyana mana cewa har yanzu ba ta dawo ba. Na yi masa godiya cikin ladabi, sannan muka juya muka koma gida.

Washegari yakama laraba Haka Abba ya yi sallama da kowa, ya fice daga gidan cikin natsuwa, kamar yadda na saba ganin sa idan zaiyi tafiya mai nisa. Na ji yana gaya wa Mumy cewa zai kwashe kusan sati biyu cameroon. A zuciyata, daɗi ya fara lulluɓeni na zaci zai bani ko da kadan ne na kudi. Ina fatan zai ce “Ramlah, ga wannan, ki siya magani ko ki yi wata buƙatarki da shi.”

Amma har ya ƙarasa mota, har motar ta tashi ta ɓace da kura a kan filin gidanmu ko sisi bai bani ba. Na tsaya a tsakar gida ina kallon ƙofar da ya bi, zuciyata cike da baƙin ciki da tambayoyi marasa amsa.

Tun jiya jikina ke fama da zazzabi, yana min illa sosai. Amma Mumy, wadda a da take da tausayi, yanzu kamar bata damu ba. Ko cikakken kallo ban isheta ba yanzu ko sannu Ko magani bata bani. Ko kallon damuwata ma bata yi. Ina kwance a ɗaki, jikina kamar an cika shi da ƙaya, amma babu mai damu da ni ko ya tambayi lafiyata.

Na lallaba da ƙyar na tashi, na nufi wajen Yaya Billy. Na tsaya a gabanta cikin ladabi da kwanciyar murya, nace:

“Don Allah, ki taimake ni da dubu ɗaya—ko da aro ne, sai na biya.”

Sai ta ɗago kai tana kallona da raini, tace:

“Idan kika ƙara damuna da irin wannan maganar, wallahi sai da mari! Tunda ba ni ce na haifeki ba, to ki sani kar ki raina ni!”

Na tsinci kaina cikin baƙin ciki. Na cije lebena na ƙasa, hawayen takaici suka cika idona. Nace mata kawai: “To.” Na juya da baya, cikin shiru da nauyin zuciya.

A wannan rana na gane cewa baƙin ciki da ƙunci ba wai daga talauci kawai yake ba – wani lokaci daga rashin ƙauna da kulawa ne daga waɗanda kake ɗauka tamkar iyayenka.

Yau ba mu da islamiyya, haka kawai na tsinci kaina a zaune a farfajiyar gidanmu ina sauraron rediyon da Musa ya kunna. Shirin "Indaranka" nake sauraro, wanda yanzu ya zama tamkar abokina mai debe mini kewa, musamman da yanzu nake cikin rashin walwala saboda rashin kudi da rashin yadda zan samu Korean films da na saba kallo a computer dina. Har sau uku Musa yana turomin, amma yanzu naji kunya na sake zuwa na roƙe shi ya ƙara turawa.

Ina cikin wannan tunanin, sai ga Mumy ta fito daga cikin gida, cikin wani haɗaɗɗen lace mai launin shuɗi da fari wanda ya matuƙar yi mata kyau. Gaskiya, in banda ƙyashi, Mumy ba ƙaramar kyakkyawa ba ce, musamman idan ta shiga irin waɗannan kayan da suke fidda ainihin kyau da kamalarta. Ta iso gabana tana kallona da ɗan murmushi kadan.

"Ke, Ramlah, ni zan fita zuwa bikin gidan Alhaji Wakili. Ki tabbata kin ƙara gyara gidan nan sosai kafin na dawo. Sai wajen ƙarfe tara na dare zan dawo. Kuma ki bar girkin yau, sauran shinkafar da ke tukunya ku ci ita da masu gadi."

Cikin girmamawa na amsa mata, "To, Allah ya kiyaye hanya Mumy. Sai kin dawo lafiya. Yaya Billy ma Allah ya kiyaye."

Yaya Billy tana kallona ta watsamin wata muguwar harara, ko amsa sallamar ba ta yi ba. Ta ɗauke kai kamar ban wanzu ba, suka shiga mota, suka ja suka fice.

Wani mugun daɗi ne ya ziyarci zuciyata, na shiga cikin gida da sauri kamar wanda aka ce masa an raba kuɗi. Na tafi kai tsaye saman gidan, ɗakin Mumy na nufa, zuciyata tana bugawa saboda tashin hankali da fargaba.

Na buɗe ɗakin a hankali, turaren alfarma da ƙamshi ya karɓe ni nan take. Na nufi inda ta aje turarukanta, na ɗauki kwalabe na tsiyaya cikin wata ƙaramin leda, zuciyata na bugawa da sauri saboda tsoron a kama ni. Na duba cikin ɗakin ko zan samu kuɗi, ban samu ko sisi ba. Sai da na juya zan fita, sai idanuna suka kai ga wardrobe ɗinta wanda yake buɗe kaɗan.

Cikin hankali na matsa kusa da wardrobe ɗin, zuciyata na cigaba da tsananta bugawa. Sai kawai na hango wasu sababbin kuɗi 'yan dubu-dubu masu yawa sosai. Take wani sanyi ya ratsa jikina, naji wani irin farin ciki mai gauraye da tsoro yana ziyartar zuciyata.

Hannu na rawa, jikina na ɗan karkarwa, na tsamo guda goma sha biyar. Wallahi idan ka ga yawan kuɗin nan zai fi dubu ɗari biyu! Na tabbata babu yadda za ayi Mumy ta lura. Na lulluɓa kuɗin cikin ledar da na ɗauko na saka turarukan, sannan na zuba ɗan maclean guda biyu ciki don na ɓoye sirrina.

Cikin sassarfa da taka tsan-tsan na fito daga ɗakin, na kulle ƙofa yadda babu wanda zai gane cewa wani ya shiga. Na sauka ƙasa da ƙafafu masu nauyi da zuciya mai nauyi amma cike da farin ciki na shiga ɗakina. Nan na adana kuɗin ƙarƙashin kayan jikina, na ɗan yi ajiyar zuciya sannan na kwanta a kan gado ina kallon saman rufi, zuciyata tana faman tunani.

Wallahi babu wanda zai fahimci irin radadin da zuciyata take ji saboda halin da nake ciki, sai wanda ya gani da idanunsa. Na sani wannan abu ne mara kyau, amma kuma ban da wata mafita da ta wuce wannan a yanzu.

Ina tsaye a harabar gidanmu cikin ɗan nisa daga ƙofar gida, sai ga Musa ya nufo ni cikin sauri. Ya tsaya a gabana yana huci kamar wanda ya zo da saƙo mai matuƙar muhimmanci.

“Ramlah…,” ya kira sunana da wata murya mai ɗauke da damuwa, “ga wata baiwar Allah a waje tana nemanki. Wai tana cewa danAllah ki fito.”

Na ɗan runtsa ido, zuciyata ta buga. “Wacece?” na tambaye shi, ina ƙoƙarin fahimtar me ke faruwa.

Musa ya ɗan sunkuyar da kansa, sannan yace, “Tace wai tana kama da abbanki...”

Baki na na ɗan buɗe, amma ban ce komai ba. Na ɗauki hijjab dina na zura a hankali, zuciyata cike da tambayoyi da shakku. Ina fita daga ƙofar gidan, idona ya sauka kan wata mota mai launin toka da ta ke a bakin titi. Na leƙa cikin motar a hankali…

Sai ga Umman Khalil...

Zaune take, idonta jajir kamar wacce ta shafe sa'o’i tana kuka. Fuskar ta kumbura, ta cika da damuwa. Na matso da takaici da fargaba, zuciyata na bugawa da karfi.

“Umma… lafiya?” na tambaya cikin murya mai sanyi, amma da karfin tashin hankali.

Ta buɗe kofa tana cewa, “Ramlah danAllah ki shigo. Mu tafi wajen Khalil...”

Zuciyata ta ɗaukaka kamar za ta tsinke. Kafafuna suka yi sanyi. Naji kamar ana janyo zuciyata da igiyar baƙin labari. Babu shiri na shige cikin motar. Driver ya ja motar, numfashina na rawa, zuciyata na doki da fargaba me ya faru da Khalil?

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA ASHIRIN DA TARA

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

A fadar Mai Martaba, hasken fitilun lantarki sun kawata falon zauren masarauta, suna sheƙi bisa ƙayatattun shimfiɗun da aka tanada musamman ga manyan masu fada-a-ji. Masu hidimar fada suna tsaye cikin girmamawa, yayin da manyan matan gidan sarauta suka haɗu bisa ga alfarma da ƙasaita.

Fulani Maryam (Mahaifiya ga haneefah) uwargidan Mai Martaba, tana zaune cikin shiga ta musamman mai bayyana matsayinta a gidan sarauta, tana lumshe idanu cikin wata irin annashuwa da farin ciki, Hajja ma da sauran matan Nasa suna zaune cikin shiga ta alfarma.

Cikin wannan yanayi ne Haneefah ta shigo zauren, kuka da hawayenta suka mamaye hankalin kowa da ke cikin zauren. Ta zo da sanyin jiki, tana tafiya cikin rawar kafa har zuwa gaban Mai Martaba Sarkin . A hankali ta zube bisa guiwowinta, ta fashe da kuka mai ban tausayi.

Gaba ɗaya idanun fada suka dawo kanta. Zuciyar Mai Martaba ta tsananta bugawa da zafin fushi. Muryarsa ta fito cikin ƙasaita da izzar sarauta.

"Menene ya faru, Haneefah? Wane abu ne ya sameki har zaki shigo mini fada da kuka irin haka?"

Cikin rawar murya da shesshekar kuka, Haneefah ta ce,

"Allah yakara maka lafiya… As’ad... ba shi da lafiya! Ya kasa cika haqqinsa na aure. Gaba ɗaya ya zame min wani abu daban. Ni wallahi na gaji da zama da wanda ba ya iya sauke haqqin aurena. Ya sake ni na dawo gida. Wallahi bazan koma masa ba."

Muryarta ta ƙare cikin kuka mai cike da tausayi, tana ɓoye fuskarta cikin tafukan hannuwanta.

Wannan magana ta girgiza zauren. Duk wanda ke cikin fadar ya shiga al'ajabi da razana.

Cikin fushi da tashin hankali Mai Martaba ya ɗaga murya yace da babban hadiminsa,

"Wambai! Ka aika wa As'ad. Ina son ganinsa a gabana da sassafe ya bayyana!"

Wambai ya amsa cikin ladabi,

"Ranka ya daɗe! an gama."

Fulani Maryam, zuciyarta na rawa da farin ciki, amma tana kokarin ɓoye murmushinta domin kar ya bayyana fili. A cikin zuciyarta tana cewa,

"Allah ya kawo mini ƙarshen wannan yaron aiki yaci."

Tana ɗan ƙarewa Hajja Sa'adatu, Matar Mai Martaba kuma mahaifiyar As’ad, kallon gefe. Tabbas wannan abu ya girgiza zuciyar Hajja, domin tuni hawaye sun taru a idanunta. Ta ɗauko mayafinta ta share kwallarta da sanyi, muryarta na raɗaɗi cikin zuciyarta tana cewa,

"Allah ka jiƙan zuciyar ɗana. Ya ubangiji ka kawo masa sauƙi."

Ƴan uwa da sauran matan Mai Martaba suna gefe suna raɗa-ɗi tsakanin su, wasu da al’ajabin faruwar lamarin, wasu kuma cike da rashin jin daɗin wannan abu da ke neman ɗauke martabar gidan masarautar.

Mai Martaba ya juya ya dubi Haneefah cikin yanayi na tausayi da izza, yace,

"Ki kwantar da hankalinki, Haneefah. Duk wanda ya ɓata miki rai, babu shakka zai gane kurensa. Fadana ba wurin wulakanta jinina ba ne."

Haneefah ta ɗago kanta cikin shaukin kuka, tana duban sarki cikin soyayya da godiya, amma zuciyarta ta riga ta gama yanke hukunci. Auren ta da As’ad ya gama zama tarihi a zuciyarta.

Cikin wannan yanayi ne dukkan wanda ke cikin fadar suka ji sanyin fargabar abinda zai biyo baya idan gari ya waye.

**********

Yau dai ranar As'ad ce ta kasance mai cike da ƙalubale da aiki tun daga safe har zuwa lokacin da rana ta yi zawali.

Fitattun fitilun zinariya na office ɗinsa ne suka haska ko'ina, suna ƙara bayyana ɗaukakar dukiyar da Allah ya mallaka masa. Kujerarsa ta fata mai launi irin fari da duhun ruwan kasa tana zagaye da kyawawan teburori masu ɗauke da litattafai da takardu masu muhimmanci.

A zaune yake a kujerar mulkinsa, cikin wata irin yanayi na tsananin damuwa da tunanin da yake ƙoƙarin samun mafita. Kwana biyu kenan yake fama da wani irin azababben ciwon kai wanda ya hana shi sukuni sosai. Amma babu abinda ke damunsa fiye da yadda zuciyarsa ta sauya gaba ɗaya tun bayan dawowar Ayshatu.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull