Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 17
Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 17: Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 17. As’ad ya matso da kulawa, ya fara shafa ta da salo Kowane motsi…
4,448 words
As’ad ya matso da kulawa, ya fara shafa ta da salo Kowane motsi nasa kara Rikitata yakeyi.
Ayshatu ta buɗe kanta gaba ɗaya ta sake jikinta, ta mika kanta, zuciyarta ta amince da kasancewa duka da shi. Tunaninta ya zube, jikinta ya amsa masa, har sai da ta kai ga matsayi na salama, ta ji kanta kamar tana shawagi cikin farin ciki.
Bayan sun gama, sai ya ɗauketa a hankali kamar jaririya, ya kai ta bathroom. Suka yi wanka tare, da kulawa da dariya mai sanyi.
Da suka dawo daga wanka, ya shimfiɗa ta akan gado, yana shafa mata kafafu da man tausa mai ƙamshi. Sannu a hankali, ta fara lumshe ido, har bacci ya ɗauke ta.
Yana zaune yana kallon fuskarta. Ya shafa gashinta, yana fadin "Allahumma baarik feeha… Allah ka kare min ita." Sannan ya tashi, ya shirya cikin kaya masu salo da tsari.
As’ad ya fita cikin custom-made Tom Ford suit, yana jin iska a cikin zuciyarsa. Direban sa ya buɗe ƙofar motar Rolls-Royce Cullinan, suka nufi wani babban wuri da yake da meeting da wani kamfani masu kayan kitchen da yake shirin kawo su Nigeria.
Yana cikin mota, sai wayarsa ta ɗau kira. Ya duba Nawal autarsa, karamar yarinyarsa da ke dubai.
Ya ɗaga, yana murmushi.
"Daddy!" ta ce cikin muryarta mai laushi da girmamawa.
"Ina kwana, my princess?"
"Daddy... ina son zuwa Umrah da friends dina su uku. Amma kuma motata tayi old model yanzu. Na gaya wa Umar, yace wai ba zai canza mun ba..."
As’ad ya yi murmushi
"Ki turawa P.A. duka bukatunku. But kisani mutunci shine gaban komai, Nawal. Kiyaye sunan mu. Idan wani ɗabi’a marar kyau ya fito daga gareki, I’ll take harsh action ki sani."
"In shaa Allahu Daddy, bazan taba baka kunya ba," ta ce da ladabi. "Nagode sosai. Allah ya kara maka arziki."
"Amin baby. Take care." Ya kashe wayar da natsuwa, lokacin da suka iso wajen meeting.
******
Ba tare da wata addu'a ba, Ayshatu ta buɗe idanuwanta cikin lumana, zuciyarta cike da jin daɗi da kwanciyar hankali.
Ta sauka daga gadon cikin silken nightdress na Victoria’s Secret, ta nufi bathroom da kafafu masu laushi a kan Persian carpet, inda ta yi brushing da miswak ɗin mint da Classic Marvis toothpaste. Bayan haka, ta fito zuwa falon suite ɗinta.
A hankali ta buɗe Hermès handbag dinta ta dakko haɗin ayar da ta saba sha domin ƙarfafa lafiyarta da inganta metabolism. Wannan haɗin na ƙunshi
Aya (dates),Kaninfari (clove),Citta (ginger),Habbatussauda (black seed),Fennel seed.
An nika su duka tare da blending na musamman daga gida. Tana shan su ne da organic fresh milk ko nono ba tare da ƙara sugar ba. Ita dai Ayshatu cikakkiyar mace bce tana da sirrin lafiyar da take riƙe sosai
Tana cikin shan hadinta a cikin kofi , sai aka kwankwasa ƙofa a hankali. Personal staff ɗinta ya buɗe ƙofar da ladabi, ya kawo mata special Turkish breakfast platter a kan tray.
Simit mai sesame,Menemen da kaza,Kofi na kahve,Tufafin cucumber da olives masu sanyDa natural honey a cikin ƙaramar tulip bowl
Ta yi murmushi cikin natsuwa, ta ce, “Saka a kan glass table,” sannan ta ci gaba da shan hadinta tana kallon hasken safe daga saman Bosphorus.
Wani siririn mugun murmushi ya bayyana a gefen leɓenta yayin da ta jingina a kujerar fur da ke falon. Ta ɗaga kofi ɗinta tana shan hadin ayar da ladabi, zuciyarta na cike da farin ciki da nasara.
“Duk dai masifar da iyayen As’ad suka ƙirƙira… Na aura masa mata yanzu dai babu su. Babu kuma wani ‘bari in tambaya’ ko 'bari in jira’. Wannan aure ya tabbata. As’ad ya zama cikakken mallaki na ni kaɗai.”
Ta lumshe ido, tana jin ƙamshin lavender da ke tashi daga turaren dakin. Zuciyarta ta ji wani irin daɗi daɗin mace da ta san ta yi nasara ba kawai a soyayya ba, har da mutunci.
Ta ɗauki wayarta, ta duba saƙon da As’ad ya aiko mata da dare
“Thank you for loving me even when I don’t feel enough. You are my calm, Aysha.”
Murmushin ta ya ƙara zurfi. Ta matso da wayar bisa kirjinta, kamar tana jin dumin kalmomin da suka fito daga zuciyar sa. “
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA TALATIN DA TAKWAS
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
A hankali na karaso bakin motar Anty Luba. Hannuna na kadawa kadan, zuciyata na bugawa da irin fatan da ba a iya furtawa fatan ganin fuskar da a da nake ɗauka kamar mafaka, fatan jin muryar da nake kallo a matsayin ta uwa... ba wai uwa ta jini ba, amma uwa ta tausayi. Sai dai kafin na isa kofar motar, sai ga sautinta ya doki kunnuwana kamar wuka mai kaifi. Muryarta tana fitowa daga wayarta, ba tare da ta san ina kusa ba. Kalamanta sun yanke min numfashi kamar ruwa mai sanyi a dare babu dumi, babu sanyi sai radadi.
“Ai wallahi sai ka ga yadda ya haukata kansa akan wannan diyar mahaukatan Ramlatu. Ya lallace! Ni fa gani nake kamar ba zai tashi ba. Har matar baban ta ce wai lalata suke yi da Khalil din! Bata ma da tabbacin tanada budurcinta.”Gabana ya fadi. Na kasa motsawa. Hawaye suka tsaya a tsakiyar idona.
Tayi dariya. Dariyar da ba dariya ba bace dariyar mugunta ce, dariyar zuciyar da ta ƙi jin tausayi. Sannan tace da wani salo mai zafi “Ai ni Zainabu Taimun dai dai da take cin ubanta. Shegiyar yarinya! Saboda ita ne zumuncin mu ya dusashe. Kaga yanzu? Kuka take yi wai masoya. Alhamdulillah da Yaya Malam ya hana auren. Ta fi dacewa ta auri wani talaka.”
Wannan karon, numfashi ya dan tsay da fita daidai Na tsaya cak, kafafuna sun kafe kamar an shuka su a ƙasa. Anty Luba? Wacce nake dauka uwar hankali? Ita ce ke furtan wannan kalamai akaina? Ita ce makiyata? Da zuciya iri haka? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.Da kyar na iya jan numfashi, sai na karasa kofar motar da jiki a raunane. Idanuna sun cika da hawayen da na rinƙa tilasta su kar su zubo. Sai na daidaita murya nace “Anty Luba... sannu da jira. Na dan tsaya ne...” Da sauri ta jiyo, kamar wadda bata san ina jiyo maganganunta ba. Sai ta canza murya, ta sanya wata ƙarya cikin lallashi “Wallahi babu yadda zanyi ne shiyasa nace ki zo. Banson Zainabu taje tayimiki wani sharri. Duk mai zuciyar imani ai zai so ki tsaya ki kare kanki.” Na yi murmushi. Murmushin da ya fi kuka zafi. Murmushin da ke kunshe da ƙaryar rayuwa, da gajiyar da zuciya ke fuskanta. Ban ce komai ba. Na bude ƙofar mota, na shiga cikin shiru. A hanya ba wanda yayi magana. Amma cikin zuciyata, akwai hayaniya hayaniyar gaskiyar da ta fara haskakawa. Ita ce Anty Luba gatana, uwar ƙarya. Ita ce ta jefa ni cikin rudani, ta lakume amana kamar abincin dare.
Da na karasa cikin gida, na tarar da Abba ya dawo. Yana zaune a falo, kamar yadda ya saba idan ya gaji daga aiki. Da nutsuwa na karasa kusa da shi, na sunkuya kadan cikin ladabi nace “Abba, sannu da dawowa.” Ya dube ni da idanu masu taushin hali, ya amsa “Yauwa Ramlatu. Yaya hanya?” Na dan gyara zama, na mikawa Mumy ledar da Anty Luba ta bani. Ban ce komai ba. Na bar kaya suka yi magana da kansu. Sai na lura... fuskar Abba tana ɗauke da wani irin nauyi. Fuskar wanda zuciyarsa ke daure da tunani. Shi mutum ne mai tausayawa, mai ƙaunar dangi da zumunci, amma yanzu kamar an ɗaure masa zuciya da sarka. Ina ganin haka na fahimta... Mumy ce ta mamaye tunaninsa. Gaba ɗaya hankalinsa yanzu, bata bar wa kowa sarari ba. Na mike da nufin barin falon, sai na ji ya kira sunana “Ramlatu...” Na juyo a hankali. Ya dube ni, “Malamin islamiyyarki ya kira. Gobe ki shirya, zaki je.” Na ɗaga kai kadan, nace “To Abba.” Na nufi ɗakina a kasalance. Da zarar na shiga, na cire kayana cikin gajiya. Jikina duk yayi sanyi, ba don sanyi na waje ba amma don gajiyar tunani, da radadin cikin zuciya.
Na shiga wanka, amma kurajen da ke jikina, musamman a gabana, sun kasa mutuwa har yanzu. Su na ci gaba da bata min kwanciyar hankali. Duk wani motsi sai in ji zafi. Wannan zafin jiki ya ƙara haddasa niƙa-niƙa a zuciyata domin ya tabbatar min da cewa ni ce kawai nake fama da wannan tashin hankali, babu wanda yake damuwa da jin ko ina lafiya ko a’a. Na bude kasan kayana, na ɗauko Maclean daga wanda na tatso agurin Mumy. Na wanke bakina da shi,Sai na zauna, na tsefe kaina jiki a raunane, zuciya a gajiye.
Na kwanta. Amma kwanciya ce ta jiki, ba ta rai ba. Idanuna suna kallon sama, zuciyata na tambaya “Ina Khalil? Ko wanne hali yake ciki kuwa? Wannan itace tambayar danake taxiway kaina. Inama ina da waya. Inama zan iya tambayarsa, in ji muryarsa, in san halin da yake ciki. Amma babu.Na juya gefe daya. Hawayen da suka kasa fitowa tun dazu sun gangaro a hankali. Na lulluɓe kaina da bargo…
Sai da dare yaraba Na farka da ihu. Wallahi na rantse, ban taba jin tsoro irin wannan ba a rayuwata. Jikina duk gumi, zuciyata kamar zata fado kasa. Har yanzu ina jin kamar ina ciki... ciki na wancan mummunan mafarkin.
A mafarkin, na tsinci kaina a cikin wani daji mai duhu. Komai ya narke da duhu, kamar rana ta ƙi fito wa duniya. Sai iska mai sanyi tana kadawa, tana shigowa ta cikin fata ta har jijiya. Duk inda na kalla, babu rai, babu tsuntsu, babu sautuka shiru ne kawai da wani nauyi a zuciyata. Na fara tafiya... amma ban san ina nufa ba. Cikin duhun nan, sai na fara jin ƙamshi ba mai dadi ba, ba kuma mai muni ba. Wani ƙamshi ne da ke tuna min da kabari. Sai na ji gabana ya faɗi.Kafin na ankara, sai wata mata ta bayyana a gabana ba zata fi tazarar taku biyu da ni ba. Gashinta ja-jayi, tsawo kamar zobe, tana kallona da idanu marasa rai. Hannunta na riƙe da wata wuka mai kaifi wadda ke ɗauke da jini mafarkin jinin ne? Ban sani ba. Ta fara dariya... wata dariya mai cike da mugunta. Kamar daga wata duniya daban. Ta ce min da murya mai ƙyarar kunne “Ke ce! Na jira wannan rana... yanzu zaki biya!” Na juya da gudu amma ƙafafuna sun ki motsi. Na yi ƙoƙarin yin ihu, amma muryata ta makale kamar an ɗaure min makogwaro. Ina kallo, tana matsowa kusa da ni. Sai ta daga wukar sama... ta sauke ta da ƙarfi! Na farka nan take. Ban san yadda na tashi ba, amma na san ihu nayi sai dai har yanzu zuciyata tana rawar jiki. Kamar mafarkin bai ƙare ba.
Washegari da safe, duk da cewa jikina har yanzu bai gama dawowa daidai ba daga wancan mafarkin, na tashi da niyyar mantawa da shi. Na nufi aikin yau kamar yadda na saba tsaftace falo, gyara curtains, da share-share. Duk abinda nake yi, zuciyata tana cikin tunani. Sai na ji muryar Mumy da Yaa Billy daga ɗakin falo. Suna magana, amma muryoyinsu cike da damuwa. Na dan matsa kusa kadan, ba don leƙa ba, sai don ji idan wani abu nake bukata na gyara.Abin da na ji ya tsaya min a zuciya.Yaa Billy ta fara da murya mai sanyi, kamar wadda ta sha kuka
"Ina sonsa Mumy... Wallahi. Ina masa mahaukacin so. Kuma ni zan iya da ita." Bansan waye wannan da ake magana akai ba. Amma kalmarta "da ita" ta janyo hankalina. Kamar ana magana ne akan wata mace, wata kishiya ko wadda ke tsakani da Yaa Billy da wanda take so. Amma ina, ni dai ban ce komai ba. Sai na cigaba da sauraron yadda Mumy ta mayar da martani cike da hushi da takaici. "Ke wai baki da hankali ne? Matar da kika zauna a gidanta, har kika gama jami’a? Kuma kinsan halinta! Ita zakice kina son mijinta?" Na tsaya cak.
Na gane yanzu, ana magana akan abokin abba wannan attajirin. Sai Mumy tace "Kingani Bilkisu, kar ki jawo min magana. Ki kalli yadda mijin ke rike hannunta a hoton da kika gani shine kikeso ki sa kanki a tsakaninsu? To! Ahir! Wallahi kar na kuma jin wannan batu a bakinki. Kada ki jawo min masifa. In banda ke da fitinarki, ina ke ina Alhaji As’ad? Masu kudin ƙasa! Ga mulki, ga kudi! Ki bar wannan batun!" sai na ji shesshekar kuka. Yaa Billy ta sa kuka ta fice daga falon da sauri, ba tare da ta ce komai ba.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA TALATIN DA TARA
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Matsa munafuka! Kibani waje shegiyar jinin munafukai da mayu. Wato laɓe kike mana ajikin ƙofa? To dan uwarki, ba As’ad ba, ko Malam Idi direba, ba zaki aura irin su ba sai dai can wani talakan.
Na zuba wa Mumy ido, amma shiru nayi, saboda wallahi banga laifi na ba. Ina gefe ina goge TV, sai kawai ta fito ta karemin zagi. Tsaki nayi a raina, dan abunsu yana isata. Wannan hantara babu inda zanji sanyi araina kowannen su baya ƙaunata.
Ban gama zancen zuciyata ba, sai ji nayi an finciko rigata ana jan ta. Ina dagowa, sai naga Yaya Billy ce. Nace da ita, “Menayi miki?”
“Me isa kike tabamin kuɗina, dan ubanki? Nagaya miki fiye da sau ɗaya why are you stealing from me?”
Na firgita nace, “Wallahi nifa ban taɓa ɗaukar miki kuɗi ba. Gyaran ɗakinki kawai nake yi... ban ɗauka ba!”
Can sai naji muryar Mumy
“Nima wannan satar nan ta dameni. Ana mun ɗauke-ɗauke! Wacce irin shigiyar yarinya ce ke? Kin zama mana annoba.”
Sai kuma Billy ta buɗe baki da wani ƙyama
“Mumy, kina gani fa? Pant ɗina bata wanke ba, ko ubanwa zai wanke?”
Na kalleta cikin mamaki nace, “Pant kuma? Ya Billy, ai bazan ma kalli naki ba, balle har in wanke”
Kasa na karasa sai mumy ta wankeni da mari. “Sa’arki ce da zaki mayarmata da magana? Dallah, ɗauka ki wanke mata! Mara hankali kawai.”
Haka na wanke. Zuciyata cike da ƙyama. Idan zan faɗi gaskiya, kudin hannuna saura ₦2,000 daga kudin da na ɗauka na Mumy. Ban jin zai isheni har naje na dawo, amma dai sai nasaka a jakar Islamiyya ta. Nayi wanka, na kwanta.
Wajen ƙarfe uku na tashi. Na shirya cikin hijabin makaranta. Abba yace na koma wannan kalmar tasa ta sanyaya raina. Wallahi zaman gidan nan bai yi mun daɗi ko kadan.
Na ɗauki jakata, nayi wa Mumy sallama, na fita.
Da na fito bakin titi, rana na lulluɓe sararin sama kamar zata haɗa da hazo. Hijjab ɗina yana tafe da iska kadan,wata hadaddiyar mota, sabuwa, mai sheƙi Na hangota bayana.
Ina tafiya a hankali, na lura motar tana binai. Cikin motar, wani kyakyawan matashi ke zaune, yana leƙena ta gefen gilashi. Baki ɗaya sai murmushi yake, irin wanda ke ɗaukar hankali amma ke sa zuciyar mace ta farka da kyar.
Na ɗan waige gefe na, sai na maida kaina gaba kamar ban lura da shi ba.
Ina gab da fita babban titin unguwarmu, kawai sai naga ya faka motar gefe. Yayi saurin fitowa, ya nufo ni da tafiya mai sauri. Sai da yazo kusa da ni sosai, sannan ya ce
"Yammata... yammata! Dan girman Allah ki tsaya mana, da gaske nake!"
Na juyo kadan, na kalleshi da wani irin kallon raini, wanda ya kamata ya fahimci ba irin yammatan nan baniba marasa kamun kai. A raina nace Wannan kuwa, ko ba’a fada ba, mai kudi ne ko yaron wani mai kudi da bai san wahala ba. Ya matsa gaba kadan, yana kara ce mun “DanAllah ki saurareni mana.” na zuba masa idanuwana sannan nace “Kayi hakuri. Ni matar aure ce.”
Atake ya tsaya cak. Baki buɗe kamar wani yaro da aka kama da laifi. Sai ya ce “Afuwan, sis. Wallahi banyi zaton haka ba. Ki gafarceni.” Ya juya a hankali, ya koma motarsa da dan kunyarsa, har ya rufe kofar da ɗan sake numfashi.
Ni kuma na karyar da kaina gefe, na tsallaka titi da sauri na samu abun hawa. Motar keke-napep kawai na iya bi yanzu. A da kuwa, Malam Idi ke kaini ko’ina mutumin kirki, mai hakuri, mai daraja. Shi ne driver ɗin gidanmu. Amma yanzu, babu komai. Shi kansa Malam Idi ya daina zuwa tun da mumy ta yi duk wani abu da zata iya, ta sa an kore shi saboda ni. Abba kuwa, bai taɓa siya min mota ba kamar yadda ya siwa yaya Billy da mumy.
Isata asibitin ke da wuya, na nuna wa napeep inda zai ajiyeni. Ya ce min
“₦500 ne kudin.”
Na cire na ba shi, cikin rashin natsuwa.
Na tsallaka cikin Asubutin u^-ɗin, ina waige-waige. Bana son na haɗu da kowamusamman wanda na sani. A yanzu, na daina yarda da kowa. Makiyana sune ke yawan nuna mini ƙauna ta boye, suna murmushi a gaba, amma zuciyarsu tamkar wuta.
Ina shiga corridor ɗin, na hango yayan Khalil ya rungume shi sosai. Khalil yana dan takawa da ƙyar, alamu sun nuna cewa ko likita ya bada umarnin hakan ne. Ko’ina ya kumbura saboda ruwan da ke taruwa a jikinsa. Fuskar sa cike da rauni da ciwo. Na karasa da ɗan hanzari, cikin tashin hankali nace
“sannu! Yaya Mujittapha, ina wuni? Ya mai jiki?”
Ya amsa cikin gajiya, yana murmushi da ladabi
“Likita yace a dan sakashi ya dinga takawa. Muka gama yanzu, muna shirin komawa daki.”
Khalil ya ɗago kai yana kallona. Ya washe baki da ƙyar, amma har yanzu idanunsa sun cika da kauna. Fuskarsa tayi duhu, tayi baki sosai, jikin sa babu kuzari ko kadan. Na kalle shi, zuciyata na karaya.
“Khalil, ya jiki? Allah ya baka lafiya. Ya yayemaka,” na faɗa da tausayi.
Yaya Mujittapha ya ce, “Za a ajiye shi nan kusa da daƙin,” yana nuna kujerun bakin corridor.
Khalil ya ɗaga kai, murya cike da rashin kuzari amma mai tsantsar shauƙi da so, ya ce
“Ramlahhhh…”
Na daga masa kai. Sai ya ce
“Zo ki zauna nan. Inason muyi magana.”
Na amsa masa da shiru, zuciyata na bugawa kamar ana buga gangi. Na karaso da sauri, na zauna a gefensa. Idanunsa ya zubamun, suna narkar da zuciyata. Na juya gefe kadan domin boye hawayen da suka fito da kansu. Na share su da sauri, amma har yanzu idanuwansa na kaina.
Ya riƙo hannuna da sauri, kamar wanda ke neman ya ɗauki numfashinsa na ƙarshe. A take, naji wani irin zafi ya ratsani zafi.Na ɗago kai da sauri, idanuna sun cika da mamaki da tsoro. “Khalil…” Na faɗa a hankali. “Jikinka zafi sosai.” Sai ya murmusa. Murmushi mai rauni,Ya ce,“Ramlah…”
Yadda ya furta sunana ya sakani jin wani abu ya girgiza ni daga ƙasa har zuciyata. Murya ce mai nauyin da ba zata manta ba.
Nan take hawaye suka zubo min. Na runtse idona, ina ƙoƙarin jure kukan da ke tasowa daga ƙasan zuciyata.
“Inaji a jikina kamar bazan rayuba... kamar rayuwata ta ƙare,” yace da ƙyar, kamar numfashi yana gujewa bakinsa. Na zaro ido, na ɗaga hannuna cikin sauri na danna kan bakinsa.
“Khalil, don Allah ka daina faɗin haka! Ka daina wallahi... Kada ka kara faɗa.”
Muryata ta katse kamar ta mai ta motsi, zuciyata na ci gaba da bugawa da karfi.
Ya ɗauke hannuna da sauri, ya kalle ni da idanuwansa masu kumburi. Ya ce cikin wata murya mai rauni amma cike da ƙauna
“Bazaki fahimta ba, Ramlah… Na soki tun kafin mamanki ta rasu. Tun lokacin da kike Primary 5. Na rayu da soyayyarki a cikin zuciyata, kullum ina mafarkin ki zama tawa.”
Ya sauke ajiyar zuciya, yana ci gaba da kallona.
“Naso a auramin ke, amma abbanki ya hana. Bayan kin kammala makaranta, shima ya ƙi amincewa. Amma har yanzu… ina jin cewa ni ba mijinki baniba, amma ina so ki sani Ina ƙaunarki.”
Ya girgiza kai, yana goge hawayen da suka gangaro a fuskarsa.
“Bansan me nake ji akanki ba, Ramlah. Amma na tabbata… ni inason ki. Duk wahala, duk rintsi, duk ƙunci da dare ya sauka, ina roƙonki ki dage da karatu. Karatun da zai maki amfani sosai.”
Ya matsa kusa da ni, ya dafa kafadata da hannun da ke rawar sanyi.
“Ki tsaya da kafafuwanki, kinji? Ki tsaya da ƙarfi. Ki dage da addu’a. Tana iya zama kawarki, uwa, babanki, yayarki duk a lokaci guda.”
Sai ya kalli idona sosai.
“Ki kula da kanki, Ramlah. Komai tsanani, komai wuya, komai kaɗuwa, karki manta ke kanki kike da farko kafin kowa.”
Fashe masa da kuka nayi. Hawaye na gangarowa. Na dafa kafadarsa, zuciyata kamar za ta fasa ƙirjina.
“Dan Allah ka yi shiru, Khalil. Dan Allah ka daina. Ban so… ba zaka mutu ba! Wallahi ba zaka mutu ba... Kai zaka rayu, ka gan ni na cika buri na!”
Na kwantar da kaina a kafaɗarsa, numfashinsa yana busa a kunne na. Wani irin sanyi mai ɗaci ya ratsa zuciyata. Lokaci ya tsaya cak. Na daina jin motsin duniya duk da hayaniyar corridor, likitoci na wucewa, marasa lafiya na gunaguni… a cikin kunnuwana, abinda nake ji kawai shine numfashin Khalil da bugun zuciyata.
“Ramlah…” ya kira sunana da wani irin sanyi mai narkar da rai. “Idan har bana nan gobe”
“Nace ka daina faɗa hakan!” na katse shi da kuka mai ƙarfi. “Kayi shiru Khalil, banaso! Ka gaya min cewa zaka rayu! Ka gaya min za mu yi aure, ka gaya min…”
Na kasa karasawa. Kalma ta tsaya a ƙirjina, ba ta iya fita ba. Kamar wata ƙura ce ta toshe ma bakina mafita. Na ƙara rushewa da kuka.
Ya ɗago hannunsa da ƙyar, ya dafa kaina, yana shafa kan kamar zai tuna wani abu da ya dade da ɓace masa.
“Ina son ki, Ramlah. Wannan ne gaskiya. Ko da ba zan kasance a kusa dake ba, zan kasance cikin zuciyarki har abada.”
Sai muka ji ƙofar corridor ɗin ta bude da ƙarfi. Yaya Mujittapha ya dawo da likita. Fuskarsa a cike da damuwa, hannunsa na nuna yadda lokaci ke kurewa.
“Bai kamata ya zauna haka ba,” likitan ya ce da sautin lallashi. “Jikin sa na bukatar hutawa, kuma dole a ba shi magani yanzu.”
Na miƙe da sauri, na share hawayena. Khalil ya kalleni da murmushi murmushi da ya fi magani, ya fi soyayya da kanta.
Na ɗago hannunsa na sumbaci tafin sa. Na ce,
“Khalil... wallahi zan dage da karatu. Zan zauna da kafafuwana. Zan roƙi Allah kullum saboda kai. Ka yi min alkawari zaka cigaba da fafutuka. Kayi min alkawari zaka tsaya tsayin daka, ka tashi daga wannan jinya.”
Ya zuba min ido, da karfin hali ya daga yatsansa daya.
“Na yi miki alkawari... Amma ki yi min wani alƙawari ma.”
“Ina jinki,” na ce cikin sanyi.
“Ki zauna da zuciyarki. Kada ki bari duniya ta karya ki. Kuma idan wani ya so ki... a nan gaba, idan ni ban samu na dawo ba, ki bari soyayya ta shigo zuciyarki. Kar ki zauna da ciwo saboda ni.”
Na riƙe hannunsa da ƙarfin da na iya. Na ce
“Khalil... bazan iya manta da kai ba. Kai ne farkon ƙaunata, kai ne tarihin zuciyata.”
Likita ya gyaɗa kai, ya ce
“Yakamata ki bashi lokaci ya huta.”
Na ɗaga masa kai cikin ɗaci, sannan na matsa gefe kadan, amma idanuna na kan Khalil har likita ya ja gadon da aka shimfiɗa shi, ya mayar da shi cikin dakin jinya.
Na tsaya a bakin ƙofa, zuciyata na rawa. Da idona nake masa kallon da ya ƙunshi duk wani abu da baki ba zai iya faɗa ba.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ARBA'IN
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Ina tsaye har yanzu a bakin ƙofar dakin jinya, jikina ya mutu da hawaye, zuciyata cike da fargaba. Cikin wannan halin, sai naji an dafa kafadata.
“Ramlah...” wata murya ta kira ni.
Na juyo. Anty Luba ce. Anty ɗina. Tana sanye da zani mai launin shuɗi, mayafinta na rufe daidai habarta. Fuskarta a cike da murmushi na tausayi, kamar yadda take kullum idan tana son ta sa ni yin abinda take so.
Ta matsa kusa, ta ɗora hannunta a kaina.
“Ina kika shiga ne? Kina kuka haka kamar yarinya?” Na kalleta kawai dan ni yanzu naganeta nagane makiyata ce wacce bata ƙaunata ko ƙadan.
Na share hawayena da gefen hijabina.
“Anty… Khalil ne. Maganarsa da yadda nake ganinsa ya firgitani. Yana faɗin kamar bazai rayuba...”
Ta ja numfashi, ta zauna kusa dani a kujerar bakin corridor. Sai ta kama hannuna da taushi.
“Ki kwantar da hankalinki mana, Ramlah. Idan har Allah ya ƙaddara ki da shi, zai dawo. Amma ki sani… a rayuwa ba komai ke zuwa yadda muke so ba.”
Na kalle ta da mamaki, zuciyata ta ɗan harzuka. Saboda nasan maganarta ba har cikin rai take ba.
“Kin san ni, Ramlah. Anty ɗinki ce. Ina sonki kamar yadda nake son ɗana. Wallahi ni a kullum ina mafarkin ganin ki kin samu farin ciki. Amma ki ƙara wayewa. Rayuwa bata tsaya kan ƙauna kawai ba. Daga farko har yanzu, ni ke tsaye a gefenki. Kin san haka ko?”
Na gyada kai, amma har yanzu na kasa gano inda kalmarta ke nufi. Sai ta ɗora
“Bari muce ma Khalil ya warke... shin ke kin shirya zama da danginsa? Kin shirya jure zaman cikin iyalin da basa sonki kinsan yadda suke zaginki kuwa? Ko kin damu da hakan?”
Zuciyata ta tsinke. Tambayarta kamar jefa ni tayi cikin kogi. Amma kafin in ba da amsa...
Sautin gudu da ƙara suka fasa corridor ɗin.
“Likita! Likita don Allah kuzo da gaggawa! Jikinsa ya tsananta!”
Muryar Yaya Mujittapha ce.
Bayan sa kuwa sai Babar Khalil ta shigo da gudu, tana kuka kamar za ta yanke numfashi.
“Likita kuzo ku taimake shi! Yana faduwa kamar mai shure!”
Likitoci biyu suka fito da sauri, ɗaya da tray ɗin allurai, ɗaya kuma da oxygen. Suka nufi cikin ɗakin jinya da gaggawa.
Na miƙe tsaye. Idanuna sun ƙi daina zubar da hawaye. Jikina ya kakkarye kamar bishiyar da aka sare. Na kalli ƙofar ɗakin da suka shiga da Khalil.