Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 18

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 18

Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 18: Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 18. Anty Luba ta dafa bayana, amma wannan karon ba ta ce komai ba. Sai…

4,457 words

Anty Luba ta dafa bayana, amma wannan karon ba ta ce komai ba. Sai kallon da ta jefa min. Kallon da ba kowanne kallon kulawa ne ke da shi. Wata siririyar dariya ta bayyana a fuskar ta. Maman khalil ganin halin danake ciki tasanya yaua Mujittapha yace natafi gida duba da yadda dare yaja sosai.Tunda na fice daga asibiti, hankalina ya bace. Zuciyata gaba ɗaya ba ta cikin jikina zuciyata a cikin dakin jinyar Khalil.

Na nemi hanyar makaranta, amma ba don nasan inda nake ba.Sai kuma na tuna makarantar da ake tashinmu karfe biyar na yamma. Sai kawai na farga cewa... lokaci ya kure. Na duba agogon da ke jikin bango 9 na dare.

Na dafe ƙirji. Zuciyata tayi shiru. Ba ta dukan tsoro, ba ta harbin fargaba. Amma na san akwai abu a cikinta fatan cewa Khalil zai rayu. Wannan ne kaɗai burinta yanzu.

Na zauna a ƙaramin benci a jikin harabar Asubutin. Na kasa motsi, kamar wata dutse. Tunani ya mamaye ni, na rasa inda zan sa kaina. Sai wata murya a cikin raina ta soma magana... “Ramlah, kina ƙaunar Khalil ne?”

Na lumshe idona. Ban da amsar hakan.A'a... ba kawai Khalil nake so ba.

Ina kaunar wanda zai kulani. Wanda zai ji damuwata. Zuciyata tana jin daɗin rarrashi. Tana buƙatar murya mai sanyi da hannu mai taushi duk abin da ban samu a rayuwa ba, sai yanzu na fara ganinsa.

Na buɗe jakata. Na duba ciki. Ko sisi babu. Gabana ya faɗi. Idanuna suka sauka ƙasa, na rasa me nake ciki. Masu mota sai hucewa suke yi a hanya, kowa cikin gaggawa.

Na tsaya a gefen titi, zuciyata a hargitse, jikina a sanyaye.

Can sai wani napeep ya tsaya. Direban ya leƙo yana dariya kadan.

“Hajiya... bakiga ruwan da ke sauka yana dukanki ba ne?”

Na ɗan dubesa da ƙyalli. “Ni banda kudin mota ne shiyasa.”

Sai ya girgiza kai yana murmushi. “To shiga, zan kaiki gida. Ba komai.”

Na yi masa godiya da murmushi mai rauni. Na shiga cikin napeep ɗin. Shiru ne ya rufe tafiyarmu, amma zuciyata na tafe da roƙo da addu’a. Na kalle shi da tausayawa. Kamar akwai sauran mutanen kirki... ba kowa ne mugu ba.

Da muka isa kofar gida, na sauka.

“Na gode masa sosai. Allah ya saka da alheri.”

Na tura ƙofar gidan cikin sanyin rai. Na shiga ciki da takun mutumin da ya dawo daga yaki ba tare da nasara ba.

Zuciyata cike da tambaya ɗaya

“Shin Khalil zai wayi gari?”

Haka na tura ƙofar gida, na shige cikin falon mu. Da ƙyar na iya furta

“Assalamu alaikum…”

Sai na tsaya. Momy na zaune a gaban kujera tana waya, tana dariya kadan, tana kuma girgiza ƙafarta kamar ba komai ya dame ta.

Ya Billy, tana zaune a ɗaya gefen palon tana kallon TV, amma duk da haka sai ta zuba min ido kamar tana jiran wani abu ya faru.

Ni kuwa ban karaso ba, ban kai kujerar ma ba... cikin minti ɗaya kawai, sai naji an finciko ni daga hannu.

“Ramlah!!!”

Abba ne!

Na juya cikin razana, amma kafin in iya cewa komai, hannunsa ya sauka a bayana da ƙarfi. Na fadi kasa da huci, idona suka cika da hawaye.

“Shin sai dare haka kike dawowa gida?! Kina yawo kamar wata 'yar iska! Ke wacece a wannan gidan da zaki kai dare har yanzu? Daman da gaske zainab take datacemun kin fara yawo ko?!”

Na yi shiru. Banza na masa. Zuciyata cike da wahala da gajiya. Na kasa magana, saboda na san komai zan ce ba zai kare ni ba.

Momy ta katse wayarta, ta dafa cinyarta kamar mai ba da shawara.

“Ka duba fa! Wannan ba karamin rainin hankali bane. Yau gaba da karfe tara ta dawo daga makaranta! Duk macen kirki da tarbiyya zata dau lokaci haka tana yawo? Waye ya dauke ta? ina ta je?”

Abba ya karaso,Ya daka min tsawa.

“ Kindaina jin magana saboda kina jin ke cikakkiyar budurwa ce yanzu? Ai sai na nuna miki cewa ni ne uban gidan nan!”

Ya dauki wayar jiƙin tv yazubamun,Na rike cikina, saboda yadda bugun hannunsa ya ratsa ƙasata kamar wutar lantarki. Na ji nauyin jiki.

Na ɗago kaina, cikin hawaye nace

“Na je asibiti ne... Khalil ne, yana fama da ciwo sosai...”

Abba ya girgiza kai, yana ci gaba da masifa.

“Kina shashanci da wani banza da ba ni na zaba miki ba! Wato sai kinyi abin da kike so? To wallahi sai na saka a daina barin ki fita makaranta! Gaba daya.!”

Kalmar nan ta ƙarshe ce ta karyani. Idona sun cika da hawaye, amma zuciyata ta ɗauki dumi. Wannan dumin ba na ƙauna bane na ƙorafi ne, na ɓacin rai ne, na daci ne da aka watsa a zuciyata.

Sai kawai ya kai hannu ya ciro wayarsa daga gefen TV, ya kunna. Ya matsa manhajar hoto, ya nuna wasu hotonw. Sai ya juyo gare ni da ƙarfi.

“Wannan hoton...! Wannan hoton fa?! Dan ubanki wannan wani irin iskanci ne?! A jikin sa kike kwanciya? Haka kika bar gida kije kina rungumar namiji?!”

Na zaro ido, jikina ya rika rawa. Ban san lokacin da nayi baya ba. Wanene ya daukemu? Innalilahi. Yanzu fa sai yakasance anty luba ko? Na fara hawaye.

Wayar ya daga sama… ya bugeni da ita a kafaɗa. Na fadi ƙasa, kuka ya ƙwace min.

“Wato ke yanzu kina da saurayi ko?! Khalil ɗin nan shi ne zakiyi wa biyayya fiye da iyayenki? Kin manta da sunan gidan da kika fito?.”

Na rarrafa a kasa, jikina na ciwo. Amma zuciyata ita tafi ciwo. Muryar sa na dukan kai na kamar ƙaho. Sai ya dakan tsawa

“Babu ke! Babu Khalil! Wallahi idan kika ƙara zuwa inda yake, idan kika ƙara haɗa kanki da shi... Allah ya isa ban yafemiki ba!”

Na kalli Mumy, cikin hawaye da ƙasƙantar da kai.

“Momy... wallahi ba haka bane. Khalil yana jinya… ban je wajen banzanci ba.”

Ta yi dariya mai zafi.

“Jinya ko? To sai me? Sai ki kwanta a kirjin marar lafiya a asibiti?! Wannan wace irin tarbiyya ce?!”

Na sunkuyar da kai. Wani irin kunci ya mamaye zuciyata. Ina cikin iyayena... amma kamar bana gida.

“Allah ka gani... ban aikata ba. Ban tozarta kaina ba. Amma yau guri da ya kamata na samu ƙauna, sai na samu wulaƙanci.”

Sai na rasa numfashi. Hawaye na gangara ba tare da izini ba. Kalmar Abba tana dukan zuciyata

“Babu ke! Babu Khalil!”

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA ARBA'IN DA DAYA

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Masifa kawai nake ji daga falo. Muryar Abba ta cika gidan gaba ɗaya, yana faɗa kamar wanda zai tarwatse dakin. Mumy na gefe tana ƙara tayashi da nata zagin. Ni kuma... ina can kusurwar falo, durƙushe a kasa, jikina rawa yake, hawaye kuma na gangarowa ba tare da izini ba.

Zuciyata babu kwanciyar hankali. Na kalli bangon gidan da nake kira gidan mu amma babu wata natsuwa da nake ji. Wannan gida da ya kamata ace ina samun kulawa da farin ciki ya zama gurin da nake jin kunya da tsoron shigarsa. Gurin da na fi jin azaba fiye da wuri ko ina a duniya.

Abba ya juyo da sauri, idonsa jajir, yana nuna ni da yatsa kamar zai soka cikin idanuna.

“Dan ubanki Ramlah! Maganin kibar nan kika kuma siya kike sha ko? Yanzu baki da hankali kenan sai ƙin illatar dakanki?” Cikin tsananin kuka da tsoro nace da ƙasa da murya “A’a Abba... Wallahi... ban kuma sha ba. Ni fa ban sha komai ba.” Sai ya ƙara daga murya, fuskarsa ta canza launi “Tashi! Tashi ki bani guri!.” Na yi saurin tashi na ja kaina gefe. Jikina yayi sanyi, ƙafata har rawa take, kamar zan faɗi. Hawaye na cigaba da gangarowa, zuciyata kuma na masa tambaya "Ni ce ‘yarsa?"Wannan irin kalaman... wannan zafin... daga mahaifi?

Sai kawai na zauna gefen bango, na dafe kaina. Zuciyata na bugawa da karfi kamar wacce aka saka cikin murhun wuta. Na rufe bakina da tafin hannu na, saboda ba na son suji yadda hawayen ke haɗuwa da hucin numfashina. “Allah ka sani... ba laifi nayi ba... Amma me ya sa na zama basa sona?”

Ina cikin ɗaki, jikina kwance a kan katifa, ido na na kallon rufin dakin amma zuciyata tana wata duniya daban. Duk da nesa da falon nake, naji muryar Mumy sosai kamar tana gabana. “Wallahi Abban Ramlah, idan da zaka taimaka ka aurar da ita yanzu, na samu sauƙi. Kaga dai hoton da Anty Luba ta turamun daga asibiti... kai, Allah ya kiyaye. Hakan ma tace shine wanda za a iya gani! Tace sauran hoton ma ba’a iya dubawa saboda muninsu.”

Na runtse idona da ƙarfi, hawaye na silalowa. Ban san me nake ji ba sai kunya da wulakanci. Wata zuciyar tana cemun Ni ba mutum bace a wajensu.”

Abba yafara masifa a falo “Zainabu! Ki dakata! Ki barni da damuwata... ni dai yanzu ina bukatar natsuwa, ba wannan masifar taki ba.”

Na dafa ƙirjina, na furta da wani kunci a cikin zuciyata “Ya Allah... idan mutuwa za ta kasance mafita, ka ɗaukeni. Ban da wanda ke sona, ko ya damu dani. Rayuwa tamun nauyi. Na gaji... na gaji da zama abin ƙyama, na gaji da wulakanci, na gaji da rashin adalci...”

Kuka na ya tsananta. Na saka yatsuna biyu a bakina ina hana kaina kara, amma zuciyata na ta kuka. Fuskata ta jiƙe da hawaye, naɗaɗɗun ciwo na zuciya ya cigaba da huda dukkan jinina kamar ƙaya.

Na buɗe baki a hankali, muryata kamar ana cire ta daga mafitsara, nace “Ya Allah... duk inda rayuwa take, ka bani mafita. Duk inda mutunci yake, ka juyo mun da shi. Amma idan kuwa hakan bazai samu ba to ka juyar da raina zuwa inda ba za a sake wulakantani ba.” Dakyar na iya tashi nayi alwala, na gabatar da salloli na. Wallahi gabana sai kai-kayi yake, zuciyata cike take da wani nauyi mai kama da ciwo. Na zauna ina shafawa jikina mai, amma radadin raina da na jiki sun haɗu sun mayar dani tamkar wanda ba ransa.

Cikin dare bayan na yi bacci na farka, zuciyata ba ta da natsuwa. Naji kamar karar waya daga falon Abba. Na tsaya a bakin ƙofa ina sauraro. Sai naji muryar yaya Usman a waya yana fadin “Abba, komai zakace akan Ramlah, bazan amince ba. Ka daina zargin yarinyar nan. Ka bari ta dawo gurina. Momy dai mahaifiyata ce, amma Abba, ka duba lamarin da idon adalci. Ramlah amanarka ce. Dama kakirani ne akan Bilkisu nasan zata iya. Amma don Allah, ka tausaya mata.”

Abba bai bari ba, sai da ya tsawatar masa, yana faɗin “Usman! Kai kake ƙarfafa ta! Tana da matsala!” Amma duk da haka yaya Usman bai daina kare ni ba. Har sai da ya ce “Abba, idan akan makaranta ne... eh, tafara zuwa makarantar yanzu. Kuma ni nake ɗaukan nauyin komai. Kudin makarantar shekaru biyar gaba ɗaya na biya. Abba, Ramlah ba fitinanniya bace.”

Na ji Abba na girgiza murya cikin mamaki “Kayi mata rijista a makarantar kudi irin haka? Usman kusan miliyan takwas fa ka biya! Ina laifin makarantar gwamnati?” Sai yaya Usman ya amsa da nutsuwa “Abba, duk da haka, Allah yabata ilimi mai amfani. Muna rokon Ubangiji yasa muga amfani da ilimin nata.”

Na jiyo sautin kashe wayar. Ina jin hakan na sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi kamar dutse ya daga daga zuciyata. Wani sanyi da kwanciyar hankali suka lullube raina. Kai! Ashe har yanzu akwai wanda ke kallona da idon tausayi. Ashe har yanzu akwai wanda ke ganina da daraja.

Na miƙe na yi alwala, na sake gabatar da salla. Cikin kuka na roƙi Allah da zuciya guda “Ya Allah! Ka shiga lamarina. Ka kare min mutuncina. Ka gafarta min. Ka ba Khalil lafiya. Ka sauƙaƙa min kaddara ta. Ka bani mafita daga wannan duniyar da ke min tsanani.”

Na durƙusa gaban Ubangiji da hawaye, amma zuciyata ta ɗan fara jin natsuwa, domin a ƙalla akwai wani yaya Usman da ke cikin mutanen da ke ganin darajata.

*****

Kwana uku kenan rabona da Khalil. Wallahi na rame fiye da yadda ake tsammani. Fuskata ta dumfare, idanuwana sun danƙare da hawaye. Kamar wadda ke fama da zazzabi, haka jikina ya koma duk a dalilin rashinsa da rashin jin halin da yake ciki.

Daman tun lokacin da Abba ya gaji da matsin lamba sai ya daukeni da kansa ya kaini wata babbar private university a cikin gari. Shi da kansa ya tabbatar da admission ɗina da komai accommodation, ID card, har da orientation pack. Amma ni ban ji daɗin komai ba. Hankalina gaba ɗaya yana asibitin da aka kwantar da masoyina.

Bayan mundawo ina zaune sai naga Musa almajirin gidanmu wanda ke aiki da Mai gadi. Sai na kirashi cikin sassaucin murya.

“Musa… dan Allah, zaka iya zuwa Asibitin Darmal Specialist Hospital ka duba min Khalil? Ka dawo ka gayamin halin da yake ciki. Zuciyata tana rawa, ban da lafiya idan banji halinsa ba.”

Musa ya girgiza kai cikin girmamawa. “To Aunty Ramlah, bakomai, zanje yanzu.”

Na janyo 'yar leda daga jakata, na ciro dubu daya daga cikin ₦10,000 da Abba ya bani don makaranta. Na mikamasa.

“Ka ɗauki wannan, sai ka hau keke Napep zuwa can. Ka duba lafiyarsa, kada kayi dogon zance da kowa ka dawo kai tsaye ka fadamin komai. Ka fahimta?”

“Na fahimta Aunty,” ya ce, ya juya da sauri.

Bayan kusan awa biyu, Musa ya dawo. Har lokacin ina tsakar gida ina haɗa lemon zaki da zuma. Da sauri ya karaso kusa dani, numfashinsa na ɗan dagawa. Na dubeshi da idon da ke cike da fargaba da tambaya.

“Musa...?” Sai ya furta cikin salo mai kwantar da rai “Alhamdulillah, da sauki. Khalil yana samun sauki yanzu. Yana bacci lokacin da naje, amma nasamu Nurse Maimuna, tace yau yaci abinci kadan. An bashi magani. Har sai da ya tambayi Ramlah, amma sai aka ce masa kinje makaranta.”

Ban san lokacin da hawaye suka gangaro daga idanuna ba. Na sauke ajiyar zuciya kamar wadda aka cire daga rana.

“Alhamdulillah Ya Allah... Na gode Maka Ya Ubangiji.” Na kama sujjada a filin tsakar gida cikin kuka, ina godiya da murna.

********

Washegari da sassafe, ƙarar agogo ta farkar da ni. Kamar yadda aka saba, zuciyata cike take da tunani iri-iri. Na mike daga gadona, na dube agogo ƙarfe shida da rabi na safe. A yau zan fara wani sabon babi a rayuwata rayuwar jami’a. Wannan ce ranar farko da zan shiga jami’a a matsayin ɗaliba, kuma ina jin wani irin ɗan tsoro da kwarjini a lokaci guda.

Na shirya cikin kayan da zan saka naje makaranta dana ware. Na lullube kaina da hijabi mai tsabta. Lokacin da na tsaya gaban madubi, ban iya gane kaina sosai ba. Ina ganin wata sabuwar ce cikakkiyar mace mai burin rayuwa, wacce ke ƙoƙarin mantawa da abubuwan da suka faru a baya.

Gaban gidanmu, motar Abba ta tsaye, Malam Idi na zaune cikin nutsuwa. Na shiga mota cikin shiru, zuciyata na dukan sauti kamar anata bugunta da karfe. Muka nufi jami’ar A.Y. Global University, ɗaya daga cikin manyan makarantu masu zaman kansu a birnin. Ginin jami’ar ya bayyana daga nesa, yana shawagi da alfarma da natsuwa. Wurin ya cika da sabbin fuskoki wasu na dariya, wasu na tunani, wasu na tsoro.

Na sauka daga mota a harabar makarantar, na kalli ɗalibai maza da mata, kowanne da jakar laptop a kafada, wasu suna ɗauke da file, wasu kuma suna daukar hoto a gaban tambarin jami’a. Na ji kamar ana kallona. Wata irin murya daga zuciyata na ce min “wannan ce farkon tafiyarki.”

Mun fara da rajista a Babban Dakin Taro. Can na haɗu da wasu ‘yan mata ‘yan uwana ɗalibai. Sun kasance masu fara’a. Mun gaisa, munyi musayar lambar waya, sannan muka zauna tare. Muryar wani jami’in makaranta ta tsinke shiru da kiran sunayenmu, yana bamu umarnin inda zamu nufa don daukar jadawalin karatu.

Lokacin da na karɓi jadawali na kuma kalli ajin farko "GST 101 Manhajar Rayuwa da Darajoji" na lumshe ido, na saki wani numfashi mai zurfi. A wannan rana na yanke shawara zan tsaya da ƙarfi, zan karanta da himma, zan rubuta labarina da hannuna.

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA ARBA'IN DA BIYU

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Bayan mun gama rajista, aka umarce mu da mu wuce zuwa ɗakin karatu na farko domin gabatar da zaman gabatarwa orientation. Hanyar zuwa ɗakin karatu tana zagaye da manyan bishiyoyi masu launin kore, kuma ginin ya keɓe da gilashi mai sheƙi. Na tsaya na kalli surar jami’ar gaba ɗaya, zuciyata na ta bugawa da sauri ba saboda tsoro ba, sai dai sabon abu da nake fuskanta.

A cikin ɗakin, mun zauna a tsari. Wurin ya ɗauki ɗalibai da dama, kowanne yana cikin natsuwa, wasu suna daukar hoto, wasu kuma suna faman rubuce-rubuce. Wata babbar malama ce ta shigo cikin tsari da kwarjini, ta fara yi mana jawabi.

“Ku kasance da gaskiya, ku bi dokoki, ku mutunta kanku da malamanku. Wannan ba irin makarantar secondary bace. Anan ne zaku fara gina kanku da gina makomarku.”Na zuba mata ido, kamar kowane kalmarta na shigar min kai tsaye cikin zuciya. Na fara fahimtar cewa jami’a ba kawai wurin karatu bace wurin canjin tunani ne. Wurin da ake kai mutum daga irin yadda yake zuwa wani matakin dabam.

Bayan zaman gabatarwar, aka raba mu zuwa rukunan ajin farko. Ni da wasu 'yan mata guda biyu da muka saba dasu tun daga wajen rajista muka haɗu a ajin “Use of English”. Mun zauna tare a layi na biyu, inda malam din ya shigo da laptop a hannunsa da projector a cikin jaka. Ya fara duba kowa da ido ɗaya bayan ɗaya.

“I know most of you think this is just English. But trust me, this course will test how you reason, how you write, and how you present yourself as a scholar.”

Yayin da yake magana, na duba cikin littafi na, na ce a raina “Ina fatan zan iya, zan tabbatar wannan dama ba ta wuce ni ba.”

Lokacin rana ya kusa. Bayan lectures na farko, na fita zuwa cafeteria. Wuri ne mai faɗi, an kawata shi da kujeru da tebura masu launin ja da fari. Na sayi meat pie da ruwan lemo, na samu wuri na zauna. A can wani saurayi ya gaishe ni, cikin ladabi da murya mai laushi. Sunansa Fahad.

Mun fara hira a hankali, ba tare da wata takura ba. Yana da fara’a, yana da nutsuwa. Daga hirar mu na gane cewa shi ɗalibi ne a Faculty of Law, kuma yana shekararsa ta biyu. “Don’t worry,” in ji shi, “Ranar farko ce ke nan. Za ki saba. Ai nima haka na fara.”

Na murmusa. Wannan karamin kalma da ya fada ta saka min ƙwarin gwiwa. Bayan mun gama cin abinci a cafeteria, na lura cewa rana ta fara ja. Fahad ya kalli agogon hannunsa.

“Ya kamata ki je ki ɗauki ID card ɗinki kafin su rufe ofis.” Na yi masa godiya, na miƙe daga kujerar, na ɗauki jakata, sannan muka rabu. Ina tafiya zuwa ofishin ɗaukar ID, zuciyata na karanta dukan abubuwan da suka faru tun daga safe rajista, orientation, ajin farko, da kuma wannan sabon abokin da na samu a cafeteria.

A ofishin, ɗalibai sun yi layi. Kowa na jiran a ɗauke masa hoto, ya karɓi kati da zai zama shaidarsa a cikin jami’a. Lokacin da aka kira sunana, na tashi na tsaya gaban kyamara. Wani mai daukar hoto ne ya ce “Kalli kai tsaye, ki murmusa kadan.” Na yi kamar yadda ya ce. A cikin wannan ɗan murmushin, akwai fata, akwai mafarki, akwai wata sabuwar ni da nake ƙoƙarin ginawa. Bayan na karɓi katin, na fito daga ofishin cikin natsuwa. Rana ta fara sauka, iska mai sanyi na busowa daga gefen bishiyoyi masu tsawo da suka kewaye makarantar. Na tsaya gefe ɗaya, na jingina da wata katanga, na duba katin ID dina sunana, hotona, da tambarin jami’a sun bayyana da kyau. Na saki ajiyar zuciya. Wannan kadan ne, amma yana nufin "na fara".

Bayan ƙarfe biyu aka sanar da mu cewa babu lecture har sai gobe. Kamar yadda yawancin ɗalibai suka ji daɗi da wannan dama, suka watse cikin nishaɗi, ni kuma nayi shiru. Na zauna cikin kaina, zuciyata na harbawa da sauri. Kawai sai naji inason naje naga Khalil.

Tun lokacin da na tura Musa ya tambaye min shi, ya ce min “yana lafiya kalou.” Wannan kalmar ta sauka a zuciyata tamkar ruwa mai sanyi. Sai dai ba ta isa ta kashe wutar da ke ci min zuciya ba wutar rashin ƙarewar tambayoyi da ƙaunar da na kasa musawa har yanzu.

Amma tsoro ya mamaye ni. Ina jin tsoro. Tsoron raina da nawa, da kuma tsoron abin da kalmar Abba ke nufi a raina. Tun wancan ranar da Abba ya gano cewa na sake kusantar Khalil, sai ya ce da karfi

“Allah ya isa! Wallahi ba zan yafe ba idan kika sake zuwa wajen wannan yaron!” Wannan kalmar ba ta bar zuciyata ba. Duk lokacin da nake jin inason na sake ganinsa, wannan kalma ce ke tsaya min a wuya kamar dutse. Ina so na yafe kaina, amma na san Abba bai yafe min ba. Kuma idan Abba bai yafe ba... shin Allah zai yafe?

A raina na tambayi kaina "Shin soyayya har ila yau zata sa ni bijirewa fushin uba?" Kallon Abba lokacin da yake faɗin kalmarsa yana cike da ɓacin rai da zafi yana yawo a idanunsa, har yanzu yana hango min a ido. Na tuna yanda nake kuka a wancan dare, na roƙi gafararsa, amma sai ya ɗauke kai. Na san babu inda zan sa kaina idan na karya alkawarina.

Na lumshe ido. Na dafe zuciyata. Wannan ba lokaci bane na jin daɗin soyayya. Wannan lokaci ne na ɗaukar matsayi matsayi tsakanin soyayya da biyayya. Na zabi biyayya. Kawai na hakura.

Na cire niyyar zuwa. Ban kuma kiran Musa ba. Ban tambaya ko Khalil yana ina ba. Na zauna a ƙarƙashin bishiyar da ke gaban hostel, zuciyata cike da murya guda

“Allah ya isa... ba zan yafe ba.”

Lokacin da Malam Idi ya zo daukaya, na shiga motar da gajiya amma da natsuwa. A wannan safiya, na fito daga gida da zuciya mai cike da rudani, amma yanzu, zan koma da zuciyar da ke cike da ƙaramin haske hasken da ke nuni da cewa abubuwa za su yi kyau, da lokaci. Na jingina a kujerar baya, na lumshe ido, ina sauraron sautin motar da ke gudu a kan titi. A raina, wata murya ta ce

“Kiyi hakuri da kanki. Ki ba kanki lokaci. Rayuwa tana da lokaci, da jarabawa, da lada.”

Da na koma gida da yamma, gajiya ta saukar min sosai kamar jaka da aka jefa. Jikina duk ya dau nauyi, kaina ma ya daina ɗaukar tunani. Na zube a kujera a falo ina sauke ajiyar zuciya. Cikin kankanin lokaci na mike da nauyi na shige ɗaki, nayi wanka da ruwa mai sanyi wanda ya dan kwantar da zafin gajiya a jikina. Na shirya cikin kayan gida masu sauƙi sannan na fito ina neman inda kayan Islamiyya suke.

“Momy, Islamiyya fa?” Na tambaya.

Tace cikin sakin fuska mara kulawa “Abbanki ne ya ce ki je.”

Na gyada kai, ba don na gamsu ba, sai don bana da ƙarfi a halin da nake ciki. Na leƙa cikin kicin babu abinci. Ko ƙamshin miya babu. Sai kwanon cornflakes da ya tsaya min idanuwa. Na haɗa shi da madara, na zauna a hankali na sha kamar wanda ba shi da gata.

Bayan haka na koma ɗaki na kwanta. Na lumshe ido amma kwakwalwata na ci gaba da tunani. Washegari lectures uku ke jirana kuma har yamma zan shafe a makaranta. A raina nace, "Ramlah, sai ki dage. Wannan ba lokacin kasala bane."

Na tashi da asuba da ɗan nauyi a jikina amma zuciyata cike take da ƙaramin ƙarfin guiwa. Bayan sallah na shirya cikin kayan makaranta, na saka hijabi, na ɗauki jakata, sannan na fita. Malam Idi ya iso da mota kamar kullum, na shiga a hankali ba tare da nayi magana ba. Hanya ba ta da hayaniya, sai zuciyata dake ta tattauna da ni.

Ni fa ɗaliba ce a Business Administration, kuma yau GST 102, BUS 101 da BUS 103 ne a jadawali na.

Lecture Na Farko GST 102 Communication Skills. Muka fara da GST. Aji ya cika da ɗalibai. Wasu na ɗaukar hoto, wasu kuma na gyara litattafai. Na zauna a baya kadan, ina mai shirin shan ilimi. Malamin ya shigo da fara’a, ya buɗe lecture din da cewa “Without communication, business cannot survive.” Ya ɗan sa dariya. Daga nan ya shiga bayani mai zurfi akan verbal da non-verbal communication, barriers, da feedback. Na rubuta sosai. Wasu lokuta nakan ji kamar lecture ɗin na magana da raina ne kamar ina karanta rayuwata cikin lecture.

Lecture Na Biyu BUS 101 Principles of Management. Wannan lecture ya rikita min hankali kaɗan. Malam ya shigo da kasala kamar wanda aka taso daga barci, amma sai ya fara magana da kwarjini “A good manager doesn’t control people. He guides them.” Ya koya mana game da planning, organizing, leading da controlling, sannan ya ambaci Henry Fayol. Kamar ana faɗa min yadda zan tsara rayuwata daga yanzu.

Lecture Na Uku BUS 103 Business Mathematics. Ni da lissafi ba abokai bane sosai, amma na shiga da shirin cin karo da kalubale. Lecture din ya rikita mutane da dama, amma na dage. Profit and loss, percentage analysis, da basic statistics ne abin da muka koya. Na rike biro kamar bindiga. Na shaƙe takarda kamar zanyi jayayya da ita.

A yau makaranta cike take da kuzari da nishaɗi. Kowa yana harkar dake gabansa wasu na zuwa café, wasu na ɗaukar hoto a harabar makaranta. Na zauna kusa da sabuwar kawata Maryam, muna tattaunawa akan test ɗin da malam ya ce zai kawo mako mai zuwa. Maryam tana da fara’a. Kamar bata da damuwa. Na dinga kallonta ina tunanin "Shin ni ma zan iya zama haka wata rana?"

Yayin da rana ta fara dusashewa, na fito daga lecture na karshe ina jin gajiya.

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA ARBA'IN DA UKU

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull