Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 20
Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 20: Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 20. Abba kullum dubu biyu yake bani, amma gaskiya ba su isheni komai…
4,480 words
Abba kullum dubu biyu yake bani, amma gaskiya ba su isheni komai ba. Makarantar mu fa, komai tsada. Ko ruwa ka siya ₦500 ne. Meat pie ma har ₦1,000. Sai dai in yi managing. Wasu lokuta sai na ci abinci sau ɗaya a rana kawai domin kuɗin su isa. Har na fara tara Canjin nawa dan naga ina bukatar gyaran jikina ina kuma bukatar kudin.
Lecture ɗin farko da muka shiga da safe, na zauna ne kawai da jiki a mace. Na kasa mayar da hankali. Ina jin kaina kamar yana zafi sosaj, ba komai ke shigowa cikin kunne na ba. Gaba ɗaya raina ya cunkushe. Ina jin ba daɗi. A class ɗin, sai kallon mutane nake yi wasu manyan mutane da make-up, wasu suna dariya, wasu suna buga TikTok, sai kuma wasu masu nutsuwa suna karatu. Gaskiya jami’a ba irin wacce na zata ba ce. Nan ne zaka ga tarbiyya, nan ne kuma zaka ga lalaci da rashin kunya, har cikin malamai ma ba a rasa irin hakan ba.
Lecture na biyu kuwa, ni da kaina nasan na zauna ne kawai domin kowa yana zaune. Na kasa gane komai. Kaina na ciwo, ciki na yana juyawa. Ko magana ban iya wa. Har mamaki nake yi yanda wasu ke iya daukan waya suna dariya a class, ni kuwa ba zan iya komai ba sai zuba ido.
Bayan lecture muka fita waje. Na tsaya gefen wani shago, na siya ruwa ₦500. Sai na sha kadan, na yayyafa sauran a fuska. Na samu wuri na zauna a ɗakin karatu, na duba diary ɗina, na fara rubuta
"Ya Allah, ka sauƙaƙa min. Ka bani lafiya. Ka cire wannan wari, wannan ciwo da wannan damuwa. Kar ka bar ni a haka, don ban da wanda zan faɗawa."
Har na zauna na rasa mafita. Ina jin kamar in kira Abba in gaya masa komai, amma sai na fasa. Kuny ta lullubeni Zan kira in ce masa, “Abba, gabana yana kaikayi kuma wari yake”??? Ai kamar raina wa mutum hankali ne hakan da kuma kunya ai. Kuma duk lokacin da ka faɗa masa wani abu mai sosa rai, sai ya ce in sanar da mumy.
Kullum na nafi son zama ni kaɗai. Idan lecture ya ƙare, sai dai in je ɗakin karatu ko in yi tafiya ni kaɗai. Wani lokacin kuma ina jin kamar in yi kuka. Amma ina? Ko kuka ba zai canza komai ba.
Yanzu haka, ina tunanin mafita. Kwana biyu kenan ban iya yin karatu da kyau ba. Bacci ma ba kamar yadda na saba ba. Ina mafarkin abubuwa iri-iri. Na rasa damuwar da ke tattare da zuciyata. Har Khalil da na rabu da shi kwana dayawa, yanzu sai mafarkinsa nake.
Wannan makon ma, na kasa kammala assignments. Gobe zamu gabatar da presentation, kuma har yanzu ban gama slides ɗina ba. Sai dai na dinga duban wasu daliban da suke da ƙarfi, sukan zo suna nuna mana cewa komai is easy. Amma ni nasan ba komai ne easy a wajena ba.
A makarantar mu, akwai abubuwan da sukan faru da sai dai mutum ya kalle su da ido, ya ɗauke rai. Amma zuciya tana cike da ƙorafi. Wasu malamai a makarantar, wallahi, Allah ya shirya su. Duk lokacin da suka shiga aji, ba abin da suke nema illa 'yan matan da suka fi kyau ko shigar zamani. Suna latsa ido kamar ba malamai ba. Za su je su tsaya kusa da mace, su fara magana da murmushi, su ce suna yaba mata da ƙoƙari, amma ashe wani abu ne suke nema a bayan kalmomin.
Wani lokaci har suna ɗaukar lambar waya suna cewa “zan taya ki da tutorial”, amma gashi kafin a jima sai su fara neman saduwa da daliba. Idan kin ki, sai su fara ba ki low marks, su hana ki shiga exam ko su ƙi amincewa da assignment ɗinki. Gaskiya wannan ba gaskiya ba ne, kuma haramun ne, amma babu mai magana saboda tsoro.
Wasu daga cikinmu kuwa Allah ya kyauta sai su ce ai dama shi ne hanya. Sai ki ji yarinya na cewa, “Ko na faɗa masa no, sai ya ba ni carry over. Na fi so in bi shi in huta.” Wannan kuma abin tausayi ne, saboda sukan cutar da kansu su yi tunanin suna samun sauƙi, amma ba su san cewa rayuwarsu na ci gaba da lalacewa ba. Da yawa daga cikinsu, ba su da burin kammala karatu da mutunci. Yanzu sai dai shigar jikin yara tops da wando ƙato suna zagaye makaranta kamar gaban mirrors. Wasu suna selfie da cinyoyinsu kawai suke so su nunawa duniya, ba ilimi ba.
Gaskiya rayuwar daliba mata a jami’a da wahala. Idan ba tsari da zuciya da hankali, sai ki lalace. Idan kuma kika tsare kanki, sai ki zama kamar bakya cikin “system.” Kullum sai kowa na cewa ke serious ce ko kuma ke religious ce. Amma sai da irin haka ne ake tsira.
Ni dai na bar kaina cikin tsarewar Allah. Dan yanda nake ji yanzu ciwon kai, wari, kaikayi, da rashin lafiyar da bana fahimta na fi buƙatar kulawa fiye da komai. Sai dai, wata sabuwa fada tsakanina da mumy jiya da dare. Tun safe banjin daɗi ba, amma ina kokarin dafa abinci. Sai mumy ta shigo da masifa, tana cewa “ke bani dankune na dakika daukai.” Na tsaya ina kallonta, ban ce komai ba. Tace “ ni kike wa shiru?” Nace, “Wallahi mumy ba haka bane. Wallahi jikina ke ciwo. Amma ban daukar miki ba Ba” Ta ce, “To ni ƙarya nake yi kenan? Kawai kina so ki rainani!” Nayi ƙoƙarin bada haƙuri, amma ba ta saurare ni ba. Tana zuwa ta zunduma min mari.
Gaba ɗaya na rikice. Idanun nawa suka cika da hawaye. Jiki na babu ƙarfi, zuciyata kuma cike take da raɗaɗi. Nace, “Wallahi Mum, ban da lafiya ne. Kika ma sake kallon jikina zaki ga...”
Amma kafin in ƙare zance, ta zage ni da kalmomi masu zafi. Tace ni ban da tarbiyya, cewa ina neman maza ne, cewa na gaji da karatu sai bariki. Wannan kalaman da marin suka fi duk ciwon da nake ji.
Na koma ɗaki na kulle kaina. Na zauna ina kuka. Kukan da ban iya bayyana shi ba. Nace, “Ya Allah, me na yi? Lafiya nake nema. Ina wurin da ba wanda ke fahimta ta.”
Daren jiya ban iya bacci ba. Na yi ta tunanin rayuwa. Shin haka ake rayuwa ne? Ko ni kaɗai ce nake cikin wannan bala’in? Gaskiya ya isheni.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ARBA'IN DA BAKWAI
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Da safe nayi kokarin tashi duk da jikina na a mace. Har yanzu kaina yana ciwo fiye da jiya. Na sha Paracetamol da safe, amma sai ciwon ke kara karfi kamar ana jujjuya kwano a cikin kwakwalwata. Na kasa cin abinci sosai, sai tea kadan da biskit. Komai a jikina kamar baya cikin hayyacinsa zuciyata na tashi, gabana na faduwa.
Amma yau presentation muke da shi, kuma ban yarda na sake karatu ba. Public Administration muke karantawa, kuma ina cikin group ɗin da za su fara gabatarwa. Na ɗauki takarduna, na zuba su a jaka, nayi addu’a, nayi shiru na jima kafin na fita.
Kafin na fita ne kuma Musa yazo. Bai shigo da fara'a ba kamar yadda ya saba. Ya tsaya a bakin ƙofa kamar wanda aka daka.
“Ina wuni,” yace da sassautaccen murya.
“Lafiya Musa? Ka ga Khalil din?” Na tambaye shi cikin sauri, zuciyata na bugawa kamar an tada karfe.
Yayi shiru. Yana kokarin duba idona, sai ya kauda kai. “Wallahi ba su barni na ganshi ba. Wani babban likita ne yace ba zamu iya ganin marasa lafiya yau ba.”
Na ce, “To lafiya kuwa? Me ya faru? Wane ciwo yake da shi da har ba a bari ana ziyara?”
Yayi karamin numfashi yace, “Na tambayi nurse. Tace kawai ‘da sauki ne’, amma bazata iya bada cikakken bayani ba. Sai dai ta ce yana samun kulawa sosai.”
“Da sauki?” Na maimaita cikin ƙara. “Da sauki amma ba a bar kowa ya ganshi? Me yasa suke boye mana komai?”
Zuciyata tayi raurau, jiki na ya yi sanyi, kaina ya fara juyawa da sauri kamar zan fadi. Sai kawai na kama bango domin kada in sulale a wajen. Musa ya matso yana faɗin inyi a hankali.
“Ki zauna mana.” yace. “Kamar kina jin jiri ne.”
Na kada kai kadan, hawaye na taruwa a idona. “Wallahi Musa idan wani abu ya faru da Khalil, bazan iya jurewa ba. Tun jiya nake mafarkinsa. Yau kuma sai ace ba a bar ka ka gan shi. Wane irin da sauki ne wannan?”
Yayi shiru, bai ce komai ba. Sai kawai ya zauna kusa da ni yana kallona da tausayi.
“Zan tafi makaranta,” na fada da karfi. Presentation ɗin mu yau ne, kuma ni ke da jagoranci.”
Musa ya tsaya yana kallona kamar ba zai yarda ba. Amma na mike tsaye na wanke fuskata da ruwa, na ɗauki hijab ɗina, na fice.
Da muka isa makaranta, zuciyata babu daɗi. Na zauna a cikin ajin da presentation ɗin zai gudana, ina jujjuya takardun da ban ma san me ke ciki ba. Idanuna sun rame, kaina kamar an dora masa dutse. Amma ina iya cewa duk da haka, na tafi da ƙwazo da nutsuwa.
Lecture ɗin ya shigo cikin aji, ya duba lissafin waɗanda ke da gabatarwa. Lokacin da ya kira sunan group ɗinmu, zuciyata ta buga. Sai na mike da ƙarfin hali, na fito gaban class. Na buɗe laptop ɗina, na haɗa projector, na fara magana.
Amma ina magana, sai na lura da wani abu da ya dame ni fiye da ciwon kai. Lecture ɗin yana kallona kamar zai cinye ni da idanuwa. Kallon da bana so, kallon da ban da buƙata, kallon da ya sa nayi kuskure na karanta “Public Admiration” maimakon “Public Administration.”
Sai na tsaya cak. Na gyara. Na yi murmushi na dole, amma zuciyata cike take da fargaba da jin kunya. Sauran daliban sai dariya suka fara yi kadan kadan. Na ji wata wuta kamar ina tafasa a ciki. Na ci gaba da magana, amma ganin irin kallon lecture ɗin ya fara damuna sosai. Ko dai yana kokarin cutar da ni ne kamar yadda wasu malamai ke yi wa wasu dalibai? Kamar yana daukar hotona da idanuwa.
Sai na kasa jurewa. Na kalli shi a ido. Ya danyi murmushi.
Subhanallah... Wannan murmushin fa na mutumin da yake kallonki ba don aikin ilimi ba, sai don wata sha’awa ko mugun nufi. Kamar na faɗi kalma guda a nan gaban aji “Sir, please stop looking at me like that.”
Amma na ƙyale. Na ci gaba da gabatarwa. Na dage da karfin zuciya, na kare abinda nake da niyyar fada, na zauna. Na kalli kasa, na ji ciwon kai yana kara tsananta.
Bayan na fito daga makaranta, jikina ya ƙara tsananta. Zazzabi ya tashi sosai. Kaina yana ƙara ciwo, jiki na yayi rauni. Na ƙara shigowa cikin gida da ƙyar, amma na ji muryar Mumy a palour tana fada kamar kullum.
“Ina gaya miki Billy! Wallahi sai dai ki fitar min da tsayayye a Samarin naki. Idan ba haka ba, sai dai ki fitar da kanki daga gidan nan! Kina neman ki jawo min bala’i! Mara tarbiyya kawai!”
Na tsaya a ƙofar palour, zuciyata na bugawa. Sai Billy ta tashi ta bar palon ba tare da ta ce komai ba. Ni kuma na yi sallama, na shigo cikin gida a hankali.
Mumy ko kallona bata yi ba. Kamar bata ganni ba kamar ba sallama nake ba. Na wuce cikin ɗakina. Na kwanta ina jin jiki na kamar ana hura masa wuta. Na rasa ina zan saka kaina. Dakyar nayi girkin dare ina Sallar isha’i na kwanta kwana biyu ko adduar bana iyayi saboda zazzabin dare dake rufeni.
Washegari da wuri nake da lecture dan haka da wuri na fita, Ina gama lecture na ƙarshe da rana, jikina kamar ba nawa ba. Kaina na sarawa sosai, idanuna na juyawa, ƙafafuna na rawa. Komai yana tafiya da ƙyar. Jikina yayi rauni fiye da yadda nake tsammani. Na dan tsaya gefe a bakin titi ina satar numfashi, sai na ga chemist a can nesa kadan. Na tattara ƙarfin da ya rage min, na nufi wajen.
“Yaya lafiya?” Cewar mai chemist din bayan na shigo da wata irin kwana da take nuna ba lafiya nake ba.
“Zazzabi ne, ciwon kai, da ciwon jiki.” Na fada cikin sanyin murya.
Ta duba min wasu magunguna, ta duba farashinsu sannan ta ce, “₦8,000 ne gaba daya.”
Na tsaya da baki a buɗe. ₦10,000 ne kacal ke hannuna –kudin da nake ajiyewa don wani abu da nake so nayi na kaina, abu mai muhimmanci. Amma yanzu lafiya ta fi. Ba zan iya hakura da magani ba.
Na dube ta, na ce “To ki bani.” Na ciro kudi na ba ta, na karbi magungunan, na fita da wata irin karyewar zuciya.
Ina shiga gida da magunguna a jaka, jikina a mace, sai Mumy tace daga saman bene.
“Ramlah ki shirya da sauri. Za mu gidan ‘yan uwan Abba. An yi rasuwa.”
Sai da gabana ya buga. Zuciyata ta fara faduwa. Na daina motsi tsawon dakika biyu. Mutuwa kuma? Ko dai... Khalil?
Na ɗan taka kadan, na ce a hankali, “Waye ya rasu?”
Ta juyo tana daure fuska tace, “Kakar su Abba ce. Wacce take zaune can kusa da su.”
Na sauke ajiyar zuciya, “Allah ya jikanta.”
Nayi shiru, na shiga ɗaki a hankali, na canza kaya. Hijab na dogo na saka, na fesa turare, Ina fitowa sai muka hadu da Bilkisu a waje
Na nufi gaban mota kamar yadda na saba. Nayi niyyar buɗe ƙofa na zauna. Sai kawai na ji tsawa daga Bilkisu “Ke gidan ubanki ne ke kadai? Ko motar ubanki ce? Wuce can, ki shiga baya!” Na tsaya, na kalle ta cikin mamaki da haushi. Amma na tuna tafiya ce ta gaisuwa. Na kasa cewa komai. Na juya na bude ƙofar baya, na zauna. Har sai da hawaye suka taru a idona amma na danne su.
Mun isa gidan cikin natsuwa. An sa kujeru a farfajiya. Muka zauna. Ana ta shigowa da ficewa, ana karɓar gaisuwa.
Ni kuma na zauna a gefen Mumy, cikin nutsuwa. Magungunan da na sha sun fara rage radadi, amma ba su kawar da gajiyata ba. Duk da haka, na zauna cikin ladabi da kamun kai. Na rufe bakina, na sunkuyar da kai. Amma a lokacin ne wasu suka fara gulma daga gefena. Wata dattijuwa daga cikin ‘yan uwan Abba ta fara magana da wata a kunnenta, amma duk inajinsu.
“To Ramlah ce dai kinganta kamar yar labarawa ko dayake balarabiyar ce tunda uwarta haka take. dayake tafara zuwa makaranta mai shigen tsada da kudi fa. Amma naga kamar ba ta damu da Khalil ba. Yaron har yanzu yana jinya, amma ki kalleta ko ajiƙinta ko adan yatsanta ahaka kamar ta Allah sai munafurci.”
Wata tayi dariya ta ce, “Ai ni nasan dai babu yanda za ayi su yi aure. Dama ita ce ta rikita Malam dinnan. Tace wai Khalil bai dace da ita ba. Dan taga tanada kyau.”
Suka sa dariya. Wani daga cikinsu ya ce, “To dan tanada kyau sai tafara raina mutane?.”
Na sunkuyar da kai. Na ƙura ido cikin tabarma. Na ma rasa wane hawaye ne nake kokarin dannewa. Gaskiya ba su san ciwon zuciya na ba. Maganar su ta fi zafin maganin da na sha dazu.
Suna ci gaba da zance. “Ai idan ba masu kudi ba wannan yarinyar bata auren dangi tabbijan bakuganta ba kamar ita tayi kanta?.”
Na ci gaba dayin shiru. Ko kallonsu ban yi. Ban ma motsa ba. Na ce a raina, “Na haƙura. Zan yi shiru, zan barwa Allah.Ina zaune, Bilkisu tana gefe tana kallona da idon ƙiyayya. Har da girgiza kai tana dan gunguni. Idan na duba, sai ta kau da kai kamar ba ni take kallo ba. Amma nasan zuciyarta kamar wuta take yanzu ni ce kowa ke magana akai haushina take ji. Bilkisu ta dade tana jin cewa rayuwata bata dace da jin daɗi ba.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ARBA'IN DA TAKWAS
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Muna zaune a gefe, nayi shiru kamar ba ni ba. Na dafe kaina saboda ciwo yana ƙara girma. Duk da magungunan da na sha da safe, kamar ba su aiki. Idanuna suna sauka da wahala, zuciyata kuma cike take da abubuwa da yawa. Har yanzu nake jin kalaman gulmar da suka yi a kusa da ni, suna yawo cikin kunne na kamar amsa.
Yaya za a ce gidan mutuwa ya koma gidan gulma? Gidan da za a tuna da mutuwa da addu’a ya koma wurin cin zarafi da wulakanci?
Wannan tambaya ce kawai da zuciyata ke maimaitawa. Sai kuma naji muryar maza suna shigowa harabar gidan sunata gaida mutane suna gaisuwa..
Alhaji Munzali ne kawun su Abba, babban mutum a cikin ‘yan uwan Abba. Idan ya shigo, kowa yana nutsuwa, domin mutum ne mai daraja. Amma yau kam, fuskar sa ta bayyana damuwa. Kamar wanda ya jima da kuka.
Yana shigowa, sai kawai ya kalli mutanen gidan. Kowa yayi shiru. Sai ya ce da murya mai rauni “Khalil ya rasu. Allah yayi masa rasuwa yanzu.”
Wani dumi ne ya zube min a kai. Wani sanyi mai ƙara daka zuciya ya ratsa gabadaya jikina. Kamar wata iska ta buga ni daga baya. Komai ya tsaya. Kamar rayuwa ta daina tafiya. Na rasa numfashi. Ina kallon Alhaji Munzali, baki na a buɗe, zuciyata na harbawa da ƙarfi. Na buɗe baki ina so in ce wani abu amma babu muryar da zata fito. Idona ya raina gani. Idanuna sun jike, sun rikice. Na ji kamar zan fashe. “Khalil?” Na furta a hankali.
Sai kawai niyi wani ƙara da karfi “A’a! Khalil bai mutu ba! Don Allah kuce karya ne!” Kowa ya juya kaina. Kafin wani ya iya tashi na saki ihu mai karfi.Na kamo hijabi na na fizge, na durƙusa kasa, sannan na fadi a kasa kamar an sare itace,Na suma. A gaban kowa.
Mutane suka fara kururuwa. Wata ta kama hannuna, wata ta duba idanuna. “Ta fita hayyacinta!” wani yace. “Da sauri a kira mota, a kaita asibiti!” Alhaji Munzali ya dakko waya da sauri ya kira Abba. “Ku zo da mota! Ramlah ta faɗi bata motsi.”
Yaya Billy da Mumy da wasu daga cikin dangin gidan suka tsorata. Kamar abin ya fi yadda suka zata. Mumy ta kasa cewa komai, idonta ya ƙafe a kaina..
Lokacin da na fadi a gidan gaisuwa, ban kuma san kaina ba. Na fadi a kasa tamkar wadda aka cire rai. Kamar wani iska ya kwashe ni, ya tafi da zuciyata zuwa wani wuri nesa. Komai duhu. Komai shiru. Ina cikin wata irin ƙasa da ba na iya kiran ta duniya ba.
Gaba daya jikina ya mutu. Na shiga doguwar suma. Likitoci suna ta kokarin dawo da ni hayyacina. A gaggauce aka kaini asibiti cikin mota, aka shigar da ni zuwa gaggawa (emergency ward). Na kwanta a gadon asibiti, hannaye na kwance, numfashina a hankali. Kamar numfashin wanda ke cikin mafarki, ba tare da mafarkin yana da dadi ba.
Likita ya dubi nurse yace, “Ta shiga doguwar suma. Amma har yanzu zuciyarta na bugawa. Jikinta na da rauni sosai.”
Bayan kusan awa biyu, na fara motsawa kadan. Na buɗe ido a hankali. Ina duba sama. Idona na yawo, amma zuciyata a cike take da wani irin zafi da na kasa fassarawa Sai na saki wani irin ihun da ya girgiza dakin
“Khalil! Khalil! Don Allah kar ka barni! Ka dawo! Khalil!” Na sanya kuka. Na fara jijjiga jikina kamar ina yaki da wani abu da ba a gani. Nurse ta rike ni da sauri, ta kira likita, ta kira family dina da ke bakin asibiti. Abba da Mumy suka shigo. Na dago kai na ina kuka, na ce, “Yace min zai dawo. Me ya sa bai dawo ba? Don Allah ku gaya min ba gaskiya bane…” Na sake faɗi. Likita ya duba ni, ya ce da nurse “Ta rasa jini. Blood pressure dinta ya sauka ƙasa sosai. Sai an sanya mata jini cikin gaggawa.” Nurse tace, “To yanzu sai mu fara gwajin wanda ya dace da jinin nata. A gaggauce aka fara duba wanda jinin sa zai dace da nawa. Ina kwance a gado, ina cikin ciwo da rashin hayyacina, amma jiki na yana kokarin faduwa gaba daya. Wata nurse ta zo ta dubi Abba “Dan Allah malam, akwai wani daga cikin ‘yan uwa da za mu iya amfani da jinin sa? Idan babu, za mu je asubuti mu siya.” Abba ya ce, “Ku fara gwada jinina dana kanina .” Aka fara da su. Sakamako ya fito bai dace ba. Aka gwada na wani daga cikin dangin abba suma bai dace ba. Har ana tunanin sai an je asibitin gwamnati don a samo jini cikin gaggawa.
Sai likita ya ce, “Mu kira Dr Hari shima babban likitane Da aka duba nasa, sai aka ga jinin sa ne ya dace da na Ramlah.
Cikin sauri aka saka mata allurar kariya, aka cire masa jini, aka soma shiryawa don sanyamin.
Mumy na zaune kusa da gadon asibiti, tana riƙe da hannuna kamar tausayinta ya kai kololuwa. Ita ce ke girgiza kai tana cewa, “Ya Allah ka tausaya wa Ramlah. Zan rasa komai idan na rasa ta.”
A gaban mutane sai tana share hawaye, tana nuna kamar tafi kowa damuwa. Har mutane suna ce mata, “Mumy ki kwantar da hankali. Allah zai bata lafiya.” Sai ta ce, “Ramlah rayuwata ce. Ko ban nuna ba, ina sonta fiye da rai na.” Amma a cikin zuciyarta, ba haka take ji ba nasani. Abba ya ce da ita, “Ki zauna anan da ita, ni zan je ayi jana’izar Khalil.”
Ta ce, “To, Allah ya karɓe sa ya yafe masa ya gafarta masa. Ka je, zan tsaya da ita.” Sai ta mayar da murmushin tausayi ga mutanen da ke kusa. Amma da aka fita, bayan mutane sun bar dakin, sai tace “Yanzu ai rayuwar ki tafara lallacewa ramlah sai kin zamana baki da gata koda na sauro ne sai tasanya dariya. Allah ya ɗauki abin da zai jawo min matsala.”
Sai tayi wani siririn dariya.
Ina kwance Jini yana shigowa jikina a hankali. Amma har yanzu ina cikin doguwar suma. Nurse suna lura dani.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ARBA'IN DA TARA
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Cikin dare na farka da tsananin kuka. Na farka kamar wacce aka tasar da ita daga mafarki mai zafi. Na dinga jijjiga jikina, ina girgiza kai, hawaye suna zuba a idona sosai. Sai na fara magana da karfi “Khalil! Khalil! Don Allah kar ka bar ni! Ka dawo mana! Ka ce min zaka warke…” Na tashi daga gadon da nake kwance, da ƙyar na ɗaga jikina. Jiki a mace, amma zuciyata kamar wuta ake hura mata. Na dinga kokarin fita daga dakin asibiti da ƙarfi, kiran sunan Khalil kamar zan same shi a wani sashi. “KHALIL! KHALIL!!” Na dinga kiran sa cikin murya mai cike da raɗaɗi.
Mumy tana zaune a gefen kujera. Tayi kamar tana bacci, amma na tabbata tana jin kiran da nake yi. Ta motsa, amma ta yi shiru.
Nayi ward din da ƙafa na ina rawar jiki. Ihu na ya firgita ma’aikatan asibitin. Nurse biyu da wani likita suka fito a guje. Daya ya ce, “Rikota! Har yanzu tana cikin shock, zata iya cutar da kanta!”
Suka riƙe ni da ƙarfi, suna kwantar da ni da tausayi. Na dinga fizge-fizge, har suka ɗauko allura suka yi min maganin saboda zazzabin dake jikinai. Har sai da jikina ya yi sanyi, suka dawo da ni dakin.
Nurse ta ɗan tafa kafadar Mumy
“Mumy, ki kula da ita hajiya yanzu duk ihun nan nata bakiji ba saboda Allah data fita babu kowa a ward dinfa?.”
Mumy ta jinjina kai. Sai suka fita suka bar mu. Ina kwance a dakin, ban iya motsawa, amma idona biyu. Ba bacci nake ba.
Mumy ta ɗauka nayi bacci ne. Sai ta sauke numfashi. Ta juyo ta kwanta a kujera, sai na ji ta fara magana “Ni baiwartace da zan tsaya ina gadinta ji wata nurse da maganar banza ai data fita tabi duniya yafi mana, haka kurum
Ta gyara kwanciya. Tana kokarin komawa bacci.
Ni dai ban motsa ba, amma zuciyata ta ji komai.
Da safe, ina kwance ban iya magana. Jikina ya yi rauni, numfashi na yana fitowa a hankali, kamar na wanda ba ya da karfi.
Sai dai har yanzu zuciyata ta kasa yadda cewa Khalil ya mutu.
Wata nurse ta shigo ta duba ni. Tace, “Alhamdulillah, kina samun sauki. Amma har yanzu jiki ba ya da karfi sosai. Sai a ci gaba da lura da ita.”
Bayan lokaci kadan, su Abba suka shigo da wasu daga cikin ‘yan uwa. Sun tsaya a bakin gadon, wasu na cewa “Allah ya taimake ki, Ramlah.” Wasu na shafa kafada, wasu na kallona da tausayi. Amma babu wanda ya san yanda nake ji.
Ban ce komai ba. Ina jin kamar wata hasara ce ta cika zuciyata har tana hana ni magana. Sai dai hawaye ne kawai suke kwaranya daga idona, koda ba na kuka da murya.
Sai ga Yaya Mujittapha, dan uwan Khalil na jini, wanda yayi karatun addini sosai, yana da nutsuwa da mutunci. Yana zuwa ya tsaya a gefen gadon. Ya kama hannuna a hankali.
Shima idanunsa cike da hawaye. Bai ce komai ba na wani lokaci. Sai ya daure, ya ce Ramlah… Khalil ya gaya min wani abu kafin ya rasu. Yace idan wani abu ya faru da shi, ki sani cewa ba ki da laifi. Ki yi masa addua. Kada ki zubar da hawayen da bai cancanta ba. Ki ci gaba da rayuwarki. Ki gina kanki. Kiyi masa addu’a.”
Na fashe da kuka. Na saki hannunsa, na dafe kaina “Khalil! Khalil!! Me yasa ka tafi?” “Kaina! Kaina!!” Na hau ihu, na zame da ƙarfi, jikina ya fara rawa. Ya Mujittapha ya firgita, ya ce “Nurse! Nurse!” ya fita da gudu ya kira su Abba da Nurse.
Nurse ta shigo a guje, Abba ya biyo bayanta da wasu daga gidan. Suka kama ni. Na shiga fizge-fizge, sai dai a ƙarshe suka danne ni, suka sake yi min allura. Jikina ya lafa. Idona ya lumshe. Numfashi ya koma a hankali.