Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 21

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 21

Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 21: Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 21. Yayin da ake zaman makokin Khalil a gida, ni kuma a nan asibiti…

4,467 words

Yayin da ake zaman makokin Khalil a gida, ni kuma a nan asibiti nake kwance. Ina kwance cikin rauni da zafin zazzabi. Cikin damuwa da rashin kuzari. Cikin raunukan da ba likita zai gane ba, sai zuciya mai fahimtar zafin rasa masoyi. Cikin wani salo mai ban tsoro, na kasance wacce ba ta da ƙarfi a jiki da zuciya. Ranar da aka tafi da shi, ni ban je ba. Ban gan shi ba. Ban ga jana'izarsa ba. Amma na ji kamar raina yana tare da gawarsa.

Yau da asuba, zazzabi ya taso min sosai. Na tashi da kyar na yi sallar asuba, jikina duk yana rawa. Na ɗora hannu a ƙirjina, ina jin bugun zuciyata da ƙarfi. Baya ga zafin rashin lafiya, bayanin jana’izar da akayi min jiya yana ci gaba da dawowa a zuciyata kamar fim.

Nurse ta shigo da allura a hannu, tana murmushi kadan kamar tana tausayina. Ta duba zafin jikina ta ce “Zazzabin ki yana da yawa. Amma da sannu zaki warke. Ki ƙarfafa zuciya.” Na kada kai kawai. Na kasa magana. Idona sun kumbura da kuka da rashin bacci. Daga nan ta fita Kusan mintuna talatin da nurse ta fita, sai na ji ana bude ƙofar dakin. Sai ga Maman Khalil da wasu ‘yan uwanta mata biyu. Suka shigo ba tare da sallama ba, ba tare da murmushi ko rahama ba. Kamar masu aikin bibiya suka shigo.

Na juyo na kallesu. Cikin ciwo, na ɗan daga kai kawai. Ina son na ce da su “Sannu da zuwa,” amma babu muryar da zata fito.

Sai Maman Khalil ta tsaya a gabana, ta dubeni da idon da ya cika da tsana, sai ta ce da karfi: “Ke ba kya jin tsoron Allah ne? Da kika kashe min ɗa! Kin tsaya kika hana shi kwanciyar hankali har Allah ya karɓi amanarsa!”

Na buɗe baki da mamaki. Kamar mafarki nake. Na sauke idona kasa, hawaye suka zubo daga idanuna. Wata daga cikin su ta ce “Allah zai saka mana! Rayuwa ba zata bar ki lafiya ba. Zaki ɗanɗani kunci.yanzu kuma sai ki ɗanɗani sakamako.”

Na kara juyar da idona gefe. Na ma rasa inda zan kalle su. Wani abu a zuciyata yana ce min “Toh ni fa ban yi komai ba…”

Amma ban iya kare kaina ba. Babu karfi, babu lafiyar jiki, kuma babu wanda zai tsaya min.

Suka ci gaba da maganganun su . Sun yi tsawon lokaci suna zagina, suna fadin abubuwan da suka firgita zuciyata. Wasu daga cikinsu suna cewa “Ai ita ce ta jawo wa ɗanmu cutar da ta kashe shi.”

“Ta raina mu, yanzu zata ga abinda rayuwa ke nufi.: “Zan tabbatar ba zata cigaba da karatu ba...” Daga karshe, suka juya suka fita. Ba su tsaya ko don su dubi yanayina na ciwo ba. Ba su yi addu’a ba.

Ban san inda Mumy take ba a lokacin. Amma ina zaton tana waje, ko tana waya da wani, ko kuma tana fakewa ne kamar ba ta sani. Duk da kuwa ta ce “zan kula da Ramlah.” Kuma duk da cewa asibitin ya cika da jama’a nurses da marasa lafiya na ji kamar ni daya ce a duniya. Duk da irin zafin jiki da nake ji, zafin zuciya da cin mutunci ne ya fi komai zafi. Na runtse ido da karfi, ina jin yadda hawaye ke kwaranya. Ban iya hana kaina ba. Ban iya daurewa ba. Na fashe da kuka. Sai na ce a raina “Me na yi wa mutane haka? Na rasa masoyi… na rasa lafiya… yanzu kuma cin mutunci?” Kamar na fasa ihu. Kamar na buɗe ƙirjina in nuna musu raunin da nake ji. Amma babu wanda zai gani. Babu wanda zai ji. Sai Allah.

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA HAMSIN

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Bentley mai baƙin fata ta tsaya a gaban babban asibitin Georges Pompidou da ke tsakiyar birnin Paris.iska tana motsa ganyaye a hankali. Pascal direban As’ad ya buɗe ƙofar baya da girmamawa. As’ad Babangida ya fito. Sanye yake da suit ruwan toka, rigar ciki fari ƙal, sai agogon zinare a hannunsa wanda ke ɗaukar ido. Takalmansa sun yi sai kyalli suke, kamar ba a taɓa taka su ba.

Shigarsa cikin asibitin ya jawo hankalin ma’aikata. Sun gaishe shi da ladabi, suna murmushi, amma ba wanda ya isa ya shige jikinsa. Fuskar As’ad a kame take. Ba dariya, ba magana sai matakin kafarsa da murya mara amo.

Elevator ya ɗauke shi zuwa bene na huɗu. Har sai da wani doctor ya leƙa ofishin Dr. Luc Morel kafin ya ce “Sir, Mr. Babangida is here.”

Dr. Morel farar fata mai kyakkyawar fuska ya miƙe da murmushi. Ya buɗe ƙofa da kansa, yana faɗin cikin yarensu “Welcome, Mr. Babangida.” As’ad ya gaishe shi da gajeriyar murya. Bai da yawan magana. Likitan ya ɗauko takarda. Ya duba da ido, sannan ya ce cikin sauƙin lafazi “We’ve gone through your tests. Blood, hormone, physical scans… all normal.” As’ad ya ɗaga ido, yana kallon shi kai tsaye. “Toh me ke hana jikina aiki me isa banda kuzari gabana yazama shanyayye?” Likitan ya dan yi shiru. Ya duba cikin idanunsa, sannan ya ce da kwantar da murya “Stress. Possibly emotional. Your body is functioning. But the signal, the drive it’s blocked. Could be the mind.” As’ad ya jingina da kujerar. Ya sauke numfashi mai nauyi. “Shekara kenan. Ina ganin abubuwa Daban-daban. Allura. Gwaji. Duba. Shawara. Likita kala-kala. Duk suna ce min lafiya. Ni kuma gashi bani da lafiya.”

Dr. Morel ya saka takardun a gefe, yana kallon shi ba tare da katse numfashinsa ba. “Some things the body cannot explain with numbers. Talk to your wife. She's part of this.” As’ad ya dan kaɗa kai, cikin ƙasa da murya.

“Na riga na gaya mata. Ta sani. Tana kokari sosai. Sai dai ni... ni kaina ban gane kaina ba.” Dr. Morel ya rubuta wani magani a takarda. “Ka sha wannan maganin,mu gwada mugani.

As’ad ya miƙe. Ya karɓi takardar, ya saka cikin aljihun rigarsa. Bai ce komai ba ya juya ya fita, Zuciyarsa Babu daɗi ko ƙadan baƙinciki sosai ke damunsa.

Yana Fita Motar Bentley na jiran shi kamar yadda aka saba. Pascal ya buɗe ƙofa, ya zauna ba tare da ce wa komai ba. Yana da hankali, ya san lokacin da magana bata da amfani. As’ad ya janyo wayarsa. Ya danna sunan "Aysha". Bayan ɗan lokaci, muryar mace mai laushi ta amsa “Yaya asibiti?”

As’ad ya ce cikin kasalalliyar murya

“Ai kin riga kin sani. Sun ce lafiya. Amma ni bana jin hakan ai kowannen su maganar sa daya ayshatu kirjina babu dadi am hurt..”

“Ka dawo gida Habibie kadaina jin komai habibie ina tare dakai kuma ni nagayamaka ban damuwa da wannan matsalar me isa kai zakana damun ƙanka da'ita?. Na haɗa ruwan ganye kamar yadda muka tattauna. Ba laifi idan mun sake gwadawa.”

“Ina zuwa.” Ya kashe wayar.

Pascal ya ja motar a hankali, yana sanin cewa tafiyar yau oga Yana ciƙin damuwa duk da baisan akan menene ba. Yayin da motar ke tafiya cikin titunan birnin da rana ke dusashewa, zuciyar As’ad na juyawa kamar ƙaho a zuciya. Duniya na ganinsa a matsayin gwarzo wanda ya mallaki kadarori da kamfanoni, wanda ke hawa jirgi na musamman, wanda agogon hannunsa ya fi albashin wasu. Amma shi fa? Shi kansa ya rasa inda jikinsa ya tsaya.

As’ad mutum ne da ya saba da komai cikin salo, A kicin gidansa, akwai chef daga Lebanon. A dakinsa, kayan turare daga Dubai da France. A rayuwarsa, babu abu da ya rasa sai wata aba da ba a saye ta da kuɗi ba.

Wannan asibiti Pompidou na 10 da ya ziyarta cikin shekara guda. Kowane na cewa “ba matsala”. Amma yana jin matsala na raye cikin sa.

Pascal ya waigo ta madubi, ya ce da siririyar murya “Sir… any other stop before home?”

As’ad ya dan jinjina kai

“No. Let’s go home.”

Gidan yana can kusa da Eiffel Tower wani katafaren gida mai bene uku, lambu mai tsada da haske da ruwa mai ratsa ta tsakiyar shinge. Amma koda suka isa, As’ad bai shiga cikin gida kai tsaye ba. Ya tsaya a gaban ƙofar mota, yana kallon sama

“Lafiya…” ya furta cikin zuciyarsa,

“…ita ce mafi girman arziki. Da ƙudinka ko matsayinka bazai baka ba.

Gidan ya yi shiru, duk da cewa ya cika da haske mai taushi da ƙamshi mai daɗi daga turaren oud da ke ɓuya a cikin falo.

Aysha tana zaune a wani ɗan karamin rumfa da aka ƙera musamman da launin fari. Ta ninke ƙafafunta a cikin babban kujera, tana kallon ruwan tururi da ke fitowa daga kwalbar herbal diffuser.

Rigarta doguwa ce mai ƙyalli, launin ash da zinare, ɗinkin Qatar ne, amma ta sa hijabi mai laushi da ba ya rufe hasken fatarta. Hannunta ɗaya yana jujjuya gilashin ruwan ganye mai haske wani hadin da ita da likitan Sudan suka tsara daga ganyen yadiya, kuka, magarya da hulba.

Kanta yana cike da tunani. Kodayake gida yana ɗauke da dukkan annashuwa da jin daɗin rayuwa zuciyarta na ɗauke da nauyin da damuwar mijinta ke sanya kanshi ita bata damuba amma shi gana daya yakasa sukuni sai kashi maƙudan kudi da yakeyi.

A gefe, wata nurse mai kula da lafiya ta shigo da tablet a hannu. “Madam, blood pressure ɗinki da sugar level sun daidaita. Should I bring in your spa therapist now?”

Aysha ta girgiza kai.

“No, leave me for now. Tell Fatima to warm the dinner. I’ll serve my husband myself.”

*****************

Yana tsaka da Aiki sosai cikin system ɗinsa. Gaban wata ƙaramar tebur mai madubin, As’ad na zaune yana latsa maballan laptop ɗinsa na Apple sabon “MacBook Titanium”, yana duban takardun karshe na jarin da zai buɗe a Dubai. Duk da kayan cikakken kwalliya da dumin dakin da ke ɗauke da AC mai daidaita ƙamshi, fuskar sa ta cike da gajiya. Gajiya mai zurfi wacce ba aiki kadai ke kawowa ba, sai tunani da tambayoyin da ba su da amsa.

A gefe, ruwan ganye da Aysha ta haɗa masa na ɗauke a cikin kwalbar “Hermès health set” da aka kawo daga Morocco. Ruwan yana da ɗan ƙamshi, ya sha bamban da duk wani magani da ya taɓa gwadawa sai dai har yanzu, bai kai da yaye masa matsalarsa ba .

Aysha ta shigo cikin dakin. Ta shigo cikin suttura mai sauƙi amma cike da kyau,doguwar riga ruwan ja mai ɗaukar ido. Turaren ta na cike dakin kafin har ta ƙaraso kusa da shi. Tana tafiya cikin wani salo na natsuwar sai taƙu takeyi ɗai ɗai.

Ta tsaya a kansa. Ta durƙusa kaɗan, ta sumbaci leɓensa, sannan ta ce cikin murya mai daɗi “Sannu da aiki Habibie... har yanzu baka gama ba? Ka tuna kana da flight fa na 5. Ko bakason ka huta?”

Ya langwabar da kansa kaɗan.

Idanunsa sun Nuna tsantsan da ƙauna da gajiya, amma ya zuba mata idanuwan yana murmushi. “Ban gama ba. Amma na gaji.”

Murmushi yayi, yana miƙa mata hannu cikin salo da kwantar da hankali. Idanunsa cike da natsuwa da narkewar zuciya. Ya langwabar da kansa, yana kallonta da irin kallon da masoyi ke kallon ƙaunatacciya bayan kwana goma sha biyu a keɓe.

Itama, jikinsa ya narkar da nata. Tayi masa wani irin kallo mai cike da salo da shagwaba. Ta zauna a jikinsa, ta ɗan jingina kamar wata yarinya wadda ke buƙatar kulawa daga iyayenta. Tana rungume shi da damƙa, sai ta furta da tura baki

“Habibie ka huta mana dan Allah. Ban son kana damun kanka da aikin nan.

Tana shafa kansa a hankali. “Ka kwantar da hankalinka. Ni fa ina nan. Aiki ba zai ƙare ba, amma ni zan iya rage maka nauyi in dai zaka bani damar.”

Sai da ya yi dariya mai rauni. Kafin ya buɗe baki, wayarsa ta yi vibration ƙara mai ƙarfi.

Ya duba sunan, ya ƙauda kansa. Ya san wannan kira na Sakina.Tun jiya Sakina ke damunsa da waya. Ko da ya rufe dukkan lambobinta, sai ta sake samunsa ta wata hanya. Ta samu wata number daban ta sake kiran sa. Bai kamata ba. Ya kamata ta fahimta ba shi da lafiyar da zai iya zama da kowace mace yanzu, amma ita ta kafe tana cewa ita da halin da take ciki haka take sonsa.

Karar wayarsa ce ta katse wannan shaukin Yana kallon wayar, ya kau da kai. Sai kira ya ƙara shigowa. Tana kallonsa. Tace da saukin murya “Bari na ɗauka.” Bai ce uffan ba. Ta kai hannunta, ta ɗaga wayar. A nan ne kawai taji muryar Sakina a gefe ɗaya, tana cike da rawar murya da wahala kamar wa

“Yaya As’ad… kana son zuciyata ta buga da ƙaunarka? Kana son in mutu saboda kai? Yayana please… duk yadda kake, I love you. Kuma… I want to be your wife.”

Ayshatu tayi murmushi mai ɗan tsuma rai, wanda bai cika da annuri ba. Murmushi ne mai ɗan ɗaurewa da juriya. Ta miƙa masa wayar cikin natsuwa. Bai ce komai ba, sai kawai ya katse kiran.

Itama sai ta fara kokarin mikewa daga jikinsa fuskarta tana nuna tsantsar kishi da damuwa riko hannunta yayi saurin yi yna maidata ƙan cinyar tasa sannan Yayi saurin jiyo da kanta, ya kama hannunta a hankali. Idanunsa suka cakuda da nata cikin natsuwa.

“Wannan kishin naki... shi ne nake jin dumi da shi a cikin sanyi. Shi ne yake tabbatar min da cewa ni ne jarumin cikin zuciyarki .”

Kawai sai ta fashe da kuka, kamar yarinya da aka ƙwace mata abin wasa. Kukanta bai da hayaniya amma yana da nauyi.

Bai bari ta yi magana ba ya kama ƙafarta da hannunsa ɗaya, yana daddanna gashinta da ɗayan hannun. Sai ya ɗora bakinsa a kan nata, ya shiga kissing da nutsuwa kamar yana shanye damuwarta da harshensa.

Kiss ɗin ba wai na wauta bane. Kiss ɗin zuciya ne. Na mutum da ya fahimci cewa shi da wannan matar a guri ɗaya zuciya suke da zama. Yana taunar ɗokin soyayyarta a leɓenta, tana saki numfashi da sauti kamar tana jin sauƙi cikin jikinta. Aysha ta dafa kirjinsa. Zuciyarta da nashi suna bugawa cikin daidaito. Sanyin jikinsa,Dumin numfashinsa.

Ƙamshin kansa da ya fi turare.

INA MANYAN MATAN SUKE NE💃

"Maza fa, ko da suna da karfi, ko da suna da kudi, wallahi suna son shagwaɓa.

Duk girman ki, dan Allah ki sauko, ki rinka yimasa kalmomi masu daɗi. Ko ba har zuciyarki bane, ki nuna masa jin daɗinki. Ki nuna masa cewa damuwarsa damuwarki ce.

Wallahi maza suna bukatar abu mai sauƙi a rinka yi musu irin shagwaɓar da yara ke samu."

“ idan kina son mallakar zuciyar mijinki gaba ɗaya... to ki rinka gaya masa kalmomi masu laushi. Ki gaya masa cewa yana da kyau, cewa yafi kowa. Ki riƙa sa hannunki cikin nasa koda babu dalili.

Wannan abu ne da maza ke mutuwa akai ba soyayyar gado ƙadai ba, soyayya kullum ana sabunta ta.”

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA HAMSIN DA DAYA

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Ƙarfe huɗu da rabi na asuba a cikin Paris. Gidan Sosai Yashiga yana tsakiyar birni,

Cikin Nutsuwa ya farka daga bacci. Ya sauko daga gadon , yana takawa a kan kafet mai laushi cikin izzarsa. Yayi nuni da hannun da remote ke curtains suka buɗe da kansu gidan yana da smart system.

Yana cikin shiri. Ranar yau zai tafi Morocco domin ƙulla sabon kasuwanci da gwamnati shirin kafa babban kamfanin kayan gini wanda zai shigo da kayan zamani daga Turkey zuwa Afrika.

Ya shiga wanka. Ruwa na fesa daga shower a hankali Bayan yayi wanka, ya shafa turaren Tom Ford, ya sa kaya daga Dolce & Gabbana farar riga, wando mai laushi, agogon Rolex na zinariya, da takalma Italian.

Da ya fito daga ɗaki, sai ga Ayshatu.

Tana sanye da doguwar rigar bacci mai silk, gashinta ya zubo a kafada, fuskarta tayi kumburi kamar wadda ta sha kuka.

“Habibie …” ta faɗa da sanyi.

Ya tsaya. “ Ayshatu. Zanyi tafiya yau.”

Ta matso kusa dashi, ta riƙe hannunsa. “Kayi cancelling tafiyar nan. Ni fa bazan iya jure zaman gida idan baka nan ba.”

Ya shafa kanta a hankali. “Ki fahimta Ayshatu. Wannan tafiya na kasuwanci ce. Yana da mahimmancu sosai. In komai ya yi daidai, zan sa hannu da gwamnatin Morocco. Wannan deal ɗin zai bude kasuwanci a kasashen Afrika biyar.”

Ta fashe da kuka. “Ni fa bana buƙatar dukiya. Bana buƙatar villa. Bana buƙatar kudi. Ni kai nake buƙata.”

Ya rungumeta. “Zan dawo. Kafin ki farga, na dawo. Kuma da zarar na dawo, zamu tafi Italy tare dani, ke, da yara.”

Ta dafa kuncinsa, tana shafa. “Ka sumbace ni sosai, kaji sosai nakeso kayi mun kiss kiss mai zafi.”

Ya sumbaci goshinta, sannan fuskarta. Ya rungumeta sosai har ta saki numfashi cikin kirjinsa. “Na saba da kamshinka. Ko turarenka da ka bari yana sa ni jin ka kusa.”

Wayarsa ta fara vibration. Pascal direbansa na waje da motar Rolls Royce Phantom.

Jirgin sa na jiran sa a Orly Airport private jet mai ɗakin zama uku, sinadaran shayi, da wifi.

Miko masa jakarsa tayi . Yace mata “Ki kula da kanki.

Ta dan yi murmushi da hawaye a idonta. “Ka rubuta min sako kowace rana. Ka kira ni da dare. Ka aiko min da hoton ka idan ban ganka ba, naji na kusa da kai.”

Ya fita. Ya shiga motarsa, yana tafiya cikin sanyi, zuciyarsa cike da nauyi.

Ayshatu ta tsaya bakin window tana kallonsa. Tana jin kamar wani yanki na rayuwarta ya tafi bakinta cike da yimasa addu'a.

Jirgin private jet ɗinsa ya sauka a filin jirgin sama na Mohammed V da ke Casablanca da misalin ƙarfe takwas na safe. Yana cikin shigar alfarma wando mai launin zinariya da riga mai haɗin fari da blue, agogon Audemars Piguet, da hular Versace.

A waje, Range Rover Autobiography na jiran sa tare da direba daga kamfanin da ke masa hidima a Morocco.Ya shiga cikin motar, yana ta kallon titin Casablanca fitilun titi, gine-gine masu tarihi, da ganyayyaki da ke busawa a iska. Ya sauka a Hotel Royal Mansour ɗaya daga cikin manyan hotel ɗin duniya. Ɗakin da aka tanadar masa yana da dakunan zama biyu, babban ofis, da filin wanka mai Jacuzzi, da fitilu.

Ya zauna a kujera, yana kallon babban taga mai fuskantar lambun hotel.

Ya buɗe wayarsa.

Kafin ya gama tunani, mai masaukin sa wani babban jami’in gwamnati ya zo daukarsa zuwa taron kasuwanci da manyan ‘yan kasuwa da ministocin kasashen Afrika.

Wurin taron yana a cikin villa na kasuwanci an kawata shi da furanni da hotunan tarihi.

Sosai Yashiga ya shiga ciki kamar sarki ana masa maraba da handshake da girmamawa. Mutane suna fadin

“The Nigerian investor.”

“The man with the West African distribution network.”

“Multimillionaire with vision.”

An kawo masa kayan shayi da snacks masu tsada. A gaban sa, an jera laptops, projectors da tablets. Ya buɗe laptop ɗinsa ya gabatar da kudurin kamfani na kayan gini, na zamani da sauƙi, da saukin farashi.

Ministan kasuwanci ya ce “Mr. Babangida, this is revolutionary. This deal will change North and West Africa.” Kowa ya tafi da salon sa, amma Sosai... zuciyarsa tayi masa dadi sosai. Da ya koma hotel ɗinsa, ya cire rigarsa, ya zauna a bakin gado. Ya buɗe wayarsa, ya duba hoto daya da ya fi ƙauna hoton Ayshatu da nawal gabadaya umar ya kwace masa yarinya wato babban ɗansa dake zaune a kasar dubai, suna zaune a bakin pool ɗin villa dinsu a Paris, suna dariya.

Ya dannawa Aysha saƙo“Ina missing dinki sosai.” Ya dan lumshe ido, ya tuno da yanda ta rungume shi, yanda take shafa masa fuska da damuwa. Ya riƙe wayarsa a ƙirjinsa kamar yana rungume da'ita. “Ko da kasuwanci ya kawo biliyoyin, babu wata kyauta da ta kai kasancewa tare da masoyiya.”

*********

PARIS

Suna zauna a cikin falon villa, turaren wuta na tashi a hankali. Ayshatu na zaune kan kujera mai launin ash, tana shan tea tana duba wayarta. Anty gimbiya ce Anty dinta ta shigo da hanzari, idonta akan ayshatu.

“Aysha, kin kyauta! Wallahi, kin zama kamar sarauniya. Gaba ɗaya kin zama ba kamar mu ba. Yanzu haka, da mutum bai san ki ba, zai ɗauka ke matar wani Sheikh ce daga Dubai! Ko? Yanzu ma sai danayiwa mai gidan magiya Yace in shigo mu gaisa yana waje yana jirana.” Ayshatu ta murmusa kadan. “kai Anty har dake a zolayar?, yanzu ba gulma ba please. Ki zauna mu sha tea tare.”

Anty gimbiya ta zauna, amma zuciyarta na ƙonewa da magana. Sai ta matso kusa, ta rage murya kamar mai labari mai kyau. “Amma gaskiya zan fada miki wani abu, ko kin so ko baki so. Na dai ji ne… Daga gidan sarauta, daga manyan mutane.”

Ayshatu ta ɗan dago kai, idonta a kanta.

“Maganar nan ce akan mijinki, As’ad. Wai baya iya komai. Wannan bangaren nan shikenan ya mutu. Bai gamsar da mace, kwata-kwata. Yanzu haka kina da kyau, kina da kudi, amma kina zama da miji wanda baya da amfani? Haka zaki ci gaba da hakura, saboda kalmomi masu daɗi da kuɗi?”

Ayshatu ta tsaya shiru na ɗan lokaci. Sai ta ajiye cup ɗin tea ta sauke numfashi.

“ Anty, me kike nufi da ‘baya iya komai’? Saboda wani ciwo ne da ya same shi, kina ganin ya daina zama namiji kenan?”

Anty ta ce da sanyi, amma da harara “To menene soyayya in ba za ki samu kulawa yadda ya kamata ba? Aysha, ki buɗe ido. Maza yanzu suna nan da yawa. Wasu na jiran mace irin ki mai kyau, mai salo, mai kyau a ciki da waje. Ke fa bazaki iya zama a haka ba, sai dai a baki wando da kudi? Gwara ki waye! Ashe shiyasa matan da yake aura suke guduwa.”

Ayshatu ta juyo gaba ɗaya. Muryarta cike da ɓacin rai tace “To ki saurare ni da kyau, anty. Idan maza suna jiran mace irin ni, to ba su isa ba. Domin su ba su san abin da nake da shi ba. Su ba su san ƙaunar da ba ta dogara da jiki ba. Su ba su san yanda As’ad ke kallona da idon mutum wanda ya fi ƙarfina ba. Idan As’ad baya iya wani abu, ni na fi kowa sanin hakan. Na fi kowa zama da shi. Amma ki sani ina tare da shi ba don jiki ba. Don zuciya ne. Don mutunci ne. Don soyayya ce mai tsarki da kowa bazai fahimta ba.”

Anty ta ɗan buɗe baki da mamaki.

Ayshatu ta ci gaba da cewa “Na zaɓi mijina lokacin da yake da ƙarfi. Kuma yanzu da yake cikin rauni, sai in gudu? Kin manta ke da ni matan musulmi ne. Miji ba wai kamar yadi bane da idan ya ƙyama, a canza ba. Miji kalma ce ta amana. Kuma ni da amana nake zaune da shi kinfi kowa sanin As'ad yafi karfina Allah ne yabani shi kuma har dake acikin masu irin wannan kalamin?.”

Anty ta sunkuyar da kai.

Ayshatu ta ce “Wanda yake bani lafiya a zuciyata, wanda yake bani kwanciyar hankali a gida, ya fi wanda zai bani daɗin minti goma, ya barni da zubar da mutunci. Ki bar wannan magana,anty, Bazata canza ni ba.”

Sosai ranta yaɓaci Gabadaya bakin ciki ya cikata karshema tace anty zanfita akwai masu jirana please.

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA HAMSIN DA BIYU.

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Gidan ya yi shiru. Fitilar cikin falon ta haskaka lafazin zaman masu daraja. Fitilun bangarori sun kashe kansu kamar sun san ana shirin fita. Ayshatu ta tsaya a gaban madubi tana kallon kanta. Sanye take da abaya mai sheƙin da launin baki, gashinta a zube, Takalmanta sun jitu da kayan jikinta Jimmy Choo heels, baki masu ɗan ɗanƙo. Hannunta na ɗauke da clutch bag daga Louis Vuitton daidai da ɗan ƙamshi na Maison Francis Kurkdjian da ke tashi.Idonta yana nuna cewa akwai abubuwan da ta riga ta ɗauka a zuciya soyayya, ƙoƙari, rashin fahimta, da gaskiyar zuciya.Tana kallon kanta, sai ta faɗi a hankali “Kada ki manta da ke. Kada ki manta da soyayyarki, da kima ki. Ko duniya tana magana, ke ki tsaya daram.”

Ta ɗauki wayarta da jakar hannu, ta fita. A kofar gidan, Rolls-Royce Ghost mai sheƙi ta tsaya, direba Pascal ya fito ya buɗe mata ƙofa

Cikin motar, an kunna AC mai kamshin vanilla, fitilar cikin ta launin ruwan hoda, kuma komai sanyi da tsabta.

Ayshatu ta zauna a baya, ta jingina da kujera. Direban ya dubeta ta madubi.“Madam, café ɗin da ke Avenue Montaigne, ko?”

Ta ɗaga kai a hankali. “Eh. Wanda ke kallon fountain ɗin nan. Ina so na sha ruwa mai sanyi... cikin natsuwa.”

Motar ta soma tafiya, tana sauƙin jiki, kamar ba a tuka ta ba.

Tana tafiya, Aysha ta lumshe ido. Tana tunani. Tana jin numfashinta. Tana jin duniyar na yawo amma tana buƙatar kwanciyar hankali.

A café, ma’aikatan waje sun shirya, masu bude ƙofa, masu sa hannu akan kujera.

Wata mata mai fata fari da tabari a fuska ta buɗe ƙofa da girmamawa. “Madam Aysha. Welcome.”

Aysha ta sauka a hankali. Tafiyarta ba ta da sauri, amma tana da nauyin kima. Café ɗin yana kallon wata fountain da ke fesa ruwa da salo, tsuntsaye suna shawagi a sararin sama, iska tana busawa da sanyi.

Aysha ta zauna. Ta buɗe menu, amma idonta bai karanta ba. Ta kalli Fatima ta mika mata

Fatimq ta ɗora kofi a bakin tebur, tana kallon Ayshatu. “Ina kallonki fa Aysha. Ki dai gaya min gaskiya.”

Ayshatu ta ɗan murmusa. “Me kuma?” Ayshatu ta ɗan lumshe ido. “Ban fahimceki ba.”

Fatima ta matso da kujerarta. “Kinamun ƙarya dai. Ki ce min kina tare da miji, amma miji wanda baya iya biya miki bukata? Haba Aysha. Da wayewarki da hankalinki da kyanki??

Ayshatu ta juyo da mamaki. “Fatima, me kike nufi da ‘biyan bukata’?”

Fatima ta saki dariya mai zafi. “Oh? Wato har yanzu ba zaki yarda ba? Ki daina ɓoye damuwarki. Ke mace ce! Sha’awa fa ba laifi bane. Kuma ki sani duk kalaman soyayya ba za su rage sha’awarki ba. Duk da kudi, duk da lambu da kayan Alfarma... ai mace ba fata kawai take so ba, tana buƙatar kulawa ta jiki.”

Ayshatu ta ɗan dago kai, fuskarta ta canza.

Fatima ta ci gaba:

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull