Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 26

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 26

Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 26: Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 26. Batare da nace ko na zaci zan jure ba, sai kawai na koma cikin…

4,489 words

Batare da nace ko na zaci zan jure ba, sai kawai na koma cikin dakin. Zuciyata tana ambaliya da wani irin ciwon da ba a gani da ido. Kowane numfashi da nake fitarwa yana cike da nauyin da zuciya ba ta saba da shi ba.

Na kalli dakin ko da za a ce mafarki ne, da na farka. Amma wannan gaskiya ce ni da mijina Bashari, a wannan gida da ba zan iya kira "gida" ba. Babu ko tabarma mai tsafta da zan zauna kai, sai wani kazamin katifa, wanda ko dabbobi ba za su kwana a kai dan jin daɗi ba.

Ina tsaye, idona na juyawa a dakin. Idan da wani gurin da zan buya in kuka, da na je. Sai ashe… ban yi sallar la’asar ba. Ba magariba ba. Ba isha’i ba.

Na ji wani nauyi ya sauka a zuciyata. Na mike a hankali kamar mai ɗauke da duhu a ƙirji. Na fita daga dakin, kafafuna ba sa jin ƙasa saboda kazanta da rashin kwanciyar hankali.

Sannan na nufi bandakin gidan…

Da na shiga sai kawai numfashina ya tsaya cak. Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!

Bandakin akwai kazanta lafiyayya.

najasa ko'ina kokuma nace warin fitsari duk yana tashi.leda da tsintsiya a kofar shigowa. Bakin bandakin kuwa, wani irin gumi da wari ke fita daga ciki har yana guba zuciyata.

Sai na tsaya ina kallon kaina. “Ni Ramlah, ‘yar mutunci, wadda ta taso da tsafta da tarbiyya yau ga ni a nan, ina shirin yin ibada a wuri da kowa zai gudu.”

Na juya, zuciyata cike da rashin mafita. Amma Allah bai manta da bayinsa ba. Na hango OMO can gefen rijiyar gidan. Sai kuma na lura Allah ya taimake ni akwai ruwa a famfon filin! Kuma akwai lantarki a cikin gidan, dakin, da ma bandakin.

Da sauri na shiga wanke hannu, kafa, da fata. Na kunna famfo na fara tara ruwa a cikin roba. Duka jikina ya cika da wani kazamin zargi kamar cuta tana yawo a fatar jikina. A gaskiya ina fama da kaikayin gaba, sannan har yanzu ina jin wani babban infection a jikina wanda ba a taba masa magani ba. Amma sai dai na mika kaina ga Allah, mai yaye dukkan ciwo.

Na jure, na yi wanka. Duk da haka, jikina bai daina jin zafi ba zafi daga cikin zuciyata ne, ba daga waje ba. Na ɗauro alwala. Na ɗauki hijab dina da towel, na koma cikin ɗaki. Tabarmar da ke wurin ko kallonta ba zan iya ba, balle in shimfiɗa ita in yi sallah. Hakan yasa na shimfiɗa dankwalina na a ƙasa na tsaya a kansa cikin daren duhu da wari.

Na ɗago hannu sama, zuciyata na ta ambato addu’a cikin kukan da ba ya fito da sauti. Sai zuciya na ta kuka hawaye kawai suke sauka.

Wani ƙara kamar an kwankwasa ƙofa da sanda ya katse mini sallah. Ba sallama, ba knocking, sai kawai aka turɓude ƙofar da ƙarfi. Na yi firgigit, zuciyata ta buga da karfi.

Bashari ne. Ya shigo batal-batal, ba rigar sama, jikinsa cike da gashi da zufa mai wari. Ya riƙe wani tsohon kwano da leda a gefe, ya ajiye a gaban dankwalin da nake shimfiɗe a kai, sannan ya wuce ya tsaya a jikin bango yana goge zufa. “Ga tuwo nan, kici kamin safiya. Gobe zan siyo miki kayan girki… kada ki kwanta da yunwa, kin ji?” Muryarsa ta cika da umarni da ba'a iya musawa. Amma warinsa ne ya fi komai karfi wani cakudadden ƙamshi ne na gumi, tabar sigari, da wani wari kamar daddawa da aka ajiye tsawon shekara. Na rufe hanci da gefen dankwalina, amma ina? “Ina zaki kai hancin ki? Ko bakya jin magana ne? Maza ki bude!” Sai da ya yi tsawa kafin ya juya ya fita, yana barin ƙamshi a ƙofofin numfashina. Ban san da numfashi nake yi ba ko da zuciyata.

A hankali, na daga kwanon.

Miyar… Ya Allah!

Wata bakar miyar tsami ce, mai kamshin citta da ganyen kabeji da ya gogu. Tuwon kuwa? Sai ka rantse da itacen gawayi akai masa bakikkiri, kullu, kuma yana fidda ƙamshin daddawa da ya farfashe.

Yunwa ta yi ƙarfi. Sai da na kai kwanon bakina, amma da farko na runtse idona.

Gaba ɗaya jikina ya karaya da sauƙin wannan wulaƙanci. Ban ci ba na ɗan ɗanɗana ne, sai kuka ya kwace mini. “Ki cinye, nace miki fa! Kina so nayi fushi ne?” Ya dawo da sauri, yana kallona da wani irin azababben yawu da hayaƙi na fita daga bakinsa. Na ce, “Wallahi bana jin ƙarfi…” “Cinye! Ko dai ki ci abinci ko kuma” ya zuba min ido yana washe haƙora, “ko kuma ki ci da hannu na in baki?.” Na fara turawa cikin tsoro. Hannu na rawar jiki, kaina a ƙasa, hawaye yana zuba cikin miya, yana hade da tuwo. Amma yana ci gaba da kallona da dariya mai tsoro. Yana faɗin Amaryata Amaryata.

Yana fita daga ɗakin, na ji yana taɗi da wasu

“Kai bash,” daya daga cikinsu ya faɗa, wanda naji an ce Abdul sunansa, “ Ya yi dariya mai hadewa da tari. “Sai Oga, sai Oga!”

“Kai Bashari, wallahi yau ka ci rabonka!”

“Kai! Wannan ba amarya ba ce alfarma ce. Uwar kyauta!”

“Sannu da saukar kwallo, wallahi muna murna!” Suna fadin haka ne, kowannensu yana riƙe da sigari, wasu da kwalbar ruwa mai duhu a hannu, suna murnar ganin sabuwar "amarya" ta Bashari. Wani daga cikinsu ya turo baki yace “Oga, amarya ta sauka, amma fa dole ne ka sanya mata tsaro kar kulya su shige gidanka.”

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA SITTIN DA BIYAR

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Tun bayan tafiyar Ramlah da Bashari, mumy ta rufe kanta a dakinta tana kuka. Kukan da a zahiri ke kama da na tausayi, amma a cikin zuciyarta wani irin kwanciyar hankali da murna suke yawo. Da kyar take iya boye farin cikin da take ji, ganin cewa ta cimma burinta ta ruguza Ramlah ta murƙushe kyakyawar makomarta. Ta dade tana karkarwa da zubar da hawaye, tana motsa baki kamar mai karanta addu'a.

Wayarta ce ta yi kara. Tayi saurin dagawa, tana kauda hawayen da take kwaɓawa, tana murza idonta kamar ba kuka take yi ba. "Sai dake Zainabu "Cewar murya daga dayan bangaren wayar. " Aiki ya kammala. Su Ramlah rayuwa ta kare. Bakin ciki zai hadu ya kasheta. Wanda yaja dake bai sanki ba Zainabu!" Mumy tayi murmushi, amma ta daure muryarta cikin tsananin farin ciki. "Wannan abunda kikayi Zainabu, kin tabbatar min da ke diyar yakaka ce. Kin gama min da babin yarinyar nan. Kuma yanzu... yanzu sai ki samo dan masu kasar mai kudi ki haɗashi da bilkisu Hakan ne zai yi daidai." Sunata dariya da tsokana,cike da nishadi da murna, kamar ba su da zuciya ko tausayi. Sai ga karar Ana bude ƙofa. A firgice ta kashe wayar. Abba ne ya shigo dakin. Yana sanye da farin dogon riga, fuskarsa cike da gajiya da damuwa. Ya tsaya, yana kallonta, ya ce "Yanzu saboda Allah Zainabu, bazaki bar kuka ba? Tun safe har dare, kuka kawai kike yi? Wannan adalci ne gareki da zuciyarki? Ramlah aure fa tayi ba wani abunne yasameta ba kuma jnada tabbacin Bashari zai kula da'ita kamar ke. Mumy ta durƙusa kasa, ta fashe da wani irin kuka. Kukan da idan baka san ta ba, za a rantse da cewa kukan gaskiya ne. "Abban Ramlah... bazaka gane halin da nake ciki ba. Ramlah itace ni, ni ce Ramlah. Na dauke ta tamkar ɗiyar cikina Yadda nakeson Ramlah kaikanka kasan banson Bilkisu. Bazan iya samjn zaman lafiya ba sai naji muryarta. Don Allah kakira min ita."

Abba ya matso kusa da ita, ya dafa kafadarta. Cikin nutsuwa ya ce "Na gode Zainabu. Na gode da kulawar ki Na gode da juriya da ƙoƙarinki wajen rainonta. Allah ya saka da alkhairi. Nagama waya da su. Sun ce sun isa lafiya. Tana cikin koshin lafiya.”

********

*************

Tunda Bashari ya fice daga gidan, zuciyata bata samu natsuwa ba. Rayuwata kamar an jingina ta ne da bango, babu hanyar fice. Ban iya cin tuwon da ya kawo min ba, ko loma biyu cikakkun ban iya hadiyewa ba ga warinsa da tsanarsa, kamar zai fashe cikina.

Nayi shiru, na mike zuwa bakin pampo na gidan, na sha ruwa sosai, amma maimakon jin sanyi sai zuciyata ta sake rikicewa. Na koma cikin ɗakin da Bashari ya ajiye kayana, wanda ya sha bamban da ɗakin mutum, balantana wanda ake kira gida. Katifar da ke cikin ɗakin yagalalliya ce ta cika da datti da wari. Na kalli katifar, zuciyata na harbawa da tsoro da kuma kunya. Na runtse ido, amma kallon kazantar da ke cikin ɗakin ya ci gaba da bayyana a zuciyata. Sai na koma palon gidan inda ma akalla iska ke shigowa, duk da akwai kura. Na karkabe wata tsohuwar tabarma, na shimfiɗa zanina, Nayi filo da jakata. Na kwanta. Wallahi, bacci ya ki zuwa. Idanuwana biyu, zuciyata biyu, numfashina na taƙaici kamar an ɗaure shi. Duk da gajiyata, sai kawai na lumshe ido. Tsoron dawo war Bashari, tsoron rayuwar da ke gabana, tsoron kaina... sun mamaye zuciyata.

Na ci gaba da kallon kofar dakin, zuciyata na tsalle-tsalle kamar wacce ke jiran bugun ƙararrawar mutuwa. Ko'ina a waje shiru yake. Wani ƙarar bishiyoyi na shigowa cikin kunne na Dare yayi nisa. Sai wajejen ƙarfe 12 ko 1 ban tabbatar da lokaci ba tunda babu agogo na ji karar ƙofa kamar an turo ta da ƙarfi. Na farka da tsalle kamar an haɗani da wuta. Na furta da firgici “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Kafin na kai ga miƙewa sosai, sai ga Bashari a ƙofar. Yana nan tsaye a bege kamar an cillosa da karfi Idonsa sun canza daga fari zuwa jajir, sai gumi dake fita a fuskarsa. Hannunsa na rik’e da wata bakar leda. Yana shigowa, yana gyatsa kamar rakumi mai ciwon makogwaro. Wani irin wari ne ya cjka dakin wari na taba, wari na datti, wari na Hammata. Na janye jikina can gefe cikin tsoro, amma bai ce komai ba. Sai ya zauna kamar dutse, ya dakko kwalbar roba daga cikin ledar. Yayi gyatsa, sannan ya kurɓi abin cikin kwalbar. Na lura sai kallona yakeyi. Na juya kaina, zuciyata na bugawa da ƙarfi.

Ya fara da zugar sigari, yana fitar da hayaƙi a cikin dakin da babu iska. Tun ina kirga kwalin da yake jawowa har sai da na kasa tantancewa. Wani kuka na saki kuka mai raɗaɗi, kuka na mace da rayuwarta ke rugujewa. “Me na yi miki kike kuka? Kafin na ankara, sai kawai naji ƙarfin mari ya sauka a gefen fuskata, yana fasa kunnuwana da duka. Kusan fitsari ne ya fito daga jikina saboda tsoro. “Uban me nayi miki ? Ni nace ki aureni? Ni nace abani ke? Dole dab.. Mai kama da aljanu! Watanni kadan zaki saba, sai kice kema na baki kisha.”

Yayi raurayi yana fizga hayaki.Wani tsoro ne ya lullube ni gaba ɗaya. Na runtse idona, amma hoton mahaifina yana yawo a zuciyata shine wanda ya bani wannan rayuwar? shi ne ya ce min “Kitafi ki zauna da mijinki, ki masa biyayya, aure ya fi komai.” Ina cikin kuka na rufe bakina ina jijjiga jikina, yana yi min ciwo. Bashari yana can yana gyangyadi, kafin wani lokaci sai kawai na ji yana yin bacci da da munshari, yana juyi kamar dutsen da aka daura a gadon kasa.

Na juya masa baya. Na rufe ido. Sai da hawaye suka shanye hanuna Na fara addu'a

“Ya Allah... idan wannan shine kaddarata, to Allah ka bani haƙuri, amma idan akwai wani mafita, ka kawo min shi kafin zuciyata ta buga.”

Da asuba, ban ji kiran sallah ba. Cikin sanyin safiya da shiru, sai kawai na farka ganin gari ya fara wayewa. Rana na hango tana ratsowa daga barin gabas, iska tana kadawa a hankali.

Na tashi da gaggawa. Cikin saƙar zuciya na fita waje, na nufi rijiyar da ke gefen gidan. Na ɗebo ruwa, na yi alwala. Na dawo ciki na tada sallah har na kammala, sannan na zauna a kan zannuwana ina karanta azkar kamar yadda nasaba tun ina gida. Wani irin natsuwa na ratsa zuciyata amma cikin wannan nutsuwar akwai wata damuwa da ke doron zuciyata, tana bushe da sanyi mai ɗaci.

Sai da safiya ta kara bayyana, rana na ƙoƙarin fito da zafi kadan, sannan na ji motsinsa. Yana tashi da gafgafa kamar wani nauyi na duniya ya danne shi.

Sai na juyo da kaina, daidai lokacin da na hango shi yana tofa wata babbar majina a gefen tagar dakin, wanda wari da kazantarta ya sa ni janye kaina da sauri, na dafe ƙirjina tamkar zai fashe.

Yana karkadawa, ya daure fuska da wani irin rashin kunya, sannan ya kalli inda nake, yana cewa "Amarya... baki tasheni nayi sallah ba? Har lokaci ya huce ke kina zaune kinata ibadarki ga mijinki baiyi Sallah ba." Na zuba masa ido. A raina nace, “sai kace dab shaye-shaye yana sallah? Wane irin ibada yake?” Na kame harshena, amma idanuwana suka ba ni mamaki. Wannan mutum da ke fita hayyacinsa dare da rana ne zai rika zargi da ibada?

Yana dubana kamar na zubar masa da albarka. Sai yace da kakkausar murya "Magana fa nake miki, kinmin banza!" Na tsaya cak, jikina yana rawa. Bakina ya ɗauki zafi, Ga warin baƙinsa da ya busoni da kyar na furta cikin ladabi "Ina kwana..."

Sai ya nufo ni da girmansa da girman zuciyar sa mai cike da maye. Da na ga yana matsowa, na ja da baya da sauri, zuciyata na dokawa kamar tana faduwa.

Ya sake dakatawa yana kallona da idanunsa jajaye da rashin natsuwa, sai yace "Me ya hana ki tasheni? Ko kin mayar dani ba musulmi bane, ko?" Cikin rawar murya nace "Wallahi bansan kana sallah ba..." Wani mugun murmushi yayi, ya ɗaga kafadarsa da kamar rashin gaskiya a idanunsa. Sai kawai ya juyo, ya fita. Na leƙa. Naga ya tafi ya ɗebo ruwa daga rijiyar gida. Ya yi alwala da gaggawa, Ya dawo ciki, ya tada sallah ba tare da natsuwa. Yana gamawa, ya fice daga gidan.

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA SITTIN DA SHIDA

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Tun bayan fitarsa na tsaya kallon gidan. Idona ya gama karantawa ainihin yadda komai ya lalace datti ya cika ko’ina, kamar gidan da ba a shiga. Jiya mun shigo cikin dare ne, shi yasa ban lura da hakan ba. Da safe, hijjab dina kawai na yafa, na saka niyyar gyara gidan. Na soma fito da tarkacen cikin dakin, har da na palon da ke tsakiyar gida. Bayan taga kuwa, na ciro bola mai yawan gaske ni kaɗai, cikin rashin ƙarfi da yunwa, amma zuciyata cike da niyyar ganin gidan ya zama wurin da mutum zai iya kwana cikin lafiya. Na cika buhuna, na kai tsakar gida kamar wata baiwar Allah da ake azabtarwa. Cikin kankanin lokaci, gurin ya canza kamanni ya zamto wani abu na daban.

Cikin gajiyata, ban ma lura da shigowarsa ba sai da ya ƙaraso kusa dani. Kwano na abinci ke hannunsa, sai murmushin da ban saba gani a fuskarsa ba.

Yace da murya kamar wanda yake jin tausayina

"Ramlatu, zo kici abinci. Kinsan ni bana wasa da yunwa."

Sai kuma ya sake cewa

"Au aiki kike yi? Lallai yarinyar nan... To yanzu kici ki huta, daga nan kuma ki shiga gidan Malam Zakari. Za'a zo a gyara gidan nan yau, zuwa dare insha Allah sun kammala."

Na ce masa

"To,"

Na zauna da sanyin jiki, na fara shan kokon da ya kawo. Duk da cewa ba shi da wani zaƙi, yunwa ce ta sa ya zame mini kamar zuma. Sai kuma yace

"Me kike buƙata daga kayan kitchen? Zan je kasuwa yanzu."

Na kalle shi da takaici, zuciyata cike da bacin rai da haushin wannan mugun aure. Sai na ce da shi

"Komai ka siya Yaya Bashari."

Sai ya fashe da dariya, yace

"Amaryata, Amaryata! Yanzu masu aikin gidan zasu zo. Zan siya miki gado da abun ajiye kaya. Wancan ɗakin da ke tsakiyar gidan na cika shi da itace za'a kwashe shi, a gyara ya zama kitchen. Amma fa sai kin yi haƙuri, wasu abubuwan ba za su samu ba a nan kauyen, kinsan kauyena ne sosai."

Na kalli fuskarsa, amma bance komai ba. Na ji zuciyata tana zafi kamar ana tsiyayar da gishiri a raunuka.

Can sai ga wasu samari suka shigo, wai su ne masu aikin. Ya ce ya samo su daga can bayan gari. Na ɗauki hijjab dina na fita tare da shi. Mun je wani gida da ke kusa, amma gidan kasa ne, ƙasa sosai. Sun gaisa da mai gidan, ni kuma na gaidashi da ladabi na shige ciki. Ina jinsa yana cewa

"Ramlatu, sai anjima zan kawo miki abinci."

Na ce "To Yaya.” Na shige cikin gidan, Na shiga gidan da sallama, cikin tsananin kunya da nutsuwa. Hijjabine a jikina, takalmina na tafe da ƙasa. Da na leƙa cikin gidan sai ga matar Malam Zakari tana tsugune, tana wanke-wanke. Hannunta na cikin ruwa, gashin kanta daure da ɗan kyalle, kayan jikinta sun jike da ruwan sabulu.

Da ta gan ni, sai ta tsaya cak. Ta buɗe baki tana kallona kamar ta hango fatalwa. Kallona ƴan kauye.

Sai ta furta cikin murya mai nuna mamaki “Heee... naganki gabana! Ke kuma daga ina ne?” ina shirin bude baki domin amsawa, sai ga Malam Zakari ya shigo Yace “Matar Bashari ce. Uwani, ki bata guri mana.”

Matar tasa, Uwani, ta miƙe da sauri kamar wadda aka cusa mata wuta. Ta share hannuwanta, tana tsaye da baki buɗe da idanu kamar za su fado. Ta ce “Matar Bashari? Wannan fa irin wadda muke kallo a TV ce masu kama da Aljanu! Wannan fa yar birni ce! wannan ce za ka ce min amaryar bashari? Maraba! Lale! Zo ki zauna,” ta ƙara da fara’a tana shimfiɗa min tsohuwar tabarma da tuni ta fita hayyacinta.

Da sallama na shiga cikin tsakar gida, na zauna a gefen tabarma. Uwani, matar Malam Zakari, ta taso da sauri, tana share hannunta da zane, fuskar ta cike da fara’a da walwala.

“Mun wuni lafiya,” na ce cikin ladabi.

“Lafiya lau! Maraba da zuwa, yarinya. Sannunki fa!” ta amsa tana murmushi, kamar dai tasanni. Kafin mu gama gaisuwa, sai Malam Zakari ya leƙo daga ɗaki “To Uwani, ki bata ruwa mana. Baki ga bakuwa bace ba?”

Uwani tace “Ai Malam natsaya ina kallon wannan kyakyawar yarinyar wallahi.” Ta miƙe cikin natsuwa, ta nufi rijiyar gidan da guga a hannu. Bayan mintuna kaɗan ta dawo, guga a cike, ta zuba ruwa a tukunya, sannan ta juya da murmushi mai cike da tambaya. "To dan Allah, wa ya ba Bashari wannan yarinya mai kyau? Ashe haka kyakkyawa suke nakasa daina kallonta malam? Kamar ‘yar fim fa! Ke kuma, ya kika yi kika amince kika auri Bashari?” Na kalle ta kawai sannan na sunkuyar da kaina. na daure, na cigaba da murmushin da ba na gaskiya ba. Uwani ta girgiza kai, ta na cigaba da faɗin "Kin san yana fashi da makami kuwa?Ɗan Daba ne! Iyayenki fa? Sun yarda ne suka ba shi ke? Wallahi mu nan ƙauye mun ƙibasa yaranmu."

Kalaman nata sun taɓa zuciyata, amma na ƙi cewa komai. Malam Zakari ya daure fuska, ya yi ƙasa da murya kamar yana ƙoƙarin dakatar da Uwani "Haba Uwani, ki daina tsokana mana. Watakila soyayya ce ta haɗa su."

Uwani ta juya tana huci "Soyayya kuma? Malam kai da kake namiji, ai ya kamata ka gane hakan ba soyayya bace. Kalli yarinyar nan da kyau... kamar kataɓata jini yafito ta jikinta!"

Ta juyo gare ni, "Ke dai wallahi baki san abinda kika shiga ba.Bashari fa? Ko mu da muka taso dashi a kauye, ba mu isa mu ba shi ‘ya’ya ba." Na sunkuyar da kai, na kasa kallonta. Ta cigaba da surutunta kamar ba ta gajiya "Kin san mutane nawa Bashari ya kashe? matar ubansa ma ya tsaneta, balle ke. Gidan mahaifinsa kuwa?kamar anyi masa tsafi baya ko kallo wajen!"

Cikin nauyin zuciya nace "Dan Allah, zanyi sallah." Ta tashi ta ɗauko wata buta ta zuba ruwa. Tacemun "To, ga ruwan nan.." Na karɓa cikin ladabi. Na fita nayi alwala, na dawo, na tsaya sallah amma zuciyata bata kwanta ba. Kalaman Uwani suna yawo a cikin kwakwalwata.

Bayan sallar, sai kawai na ji ta ƙara magana daga cikin ɗaki "Ai mahaifinki ma... ban san irin tunaninsa ba.

Ina zaune a cikin ɗakin Uwani ina shirin fitowa kenan, sai kawai na jiyo ƙarar kwalba a waje, sannan Naji ana kiran “ Ke amarya, fito ki karɓi abincin ki. Ko so kike ki mutu da yunwa kafin mu fara zaman aure?”

Na fito da sauri. Ina zuwa bakin ƙofar gida, sai na hango Bashari tsaye, sanye da farar riga da hula a hannu, yana murmushi. Hannunsa ɗaya na rik’e da leda mai dauke da abinci, ɗaya kuma da ragowar sugari Ya miƙo min kayan cikin ɗabancinsa “Ga abincinki nan. Na ce bari na kawo miki da kaina saura kuma kice bazakici ba.” Na karɓa cikin ladabi, na ce da shi “Nagode sosai, Yaya Bashari.” yayi murmushi yana zukar Sigari yana busawa gefe. Sannan ya yar ya taka ragowar sigarin yana faɗin “ zanje birni yanzu zan iya yin dare zan kuma iya kwana ki zauna nan gidan Malam zakari aliyu zaizo yakawo miki abinci dadare ki kula da uwani dan muguwar munafukace kinji ko?. Nadaga masa kai nayi hanyar komawa ciki sai naji yace “ke bakzakiyimun addu'a ba? Eh? Zan sassaɓamiki fa eyane eyane..” cikin rawar murya Nace Allah yabaka hakuri adawo lafiya. Yaja kafarsa suɓuti subuti yatafi.

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA SITTIN DA BAKWAI

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Na kalli kwanon abincin da Bashari ya kawon min, zuciyata cike da takaici da baƙin ciki. Wata shinkafa ce cikin kwanon, miyar baƙin-kirin da kamshin man gyada ya ɗoke hancina kamar ba da tumatur akayita ba, sai yanka nama guda daya, da kwalban lemo da pure water a acikin ledar. Na sauke ajiyar zuciya, na ce “ Yanzu ta ina zan iya cin wannan kazamin abincin?.” Na ɗauki kayan da kyau, na yi sallama na koma cikin gidan Malam zakari Na zauna a bakin tsohuwar tabarma, na ajiye abincin a gefe, zuciyata babu dadi. Ina cikin tunani ne, can sai na jiyo muryar Uwani daga gefe tana faɗin “Ehee lallai kam! Soyayya kukeyi kenan! Shi yasa ya kawo miki abinci da kansa ko? duk iskancin bashari yakawo miki abinci Abunnan akwai sihiri gaskiya.Yama kikace sunanki? Yanzu Ke duk mazan birni maza nagari masu kyau sun ƙare ne? kin rasa wanda za ki so, sai Bashari kazami irin sa? Ɗan daba cikakken mara tarbiya mara tsoron Allah Wallahi sai kin gaya min ko asiri yayi miki.” Na dago kaina cikin mamaki, na kalleta. Amma sai nayi dariya cikin raini. Uwani dai ita ke kiran wani kazami duk kazantar dake tattare da'ita? IkonAllah. Na ɗan juyar da kaina nace “Wannan rayuwar Mutumin da bashi da kyau a jikinsa, shi ne zai riƙa yawan zagi da ƙazafi. Wai me ya dameta da ni? Ko don ta ga Bashari ya bani abinci ne?” Na cigaba da kallonta ba tare da nayi magana ba. Kamar wanda aka riga aka gaya mata duk abinda ke zuciyata, sai ta ce “Kallon ki nake yi! Sai kin bani amsa fa! Waye ya haɗa ki da Bashari? Ko dai kema 'yar daba ce kamar shi?.” Wani abu ne ya tokare makogwarona. Zuciyata kamar za ta fashe.na ci gaba da kame kaina. Babu kalmar da ta fito daga bakina amma idanuna sun ciko da hawaye. Duk da hawaye bai gangaro ba.

Na ajiye kwanon abincin a gefe, zuciyata cike da ƙunci. Idona na kallon Uwani, tana gyafe sai faman susar ƙai takeyi sai kuma kallona da takeyi kamar wata mayya, kawai naga taja gyalenta ta fice daga gidan.

Ba a dade ba, sai ga mutane sun fara shigowa, fuska cike da sha’awa da zazzafar tambaya. Gaba ɗaya mutanen kauyen sai kallona suke kamar an kawo musu sabon fim daga birni. Wasu daga ciƙinsu suka fara faɗin "Wannan ce matar Bashari?" "Ita ce? Ke kuwa me kika gani?"

Wata mace ta ce, “wannan abun da mamaki kyakyawar yarinyar nan he kuce matar bashari ce?.” Ganin hayaniyar da suke yi da yadda suke kallona kamar wata dabba a kasuwa,Na juya musu baya, na koma kan tabarmata, na kwanta da kyar, na rufe fuska da zanina. Hayaniyarsu tadameni Amma daga ƙarshe bacci ya dauke ni.

Yunwa ce ta tashe ni, Na duba taga, gari har ya fara duhu. Na ɗauki buta na shiga bandaki. Allah ne kawai ya san irin wari da kazantar da ke tashi a cikin bandakin Na riƙe hancina da ɗayan hannu, ɗayan kuma na ɗaga doguwar rigata, na cire pant dina, nayi fitsari a tsaye. Ban iya tsugunnawa ba, domin kurajen gabana suna cutar da ni sosai idan na tsugunna. Idan na tsugunna nasan na haifarwa daƙaina wani sabon ciwon ne dan tabbas sai na dauki wani sabon infection.

Na fito na wanke hannuna, na ɗora alwala, na tada sallah. na zauna ina karanta addu'a da tasbihi. Amma zuciyata na tafasa da wani irin bakin ciki mara misaltuwa.

Can sai na ji sallama daga bakin ƙofa. Muryar Uwani ce tana cewa "Gatanan, shigo mana!" Sai ga wani matashi ya shigo, fuskarsa cike da fara’a amma kana ganinsa kasan cikakken ɗan shaye shaye ne saboda mamki kawai sai naga Ya durƙusa har kasa “Allah ya ƙara miki lafiya matar oga! Muna murna da zuwanki. Wannan abincin ki ne. Inji oga, sai gobe zai dawo." Na ce, “Nagode.”

Yashageɗe kafaɗa yaja kafafuwansa yafita.

Uwani ta dawo kusa da ni, ta zauna tana ɗan murmushi. “ Ai Wannan dakike ganinsa shima cikakken ɗan dabane sunansa Aliyu Awilo To ke yanzu wannan rayuwar ce kike so? Ke da aka haife ki a birni.Rayuwar kauye babu daɗi fa. Bance komai ba. Nakauda kaina gefe, zuciyata na harbawa da takaici. Na ɗaga kwanon abincin da Bashari ya kawo dazu, na ce "Gashi kici ko?,." Uwani ta karɓa da murna. Tana ta cin abincin. Can kuma tace “Ai a nan ba kullum ake da abinci ba. Idan Malam ya fita ya samo kunu, to shine zamu sha. Wani lokaci fa yakan dawo da gyaɗa kawai mu dafa. Ko kuma miyar kuka da gishiri kawai.”

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull