Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 25

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 25

Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 25: Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 25. “Ni ce za a tura auren nan ba da so ba.

4,494 words

“Ni ce za a tura auren nan ba da so ba.

Mumy na fita daga dakin falo, kai tsaye ta nufi nata dakin kamar wadda ta samu lamban cin nasara. Fuskarta cike da murna, keta dariya kamar an kashe mata abokin gaba. “Na gama da ke Ramlah. Wallahi sai kin fuskanci yadda ake wulaƙanci da gaskiya.”

Tana shiga daki, ta zube a gadonta, ta ɗauki wayarta cikin sauri. Ta kira Y'akaka aunty dinta da suke hadin baki wajen gulma da tsare sirrin su. “Y'akaka! Aiki ya kammala wallahi. AURE Ramlah! Hahaha! Aure da Bashari fa!”

“Ni yanzu zan huta da kwallon mangwaro wato yarinyar nan mai girman kai. Zan huta da annobar gida wato Ramlah!”

Murmushi mai cike da mugunta ne ya bayyana a fuskarta. Idonta ya dau sheki kamar na maciji mai jin nasara. “Kuma danake gaya miki... Abbansu ya kira Bashari ya kuma amsa da gamsuwa. Wallahi a gobe za'a daura auren.Kayan daki fa? Ina! Ni ba zan tsaya yi mata kaya ba zandai cillata da kayan jikinta da na tufafinta. Ai daban ne daita, sansanin dabar tasu ce zata.

Y'akaka tana dariya a waya, tana faɗin“Lallai yau kin cinye ta Mumy. Wannan ai ba dafa ba ne wannan dafa da gishiri ne har da yaji!”

Mumy ta ce “Wallahi ko auren ta yi ko ba ta yi ba ni dai na yanke hulda da ɗiyar kishiya Zan tabbatar ta yi nadama har gaban kabari.”

___

Na shiga dakina da ƙafa mai rauni, na jingina da ƙofa na sulale ƙasa kamar jarirai da aka cire wa mafita. Na fashe da kuka. Kukan da bai da salo. Kukan da ba a iya tsayarwa. Kuka mai ciwo fiye da duka. Na riƙe kirjina. Na ce da kaina “Me nayi wa duniya? Me yasa iyayena suka fi ƙaunar cutata akan su kare ni?” Na miƙa hannu na ɗauki wayata, da fatan zan samu wanda zai ji ni, wanda zai ji zafin da nake ciki wanda zai tsayar da wannan auren da nake tsoro kamar mutuwa. Na shiga layin wayar Yaya Usman, na gwada kiransa sau ɗaya bai shiga ba. Sau biyu… har uku… still not reachable,Wayar tayi shiru kamar babu duniya a kanta. Sai na ji kamar an ƙara dora dutse a zuciyata. “Ya Allah, wa zan kira yanzu? Wa zai saurare ni?” Sai na ɗan goge hawayena da yatsa, na duba lambobin wayata.

Na hango Khalil. Khalil ya mutu wayoo Allah na Amma a wannan lokacin… sai na ce “Inama da shi za a haɗani… inama da shi ne Na sanya kuka. Kuka mai sanyi, mai fasa zuciya, mai rikita kai. Kuka da ko bango da ɗaki sun kasa jure wa. “Inama… inama… inama shi ne. Inama zan iya guduwa tare da shi… inama kana raye khalil.” Kuka nake yi kamar mara lafiya mai buƙatar taimako.

Ina jin numfashina na rikicewa. Zuciyata na sarawa. Kaina na juyawa. Sai na tashi da ƙyar, na ɗauki magunguna paracetamol da aspirin, ko zai saukar da wannan ciwon zuciya da jiki. Na sha su da ruwa. Ban ci komai ba tun safe amma bana iya tunanin ci.

Kafin dare yayi sosai, na fara jin zazzabi ya mamaye jikina. Ya fara rawa, sai zafi da dumi ke ɗaukar kaina gaba ɗaya.

Fuskata ta fara yin ja, idanuna sun kumbura da kuka. “Ya Allah… ka duba halin da na shiga. Ka fitar da ni daga nan cikin rahamarka.” Babu wanda ya shigo dakina. Babu wanda ya tambaye ni. Babu wanda ya lura da irin halin da zuciyata ke ciki.

"Inama Allah... Inama ace mahaifiyata bata mutuba..." Wannan kalmar ce kawai nake iya furtawa a cikin zuciyata cikin dare, cikin zafi, cikin rashin mafita. Wallahi da mahaifiyata bata mutuba ba, da bana kiranta “Mumy”.

Wannan Mumy da nake kira uwa bata da tausayi. Bata da zuciyar da zata ji kuka na.

Da ace uwata mai rahma ce har yanzu tana raye… Da ba zan kasance cikin wannan hali ba na wahala, na matsin lamba, da aure da bana so. Da zan zauna a jikinta in fadi damuwata, ta shafa kaina, ta ce “Zan kare ki.”

Da ba zan sha zazzabi a daki ni kaɗai ba, sai turaren kamshi da dumin lullubi daga hannunta, Kullum nake addu’a “Ya Allah, ko mafarki ne, ka bar ni in ganta.” “Ka bar ni in rungumeta sau daya.” “Ka bar ni in ce mata Ina sonki, na rasa ki, ki dawo mana.” Na fashe Da kuka..

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA SITTIN DA BIYU.

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Da ƙyar na lulluɓa jikina da bargo, na matse idona da karfi kamar hakan zai tilasta zuciyata ta kwanta. Amma bacci bai zo ba. Sai firgici, rawar sanyi, da tunani mai nauyi. Na kasa gane me yasa duniya ta juya mani haka me yasa rayuwa ta koma kamar mafarki mai daci? Na sauke ajiyar zuciya. Har da magani na sha domin natsuwa, amma har cikin baccin ma, zuciyata tana kuka.

Washegari da sassafe, na farka da karar murya da tafiya da takalma a cikin gidan. Na leƙa ƙofar dakina sailing vna hango palon gidan ya cika da dangi, musamman ‘yan uwan Abba maza da matasa da dattawa. Muryar Mumy ce na fara ji tana fadin “Anty Luba, zo mu hada kayan Ramlah lokaci ba ya tsaya wa.” Suna shigowa dakina da ledoji da jaka. Anty Luba ta riƙe wata buhu ‘bakko’ ba ma akwati ba. Sun fara zubawa cikin sauri kamar wasu ‘yan haya. Na zauna a gefe, idona na bin su, amma zuciyata na zubar da hawaye kamar kogi. Ban ce musu komai ba. Har suka gama. Daga bisani sai na mike na shiga wanka amma ba dan na shirya aure ba, sai dan ina jin zafi a jiki da zafi a zuciya.

Bayan na fito daga wanka, na tafi gaishe da kannen Abba da ke zaune a falo. Sai na ci karo da Uncle Hamza, yana kallona da kallo mai cike da damuwa. “Ban ji daɗin zabin da kika yi ba, Ramlah. A gidana ma akwai Abubakar da Mubarak, baki zabesu ba, sai Bashari?” Na ji duk wata magana ta makale a makogwarona. Ban iya cewa komai ba

saboda na tuna da kalmar Abba “Idan kin ƙara cewa ba za ki auri Bashari ba, sai na tsine miki. Ban yafe ba!” Sai na sauke numfashi, na ce da rauni “Indai hakan ne farin cikin Abbana, to nima farin cikina ne.” Uncle Hamza ya kurbi kalmomin nan da wata irin fushi da tausayi. Ya dubi Abba da ƙarfi, ya ce “Haba yaya malam! Wallahi kun tilasta wa yarinya. Wannan ba aure ba ne azaba ce!” Abba ya kalle shi, bai ce komai ba. Na tashi da ƙyar, na juya na Na koma dakina amma da na shiga, ban gane shi ba.Naturar da Mumy da Anty Luba sun kwashe komai.

Kayana a cikin buhun “bakko”, ba ma akwati. Kamar matar da ake korar aure. “Wannan Anty Luba ce? Ita ce wadda kullum take nunamin soyayya? Ita ce da murmushi take ce min ‘ki tsaya da karatu Ramlah’?

Ita ce yanzu ko kallona batayi ba?”

Tana gefen Mumy, tana murna kamar suna shirin mika min tikitin hijira zuwa rayuwar azaba,Na zauna a gefe.

Anty Luba ta dawo dakina, ta zauna a gefena kamar wadda zata bani shawara. Amma sai tace “Ashe rabonki da Bashari ne ba Khalil ba? Ashe Khalil ya ƙare kenan, yanzu rabonki ya kashe shi kenan?” Na dan kalli fuskarta, ba da ƙiyayya ba, ba da mamaki ba amma da daddawan zuciya da ba ta da mafita.

Na murmusa kadan, na ce “Allah ya yi. Shine mijina. Anty, ki yi mana addu’a.”Ta dan buɗe baki, ta ce “Allah ya bada zaman lafiya.”

Na san ba addu’a bace a zuciyarta duka maganganu ne na wulaƙanci da cin mutunci.

Ina zaune a cikin ɗakina shiru kamar kabari. Sun tafi da komai. Sun tafi da kayana, da ƙuruciyata, da burina. Sai ragowar ƙamshin turarena da yake shawagi cikin iska, kamar tunawa da wata ni’imar da ta shuɗe.

Nike nan… Ina kallon bango. Bango da ya zama shaidu a cikin kuka da firgici.

Kamar mafarki, sai ga Yaya Bilkisu ta shigo. Fuskar ta cike da mamaki, da bacin rai, da wata guntuwar tausayina da ban zata ba daga gareta.Ta zauna a kusa da ni, tana kallona da damuwa. Sai tace "Ke Ramlah, baki da hankali ne? Zaki yarda su yi miki auren dole?"

Ta matse hancinta, ta girgiza kai da takaici. Sai ta ci gaba "Wallahi ko videos ma Mumy ta sanya ta saka aka tura miko sannan ta kunna kina shiga bandaki dataji karar motar Abba, ina kallonta! Wannan Bashari kike yarda da shi? Wannan ɗan daba? Wannan mashayi? Wannan mai makami? Kinsan yadda kike da kyawu kamar 'suffer matan manya, kina da daraja, kina da ilimi amma yanzu kike barin su jefa ki cikin wuta da rai da ido? Ramlah, na rantse miki ki gudu! Ki bar gidan nan! Ki je family house, ko wajen su kakarki. Kada ki yarda da wannan mugun auren."

Na kalleta. Kuka ya turnuke ni. Hawaye ba su tsaya ba. Sai na ce da muryar da bata da ƙarfi "Ya Billy... nagode da shawararki. Wallahi ina jin kalamanki a zuciyata. Amma ba zan iya guduwa ba.Na amince. Na amince da auren. Na amince da hukuncin da Abba ya yanke saboda banason tsinuwar mahaifina ta hau kaina. Ko da kuwa wannan aure ne da zai yanka naman jikina da ruwan wuta.Koda kuwa raina ba zai samu salama ba, zan daure. Koda na rasa farin ciki, zan yi aure domin biyayya." Na fadi haka ina fashewa da kuka.Yaya Bilkisu ta kura min ido. Bata ce uffan ba. Sai daga ƙarshe ta tashi tana girgiza kai da masifa. Ta ce "To ai sai ki ɗauka da kanki. Wallahi ba za ki ce ban gaya miki ba Ki gama da kanki. Amma wallahi kin zalunci kanki, kin sallami burinki." Ta fita, ta barni cikin dakin da ya cika da shiru.

---

Wajen ƙarfe goma sha biyu na rana, rana na haskaka sararin sama da kyan fitilarta, duk da cewa a cikin zuciyata tamkar ƙirin dare ne duhu, ba haske. Mutane sun yawaita a gidanmu, sai hayaniyar gaisuwa da dariya ke tashi.

Kamar almara, Bashari ya iso. Ba shi kaɗai ba, tare da kawunsa guda biyu mutane masu fuskokin ƙasa da dariya mai ɗaci.

Suka shigo falon cikin takun izza, jikinsu sanye da hadadden shadda 'Getzner' mai launin zinariya da rawaya. Tufafin nasu sun sha guga, suttura masu sheƙi da ƙamshi. Sun shiga cikin falon da nutsuwa, suka tsugunna cikin mutunci. “Assalamu alaikum.” Sai gaisuwa ta biyo baya canji-cinji na "Lale-lale, maraba da zuwa", kamar waɗanda ke murnar abun da ke faruwa.

An karanta fatiha.

An daura aure.

Auren da ban ji soyayya ba a cikinsa, auren da naji kamar ana rufe ni a cikin akwati ba tare da iska ba.

Bashari ya zauna da ƙarfin zuciya, yana cewa “Na karɓi auren Ramlah diyarki a kan sadaki naira dubu hamsin, na amince da sharuɗɗan aure.” Sauran mutane suka amsa da “Allah ya amsa. Allah ya bada zaman lafiya.”

Amma cikin zuciyata:

Shin ni fa? Me nake ji? Wani abu ne mai nauyi na danna kirjina, kamar zuciyata ta tsaya amma ba ta mutu ba.

Abba ya ɗago da murmushi mai ɗauke da girman kai. Ya kalli Bashari, ya ce da shi a fili “Kai fa kana da sana’a ko? Kana da abin yi?”

Bashari ya gyara zama, ya kada kai “Eh Abba, ni ina sana’ar tukin mota da siyar da kayan itace. Kuma ina da gida a can ƙauyenmu.” Sai Abba ya ja dogon numfashi, ya sa hannu cikin aljihunsa, ya fitar da wani envelope mai kauri. Ya mika wa Bashari yana fadin “To, ga wannan. Naira Miliyan Biyar ne. Wannan shine kudin kayan dakinta. Ka je kasiya, ka bata duk abinda mace ke buƙata. Na barmaka Ramlah halak malak.” Daga nan ya ɗago hannunsa sama, ya fadi “Allah ya baku zaman lafiya. Allah ya sa wannan aure ya zama albarka gareku.” Bashari ya durƙusa da girmamawa. Fuskarsa cike da godiya, idonsa da hawaye “Na gode sosai Abba. Wallahi wannan alfarma da nayi mafarki ban taɓa tsammanin zan gani da ido ba. Zan kula da Ramlah fiye da komai. Allah ya saka da alkhairi.” Ya ɗago ya kalli Mumy, yana kallonta kamar uwa “Mumy, na gode sosai. Allah ya saka da lada. Kin bani diyar ki, ni kuwa zan riketa amana.” Mumy tayi murmushi “Kai ɗan kowa ne. Kai yanzu namu ne gaba ɗaya.”

Na ji kamar ana rufe ni a ƙofar mafita. Ina kallon fuskoki na murmushi amma ba wanda ya leƙa cikin zuciyata.

Bayan daura aure, mutane na ci gaba da gaisuwa da godiya. Na zauna a cikin daki amma na ji kamar zan huta ne da kwana a tsakar rana, ba da miji ba. Ban san da wani farin ciki ba, sai da wasu hawaye ne ke cin karo da ni a ƙasan zuciyata. Auren da bai da tushe a so, ya fara a tsaye da addua da miliyoyi amma ba da albarkar zuciyata ba.

Ina zaune a ƙasa, durƙushe da jiki mai rauni, cikin ɗaki da ya zame min kabari tun da aka fara maganar aure. Sai ga Abba ya shigo. Muryarsa mai sanyi ta shiga kunnuwana cikin sallama “Assalamu alaikum, Ramlahtu.” Na ɗago kai a hankali, idanuna cike da hawaye da azaba. Sai ya matso kusa dani, ya zauna a gefen katifa sannan ya miƙo min wasu takardun kudi. “Ga sadakinki,” ya ce.

Na kalle shi. Hannu na rawa. Ban kai ga karɓa ba, sai ya ɗan daka min tsawa wani irin raɗaɗi ne ya tsinka zuciyata. Da rawar jiki, na karɓi kudin kamar na karɓi takardun da suka goge ni daga littafin rayuwa ta. “Alhamdulillah,” Abba ya ce, yana mai sauke ajiyar zuciya. “Yau na sauke nauyin dake kaina. Kitashi ki je, ki bi mijinki. Ina roƙon Allah ya baku zaman lafiya.” Sai ya dan dakata, yana kallona da idon da ke cike da ƙarfi da tsawa, ya ƙara “Kisani idan har kika bijire wa aure, to tabbas ban yafemiki ba. Ki yi masa biyayya, kinji ko?”Cikin kuka mai nauyi na amsa “Na ji, Abba. Kuma zan yi yadda ka ce.” A gefe, Kawu Hamza ya ɗan girgiza kai da takaici, ya ce “Haba Yaya Malam! Wannan aure fa babu tsari, babu kamu, babu yini, babu lefe. Wannan fa faɗuwar kima ce!” Kafin ya kai ƙarshe, Abba ya ce da murya mai zafi “Hamza! Duk abinda ka lissafa, akwai wanda Allah ya ce sune sharudan aure? Ka fita sabgar nan kafin in bata maka rai, tunda naga kai da kanka ba ka da hankali.”

Dakin ya cika da shiru. Fuskar Kawu Hamza ta canza, ya hadiye mamakinsa ya juya ba tare da ya ƙara magana ba. “Ke kuma,” Abba ya ce, yana kallona da karfi. “Mike! Ki je, mijinki na jiranki.”

Na miƙe da kyar, jiki a sanyi, na zura hijabina. Kamar gawar da aka shiryawa jana’iza ba amarya ba.

Na fito waje. Sai ga Mumy ta fito daga ɗaki, tana kuka mai kama da murmushi. Ta riko hannuna, ta ce “Ramlah… Na yafemiki. Allah ya sanya wannan aure ya zama sillar farin cikinki, Insha Allahu. Zamuzo miki ziyarar gida idan kun nutsu. Ki bi mijinki. Ki riƙe zaman aure da hakuri. Kibisa, kinji?”

Ban iya ce mata komai ba. Sai wani sabon kuka ya kubuce min.

Anty Luba ce ta zo, tana riko da hannuna. Tana fitar dani waje, zuciyata kamar za ta faso ƙirji. Na dago idona…

Gabana ya yanke. Kafafuna sun tsaya. Na ga Bashari.

Wani katoton namiji ne, mai dogon jiki da baƙin fata. Fuskarsa cike da gyambo da alamomin shaye-shaye da rikicewa. Bakin sa ya kone da sigari. Yana ta faman juyar da leɓe kamar mai fama da jaraba. A fuskar sa akwai yanka-yanka, kamar wanda yasha fada ko karan wuƙa.

Idanunsa kuwa? Kamar na dabba. Ba su cike da tausayi ba, balle kwarjini.

Wani irin rawa ne ya kama jikina. Hannuna ya saki. “Wannan shi ne mijina? Wannan dan daba? Wannan shi ne aka mallaka ni gare shi?”

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA SITTIN DA UKU.

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Ina tsaye a bakin ƙofar gida, ƙafafuna kamar an dasa su a ƙasa. Jikina ya mutu da jin nauyin zuciya. Sai na ji muryar Abba da nutsuwa "Zo ka karɓi matarka, Bashari. Allah ya baku zaman lafiya. Allah ya kiyaye hanya.”

Wannan kalma ta cika duniya ta. Ita ce kalmar da ta rufe duk wata damar da nake da ita kalmar da ta maida ni cikakkiyar amarya... ga wanda ba raina ya zaɓa ba. Bashari ya tunkaro ni da murmushi, sai dai ba murmushin annuri bane, murmushin mugun niyya ne irin wanda ya fi dariya tsoro.Hakoransa sun yi ja, suna nuna tarihin ƙonewar sigari da shaye-shaye. Zai iya ban dariya idan bana kuka. Yana takowa dabal-dabal kamar wanda ya saba da rawa, ba da ɗabi’a ba. Sai ya nufo kusa dani, ya rik’e hannuna da hannunsa mai kamar na maƙerin wuta. Atake... Na fashe da kuka.

Kukan da ba na jin zafi ba, sai dai na karayar da bata da mafita.Abba ya nufo, “Yabashi ni…” Ni kuma ina nan, ina ji, ina gani. Zuciyata na kai ƙololuwar karaya.

Na san yau, gidan da na taso a ciki ya sallameni. Sallama da hawaye ne, ba da albarka ba. Abban da ya renini shine yau ya mika ni ga mutum da ba ya jin tausayin da yafi na rakumi.

Daga wannan rana na daina kiran kaina “amarya.” A ranar da na hau motar Bashari, na san rayuwata ba zata sake komawa kamar da ba. Mun hau mota cikin ruwan dare. Na zura hijabi na launin ruwan kasa, ko da kuwa zuciyata ta fi kowane dare duhu. Bashari na gefena yana tuki kamar yana tuka wuta.

Motarsa irin tsofaffin Honda ne, ruɓabbiya, mai kujeru da ke cika da ƙura da wari. Inna lillahi… “Zan daure,” na faɗa a zuciyata. “Idan aure ne, zan jure.” Amma da kyar na iya numfashi. Wari ke tashi daga bakinsa kamar cakuda sigari da giya da wariyar ciki.

Yana dariya, yana tari, yana kurɓar wani ruwan da ban sani ba. “Ke Ramlah,” ya ce da murya kamar wani tsohon rago, “Kin saba da kauye kuwa?” “A’a,” na ce da ƙanƙantar murya. “To yanzu nan zaki zauna. Zaki koyi zaman gaskiya. Nima zan koya miki yanda ake zama da miji!” Ya ƙara dariya dariyar da sai mugunta ce kadai za ta iya haifar da ita.

Nikam na rasa irin wannan uba da Allah ya bani. Abba... mahaifi na dai, amma kamar ba shi. Mumy ce ta fi kowa hannu a cikin lamarin da makircinta da kaifin harshe ta juya zuciyarsa. Abba ya san Bashari ya san dabi’unsa, ya san irin rayuwar daba da rashin mutuncin da ke cikin shi. Amma saboda momy, sai ya watsar da ni, ya amince da auren da na ƙi, har ya tura ni wani kauye, inda babu kulawa, babu jin daɗi, babu gata.

Amarya ce ni, amma babu lefe, babu sabbin kaya, babu wani muradin aure. Sai tursasawa, sai shiru, sai kukan zuciya. Muryata ta mutu a cikin gida, murmushina ya shige ƙasa. Idanuwana suka cicciko da hawaye, masu zafi da nauyi. Na share su da sauri, na dafa ƙirjina, ina furta da karamin murya “Ya Allah, ka jikan mahaifiyata. Ka bani mafita daga rayuwar da aka zubamin da ƙarfi, ba da niyya ta ba.”

Tafiyarmu ta ɗauki fiye da awa uku a ƙarƙashin guguwar dare. Motar tana rawar sanyi, kamar zuciyarta ma na kuka. Ruwan sama na ta bugun gilashin taga da ƙarfi kamar yadda tsoro ke bugu a zuciyata, har yana kara da numfashina.

Shiru ne ya lullube cikin motar. Ban iya magana ba, ban iya kallonsa ba. Na kifa kaina a ƙirjina, idanuwana a lumshe, zuciyata na karanta addu’a cikin sirri

Sai da muka kusa fita daga cikin dajin hanya kafin ya ce wani abu. Muryarsa mai sanyi, amma babu tausayi a cikinta “Ki share hawayen nan. Wannan ba kuka ne zai canza ba. Wannan shi ne rabonki.” Na juyo a hankali, na kalleshi. Idanunsa basu motsa ba, kamar mutum ne da zuciyarsa ta dade da daskarewa. Na kasa cewa komai. Har murya ta min nauyi.

Da muka iso kauyen, rana ta ɓace gaba ɗaya. Duhu ya fara ratsa sararin sama, iska mai ɗauke da wari da danshi na kada bishiyoyin da suka yi tsufa a bakin gidaje. Bishiyoyi ne dogaye, suna sossai kamar shaidu ne na wani zamani mai nauyi.

Kasa cike da laka ce. Kowane mataki da nake ɗauka yana haifar da faɗawar takalma cikin danshi. Motar da muka zo da ita ta tsaya ba nesa da wani gini wanda Bashari ya ce shine “gidanmu”.

Ginin kamar ya dade yana fama da sakaci. Bango ne fari amma an rufe farinsa da tabon duhu kamar jinin dabbobi ko ruwa mai wari da ɗumi. Gaba ɗaya babu kofar arzuki sai wani tsohon karfe da aka jefa a bakin ƙofar wanda ma ya gaji da tsufa. Gidajen da ke kusa da shi suma ba su fi wannan ba wasu da rufin da ya karye, wasu da tagogi marasa gilashi, wasu ma tamkar gida ne da aka manta da su gaba ɗaya.

Na tsaya a waje, zuciyata na bugawa da karfi. Tsoro ya rufe ni. Idanuwana suna kallon wannan ginin da ba zan iya kira gida ba.

Bashari ya juyo, yana fuskanta da ɗan daga kai, kamar wanda ya gaji “Shigo mana!” ya ce da tsawa. Na ja numfashi na danne kuka, na daga ƙafata cikin jiki-jiki, na shiga ciki kamar mai tunkarar masifa. Cikin gidan yafi ban tsoro fiye da waje. Wani ƙamshi mai nauyi ya buga min hanci haɗin gumi, sigari, ƙwaya da datti. Idanuwana sun fara saɓa da duhun wajen, sannan suka hango Wata tabarma ce daya, mai ƙyama da tabo, a tsakiyar daki. A gefe akwai gado, amma katifar da ke kasa kamar rubewa tayi. Buhun shinkafa ne a wata kusurwa, an daura wasu riga da suka baci a kansa. A ko’ina kuma akwai ledojin sigari, kwalaben lemo da tsakuwa, wasu a bude kamar an sha kwaya a ciki. Ban iya matsawa ba. Na tsaya cak, na dafe ƙirjina. Wannan ne gida? Wannan ne aure? Wannan ne rayuwar da zan fara?

Na tsaya a bakin kofa, jikina na rawa. Hannayena biyu na matse su a ƙirjina. Na kalli dakin, idanuna sun cika da hawaye.

Sai Bashari ya juyo da ido mai nuna jin haushi “ki shigo mana! Ko kuna so makwabta su zo su ga ki a waje?”

Tsawar tasa ta katse numfashina Sai naja numfashi, na shige ciki a hankali kamar wata yarinya da aka tura rami. Tunda na shiga, zuciyata ke ta cewa "Ya Allah, ka jarrabe ni da jarabawar da zan iya ɗauka... ka tsare ni daga kaskanci da cutar zuciya."

Na kalli dakin da na shigo cikinsa bangon nan mai dusar tabo, rufin da kwari ke zagaye kamar suna shagali, katifar datti cike da ƙura da wariyar faduwar rana. Ina tsaye tun fitowarmu daga mota har yanzu ban iya zama, ballantana na kwanta. Kowane gefe na dakin wani abu ne ke sheƙi da ƙazanta. Na dubi sama, inna lillahi…

Sai ga Bashari ya dawo daga dakin waje da wata tsohuwar tsintsiya da ke zazzare kamar wadda karnuka suka baje kai a kanta. Ya miko min da murya mai ban tsoro “Ga tsintsiya. Ki share. Gidan mace ke nan fa, ko? Ni ba shara nake ba.” Na karɓa ba tare da kallo ba, na fara share-share da gwiwa. Kamar raina yana fita da kowanne gefe da na goge. Datti kamar shanƙo yana tashi sama, numfashina ya fara ɗauke wa. Na dinga janyo shara, ledoji, kwali, buhun wake da ya ɓarke, da kwandon gawayi da aka jefar a tsakiyar ɗaki. Hankali na yana rawa. “Ya Allah… Wannan aure ne ko hukunci?”

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA SITTIN DA HUDU

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Ban gama sharewa ba, sai ya koma yafita daga daƙin alokacin ne nafito daga dakin ina neman abun shara amma babu tsaya gefe da gun uwar ɗakin, a cikin wani irin yanayi da babu kalma a duniya da za ta iya fassarawa. Hannuna na riƙe da ƙaramin yatsa na tsintsiya, amma zuciyata cike take da wani nauyi da ba na jiki ba nauyin ruhi ne da tunani, nauyin da nake jin kamar zai taɓe ni.

Ina son in kwashe, amma ban san inda zan zubar da sharar ba. Ko'ina ya cika da tarkace. Wajen ya fi kama da dandalin bola fiye da gidan zama. Duk inda idanu suka kai buhuna, ledojin sigari, kwantena na giya, da tarkacen da ko baƙin rana ba za ta iya bayyana su.Na ɗaga kaina a hankali, zuciyata na juyawa da tambaya mai raɗaɗi "Ina Ramlah? Ina yarinyar da ta taso cikin tsafta da mutunci? Wacece wannan da ke tsaye da tsintsiya a hannu, da hawaye a ido, a cikin kazanta mara iyaka?" Kafin in samu amsa daga zuciyata, sai na ji muryarsa a bayana ta fito da ɗumi irin na wuta a ƙarƙashin kankara “Ramlatu, idan kin gama sharar, sai ki watsata nan.” Kalmar tasa kamar ta fasa kunnena. Duk wani yunƙurina na kwantar da hankali ya watse. Na tsaya cak, numfashina ya ɗan tsaya. Amma ban juya ba. Ban ce komai ba. Sai zuciyata kawai da take ta bugawa tamkar ana dukan ƙaho cikin daki mai kaɗaici.

Na ɗan matsa da ƙafafuna a hankali, ina ƙoƙarin jure wa warin da ke hana numfashi. Kowanne numfashi kamar ana shaƙa min ƙanshi ne da daddadɗen datti na dan Adam, na sigari, na sharar da ba a taba kwashewa ba. Idona ya kai can gaban ɗakin, inda wani kwando mai fashewa da tarkace ya tsaya kamar wani gini. Amma kafin in ɗan taka gaba, sai na ji motsi a bayana.

Kafin na juya gaba ɗaya sai kawai na hango shi Bashari. Ya durƙusa yana dibar wata sharar ya zubata cikin rigarsa kamar zai ɗora wa kansa naɗi ne. Rigarsa ta baci sosai. Ta tashi da kazanta, Da wani irin yanka da kuzari, ya fizge rigar nan daga jikinsa, ya jefar da ita a gefe. Sai gurnani yayi, yana dariyar da ta fi kuka firgita mutum. “Menene amfanin hanuna idan ba zan kwashe ba?” ya faɗa da ƙarfi, yana kallona “Haba amarya! Wannan ai shine auren!”

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull