Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 24

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 24

Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 24: Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 24. Dakin ya cika da ƙamshin Le Labo Santal 33, wanda aka shafa akan…

4,497 words

Dakin ya cika da ƙamshin Le Labo Santal 33, wanda aka shafa akan labulen dakinsa. Haske mai sauƙi na shiga ta bangon gilashi mai duba birnin. Komai yana cikin tsafta da tsari. A gefe, Bang & Olufsen speaker na kunna kiɗan jazz instrumental, ba tare da surutu ba.

Yana tsaye kusa da tagar dakin, yana kallon Eiffel Tower a nesa. Ya ciro wayarsa, Vertu Signature Cobra, da aka kera musamman. Ya shiga contact list, ya danna sunanta“Ayshatu ❤️”

Ringing...

Ringing...

Babu amsa.

Yayi shiru. Ya sake kira. Har sau uku. Amma har yanzu babu wani da ya daga.

Ya janye wayar a hankali, ya kafe tagar.

Bai tsaya jiran lokaci ya wuce ba. Ya ɗauki key ɗinsa, ya shiga motarsa da direba. Suka nufi residence dinta, wanda ya saya mata ne kwanakin baya. Wurin da ya fi yi mata tsari da tsaro, tare da kwanciyar hankali.

Suna isa, yayi saurin shiga. Amma ɗaya daga cikin yaran aikinta ya zo da nutsuwa

“Monsieur, madame Ayshatu bata nan. Ta fita tun jiya, bata fadi inda zata je ba. Babu waya, babu sako.”

As’ad ya tsaya, kamar mutum da aka cire rai. Bai ce uffan ba..

Yana komawa part ɗinsa, ba ce wa kowa komai ba, ya nufi private bathroom dinsa. Ya tube rigarsa, ya shiga cikin Jacuzzi spa bath, mai cike da dead sea minerals da kumfa. Ruwa mai zafi ya fara ratsa jikinsa, amma babu ruwan da zai iya wanke tunanin da ke kansa.

Yana fitowa, ya fesa jiki da Acqua di Parma Colonia Oud, wanda ya saba amfani da shi a lokacin damuwa. Sai ya shiga cikin bedroom dinsa ya kwanta.

******

Tana cikin motarta, hancin iska na busa mata a fuska tana kallon waje. Gashinta na rawa a hankali a cikin iska. Yamma ta kusa kama dare, amma zuciyarta cike take da ƙoƙarin kwantar da hankali da tunani. A gabanta, ta hango motoci biyu a harabar gidan Rolls Royce Cullinan da Maybach S-Class, waɗanda As’ad ke amfani da su musamman idan ya dawo daga tafiya mai nisa. Sai ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfi. Hannunta ta taɓa kirjinta, kamar tana ƙoƙarin janye bugun zuciyarta. “As’ad ya dawo.”

Kallon motocin ya tabbatar mata fiye da kira ko saƙo. Ko da bata samu wani saƙon daga gare shi ba, zuciyarta ta tabbatar "Wannan ba kowa bane shi ne."

Sai kuma wani nauyin nadama ya sauko mata. Ta san irin ciwon da rashin dawowarta zai iya jawo masa. Ta kuma san cewa As’ad na iya tunanin ko bata da lafiya.

Amma ita fa ba haka take ji ba. A zuciyarta, ficewar da ta yi tamkar hanyar neman nutsuwa ce. Tana so ta fahimci kanta, da jin inda rayuwarta take nufa.

Amma yanzu… ya dawo.

Ba tare da ta zaga bangarensa ba, ta nufi shashenta. Da ta shiga, sai ta tsaya a gaban madubi, tana kallon kantafuskar da ta ɗan rame da gajiya, amma tana ɗauke da kyau da kamewa. Wani irin taushin zuciya ya lulluɓe ta.

Ta buɗe wardrobe dinta ta fitar da shigar da yafi so doguwar rigar silk, mai launin ruwan hoda mai dumi, da ɗan laushin kamshi daga Baccarat Rouge 540 da take fesa masa idan yana kusa. Tana ɗora ɗan ƙaramin veil mai launin milk white a kanta, Tayi kyau sosai Tunaninta ya koma kan yadda Alhaji Muqaddam ke sumbatar jikinta da salon da ya sha bamban da na kowa. Jarumi ne, mai kuzari da salo, kuma yana sa ta ji daɗin kasancewa tare da shi. Ta jingina, tana murmushi har sai da dariya ta kubce mata. “Wallahi ina jin daɗin zama da shi… I so love being with him,” ta faɗa da karamin murya, tamkar tana amsa wa zuciyarta.

Ta bada umarni a ɗakin girki da a haɗa abinci mai sauƙi grilled lamb chops da creamy mashed potatoes, tare da salad mai danɗanon lemon da honey mustard.

Itama ta haɗa fresh mint tea da kanta, ta zuba a cikin kofin karfe mai sheƙi, ta ɗora akan tray mai daɗaɗɗen ƙamshi.

Daga nan, ta ɗauki tray ɗin, tana jin bugun zuciyarta yana ƙaruwa a kowane mataki da take ɗauka. Rayuwarta na iya sauyawa da kalma guda.

hankali ta buɗe ƙofar. Dakin na As’ad yana cike da hasken fitilun golden chandelier, sai jikin bango mai launin ash da kayan fatar fata suka cika shi da nutsuwa. A gefe, yana zaune a cikin babban kujerarsa na fata, yana aiki a kan system dinsa MacBook Pro 24-inch edition.

Yana cikin duba bayanai ne, yana rubuta wani report na bankin da yake aiki da shi a Switzerland. Amma da ƙamshin turarenta ya cika dakin bai buƙaci kallon wayarsa ko jin kofa ba. Ya san ita ce.

Da ya dago ya ganta, sai ya ajiye system ɗin. Ya miƙe a hankali. Jikinsa yana fitar da zafi da zafin so. Yana kallonta da irin kallon da zuciya da ido ke fassara tare. Bai ce komai ba. Ya buɗe hannuwansa.

“I missed you, matata.”

Yana cewa da murya mai nauyi, mai kaɗa jiki kamar kiɗan da ke fitar da nutsuwa daga jiki zuwa ruhi.

Tana kallonsa, itama idonta cike da wani yaji mai nauyi. Sai ta aje tray ɗin a gefen coffee table. Tayi ƙoƙarin fasalta dariya, amma ba dariya ba ce tausayin kai ne.

“Ina kikaje?” Ya tambaya yana matso da ƙamshin jikinsa gareta.

Ta ɗan kauda kai, tana sosa gefen hijabinta da yatsanta. Sai tace da laushi “Na je shopping ne. Bansan cewa ka dawo ba...”

As’ad ya kalle ta da dan ƙorafi a idanunsa, amma babu fushi zuciyarsa ta fi soyayya da rauni fiye da tuhuma.

“Ni kuma... Na dawo ne don nayi surprise dinki. Na zata zan same ki a gida.”

Ta bata rai kadan, alamar ta taɓara “Ka yi hakuri...”

Ya matso, ya kamo tafin hannunta da natsuwa. Ya shafa bayan hannunta kamar yana karanta sirrin cikinta.

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA HAMSIN DA TARA

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Kwana biyu da suka wuce, jikina yana dan samun sauƙi ba kamar da ba. Wannan ƙaramar sauƙin ne ya sa na samu kuzarin gyara gidan gaba ɗaya, har da wardrobe na Abba da Momy. Ban sani ba, amma yau kam na ji wani natsuwa a zuciyata da ya sa komai yake yi min daɗi.

Na cire kayan da suka tsufa, na wanke taga da labule, har da sabunta fasalin kujerun. rayuwa da tsafta, shiru, da sabuwar ni.

Kasancewar muna hutun makaranta, rayuwata yanzu ta takaita idan na gama aikin gida, babu abinda nake yi illa kallon Korean film. Na saba da hakan sosai“My Name,” “Queenmaker,” “True Beauty”, duk sun zame min abokai.

Wani lokaci kuma, ni da Maryam sai mu sha hira a waya. Ita ce abokiyar hirata yanzu. Sau da dama tana cewa zata zo gidanmu, amma tsoron halin Momy ke hana ni cewa ta zo. Ba wai tana tsanarta ba sai dai akwai wata tsananin dokarta da ke hana ni samun sauƙin shigowa da mutane gidan.

A zahiri, komai yana tafiya dai-dai. Amma a boyayyen ɓangaren zuciyata, akwai abu daya da ke damuna amma bana da yanda zanyi na bayyana shi.

Gaba na Har yanzu yana wari. Yana bugawa. Wani lokaci har ina jin wata irin kasala da rashin kuzari. Na sha niyyar zuwa asibiti, amma sai na kasa yanda zan gaya wa likita hakan ba tare da jin kunya ba. Sai na kanyi shiru, in ɗora damuwar a zuciya, kamar zan iya jurewa har ya wuce da kansa.

Yau Jumu’a ce. Ranar da nake ganin mafi tsarki a mako, kuma mafi cike da sakonni daga zuciya. Da safe, na kira Musa, nace masa ya turo min sabon fim. Ya aika min da “Business Proposal” fim mai dariya da soyayya, ya rage min nauyin zuciya.

Daga nan na nemi izinin fita daga Umma. Na gaya mata zan je dubiyar classmate dita Ita kuma ta ce “Toh, Allah ya kiyaye. Kada ki ɗade.”

Na kira Maryam Muka hadu a wata unguwa kusa,Haka muka je muka duba Yasmeen yar ajinmu ce, kuma course ɗinmu ɗaya. Tana ɗan fama da zazzabi da kasala, amma ta fara jin sauƙi sosai. Dakin da take kwance a ciki na asibitin bai da girma sosai, amma yana da tsafta da iskar da ke motsa labulen window a hankali.

Muna kan hanya ne bayan mun fito daga asibitin, sai Maryam ta fara gayamin wata magana mai ɗan ɗaukar hankali. Ta ce

“Wallahi ina fatan aure zanyi nan kusa. Da ace a cikin samarin da ke zagaye da ni, ɗaya zai zame min mijina, ai da rayuwa tafi ni Aure nakeso wallahi amma yan iska kowanne kana masa maganar auren sai ya gudu.”

Na dube ta da mamaki. Murmushin da nayi ba wai dariya bace yana ɗauke da tambaya da jin baƙin ciki mai sauƙi. Ni kam bance komai ba. Sai kawai na bita da kallon ido, amma zuciyata tana cike da tambaya

Mun rabu da Maryam a layin gida, na shigo gidan da nutsuwa. Ban san cewa wani abu ya faru a baya ba, sai daga baya na fahimta.

Ashe Mumy ta kira Musa a waya, ta ce ya turo mata fina-finai. Ban sani ba, ban ji ba, kuma na zata fim ɗin da ya turo da safe shine itama takeso. Tunda nasan yadda Mumy ke da “zero tolerance” akan fina-finai kila tana so ta duba ko suna da kyau.

Ni kam tun da na shigo gida na nufi kitchen. Na dafa jollof ɗin taliya, nayi musu abinci mai sauƙin mai ɗan ɗanɗano.

Na shiga bandaki Bayan na shiga bandaki domin wanke fuska, Abba ya dawo gida daga offices. Ya shigo cikin nutsuwa, yana sallama kamar yadda ya saba amma yau babu wanda ya amsa saboda babu kowa gurin. Ya tsaya a tsakar gida, yana duban falon da ke cike da shiru da ƙamshin turare Sai fan ɗaya ke kadawa, yana fidda iska mai sanyi.

Ya nufi dakina da niyyar gayamin sakamakon jarabawa da ya gani a sakon wayarsa. Sai dai, kafin ya kai ƙofar daki, wani abu ya tsayar dashi.

Wani nishi ne mai ban tsoro ya doki kunnensa. Nishin mace. Nishin namiji. Muryoyin jin daɗi amma ba daidai ba. Sautin mara dadin ji Zuciyarsa ta fara bugu da ƙarfi, kamar ana dukan ƙaho a ƙirjinsa.

Ya buɗe ƙofar dakina da juyayi. Idanunsa sun sauka kai tsaye kan laptop dina, wanda aka barta bude. Haske da sauti suna fitowa daga cikin bidiyo wanda ko magana ya fi ƙarfin bayani.

Wata mace da wani namiji ba kaya a jikinsu, suna saduwa da juna da ƙwarewar da ta keta duk wata al’ada da ɗabi’a.

Abba ya tsaya cak. Jikinsa ya daina motsi. Idanunsa sun zube akan allon. Hannunsa ya saki jakarsa da ta faɗi kasa da ƙara. Zuciyarsa ta shiga tsalle-tsalle. Bai iya buɗe baki ba. Sai kawai hawaye suka sauka daga idonsa

Tana cikin waya a tsakar gida ne, sai ta ji motsin ƙarar jakar da ta faɗi. Ta shigo da sauri tana faɗi “Abban Ramlah, ban ji sallamarka ba! Har ka dawo?”

Sai idonta ya sauka akan laptop ɗin da ke bude. Ta tsaya cak

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Wannan fa... me nake gani haka? Iskanci a cikin gidanmu? Ramlah ce ke kallo ne?.”

Sai ta dafe kirjinta, idonta ya cicciko da hawaye. Abba ya rufe laptop ɗin da ƙarfi amma da jin zafi. Ya zauna a gefen gado, ya rasa inda zai kalli Mumy. Jikinsa ya daina motsi.

Ya ce da wata murya mai rauni:

“Ya Allah… yanzu haka muka gaza? Ashe haka tarbiyya ta kare?”

“Abinda na gina shekaru goma sha tara… ya faɗi a rana guda.”

Na fito daga toilet ina shafe fuska da tawul, jin karar mutane a daki. Amma da na fito, na hango su Abba da Mumy a tsaye cikin dakin da shiru.

Idanun Abba sun makale a kaina. Zuciyarsa kamar ta faɗi. Kafin na isa inda suke, sai ya fizgeni. Ya kwada min mari biyu da suka sa na durkushe a ƙasa. Tawul dina ya zame, na rufe fuska da hannuwana. Jikina ya daina motsi. Cikin kuka mai tsuma zuciya nace

“Abba…”

Amma kalmomi sun makale. Bai saurara ba. Bai duba ko da ni ne na yi ko wani ne ya tura min bidiyon ba. Zuciyarsa ta cika.

Ya furta da murya mai fashewa

“Kin karya zuciyata, Ramlah.”

Cikin zuciyata akwai tambayoyi da ni kaina ban da amsa gare su.

Wai ni me nake kallo ne? Ta yaya wannan bidiyo ya shiga system dina? Musa ne ya turo? Ko wani ya hack laptop dina? Ko dai wata curiosity ce da ta fi ƙarfin hankali?

Zuciyata ta tsinke.

Gini da tsarinta ya rufta.

Ina son faɗa cewa bana kallon fasikanci. Ina son bayani. Ina so in kare kaina.

Amma kalmomi sun ɓace. Ban san inda zan fara ba.

Duniya ta birkice min. Shiru ya ba ni wahala. Kallon Abba da Mumy ya fi min ciwon mari.

Kunyar Allah, kunyar kai, kunyar iyaye duka sun riskeni lokaci guda

Sako Zuwa Ga Masu Karatu

Wannan labari ba wai na nishaɗi bane. Labarin gaskiya ne da ke faruwa a rayuwa ta gaskiya.

Yara da yawa suna fuskantar shigar hotuna marasa kyau da bidiyo masu lalata ta hanyar da ba su shiryawa ba.

Amma rashin fassara, rashin tattaunawa, da tsoron magana na haifar da karayar gida gaba ɗaya.

Iyaye ku saurari yayanku. Kada ku yanke hukunci nan da nan. Ku basu dama su bayyanawa.

Yara ku kare kanku. Kar ku bari fasikanci ko wani ke turawa ya ƙone amana da tarbiyya a hannunku.

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA SITTIN

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Abba yana zaune yana huci, idanunsa jajir, hannunsa a lumshe cikin fushi da kunya. Zuciyarsa na kukan da baki ya kasa furta. A gabansa, Ramlah ta tsugunna, jikinta a kasa, tana ta kuka kamar rai zai fita. “Abba… wallahi… wallahi ba ni na saka ba..Ni… ko da wasa… ban taba kallon wannan ba. Abba, na rantse da Allah…”

Sai dai kamar ba magana ke fita daga bakinta ba. Kamar ba kunnuwan sauraro ke wajen Abba ba. Sai ya daga hannu da karfi, ya buge ta a baya da takalmi mai ƙarfi. Ta yi kicibis da bango, ta sake komawa kasa tana kuka. Sai ya sake ɗagowa, ya daki ta a kafaɗa da ƙarfi, yana cewa Kallon fasikanci, Ramlah? Kallon haramci? Kina kallon abin da zai lalata miki zuciya da idonki, ya kuma jawo miki fushin Allah?! Ramlah... acikin gidana? Wannan tarbiyyar da muke miki kenan?” Ya daga ƙafa, yana girgiza kai cikin takaici. “Daman abunda na siya miki kiyi da laptop din kenan? Daman karatun da kikeyi da'ita kenan don ki zauna kina kallo kamar ‘yan iska?” Ya furta kamar zai fashe da kuka. Cikin murya mai raɗaɗi, ya ƙara cewa “Shin Allah yana kallonki kina kallon fasikanci ba tare da jin tsoro ba? Ina tsoron abinda zai faru da ke gobe... idan kika mutu kina kallon fa kicewa Allah me”

Mumy, da ke gefe, ta fashe da kuka.hawaye na gangarowa ba tare da ƙarewa ba. Ta matso kusa da Ramlah tana dafe kirji, murya na rawa “Na shiga uku, Abban Ramlah… na shiga uku! Ramlah, wallahi kullum sai na faɗa. Sai na ce ki ji tsoron Allah. Sai na tunatar da ke cewa Allah yana kallon duk abinda kike yi. Ashe baki ji ba? Ashe baki daina ba?” Ta share hawaye da gefen zani, tana girgiza kai cikin karaya da fargaba. “Kwanaki na faɗa miki akan hakan, ko? Ban faɗa miki ba, Ramlah?” Ta tsaya, tana kallon idon Ramlah da cikakken takaici da rudani. “Wallahi kin ci amana. Amana ta uwa. Amana ta Allah.

“Abba…ban taba ba ka saurareni wallahi wallahi Allah bantaba ba wallahi… ba ni nake turawa ba. Musa ne… shi ke turo… amma ba ni nake saka shi ba, ni korean film nake sawa ya turomin bantaba kallon tsiraicin kowa ba wallahi Abban…”

cikin wani irin ɓacin rai Abba yakifa mata mari da sai da jini ya fito ta hancinta yace mata “ Bazakiyimun shiru ba sai naci ubanki agurin nan sakarya mara hankali wacce bata tsoron haduwarta da Allah.” Abba ya buge tebur da ƙarfi. Mumy da ke gefe sai kuka take.

Abba ya janyo wayarsa cikin rawar jiki, yana murza lambar Musa. Bayan gaisuwa ta gaggawa, ya ce “Kazo gidan nan yanzu! Ina so in tambayeka abu daya.” Bayan mintuna goma, Musa ya iso gidan cikin firgici. Da ya shiga, ya hango Ramlah a kasa tana kuka. Mumy da abba suna gefe, fuskar su cike da takaici.

“Musa,” Abba ya ce da muryar da ba a saba ji daga gare shi ba. “Wane irin bidiyoyi kake turawa wa Ramlah?”

Musa ya ɗan kau da kai. Zuciyarsa na bugawa. Ya ce “ ni dai, bansan kowanne irin film baniba Abba saboda kaga ban iya karatun hausa ba tana rubutamun ne a takarda aje a turamata kuma irin jajayen mutanen nan ne.”

Abba yasallami musa yakara kifamun mari da yasanyani kara rushe da kuka.Abba ya dubi Ramlah tayi ƙasa, hawaye kamar ana feshin ruwa. Sai ya buɗe baki a hankali, amma kalmomin da suka fito masu zafi.

“To wallahi… tun da ke kika saka kanki cikin iskanci… aure za kiyi. Aure! Idan abunda kike nema to tabbas sai dai agidan aure bazaki lallacemun ba bazaki jawomun abun kunya ba bantaɓa aikata zina ba bantaba ba wallahi kema baki isa ba. Aure zanyi miki gobe goben nan nagayamiki. ”

Daga cikin kuka da firgici, Mumy ta tsaya, tana kallon Abba da hawaye a idanunta. Duk da tsoron da take ciki, ta ji lokaci ya yi da zata faɗi gaskiya. “Abban Ramlah…Ramlah… ta dade tana son aure. Tun watanni da suka wuce na lura da sauyin halinta. Sai dai… ni ce naki gayamaka Abba ya ɗaga kai da mamaki, yana kallon matarsa kamar bai ganeta ba.

“Kika ki gayamun ? Me ya sa?”

“Saboda… ina so ta samu karatu da cikakken gata kafin aure. Ina son ta kai wani matsayi a rayuwa. Ina son ta sami ilimi wanda zai zama kariya a rayuwarta idan mijin ya ki, duniya ta fadi, ko wata matsala ta taso.Bana so ta yanke abin da bazata iya jurewa ba. Sai nake cewa idan ta shiga aure da zuciyar da bata gama girma ba, za ta fuskanci bala’in da zai fi haka.” Muryarta na rawa, tana mai janye idonta daga kallon Abba. “To amma gaskiya ne, Abba… ta fi ƙarfi. Tana son auren gaskiya. Kuma idan bakar sha’awa ya fara shige mutum, kuma babu mafita, shaidan yakan ja hanya..Na kasa tsayawa da ƙarfi. Na bar ta cikin duhu… ban tallafe ta da mafita ba. Na yi kuskure.”

Abba bai ce komai ba nan take. Zuciyarsa ta cika da abubuwa daban-daban fushi, tausayi, mamaki, da tunani mai zurfi. Sai ya zauna a kujera, yana sauke ajiyar zuciya. Idonsa ya kau da kallon kai tsaye, kamar yana tuna duk irin kokarin da yayi a kan tarbiyyata da yadda abu ya juya a lokacin da bai ɗauka ba.

Dakin ya dauki shiru, kamar an tsayar da lokaci. Sai kukan zuciya ne kawai ke karade falon. Tsit kamar fuskokin bango ma sun girgiza da abinda suka gani da suka ji.

Muryar Mumy ce ta kaure, cikin yanayi na rashin karfi da tausayawa “Abban Ramlah… tunda auren take so, tunda wannan ne mafita da kake so, ga Bashari. Ka aurar da ita gare shi. Ka sanshi, ka san komai nasa. Yaro ne mai hankali a gabanka. Ni ce naki gaya maka tun da fari, saboda ina fatan ta gama karatu. Amma yanzu, bari mu kawo karshe. Zuciyarta na bukatar mafita ba zato ba tsammani ba. Aure ya fi lalacewa, ko ba haka ba?”

Abba ya dago kai daga inda ya ke zaune, idanunsa jajir, numfashinsa yana fita da nauyi. Ya kalli matarsa na kusan dakika goma, sannan ya ce da murya mai kulle karfi da doka “Na amince. Ki sanar da Bashari yanzu ya turo magabatansa gobe zai aure Ramlah. Yau gobe, cikin sati, farkon wata… ko yaushe. Har abada, halak malak na bashi ramlah Wannan shine mafita.”

Ni kuwa Ramlah duk jikina ya saki. Idanuwa na suka firfito da hawaye tamkar ruwan damina. Da karfi na mike daga inda nake tsugunne, na durkusa har kasa na kama ƙafafun Abba. Raina na rikicewa. Cikina na murdawa. Zuciyata na harbawa da tsoro fiye da rashin lafiya. “Abba… don Allah... Abba… karka bani Bashari. Wallahi, bana sonsa. Wallahi, bana kallon batsa. Bana aikata abinda kuka gani da gangan. Wannan abu da ya faru, Allah ne shaida bani na kunna ba bani na kallah ba.”

Na sa kuka da karfi. Na rike ƙafarsa kamar na rike hanyar numfashina. Ni fa ba zan iya rayuwa da Bashari ba. “Abba, ba shi da tarbiyya. Kai ka fi kowa sanin hakan. Duk wannan watanni, kana gani da ido ni banason aure ni bance ina so ba ni bana kallon batsa.”

Abba ya fizge ƙafarsa daga hannuna da karfi, yana kallona da idanu masu cike da wuta da takaici. Ya tsaya, ya matso kusa da ni.

“Ke dai yanzu ne kike yin kuka? Lokacin danakeso ki rike tarbiyya, sai kin kulle daki! Lokacin da na saya miki system, sai kika mayar da shi makaman fasikanci. Yanzu kuma kina kuka saboda ni na zabar miki mafita? Bijirewa hukuncina dai-dai take da tsinuwa a kanki, Ramlah!”

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA SITTIN DA DAYA

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Bai kare da haka ba. A cikin fusata, ya hankadeni gefe, sannan ya kwadawa fuska ta mari guda mai zafi da sautin da ya karade dakin. Na faɗi kasa, na rik’e kaina ina shiru bana jin jiki na, ina jin yankan zuciya ta ne kawai. Mumy, daga gefe, sai ta zube ta dafe kirjinta, tana kuka, tana girgiza kai. Muryarta ta kasa fita sosai, sai da tayi jinkiri, sannan ta ce da karfin gwiwa “Abba… dan Allah… kar ka tilasta mata… Ni na san Bashari. Bashida kirki da biyayya, Ramlah ba zata iya da shi ba. Wannan aure zai zama azaba. Kamar wuta ce za ka cusa mata ka ce ta zauna a ciki saboda ka ji zafi.”

Amma Abba ya fizge jikinsa da zuciya, yana cewa “Na gama magana. Aure za a yi. Ni ubanta ne. Na fi kowa sanin me ya dace da ita.”

Ya juyo ya fice daga dakin da sauri, yana mai murza makulli da karfi. Kamar ana fitar da hukuncin da ba za a iya soke shi ba. Kujifa abunda mumy takeyi sai ba'itace ta zuga abba ba kuji ba. Amma tana ganin yafita tamike tana murmushi da dallamun harara.

Wallahi ba zan taɓa manta ranar ba. Ranar da rayuwata ta karye. Ranar da duk wata ƙaramar fata da nake da ita ta narke kamar ƙanƙara a rana.

Na zauna a gaban mumy, na durƙusa, na rasa abinda zan ce in ba rokon ta da kuka ba. “Mumy… baki ji me Abba ya ce ba? Baki ga abinda yake shirin yi ba? Dan girman Allah, dan zatin Allah, ki taimake ni. Ki tsaya ki saurare ni kada ki bari a auramin Bashari.”

Sai ta yi dariya. Dariyar da har yau take min ƙara a kunnena muguwar dariya, dariyar da bata da tausayawa.“Auren Bashari? Ai babu fashi, Ramlah. Tunda ubanki ya yanke hukunci ko kiyi biyayya, ko ki karɓi tsinuwar iyaye a kanki”

Na share hawayena, sai na fara bayani. Ba na buƙatar hawaye kawai gaskiya na buƙata ta kare ni. “Mumy… na san Bashari tun ina ƙarama. Ranar da Abba ya samosa yana kan hanya, yana shaye-shaye, yana dabanci, ya ɗaukosa gida. Ni ina tsaye. Na gan shi da idona. Na ji muryarsa, na ga yadda yake ruɗewa cikin rikicewa.Abba ne ya sa shi a makaranta. Abba ne ya biya masa kudin karatu. Abba ne ya ɗauke shi a matsayin ɗa. Amma duk da haka bai sauya ba.Nasha jin sunansa a rediyo. Nasha ji suna cewa yansanda na nemansa. Nasha ji an ce ya kashe mutum, amma masu kuɗi suna toshe labari.Na sha jin mutane suna cewa bashida halin zaman aure, bashida tausayi, kuma mutum ne mai tarin boyayyen laifi."

Abba ya turo ƙofa da ƙarfi ya shigo dakin. Na tsugunna a ƙasa ina kuka, na riƙe ƙafar Mumy kamar ƙa’idar rayuwata na rataye da mafita daga bakin ta.

Zuciyata na bugawa da tsoro, da fatan zata tsaya ta saurare ni. Amma bata ce komai ba.

Abba ya tsaya yana kallona da fuska cike da fushi, numfashinsa yana fita da huci. “Wallahi, Ramlah, idan kika ƙara cewa ba za ki auri Bashari ba to ki sani ban yafe miki ba. Ko da kinaso ko bakyaso aure ɗin nanysai nayi miki. to kisani Allah ya isa!” Kalmarsa ta tsaya cikin zuciyata kamar dutsen dutse. Sai na fashe da wani kuka mai zurfi, na matse kafar Mumy da hannuwana biyu. A ƙofar dakin, Yaya Bilkisu ce tsaye – wacce ko da wasa ba ta taɓa ra’ayin ta tsaya min baya. Amma yau… yau ta ce “Abba, amma fa Bashari… haba dai Abba! Bashari fa?” Idanunta sun cika da damuwa, da mamaki. Bilkisu ta tsaya min? Duk da yadda ta tsaneni, sai ta ce gaskiya. “Wannan mutumin dai fa, Abba, mun san shi. Kusan kowa ya san shi mutumin banza ne”

Kafin Abba ya iya cewa komai, na ɗago da fuska cike da hawaye, na ce da shi cikin murya mai rauni “In shaa Allah, Abba… ni mai biyayya ce gareka. In shaa Allah… na amince.” Sai na fashe da sabon kuka, wanda ko zuciya ba zata iya ɗauka ba.Ya kalleni, idonsa ya sauka a kaina, amma ba alamar tausayawa ko jin kai. Sai ya ɗago kansa sama yana furzar da iska mai nauyi da damuwa.

Yaya Bilkisu ta ɗan matsa gaba, ta juya ga Mumy cikin ɓacin rai “Haba Mumy! Wannan shi kike goyon baya? That illiterate, that drug man? amma wannan zalunci ne. Duk da haushinta nake ji, amma wallahi babu adalci a wannan aure.”

Mumy ta ɗago kai da ƙyar, ta buga hannu a ƙasa, sannan ta ce da masifa: “Ku yi shiru! Ku bar ni da 'yata! Wannan aure za a yi ko da me. Ai tunda ita ba ta da hankali, dole mu tsare ta.”

Ni kuwa a ciki, bani da ƙarfi, bani da dama. Abba ya tsine, Mumy ta tabbatar, Yaya Bilkisu ta faɗi gaskiya amma babu wanda ya tsayar da komai. “To ni fa fa?”

“Ni ce aka yankewa hukunci ba tare da tambayata ba.”

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull