Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 28
Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 28: Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 28. A tsaye yake a ɗaya daga cikin manyan windows ɗin yana kallon waje.…
4,468 words
A tsaye yake a ɗaya daga cikin manyan windows ɗin yana kallon waje. Can sai idonsa ya sauka kan wata mace da ta fito daga cikin Range Rover SV Black Edition, tana sanye da gilashi mai kauri da mayafi. Gajeriya ce, kyakyawa, cikakkiyar mace. Ya ɗan jinjina kai, zuciyarsa cike da mamaki “Kai... kamar Ayshatu... amma ba zai yiwu ba. Ayshatu ba za ta fita haka ba... ko kuma?” Sai ya ja da baya, yana kokarin tuna. daidai yadda Ayshatu ke tafiya. Ko da yana ƙoƙarin watsi da tunanin, wani murɗaɗɗen mamaki ya cika masa zuciya. Ya nisa, ya ce a zuciyarsa “No... ba ita bace. Amma... wannan kamannin... tafiyar... yaushe Ayshatu ta fara tuki ita kaɗai?” Ya ɗan runtse ido, sannan ya juyo. Zuciyarsa ta soma hargitsi. A karo na farko a rayuwarsa, yana jin wani abu mai sa masa rauni da tuhuma a zuciya.
Ya janye labulen window ɗin, ya ce “Kila I'm just imagining things... maybe I'm just tired. I need rest.”Ya koma cikin royal bedroom ɗinsa, ya rufe ƙofar a hankali.
Tana shigo cikin ɗakin Alhaji Muqaddam da zuciyarta cike da tambayoyi. Kafin ta samu damar buɗe baki, ya matsa kusa da ita, hannunsa ya kamo "Ayshatu..." muryarsa cike da jaraba "ba zan ƙara ɓoye yadda nake ji ba." Kafin ta iya magana, ya jingina da ita, hannunsa yana sosa gefen fuskarta da yatsansa. Ta kasa motsi bakin ta buɗe, amma babu kalma daya da ta fito.
Sannu a hankali, ya sunkuya, ya sumbaci labbanta. A daidai lokacin, zuciyarta ta buga sau biyu, hannunta ya hau kirjinsa, ba don tureshi ba,Ta ja baya kadan. "You're too intense... This isn't fair," ta ce, muryarta tana rawa. Ya ɗan yi murmushi, idonsa yana rike da nata. "More than your weak husband, ko?" Ya lumshe ido. "Ki duba yadda kike kinsha kyau, Ayshatu. Allah ya baki gayu da karsashi. I want tonight to be real. Between us. Ba saboda wani ba sai saboda ke.”
Ayshatu juyo daga gare shi, idonta na kallon taga.
"Muqaddam..." ta furta cikin ƙasa da murya. "Ka sani ba haka rayuwata take ba. Ba haka na saba ba."
Yazo daga bayanta, yashiga shafawa . “Amma ke ba irin sauran bane,Kin fi karfi fiye da yadda kike tunani. Kuma... kina jin kamar ni ma ina da wani iko a zuciyarki.”
Ta juyo, idonta cike da hawaye da fushi da rudani. “Ka san ina da miji. Wannan abin da muke yi... haramun ne.”
Ya matso, hannunsa a gefe. "Sai ki ce ba kya jin komai idan kina kusa dani? Ki kalli idona, Ayshatu, ki faɗi gaskiya."
Zuciyarta na kara bugawa da kowane kalma. Sai ta sunkuyar da kai, murya kamar tana ƙara fashewa “Ban san yadda zan iya jurewa ba. Amma na san cewa na riga na shiga cikin wani abu mai hadari.”
Ya kai hannu ya kama nata, a hankali. “To mu fada tare. Idan hadari ne, sai mu ƙetare tare. Amma ki daina gudu daga gaskiyar da zuciyarki ke faɗi.”
Ayshatu ta tsaya a gabansa, jikinta har yanzu yana rawa ba saboda tsoro ba, amma saboda wani sabon yanayi da take jin kanta tana ciki. Idanunta suka haura zuwa nesa,Yayi gaba kadan, hannunsa yana tafiya zuwa gefen fuskarta, yatsansa yana latsar gashinta da tausayi. “Idan ba kya son wannan, zan dakata yanzu,” ya furta da ƙasa da murya..
Shiru tayi shiru mai nauyi da ma’anasannan ta ɗaga hannunta ta kamo nashi. “Ka dade kana son na?” ta tambaya, muryarta na rawa
Ya girgiza kai. “Na dade ina jin ki, Ayshatu. Ba kawai so ba. Da wannan kalma, ya matso ya sumbaci goshinta, sannan hancinta, sannan labbanta. Ta saki numfashi mai nauyi, hannunta ya hau wuyansa.
Zuciyarsu biyu suna bugawa da sauti daya, hannayensu suna haduwa da ƙwarin gaske amma cike da tausayi. Ta furta cikin rauni, "Ka nuna min cewa wannan ba mafarki bane."
Baya wani jinkiri, ya ɗauke ta a hankali zuwa kan gadon dake gefen dakin. Babu wuce gona da iri. Komai yana tafiya da hankali da nutsuwa zuciyoyinsu biyu suna magana da juna, jikinsu yana tabbatar da soyayyar da kalmomi ba za su iya fassara ba.
Kiss ɗin da suka raba yana ɗauke da komai sha’awa, jin daɗi, da alkawari.
*****************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA SABA'IN DA DAYA
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Washegari da asuba, Ayshatu ta farka cikin nutsuwa, ta yi wanka da hadaddun spa oils da suka shaƙa ɗakin da kamshin lavender da vanilla blossom. Ba tare da ɓata lokaci ba, ta fice daga hotel ɗin cikin ƙamshi da class.
Tana shiga Villa, zuciyarta gaba ɗaya ta sauya. Kamar bidiyo, hotunan daren jiya da Alhaji Muqaddam suka ci gaba da dawo mata. Yadda yake kallonta da ido masu tsananin girmamawa da salo. Yadda hannunsa ya taɓa nata da sakon natsuwa mai daɗi da amincewa. Duk soyayyar As’ad, idan ta keɓe da Alhaji Muqaddam shi kaɗai ne a idonta.
BANGAREN AYSHATU
Zaune take a cikin ɗayan main living nata ɗakin da aka ƙawata da handmade Moroccan rugs, Versace gold side chairs, da Crystal centre table. A gaban ta akwai Apple MacBook Pro, wayarta ta Vertu limited edition, da kuma ƙaramar kwalbar Rose Dior perfume.Tana duba sabbin kayan luxury designers da take niyyar ordering daga Milan da Qatar bags, heels, da perfume na musamman.
Ɗaya daga cikin manyan chef dinta ta shigo cikin ladabi, hannunta ɗauke da Morning Tray Service Mocha tea,Light egg sauces,Warm croissant stuffed with cheese.
Nicole ta tsugunna da ladabi, tana cewa da muryar turanci mai taushi “Ma’am... oga has arrived, he’s now in his private suite.”
Ayshatu ta ɗaga kai, ta ɗan murmusa, amma bata ce komai ba. Ta karɓi tray ɗin tare da daddana wata ƙarama waya da take a kusa da kujerarta. Tana magana da ɗaya daga cikin personal chef dinta.
“Make something light for hub... thirty minutes, just fruits and detox. Thank you.”
Ta ajiye wayar. Ta ci abincinta da salon mace mai jin daɗin zaman duniya. Bayan kimanin mintuna 35, ta miƙe. Sai da ta shiga dressing walk-in closet, ta ɗauko silk bubu, mai launin champagne gold, sannan ta fesa Maison Francis Kurkdjian Baccarat Rouge 540.
Daga nan ta nufi sashen As’ad cikin nutsuwa da ladabi.
Yana zaune cikin Penthouse ɗinsa mai hawa biyu da ke tsakiyar Champs-Élysées. Lungu-lungun gidan cike suke da kayan alatu daga Versace rugs zuwa crystal chandeliers, hasken safiya yana ratsowa ta tagogin floor-to-ceiling glass, yana yawo a kan golden-trimmed dining table mai kujeru goma.
Yana danna MacBook Pro M4, yana waya da hannunsa ɗaya. Ayshatu ta shigo, fuskarta cike da murmushi mai tsada, tana sanye da laced luxury Bubu daga Elie Saab. Kamshin turaren Maison Francis Kurkdjian ya cika falon.
Da ya ganta, ya sauke murmushi irin murmushin attajirai da suka saba da komai. Itama ta mayar da martani da murmushin da ke ɓoye soyayya da sirri. Ya ajiye system ɗin, ya buɗe hannayensa da salo wata irin alamar "taho ki shige jikina" ƙarasowa kamar wata yarinya mai shagwaɓa, ta faɗa jikinsa.
"Habibie, you smell different today. Did you change your perfume?" ya tambayeta cikin murya mai laushi.Ta ɗan gigice, ta ce, “Friend dina tazo da wani sabon turare, na fesa kawai...”
Ya sumbaci baƙinta a hankali, yana fadin, “Still... It’s a smile different, Ayshatu. I hope you're okay.”
Dariya tayi cikin kwanciyar hankali, tace “Yes I am, Habibie. Let me bring your breakfast.”
Ta miƙe ta fita, ta dawo da light continental breakfast scrambled eggs, smoked salmon, orange juice da waffles. Ya ɗan ɗaci yace mata ya koshi, sannan suka zauna suna tattaunawa.
“New business project nake shirin farawa,” ta faɗa cikin salo.
Yayi dariya mai daɗin ji. “Bakida kuɗi ne?”
Ta saukar masa da wani French kiss a hankali, tana sosa ƙirjinsa. A ranta tace “Tunda baka da amfani da gabanka, meye amfani da wannan ƙaunar?” No habibie ai nayi amfani da black card dinka ma kawai inason signing ne. “ Bakida damuwa rabin ran habibie.”
Wayarsa ta ɗauki kira. Sai ya ce "You can come in.” “Wanene Habibie?” Ayshatu ta tambaya tana shirin yin tsokaci.
"Umar ne. Ya sauka tun jiya."
Ayshatu ta ce “A’a? Yau babban yaya ne a kasar? Mashaa Allah! Tare suke da Nawal ne?” "A’a, Nawal tana can Sorbonne, tana gamawa da wani short course. Umar ya zo ne shi kaɗai."
Bai gama rufe baki ba, sai Ayshatu ta dauki wayarta, ta buɗe WhatsApp, ta rubuta wa Alhaji Muqaddam "I'm missing you, dear."
Shi kuma ya mayar da saƙo "Nima bacci na kasa. Juyi kawai nake. You're so wet, my baby." Ta lumshe ido cike da jin daɗin sakon. Sirrinta. Sirrin zuciyarta. Sai ta goge saƙon ta aje wayar.
Da Umar ya shigo babban ɗan As’ad babban mutum, nagari, mai hankali. Yana shigowa, Ayshatu ta tashi cike da fara’a.
“Papa! Yau kai ne a gidan? Ina son zuwa tun watan da ya wuce amma dad ɗinku ya hana ni.” “Muna jiran ki, Maahma,” Umar ya ce, yana kallonta da kulawa. Sai ya dubeta sosai, ya ce “Jiya kamar naga ke a wani hotel?” Ayshatu ta ɗan zaro ido. "Ni kuma? A’a, jiya ko gida ban fita ba. Maybe someone that looks like me." Umar ya danyi murmushi. Sai ya kalli scarf dinta shidai kamar shine ya gani a hotel ɗin jiya. Da sauri ta turawa Muqaddam saƙo “Please, kasamar mana gida, banson hotel.”
“No problem baby. Zakizo anjima?”
“No, yananan fa, sai gobe zai tafi... then zakaganni.”
Ayshatu ta ce "Bari nakawo maka breakfast."
Ta fice. Umar ya zauna kusa da mahaifinsa As’ad. Kallon dake tsakanin su ba za ka ce uba da ɗa bane sai ka ce abokan tarayya a empire. "Good morning Dad," Umar ya faɗa cikin girmamawa. As’ad ya shafa kansa yana cewa "Just 5 months da ban ganka ba, ka dawo kamar wani zaki? ka ɗauke min 'ya!"
Suka yi dariya. Sai Umar ya ce "Nazo ne game da maganar wanda Nawal ke so. Zasu turo Monday." "Allah yasa alkhairi. Na bincika komai the boy’s profile is clean. InshaAllah gobe zamu koma Naija." Umar ya ɗan ƙame, ya ce "Dad... ina so muyi magana... game da lafiyarka. Nasan kayi magani, ka ga likita, but... Ayshatu are you really okay with her?"
As’ad ya saki wani murmushi mai zurfi.
"Ayshatu ce mace mafi girmamawa da na taɓa aura. Tana sona yadda nake, ta karɓe ni yadda nake. She's my pride." Umar ya ce "But Dad, I think" "Enough, Umar," As’ad ya katseshi. "I'm okay with her, and she's okay with me. That's what matters."
Ayshatu na shiga dakinta, ta juya ta sa key da sauri, ta tabbatar da cewa babu wanda zai iya turo ƙofar. Ta leƙa gefe, ta kalli bangon dakin "Ko'ina akwai camera .. sai toilet."
Sai ta janyo wayarta, ta shige toilet cikin natsuwa, ta zauna akan tile, sai ta kira Alhaji Muqaddam a video call.
Da ya ɗaga, fuskar sa ta bayyana cikin haske, yana kwance, yana kallonta kai tsaye. "Baby... I’m missing you."
"Nima," in ji Ayshatu cikin rauni da sha’awa. "Wallahi nayi calling ne saboda na kasa hakuri akanka."
"Ina nan kwance tunda safe, amma ban iya komai ba... Sai tunaninki haka abokina ya more da macce irinki?. Wallahi I just need you now.”
Ayshatu ta sunkuyar da kai. Sai ta ce da muryar da ta cika da buƙata "Muqaddam... ban son mu kara haduwa a hotel ba. Ka samar mana da wani wuri na sirri...Private place."
Ya ce da sauri "Ai baki da damuwa. Kicire kayanki gaba daya.”
Sai ya furta "Budemun rigarki, naga….. sun cika tunani na tun jiya." Ayshatu ta dan yi jim.
"Ba zan iya ba... ka bar ni haka." "Haba baby na... kin san ni da ke Bama haka, Kinga yanzu haka... na kasa barci, na kasa cin abinci. Gani fa…" .
Ayshatu ta cika da rawar jiki. Duk jiki ya soma tafasa, tunani ya daina tsayawa a daya wuri. Sai ta rage rigarta... sannan ta cireta gaba ɗaya. Breast sun fito, farare, jikin ta ɗan rawa. Ta daga wayar, tana nuna jikinta duka.
"Ka ganni yanzu?" "Na ganki. Kuma gobe ina jiranki...”
ANYA WANNAN DAƁIA DA AYSHATU TAKEYI ZATQ ƘAITA GA DACEWA??ALLAH KARABAMU DA CIN AMANA DA YAUDARA DA RASHIN TSORON ALLAH
*****************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA SABA'IN DA BIYU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Wata ni’ima ce da dare ke saukowa cikin sanyin iska. As’ad na tsaye a gaban window, yana kallon hasken titi da yake sauka akan motarsa ta Maybach.
"Habibie..." muryarta ta fito da laushi, kamar yanda zuciyarta ke rauni.
Ya juya a hankali, yana kallonta da idanun da ke ɗauke da wani irin so soyayyar da ba a yawan samu a tsakanin mutane. Ya zo kusa da ita ya durƙusa, ya dafa cinyarta cikin tsantsar kulawa.
"Zan tafi Nigeria gobe. Anshirya komai," ya faɗa da natsuwa.
Cikin rawar murya tace, "Ni kam banaso ka tafi... Duk lokacin da kake tafiya kamar za a yage wani ɓangare na zuciyata." Hawaye ya gangaro daga cikin idanunta masu ƙyalli.
Ya share hawayenta da ɗan yatsansa, sannan ya kamo hannunta cikin nasa. "Ayshatu, rayuwata babu armashi idan ba ke. Amma akwai abubuwan da dole sai na yi domin mu, domin rayuwarmu."
Tayi shiru, amma hawaye na ci gaba da zuba. Ya jawota jikinsa sosai, yana shafa bayanta cikin taushin soyayya. "Ko tafiya nayi, karki taɓa jin nesa ya raba ni dake. Kin mallake zuciyata gaba ɗaya, Aysha."
Tana jin daɗin maganganunsa, amma har yanzu zuciyarta na ƙi sakar sa. Sai ya zare murfin wata ƙaramar golden box daga aljihunsa, ya buɗe ya zaro zoben Cartier Diamond Band ya sa mata a yatsa.
“Ina son ki fiye da yadda zan iya faɗa, ki riƙe ni da addu’a... Zan dawo da wuri.”
Ta saki kuka kamar ƙaramar yarinya, ya tura kanta bisa ƙirjinsa yana rarrashi. Daga nan suka shafe daren cikin soyayya mai cike da natsuwa da salo.
WASHEGARI
As’ad na cikin custom-made suit na Louis Vuitton, yana shirin fita.Ayshatu na zaune gefensa cikin wata hadaddiyar satin robe mai kyau idanunta cike da hawaye.
“Please Habibie… Don’t go yet.” Ta faɗa da wata murya mai sanyi, tana riƙe da hannunsa tamkar wani jariri mai buƙatar kulawa.
As’ad ya kalleta cikin nutsuwa, ya shafa kumatunta da yatsansa mai santsi, yana sauke numfashi.
“Ayshatu… ba zan taɓa barinki da zuciya ɗaya ba. Amma Naija na kira... Umar na bukata a wajen saranar Nawal. Kuma akwai wasu business meetings da zan halarta. Zan dawo cikin sati biyu kacal.”
Ayshatu ta jingina kanta a ƙirjinsa, tana sumbatar wuyansa. “Na saba da ɗumin jikinka, Habibie. Wannan gidan ba daɗi idan baka nan.”
As’ad ya janyota ya ɗora kanta a kirjinsa yana kallon hasken Eiffel Tower daga tagar gilashi mai fadi. Ya ce cikin wata irin murya mai motsa rai, “I love you Ayshatu... ba duniya zata raba ni dake ba. Zaki zama sarauniyar zuciyata, ko menene. And I’ll always come back home… to you.”
Ta ɗan murmusa tana sosa gefen fuskarsa da yatsanta, amma hawaye na sauka. “Idan ka tafi, waye zai dinga sumbatar gashina? Waye zai kira ni My Queen da gaske?”
Sai ya ɗan turo da hancinsa yana dariya kadan, “Wani zai kira ki Baby, wani kuma ya sayar miki da expensive perfumes amma ni zan kira ki My World.”
Sun rungume juna cike da ƙauna kafin ya fice, yana shafa kanta. “Take care of the house. Don’t forget to drink your chamomile tea before bed.”
Ayshatu ta bishi har bakin ƙofa, Ba tace komai ba, kawai ta tsaya tana kallonsa, idanunta cike da hawaye.
Yana buɗe ƙofa, ya sake juyowa ya dawo ya rungumeta, yana sumbatar goshinta. "Ki kula da kanki."
Sai da motarsa ta ɓace daga gani kafin Ayshatu ta saki ajiyar zuciya ta saka sai kawai ta fashe da dariya tana faɗin, “Sannu da tafiya, Habibien duniya. Amma Alhaji Muqaddam ya fi ka komai.. Tana shiga daki, ta canza kaya, ta nufi wardrobe ɗinta ta zaro Goyard bag guda biyu da kuma Chanel tote ta cika da kayan da zata bukata.
Ta ɗauki wayarta, ta kira Muqaddam, tana murmushi.
“Baby, I’m coming over. I miss your scent already.”
Muqaddam ya amsa da “The house is yours. Gidan yana jiranki.”
A cikin mintuna talatin, wani Mercedes Benz S-Class mai number plate “M-QDM 1” ya zo ya ɗauketa. Driver nata ya bude mata kofa, tayi settling cikin leather seat mai sanyi da kamshin Italian interior.
Ayshatu ta fice daga gidan As’ad cikin halin da ko tsuntsu bai ji, balle mutum. Amma zuciyarta ta cika da sha’awar wani… yayin da wanda ya fi ƙaunarta ke jiranta a Naija, cikin amana da soyayya. Alhaji Muqaddam yana falo, cikin dogon wando da riga mai kyan gaske, yana karanta wani kasuwanci a system. Ganin Ayshatu sai ya miƙe yana fadin:
"Baby... You came."
Tana ƙarasowa ta faɗs jikinsa kamar wata marainiya da aka manta da ita. "I missed you," ta ce da sanyi a muryarta.
"Ina nan yanzu. And you won’t have to be lonely again," ya faɗa yana ja da ita har cikin Luxury Living Room, inda komai ke sheƙi da tsari na manyan masu kudi.
********
Washegari da safe, garin Paris ya kasance cikin sanyin hasken safiya da iska mai ɗauke da ƙamshin barin hunturu. A wajen da ba kowa ke zuwa ba Private Terminal na Bourget Airport wani jet mai launin white pearl da fari ya tsaya yana jiransu.
As’ad na sanye da farin Zegna Agnona senator, da takalman Louis Vuitton masu ƙyalli. Hannunsa ɗauke da iPad ɗin business schedule, sai agogon Cartier da ke haskawa. Umar, ɗansa, yana bayansa cikin black Dolce & Gabbana suit sharp and commanding.
Suna tahowa cikin natsuwa, matakin kowane ƙafarsu yana nuna power. Ma’aikatan filin jirgin da ke kula da VIP suna tsaye daga gefe suna rusunawa da gaisuwa “Welcome Your Excellency, Mr. As’ad Babangida. Your jet is ready.”
Yayi murmushin manyan mutane, yana girgiza kai cikin salo. Umar ya kalle shi yace “Dad, even after all these years, I still get chills seeing how much respect you command.”
“Zuciyar mai nutsuwa ba ta ƙasƙantar da kai, Umar,” As’ad ya faɗa, yana taka gangar tafiya zuwa jirginsu.
Wurin zama cikin jirgin ya kasance mai alfarma ce da kowa ke mafarkinta cream leather seats, gold plated trims, da furen blue hydrangeas masu ƙamshi. Ana shan espresso daga Versace gold mugs, da nutsar da kansu a cikin taskar business updates da Umar ya shirya.
As’ad ya ɗan danna remote, plasma screen ta kunna, showing the flight path to Nigeria. Yace "Gobe zamu isa fadar Sarki kai tsaye. Kayi magana da Palace manager din?" "Yes dad, every royal protocol is set. Sarki yana jiranmu kamar yadda ya saba. Kai fa har yanzu kaine fitilar gidan nan.”
As’ad ya lumshe ido, yana maimaita zikirin da ya saba kafin tafiya. Jirgin ya ɗaga.
ABUJA PRIVATE AIRPORT TERMINAL
Saukar jirgin ya kasance cikin tsari da ƙima. Gidan jirgin masu kudi na Abuja an rufe shi gaba ɗaya don karɓar As’ad Babangida. Black Rolls Royce Cullinan, Bentley Mulsanne, da Maybach S600 Guard suka jeru a gaban red carpet.
Royal drummers na masarauta suna busa kaɗe-kaɗen masu daraja, yan tsakar gida na Sarauta suna tsaye cikin rigunan masarauta da rawani. Gaban kowanne motar akwai furen farin lilies da tambarin gidan sarauta.
Sarki ya aiko da babban Dan Majen Fada domin ya jagoranci tarba. “Fadar Sarki tana farin ciki da dawowarku, Ranku ya daɗe. Masarauta ta buɗe ƙofa gareku.”
Umar ya kalli mahaifinsa, yayi murmushi yace
"Dad, this is home. You’re a born royal, no matter how far you go."
Motar As’ad ta fice daga tashar jirgin, tana bi ta cikin tsararren convoy. Titi ya kasance a rufe, 'yan sanda da guards na Fadar Sarki na yi musu rakiya. Mutane na gefen hanya na rusunawa suna gaisuwa, wasu na ɗaukar hotuna daga nesa.
Wanda bai san ko waye As’ad ba, daga wannan tarba sai ya fahimci ba kowane attajiri ne yake da alaka da masarauta ba.
Gidan Sarki ya kasance ƙatuwar fada da tarihi. Babban kofar shiga ana yaye ta da rubutun Larabci, ƙasa na murjani, sannan tagogi na stained glass. Da zarar suka shiga "Masarauta ta buɗe hannunta ga ɗanta. Barka da zuwa, Alhaji As’ad Babangida ɗan sarki kuma Attajirin kasarmu,” cewar Sarki, yana miƙa hannu da murmushi mai cike da ƙwazo da soyayya.
“Godiya nake, ya Mai Martaba. Wannan gida ne na alfarma da albarka.”
As’ad ya rusuna da ƙwantar da murya irin ta masu hali. Daga nesa, mahaifinsa ya kalli Umar yace: “ Muna maraba da umaru Farouk Jikan Babangida” Umar yazo yarissina yana masa gaisuwa ta girmamawa “Wannan ɗa ne na daraja, wanda kowa ke alfahari da shi.” Sarki yafaɗa yana murmushi.
********
A cikin ɗaki mai yalwa da tsari irin na sarauta, Haneefa tana kwance saman lafiyayyen katifarta, zuciyarta cike da shiru. Duk da zaman sarauta, amma rayuwarta na cike da sake-saken tunani, musamman tun bayan rabuwarta da As’ad.
Tana cikin wannan tunanin ne sai aka buga ƙofar da karfi, ƙofar ta buɗe. Wata daga cikin ‘yan munafurcin masarauta, mai suna Gwaggo Lanti, ta turo kai cikin ɗakin tana sanye da alkyabba mai sheƙi “Haneefa… Ai wallahi Allah ya ƙaddara! Kin ga tsohon mijinki As’ad? Ashe dama mace zata rasa rabo irin naki har ta bar namiji irin As’ad?”
Ta tsaya tana kallon Haneefa da murmushi mai cike da ƙyashi, sannan ta cigaba “Gashi can yazo da ɗansa Umar ɗan Dubai fa! Yasha gayu, ga kyau! Ni dai gaskiya nayi bakin ciki da rabuwarku, amma yanzu kin ci amanar kanki da kanki.”
Kafin Haneefa ta iya cewa komai, sai Zainu, yayarta ta shigo cikin ɗakin tana dafe da hannu “Ai kema kinsan Haneefa ta cuci kanta. A yanzu da zata ci gaba da gina rayuwa da As’ad sai ta zabi ta bige da faɗa, da gardama, sai gata ta rasa komai. Ke kika lalata rayuwarki da hannunki.”
Haneefa ta ɗaga ido tana kallon su, ba tare da tace komai ba. Tayi shiru amma idanunta sun cika da hawaye da bata bari sun zubo ba.
Ta daure murmushinta cikin haƙuri, ta ce a hankali “Zainu… Ina kika ganshi?”
Zainu ta tabe baki, ta ce “Ina? Ashe ba kuji ba? Yanzu yanzu ya shiga fada tare da Umar. Na gansu da idona. Kuma ba karya zance ba… duk wani abun da kika rasa na rayuwa yana hannunsa yanzu.”
Cikin sauri Haneefa ta miƙe. Zuciyarta ta buga ba dan wata sha’awa ba, sai dan wani kishi na zuciya, wani murɗi na cikin rai.
Ta sa gyale a kai, ba tare da ta saurari ƙarin zuga daga Zainu da Gwaggo Lanti ba, sai ta fice da sauri, takalmin ta na sheƙi da karan ƙasa.Tana ficewa suka bita da ido.
Gwaggo Lanti tace“To ai fa ba da an kalli baya ake gina gobe ba. Amma dai muryarta na nuna har yanzu tana da ruwa a zuciya.”
Zainu ta murmusa “Ko kuma da gaske take so ta dawo, sai dai... yanzu wallahi yafi karfinta.”
*****************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA SABA'IN DA UKU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Yau garin mun tashi da hadari.
Gajimare ya turnike sararin sama, iska na kaɗawa da ƙarfi Abin ya ƙara cusa damuwa cikin zuciyata.
Kusan kwana uku kenan Bashari bai dawo ba.
Kafin ya tafi, ya ce min akwai wani 'aiki' da zai yi. Amma tafiyarsa ta zamar min wata 'yar walwala a zuciya. Domin wallahi... tsoron Bashari nake ji. Bai fi kwanaki biyu ba cikin dare sai ya ɗauki makami ya fita kamar ɗan fashi. Idan ya dawo kuma yayi shaye-shayensa,
Idan ya ɗan sha, sai ya hau ni da duka kamar jakarsa!
Zan kasance ina kuka, ina kukan da ba ya tsayawa, amma sai ya ɗora. Ba ni da ƙarfi, ba ni da gata. Tun da farko ban gane ba, har sai da Babah ta ce min “Ke yarinya, idan kika ji Bashari ya dawo cikin dare, to ki ruga, ki buya! Wallahi ba a hayyacinsa yake ba!”
Danaji karar ƙafarsa nake guduwa. Har na zama kamar berar gidan da ke tserewa don ta rayu. Na daina sanin kwanciyar hankali. Rayuwa na... ta zama kunci da fargaba.Idan dare yayi, ba zan iya bacci ba. Idan rana ta fito, zuciyata na bugawa. Ina tsoron kada na ga Bashari ya shigowa.
A nan kauye babu wanda zai ce masa komai. Kowa na tsoronsa. Ɗan daba ne, kuma ba kowa ne ke son jefa kansa cikin rikici da shi ba. Koda yake yana da mahaifi da uwa, sai ka rantse bai da wata alaka da su. Gidansu baya shiga. Iyaye na kauyen nan ma ba su so ‘ya’yansu suyi hulɗa da shi.
Kusan sati guda kenan ba mu samun huta. Allah ya taimake ni da wata ƙaramar torchlight da Bashari ya sayo min, ita nake amfani da ita wajen haska gida idan dare yayi. Sai dai duk da torchlight da system da wayata da na samu daga gida, babu wutar lantarki ko ɗigo. Gidan ya dinga ɗim, na zauna cikin duhu ina haska kaina kamar wata baƙuwar bakar fitila.
Ganin hadari ya haɗu da iska ke kadawa sai na kwashi shanyar kayana da na ɗora a jikin ƙugiya, Kurfuto da na dafa abincj kuma na ajiye su cikin kitchen , ina gyarawa, sai na hango Habu jikan Babah yana kokarin shigowa cikin gidan.
Habu ɗan ƙarami ne, yana da shekara goma sha ɗaya, Shi ke taimaka min yanzu idan ina buƙatar ɗan taimako a gida. Babarsa da farko bata yarda na riƙe shi ba saboda tsoron Bashari. Sai dai yaron mai kwadayi ne, tun da na fara bashi abinci sau ɗaya, sai ya fara zuwa kullum. Ni kuma ina tausaya masa, saboda kullum kamar bai ci komai ba.
A yau ma, yana shigowa cikin kitchen ɗin sai ya tsaya yana kallona. Na kalle shi na ce,
“Habu, ga abincinka nan. Ganin hadari ya fara haɗuwa, ka ɗauka ka wuce gida kafin ruwa ya fara sauka.”
Sai ya sosa ƙeya, ya ce da fara’a,
“Tohm, nagode Antin Birni. Allah ya saka da alheri.”
Ya ɗauki abincin cikin farinciki, sannan ya juya da sauri ya fice, yana ɗan rera waka kamar yaron da aka bai wa gwal.
Na bishi da kallo, zuciyata cike da tausayi da kauna. Yaron nan ya fi mutane da yawa tausayi da ƙauna, duk da karancin shekarunsa.