Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 29
Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 29: Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 29. Sai iska ta kara tasowa. Wani guguwa ya kwashe ƙofofin kitchen ɗin,…
4,488 words
Sai iska ta kara tasowa. Wani guguwa ya kwashe ƙofofin kitchen ɗin, ina tashi zan rufe kofofi sai wani faɗuwa naji a bayana. Torchlight dina ya faɗi ƙasa ya mutu. Na sunkuya na ɗaga shi, na busa. Na kunna shi a hankali yana ɗan haske kadan.
Nace cikin kaina, "Allah dai ka kare ni daga dukkan sharri a gidan nan."
Daga nan na koma ɗaki. Na zauna kan tabarma da aka shimfiɗa tun safe. Wato duk bayanin da zan muku game da Bashari, wallahi bazaku taɓa fahimtarsa ba ko kaɗan. Sai dai in fa kun ganshi da idonku. Wannan mutumin ko in ce, wannan halittar ba wai ɗan daba bane kai tsaye, cikakken aljani ne cikin mutane. Idan nace muku babu wata makociya da ke shigomun, kuna iya ɗauka kamar ƙarya nake yi, ko? To wallahi da gaske nake yi saboda kowa a kauyen nan yana tsoronsa, balle ni da nake da aure da shi.
Babah ce kaɗai ke shigowa wajena ita ma ba yanda take so take shigowa ba, dan har ita ma ba a kyale ta.
Da dare yayi, bayan sallar isha’i, na zauna ina lazumi a tsakar ɗaki. Na sanya hijjabina, na jingina a bango, ina karanta “Hasbunallahu wa ni’imal wakil” kamar yadda Babah ta koya min. Ta ce idan ina karanta hakan, komai tsorona zai ragu. Kuma Allah zai tsare ni.
Kamar kullum, sai nayi kwanciyata kan kujerar tsakar ɗakin. Ina kokarin tashi na rufe ƙofar ɗaki, kawai naji an banko ƙofa da ƙarfi! Ji nayi kamar zuciyata ta tsaya! A firgice na mike, nayi kokarin guduwa zuwa ɗaki kawai sai na hango shi...
Kamar an cilloshi. Fuskar nan tasa cike da yanka-yanka, wasu wurare har sun kumbura. Jikinsa duk ya baci da jini. Wata kalar wari ne mai cike da tsami da shan jini ya doki hancina. Ina kallonsa kamar wanda ba mutum bane. Ba a cikin hayyacinsa yake ba.
Na sauke ajiyar zuciya, na yi saurin ja baya, amma ya riga ni ya fizgo hijjabina ya rufeni da duka. Ba wata tambaya, ba wata magana duka kawai! “Ke karuwa ce! Yar iska ce! Ke! Dama haka kike? Kin boye cikin shege a cikinki!” haka yake yimin ihu yana caccaka mini duka, yana tura ni bango da ƙarfi kamar jaka.
Na hau ihu, "Wallahi ban aikata komai ba!" amma wannan ba zai hana shi ci gaba da wulakanta ni ba.
Ya kamo ƙuguna, ya buge ni da bango, sai ya ce: “Ni ba dan iska bane! Amma ke sai yanzu nasan ke karuwa ce!”
Duk da kokarina na guduwa, babu hanyar tserewa. Kawai sai muka ji an banko ƙofar gida da ƙarfi. Wani saurayi ya shigo da gudu Aliyu Awilo, babban ɗan daban gari, wanda shi da Bashari suke tafe.
Ina zaune a ƙasa, jiki a sarke, sai kawai na ji shi yana fadin
“Haba oga! Haba aljanin dare! Wannan maccen ka ke bugawa haka?!”
Kafin Bashari ya ankara, Aliyu ya zaro wata allura daga aljihunsa ya soka masa a hannun hagu. Bashari yayi wani irin ƙara kamar zaki, sai kuma ya fara dushewa a hankali kamar bishiyar da ruwa ya tsinke. Ya rufta a ƙasa yana nishi kamar mara lafiya, yana karyar baki har bacci ya ɗaukesa.
Ina zaune gefen bango, jiki a sarke, hannu na rawa. Na kasa motsi, zuciyata na bugawa kamar za ta fashe. Sai Babah ta shigo cikin tashin hankali tana sanye da mayafi, ta hango ni a ƙasa tana fadin.
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Ya ubangiji! Wannan mutumin wata rana zai kasheki wallahi! Ramlah ki tashi mu tafi!”
Ta karaso ta tsalleke jikin Bashari, ta rungume ni kamar yarta . Amma ni nakasa jikina yayi sanyi, hawaye na gangarowa
Babah ta girgiza ni tana kuka
“Allah yasa bai bugeki da wuya ba Ramlah... Allah yasa...”
Na ƙara rungume ta. Na rusa kuka kamar ƙaramin yaro. A cikin zuciyata ina fadin
“Ya Allah, me nayi da na cancanci irin wannan azabar?”
*****************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA SABA'IN DA HUDU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Baccin ya ɗaukeni ne cikin ciwo da gajiya, amma da safe na tashi da duka jikina yana rawa da zafin zazzabi. Bashari kuwa ban gan shi ba a gidan. Da ƙyar nayi sallar asuba, na dora farar shinkafa ba tare da yaji ba kawai Maggi na sa domin babu ƙarfin da zan iya dafa komai mai nauyi.
Ina jin bude ƙofa da ƙarfin gaske, sai na ruga da gudu na shige ɗaki. Ashe Bashari ne, sai yasa dariya yana cewa,
“Wato na zama abun tsoro gareki ko?”
Kafin na ma ce uffan, naji Aliyu ya karɓa da magana mai zafi “Ai da gaskiyarta da ta zauna kana shigowa ka halakata da duka a wofi” Bashari ya saki wata ballagazar dariya yana faɗin “Kai Aliyu, ka daina shirme! Kana jin abin da ta ce? Ta ce fa Ramlah cikakkiyar karuwace ce mai bin maza. Kada na sake nayi wasa da ita! Gaskiyar Mumy ce, zan koya mata hankali...”
Cike da firgici da baƙin ciki, na dafe kirjina ina furta “Innalillahi... Mumy?”
Idanuwana suka cika da hawaye, zuciyata ta shiga wani irin radadi da ya fi ƙarfin jiki. Wane irin sharri ne wannan? Nayi auren ma bazata kyaleni ba yanzu kuma sharrin karuwanci tayimun.
Daga can naji muryar Aliyu awilo yana kwarara wa Bashari ihu yana fadin “Kai Oga! Kana ganin wannan sharrin gaskiya ne? Ka manta yadda kishiyar Babanka ta yaudare ka a baya? Ka manta yadda ta jefa ka cikin halaka? Wannan mumy take ko wa wallahi karya takeyi shegiya munafukar tsuhuwa”
“Kai ka kalli Ramlah tayima kama da ƴan bariki? Na tabbatar maka idan yar bariki ci yo tabbas wallahi saita gudu lokacin da akace za'a aura maka ita amma ka kalli yadda tayi biyayya kuma gana ganin yar bariki haka? Kasan irin yan iskan matan nan fa idan ka rasa da hannu ka rasa da kafa! Allah ya baka wannan yarinyar mai kamun kai, amma ka tsaya kana sauraron gulmar tsohuwar guzuma!”
Sai naji Bashari yayi shiru, daga nan sai yace
“Kaga fa Aliyu, wannan tsohuwar guzuma zata canza min kwakwalwa ne. Amma ai nasan irin matan bariki, basa jin magana balle ita wannan yarinyar ƴar aljanna.”
Aliyu ya goge hanci da bayansa yana cewa “To sai ka gama bugun kwakwalwarka ne? Dan Allah Oga, wannan yarinyar fa ta amince dakai lokacin da duniya gaba ɗaya ke gudunka. Ta tsaya maka lokacin da kowa ya kaurace maka. Wlh Ramlah ba mace bace da za’a watsar da ita kamar pepsi a titi! Nagaya maka ka riketa hannu bibbiyu wallahi. Ka bawa makiya mamaki Oga, ka riƙe ta da hannu biyu. Ka share sharri, ka goge abin da ya baci. Wallahi matarka irin 'yan Aljanna ce!”
A gefe na, zuciyata na karɓar kalmomin Aliyu da wani sanyi. Duk da shi dan daba ne, yana iya fadar gaskiya cikin dukan irin salon titin da ya saba. Amma Bashari, sai na kasa gane inda zuciyarsa ke karkata.
Na saka ƙeya daga daki ina sauraron su cike da tausayi. Shin kalmomin Aliyu zasu canza tunanin Bashari? Ko kuwa sharri da gulmar Mumy sun riga sun yi zurfi a zuciyarsa?
Na saka kai a ƙeya ina leƙen su daga kofar daki. Zuciyata na bugawa kamar ana harbi da sandar tsinke. Na kasa gane me nake ji tsoro ne? Mamaki? Ko wani sabon abu da har yanzu ban saba jin sa ba?
“Wallahi Oga, idan ka bar wannan yarinyar ta fita daga rayuwarka, sai dai ka rasa nutsuwa har tsawon rayuwarka.” Cewar Aliyu, yana mai kaɗa ƙafafunsa cikin sandar girman kai irin ta 'yan daba.
“Kai ka duba fa! Wata rana zaka dawo daga sararka ko nace shaye shaye ka tarar da dakin ka na ƙamshi, ta dafa maka abinci da tufafi a wanke. Waye ya yi maka haka a rayuwarka? Sai fa Ramlah.”
Bashari ya ƙwanta a kasan gurin, ya ciro sigari daga aljihunsa ya cizge. Ya ɗauko lighter ya kunna, sai ƙamshin hayaƙi ya cika filin gurin “Dama kasan me? Rayuwa tana da rikice-rikice. Amma gaskiya na fara gajiya da wannan sharri. Kullum sai Mumy ta kirani ta zagi yarinyar nan me tatare mata ne.”
Aliyu ya yi dariya yana cewa,
“Haka ake so! Wannan ne Bashari ɗan titi! Kada wani ya juya maka kwakwalwa kamar waina a tukunyar gawayi.”
Ya matso kusa da shi yana daga hannu
“Oga, ka dawo nefa! Wannan shine gangster Bashari na gaske. Wanda idan ya so mace, to sai dai Allah ya ɗauki rayuwarta.”
Na girgiza kai da hawaye a idona. Ina sauraron su, ina jin yadda su ke magana da salo irin na titi da layin masu shaye-shaye, amma duk da haka kalmomin Aliyu sun taɓa zuciyata.
Sai na ji muryar Bashari, a hankali, kamar mai tunani.
“Zan kirata... In ta fito, zan ce mata... Tayi hakuri ko?.”
Ya tashi daga kasa ya nufo ƙofar dakina. Cikin rawar jiki na ja hijabi, na share fuska, na haɗiye kukana Kafin na gama gyarawa, sai na ji dukan ƙofa da faɗin
“Ramlah... Ki fito mana. Kin ji?”
Bansan yadda na iya tashi ba. Bansan yadda ƙafafuna suka ɗauke ni zuwa ƙofar ba. Amma na buɗe... Na leƙo... Na haɗa ido da shi.
Wannan idon nasa da ke yawan yawo da fushi da shegen girman kai, yau ya tsaya cik da nutsuwa. Sai na tsinkayo kamshin hayaƙin sigari a jikinsa, da kayansa masu datti da da bai canza ba tun daren jiya.
“Na ce... ki fito, ki zauna... ina da magana dake.”
Na yi shiru. Sai na ɗan matsa gefe, na zauna a bakin kujerar falo. Aliyu ya kama gefe, yana buga ƙafa kamar mawaƙi a titi. Shi dai duk ya mayar da hankalinsa ga danna waya.
“Ramlah...” Bashari ya fara da sautin da ban taɓa jin sa da irin wannan sanyi ba. “kiyi hakuri bazan kuma dukanki ba inshaa Allahu.”
Na ɗago kai na kallesa. Kamar zuciyata ta tsaya. Wannan kalma daya, ita ce mafarkin duk wata mace da aka cuta da sunan aure.
“Wlh bansan ya akayi na yarda da gulmar Mumy ba. Ashe sharri take miki ta aura miki ni dan taga ta cuta miki.” Ya dafe kansa da hannuwansa biyu, yana ƙara cewa
Aliyu ya tabe baki yana cewa
“Kai wannan gaskiyar ce Oga. Nace maka fa wannan yarinyar tana da class, tana da nutsuwa. Kana ganinta kasan batayi kala da mazan titi ba. To wanne irin karuwa ce ne da zata hana kanta fita?”
Bashari ya juya gare ni, ya ce
“Ramlah, na daina sauraron matar nan kuma zan bata mamaki wallahi.”
“Na gode da hakurin ki.” Ya ce yana lumshe ido. “Inason ki koya min yadda ake zama da mace. Inason ki koyar da zuciyata zaman aure.”
Aliyu ya dara yana tafa hannu
“Ayyahh Oga! Wallahi kayi soyayya irin ta 'yan layi! Wannan shine Bashari gangster ɗan daba da zuciya mai laushi!”
Sai duk suka yi dariya. Yana tsaka da tattaunawa da ni da wani irin salo mai taushi da na kasa fahimta ko gaskiya ce ko wata hanya ce ta sako ni cikin dabara, sai wayar Aliyu ta fara kara da ƙarfi. Ya zaro wayar daga aljihu ya danna answer, sai naji yana faɗin
“Toh Chief! Ina nan zan zo yanzu... Eh… wlh akwai babban aiki yau... Kada kowa ya sha komai, kada kowa ya matsa... zan zo da wuri!”
Bai ce komai ba, sai ya kalli Bashari da murmushin dabara yana faɗin
“Oga... sai anjima. Akwai mission ne, babban aiki... kada ka fasa abunda muka fara.”
Bashari ya gyara zamansa yana dariya irin ta 'yan daba, yace
“Kai dai ka je, idan matsala ta taso sai na kira ka.”
Aliyu ya fita da sauri, yana buga takalmansa da ƙasa kamar wanda ke fita don fadan titi.
Ni kuma na zauna shiru ina bin duka yanayin da kallo. Zuciyata har yanzu ba ta gama saita kanta ba. Ko kalmar “kiyi hakuri” da Bashari ya faɗa, ba ta gama samun izinin zama a zuciyata ba. Na kasa gane, shin gaskiya ne ko wata sabon dabara ce?
Cikin wannan tunanin, sai na ji karan kunna sigari. Na ɗago kai a hankali, sai na ganshi ya haɗe gira yana zuka hayaƙi da salo, yana saukewa cikin iska kamar wanda yake cikin club. Sai na zame daga kujerar, na mike a hankali na shige ɗaki.
Wallahi tsoronsa nake ji. Wani irin mutum ne da ba za ka iya hasashen yadda zai sauya halinsa cikin daƙiƙa guda ba?
Na zauna a gefen gado ina kallon ƙasa, amma sai kawai naji motsin takalmi... kafin na ɗago kai, har ya tsaya a gabana. Idanuwansa sun cika da wani irin haske mai ban tsoro.
Sai kawai ya kwantar da murya yana wani dariya da nake jin tamkar ana tsage dutse a kunne na
“Yar kwalisata... Haka zakiyi ki barni ni kadai? Ai na baki hakuri ko baki hakura ba...”
*****************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA SABA'IN DA BIYAR
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Cikin dare na farka jin wani irin nishi yana karade gidan, kamar numfashin mutum mai fama da zafi ko radadi. Cikin firgici na tashi da sauri, zuciyata na bugawa da ƙarfi. Na fito daga ɗaki ba tare da mayafi ba na manta da komai sai kawai na fita.
A can gefen rijiya na hango Bashari kwance a kasa, hannunsa yana fidda jini sosai, har da kansa ma ana malala jini daga gefensa. Na zare idanu, numfashina ya ƙi daidaituwa. Na faɗi da ƙarfi, "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!" Na nufesa aguje cikin tsananin firgici da razana.
Duk da tsorona, hankalina ya gaza barin na tsaya gefe. Na cire ƙwallin kaina na shiga nannade masa hannun, na matse inda jinin ke fitowa. Kuka kawai nake kamar wacce akayi wa mutuwa.
Shi kuwa... sai yayi murmushi. Murmushi mai ciwo, mai wuce zuciya. Yace da wata murya da ta kada zuciyata,
"Yar kwalisa... ki dakko mun ruwa kinji?"
Sai kawai na gyada kai da hanzari, na nufi ɗaki na dauko masa ruwa cikin kwano. Na dawo, har lokacin hawaye na zuba a kuncina. Na tsugunna gefensa ina bashi.
Na ɗan tattara ƙarfin hali nace cikin in'ina,
"Dan Allah... Bashari, kadaina shaye-shaye. Wallahi zaka hallaka kanka."
Cikin mamaki naji bakina yana rawa da tsoro, na rufe shi da hannu nan take, zuciyata na bugawa da ƙarfi kamar zai fito waje. Na tsaya ina tsoronsa kamar yadda na saba, amma sai yayi wani kallo da baj saba gani ba.
Ya zuba min ido da wata irin nutsuwa da nake jin kaman bashi da ita. Sai kuma ya ɗaga hannu da ƙyar yana goge min hawayen da yatsansa, yace da karamin murya mai rauni "Wai ke ... ke kike tausayin dan daba irin ni?"
Ya saki murmushi mai ciwo da ɗaci.
"Ni Bashari, mai shaye-shaye, mai fada da mutane, wato ni da kowa ke gudu... amma ke har kuka kike min saboda na jikkata. Wannan rayuwar ba ta da mutunci, Ramlah..."
Sai ya lumshe idonsa yana karanto kalmomin kamar yana cikin mafarki. Na tsare shi da ido hawaye na cigaba da zuba, zuciyata cike da tausayi da ruɗani. Wani ɓangare na zuciyata na jin tsoro, amma wani ɓangaren na jin yana bukatar taimako.
Cikin wani irin sautin da nake jin kaman kar ya ƙare, yace "Na rasa komai... amma yanzu kamar ina jin da ke akwai abin da zan so na rike... ko da ace ba ni da arziki."
Sai ya juyo ya kalleni da idanuwansa da suka kumbura da gajiya,
"Ke da yawarki... wallahi ban son wannan kukan! Kuma nace miki ban kuma dukanki ba ai."
Ya juya ya shiga ɗaki ya faɗa kan kujerarmu da karfi, sai kawai naga ya zare kwalba daga aljihunsa. Daga nan na saki numfashi da ƙyar, zuciyata na tsalle a ƙirji. Idanuwana na kallon kwalbar hannunsa da tsananin tsoro.
Dazu kafin ya dawo, Aliyu ne yazo gurina.
Ya zauna a bakin ƙofar ɗakinmu yana fadin
"Ramlah, dan Allah ki taimaka. Ki taimaka ki dinga hanawa Bashari shaye-shaye. Wallahi irin kayan da yake sha yanzu sun fi ƙarfin hankalinmu. Wannan kwalbar da ke hannunsa ba ta titi bace daga manyan da yake musu aiki suke bashi. In har yana cigaba da haka, wata rana zai halaka kansa."
Nayi shiru ina kallonsa cike da fargaba,
"Aliyu... ni tsoro nakeji. Ban san yaya zan fara fuskanci hakan ba."
Sai yace da ni da karfin gwiwa,
"Ki ajiye tsoronki gefe. Ke matar sa ce yanzu. Idan ba ke ba, wa zai taimaka masa? Ya kamata ki tsaya masa. Yana buƙatarki."
Na haɗiye yawu, zuciyata cike da rudani. Sai dai na tuna da halin da nake ciki, na dubi Aliyu nace,
"To... insha Allah. Zan ƙoƙarta. Amma Allah ina tsoro."
Na dawo cikin dakin lokacin da Bashari ya zaro kwalbar daga aljihunsa. Na zaro ido ganin zai sha, zuciyata na harbawa.
Cikin sauri nayi gaba dashi,
"Bashari... dan Allah. Ka dena. Ka dena . Wannan ba hanyar waraka bace, wannan hanyace ta hallaka."
Sai ya zubamin ido, yana kallona kamar yana son yaji idan zuciyata ta canza a kansa. Ya ɗan zabura kamar zai dakeni, na rufe kaina da hannuna ina jiran zafi. Amma sai ya tsaya cak, ya juya ya koma ya kwanta kan kujerar kamar wanda aka kashe masa kuzari.
Shiru yayi... baice komai ba.
Kamar mutumin da yayi nasara da kansa. Idanuwansa na kallon sama, numfashinsa yana fitowa da nauyi.
Ni kuma, jikina yana rawa.
Sai na nufi ɗakin na koma bisa katifata, na tattara jikina kamar wacce ke cikin kankara. Na lumshe idona ina fatan wannan daren ya kare lafiya.
Can daga ɗaki sai na jiyo sautin sharɓar ruwa daga kwalba.
Nayi shiru, zuciyata ta buga da ƙarfi. Sai na juya gefe na riƙe ƙirjina ina fadin,
"Ya Allah... Ka shige mun gaba."
A haka bacci ya ɗaukeni, cikin firgici da ɓacin rai.
Acikin baccina naji yana mun masifa "Ina rigata ja, kin ganta ne?"
Sai na danna lebena cikin taushin rai nace
"Ban gani ba."
Ya girgiza kai kawai ya ɗauki wata rigar ya fice daga dakin.
A cikin daren ma, na sake jin wata hayaniya. Na dan leka kadan, sai naga yana waya, kwalayen taba kuwa ya zazzage, yana zuga yana cillar da hayaƙi kamar wanda zuciyarsa ke cike da rudani.
Can kuma sai ga wani kira ya shigo masa, ya miƙe ya fita. Ni kuma, baccin nawa ya ɓace gaba ɗaya. Nan na tashi nayi alwala, na zauna ina ta lazumin: 'Yaa Hayyu, Yaa Qayyum'.
Saboda wallahi sirri ne babba. Idan kina cikin damuwa, kika riƙe wannan zikiri da gaske, to inshaa Allahu zaki ga sauƙi fiye da tunani.
Haka na zauna har lokacin asubahi ya karato. Sai ga shi ya dawo gida, amma ban kulasa ba. Ya yi alwala, ya gabatar da sallah, sannan ni kuma bacci ya ɗaukeni cikin nutsuwa…”
A cikin magagin bacci, sai na ji kamar yana ta ashar da masifa. Muryarsa na tashi sama da ƙasa kamar wanda yake faɗa da iska ko kuma yana zubar da zuciya. Amma saboda bacci ya rinjaye ni, ban iya gane me yake faɗa ba sosai.
Daga baya kuwa, komai ya ɗauke min kamar mafarki. Ban san yadda abubuwa suka kaya ba. Komai ya koma shiru. Sai dai zuciyata ta cika da damuwa da tambayoyi marasa amsa…
*****************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA SABA'IN DA SHIDA
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Washegari...
Kafin na farka ma, Bashari ya rigani barin gida. Kamar yadda ya saba, shiru-shiru, ba sako, ba magana, ba sallama. Rayuwa da shi har yanzu kamar dare mai baƙin ciki ce. Ina tsoron shi fiye da yadda mace ke tsoron duhu idan wuta ta ɗauke.
Da na farka, dakin ya cika da shiru. Na fito sannu a hankali na soma aikin gida. Na share daki, na gyara kicin, na duba rijiyar mu ko ruwa ya rage, har sai da na gaji da aiki sannan na ɗan ja kujera na zauna dafe da kaina.
Sai ga Habu, ya shigo da ledar shara a hannu. Yayi min sallama da murmushi, na amsa da sassanyar murya, duk da zuciyata tana cike da damuwa.
“Antin birni, oga ya fita tun da safe kenan?.”
Na gyada masa kai, nace “Ni ma na farka ban gan shi ba. Amma ai dama ya saba fita ba tare da gayamun ba.”
Habu ya fara wanke kwanuka, yana wasa da ruwa yana fadin “Ai Antin burni mutanen kauyen nan sai gulmarki suke wai yadda oga ke kula dake kowa haushinki yakeyi he zaginki suke.”
Ban ce komai ba, amma zuciyata taji kamar na fashe da kuka. Habu ya lura, ya yi shiru.
Muna cikin hakan sai naji kara daga waje. Yaran gari sunata ihu NEPA Da sauri na tashi da dariya a fuskata, na je na sa wayata da system a caji. Duk da zafi da zubar hawaye da rayuwar nan take bani, naji rabin zuciyata ya huta saboda wannan wutar.
Na koma kicin, sai ga Habu ya zubda shara, ya fara soya wainar fulawa. Muryarsa kamar ta karamin yaro da ya ga abinci
“Anty birni yau fa nasan zamu ci dadi!”
Nayi dariya nace “ Ai habu barni da wainar nan murnan wannan nepa din tafimun ta wainar. Habu wai ba’a samun karas da irin su Kabeji a nan ƙauyen? ko kanti babu ko?”
Ya girgiza kai “Antin birni, ba a noma caras a wajejen nan. Sai dai daga can gabanmu ko kuma in sun shigo da tallah daga birni. Kanti kuwa da wuya ki samu waɗancan kayan sai dai k'ank'amai irin na gari.”
Na sauke ajiyar zuciya nace “Amma naga Bashari ya kawo mun kwan zabbi jiya...”
Habu ya girgiza kai “Eh, ai su ma a nan muke dasu zabbi ne a kauyen nan sosai, musamman a damina. Mu mu ke kaiwa birni idan mun tara. Amma dai, waje-waje idan sun shiga da tallah sai a samu caras da kayan birni.”
Nayi dariya nace “To ai nagode, gobe sai muyi burodi. Kai zan nuna maka yadda ake sarrafa shi.” Yayi dariya har yana dafe ciki “Antin! Kin iya burodi he naci nagaji kinsan ƴan kauye da son burodi?”
Na daga gira ina dariya nace “Kai dai zaka gani. Bashari yasiyomun fulawa ai kwai kuma gashi babah tabani acikin kayan da bashari yasiyo naga har da yeast da bking powder!”
Habu Yace “ Suma kayan haɗin burodin ne antin Birni?” Nadaga masa kai. Bayan mungama wainar na zuba masa tasa Ya juya ya tafi, na kulle ƙofa, na shige ciki.
Bayan sallar isha’i, sai jin karar hayaniya daga bakin titi. Na kunna torchlight dina na leƙa ‘yan daba ne sun kaure da faɗa da ‘yan sintiri! Ana jifa da duwatsu, ana faɗa da takalma da sanda.
Sai ga Babah ta shigo da gudu cikin gida tana fadin “Ramlah ki rufe kofa! Faɗa ne tsakanin ‘yan daba da sojojin kauye!” Zuciyata ta buga. A wane hali ne zan tsinci kaina idan aka ce Bashari na cikin su? Bayan wani lokaci, sai naji an kwankwasa ƙofa da ƙarfi!
Zuciyata sai da ta tsaya daga bugawa na ɗan lokaci. “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un...” na faɗa da ƙarfin zuciya, na nufi ƙofar da torchlight a hannu.
Fuskar sa cike da jini, rigarsa ta yage, hannu daya yana riƙe da gefe kamar ciwo ne.
“Ramlah... ki bude min...” Na buɗe da tsoro. A wannan lokacin bansan ko zuciyata ce take juyawa saboda tsoro ko tausayi ba.
Na kama shi na shigar da shi ciki. Na duba ciwon da torchlight dina, na ga an sare shi da abu mai kaifi. “Bashari... wai me ke faruwa da kai ne haka? Me kake nema a duniya da har zaka shiga rikicin irin wannan?” Ya yi min shiru. Na je na debo ruwa da auduga na shiga share masa jini, ina hawaye ina fadin “Dan Allah kayi hakuri, ka daina shaye-shaye. Ka daina bin ‘yan daba. Ka daina fitina... Ni mace ce, amma kullum tsoronka nake ciki.”
Yayi murmushin rainin hankali. Ya ce “Kina sona ne?” Ban iya amsa ba. Ina kallon sa da hawaye. Amma dai akwai gaskiya ni baƙin ciki ne ya kaini cikin gidan Bashari. Auren dole, rayuwar da bata da dadi.
Ban gama rufe bakina ba sai kawai na ji wayarsa tayi kara. Ya ɗauka da sauri yana faɗin “Kutmar uban kayayyasa! Aliyu ku rufemun shi. Wallahi yau sai na yanke masa hannu, uwarsa sai tayi jinya mai ƙarfi!”
Kafin na ankara, sai na ga yana kokarin ficewa cikin fushi da huci. Nayi ta maza na riƙo hannunsa, zuciyata cike da tsoro da tausayi nace
“Dan girman Allah Bashari, ka tsaya. Wannan abun da kake kokarin yi ba zai amfane ka ba. Ka duba jikinka, duk rauni da ciwo ne. Wannan ba hanyar waraka bace.”
Kawai sai ya hankadeni gefe, jikina ya fada saman kujerar tamu. Yana cike da tsiwa da tsananin fushi yace
“Ware-ware ke kuma malama? Ke wacece da zaki tsayar dani? Dalla matsa kafin na zubamiki mari a fuska!”
Na fashe da kuka, sai ya fita da sauri kamar zaki yana neman abinsa. Sai kuma kaman dawowa ta daga sama, ya dawo cikin ɗan lokaci. Yana maida numfashi yana fadin
“Ko an kwankwasa, kada ki buɗewa kowa! Kin ji ni? Kuma rufemun baki da wannan kukan naki, wallahi Ramlah...”
Yana fita na share hawayena, zuciyata cike da bakin ciki. Wallahi idan har banyi wani abu ba akan rayuwata, wannan Bahsari zai iya cutar dani fiye da tunani.
Na nufi inda wayata take, na kunna ta cike da fargaba, jin sanyin hasken fuskar wayar yasa hawaye ya sake gangaro min. Na duba balance, na hango inada kusan ₦3,000 a ciki. A take na fara laluba number Abbana, na yi kiran farko ba a daga ba. Sai da na kara kira sannan aka daga.
Mumy ce ta dauka. “Amarya! Wannan kira lafiya?” Na dafe kirjina, cike da rawar murya nace, “Mumy ina wuni? Kuna nan kalau? Ina Ya Billy?mumy ko nemana bakwayi.”
Sai ta kwashe da dariya tana cewa “Mu nemi ki? Me zamu nemi ki da shi? Kinyi aure ba, ina fatan kin fara shaye-shaye yanzu, ko kuwa kuna fita da Bahsari daba? Kina da ciki ne ko? Kalli rayuwarki gaba ɗaya bata da albarka! To ina albarka da auren ɗan daba, ɗan iska da rayuwarsa ta kare a shan jini?”
Ta kara cewa “Kuma na ja miki kunnenki. Kada ki sake kiran Abban Bilkisu. Ya riga ya jefar da kwallon mangwaro, ya huta da kudan kansa.”