Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 30

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 30

Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 30: Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 30. Wayar ta katse kafin in kai labari, kuma duk yunkurina na sake kira…

4,476 words

Wayar ta katse kafin in kai labari, kuma duk yunkurina na sake kira sai naga tayi blocking dina.

Na durƙusa a ƙasa ina kuka sosai, kamar raina zai fita. Maganar da Aliyu ya taba faɗa ta dawo min “Mijinki ne yanzu Ramlah. Kokarinki wajen gyarashi harda ke zai shafa.”

Na share hawayena, na girgiza kai ina fadin “In shaa Allahu, sai na yi iya kokarina.”

Na juyo sai naga Bashari tsaye a bakin kofar yana kallona da wani irin kallo mai cike da tambaya. “Ƴar kwalisata… uban waye ya taɓa ki?” ya tambaya.

Na juya gefe ban ce komai ba. Ya karaso ya rikeni da hannu, ya ɗaga murya “Magana nake miki fa Ramlah!” Bansan yanda nayi ba, kawai sai na kwace hannuna, na saka ihu ina fadin “Ka gyara rayuwarka Bashari! Ko ka sake ni, wallahi nagaji! Wannan irin rayuwar wane irin azaba ce? Ka sauwake min, ko da hakan zai zama silar fushin Abbana kaina!”

Na fashe da kuka kamar raina zai fita. Shi kuma ya tsaya kallona, kamar yana kokarin fahimtar abinda na faɗa, amma zuciyarsa bata yarda da gaskiya ba.

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA SABA'IN DA BAKWAI

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Bashari ya tsaya cak yana kallona da wani irin kallo mai ban tsoro. Na kura masa ido cikin hawaye da gajiya, zuciyata kamar zata fashe. Kamar wanda ba zai ce komai ba, sai kawai ya ɗan janye hannu daga nawa, yana sauke numfashi da ƙarfi.

“Ramlah...” ya kira sunana da wata murya mai ƙasa ƙasa wadda banyi tsammanin zata fito daga bakinsa ba.

“Ina kokari... amma kinsan ni nasaba da wannan halin sama da shekaru. Ni fa Bashari ne! Wannan shine rayuwata tun kafin ki shigo cikinta.”

Na girgiza kai ina kallonsa, “Ai dan baka da hali ba dole bane ka ci gaba da zama haka har abada. Ina so ka canza ne Bashari. Ka daina shaye shaye, ka daina bugeni. Ka zama mijin da zan iya rayuwa da shi da salama.”

Ya juya ya shige cikin ɗaki baice komai ba. Ni kuma na zauna a ƙasa, na tallafe kaina da hannu biyu ina kuka kamar ranta zai fita. Na lura da cewa har yanzu bana jin ƙaunarsa, amma ina so na gyara rayuwata, kuma tunda an daura aurena da shi, sai dai in yi hakuri, ko har Allah ya kawo min mafita.

Sai ga shi ya fito da rigarsa a hannu, yana fadin, “Zan fita.”

“Zaka sha kwaya kenan ko?” na tambaye shi da ɗan tsoro a muryata.

Ya tsaya, ya juyo, ya kalleni daga sama har ƙasa, sai yace, “Ba sai kin sani ba.” Yayi hanyar fita.

Ina kallo ya bankado ƙofa ya fice, har sai da naji ƙarar takalmansa na nisa da ƙofar. Sai na durƙusa, na rungume ƙafafuna ina kuka, “Ya Allah Ka kawon mafita daga wannan rayuwar...”

Yana fita, sai kuma ya dawo, yana kallona cikin rashin nutsuwa ya ce“Kin dafa abinci?”

Na nuna masa flask da hannu ba tare da na ce uffan ba. Yaje ya bude, yaci kadan, sai kuma ya fara yawo a falon kamar wanda ke taƙura. Yafita, ya dawo, sai naga ya yi alwala, ya tada sallah.

Abu ɗaya da har yanzu ke bani mamaki kenan Bashari da wannan halin nashi, amma wallahi ibada ba ya wasa da'ita. Baya barin sallah ko a cikin masifa. Wannan shi ke bani mamaki da tausayinsa lokaci guda.

Yana idarwa, kawai naji ya buɗe baki da masifa “To yanzu da kika hanani shan barasa me kikeso nayi? Ke babu abin da kika iya sai kuka da magana! Ni kuwa barasa ce ke sanyani nishadi, yanzu kuma kika ce nadaina, to me zanyi?”

Na daure, nace dashi da ladabi “To, kaje kayi wanka, ka wanke bakinka ka huta...”

Sai ya hau ihu “To dole ne? Ke fa kin fara bani haushi wallahi!”

Sai ya juya ya fita. Bayan dan lokaci, naga ya dawo daga wanka, jikinsa dauke da ɗan ruwa. Nace masa “Don Allah, kada ka mayar da kayan da ka cire, bar su a gefe, zan wanke.”

Ya kalli kayan sannan ya dubeni “Ai ba suyi dattiba, yar kwalisa, sawata shida fa!”

Nayi murmushi nace “Don Allah, kada ka mayar.”

Sai ya ja numfashi, yace“To,” sannan ya canza su da wasu kuma ga kayan fa yanadasu sosai Sai naji ya tsaya yana kallona daga nesa.

“Ƴar kwalisa… Nasha taba to? Dan Allah karna haukace.”

Cikin dabara na dafe cikina nace: “Wash… Allahna… Yana mun ciwo...” Kawai sai naga ya karaso da sauri yana fadin “Sannu! Sannu yar kwalisa, kina da lafiya ina ke miki ciwo?”

Ya fita da sauri daga gidan. Ina cikin mamaki, sai ga shi ya dawo da kwalin magani a hannu paracetamol yana bani yana fadin“Na dakko a mota, kin san banajin daɗi idan naji ba lafiya…”

Na karɓi maganin a hankali, kaina a ƙasa, na shanye shi da ruwa. Shi kuwa ya zauna kusa da ni a gefen kujerar falo, yana kallona kamar wanda ke so yayi magana amma yana jinkiri. Sai can ya furta da ƙasa-ƙasar murya “Ina ƙoƙari ƴar kwalisa... Wallahi bana jin daɗin yadda rayuwar nan take tafiya. Na gaji da kasancewa haka... amma...” Ya tsaya ya juya fuska kamar zai ɓoye hawaye. Wannan kalmar tasa ce ta fara taɓa zuciyata sosai. Ni danake kullum ganin Bashari a matsayin mugun namiji, a yau sai na fara jin wani sabon abu game da shi.

“Ka sani, Bashari,” na ce a hankali. “Rayuwa bata tsaya a kan ɗan daba ko mai kyau ba. Tana tsaya ne akan wanda ya yarda da canji. Ni na yarda da kai.” Ya dubeni kamar bai yarda da abinda na faɗa ba. Sai yayi murmushi mai sanyi, yana fadin “Ni kuma wallahi zan kokarta, Ramlah. Amma ki sani, shaye-shaye fa ba abu mai sauki bane, ba dare daya ake daina shi ba.”

Nace masa “Sai mu fara da jinkirta. Kodayake ka sha yau, amma gobe ka ƙi sha. Ka rage a hankali har Allah yasa ka daina.” Ya ɗan jinjina kai yana gyara zamansa, ya tashi ya ɗebo ruwa ya bani da hannunsa, sannan ya zauna. “Kina buƙatar wani abu? Kamar tea ko wata abu?” Nayi dariya nace: “Kai kuma har tea kake tambayata?” Ya maida. Ina kallonshi cike da tausayi gaba daya rayuwarsa babu nai gyara masa ko mai ganin abunda yakeyi Mutane na tsoronsa kamar me iyaye sun sallamashi.

Washegari.

Ina tashi daga barci na tarar da gidan ya gyaru fiye da yadda na saba gani. Ko’ina tsaf, wanki a rataye, jikinsu har sun kusa bushewa Kayanmu duka an wanke su. Abin mamaki, wayar Bashari sai ringing take, amma yaƙi daga wa. Kawai sai ya jefar da ita a gefe, kamar bai ma damu da ita ba.

Ina fitowa daga ɗaki da hijab na, sai naga ya tsaya a tsakar gida, yana siffanta shara da salo irin na maza masu iya aiki. Yayi murmushi, ya kalle ni yana faɗin“Ƴar kwalisata, ya jikin naki?” Na ƙara murza idanuwa, na tura baki nace “Yaya Bashari, shine baka tashini ba har ka gama aiki? Kai da kanka ka share ka wanke?” Yayi dariya irin ta farin ciki yana matsowa kusa da ni“Toh ai na iya aikin nan fa. Na girma a titi babu wanda yakemun ni nakeyi da kaina. Wannan aikin ya zama hutu a gare ni yanzu.”

Na yi dariya ina kallonsa cikin mamaki. “Toh yanzu me zaka bani nayi breakfast?” Na tambaya. Yace “Ki zauna kawai, ƴar kwalisa. Bari na kawo miki abin karyawa.” Na shiga nayi brush, sannan na zauna a ɗan ƙaramin darduma da muka shimfiɗa a ƙofar ɗaki. Can sai ga Bashari ya fito da tray a hannunsa, yana cike da burodi, shayi mai kauri, da ƙwai. Ya aje gaban teburin katako da muke amfani da shi. “To ga naki nan,” yace yana dariya.

Na ɗan kalli kwalin shayin nace “Waya koya maka kunna gawayin? Ko wata kakira ta kunna maka?”

Yayi dariya ya ɗaga gira: “Ke fa kina manta wanene ni? Ni fa Bashari ne! Dan titi, dan da baisan wani ya taimaka masa ba ɗan da mahaifinsa baya kallo da daraja ko kema, amma yanzu... ina ƙoƙarin zama mutumin kirki.”

Na ɗago idona a hankali na kalleshi, nace “A’a, yanzu na fara yarda cewa canji yana yiwuwa…” Ya tsaya yana kallona cike da tausayawa. Sai ya zauna a gefena, ya ɗauki kwai guda yana faɗin “Inaso ki sani ƴar kwalisa... duk da halin da nake ciki a baya, yanzu na gane cewa akwai wata rayuwa mafi daɗi da daraja fiye da shan giya da rikici. Idan har zan gyara saboda ke, to zan gyara.”

Na lumshe ido cikin nutsuwa, zuciyata cike da wani irin sanyi. “Idan da gaske ne zaka sauya, to ina tare da kai. Zamu gyara rayuwar nan tare,” na faɗa a hankali.

Ina zaune gefe ɗaya ina karyawa a hankali. Bashari kuwa ya zauna yana kallona kamar wanda aka saka a ɗaki mai shiru. Ban ɗaga kaina ba, amma ina jin idanuwansa a kaina kamar wuta. Wayyo Allah! Wannan kallo nasa... ya cika da abu biyu so da nadama.

A hankali ya janyo kujerar katako, ya zauna daf da ni, ya miƙa hannu ya ɗauki kwai yana tambayata da siririn murya “Ƴar kwalisa... kin yarda na zamo sabon mutum? Zaki zauna dani zaki haifamun yara wallahi zan kula dasu zan so su zan tarairayi su sosai zance musu Allah yayi muku albarka tunda ni bantaba samun wanda ya gayamun ba.”

Na ɗago kaina da jin sanyi a zuciyata. Idanunsa sun cika da ƙwallab, idanuwansa masu kauri sun kafe nawa kamar zai karanta tunanina.

“ Inshaa Allah na daina shan giya..”

Ya faɗa yana kai hannunsa ya gyara gashin gefen fuskata cikin nutsuwa. Idanunsa sun cika da wata irin sha’awa mai kyau, Na juya kai da kunya, zuciyata na bugawa. Bashari ya lumshe ido yana murmushi, ya ce “Kallo ɗaya zan maki yau, Ramlah, sai ki dinga tunawa dashi har gobe. Na sha kallon mata, na san kallo. Amma wadda nake kalla yanzu, ita ce rayuwata.”

Na juya masa baya ina jin jikina ya yi sanyi. Amma sai naji hannunsa ya kama nawa a hankali, kamar mai neman gafara, kamar mai neman farin ciki “Ki amince dani, yar kwalisa. Ki taimaka mun na canza , wallahi. Baki ma sani ba... soyayyarki ce ke ci gaba da gyara ni

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA SABA'IN DA TAKWAS

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Yar kwalisa… bakisan wanene ni ba, amma zan fada miki yau. Ni na tashi ne cikin masifa da bala’i, kamar wanda aka haifa cikin wuta, ba cikin uwa ba. Bansan mahaifiyata ba domin ta mutu tun ina shekara 1, ba'a taɓa bani damar jin dumin soyayyarta ba. Abin da na sani kawai wata azzalumar mace ce da ake ce mata uwa, alhali zuciyarta cike take da garwashi da bakin ciki. Ita ce kishiyar uwata . Ita da uban da ya haife ni wato uban da bai taba tsayawa ya ce ‘Bashari ya ci abinci kuwa?’ yaje makaranta? zo gareni zo ka zauna kusa dani zo muci abinci Su ne suka lalata rayuwata. Su ne suka mayar da ni gabar da kowa ke gudu. Su ne suka dora ni a hanya ba tafarki ba, hanya ce mai duhu, babu kwakkwaran rana, sai ƙiyayya da kunci.

Ina so ki sani, bani da labarin makaranta, yar kwalisa. Ilimi kuwa, kamar wuta nake gani idan na hango kwalejin yara. Wani lokacin sai na tsaya a bayan bango ina kallon yaran da suke sanye da fararen uniform, sai na danne numfashi kamar wanda zuciyarsa ke karyewa. Ina jin kamar na shiga, amma ni fa... bansan abinda ake cewa “class” ba.

Bani da sabulu a lokacin, bani da takalmi, balle pencil. Sai wata rana mahaifinki ya tsare ni bayan na buge masa mota da ƙwallo, nace masa “DanAllah kayi hakuri baba bansani ba” abun mamaki bai dakeni ko zageni ba kamar yadda nasaba jin wasu iyayen sunayimun amma sai ya tsaya yana kallona kamar ya gane wani ciwo a raina. Ya kaini gidansa, ya bani abinci, ya bani sabuwar riga, sannan ya ce 'kai Bashari zaka iya zama mutum .'

Wannan ne karo na farko da wani ya faɗa mun cewa zaka iya. Amma kafin hakan – gaba ɗaya duniya minene? Bala’i ce.

Kinga yanzu kuma… ke kike so ki kirani “miji”? Kike kokarin gyarani? Kike sa min ido da addu’a?

Yar kwalisa… ki sani, ke kika fara bude wani tagwaye a zuciyata. Ki sani, ina mayar da kallo idan kina kallona. Ki sani, bana jin kunyar fadin gaskiya ni cutar zuciya na yi. Amma ke, kina shirin zama magani.

"Ramlah... kinga ni ba daga gida na gari na fito ba. Ban san uwa ta ba. Tun ina ƙarami, kishiyar uwa ce ke kula dani. Amma wallahi babu wata kulawa sai duka da cin mutunci.

Uba na kuwa yana kallon abubuwan da ake min kamar ba shi ya haife ni ba. Rayuwa ta a gida kamar a cikin kurkuku take.Na taso babu ilimi, babu kulawa, sai wahala.

A haka na fara fita gari. Can na fara saduwa da wasu manya masu kuɗi ‘yan siyasa da ‘yan daba. Idan suna son wani aiki wanda ba su da ƙarfin zuciya suyi, sai su ce, “Ku kira mun Bashari.”

Sai su bani kudi su ce na je na yi musu wani aiki na dare. Akwai lokacin da zan fita gida da karfe 9 na dare, sai in dawo da asuba.

"Na fara shaye-shaye ne saboda damuwa da ƙuncin rayuwa."

Wani lokaci nakan zauna in zubda hawaye kawai ba tare da wani dalili ba. Na rasa me nake so a rayuwa.

Sai wani daga cikin ‘yan daba ya bani abu ya ce, “Sha wannan, zai rage mika damuwa.”

Daga nan ne na fara. A hankali na fara sabawa. In ban sha ba bacci baya daukata. Haka na koma cikin duniyar maye.

“Ke ce mace ta farko da kika taba tambayata ka ci abinci? Ka yi brush? Ka yi wanka?”

“Wannan abu ya taɓa zuciyata sosai Ramlah. Wallahi, na fara tunanin sauyawa ne saboda ke. Amma fa ba abu ne mai sauƙi ba. Wannan rayuwar da nake ciki na dasa ne, na rasa hanya ta fita.” “Amma idan har kina tare da ni kike min nasiha watakila Allah zai kawo sauyi.”

Bayan mun gama karya, cikin natsuwa Bashari ya juyo ya kalleni da ido cike da nauyi da ƙauna.Sai yace da murya mai rauni, “Ramlah... zanyi tafiya zuwa birni yanzu. Amma don Allah ki kula da kanki sosai. Idan har wani abu ya sameki sai naji kamar zuciyata ta fashe.”

Nayi shiru, ina kallonsa da idanuwa masu hawaye. Sai na ce masa “DanAllah Bashari, kada ka hana Habu ya shigo. Wallahi yana kwantar min da hankali sosai idan ka fita.”

Ya juyo yana kallona kamar yana nazari a raina, sai yace “To shikenan. Amma ki rike kanki sosai, ki ci abinci. Ki huta, ki cire damuwa.”

Na gyada masa kai da hawaye a idona, ina jin wani irin yawan tausayinsa ya cika zuciyata.

Sai yace “Kwalisata... Allah yayi miki Albarka.”

Sai na ce da muryar kuka

“Ameen... ka tafi lafiya, Allah ya kareka daga sharri da haɗari.”

Yayi murmushi mai ɗauke da farin ciki da kuma wani irin ƙaramin ciwo, ya juyo ya fita, ya barni tsaye a ƙofar ɗakin da hawaye.

Ina komawa cikin gida, na sauke ajiyar zuciya na ɗauki wayata, nace bari in kira Maryam. Tunanina gaba ɗaya yana makaranta ne yanzu kullum sai na rika jin kamar na koma. Na kira Maryam sau biyu bata ɗauka ba, nace watakila tana lecture. Sai na nemi lambar yaya Usman, ko da yake bata shiga gaba ɗaya ba. Na kira yaya Abbas, amma sai naga “switched off” na fito.

Nace kai, yau duk kiran da nake yi kamar ana min ƙyashi. Na ajiye wayar a gefe, na kunna system dina, nace bari na dan kalla wani Korean film ɗin nan da ke rage min kaɗaici. Na zauna ina kallonshi da nutsuwa alamar cajin ɗin yana gab da karewa kenan, sai na kashe system ɗin, na ajiye a gefe.

Na tashi cikin natsuwa, na shiga dafa abinci. Tuwo na nayi, na haɗa miyar kuka. Kodayake babu nama, amma da daddawa da Maggi nayi. Na gyara gidan gaba ɗaya, na share, na gyara gado, na sake shimfiɗa zani.

Bayan haka, na nufi gidan Uwani wai an ce batada lafiya. Ko da na isa, kafin ma in ce komai, sai Uwani ta bige da tambayoyi kamar wata 'yar jarida.

“Ke Ramlah... ya dai? Har yanzu bakiji komai ba? Ke ko lafiya ne kuwa? Kinga fa shekara nawa kenan da auren nan, har yanzu ko juna biyu babu? Ko dai ke juyace.?”

Na kalleta da mamaki nace mata Dubaki nazo nayi ba wai tambayoyi nazo kiyimun ba Ai haihuwa Allah ke badata ko? Yajikin Naki Allah ya baki lafiya sai anjima nafaɗa ina barin gidan da takaicinta.

Bayan na dawo daga gidan Uwani, na duba wayata, sai naga kira kusan guda biyar an yi min. Na shiga neman Maryam, da na kira, ba da jimawa ba ta daga. “Ramlah ina kika shiga dan Allah? Naje gida har sau biyu amma ana cewa bakya nan. Mai gadin ku ma yace wai kina can, kin yi aure.”

Na lumshe ido ina ajiyar zuciya, cike da nauyi nace “Eh Maryam... na yi aure.” “Astagfirullah! Amma baki kyauta ba, baki sanar da ni ba. A ina kika yi auren?” Na dan yi shiru, sannan nace da karamin murya“Ai Maryam... nima kamar ba ni aka yi wa ba. Na zo na tarar da maganar auren, ba a nemi shawara ta ba. An daura aure ne kawai aka ce an ba ni wani a wani kauye, ni ma ban ma tuna sunan garin ba.”

Ta yi ajiyar zuciya tace “To makaranta fa? Kin san fa muna strike har yanzu.” Nayi dariya kadan nace “Kai Maryam naji dadi wallahi. Tunani nake yaya zanyi idan komai ya dawo normal. Na rasa yadda zan ci gaba da karatu yanzu.”

Sai kuma ta dan dakata tace “Amma kamar bakya cikin farin ciki Me yake faruwa?”

Nayi murmushi nace “Bakomai Maryam. Komai zai daidaita insha Allah. Zan saka wayata a caji, in nayi charge zan kara kiran ki.” Tace “To shikenan, ki kula da kanki fa.”

Na kashe wayar cikin sanyi na sauka ta gefe, sannan na tashi na yi alwala. Bayan nayi salloli na, zuciyata cike da nauyi, na kwanta.

A Cikin bacci na…

Na fara jin kamar ana bubbuga numfashi kusa da kunnuwana, tare da wani lallausan shafi da bai daɗe ba sai ya rikita min baccin. Wani hannu mai ɗumi yana yawo a hankali akan gefen fuskata yana shafawa kamar ana tausa zuciyata ne, ba fata ba. Sai na ji an sauke sumulun numfashi a wuyana… kafin harshen sa ya dan lasa gefen wuyana a hankali.

Wata irin murɗaɗɗiyar kasala ce ta mamaye jikina. Fuska ta sai ya cigaba da lasawa a hankali, kamar yana kwantar da hankali ne, yana narke min zuciya. Daga wuyana sai gefen habata, yana shafar hancina da yatsunsa a hankali. Numfashinsa yana buga min fuska, yana sauka da nauyin da zuciyata bata saba da shi ba. Amma kafin na gama narkewa cikin wannan yanayi, sai na fara jin an ja rigata kadan a hankali kamar yana neman cire ta ne. Nan take wata irin kara ta fito daga bakina karar tsoro da ruɗani na farka a firgice

A gabana... sai ga Bashari. Fuskar nan tasa babu annuri, idanunsa cike da wani iri...

Kafin na buɗe baki sosai, sai naji ya matso… ya rungume ni da karfi, kamar wanda zai ɓalle da hawaye. Ajiyar zuciya yake saukewa kamar mai raɗa cikin dare. Cikin rawar jiki nace

“Dan Allah… kabari. Haba.”

ƴar kwalisa, hauka kike so nayi?”

Amma sai naji yana cewa

“Ina bukatarki… don Allah.”

Na rasa nutsuwata gaba ɗaya. Na fashe da kuka… amma bai sakeni ba. Sai dai ya ƙara matse ni, yana matsowa da bakinsa zuwa ƙan nawa

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA SABA'IN DA TARA

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Na rufe idanuna da ƙarfi kamar zan iya buɗe su na tarar da komai mafarki ne. Amma a'a… jin ɗumin jikinsa da kukan da ke ɓoye a cikin ajiyar zuciyarsa ya tabbatar min cewa wannan gaskiya ce, ba mafarki ba.

"Bashari... Dan Allah..." nace cikin kuka, amma muryata ta ɗauki wani salo na rauni, kamar wata karamar yarinya da take nema a rarrasheta.Na zame jikina da karfi, sai dai ban samu na kuɓuta ba. Hannuwansa sun zagaye ni kamar igiyar ƙarfe. Idanunsa suna cikin nawa, kamar yana karanta komai da zuciyata ke tunani.

“Ƴar kwalisa… me yasa kike guduna ne? Me yasa kike jin tsoro na kizo naji dumin jiƙinki kizo dan Allah..”

Ya dora goshinsa a wuyana, yana fadin

“Na rasa nutsuwa Ramlah… na rasa haske. Kowane dare ina mafarkin ki. Kullum kamar kina kirana daga wani wuri mai dumi. Amma da safe, sai na wayi gari cikin duhu. Kawai ke ce kike saka ni jin cewa nima dan adam ne…”

Na lumshe ido, zuciyata na tafasa. Wani bangare na zuciyata na cewa ki ture shi, amma wani bangare kuma na cike da tausayinsa... da tausayi mai sa hawaye.

Sai ya ɗago fuskarsa kadan, yana kallon idanuna cikin natsuwa.

“Kina tsoron ni, ko?”

Na ɗan girgiza kai da ƙyar, nace da ƙaramar murya, “A'a... bana tsoranka... kawai bana yarda da zuciyarka yanzu ma haka kasha taba bashari bazaka taɓa canzawa ba .”

Ya ɗan murmusa, murmusin da yafi kama da kuka.

“To yau ki daina. Ki ba ni dama, ki zama tunanin farko da nake yi da safe. Ki ba ni damar canza sunana daga Bala’i zuwa ‘soyayya’. Ramlah… zan so ki. Ko da na ci amanar kaina, ba zan ci amanarki ba.”

A hankali ya mike daga kan gadon, murmushi a fuskarsa, idanuwansa jajaye kamar wanda ya shafe daren cikin mafarkin da ba su zo da mafita ba. Cikin wata murya mai sanyi da kasala, ya ce,

“Ƴar kwalisa… bazan taɓa takuramiki ba har sai kin amince dani da kanki. Kuma wallahi sigarin da nasha kara ɗaya ne, saboda naji kamar zan sake komawa.”

Ya dafa bango, yana kallona da idon da ke magana da kansa.

“Ke fa kina gudun ɗan shaye-shaye ko? Kina tsoron ace mijinki ɗan daba ne, wanda ba zai iya zama uba ba? Haka ne? Na fahimta. Kowa yana ƙin kazamar rayuwa.”

Yayi dariya mai ciwo, yana ƙoƙarin ɓoye raunin da ke cikin zuciyarsa.

“To amma ki sani... iyayena su ne suka fara kashe ni tun ina ɗan shekara huɗu. Ba wai da wuka ba, da kalmomi ne. Da rashin kulawa. Da barina cikin ruwan sanyi, da barina cikin yunwa da duka da tozarci. Rayuwata ta yi tsami kafin na san daɗin zuma.”

Ya lumshe idonsa, kamar yana ƙoƙarin fitar da wani abu daga zuciyarsa.

“Wallahi ban taɓa kashe rai ba. Amma nayi sara, nayi suka, nayi fada. Na yarda an cuce ki da aka baki ni a matsayin miji. Wallahi basu kyautawa nutsatsiyar yarinya kamar ke ba. Ki gafarce ni... yanzu bari na kwanta a palour. Ki kwanta lafiya.”

Yayi gaba cikin natsuwa, ya fita daga dakin kamar wanda ke gudun kallon tausayi.

Na tsaya ina kallon ƙofar da ya rufe, hawaye suka cika min ido. Me yasa nake jin tausayinsa? Me yasa wani ɓangare na ke cewa zai iya sauyawa? Me yasa naji kamar na taɓa jin zafin da ya ji, ko kuwa ni ce nake mayar da tausayi ya rinjayi hankali?

Na sunkuyar da kai, na runtse idona.

“Allah Ka shige min gaba,” nace a ranta.

Sai na tashi, na gyara gadon da ya zauna akai, na zuba ido zuwa ƙofar da ya fita ta. Ba tare da wani tunani ba, sai na zare hijabi na Nayo alwala, na shimfiɗa zani, na tada sallah.

Ina addu'a da hawaye. Na ce

“Ya Allah... idan har wannan mutumin yana da rabona, Ka shiryar da shi... Ka bani jarumtar jure masa... Idan kuma ba ni ka yi masa ba, to Ka raba mu cikin sauƙi da albarka.”

Ina idar da sallah, na kwanta. Amma zuciyata bata huta ba. Tunanin Bashari ne ya mamaye ni.

Shi kuma... yana kwance a palour, rufe da bargo mai tsufa, yana kallon rufin dakin kamar yana ganin mafita daga cikin lalatacciyar rayuwarsa.

A hankali na mike, na leƙa palour. Na gan shi kwance a ƙasa, ya lullube jikinsa da tsohon bargo. Idonsa a lumshe, numfashinsa ya daidaita kamar wanda ke cikin mafarkin da bai san yadda zai farka ba. Wani abu ya taso a zuciyata… tausayinsa ya cika ni. Wannan ba kawai mijina bane wannan mutumin ne da duniya ta rinjaya, ta zubar da shi kamar ɓargo mai datti.

Na taka a hankali zuwa gare shi. Sai na tsuguna gefensa, na dora hannuna akan kafadarsa cikin sanyi.

“Bashari…” na kirashi da sassanyar murya.

Ya bude idanu a hankali. Idonsa cike da dariya da ƙauna da mamaki.

“ƴar kwalisa...” ya faɗa da murya mai rauni.

“Ina so ka sani… bana ƙin ka. Abin da nake gudu shine abinda kake aikatawa. Shaye-shaye ne ke hana rayuwar ka daidaita. Amma kai Bashari... kana da zuciyar mutum.”

Ya lumshe ido.

“Kin gane ni fiye da kowa. Amma kin sani Ramlah, bana tunanin zan iya tsayawa na canza idan babu wanda ke tare da ni. Ni da kaina ba zan iya ba. Amma idan ke… idan har ke zakiyi min rufa, wataƙila zan iya canzawa.”

Na dafa kafadarsa, na ce da kishi mai sanyi a zuciya

“Zan taimaka maka. Amma ka taimaka wa kanka ma. Ka farka daga wannan baccin rayuwa.”

Yayi shiru yana kallona.

Sai ya kamo hannuna a hankali, kamar zai rasa ni, yace

“Ina jin ki sosai Ramlah. Da farko nayi tunanin kin tsani ni, amma yanzu naga kin fi kowa fahimtata. Wallahi zan canza. Bana so ki zubda hawaye saboda ni.”

Wani irin numfashi ya fito daga zuciyata. Sai kawai naji hawaye sun zubo a idona. Na ce cikin kuka

“Ina fatan Allah zai taimake mu. Domin ban san yadda zamu iya ba tare da shi ba.”

Sai ya tashi zaune, ya kamo hannuna biyu.

“Mu yarda da Allah. Mu tafi tare cikin sabuwar hanya.”

Na gyada masa kai.

******

Cikin kwana biyu sai rigima ta kaure a ƙauye.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull