Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 32

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 32

Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 32: Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 32. Ko minti goma banyi da kwanciya ba, bacci ya fara mamaye jikina.…

4,468 words

Ko minti goma banyi da kwanciya ba, bacci ya fara mamaye jikina. Idona ya lumshe, zuciyata na sauke numfashi cikin shiru. Cikin wannan natsuwa, sai na ji muryarsa a hankali yana cewa:

“Ƴar kwalisa... danAllah... na kwana a gadon yau?”

Na buɗe idona a hankali. Bansan me zan ce ba. Na rasa ko mafarki nake yi ne, domin wannan ba irin Bashari bane da na saba gani. Muryarsa cike da ladabi da nutsuwa.

Na daga masa kai a hankali. A gaskiya... nima jiya na ji daɗin kwanciya a jikinsa. Daɗin da ya sha bamban da komai da na taɓa ji. Mafarkai na na mugaye da ke yawan addabar zuciyata har dare, duk basu zo ba. Wata nutsuwa ce ta sauka.

Yana kallona da idanunsa masu taushi, ya ƙarasa ya kwanta a gefe. Sai ya ce cikin rauni, “Zan iya rungumeki? Babu abinda zan miki… Wallahi.”

Baki na ya buɗu kamar zan ce wani abu, amma kalmomi sun makale a maƙogwaro. Idona ya faɗa cikin nasa, sai kawai na juya a hankali.

Yana ƙarasowa kusa dani, ya sa hannunsa ya ja ni a hankali zuwa jikinsa. Zuciyata ta fara dukan kamar ana bugunta da ƙwanƙwasa. Amma ba saboda tsoro ba saboda wani sabon yanayi da ban saba ba.

Ya janyo ni gaba ɗaya cikin jikinsa. Numfashinsa na bugun bayan wuyana. Hannunsa ya zauna a kafadata, yana shafewa a hankali. Wata sanyi mai dumi ya lullube jikina gaba ɗaya.

Amma sai na ji… hannunsa ya gangara. Ya sauka a kirjina. A nan ne na ji wani mugun shock ya kama jikina. Na kasa motsi. Idona na lumshe da ƙarfi. Kwakwalwata kamar za ta tashi sama, zuciyata na harbawa da karfi.

Bansan me ke faruwa da jikina ba. Amma na san wannan ba tsoro bane. Wannan wani yanayi ne mai cike da daɗi... da jin daɗin kasancewa kusa da wanda kake so, koda ba ka furta hakan ba.

“Na ƙosa ki fara sona,” ya faɗa da wata murya mai raɗa.

Ban ce komai ba. Amma numfashina ya nuna masa komai. Hannunsa ya ɗan matsa ya kama hannuna. Sai ya riƙe shi a kirjinsa. “Kiji yadda zuciyata ke bugawa saboda ke.”

Na lumshe idona da hawaye masu ɗumi. Kamar wata damuwa ce ta narkewa cikin zafin kulawarsa.

Sai ya ce, “Zan iya kwana da ke haka... babu wani abu... sai numfashinmu kawai?”

Na gyada kai. Ya matse ni a jikinsa. Na ji kamar wannan gabar jikinsa ce mafakata. A can ne nake so in kwana… kuma in tashi.

Washegari da safe ban farka da wuri ba. Sallar asubah ta shude kamar iska. Idanuwana sun kasa buɗewa, zuciyata cike da dumin daren jiya. Sai da safe sosai har kusan goma na farka da cikakken numfashi mai nauyi. Na mirgina daga gefen gado cikin natsuwa, na ɗan shafa filon da har yanzu yana ɗauke da kamshin jikinsa. Wani sanyi ya ziyarci zuciyata.

Na miƙe da gajiya, amma cikin nishaɗi. Na kalli dakin, sai naga tsaf. Gidan duk an gyara, carpet ya sha tsinke, kitchen tsaf kamar ana jiran baki. Wanke-wanke babu ko leda guda, komai daidai. Ashe Bashari ya gyara gida kafin ya fita...

Ina cikin shan shayi a ƙanƙanin cup, sai Uwani ta shigo kamar wadda aka biyo da labari.

“Ke dai kin kwana lafiya Ramlah,” ta faɗa tana kallona da murmushi mai cike da sirri. “Kin san me ya faru kuwa?”

Na kalleta da kallon tambaya, amma ban ce komai ba. Na ɗauko mata cup na zuba mata shayi. Tana karɓa, tana cewa

“Rigima babba ta kaure yau da safe. Ke kin san filin da ke bayan gidan su Bashari? Ashe wai uban Bashari da shi suke rikici. Bashari ya fita waje da makami fa! Dakyar aka raba su.”

Na ɗan juya kai, zuciyata ta fara bugawa. “Makami?” na maimaita a hankali.

“Eh mana,” Uwani ta ce tana gyara zama. “Wallahi matar uban Bashari ke zuga shi. Ke dai ki tsaya Allah ne yasan abinda ke tsakanin su.”

Na saki wani sassanyan ajiyar zuciya. Ban ce komai ba. Na ci gaba da shan shayina a hankali, na zuba mata nata cup. Ta sha, ta mike ta tafi.

Na san halinta ba zata taɓa tafiya ba indai ba labarin Bashari na bata ba. Wannan karon dai sai ta hakura.

Bayan ta fita, sai na ga wayar Bashari a gefe kusa da gado. Na ɗauka da murna kamar na ɗauki wata kyauta. Cikin nutsuwa na duba contact list. Na saka number Abba a ciki, zuciyata cike da burin jin muryar wanda ke da daraja a idonsa.

Sai da ya kusa kira na hudu kafin aka ɗaga. Muryata na ɗan rawa, nace, “Abba, ina kwana? Ramlah ce.”

Na ji dariyarsa a gefe, mai dumi. “Auta! Yanzu saboda Allah ke bazaki kirani ba ki gaidani?”

Na saki murmushi cikin jin kunya. “in nakira bana samunka shiyasa…”

“Lafiya ko? Badai wani abu ba?” ya tambaya cikin damuwa. “Yayanki Usman yazo nan, muna nemanku, ba a samu ba. Ashe Bashari ya sauya wayar.”

Na ce, “Lafiya lau. Ina Yaya Abbas? Ina Billy? Ina mummy? agaidasu”

“Zasu ji. Ramlatu, ki rike mijinki da kyau. Ki yi masa biyayya. Wallahi bana so wani abu ya raba ku, sai dai mutuwa.”

Sai na lumshe ido. Wani zafi ya ratsa zuciyata kalaman da suka nuna amincewa da Bashari fiye da yadda mutane suka saba dubansa. Shi da mutane ke ganin dan daba ne, dan maye... Abba na masa kallon cikakken namiji.

“Zan yi iya kokari na, Abba,” na ce a hankali, hawaye yana makale a gefen idona.

“Allah ya baku zaman lafiya,” ya faɗa kafin muka ajiye wayar.

Bayan ‘yan mintuna, na ji ƙofa ta buɗe. Bashari ya dawo. Amma da zarar ya shigo, sai na fahimci cewa ba shi da walwala. Fuskar sa a murtuke, kamar wanda aka takura masa da duniya gaba ɗaya.

Bai ce komai ba. Bai kalle ni ba. Ya cire rigarsa ya shiga bandaki. Bayan ya fito da jiki mai danshi, sai ya zauna a kujerar daki, yana fesa turare kamar wanda ba ya cikin hayyacinsa.

Bansan me ke damunsa ba. Amma na san… akwai abu mai nauyi da ke cin zuciyarsa. Ko sannu da dawowa bai amsamun ba

Na zauna a gefe ina kallonsa, zuciyata cike da tausayi. Wane irin ciwon zuciya ne haka ke yawo da shi? Ina so in tambaya. Ina so in matsa kusa. Amma shiru nayi.

Kalaman Abba suka dawo mini a kunne “Ramlatu, ayiwa miji biyayya dai. Ayita hakuri.”

Sai na lumshe ido na ce a zuciyata Zan yi. Amma ya kamata shima

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA TAMANIN DA UKU

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Cikin wani shahararren wurin shakatawa mai suna Shangri-La Rooftop Lounge, dake tsakiyar birnin Paris, wanda ke ɗauke da kyakkyawan daki mai kallon Eiffel Tower, Ayshatu ke zaune cikin rangwamen soyayya da wani mutum mai muhimmin matsayi da kowa ke jin tsoronsa Alhaji Muqaddam.

Ayshatu ta sa wata Versace short dress fara, da ba ta rufe gwiwarta ba. Gaban kirjinta a bude, sai glass da mask masu Fendi design suka kammala kyawun fuskar da ta zubo gashinta a baya.

Alhaji Muqaddam, sanye da Gucci shirt budaddiya da short wando mai sauƙin launi, yana sanye da Rolex Oyster Perpetual Platinum a hannunsa, ya kafe ta da wani irin kallo da ke narke zuciya.

"Kwana biyu da bakizo ba din nan, naji kamar nayi madness, Ayshatu," ya faɗa da murya mai sanyi, yana tsunduma cikin idonta. "I love you so much wallahi..."

Ayshatu ta sauke murmushi mai cike da nishaɗi. "Ka sani dai cewa bani da ikon boyewa. Yanzu ma na lallabashi ne, yana can wajen Prince babansa, zai ɗauki lokaci kafin ya dawo. I'm missing your touch nima yanzu idan ya taɓani, ban jin wani abu…"

Alhaji Muqaddam ya bushe da dariya, yana rungumarta da damƙa, ya ce

“Wannan ai ba sabon labari bane. Ragon namiji ne shi, kullum sai rigimar maganin ƙarfi yake. Kuma... wallahi idan kin ce ‘I love you’ gareshi , inajin kamar ana tsaga min zuciya da reza saboda bana son wani yayi miki kusanci ko magana babu yadda zanyi da as'ad.”

Ayshatu ta zaro ido, tayi masa tsaki. "Wallahi na gaji dashi but bazan taba iya rabuwa dashi ba …"

Muqaddam ya matsota sosai, ya ja wuyanta yana shinshinawa da nutsuwa. "Yanzu daga nan Le Bain Spa zamu wuce. Na tanadar maki tausa da massage har zuwa dare. Sai mu kwana a Hotel Barrière Le Fouquet’s a Champs-Elysées. Baby, I miss you too."

Ya rada mata a kunne "You’re the reason I still believe in love… ."

A cikin wani VIP suite da aka tanadar da white petals, vanilla candles, da sautin slow French jazz, Ayshatu ta yaye doguwar rigarta na Versace, tana shiga cikin rigar tausa da aka ajiye mata. Masassaka biyu na mata sun shigo cikin shiru, suna fara aiki akan kafa da bayanta, yayinda Alhaji Muqaddam ke zaune yana kallonta kamar zai shanye ta da ido.

Zuciyarsa cike da jin daɗi da raɗaɗin ƙaunar da ke neman ƙone zuciyarshi. “Kin san kina bani damar jin kamar ba ni kaɗai nake da mummunan ciwo a rayuwa ba.” “Ni?”

“Eh, ke. Koda kina tare da wani, zuciyarki ba nashi ba ce. Kuma na san shi baya fahimtar ki kamar yadda nake fahimta.”

Ayshatu ta buɗe ido cikin rauni, sannan tace “Muqaddam… idan gaskiya ce wannan da kake faɗa… to me yasa baka ce min ki rabu da shi ba?”

“Saboda na san aurenki ba irin wanda za a iya rabawa da sauki bani ba. Kuma bana son ki rasa komai saboda ni. Ina son inbi komai a hankali.”

Bayan tausar da suka gama cikin dare a cikin ɗaya daga cikin gidajen private estate da Alhaji Muqaddam ke da shi, ya ɗauki Ayshatu da kansa suka shiga cikin babban gidansa.

Gidan yana da pools guda biyu, indoor jacuzzi, da roof garden .

Suna shiga ciki, Alhaji Muqaddam ya janyo hannunta, yana kallonta da idon sha'awa da muradin soyayya. Ya ce mata da raɗa

“Ke tawa ce yau.”

Ba tare da wani bata lokaci ba, cikin zafi da ƙauna ya fara cire mata kayan jikinta, yana sumbatar ko'ina na jikinta. Gaba ɗaya Ayshatu ta nutsa cikin wannan mahaukaciyar soyayya. Basu tsaya tunani ko tambayar me ke gaban su ba. Suna jin dadi da kasancewa cikin juna haram, amma daɗin sa ya goge dukan tsoron da ke zuciya.

A gefe guda kuma, wayar Ayshatu sai rawa take. Kira. Text. Kira. Sako. Amma bata kalla ba. Bata ma motsa ba.

As'ad ne ke kira Amma da gangan ta dinga watsi da kiransa. Ba wai bata gani ba… a’a. Tana ganin su, tana karanta sakonnin sa, tana jin kiransa… amma ta ƙi tankawa. Domin zuciyarta tana fadi cewa idan bata yanke da shi ba, ba zata samu soyayyar Alhaji Muqaddam da arzikinsa ba.

"Zan bar As'ad," ta furta a hankali, tana shafa fuskar Alhaji Muqaddam bayan sun gama wanka tare. “Zan aure ka. Na tabbatar.”

Alhaji ya yi dariya, yana wasa da tafin hannunta. Sai ya ce

“Yau zaki ji wani abu.”

Ya ɗauki wayarsa, ya danna wani abu. Sai yace, “Duba account dinki.”

Ta ɗaga wayarta da sauri. Zuciyarta na dokawa kamar mazuru. Sai kawai taga alert

₦50,000,000 (Naira Miliyan Hamsin) ya shigo cikin account dinta.

Idanunta suka cika da hawaye. Amma ba hawayen damuwa ba hawayen daɗi. Ta rungume shi da ƙarfi.

“Na rasa yadda zan gode maka… wallahi na rasa…”

Ya shafa bayanta, yana lumshe ido. “Ni nasan me kike so Ayshatu. Kuma zan baki komai.”

A dai-dai wannan lokacin sai wayarsa ta fara kara. Yayi saurin ɗagawa, yana kallon Ayshatu da dariya, sai ya toshe mata baki da hannu, yana nuna mata da ido cewa wayar mai mahimmanci ce.

A bangare na daban, muryar mai kira ya fito mai tsanani da izza.

“Muqaddam, kanajina?”

Muqaddam ya gyara zama, ya ce, “Yes. Inajinka, As’ad.”

As’ad ya ce da murya mai taushi amma mai ɗauke da karfi

“Yaushe zaka canza? Wani yaro na yace ya ganka a Paris da wata mata. Kana matawa ne da darajar aure? har matanka biyu sun fara koka akan rashin basu lokaci. Amaryarka ma ta kira ni. Tana kuka. Kai fa... ya kamata ka gyara.

Muqaddam yayi ajiyar zuciya. “Ai da madam nazo wannan karon bai ganeta ba. Kuma... I’ve changed. Am not into any womaniser thing again. Wallahi na daina.”

As’ad ya yi shiru kadan. Sai ya ce

“Hakan shi ne ya kamata. That’s good for you..”

Muqaddam ya kashe wayar. Idonsa ya dawo kan Ayshatu, yana kallonta da murmushi mai zurfi. “Wannan wayar… tunanin cewa As’ad zai iya kamani da ke… sai naji kamar zuciyata ta tsinke.”

Ayshatu ta kalle shi da murmushi mai zafi da so. “Ka kame ni. Ka mallake ni. Kuma wallahi zan tsaya da kai har abada… sai dai kaddara ta raba mu.”

Yayi dariya ya ce, “To yanzu... .”

Ya janyo hannunta. Kuma suka shige cikin dadi da zunubi.. ƙarar numfashi biyu kawai ke ɗaukar kunne a dakin. A inda fitilar dakin ke yawo a hankali kamar tauraruwa mai rawa, Ayshatu na kwance a gefen gado, jikin ta ya lafa cikin natsuwa da saukin zuciya.

Muqaddam ya matsa kusa da ita, yana sauke numfashi a wuyanta. Hannunsa ya gangaro ya kama kafadarta, sannan ya ja rigar satin da ta lullube jikinta, ya sauya matsayinta zuwa cikin jikinsa.

A hankali, kamar marubuci yana zane da fensir a takarda mai laushi, ya ɗora hannunsa a saman ƙirjinta ba cikin hanzari ba, ba da karfi ba amma cikin kulawa, nishaɗi, da jin daɗin da aka tara tsawon kwanaki.

Ya fara sarrafa fuskar nononta da yatsunsa. Yana shafawa kamar yana karanta halittarta da yatsunsa. Gaba ɗaya jikinta ya ɗauka da karfi. Zuciyarta na buga kamar ƙarar rawar ganguna.

Ayshatu ta buɗe ido da sauri, ta kama hannunsa, amma maimakon hana shi sai ta matse shi a jikinta. Idonta ya canza, numfashinta ya zurma cikin sauri.

Muryarta ta kasa fita. Amma jikin ta ya mayar da martani kamar wata jaruma da ke karɓar labarin so da shauƙi da jin daɗi.

Hannunta ya kama fuskar sa, ta janyo bakinsa zuwa nata. Kissing ɗin da suka yi a wannan lokaci ya canza komai. Yana da nauyi, yana da girmamawa, yana da tsantsar buƙatar juna. Zuciyarsu na narke a cikin juna kamar jikin ruwa da zuma.

Hannunsa ya cigaba da yawo a hankali. Bai yi gaggawa ba. Amma yanda yake sarrafa jikinta yana tabbatar mata da cewa ya fahimci mata fiye da kowa.

Tana jan numfashi da karfi. Fuskar ta na cike da nutsuwa da karaya. Amma soyayya mai ƙarfi tana karɓe jikinta gaba ɗaya.

“Please... kar ka tsaya,” ta furta cikin ƙasa-ƙasar murya.

Ya ce da ita cikin raɗa, “Zan tsaya ne idan zuciyar ki tace haka… ba idan kike jin daɗi ba.”

Ya gangaro zuwa kirjinta. Yana sumbatar fatar nononta kamar wacce take da daraja a sararin halitta. Jikinta na girgiza. Kafafunta suka narke kamar wadda ta jima da rasa ƙarfinta.

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA TAMANIN DA HUDU

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Zaune yake a cikin katafaren shashinsa, wanda yake gefe da sashen sarki, a cikin Fadar Gidan Sarauta da ke tsakiyar babban birni. Zanen bangon falo sun haɗa zinariya da fari, kayan dakin kuma su ne Italian mahogany, mai cike da tarihi da daraja.

As’ad Babangida, ɗan sarki na uku a jerin masu gadon sarauta, yana sanye da farar shadda mai fenti mai launin royal blue, yana zaune a kujerar alfarma. Kusa da shi, kaninsa Abba, yana ɗauke da laptop, suna lissafin kasuwancin su daga siyar da filaye a Maitama da Wuse 2, zuwa kayan shigo da gine-ginen kasashen waje.

Sun shagala cikin magana, As’ad yana duba wani babban project da suka fara a Dubai. Wani aiki ne na gine-gine a gabar ruwa da ke Palm Jumeirah – inda zasu samar da luxury apartments ga manyan masu kudi daga Afirka.

Daga kofa sai suka ji sallama. Wasu daga cikin ma’aikatan gidan sarauta suka shigo, dauke da abinci da drinks. Suna ajiyewa cikin girmamawa da ladabi.

“Allah ya ƙara maka lafiya, yallabai,” suka faɗa suna durƙusawa.

As’ad ya ɗaga kai. Yayi murmushi kaɗan. Abba ya gyara zama, ya ɗan juya ga yayansa.

“Yaya... akwai wani matashi da ya ce yana neman Firdausi. Yaron yayi magana da ni. An ce an bincika shi. nayi da kaina kafin a cigaba da wani abu.”

As’ad ya juyo da idonsa a hankali. Idon nasa mai tauri amma da zurfin hankali, yana ƙoƙarin fahimtar wane hali ne wannan matashin zai iya kasancewa.

“Katurawa PA bayanansa. Zan duba shi da kaina,” ya ce a nitse.

Ya ɗauki tuffa mai sanyi, yana kallon gefen window da ke kallon filin kwallon gida.

Amma zuciyarsa ba cikin falon take ba. Tun bayan da Ayshatu ta barshi da cewa tana tafiya Paris domin wani “business”, hankalinsa bai kwanta ba.

Kwanaki biyu kenan bata amsa kiransa ba. Ko text babu reply. Kamar an share shi daga rayuwarta. Tunanin hakan yana cin masa zuciya. A ina ta shiga? Me take boyewa? Shin zuciyarta ta barshi kenan?

Ya dafe kai da hannunsa. Sai yaji sallama daga bakin kofa.

Wani bawan gidan ya shigo da sauri, yana fadin

“Ranka ya daɗe, Hajiya ce ke nan da kanta...”

Nan take suka mike tsaye da girmamawa, mahaifiyarsu, uwa mai daraja a gidan sarauta.

Abba ya nemi izini ya bar shashen. “Yaya, zan je na duba clients ɗin Land project na Victoria Island,” ya faɗa da girmamawa.

As’ad ya gyada kai. Amma zuciyarsa na cike da tambayoyi.

Ina ayshatu yashiga da har zata share ni haka no call no text

Ya lumshe idanu, ya ɗora hannunsa a zuciyarsa. “Allah yatsaremun ke,” ya ce da kansa.

Tana shigowa, fuskarta cike da natsuwa da kamala, har kallo ɗaya na nuna uba da uwa sun ciyar da ita da tarbiyya. Kamar yadda ake a gidan sarauta, As’ad Babangida, ɗan sarki, ya miƙe da sauri, ya tsugunna gaban mahaifiyarsu Hajja.

“Ranki ya daɗe, Allah ya ƙara miki lafiya,” ya furta cikin muryarsa mai cike da ladabi da natsuwa.

Ta kallesa da ido biyu ido da ba sa ruɗu da son zuciya, ido da ya ga duniya da tarbiyyar daraja. Ta ɗaga hannunta, ta yi masa albarka, kafin ta zauna.

Bayan ta dafa cup ɗin tea da aka shirya mata, ta dan kurbi kadan, sannan ta ɗaga kai ta dubeshi kai tsaye, da harshen masu daraja

“As’ad,” ta fara da murya mai laushi, “ka daina tafiya da zuciyarka a gaba. Kai ba yaro bane. Ka farka. Ka duba matsayin da Allah ya ɗaukaka ka da shi. Ka duba irin darajar da gidan sarauta ya saka maka. Ka duba yadda duniya ke kallonka.”

Yayi shiru, ya sunkuyar da kai. Ita kuwa ta ci gaba da magana cikin Nutsuwa

“Na zauna da Firdausi dazu. Tana nuna min hotunan Ayshatu a Paris. Bakin wani teku. Da wani mai shigar zamani. Na kalle su da idona. Kai ne mutum mai tsarki? Kai ɗan musulmi ne? Mai daraja? To ina ganin hakan zai maka?”

“Ka sani,” ta ci gaba, “Ayshatu mace ce. Karancin shekaru da tunani sun yi mata yawa. Tana bukatar namiji mai hankali a kusa da ita wanda zai janta, ba wanda zai zagaya da ita. Kuma kai, da kanka kasanar da Mai Martaba cewa har yanzu ba ka da cikakkiyar lafiya. Ka na da ciwo. Shin wannan irin juyayi da kake ciki... zaka iya jure zama da mace kamar ita?”

As’ad ya dago a hankali. Murya da ta ƙunshi natsuwa irin ta ɗan sarauta, ya ce

“Hajja... Allah ya ƙara miki lafiya. Na saurare ki da zuciyata. Kuma gaskiya ne duk kalmomin ki. Amma bari na gaya miki, shekaran jiya kafin tafiyarta, maganar da muka yi ita ce mafi tsayi cikin duk wata muhawara da muka taɓa yi. Na sanar da ita da kaina cewa halin da nake ciki jiki da rai bai dace da in jawo ta cikin matsaloli na ba.”

Ya dan yi ajiyar zuciya. “Duk da haka, na ce mata in sauwake mata idan har zamana da'ita akwai cutarwa Amma ta ce... ita bata bukatar namiji yanzu. Kuma cikin kuka, ta roƙeni da na janye irin maganar nan gaba ɗaya.”

Hajja ta lumshe ido. Numfashinta ya sauka. Daga baya ta ce

“To. Idan hakan ne, to Allah yasa hakan shi ne alheri. Munyi waya da Amina ta ce zasu sauka nan da yamma. Kana da shirye-shiryen ganawa da su?”

As’ad ya ɗaga kai da kamewa. “Ina jiran su. Kuma ina fatan zasu same mu lafiya. Zan cigaba da karɓar shawara daga gare ki, Hajja. Kin fi kowa sanin da girma ya ke.”

Ta murɗa hannunta cikin nasa. “Wannan shi ne gatan rayuwa. Kada zuciyar ka ta dauke ka daga alkibla. Kai ɗan sarki ne. Amma kai ma mutum ne. Zuciya da ƙauna suna shigowa, amma darajar mutum tana cikin yadda ya sarrafa zuciyar sa da hankali.”

A nan sukayi shiru. Sai saukar iska ta shiga falon cikin sanyin AC mai ƙamshi da nutsuwa. Abincin da aka ajiye bai motsa ba. Zuciyar As’ad tana ta lissafi gaskiya, da natsuwa... ko idan hakan zai neme shi da hawaye.

Awanta guda tana zaune saman bene, ta jingina da jikin katanga, idanunta suna kallon ƙasa. Tana tunanin fitar As’ad kamar yadda ta saba gani duk safiya. A yau dai zuciyarta na cike da begen ganin gilmawar sa. Amma abin mamaki yau ko sautin takalminsa bata ji ba.

Sai zuciyarta ta cika da wani baƙin ciki da bata san asalin sa ba. Kamar a karye take. Kamar zuciyarta ta tsage. Da sauri ta miƙe, ta juya domin komawa ciki. Sai kuma ta hangi yayarta a bakin ƙofa tana kallonta da murmushi mai cike da raɗaɗi.

“Wato Haneefah... bazaki daina wahalar da zuciyarki akan yaya As’ad ba ko?”

Ta ƙarasa tana ɗaga gira.

“Wallahi iska ke wahalar da ƙara. Dan kuwa yaya As’ad ya daina kallonki tun da dadewa. Kina wahalar dakanki ne? Mutum wanda ya baku nisan da bazaki iya matso kusa da shi ba...!”

Haneefah ta fisge tsaki ta ce da karfi

“Ni na gaya miki shi nake kallo? Bazan zonan nasha iska ba!”

Yayarta ta juya, tana murmushi mai cike da raini “To, Allah ya ja da shan iska . Sai acigaba da shan iska.”

Taci gaba da tafiyarta, tana girgiza kai kamar mai tausayin ’yar uwarta. Haneefah kuwa ta tsaya tana binta da harara, zuciyarta cike da ɓacin rai. Ta dafe ƙirjinta kamar mai jin zafi daga ciki, sannan a hankali ta gangara daga saman bene.

Kamar an aikota, bata tsaya a ko’ina ba sai wajen shashen As’ad. Tana matakin kusantar ƙofar, sai zuciyarta ta buga da sauri. Amma Allah Ya taimake ta yawancin masu tsaro sun tafi sallah. Sai ‘yan fadawa kaɗan suka rage, suma ba su hanata shiga ba, ganin dai cewa ‘yar gida ce.

Kafin ta shiga, sai kuma ta tsaya cak. Ta jingina da bango, tana shan numfashi da ƙyar. Daga bisani ta fasa shiga gaba ɗaya, ta juya da hanzari kamar wadda taji wani abu ya faɗo mata.

Tana isa dakinta, ta rufta kan gado kamar wacce aka yi wa wani azaba. Ta fashe da wani irin kuka mai ƙuna, wanda yafi ƙarfin hawaye na fushi. Kukanta ba na jarumta bane, kukanta ba na kunci ba ne kawai kuka ne na tsantsar soyayya da begen wanda zuciya ta jingina da shi amma bai ma lura da hakan ba.

“I love him... ina sonsa sosai... wallahi bansan ya akayi ba. Amma zuciyata bata ƙara dukan kowa sai shi. Ashe haka ake jin ƙauna...?”

Kalmar “Yaya As’ad” tana yawo a bakinta kamar wani nau’in salati da take faɗa, domin ta samu kwantar da zuciya. Ta matso da bargo ta lulluɓe kanta gaba ɗaya. A cikin zuciyarta tana karanto addu’a ɗaya

“Ya Allah, Nayi kuskure abaya nayi kuskure wallahi amma ina kaunarsa ina sonsa ka sauƙaƙa mini hanyar samun sa.

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA TAMANIN DA BIYAR

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Zaune suke cikin babban falon da aka kawata da kayan alfarma tagogi masu fesa haske, labule masu kauri da walƙiya, da kayan zinariya a ko'ina. Hajja tana zaune bisa kujerarta mai kaurin tarihi, tana ɗaga murya kamar yadda ta saba idan tana magana da damuwa.

Abba ɗan sarki kuma yayan Firdausi ya zauna yana kallonta, hannunsa na kan cinyarsa, alamun cewa damuwa da ɓacin rai sun fara ƙaruwa. Firdausi kuwa na tsaye, tana girgiza kanta da hannayenta a kugu “Wai bazaki bar wannan maganar ba Firdausi?” Abba ya faɗa da ɗan ɗaga murya, idanuwansa sun cika da gajiya.

Firdausi ta tabe baki, ta ce da ƙarfi, “Hajja ki saurareni! NaranTSE miki da Allah Ayshatu yawon banza takeyi kawayenta duk lalatattu ne su kadai... Idan kun ƙi yarda da ni to ku kalla wannan hoton hannun wa ne a bayanta a bakin teku? Sai kuma ku ce nayi shiru? Wannan matar tuni na fahimta babbar asararriya ce!”

Hajja ta kalleta da nuna alamar kaɗan ke rage ta ɗaga mata murya. Amma Firdausi ba ta tsaya ba. “Kun manta mahaifiyarta fa? Ita ce tsohuwar wadda ta so ta mallaki sarki ta hanyar asiri. Da yaki, sai ta juya ta shirya karyar bashi aure har aka aura Ayshatu ga ɗanki? Wannan yarinya ta gaji halin mahaifiyarta yaudara da ƙwace zuciyar maza da wayo.”

Fuskar Abba ta canza. Duk da yana zargin Ayshatu da abubuwa tun can, musamman saboda abokansa biyu sun ce sun ganta a wani babban hotel da wani dattijo, amma zuciyarsa ba ta gama yarda ba. Duk da haka, a matsayin sa na cikakken ɗan sarki da masanin rayuwa, bai so ya yarda da zargi ba tare da hujja mai ƙarfi.

“Ki rufe bakinki, Firdausi,” ya ce da ƙarfin hali, “Matarsa ce fa! Kuma wallahi idan na sake jin kin ambaci sunanta da ƙarya ko rashin mutunci, sai na nuna miki ni waye. Kema ki sani, Allah yana saurare, yana gani. Zarginki zai iya kai ki ga zalunci.”

Firdausi ta dafe ƙirji, ta ce da zafin rai, “Ni fa gaskiya nake faɗa, Abba! Kawai saboda hajja ta ce ayi shiru shine zaku lallaɓata? Wannan lash money din Ayshatu ce fa lallai ba zai wuya ba bata yaudare yayana ba!”

Hajja ta ɗaga hannu da natsuwa, duk da fuskarta ta nuna ba farin ciki take ciki ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull