Kenza eBookz

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 6

Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 6

Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 6: Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 6. "Kada ki dade, kin san ke ce za ki dafa abincin dare."

4,478 words

"Kada ki dade, kin san ke ce za ki dafa abincin dare."

Na ce

"Ba matsala, Mumy."

Yayin da nake kokarin fita, sai ga Yaya Billy ta fito daga dakin ta cikin wani riga da wando na zamani mai kama da jumpsuit, ta kalle ni da dariya.

"Auta, ki jira, zan kai ki."

Na saki murmushi nace

"Aa, Yaya. Malam Idi direba zai kai ni."

Ta daga kafada cikin rikon lamarin:

"To, ba damuwa."

Na fito daga gida, iska tana kada gashina cikin sanyin yamma. Na isa bakin kofa, na ga Malam Idi yana jiran fitowata a gefen motar. Na shiga cikin motar cikin natsuwa, na ce

"Dan Allah, ka jira ni bayan na shiga gidan su Fatima. Ba zan jima ba."

Ya gyada kai cikin girmamawa.

Ina shiga cikin gidan su Fatima, sai ga ita da wasu kawayenmu na makaranta sun fito, kowacce cikin shigar zamani mai kayatarwa. Fatima ta hango ni ta saki murmushi.

"Ke! Nace wa Malam Idi yatafi, ki kwantar da hankalinki, zan dawo dake da kaina."

Na dan waro ido cikin mamaki.

"Amma na riga na ce masa ya jira ni..."

Fatima ta yi dariya

"Ki kwantar da hankalinki.”

Da na shiga part din Fatima a gidansu, hankalina ya yi mugun tashi. Na tsaya a bakin kofa ina kallon yadda su Teemarh da sauran kawayen Fatima suka yi shigar zamani, kowacce sanye da mini skirt da wata armless ta makale a jikinsu. Gaba daya yan ajinmu sun cika wajen, kowacce cikin kwalliya mai jan ido. Na tsinci kaina ina jin kunya kamar na yi wani laifi.

A daidai wannan lokacin ne na ji Wafiya, yar ajinmu, tana maganganu da muryar raini

"Ke Teemarh, ya zaki gayyato mana wannan yar kauyen? Duba wata shiga da ta yi!"

Na ji maganar Wafiya ta soki zuciyata kamar mashi. Cikin kankanin lokaci, wasu daga cikin kawayen suka fara kallona da harara, wasu kuma na murmushi irin na mugunta. Teemarh ta matso kusa da ni tana roko

"Dan Allah, ki taimaka ki saka kayan nan. Wallahi, ko hotuna ba za a yi ba. Kuma fa iya matane!"

Duk yadda ta yi magiya, na tsaya kai tsaye, zuciyata cike da kunya da tsoro. Sai ga Wafiya ta kara magana tana kallon ni da wani irin kallo mai cike da wulakanci

"To ita tasanya me? Matar da ko nonuwa bata faraba, babu wani shape, ba komai!"

Na ji kalmarta ta yi min zafi kamar wuta, raina ya baci sosai. Amma na karbi kayan da Teemarh ta ba ni na shiga daki na saka. Lokacin da na fito, sai na ji kunyar duniya ta lullube ni, don haka na zura abaya a kai. Duk yadda suka yi kokarin cire min, na ki. Karshe na ce wa Fatima

"Sai dai kawai na koma gida."

Fatima ta saki fuska cikin damuwa

"Aa, kada ki koma. A haka kawai mu tafi."

---

Abba yana dawowa gida ya fara tambaya inda nake. Mumy ta amsa cikin tsoro

"Wallahi, ban san inda ta tafi ba. Ba ta sanar da ni ba. Malam Idi ne ya ce tun karfe biyar ya kai ta gidan kawarta. Nace masa ya jira ta dawo, amma tace zata dawo da kanta.

Abba ya kashe wayar cikin takaici. Ya dube ta yana fadin

"Zainab, ya zaki bar yarinya har karfe goma na dare bata dawo ba? Gashi babu waya”

Mumy ta fashe da kuka tana cewa

"Abba, yanzu na lura cewa ta fara canzawa. Wallahi tsoro nake ji yanzu."

Abba ya sa hannu ya shafa kansa, yana jin zuciyarsa tana tafasa. Lokacin da karfe 12 ta kusa yi, ga shi momy ta dinga zugashi da cewa

"Kana gani, yarinyar nan tana neman lalacewa. Gaba daya ta canza!"

*****

Wurin ya cika da hayaniya da nishadi. Kowanne bangare yana da mutane cikin kwalliya, manyan yaran gari sun taru sosai. Na ji tsoro ya lullube ni ganin babu mai shiga irin ta ni. Wani saurayi ya nuna ni yana dariya

"Teemarh, wannan fa me aikin gurin ce?"

Teemarh ta amsa cikin dariya:

"Aa, kawata ce."

Na tsinci kaina cikin kunya mai tsanani, zuciyata tana dukan uku-uku.

Kawai sai na ji wani ya rungume ni ta baya. Na waigo cikin tsananin mamaki, ashe Fareed ne! Cikin fusata na tureshi ina masifa

"Me haka? Me yasa kake min haka?"

Ya tsaya yana kallona kamar zai yi kuka.

"Dan Allah ki yi hakuri. Wallahi, ban nufi cutar ki ba."

Ya tsugunna yana mikon flower hannunsa yana dariya har da hawaye. Cikin wannan lokaci, MC ya fara yabonmu yana cewa

"Ah, yau an samu sabuwar soyayya a gurin!"

Na yi murmushi duk da kunyar da nake ji. Fareed ya karaso kusa da ni yana narkar da kalamai masu dadi. A haka muka zauna guri daya.

Bayan dan lokaci, aka kawo min snacks da drinks. Ina jin wani abu ya taso daga cikina kamar jiri. Nace masa ya dakata da dan jira. Sai na yi dabara na ce

"Zan je na sallami driver."

Fareed ya amsa cikin fara'a:

"To, ni zan raka ki."

Na samu nasarar fita daga cikin gida, amma sai Teemarh ta ce

"Wallahi, mun riga da mun sallami Malam Idi."

***

A lokacin ne na gane cewa dare ya yi sosai. Kamar an doke ni da tsoro, na cire takalmina na fara gudu. Na yarda cewa ni 'yar kauye ce, amma wannan kunya ta fi karfina. Har na fara ganin titi babu mota, na yi kokarin tsallaka, amma jiri ya kwashe ni har na sulale akasa. Na rasa yadda zan yi, kuka na ratsa zuciyata, zuciyata na bugawa kamar ana kokarin tsaga kirjina.

Baiwar Allah! Ban san yadda nake ba, amma dai na ji kamar numfashina yana neman daukewa. Na tsinci kaina a kwance a gefen titi, sanyi yana shigar jikina har cikin kasusuwa. Kamar mafarki nake yi—wani abu mai nauyi yana dannawa a kirjina, yana hana ni yin motsi ko ɗaya.

A nan ne na fara jin wani ƙara yana kusantowa, kamar na mota. Sai ga haske ya bayyana a fuskata. Na so in yi ƙoƙarin miƙewa, amma sai jiki na ya ƙi bani damar yin komai. Na ji horn yana ƙara ƙarfi, amma ko kaɗan ba zan iya motsawa ba.

Na ji muryar wani mutum yana masifa daga cikin mota

"Ke! Wacce irin mahaukaciya ce ke kwance a titi haka? Ba kya jin horn ne?"

Ina cikin kokarin bude ido na gane muryar, sai kawai na ji ya ƙaraso kusa da ni. Ya durƙusa yana girgizani, yana cewa

"Ramlah! Ramlah! Ya salam! Me ya same ki?"

Daga nan na ji ya dauke ni da hannayensa biyu, yana saka ni a cikin motarsa da sauri. Da alama hankalinsa ya tashi sosai, don na ji yadda zuciyarsa ke bugawa. Ya shiga mota, yana ta faman danna burƙi kamar zai fasa.

Daga cikin kunnuwana, na ji yana ta ambaton sunana, yana roƙon Allah

"Ya Allah! Kada ka jarabce ni da wannan masifa. Don Allah, Ramlah, ki tashi."

Daren ya yi tsawo sosai. Bansan yaushe muka isa gida ba, amma na ji lokacin da Khalil ya danna horn da ƙarfi. Mai gadi ya fito da sauri, yana tambaya

"Wa ne haka da wannan hayaniya?"

Khalil ya ce

"Ni ne, Khalil! Bude mana!"

Da sauri mai gadi ya buɗe ƙofar, Khalil ya fito daga motar yana kiran Abba da gaggawa.

"Abba! Abba! Ga Ramlah nan!"

Na ji muryar Abba tana matsowa kusa, cike da damuwa.

"Khalil, me ya faru da ita? Me ya kai ta titi wannan lokaci?!"

Cikin rawar murya, Khalil ya ce

"Wallahi, Abba, na same ta ne kwance a gefen titi. Bana tunanin tana cikin hayyacinta."

Na ji yadda zuciyar Abba ke bugawa da ƙarfi, yana cewa

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ramlah! Me yasa za ki fita haka cikin dare?"

Muryar Mumy ta biyo baya cikin kuka.

"Abba, na ce maka fa, yarinyar nan ta fara canzawa! Wannan ai ba dabi'arta ba ce!"

Na ji kalamanta sun tsaga zuciyata. Cikin wannan mawuyacin hali,Cikin in’ina na yi ƙoƙarin buɗe ido, amma na kasa. Na ji muryar Abba tana ratsa kunnena kamar tsawa

"Subhanallah! Ramlah! Wannan wanne irin hali ne? Me ya kai ki titi cikin wannan yanayi?"

Ina kokarin magana, amma bakina ya mutu. Na yi ƙoƙarin furta wasu kalmomi, amma sai kawai na ce cikin rauni

"Abba... ni... ni... Fatima ce..."

Kawai sai na ji hannunsa ya buge gefen fuskata da wani lafiyayyen mari. Garin tangal-tangal na bugu, sai na sulale ƙasa, amma ina jin yadda yake ƙara masifa

"Wallahi yau sai na koya miki hankali! Kinaso ki maida ni abin dariya a gari?"

Na san Abba yana cikin tsananin fushi, amma jikina ya kasa tashi. Na ji Khalil yana cewa

"Abba, kayi haƙuri, don Allah! Ba ta cikin hayyacinta!"

Amma Abba bai saurare shi ba. Sai kawai ya sake fincikoni daga ƙasa, yana fizgar rigata kamar kayan wanki. Ji nake kamar numfashina yana tafiya, amma na kasa magana.

"Ramlah! Kin ci amanata! Na tsare ki, amma kika fita cikin wannan shiga?"

Duka yake ta faman kai mun, ko ina na jikina yana ciwo. Na san Abba yana cikin fushi, amma ni kam kwayar da na sha ta hana ni fahimtar abubuwa. Sai dai kawai na yi murmushi, idanuna suna juya, na furta

"Abba... ni... ni ba laifi na bane... Fatima ce... Fareed..."

Abba ya sake kai min wani duka a kai. Na ji wani irin ƙara a cikin kwakwalwata, na yi ƙoƙarin miƙewa, amma duniya ta birkice. Na faɗi ƙasa, zuciyata na neman tsayawa.

Ina jiyo muryar Khalil yana kuka, yana cewa

"Abba, ta daina motsi!"

Na ji Khalil yana cewa cikin kuka

"Abba, don Allah, ta daina numfashi! Mu tafi asibiti!"

Na san Abba yana tsaye a gurin, yana tunanin wani abu. Amma duk da haka, babu wanda ya motsa ni ko ya taimaka mun. Abba na ta faman sauke ajiyar zuciya, kamar wanda ya yi nadama, amma bai ɗagani ba.

Ji nake kamar ƙwaƙwalwata na tsagewa, kuma zuciyata tana tsinkewa da raɗaɗi.

A hankali na ji Khalil yana magana da Momy da Bilkisu. Momy ta ce

"Ko dai kai ma kana cikin wannan shirmen nata ne? Khalil, kana son kare yarinyar da ta lalace!"

Khalil ya amsa da murya mai kaushi

"Momy, Ramlah ba haka take ba. Ku dai kuna neman ganin ta wargaje ne don ku samu farin ciki!"

Momy ta yi tsaki, tana cewa

"Kai dai kana kare lalatacciya. Na ji Khalil yana furta

"Wallahi, Ramlah ba haka take ba.”

kwayar da na sha ta sake mamaye ni, na ji idanuna sun rufe gaba ɗaya. Duniyar ta koma duhu.

Cikin in’ina na yi ƙoƙarin buɗe ido, amma na kasa. Na ji muryar Abba tana ratsa kunnena kamar tsawa

"Subhanallah! Ramlah! Wannan wanne irin hali ne? Me ya kai ki titi cikin wannan yanayi?"

Ina kokarin magana, amma bakina ya mutu. Na yi ƙoƙarin furta wasu kalmomi, amma sai kawai na ce cikin rauni

"Abba... ni... ni... Fatima ce..."

Kawai sai na ji hannunsa ya buge gefen fuskata da wani lafiyayyen mari. Garin tangal-tangal na bugu, sai na sulale ƙasa, amma ina jin yadda yake ƙara masifa

"Wallahi yau sai na koya miki hankali! Kinaso ki maida ni abin dariya a gari?"

Na san Abba yana cikin tsananin fushi, amma jikina ya kasa tashi. Na ji Khalil yana cewa

"Abba, kayi haƙuri, don Allah! Ba ta cikin hayyacinta!"

Amma Abba bai saurare shi ba. Sai kawai ya sake fincikoni daga ƙasa, yana fizgar rigata kamar kayan wanki. Ji nake kamar numfashina yana tafiya, amma na kasa magana.

"Ramlah! Kin ci amanata! Na tsare ki, amma kika fita cikin wannan shiga?"

Duka yake ta faman kai mun, ko ina na jikina yana ciwo. Na san Abba yana cikin fushi, amma ni kam kwayar da na sha ta hana ni fahimtar abubuwa. Sai dai kawai na yi murmushi, idanuna suna juya, na furta

"Abba... ni... ni ba laifi na bane... Fatima ce... Fareed..."

Abba ya sake kai min wani duka a kai. Na ji wani irin ƙara a cikin kwakwalwata, na yi ƙoƙarin miƙewa, amma duniya ta birkice. Na faɗi ƙasa, zuciyata na neman tsayawa.

Ina jiyo muryar Khalil yana kuka, yana cewa

"Abba, ta daina motsi!"

Na ji Khalil yana cewa cikin kuka

"Abba, don Allah, ta daina numfashi! Mu tafi asibiti!"

Na san Abba yana tsaye a gurin, yana tunanin wani abu. Amma duk da haka, babu wanda ya motsa ni ko ya taimaka mun. Abba na ta faman sauke ajiyar zuciya, kamar wanda ya yi nadama, amma bai ɗagani ba.

Ji nake kamar ƙwaƙwalwata na tsagewa, kuma zuciyata tana tsinkewa da raɗaɗi.

A hankali na ji Khalil yana magana da Momy da Bilkisu. Momy ta ce

"Ko dai kai ma kana cikin wannan shirmen nata ne? Khalil, kana son kare yarinyar da ta lalace!"

Khalil ya amsa da murya mai kaushi

"Momy, Ramlah ba haka take ba. Ku dai kuna neman ganin ta wargaje ne don ku samu farin ciki!"

Momy ta yi tsaki, tana cewa

"Kai dai kana kare lalatacciya. Na ji Khalil yana furta

"Wallahi, Ramlah ba haka take ba.”

kwayar da na sha ta sake mamaye ni, na ji idanuna sun rufe gaba ɗaya. Duniyar ta koma duhu.

Fareed yana tsaye a bakin ƙofar gidan, zuciyarsa kamar ta fashe saboda takaici. Idanunsa sun yi ja, yana huci kamar maciji. Ya dinga tafiya sama da ƙasa tamkar wanda aka turo cikin bala'i.

Yana cikin wannan yanayi, sai ga Fatima ta fito da sauri, tana ƙoƙarin yi masa magana.

"Fareed, don Allah kayi haƙuri. Ba ka ga yadda ta gudu ba? Ni ma ban san ta tsere ba."

Fareed ya dakatar da ita da tsawa, yana harararta da fuska a tamke.

"Ke! Kina da hankali kuwa? Kwanan nan kika ce min komai na hannunki! Ashe karya kike? Kina ganin irin kwayar da na sha kuwa? Ita kanta kwayar da kika saka mata ta fi tsada fiye da yadda kika tsara! Yaushe ta sami ƙarfin guduwa bayan na gama saka mata?"

Fatima ta marairaice, tana ƙara matsowa kusa da shi.

"Don Allah, kayi haƙuri. Wallahi, ban san ta tsere ba. Na rantse maka, har hotel zan kawo maka ita, ka kwantar da hankalinka."

Fareed ya yi wata irin dariya mai ciwo.

"Hotel kuma? Bayan ta riga ta gudu? Ke baki san halin da nake ciki ba! Ba ki fahimci yadda kwayar nan ke aiki ba? Me yasa kika bar ta ta tsere?"

Fatima ta kai hannu tana ƙoƙarin rike shi, amma ya ture ta da hannu ɗaya.

"Ni narasa uban me yake cikin jikin wannan Ramlah ɗin da zaka damu da ita haka! Kai! Ko nonuwa cikakke bata da su!"

Fareed ya sake yin tsaki, yana huci kamar zai fashe. Fatima na cigaba da bashi haƙuri, amma ya ja tsaki ya bar wurin cikin bacin rai, yana cigaba da surutai.

****

A ganinku, shin Ramlah ta yi kuskure da amincewa da gayyatar Fatima?

Me kuke tunani game da yadda Abba ya yi fushi? Shin akwai wani uzuri da zai iya saukaka hukuncinsa?

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA GOMA SHA BIYU.

Gidan Mai Martaba Sarki ya cika da mutane. Kowa na cikin shiga ta alfarma, rawanin sarauta da shaddodi masu walkiya sun cika harabar fada. Manyan baki sun hallara don halartar daurin aure. As’ad, ɗan sarki, ya fito daga sashensa cikin shadda light blue mai ɗaukar ido. Ya sanya hula a kansa, domin ba ya son rawani kwata-kwata yana jin nauyinsa sosai.

Sai dai duk da wannan kyakkyawar shiga, fuskarsa cike take da damuwa. Ba auren kansa ke damunsa ba Haneefa ce, wacce zai aura. Tana ɗiya ga Fulani Maryam, autarsu mahaifinsa mai martaba, mace mai zafin zuciya da rashin kirki. Tun yana yaro As’ad ya san Fulani Maryam da mahaifiyarsa basu ga maciji ba, kuma Haneefa ta ɗauki wannan gaba da muhimmanci kamar gadon kabilanci.

As’ad bai taɓa yin zaɓi ba tun yana ƙarami. Umarnin fadar sarauta tamkar doka ne gare shi, kuma ba shi da ƙarfin musantawa. Duk da haka, zuciyarsa tana kuka.

"Ba zan taɓa samun mace kamar Ayshatu ba," ya furta a hankali, yana mai shafa sumar kansa da hannunsa mai ƙarfi. Duk da haka, dole ne ya amince da kaddara.

Da ya isa fadar, ya shiga ya gaida kowa, sannan ya samu guri ya zauna. An yi dukkan al’adar sarauta, ana kabbara da addu’o’i. Limamin fada ya ɗaga murya

"An daura auren As’ad ɗan Mai Martaba da Haneefa ‘yar Fulani Maryam bisa sadaki naira dubu dari biyar."

Mutane sun yi ihu na murna, amma ba kowa bane ya nuna farin ciki da gaske. Wasu na ganin As’ad bai da kirki sosai wajen kula da mata, domin yana da tsananin son girmamawa. Sai daidaikun makiya suka yi murmushi, suna ganin shi ma ya samu matar da za ta yi masa galaba.

Da As’ad zai tashi ya bar gurin, Sarki ya yi masa nuni da hannu ya zauna. As’ad ya sunkuyar da kansa cikin girmamawa.

"As’ad," Mai Martaba ya fara da murya mai cike da izza, "ka sani, wannan aure amana ce gareka. Kada ka manta, yar uwarka ce kuma diya ga wacce na fi so a gidan nan Fulani Maryam. Kula da ita kamar yadda kake kula da kanka."

As’ad ya ɗaga kai cikin ladabi. "To ranka ya daɗe."

Sarki ya cigaba, "Na ba da izinin a buɗe mata ɗaya daga cikin shashenka. Za a gyara shi yadda ya dace, kuma duk abin da take bukata zan sa a zuba mata. Ka tabbatar kana kula da ita kamar yadda ya kamata."

As’ad ya amsa da girmamawa, amma zuciyarsa na cike da mamaki da takaici. Waziri ya danyi dariya a gefe, ya ce, "Yallabai, wannan al’amari yana buƙatar hikima."

As’ad ya yi ajiyar zuciya. "Waziri, ba na ganin zan iya rayuwa da mace kamar Haneefa. Halayyarta tamkar na mahaifiyarta ce."

Waziri ya yi murmushi mai ma’ana. "Kai dai ka yi haƙuri, Yallabai. Soyayyar sarauta tamkar lauje ne cikin naɗi. Ka ɗauki wannan al’amarin da hikima."

Bayan shagulgulan daurin aure sun lafa, As’ad ya koma sashensa, yana tunanin yadda zai iya rayuwa da Haneefa.

Cikin Masarauta, gidan Mai Martaba ya gauraye da murnar daurin auren As’ad da Haneefa. Fada na cike da ƙamshi da kyakkyawan tsari na sarauta. Fulani Maryam tana zaune cikin wata rumfa, tana tattaunawa da iyalai da danginta. Fuskar ta cike da annuri, tana jin burinta ya kusa cika.

Haneefa na kusa da ita, sanye da alƙyabba mai sheƙi, tana murmushi. Ta kalli mahaifiyarta, tana dariya.

"Mama, bari na tafi wurinsa yanzu."

Yayarta ta kalleta da tsawa, "Ke Haneefa! Bakida kamun kai ne? A haka zaki je wurin mijinki?"

Cikin tsananin fitsara, Haneefa ta watsa mata harara. "Ke kuma, me ya dameki? Ai yanzu ni matar As’ad ce!"

Fulani Maryam ta gyara zama, ta ɗaga hannu. "Ku yi shiru! Ba yanzu ba, ki jira. Ni zan turaki daga baya. Yanzu ki bar wannan zancen."

****

Dare na yi, Fulani Maryam ta shirya cikin baƙar alkyabba, ta bar fadar cikin wata mota mai ƙyalli. Tafiyarta ta kai ta wani wuri mai nisa, can gefen gari, inda tafkeken daji ya mamaye ko'ina. Da ta isa, ta tsayar da motar ta. Ta kalli duhun da ke gaba da ita, sannan ta taka ƙasa a hankali.

Ta isa tsakiyar fili, ta durƙusa, sannan ta buga ƙasa sau uku da sanda. Nan take, ƙasa ta fara girgiza, iska ta canza zafi. Wani halitta ya bayyana mutum kamar ba mutum ba, yana dariya mai razana, idanuwansa ja kamar wuta.

Ya kalle ta da murmushi mai ban tsoro.

"Menene diyarmu? Me zaki bayar kafin mu saurareki?"

Fulani Maryam ta ciro wata ƙaramar ƙwalba daga aljihunta, tana murmushi mai cike da mugunta.

"Ga jinin jikata ga gashinta na ciro. Jikar tawa dake jinya a asibiti. Ba ta da tsari, ba ta da ibada. Halak malak!"

Halittar ya danyi tsalle mai ban tsoro, yana dariya.

"Mun karɓa! Aikinki ya cika. Me kike so daga garemu?"

*****

Ta gyara rawaninta, ta kwantar da murya cikin izza.

"An daura auren diyata da As’ad. Ina so ya zama tamkar bawa gareta. Ya ƙaunace ta fiye da kowa. Idan da hali, ka fitar masa da mazantakarsa gaba ɗaya. Kuma ka yi masa ciwon da zai dinga sassaka shi lokaci bayan lokaci."

Mutumin ya tsaya yana nazari, yana mai buga ƙasa da sanda.

"Aikinki mai wahala ne. Munganshi yana da tsari, yana da ibada. Amma naga wata kafa. Lokacin da sha’awarsa ta motsa ko yana cikin tsananin fushi, baya ambaton Allah. Wannan ne lokacin da za mu iya galaba kansa."

Ya fiddo da wani ɗan ƙaramin ƙwalba mai ƙamshi mai kashe tunani.

"Wannan turare za ta shafa a jikinta kafin ta kusance shi. Zai rude da ƙauna gareta. Wannan kuma garin abinci ne idan ya ci, gabasa zai mutu har abada. Amma kafin hakan ya faru, sai ta sa shi ya kusance ta gabanta. Daga nan, sai abinda tace masa."

Fulani Maryam ta yi dariya mai cike da farin ciki.

"Yanzu dai burina ya cika! Haneefa za ta mallake shi har abada."

Mutumin ya yi wata dariya mai cike da zafi.

"Amma ki kula idan ya samu nutsuwa ko ya yi ibada a lokacin da turaren ke jikinsa, to komai zai wargaje dole sai tana shagalar dashi."

Fulani Maryam ta ɗauki kayan tana murmushi, sannan ta juya ta tafi cikin annashuwa. A ranta tana jin cewa yanzu As’ad ba zai taɓa samun kwanciyar hankali ba.

Shin wannan mugun shiri zai yi tasiri ga As’ad?

******

Da As’ad ya koma ɗakinsa bayan taron fadar, jikinsa ya yi nauyi kamar an ɗora masa dutse. Zuciyarsa tana cike da tunani, yayin da wani mugun ciwon kai ya fara tasowa. Yana jin tamkar duniya ta nannade shi. Ya cire hularsa, yana shafa sumar kansa, sannan ya nufi bayi ya yi wanka mai sanyi domin samun nutsuwa.

Ya fito daga wanka yana ɗan jin sauƙi, sai ya kwanta a kan katifar alfarma mai laushi. Ba a jima ba ya fara jin nannauyar bacci na ɗaukarshi. A lokacin da yake cikin barcin, sai ya ji wayarsa tana ƙara. Da farko kamar ba zai ɗauka ba, sai kuma ya miƙa hannu ya ɗauki wayar daga bedside. Ya dubi sunan da ya bayyana akan allon Ayshatu.

Nan take zuciyarsa ta yi wata irin kuna, amma sai ya daure, ya danna kiran.

"As-salamu Alaikum," ya furta cikin raunin murya.

Jin kukanta ne ya kara ƙara masa ciwon kai. Ya dafa kansa, yana mai jan numfashi.

"Habibie... me ya sa? Me yasa?" Ayshatu ta furta cikin kuka mai cin rai.

As’ad ya katseta cikin sanyin murya.

"Ki yi haƙuri, Ayshatu... banda iko ne."

Ayshatu ta yi shiru na ɗan lokaci, sai kuma ta fashe da sabon kuka.

"Yanzu haka za ka bar ni? Habibie... me yasa?"

Ya lumshe idanunsa, yana jin tamkar ana tsinke masa zuciya.

"Kitayani biyayya, Ayshatu. Nasani, ke yar albarka ce. Banda yadda zan yi."

Kukanta ya ƙara ratsa zuciyarsa, amma ta san cewa duk maganarta ba za ta canza komai ba. Ta yi shiru tana sharɓar kuka har ta gaji, sannan ta yi sallama a hankali.

As’ad ya jingina kansa da gado, yana jin zafin abin da ba shi da ikon gyarawa.

A gefe guda kuma, a cikin ɗakin Fulani Maryam, Haneefa tana ta kai-kawo, fuskarta cike da rashin jin daɗi.

"Mama, wai bazan je wajensa ba? Tun dazu nake roƙon ku, amma kun hana ni. Wallahi bazan iya jurewa ba, ina son ganin shi!"

Fulani Maryam ta kalleta cikin murmushi mai cike da mugunta. "Ki kwantar da hankalinki, diyata. Na san abin da nake yi."

Ta miƙa mata wani ɗan ƙaramin ƙwalba. "Ga wannan turaren, ki shafa a hannunki kafin ki tafi. Sannan ki rungume shi da ƙarfi idan kin shiga. Wannan ne sirrin nasara."

Haneefa ta amshi turaren tana murmushi. "Na gode Mama! Yanzu na tabbata zai soni."

Ta juya da farinciki, tana shirye-shiryen tafiya.

****

A cikin ɗakin Hajja, Fiddausi ta shigo da fuskar baƙin ciki.

"Hajja, kina gani kuwa? Haneefa ce za a ba yaya As’ad? Wallahi wannan zalunci ne!"

Hajja ta yi ajiyar zuciya. "Ku yi masa addu'a kawai, Fiddausi. Ko ni mahaifiyarsa bai saurare ni ba. Wannan al'amari ya riga ya zama doka."

Fiddausi ta tura baki, tana fadin, "Amma Hajja, ai wannan auren ba daidai bane. Fulani Maryam fa? Wace uwa ce zata so haɗa zuria da ita?"

Hajja ta dube ta da ido masu nuna damuwa. "Ki rabu da maganar nan, Fiddausi. Na faɗa miki tun farko Sarki ya riga ya yanke hukunci. Kaddara ce."

Fiddausi ta yi tsaki, tana jin takaici. "Wallahi wannan abu bai min daɗi ba."

Hajja ta ce, "Ki yi haƙuri, ki bar komai ga Allah. Ba mu da wani zaɓi."

Sashen As’ad cike yake da yalwar dukiya da tsari irin na sarauta. Babban falonsa yana sheƙi da fitilar zinariya, kujeru masu ɗaukar ido suna zagaye da teburin da aka kawata da tulunan furanni. Daga gefe kuma, akwai tagogin gilashi masu tsawo da ke kallon lambun gidan. As’ad yana tsaye a gefen tagar falon, yana waya da Waziri, yana tattaunawa da shi cikin murya mai cike da girmamawa.

Yayin da yake cikin wannan yanayi, sai ya ji wani ƙamshi mai daɗi ya cika falon. Ya dan waigo da kai kadan amma bai ga komai ba, sai ya cigaba da wayarsa. Amma kafin ya ankara, sai kawai ya ji hannaye masu laushi sun zagaye bayansa, suna rungume shi da ƙarfi.

Tamkar an zuba masa ruwan sanyi haka ya ji, jikin sa ya yi matuƙar tsuma, zuciyarsa ta buga da sauri. Wani irin raɗaɗi ya sauka a kansa kamar an danna masa ƙaya. Ya juya da sauri cikin zafin nama, yana ƙoƙarin tureta, hannunsa har ya ɗaga tamkar zai kai mata mari.

Kafin ya kai hannunsa ga fuskarta, sai kawai ta ƙara manne masa, tana rungume shi da ƙarfi fiye da da. Jikinsa ya mutu, hannunsa ya yi sanyi, tamkar an cire masa kuzari. Ya kasa dukan ta.

Cikin murya mai raɗa, Haneefa ta furta,

"Ranka ya daɗe..."

Bai san lokacin da ya furta "Uhmm..." ba, yana kallonta da idanuwansa da ke kokarin sauyawa gaba ɗaya.

Haneefa ta ɗago da kai daga ƙirjinsa, tana kallonsa da murmushi mai cike da mugunta da salo. Idanunta suna ƙara narkar da zuciyarsa tamkar an zuba masa ruwan zuma.

"As’ad... Na kasa samun nutsuwa ne."

Yana ƙoƙarin yin magana, amma muryarsa ta yi rauni. "Haneefa... me kike yi haka?"

Ta ɗora hannunta a ƙirjinsa, tana wasa mai laushi. "Na san kai mijina ne. Na san cewa dole ne mu kasance tare. Ina son ka."

As’ad ya kalli hannunta a jikinsa, zuciyarsa na rawa. Ya yi ƙoƙarin tura ta a hankali, amma sai kawai ya ji tamkar ƙarfinsa na raguwa.

Haneefa ta murmusa, ta ƙara lallaɓa ta matsa kusa, tana fitar da numfashi a hankali kusa da kunnensa.

"Ranka ya daɗe, ba na so ka ji damuwa. Ni zan yi maka duk abin da kake so."

As’ad ya rintse idanuwa, yana jin tamkar wani kulle ya ɗaure masa zuciya. Duk ƙoƙarinsa na tsayayya ya gagara.

Nikam nace As'ad har ankamu Ne????

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA GOMA SHA UKU

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull