Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 8
Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 8: Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 8. As’ad ya shiga falon cikin nutsuwa, yana sanye da riga mai launin…
4,464 words
As’ad ya shiga falon cikin nutsuwa, yana sanye da riga mai launin rawaya da alkyabba mai ruwan gwal. A bayansa, Haneefa ce cikin doguwar riga mai launin ja, kanta a duƙe, tana biye da shi a hankali.
Hajja, matar sarki kuma uwar gida, tana zaune bisa kujerar alfarma, tana duba wani littafi na addu’a. Tana ganin su sun shigo, sai ta saki murmushi mai cike da kulawa.
"As’ad ɗana, kun shigo lafiya."
As’ad ya rusuna da ladabi. "Hajja, ina kwana?"
Haneefa ta duƙa a gefensa cikin ladabi. "Ina yini Hajja."
Hajja ta gyada kai cikin murmushi. "Lafiya kalau, ku zauna."
As’ad ya zauna a kujerar kusa da Hajja, yayin da Haneefa ta tsaya a gefensa, tana daidaita mayafinta da natsuwa.
Hajja ta dubi Haneefa cikin kulawa. "Haneefa, ya gida?”
Haneefa ta sunkuyar da kai. "Alhamdulillah, Hajja. muka yanke shawarar zuwa gaishe ki."
Hajja ta yi murmushi. "Nagode da girmamawa. Allah ya albarkace ku."
"As’ad, bakada lafiya ne” Hajja ta tambaya, tana kallonsa cikin kulawa.
As’ad ya gyada kai a hankali, amma idanunsa suna kallon Haneefa kamar mai bin umarni. Haneefa ta dan kalli As’ad ta gefen ido, ta saki murmushi kadan.
Hajja ta daidaita zamanta, tana kallon yadda As’ad ke zaune tamkar wanda aka ja da igiya. Idanunsa sun lumshe kadan, kamar mai cikin bacci, amma duk lokacin da Haneefa ta motsa, sai ya bita da kallo.
"Ya As’ad, lafiya kuwa?" Hajja ta tambaya cikin damuwa.
Ya ɗan gyara zama. "Lafiya, Hajja."
Haneefa ta katse shi da sauri cikin murmushi. "Eh, Hajja. As’ad yana gajiya ne."
Hajja ta kalle su duka biyu, tana jin tamkar akwai wani abu da ba dai-dai ba. Amma saboda nutsuwar Haneefa da ladabin da ta nuna, sai ta dan rage zargin da take yi.
Bayan sun gaisa, Haneefa ta ɗan matso kusa da As’ad, ta dafa kafadarsa da natsuwa. "My Kankan, tashi mu tafi ko? Ka san dai Hajja na bukatar hutu."
As’ad ya mike kamar wanda aka umarta, yana kallonta da murmushi mai rauni. "To, Haneefa."
Hajja ta yi murmushi mai cike da damuwa. "Kuna tafiya kenan?"
Haneefa ta gyada kai. "Eh, Hajja. Sai mun sake dawowa daga baya. Allah ya kara lafiya."
"As’ad, kada ka manta ka dawo kusa dani idan ka samu lokaci."
As’ad ya sunkuyar da kai. "Zan dawo, Hajja."
Yayin da suke fita daga fadar, Hajja ta tsaya kallon su har suka bace daga gani. Ta sauke numfashi mai nauyi, tana jin wani abu yana damunta.
"Ya Allah, ka tsare ɗana daga sharrin komai," ta furta a hankali.
******
A cikin ɗaki mai faɗi na fadar sarauta, wanda aka kawata da kyandirori masu ƙamshi da zanen zinariya, Fulany Maryam tana zaune bisa wata shimfiɗa mai launin ja. A gefenta, matar da ke taimaka mata tana durƙushe, tana haɗa wani magani a cikin ƙwarya mai faɗi.
Fulany Maryam ta gyara zamanta cikin izza, tana mai dariya mai ɗauke da tsana. "Daga nan za a tabbatar da cewa Hajja ba za ta sake jin daɗi a rayuwa ba. Na sa aka yi wannan aure ne domin na wulakanta ta da ɗanta gaba ɗaya."
Matar ta ɗago kai cikin alamar damuwa. "Amma Fulany Maryam, idan har maganin nan ya yi tasiri ya hana shi aiki gaba ɗaya, Haneefa fa zata iya guje shi. Kinsan dai Haneefa da son maza."
Fulany Maryam ta kyalkyale da dariya mai cike da izza. "Ke dai ba kya gane wayon mugunta! Da haka nake so! Idan As’ad ya zama marar amfani gaba ɗaya, Haneefa za ta fara tsanar shi. Kuma idan har ta guje shi, hakan zai zama babbar tozarci ga Hajja."
Matar ta ƙara dubanta cikin tsoro. "Amma Fulany Maryam, kin san cewa yanzu Haneefa ta nutsu sosai. Da alama Allah ya taimake ki, ta daina yawon banza. Amma idan maganin nan ya hana As’ad aiki gaba ɗaya, ba kya ganin hakan zai iya haifar da matsala?"
Fulany Maryam ta harare ta, tana nuna rashin jin daɗi. "Ke kuwa ba kya gane komai! A cikin cikar burina, har ɗiyata ba zan bar ta ba. Na sa aka yi wannan auren ne don ganin Hajja ta rasa dukkan farin cikinta. Kuma idan hakan ya faru, zan tabbatar da cewa As’ad ya zama kamar cikakkiyar mace.
Matar ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ce, "Amma idan hakan ya faru, ko Haneefa ta guje shi, ya kike ganin za a fahimci hakan? Sarki fa zai iya gano cewa akwai wata mugunta a baya."
Fulany Maryam ta ɗaga kai cikin izza, tana dariya mai sauti. "Ai shi ne burina! Na tabbatar cewa da zarar Haneefa ta rasa jin daɗin zama da shi, zata yi kuka ta fice daga gidan. Hajja za ta rasa ƙaunar ɗanta kuma sarki da kansa zai nisanta kansa da shi. Kuma idan hakan ya faru, zan tabbatar da cewa As’ad ya zama tamkar wata cikakkiyar mace, marar amfani, wacce babu mace da zata iya zama da shi."
Matar ta ɗan ja baya cikin tsoro. "Amma Fulany Maryam, idan har hakan ya sa As’ad ya haukace, hakan zai iya zubar da mutuncin gidan sarauta."
Fulany Maryam ta yi dariya mai tsanani. "Ba ruwana da mutuncin gidan sarauta. Ni dai burina shi ne in ga Hajja da ɗanta sun wulakanta, sun rasa farin cikinsu. Zuciyata ba za ta huta ba sai na tabbatar da cewa As’ad ya zama marar amfani. Idan hakan ya faru, zan tabbatar da cewa ko wata mace ba za ta iya zama da shi ba."
Matar ta dubi Fulany Maryam cikin mamaki. "Me yasa kika tsani Hajja haka Fulany Maryam? Ai da alama ba ta yi miki komai ba."
Fulany Maryam ta tsuke fuska tana jan numfashi. "Ke dai ba kya gane wayon zuciya. Tun farko Hajja ba 'yar sarauta bace. Ba ta fito daga gidan masu mulki ba. Soyayyar sarki ce kawai ta kawo ta fada. Ta kwace min duk wata kulawa da girma da na kamata in samu. Ai ni ce ya kamata in zama mai juya duk matan sarkin amma ita Banda ita!"
Matar ta saki baki tana jin mamakin yadda mugunta ta ratsa zuciyar Fulany Maryam. "Amma Fulany Maryam, idan aka gano wannan makircin, faɗar sarauta za ta girgiza."
Fulany Maryam ta yi tsaki. "Ai duk wanda ya gano, na riga na shirya yadda zan rufe bakin sa. Babu wanda zai iya kawo ƙarshen wannan makirci nawa!"
****
Gidan sarauta ne mai cikakken tsari da alfarma. Masallacin fada yana kusa da babban zauren taro, shimfidarsa tana cike da jajayen kafet masu tsari na alfarma. Fitilu masu walƙiya suna haska harabar masallacin, yayin da ƙamshin turaren Misira ke tashi a ko’ina.
As’ad ya kammala alwala cikin nutsuwa, ya shiga masallaci don yin sallar Isha’i. Bayan ya gama salla, ya ɗauki alƙur’ani don yin karatu. Amma da ya bude shi, sai ya ji wani irin nauyi yana ratsa jikinsa.
Ya yi kokarin karanta Suratul Fatiha, amma bakinsa ya kasa furta komai. Yana jin kamar wani abu ya ɗaure masa harshe. Ya lumshe ido, yana neman kwanciyar hankali, amma ya gagara. Me yake damuna haka? ya tambayi kansa.
Daga karshe, ya rufe alƙur’anin cikin sanyin jiki, ya jingina da bango. Zuciyarsa na bugawa da sauri, ya tsinci kansa cikin tunanin Haneefa. Da alama zuciyarsa ba ta kwantar da hankalinsa ba. Ya yi addu’a da ƙyar, sannan ya fita daga masallaci yana jin tamkar an masa wani nauyi a jiki.
Da ya shiga cikin zauren gidan sarauta, sai ya ga bayin fada suna ta zirga-zirga suna shirye-shiryen biki na gaba. Ya nufi bangarensa, yana shirin hutawa kafin dare ya tsala.
Da ya tura ƙofar ɗakinsa, sai wani ƙamshi mai taushi ya doki hancinsa. A hankali ya shiga, ya rufe ƙofa da baya, ya tsaya yana kallon cikin ɗakin. Sai ya ga Haneefa a tsaye a tsakiyar daki, tana sanye da doguwar riga mai launin ja, amma cikin siririyar top da ta bayyana cikinta.
Gashinta ya barbazu har bisa kafaɗa, fuskarta ta yi matukar kyau, tana murmushi mai cike da salon jan hankali. As’ad ya tsaya a bakin kofa yana kallonta kamar wanda aka tsayar da lokaci.
"Marhaban da Sarkin zuciyata..." ta furta cikin wata murya mai rauni.
Ya yi ƙoƙarin magana, amma ya gagara. Zuciyarsa tana tsalle kamar tana neman fadi. "Haneefa... me kike yi haka?"
Ta matso da siririyar tafiya, ta kama hannunsa a hankali. "Na ga kanada gajiya, sai na ce bari na shirya maka wanka mai dadi."
Ya girgiza kai kamar wanda aka rikita. "Uhmm... na yi salla yanzu... amma..."
Ta sanya yatsanta a labbansa. "Shii... bana son surutu."
Ta dora kansa a kafaɗarsa, tana lasar wuyansa da harshenta mai laushi. "My Kankan... ka barni in sa ka ji daɗi."
Ya saki numfashi mai nauyi, jikinsa yana saki kamar ba nasa ba. Zuciyarsa na tsalle-tsalle, yana jin wani abu yana cike masa kai.
Haneefa ta ja hannunsa har bakin gado, ta sanya shi ya zauna a kan shimfiɗar alfarma mai launin ruwan gwal. Ta fara cire masa rigarsa a hankali, tana zuba masa idanuwa masu cike da kwarjini.
"Na lura kana gajiya... Bari na taimaka maka."
Ta kwance masa alkyabbarsa, tana shafa bayansa cikin salo mai rikitarwa.
Da suka gama wanka, ta shafa masa mai mai ƙamshi, tana murza wuyansa da ƙirjinsa a hankali. "My Kankan... ba ka san yadda nake sonka ba."
Ya rufe ido, yana jin tamkar numfashinsa yana neman tsayawa. "Haneefa..."
Ta yi murmushi tana shafa sumar kansa. "Ka san dai na fi kowa iya sanyaya maka rai. Kada ka damu da komai."
A wannan lokacin sai wayarsa ta yi ƙara. Ya ɗauka, sai ya ga sunan Aysha a jikin screen. Haneefa ta kama wayar da hannu guda, ta kashe ta a hankali.
"Ba zai ɗauka ba," ta furta cikin murya mai kwantar da hankali.
Ya yi shiru yana kallonta, kamar wanda aka rufe masa baki. "Amma... Aysha ce..."
Ta daura kanta a kirjinsa. "Bana son wani ya katse lokacinmu."
Bayan sun kwanta, Haneefa tana shafa sumar kansa. "My Kankan... gaskiya na gaji da zama a nan. Gobe mu koma Abuja."
Ya juyo cikin mamaki. "Abuja kuma da sai qfter 2weeks?"
Ta gyara kwanciyarta a jikinsa. "Ni gobe nakeso.”
Ya yi shiru na dan lokaci, yana kallonta cikin damuwa. Amma kafin ya ce wani abu, ta sumbaci goshinsa tana cewa, "Ka sani cewa kai ne kadai namiji a zuciyata."
Ya sauke numfashi. "To... zamu tafi gobe."
Ta saki dariya tana shafa fuskarsa. "Na san cewa ba zaka ƙi ba."
Ta sake kwanciya bisa jikinsa, tana lasar wuyansa cikin soyayya. "Bari in sa ka manta da komai..."
As’ad ya rufe ido, zuciyarsa tana bugawa da sauri, yana jin tamkar ya narke a jikinta. Bai san me yasa yake jin haka ba, amma ya san cewa yanzu ba zai iya cewa a’a ga Haneefa ba.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA GOMA SHA SHIDA
Yammacin Dubai yana kyalli da hasken fitilu masu launin zinariya da fari, ana hango tekun Gulf daga tagogin gida mai hawa biyu na Amina. Gidan yana cikin unguwar Palm Jumeirah, wani wuri na alatu da tsari, inda manyan gidaje ke bayyanar da ƙayatarwa.
Falon gidan yana da salo na zamani kujeru masu launin toka da fata daga Roche Bobois, shimfiɗa bisa darduma mai launin beige, da kuma chandelier mai kyalli a tsakiyar falon. A gefen bango, akwai wani babba TV mai fuskar madubi daga Samsung, yana kunna wani shirin na Dubai One
Amina tana zaune a babban falon, ta ajiye wayarta a kan teburin gilashi mai ɗauke da tsadaddun furanni na tulip. Yaron nata, Imran, yana tsere- tsere a kan darduma.
Mamah ta jingina a kan kujerar fata mai taushi, ta rungume wayarta cikin damuwa. Har yanzu kiransa bai shiga ba. Ta danna lambarsa sau uku, amma ko ɗaya bai ɗaga ba. Ta cije leɓɓenta cikin takaici, zuciyarta na bugawa da ƙarfi.
Da ƙyar ta ji ƙaran takalmin Aminatu daga ƙofar falon. Aminatu ta shigo cikin tsadaddiyar rigarta mai launin sky blue, kanta a ɗan sunkuye.
"Mamah, lafiya kuwa? Kamar kina cikin damuwa," Aminatu ta tambaya, idanuwanta cike da damuwa.
Mamah ta ɗaga kai cikin gajiya, ta ɗan furzar da numfashi. "Sai kiransa nake yi, baya ɗauka. Na tura masa saƙo har yanzu bai amsa ba. Aminatu, kinga abinda nake gudu ko? Wannan sabuwar matar tasa... 'yar gidan Fulany Maryam ce. Tun da ya aure ta, duk wata kulawa ta ƙare.
Aminatu ta dafa hannun Mamah cikin kulawa. "Mamah, ki kwantar da hankalinki. Kinsan fa Dadynmu ba haka yake ba. Wata kila yana cikin taro ne."
Mamah ta girgiza kai cikin takaici, tana gyara gyalen da ya ɗan subuce. "Aminatu, kin san yadda nake ji kuwa? Tun da ya aure wannan sabuwar matar, na rasa farin cikina. Mutumin da a rana sau uku yake kiran ni, yanzu ko amsa saƙo na ma baya yi."
Aminatu ta kalle ta da tausayawa. "Mamah, ki daure ki yi haƙuri. Wata kila suna buƙatar lokaci ne. Kuma ki san fa wacece ya aura—'yar gidan Fulany Maryam ce, mace mai jan hankali da wayewa."
Mamah ta tsuke fuska, idanunta suna nuna zafin zuciya. "Aminatu, ba ki san irin soyayyar da nake yi wa mahaifinku ba. Ba ki san yadda zuciyata ke karyewa ba. Na rasa yadda zan bayyana miki. Na ba shi komai soyayya, kulawa.
Aminatu ta saki numfashi, tana ƙoƙarin kwantar da hankalin mahaifiyarta. "Mamah, ki yi haƙuri. Ki daina tunanin komawa Nigeria, ki tsaya anan ki basu lokaci."
Mamah ta dafe ƙirjinta, tana jin yadda zuciyarta ke raɗaɗi. "Aminatu, wallahi wannan zafin ya yi yawa. Ni fa matar farko ce! Na san komai game da shi. Na san yadda yake so in kwantar masa da hankali. Amma yanzu, kamar na zama tamkar kango ne babu kowa, babu kulawa."
Aminatu ta sake zama kusa da ita, tana riƙe hannunta. "Ki yi haƙuri, Mamah. Ki tuna cewa soyayya tana da wuya wani lokaci. Amma ina jin cewa Dadynmu zai dawo da kulawarsa da zarar abubuwa sun lafa."
Mamah ta kalli hasken birnin Dubai daga saman bene, tana jin sanyi na ratsa jikinta.
Ta duba wayarta, har yanzu babu wani kira ko saƙo daga shi. Ta rufe idanuwanta, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri. Wata mace za ta maye gurbina a zuciyarsa?
Ta tashi tsaye cikin zafi, tana kallon Aminatu da idanu masu nuna kishi. "Aminatu, wallahi ina jin zan koma Nigeria. Ba zan iya ci gaba da zama a nan ba. Aminatu ta girgiza kai cikin ƙoƙarin lallashi.
Mamah ta koma ta zauna, tana lumshe idanuwa cikin gajiya. A zuciyarta, tana jin kishin wannan sabuwar matar yana ci gaba da yi mata zafi. Ya Allah, ka dawo min da mijina. Aminatu ta ɗan ja numfashi, tana kallon mahaifiyarta da tausayawa. Ko da yake kishi yana ci, amma dole ne Mamah ta yi haƙuri. Auren gidan sarauta ba zai taɓa kasancewa cikin sauƙi ba.
****
Babban falon gidan yana da faɗi da tsari mai ɗaukar hankali. An kawata shi da fitilun zinariya masu laushi, yayin da bango mai launin ruwan toka ya ƙara wa falon ɗaukaka. A gefen falon, akwai wata ƙatuwar kujera mai matasai na fata, inda mahaifiyar Khalil ke zaune cikin nutsuwa.
A ƙasa, Khalil ya tsugunna cikin ladabi, idanuwansa cike da hawaye da damuwa. Zuciyarsa na bugawa da ƙarfi kamar zai rasa numfashi.
Mahaifiyarsa ta kalle shi, tana gyara gyalen kanta. "Khalil, ba wai bana sonka da Ramlah ba ne. Na san kana ƙaunarta sosai. Amma mahaifinta... wallahi, baya sonka kwata-kwata."
Khalil ya dafe kansa da hannuwa biyu, hawaye suna kwarara daga idanunsa. "Mamanmu, dan Allah, ki taimake ni. Wallahi ina sonta sosai. Kinsan fa tun tana ƙarama nake sonta. Ko da bata gama makaranta ba, ki neman mun aurenta haka."
Maman Khalil ta sauke numfashi mai nauyi, tana kallon ɗanta cikin tausayawa. Ta ɗan sunkuyar da kai, tana magana cikin rauni. "Khalil, na fahimci yadda kake ji. Amma mahaifinta ya faɗa a fili cewa ko maza sun ƙare, ba zai ba ka Ramlah ba. Ina tsoron abinda zai iya faruwa idan aka ci gaba da matsawa."
Khalil ya goge hawayensa da bayan hannunsa, yana ƙoƙarin saita numfashinsa. "Mamanmu, wallahi zuciyata ba za ta iya jurewa ba. Bansan me yasa mahaifinta baya sona ba. Ina ji a zuciyata cewa ita ce cikar burina."
Maman ta dafe zuciyarta, tana jin yadda kukan ɗan nata ke tsaga mata zuciya. "Khalil, dan Allah, ka daina jawo min magana. Ka gane ni ba mai ƙarfi ba ce, kuma kasan halin Zainab matar uban Ramlah.
Khalil ya fashe da kuka mai sauti, yana kallon mahaifiyarsa da idanu masu bayyana raɗaɗi. "Mom, wallahi bazan iya ba! Nayi ƙoƙarin mantawa da ita, amma zuciyata taƙi yarda. Ko da mahaifinta baya sona, ki taimaka ki nema min ita."
Ta kai hannu ta share hawayen dake kwance a fuskar Khalil. "Dan Allah, ka gane halin da ake ciki. Kafin a kai ga matsala, gara ka hakura da wannan soyayya."
Khalil ya girgiza kai cikin murya mai cike da ƙarfi. "Mom, wallahi bazan iya daina sonta ba. Soyayyarta ta ratsa jikina. Na san cewa tana sona, kuma ban taɓa ganin wata mace da zata iya maye gurbinta ba."
Bayan Mamah ta tashi ta bar falon cikin raɗaɗi, Khalil ya zauna a ƙasa, yana jin kamar zuciyarsa zata fashe. Me yasa soyayya zata zama haka? Me yasa zan rasa farin cikina saboda banbanci na iyali?
Ya share hawayen da suka yi masa kwance, sannan ya mike tsaye cikin dauriya. "Dole ne in gwada nema daga Babah."
Ya nufi ɓangaren mahaifinsa cikin sauri, zuciyarsa na bugawa da fatan samun mafita. Da ya isa, sai ya samu mahaifinsa yana waya. Ya tsaya daga gefe, yana jiran ya gama.
Bayan an gama wayar, Khalil ya tsugunna cikin ladabi. "Baba, dan Allah, ina neman alfarma."
Babah ya kalle shi da nutsuwa. "Me kake nema, Khalil?"
Cikin rawar murya, Khalil ya ce, "Baba, dan Allah, ina neman aurar Ramlah."
Mahaifinsa ya sauke numfashi mai nauyi, yana kallon Khalil da idanu masu nuna damuwa. "Khalil, ka yi haƙuri. Mahaifinta ya riga ya faɗa cewa ko maza sun ƙare, ba zai baka ita ba."
Khalil ya lumshe idanu, hawaye suka taru a gefen idanunsa. "Amma Baba, me yasa? Me yasa baya sona?"
Babah ya gyara zamansa. "Khalil, matsalar ba kai ba ce. Matsalar ita ce Zainab marikiyar Ramlah. Kin san yadda take da tsauri da son mulki. Tana ganin cewa ba ka dace da yarinyar ba."
Ramlah tana shigar rayuwar TikTok, tana jin daɗin yin bidiyo da wallafawa. Duk da cewa tana jin daɗin sabon salon rayuwarta, har yanzu tana ƙoƙarin neman goyon bayan mahaifinta don biyan kuɗin makaranta.
*******
Karfe shida na safe, na kammala duk wani aikin gidan da aka saba. Na gyara dakina, na gyara gado, na share bene mai launin toka. A gefen gado, na ajiye system dina, na kunna don kallon Korean film.
Ina jin yadda labarin ya fara da ƙayataccen salo, amma hankalina ya fara tashi da tunanin TikTok. Ji ya kamata in duba yadda aka karɓi sabon post ɗina na jiya.
Bayan na duba lokaci, sai naga karfe bakwai tayi. Na kashe system ɗin, na miƙe tsaye, na nufi bandaki don yin wanka. Bayan na gama, na ɗaura gyale mai launin ruwan ja, na buɗe TikTok. Wallahi jiya na tabbatar cewa kaina a duhu yake, na faɗa a raina ina dariya. Ina buɗe feed ɗina, sai na fara ganin post-post na yan gayu. Wasu suna rawa, wasu suna tsokanar juna. Wani video na wata yarinya tana tafi da salon ban dariya sai na yi murmushi. Wasu kuma sai na danna "next" saboda basu birge ni ba. Haka TikTok yake?, na faɗa ina gyara gashina a gaban madubi. To nima fa ba zan bari a bar ni a baya ba! Na ɗauki wayata, na danna camera mode. Na zaɓi wata waka ta Hamisu Breaker wata da ta fi shahara a TikTok. Na kunna duk fitilun da ke dakina, don haske ya fito da kyau.
Na ajiye wayar a kan madubi, na fara rawa a hankali, ina jujjuya idanuwa, ina saitawa da murya. Kai! Na lura da yadda fuskata ta yi kyau sosai a cikin bidiyon.
Na tsaya na kalli bidiyon na, na ga yadda na yi kyau, sai na saki murmushi. Wai shi TikTok din nan yana sa mutum ya ji kamar tauraro. Na sa wasu hashtags kamar yadda Fatima ta koya min #YanGayu #Beautifu l#HamisuBreaker #TikTokTrend. Na danna Post, sannan na aje wayar a kan gado, zuciyata cike da farin ciki. Na fita daga dakin ina dariya, zuciyata na jin daɗin wannan sabon salon.
Gidanmu gida ne mai kayatarwa sosai. Abbah yana da kudi, amma ba irin masu saki nan ba. Kowane abu a lisafi yake yi. Gidansa yana da faɗi sosai, an gina shi da salo na zamani. Falo mai tsawo, kujeru masu launin toka da fari, da fitilun chandelier masu ƙyalli.Komai a gidan ya nuna cikar arziƙi, amma kuma akwai dokoki sosai. Abbah mutum ne mai tsauri a harkar kuɗi. Duk da kuwa muna da komai, sai an yi lissafi sosai kafin a kashe kudi. Na shiga falon, na ganshi yana zaune bisa kujera mai kauri yana karanta jarida. Na yi tsuguno, na gaishe shi da ladabi.
"Sannu da safiya, Abbah."
Yayi murmushi kaɗan, ya ɗaga kai. "Yau kin tashi lafiya?"
"Eh, Alhamdulillah."
Ban tsaya karɓar komai ba, duk da cewa ina so in yi masa magana kan WAEC da NECO, amma na bari malamin mu ya masa magana. Kar na matsa masa, ko kuma ya ce ba zai biya ba. Na shiga kicin na ɗauki ruwan zafi, sannan na koma dakina cikin nutsuwa. Ina kwance a kan gado, wayata ta yi ƙara notifikeshan TikTok. Na duba, sai naga comments suna tururuwa. Wasu na cewa
"Kai Baby Girl! Kina da kyau!"
"Salon ki yana birgewa!"
"Muna son ki sake yi."
Na saki murmushi mai cike da jin daɗi. Haba! Ai ba zan tsaya nan ba. Sai Natashi nakara dasawa ƙaina camera wannan karan wakar ado gwanja nabi ina dan ram gaji.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI
Ranar Litinin ce, rana na zafi sosai. Makarantar ta cika da ɗalibai suna fita bayan kammala jarabawa. Ina tsaye a bakin ƙofa tare da ƙawayena, muna ta hira da dariya. Duk da nishaɗin da muke ciki Ina tsaye a bakin kofa tare da Fatima, ina nuna mata wayata cike da farin ciki. "Fatima, ki duba nan! Na samu followers dubu guda a TikTok!"
Fatima ta sanya hannu a baki cikin mamaki, tana murmushi. "Kai! Wallahi, kin yi ƙoƙari! Na faɗa miki cewa video ɗin nan zai tafi. Dubi views ɗinsa 200k! Wannan fa babbar nasara ce!"
Na yi dariya, na girgiza kai. "Gaskiya ban yi tsammani ba. Kawai na ɗora shi da zuciya ɗaya. Amma yanzu kuwa, zan ci gaba da dagewa. Idan na koma gida ma, zan sake yin wasu sabbin videos."
Fatima ta yi dariya tana bugun kafa. "Ai haka ake so! Idan kika dage, wallahi har miliyan za ki kai. Ki ci gaba da kirkira abun dariya da kuma salon ki na musamman!"
Na yi murmushi mai cike da jin daɗi. "Gaskiya zan dage. Wallahi, yanzu na fara gane cewa da gaske ana jin daɗin abubuwan da nake yi!”
A dai-dai wannan lokacin ne Fatima ta ce, "Kawata, akwai party da za mu yi!"
Na ɗan yi jim kaɗan, cikin mamaki nace, "A ina ne?"
"Isler Hotel," ta amsa tana murmushi. "Babban yaron garin nan ne zai yi celebrating na samun zabe. Zakije kuwa?"
Na ɗan ja baya, kamar zan ce a'a, sai kuma na tuna da maganar Mumy a kwanakin baya: "Idan ba ki shiga jama'a ba, tayaya za a sanki har ki zama 'yar gayu?"
Na ciji leɓe, zuciyata na bugawa. "Zanje, amma gaskiya ina tsoro wallahi."
Fatima ta yi dariya tana buga kafa. "Ai komai lafiya lau! Ni kaina zan je, kuma da yawa daga cikin ƙawayenmu za su halarta. Ki daina tsoro. Idan kina tare da ni, babu abin da zai faru!"
Na lura da yadda wasu daga cikin abokaina suke magana cikin sirri, suna kallona daga nesa.
Ina cikin wannan tunanin, sai na ga wata mota mai launin toka ta tsaya a gefen hanya. Na ɗan yi juyawa da mamaki, amma ban yi tsammanin komai ba har sai da na hango shi Khalil!
"Khalil?" na furta cikin ƙaramin murya. Me yake yi anan? Mahaifina ya sha faɗa masa cewa ba zai taɓa amincewa ya aure ni ba. Me yasa ya zo nan? Salon yajawomun wata matsalar?
Ban taɓa jin daɗin kasancewa da wani kamar Khalil ba. A duk lokacin da muka haɗu, yana sa ni jin inada daraja da kima yana ƙaunata nasani tun ina yarinya haka ko'ina yana biye dani hakan kuma yasanya kowa yasani acikin ahalina . Khalil mutum ne mai taushi da kulawa. Amma Abbah ya ƙi amincewa da shi saboda rashin aikinsa da wasu maganganun da ya ji daga mutane akan abarni Saka saka ina kulashi ko primary ban gama hakan yasanya yatsaidashi.
Tun daga lokacin da Abbah ya sa masa hani, Khalil ya daina zuwa wajena. Na san yana ƙaunata. Amma yanzu tsoro nakeji.
Lokacin da ya iso kusa da mu, ƙawayena suka ja baya. Na yi ƙoƙarin yin murmushi, amma fargaba ta fara mamaye zuciyata.
"Khalil, lafiya? Me ya kawo ka nan?" na tambaya cikin mamaki.
"Ramlah, ba wani abu bane. Na zo ne in ɗauke ki. An samu gaggawa a gida."
Na kalli ƙawayena, sannan na juya gare shi. "Gaggawa? Amma me ya faru?"
"Ba zan iya faɗa anan ba," ya ce cikin sanyin murya. "Don Allah, ki yarda mu tafi, zan faɗa miki komai a hanya."
Ban yi tunanin abin zai zama haka ba. Na shiga motar, zuciyata na bugawa. Khalil ya kashe ƙofar, sannan ya fara tuka motar cikin sauri.
"Khalil, me kake yi? Ina za mu?"
Ya ɗan yi shiru, sannan ya kalle ni ta madubi. "Ramlah, ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba. Na yanke shawara zan tafi da ke zan aure ki ko da ba su yarda ba."
Naji jikina ya yi sanyi. "Khalil, wannan ba daidai bane! Soyayya ba haka ake yi ba!"
"Ramlah, kin san irin yadda nake ji game da ke? Na gwammace na gudu da ke fiye da na rasa ki."
Na yi kokarin kiran wayata, amma Khalil ya lura. Ya ja wayar daga hannuna, yana girgiza kai.
"Ba zan bari ki kira gida ba. Zamu tafi wani wuri mai nisa. Zan aure ki da kaina."
Na fara kuka. "Khalil, don Allah ka tsaya. Abbah zai kashe ni idan ya gano wannan."
"Ki yi shiru, Ramlah. Ki kwantar da hankalinki. Ina sonki sosai. Ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba."
A wannan lokacin, na fara gane cewa soyayyar Khalil ta rikide zuwa wani abu mai haɗari. Yana kallona ta madubi, amma hankalinsa a rikice. Na yi ƙoƙarin kwantar masa da hankali, amma zuciyata cike da tsoro.
"Khalil, ka tsaya, don Allah. Wannan ba hanyar da za mu bi ba. Na san kana sona, amma ba haka ake tafiyar da soyayya ba."