Kaddarar ramlah book 1 complete - Chapter 9
Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 9: Kaddarar ramlah book 1 complete Chapter 9. Sai ya tsaya tare da daka birki a wani gefen hanya, yana numfashi da…
4,497 words
Sai ya tsaya tare da daka birki a wani gefen hanya, yana numfashi da ƙarfi. "Na rasa mafita, Ramlah. Na rasa yadda zan ci gaba da rayuwa ba tare da ke ba." Ya kalli cikin idona, yana ɗan murya.
Haka Khalil ya yi ƙoƙarin shigar da ni ta ƙarfi cikin gidan da muka zo. Yayin da muka shiga, na ji zuciyata tana bugawa kamar ana dukan ganga. Wurin shiru ne, babu motsin rai ko tsuntsu, sai ƙarar zuciyata da ƙafafun Khalil suna dokawa ƙasa.
Da kyar na iya tsayawa a kan ƙafafuna, amma duk yadda nake roƙon sa da magiya, yana kallona cikin idanu da wani irin yanayi na zafin rai da kishi. Wani ɓacin rai ne ya bayyana a fuskarsa, kamar yadda wutar daji ke cinye koren ciyayi.
Ya ja hannuna da ƙarfi, ya tura ni cikin wani ƙaramin falo. Ƙofar ya kulle da sauri, sannan ya yi tsaye yana haki, yana kallona da idanuwansa da suka koma kamar na baƙin ƙogi cike da bacin rai da tsantsar ciwo.
"Mahaifinki bai isa ya hanani ke ba!" ya furta, muryarsa na rawa. "Zan tabbatar da cewa ba zai iya raba mu ba. Soyayyarki na cikin jinina, Ramlah! Shekara goma sha biyar ina jiran wannan lokaci. Yanzu za a ce na fasa? Wallahi Sai Na kusance ki Nayi miki ciki Ta yadda mahaifinki bai isa yarabamu ba kuma sai Ya auramun ke Wallahi."
Na tsaya kallonsa, hawaye na gangarowa bisa kumatuna. Na kasa gane yadda soyayyarsa ta koma kamar makami mai lahani. "Khalil, don Allah, ka tausaya mini," na furta cikin kuka mai rauni. "Ba haka ake tafiyar da soyayya ba. Ni marainiya ce! Ka yi hakuri, dan Allah!"
Amma Khalil bai saurare ni ba. Sai ya cigaba da matsowa kusa, yana magana cikin wani irin yanayi na rashin nutsuwa. Na ji wani irin tsoro yana taso daga zuciyata zuwa duk wani sashe na jikina. Na yi ƙoƙarin tserewa, amma yana rike da hannuna da ƙarfi, kamar wanda yake tsoron in tsere masa har abada.
"Matsalar ki ce ba ki gane ba, Ramlah," ya ce cikin muryar da ke haɗa kuka da fushi. "Na rasa mafita. Na rasa yadda zan ci gaba da rayuwa ba tare da ke ba.” Cikin bazata ya fizgo rigata yana rabani daita haka skirt din makaranta ma yana kokarin yagamin inaja ina kuka sosai Amma sai da yarabi da skirt dina sannan yashiga tuɓe kayan jikinsa Innalillahi wa inna ilaihirraji’un Nashiga uku Na shiga uku DanAllah khalil karka wulakantani Amma ya toshemun baki yana kokarin hayemun….
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA GOMA SHA TAKWAS
Bayan sallar Magariba ne hankalin Momy ya fara tashi. Na san hakan saboda duk lokacin da aka fara kunna fitilar dare har ya kai ga shudewa, ni dai ban dawo gida ba. Duk yunkurin da Momy ta yi na kiran lambar Malam Idi ya ci tura lambar ba ta shiga ko ɗaya.
A lokacin da Abba ya dawo daga aiki, hankalin kowa ya yi mummunan tashi. Na san cewa Abba yana cikin gajiya daga aikin sa, amma lokacin da ya shigo falon, sai na ji muryarsa cikin damuwa yana tambayar Momy
"Lafiya? Me ya faru?"
Momy ta kalle shi cikin damuwa, tana girgiza kai.
"Wallahi har yanzu Auta ba ta dawo gida ba tun da safe da ta tafi makaranta. Na kira lambar Malam Idi sau da dama amma ba ya shiga."
Abba ya runtse idanu cikin damuwa, ya nufi inda yake ajiye wayarsa. Na san cewa yanzu Abba zai yi duk abin da zai iya don gano inda nake. Nan take ya umarci wani daga cikin mutane su je gidan Malam Idi don jin inda nake. Kafin lokaci ya ja, an dawo da amsa daga gidan Malam Idi cewa wani mutum ne ya zo ya ɗauke ni daga makaranta, yana tunanin ko Yaya Abbas ne. Wannan labari ya girgiza Abba sosai.
Abba ya dafa kansa cikin tashin hankali, yana magana a hankali kamar ba da gaske yake ba
"Wani ne ya ɗauke ta daga makaranta? Waye wannan?"
A daidai lokacin ne kuma Yaya Abbas ya shigo cikin gaggawa.
"Abba, me ya faru ne?" ya tambaya cikin damuwa.
Abba ya kalle shi cikin fusata, ya ce
"Wani ya ɗauki Auta daga makaranta. Ba wanda ya san inda take yanzu haka."
Momy kuwa ta rike zuciyarta tana kallon Abbas
"Abbas, nifa hankalina ya tashi. Kada dai wadancan kawayen banza nata su ja ta cikin abin da bai dace ba. Yau fa na shiga uku!"
Yaya Abbas ya girgiza kai, yana kokarin kwantar musu da hankali.
"Momy, Auta ba irin wannan bace. Ba ta da halin bin kawaye haka kawai."
Sai ga Billy ta fito daga daki cikin tsoro.
"Abba, na kira kawarta Fatima. Tace wai wani mai suna Khalil ne ya zo ya ɗauke ta."
Ran Abba ya baci sosai, har ya kai ga ɗaukar wayarsa cikin hanzari. Ya kira mahaifiyar Khalil a daren, yana yi mata fada kan dalilin da yasa danta zai ɗauki yarinya ba tare da sanin iyayenta ba.
Mahaifiyar Khalil ta nemi gafara cikin nadama, tana cewa babu inda zai kai ta. Ta kuma yi masa fada kan wannan rashin tunani. Sai dai wannan ba ya rage fushin Momy ba, wadda ta fara zazzaga zagi.
"Wallahi, dama na san Khalil ne ke zuganta! Daman shi ne ya sa ta fara fitsara da rashin kunya. Wannan dai sai an lallata tarbiyar yarinyarta saboda irin wannan hali!" Momy ta fada cikin bacin rai.
Abba ya rasa abin cewa saboda tashin hankali ya yi masa yawa. Ya yi shiru yana tunanin abin yi. Yaya Abbas kuwa ya cigaba da kokarin kiran lambar Khalil, amma har yanzu ba ya dauka.
Da suka ga zaman gida ba zai amfana ba, Abbas ya ce
"Abba, bari mu ja mota mu fita. Zai fi idan muka bincika da kanmu."
Abba ya amince, suka fita cikin hanzari. Har lokacin Momy tana cikin fargaba tana cewa
"Wallahi idan aka sake ganina tare da wannan yaron, zan hukunta ta da kaina!"
Ko da su Abba suka fita, babu inda ba su je ba amma babu ni babu labarina. Har wasu abokan Khalil din ne aka tambaya amma kowa sai yace ai ba su gan shi ba. Da kansa Abba ya je gidan su Khalil, ya samu mahaifinsa yana tambayar inda ɗansa yake. Mahaifin Khalil ya ce ba shi da labarin inda ɗansa yake, amma ya tabbatar wa Abba cewa za su yi bincike domin gano inda suke. Saboda tsananin damuwa da tashin hankali, Abba ya fara kuka. Yaya Abbas ya shiga bashi baki akan babu abin da zai same ni.
***
Su Momy dake gida kuwa, dariya ta sa bayan fitar Abba, tana barin falon cike da murna.
"Alhamdulillah! Wannan shine abin da nake fata. Insha Allahu sai na tabbatar da cewa ta yi ciki ta kawowa abba cikin gidan nan."
***
A bangaren Yaya Billy kuwa, daki na ta shiga ta bincika ko'ina amma ba ta samu komai ba. Hakan yasa ta saka dariya itama, sannan ta fita. Na lura cewa tana jin dadin wannan hali, kamar wani abu ne aka yi yadda take so.
*******
Na rasa gane me ya same ni. Zuciyata kamar ta faso ƙirji. Hankalina ya gama tashi, ban san abin yi ba. Ina kallon khalil idona ciƙin nasa yacire wandonsa yana kokarin hawa jiƙina gaba daya jikina rawa yakeyi Narasa da yaren da zan yi masa bayani..Cikin wata murya mai rauni da ba ta fita da kyau ba, na dubi Khalil, wanda ke tsaye yana kokarin taɓoni, yana kallona da idanu masu cike da fitina. Cikin hawaye da zazzafan kuka nace masa
"Wannan ce soyayyarka gare ni? Khalil, So kakeyi ka batamin rayuwa, ka rusa duk wani abin da na dogara da shi. Wannan ita ce ƙaunarka gareni? Khalil, wannan ce kaunar da kake ikirarin kana yi min? Shikenan... ka rusamun rayuwata kayimun Abunda kake gani mafita ce gareka ba rusa rayuwata ba.
Na fashe da kuka, wani irin kuka mai cin rai, wanda ya kunshi duka matsananciyar radadin da zuciyata take ciki. Na san cewa a wannan lokacin banda mai taimakona sai Allah banda ikon yin komai.. Na ji kamar komai ya ruɗe, tamkar duniya ta gama rugujewa a kaina.
Khalil kuwa ya rasa abin cewa. Cikin hanzari ya fara jan baya yana ƙadamun ƙai yana faɗin kiyi hakuri bazan aikata ba kiyi hakuri…ya tattara kayansa yana kuka kamar ƙaramin yaro. Muryarsa na rawa yana cewa
"Ki yi haƙuri Ramlah, ki gafarta min... wallahi ba haka na yi niyya ba bazan aikata ba bazan aikata ba."
Ban tsaya sauraronsa ba. Na kwashi wasu kayan da suka rage a dakin cikin gaggawa. Na yi saurin saka siket dina, amma rigar ta yage. Cikin rashin zabi, na dauki hijabin makaranta na, na rufe jikina sannan na fice daga dakin da hawaye suka gama jiƙa fuskata..
Na fito waje, na same shi yana tsaye bakin mota yana jiran ni. Ba tare da ya ce komai ba, ya bude min kofa, na shiga. Motar ya ja cikin shiru, babu wanda ya iya cewa komai. Na ci gaba da kuka kamar zan rasa numfashi. Ya kalleni yashiga lallashina akan nayafe masa sharrin shaidan ne da soyayyata..
A hanya sai ga Khalil ya tsaya a wani wurin siyar da kaya. Na ga ya sayo wata sabuwar abaya ya miko min.
"Ramlah, ki saka wannan... don Allah," ya ce cikin sanyi.
Na karbi abayar ba tare da kallonsa ba, na saka, sannan na koma cikin shiru. Har lokacin kukan nawa bai tsaya ba. Na rasa yadda zan bayyana bakin cikin da ke cike da zuciyata. Khalil bai ce uffan ba har muka iso kofar gidanmu.
Na fita daga motar da kyar, saboda jikina babu ƙarfi. Khalil ya tsaya daga nesa yana kallona har na shiga gida. Na san cewa zuciyata na iya bugawa ko yaushe, saboda tsananin nauyin da take ji, yanzu da yayimun fyade Fa? Shikenan rayuwata ta lallace?? Shikenan Narasa farin cikin? Wayooo Allah na Nagode daga sanya yafasa..
Ina shiga cikin gidan, na ji duniya ta fara juyawa. Sai gani a kasa, na sulale a bakin kofa. Masu aikin gidanmu ne suka hango ni, suka yi gaggawar kawo dauki. Abba da kansa ya fito cikin hanzari ya dagani.
"Subhanallah! Ramlah, lafiya?!" ya tambaya cikin rudani.
Na rike hannunsa ina kuka kamar zan mutu.
"Abba... Abba... na shiga uku! Khalil ne ya saceni abba.."
Ya dubi masu aikin gidan da suka yi tsuru suna kallona.
"Ku kawo ruwa, da sauri!" Abba ya umurce su.
Bayan sun kawo ruwa, ya yayyafa min a fuska, sannan na bude idanu cikin tsananin rauni. Momy ta fito tana tambayar abin da ya faru. Abba ya ce
"Ina da zaton cewa an yi mata wani abu. Wannan ba halinta bane."
Momy ta kalle ni cikin tsananin fushi da damuwa.
"Ramlah, me ya faru? Don Allah ki fada min."
Na ci gaba da kuka, na kasa magana. Hankalin kowa ya tashi. Abba ya kalli Yaya Abbas da ya shigo cikin gaggawa.
"Abbas, ka kira 'yan sanda yanzu-yanzu."
Sai dai Yaya Abbas ya ce
"Abba, a bari na fara kira Khalil mu ji daga gareshi. Wannan lamari yana bukatar sanin gaskiya daga dukkan bangarori."
Abba ya amince, amma har lokacin zuciyarsa na bugawa da karfi. Yaya Abbas ya yi kokarin kiran Khalil, amma lambarsa bata shiga.
Na jingina a kan gwiwar Abba, ina jin tamkar rai zai fita. Cikin zuciyata naji wani nauyi mai girma. Na ji muryar Momy tana cewa
"Wallahi yau zan ga iyakar wannan abin. Khalil sai na hukunta shi. Wannan rashin kunya da rashin tarbiyya yana son ya lalata min yarinya!"
Abba ya tsayar da ita da hannu.
"Ki yi hakuri Momy. Mu ji yadda lamarin yake da farko."
Amma Momy bata iya boye fushinta ba.
"Toh, idan wannan yaron ya lalata min rayuwar 'ya, wallahi sai ya yi nadama!"
Yaya Abbas ya dawo da rashin nasara wajen kiran Khalil.
"Abba, lambarsa bata shiga.”
*******
Na bude idanuna a hankali, ganin hasken safiya na shigowa daga tagar dakin ya sa na motsa kadan. Kai na ya yi nauyi kamar an loda kaya a ciki, idanuna kuwa suna luhu-luhu tamkar ban samu bacci ba duk dare. Na runtse idanuna na sake bude su, sai kawai na ji muryar Abba daga kusa da gadon.
"Ramlah, tashi ki yi sallah. Kada ki bari lokaci ya wuce."
Na juyo daga kwanciyata da kyar, zuciyata tana bugawa cikin kasala. Na ce, "To, Abba." Na mike da kyar, ina jin yadda jiki na ke yi mini nauyi. Abba ya tsaya har sai da na mike tsaye sannan ya fice daga dakin.
Da na kammala sallah, na koma na zauna a kan gado ina tunanin yadda dare ya kasance mini. Ban ma san lokacin da na yi barci ba saboda yanayin ciwon kai da na ji jiya. Kafin na gama tunani, sai ga Abba ya dawo da kofin shayi a hannunsa.
"Ki sha shayi kafin ki huta," ya ce, yana ajiye kofin a gefen gado. Na kalli fuskar sa da kulawa, duk da cewa na san yadda Momy take ganin wannan kulawar a matsayin wani abu da ba ta yi tsammani ba.
"Nagode Abba," na fada a hankali, ina jin wani sanyi a zuciyata. Wannan al'amarin ya ban mamaki sosai, musamman ganin yadda Momy take nuna bambanci tsakanina da Billy. Amma Abba bai damu da hakan ba.
Na karba kofin shayin cikin nutsuwa, na kurba kadan yayin da na ji sanyin zafin na shiga zuciyata. Na kalli Abba yana murmushi, sai ya ce, "Ki koma ki huta bayan kin sha."
Na kada kai, na san cewa idan Momy ta ga hakan, ba lallai ne ta ji dadi ba. Da zarar Abba ya fita, na ji motsi a tsakar gida. Na hango Momy tana yawo a cikin kicin kamar tana cikin tashin hankali. A wani lokaci, sai ta tsaya tana zuba tagumi.
"Me yasa Abba yake nuna wa Ramlah soyayya haka? Me ya faru?" na ji ta furta cikin sanyin murya. Sai na sake mayar da hankalina ga shayin da ke gabana, amma zuciyata ta cika da tambayoyi.
Ina cikin wannan tunani, sai ga Abba ya sake dawowa falo. Ya tsayar da ido kan Billy da take zaune tana latsa waya.
"Ke Bilkisu," Abba ya kira ta cikin natsuwa. "Ki dafa wa Ramlah abinci kafin ta farka."
Billy ta dan tabe baki, tana kallon Abba cikin rashin jin dadi. Kafin ta yi magana, sai Momy ta yi saurin cewa, "Abban Auta, bari ni na dafa mata. Babu damuwa."
Abba ya kalle ta da mamaki, yana fadin, "Zainab, ni nasan cewa Bilkisu bata aiki a gidan nan, amma kullum Ramlah ce ke fama. Yanzu haka ba ta jin dadi, amma kalli gidan nan? Aikin gida fa wajibi ne ga kowa."
Momy ta saki fuska kamar tana so ta ce wani abu amma bakinta ya mutu. Sai ta kalli Billy da idanu kamar tana fada da su. Billy kuwa ta kau da kai, tana cigaba da latsa wayarta.
Na ji zuciyata tana tafasa amma na danne. Lokacin da Abba ya fita, Momy ta nufi dakin Billy tana fadin, "Wallahi babu abinda zan yi. Idan yana so, sai shi ya yi." Na kalli yadda Momy ta shiga dakin da karfi ta rufe kofa. Na jinjina kai, zuciyata tana cike da mamaki.
"Me ya sa Momy ke yi min haka? Me yasa soyayyar da Abba ya nuna min take tada mata hankali?" Na tambayi kaina cikin sanyin murya, zuciyata na jin raɗaɗi.
Abba na fita daga Gidan yatafi offices, yana gayawa mumy ta kula dani fa sosai kar kuma nayi aikin komai agidan nan makaranta ma yace bazanje ba. Cikin zuciyata, na ji kamar an yaye mun wani nauyi, amma kafin na samu natsuwa, sai ga Mumy ta banko kofar dakin nawa cikin tsananin fushi. Fuskar ta cike da masifa, idanunta sun kada ja, alamar ranta ya gama baci.
"Wato ke?!" Ta fara magana cikin karaji, tana daga hannayenta kamar wadda zata kai mun duka. "Kin je kin gama yawon iskancinki, kun gama zinace-zinacenkku da Khalil, shine zaki dawo kina hadani da mijina? Shegiyar yarinya!"
Na zuba mata idanuwa cikin mamaki, jikina yana rawa. Kalaman ta suna shiga zuciyata kamar kibiya. Baki na yaki buduwa, na kasa cewa uffan.
"Zaki tashi ki shiga ki gyara mun gida ko kuwa sai na ci ubanki a cikin gidan nan? Ko an gaya miki ni baiwar uwarki ce? Shegiya, munafuka! Mara tarbiyya mai yawon bin maza!"
Kalaman sun sake harbawa zuciyata, suna tashi mun wani ciwo na daban. Na ji wani irin raɗaɗi a cikin zuciyata da ya hana ni natsuwa. Cikin tsananin damuwa, kukan ma ya ki zuwa. Ban iya cewa komai ba, sai dai kawai na zuba mata idanuwa, hawaye suna yawo a gefen idanuna.
Na rasa yadda zan yi, jikin nawa yana rawa kamar wanda aka doki zuciyarsa. Tunanina yana komawa baya, inda rayuwata ta kasance cikin kwanciyar hankali da soyayya. Me yasa rayuwa ta zama haka? Me yasa zargin da bata da asali ya zamo min karfen da ya tsaya mun a wuya?
Kafin na gama tunani, sai kawai na ji saukar marin ta a fuskata, wani gigitaccen mari wanda ya sanya na rike kunci cikin tsananin azaba. Na mike tsaye da sauri, na zaro idanuwa, zuciyata na bugawa kamar tana neman tsagewa.
"Ina zaki je?" Mumy ta sake kwalla mun ihu. "Wallahi zaki zauna nan har sai na yanke hukunci. Wallahi, sai kin gane kurenki a yau."
Na fashe da kuka, kuka mai cike da tsananin takaici da ciwon zuciya. Har yanzu bakina a rufe yake, na kasa cewa uffan. Wani murdaddan zafi ne ya mamaye jikina, numfashi na yana fita da kyar.
Na juya a hankali, na zauna a kan katifa, jikina yana karkarwa. Kalaman Mumy sun cika kunnuwana, har wani irin ciwon kai ya fara kamani. A cikin zuciyata, ina rokon Allah ya bani karfin guiwa da ikon jure wannan jarabawa.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA GOMA SHA TARA
Bayan Mumy ta gama yi mun masifa tare da marin da ya girgiza dukkan zuciyata, na zauna a kan katifa ina kuka mai tsanani. Amma ba jimawa ba, sai na ji zuciyata ta fara tsorata da abin da zai biyo baya. Na san cewa idan har na ci gaba da zama haka, zai iya zama wani sabon laifi a idanun Mumy.
Cikin tsananin fargaba, na share hawayena da sauri, na mike tsaye. Dakin ya yi shiru, sai karar zuciyata da nake ji tana bugawa tamkar gangar rawa. Na duba gefen dakin, na hango kayan da suka watse saboda cunkoson da aka yi a lokacin Mumy tana masifa.
A hankali na fara gyara dakin, na tattara duk wasu kaya, na wanke kwanonin da suka taru a gefe. Idanuwana sun kumbura saboda kuka, amma ban damu ba. Na san cewa gyaran gidan zai rage min zargi a idanun Mumy.
Bayan na kammala gyaran dakin, na fito falo cikin tsananin tsoro, na fara tattara kayan wanki. Na kai su waje, na zuba ruwa a cikin kwandon wanki sannan na fara wankewa cikin sauri. Duk da jikina yana ciwo saboda marin da na sha, na dage ina kokarin kammala aikin.
Bayan na gama wanki, na shiga cikin kitchen na fara dora girki. Na san cewa idan Mumy ta dawo ta ga komai a tsaf, zata rage mun tsangwama. Na jajjaga albasa da tumatir, na soya cikin tukunyar miya. Da yake an kusa lokacin cin abincin rana, na yanka doya sannan na dora ta a kan gas.
Dai-dai lokacin ne Mumy ta sake shigo cikin kitchen din, tana kallona da wani irin kallo na wulakanci.
"Ke, ban ce ki gyara gidan ba? Ko kuwa kinzo kina yin wani sabon iskanci a nan ma?"
"Mumy, na gama gyara dakin da wanki, yanzu kuma girki nake yi," na fada cikin rawar murya.
Ta girgiza kai cikin rashin jin dadi. "Yanzu ke idan kina yin aikin gida, zaki samu tsarki ne? Mara tarbiyya kawai! Wallahi kin lalace.”
Bayan ta gama masifar ta, ta juya ta fita, tana ci gaba da zuba zagi. Na tsaya na kurawa kofar kitchen din ido, zuciyata tana tafarfasa. Ban san lokacin da na dauko wayata ba. Na bude TikTok, zuciyata tana neman nishadi don rage radadin ciwon da kalaman Mumy suka haifar.
Na kunna waka mai sa rawa, na fara taka rawa cikin kunci da takaici. Na zabi wasu dabaru na rawa da nake jin dadi a kai, na hau yi cikin raye-raye masu motsa jiki. A lokacin, na rika jin kamar nishadin da nake nema ya fara zuwa.
Na danna "post" a TikTok, na dora bidiyon ba tare da tunanin me zai biyo baya ba.
Bayan na gama rawa, na sake zaunawa a kan kujera cikin falo, zuciyata tana cike da damuwa da mamakin yadda rayuwa ta sauya a kaina cikin kankanin lokaci.
*************
Bayan kwana biyu, na samu sauki sosai daga damuwar da ta addabe ni. Na shirya cikin kayan makaranta, na fesa turare mai dadi, sannan na dauki littafaina na fita. A yau na kuduri aniyar cewa zan mayar da hankali sosai a karatu. An kusa fara jarabawar WAEC, kuma Abba yana da burin mu ci gaba da ilimi yadda ya kamata.
Tun da Abba ya bayyana cewa yana so mu tafi Dubai ko London don karin ilimi idan muka kammala, Mumy ta fara nuna rashin goyon baya. Ta dage tana fadin cewa ita ba za ta bar diyarta ta tafi nesa ba, kamar yadda ya faru da Yaya Billy, wacce take ganin ta sha wahala sosai daga nesa.
A makaranta, lokacin break ya yi. Na zauna tare da Fatima a gefen bishiyar mangwaro da ke bayan ajin mu. Muna hira cikin nishadi, sai Fatima ta dauko wayarta tana dube-dube.
"Ramlah! Kin san kuwa cewa yanzu kin zama fitacciya a TikTok? Ki duba, kin kai dubu dari (100k) a followers!"
Na kura mata ido cikin mamaki. "Fatima, wannan ai ba komai bane. Abun da ya dame ni shine yadda maza suka cika comment. Wallahi akwai wanda har ya ce zan yi dadin kwanciya."
Fatima ta ja numfashi, ta harare ni cikin wasa. "Ke kuwa Ramlah, kina nufin kina tsoron haka? Ai wannan damar ce! Kina iya amfani da wannan farin jini ki tara kudi."
Na yi murmushi mai ciwo. "Wallahi Fatima, bani da ra'ayin hakan. Ni kawai ina son inyi nishadi ne, ba don wani abu ba."
Ta yi dariya, tana cewa "To fa, amma ke dinma kinyi shahara. Kuma akwai wadanda suke ganin cewa kin fi kowace yarinya kyau da iya rawa."
Bayan an tashi daga makaranta, na nufi gida cikin natsuwa. Na shiga daki na, na canza kaya don in tafi Islamiyya. Bayan na dawo da yamma, na shiga kitchen don dora girki. Ina cikin shirya kayan miya, sai ga sakonnin Khalil kala-kala a wayata.
"Ramlah, ki yi hakuri. Ba ni da laifi. Wallahi ban so abin ya kai haka ba."
Na harari wayar, na watsar. Ban da lokaci na kula da shi.
****
Dare ya yi, ina cikin falo ina kallon wani shirin talabijin, Abba ya shigo tare da Yaya Usman. Na yi saurin tashi na yi masa sannu da zuwa.
"Yauwa, Ramlah. Yau na gaji sosai. Na gode da girki," Abba ya fada yana murmushi.
Daga nan, sai muka zauna muna hira har zuwa lokacin da Mumy ta shigo cikin palon da fuskar da ta canza. Abba ya lura da yanayin fuskarta, ya dan juyo yana tambaya:
"Lafiya dai ko?"
Mumy ta durkusa a gabansa, tana rik'e wayarta. "Abban Ramlah, akwai matsala fa. Ka ga abinda 'yar ka take yi a TikTok? Wallahi na rasa me yasa yarinyar nan take neman lalacewa!"
Abba ya kalli Mumy da mamaki. "Me take yi a TikTok?"
Mumy ta mika masa wayarta. "Ga bidiyonta nan, tana rawa cikin rashin kamun kai. Mutane sun fara magana a gari. Har maza sun fara yi mata tsokaci mara kyau."
Abba ya karbi wayar yana duba bidiyon. A take fuskar sa ta canza.
"Me yasa zaki dora irin wannan bidiyo? Ba na son rashin nutsuwa a cikin gidan nan!"
Na zaro idanuwa cikin tsoro. "Abba, wallahi... wallahi kawai nayi nishadi ne..."
Kafin in kai ga rufe baki, sai na ji saukar marin da ya girgiza dukkan jikina. Abba ya mike tsaye cikin fushi, yana nuna ni da yatsa.
"Ni na gaya muku bana son rashin kamun kai! Kina neman daukaka ta hanyar Rawa? Ramlah, wannan ba tarbiyya bace!"
Mumy ta fashe da kuka. "Ka ga abinda na fada maka! Mutane suna cewa yarinyar mu tana neman lalacewa. Abba, sai mu dauki mataki kafin ya wuce hankali."
Abba ya juya gare ni, yana fadin
"Tashi ki bace mun daga gani! Wallahi ki tara kayanki ki fita daga gidan nan idan haka kike so. Iskanci kika zaba? To sai ki bar mun gida!"
Kukan da nake yi ya gagara tsayawa. Na yi ta rokon Abba da Mumy, amma suna nuna rashin jin dadi da damuwa. Abba ya sake marin fuska ta, yana daka tsawa
"Idan haka kike so, ki shirya ki tafi gidan Khalil tunda shi kike so! Wallahi ban haifi marar kamun kai ba!"
Na kasa magana, zuciyata tana kuna tamkar wuta. Na durkushe a kasa, ina rike kuncina da hannu biyu. Ban taba ganin Abba cikin irin wannan fushi ba. Bayan wannan masifar da ta faru a gida, na kwana cikin kuka da damuwa. Na kasa samun natsuwa duk tsawon dare, zuciyata na tafarfasa da ciwon da marin Abba ya haifar. Na rike kuncina da hannu daya yayin da dayan hannun na ke rike da mayafi, na kwanta a gefen katifa kamar wadda aka azabtar.
Da safe na mike da kyar, jikina duk ciwo saboda dukar da Abba yayi mun. Na yi wanka da kyar, na sa sabuwar uniform, na daura gyale a hankali. Na dubi fuskata a cikin madubi, na ga idanuna sun kumbura saboda kukan da nayi daren jiya.
Na fito daga daki, na shiga kitchen don dora girki na safe. Mumy tana falon tana duba wayarta, tana yiwa Yaya Zainab magana da sassanyar murya. Na dan yi shiru a bakin kofa, ina jin yadda take korafin cewa "yarinyar nan tana neman ta bata mana suna a gari."
Cikin jin haushi, na daure na cigaba da aikin girki, amma zuciyata na tsananta bugu. Na san cewa ina cikin tsaka mai wuya.
Da na dawo daga makaranta, jikina duk a sanyaye saboda tunanin abin da ya faru da ni kwana biyu da suka wuce. Na dade ina tunanin yadda zan gyara kuskuren da nayi, har na yanke shawarar gogewa duk wasu bidiyona daga TikTok. Na san cewa hakan ne kawai zai rage damuwa a gida.
Da na shigo gidan, na same su a falo, Abba yana zaune cikin tsananin fushi, Mumy kuma tana gefe tana cigaba da korafi kamar yadda ta saba. Na tsaya daga bakin kofar falon, zuciyata tana tsananta bugu. Abba ya dago kai yana kallona da idanunsa wadanda suka nuna karara cewa ransa a bace yake.
"Ramlah!" Ya kira sunana cikin karfi.
Na durkushe a wajen, hawaye na zubo daga idanuna. "Abba, na dawo daga makaranta."
"Ke! Ki tattara ki fice mun daga gida! Bazan iya zama da marar kamun kai kamar ke ba!"