Kenza eBookz

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 13

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 13

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 13: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 13. "Ke! Ki tattara ki fice mun daga gida!…

3,366 words

"Ke! Ki tattara ki fice mun daga gida! Bazan iya zama da marar kamun kai kamar ke ba!"

Cikina ya murda tamkar an doka ni da guduma. Na kalli Abba cikin tsoro da tsananin damuwa. "Abba, don Allah kayi hakuri! Wallahi na goge dukkan bidiyona daga TikTok. Bazan sake ba. Idan na fita, ina zan tafi? Abba, nifa bantaba aikata iskanci ba, don Allah kayi hakuri."

Abba ya girgiza kai cikin takaici. "Ramlah, kin cutar da ni! Kin bata mun suna a gari. Mutane suna tambaya akan ki tamkar ba ni da tarbiyya. Wallahi, idan ba ki fita daga gidan nan ba, zan yi abin da na rantse!"

Mumy ta daga murya tana cewa, "Wallahi ka daina tausaya mata! Wannan yarinya ba zata natsu ba. Ka koreta kawai! Kalli yadda aka koma magana a gida, mutane sun fara tambayar mene ne ya samu 'yar gidan Malam Ibrahim!"

Na zube a kasa ina kuka, zuciyata na kuna kamar wuta. "Abba, don Allah, nayi kuskure ne. Wallahi bazan kara ba. Na goge komai! Na canza, kuma na gane cewa nayi kuskure. Don Allah kada ka kore ni."

Dai-dai lokacin, sai ga Yaya Abbas ya shigo cikin falon. Yana ganina a kasa ina kuka, ya yi saurin karasowa, yana duban Abba cikin mamaki.

"Abba, lafiya? Me ke faruwa ne?"

Abba ya nuna ni da hannu, yana fadin, "Wallahi, Abbas, idan wannan yarinyar bata bar mun gida ba, zan yi abin da na rantse!"

Yaya Abbas ya kalle ni cikin damuwa, sannan ya kalli Abba cikin natsuwa. "Abba, don Allah kayi hakuri. Ramlah bata da inda zata je. Ta goge bidiyonta, kuma ta gane kuskurenta. Bamu ba ta wata dama ba?"

Mumy ta harari Abbas cikin takaici. "Yaya Abbas, ka daina sa baki! Ita dai lalacewa tayi, kuma bazata gyaru ba!"

Yaya Abbas ya dauki tsaki, ya kalli Mumy. "Mumy, ki daina zugawa! Wannan ba maganin matsala bane. Ai abin da ya wuce ya wuce. Duk wani abu da aka yi, Allah zai gyara ai abun mugodewa Allah ne dayasanya har aka gani yanzu."

Abba ya sauke numfashi, ya kalli Abbas cikin fushi amma a hankali fushin nasa ya fara raguwa. "Kai ma ka san cewa wannan abin da tayi ya kai makura.”

Yaya Abbas ya zauna kusa da Abba, yana fadin, "Abba, ka tuna fa cewa ita din yarinyarka ce. Idan muka koreta, ta ina zata fita? Kuma menene ma zai faru da ita a waje? Kayi hakuri, wallahi tayi nadama."

Abba ya ja numfashi mai karfi, ya kalli ni da idanu masu tsananin tsawa. "Ramlah, wannan shine na karshe! Idan kika sake aikata irin wannan abu ko wani abu da zai jawo mana magana, wallahi sai kin bar gidan nan har abada! Baki da sauran uzuri!"

Na daga kai a hankali, ina kuka, na goge hawayena. "Nagode Abba. Wallahi bazan sake ba. Na yi alkawari zan gyara halina."

Yaya Abbas ya kama hannuna yana rarrashi. "Kin ji ko Ramlah? Ki natsu, ki daina abubuwan da zasu sa kowa ya zarge ki."

Abba ya mike daga kujera yana girgiza kai. "Ba zan kara dauka ba idan wani abu makamancin wannan ya faru. Kuma ki daina amfani da TikTok gaba daya. Baki da wani abu da zai rufe ki sai karatu. Na gama magana."

Na gyada kai cikin jin kunya, na share hawayena. Mumy ta yi tsaki, ta juya ta fita daga falon, tana cigaba da mita. Yaya Abbas ya dube ni, ya yi murmushi mai sanyaya zuciya.

"Ki daina kuka, kin ji? Na san kina cikin tsaka mai wuya, amma ki natsu. Abba ya yafe miki amma kada ki sake abinda zai sa ya fita daga hayyacinsa."

Na yi masa godiya cikin sanyin murya.

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA ASHIRIN.

DUBAI INTERNATIONAL AIRPORT...

Wata katafaren motar alfarma ce ta tsaya a bakin ƙofar VIP na filin jirgin sama na Dubai International Airport, inda ake ganin yanayin tsare-tsaren masu kuɗi kawai. Daga cikin motar ta fito, sanye cikin shiga mai tsada - farar foguwar riga ta Valentino, wadda ta yi rolling da kanta cikin salo. Gilashin ido na Gucci mai launin toka ya ƙara bayyana kyanta, tana tafiya cikin nutsuwa da kima, kamar wacce aka shirya don kasaitaccen liyafa.

Kafin ta shiga cikin jirgin, direbanta ya buɗe ƙofar cikin ladabi, yana mai cewa

"Madam Ayshatu, jirginku na jiran ku."

Ta ɗan gyaɗa kai da murmushi mai taushi, sannan ta taka cikin sauƙi zuwa cikin jirgin. Jirgin kuwa ba ƙaramin Na alfarma ba ne wata katafaren Gulfstream G700 Private Jet, mai ɗauke da cikakken ɗakin kwana, falo na alfarma, da kuma ofishin sirri. An tsarashi da kujeru na fata masu sheƙi, launin fari da ja a ko'ina, yayin da ɗakin ya cika da ƙamshin turaren Tom Ford Oud Wood.

Ta zauna kan babban kujera mai launin toka, tana lumshe idanu cikin annashuwa. Da sauri ta ɗauki wayarta iPhone 15 Pro Max, tana duba ko mijinta ya kira ko ya amsa saƙonninta. Amma har yanzu shiru. Ta aika masa da saƙonni masu yawa a cikin WhatsApp, amma babu alamun cewa ya karanta.

Tana jin wani irin tsananin fushi yana tasowa, amma ta daure, tana kwantar da hankalinta. As'ad, mijinta, attajirin da ya mallaki katafaren kamfanin gine-gine da harkokin kuɗi a Dubai da Nigeria kuma ɗa na hudu ga sarkin Garin, bai taɓa yin wannan irin shiru ba. A koyaushe yana amsa kiran ta ko saƙon ta. Amma yanzu? Wata zuciya ta ɗauke ta har sai da ta danna numfashi mai nauyi.

Jirgin ya tashi cikin nutsuwa, ta rike kofin ruwan Zuma mai sanyi da aka ajiye mata daga mai yi mata hidima a cikin jirgin, tana ci gaba da duba wayar. Har ta sauka a filin jirgin saman Charles de Gaulle International Airport a Paris, babu wani kira daga As'ad.

Direbanta ya yi mata gaisuwa tare da cewa:

"Madam Ayshatu, motar da aka tanada don ku na jiranku."

Ba tare da magana ba, ta shiga cikin motar Rolls-Royce Phantom, wacce ta kasance tana jiranta. Sannan suka nufi katafaren otal ɗin da aka shirya mata Ritz Paris, daya daga cikin otal-otal mafi tsada a duniya.

Ta kara gwada lambar mijinta sau uku, amma har yanzu ba'a daga ba. Da takaici, ta yi tsaki mai tsawo tana kwanciya a kan gadon otal din, cike da damuwa.

"Da Ayshatu kake magana, As'ad!" Ta furta a hankali, tana jin wani irin nauyi a zuciyarta.

PARIS, FRANCE...

Tana cikin ɗakin otal na Ritz Paris, Ayshatu ta kalli agogon zinariya na Rolex Daytona dake hannunta. Wata murya mai laushi daga cikin wayarta ta sanar da ita cewar tana da saura awanni biyar kacal kafin ta bar Paris ta nufi Najeriya. Wannan lokaci kaɗan ne, don haka sai ta fara sauri wajen kammala duk wasu ayyuka da suka kawo ta garin.

Bayan ta gama wasu muhimman ganawa da wakilan kamfanin da As'ad, ta koma ɗakinta don yin wanka. Bayan haka, ta zabi wani haɗaɗɗen kaya wanda ya dace da yanayin hutawa da tafiya riga da wando palazo na Balmain, mai launin toka mai duhu, wanda ta yi rolling da zane mai kyau a kanta. Fuskar ta a maƙure da gilashin ido mai duhu na Dior, sai ƙamshin turaren Creed Aventus for Her ya mamaye ɗakin. Duk wanda ya ganta, ba sai an gaya masa cewa matar mai kudi ba ce ba.

Ta sauka daga ɗakin otal cikin nutsuwa, direbanta yana jiran ta a waje tare da motar alfarma Bentley Mulsanne. Bayan sun isa filin jirgin sama, ta hau cikin jirgin sirrin ta cikin girmama.

LAGOS, NIGERIA...

Bayan awanni da ba su wuce uku ba, jirgin ya sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammed International Airport, maimakon a filin jirgin sama na birnin tarayya Abuja kamar yadda aka tsara farko. Wani sabon tsari da aka yi ya sa dole ta sauka a Lagos saboda wasu muhimman ayyuka data tsara a can.

Daga nan aka yi mata iso zuwa daya daga cikin manyan otal-otal na garin Eko Hotel and Suites wanda aka tanada don hutawar ta. Tana shiga, wani mutum mai kula da baƙi ya ɗauke mata jakar ta cikin ladabi, yana mai cewa

"Barka da zuwa, Madam Ayshatu. An tanadi daki mai alfarma a gare ki."

Ta yi murmushi kaɗan, tana tsayar da shi da hannunta. Bayan ta shiga dakin, ta ajiye wayarta a kan gadon alfarma, sannan ta zauna tana yin la'akari da duk abubuwan da suka faru cikin kwanaki kadan. Tana jin nauyin gajiya, amma ta san cewa a nan ne zata samu damar hutawa kafin ta tafi birnin tarayya.

Bayan ta ci abinci mai sauƙi na girke-girken Continental, ta sake shigewa cikin wanka mai sanyi. Bayan haka, ta canza kayan ta zuwa Atampha mai launin shudi da zinariya, wanda ya bayyana kyanta na Hausa Fulani sosai. Ta yafa likaf mai haske a saman kanta, har ba wanda zai gane cewa itace matar attajirin nan da duniya ke magana akai.

Tana barin otal din cikin salo mai cike da wayewa da kamewa, ta samu damar fita ba tare da wani ya gane ta ba. A wannan lokaci, tana da wani tsari mai matukar muhimmanci a Lagos kafin ta zarce zuwa Abuja.

Tafiyarta ba ta yi sauƙi ba, saboda motar ta nufi wasu unguwannin da ke cikin garin Lagos. Bayan tafiya mai nisa da kusan sa'a guda, ta ji kamar an sauke nauyi daga zuciyarta, yayin da ta iso wani yanki da ke kusa da kasuwa. Tana ganin yanayin kasuwar nan, sai ta fahimci cewa wannan ba sabon wuri ba ne a gare ta. Duk da sauye-sauyen da aka samu, akwai alamun cewa ta saba zuwa wannan wuri a can baya.

Ta taka cikin kasuwar, tana tafiya cikin natsuwa. A cikin kasuwar, ta tsaya a wajen da ake sayar da kyalle, inda wani babban fili ke cike da jan kyalle masu kyau da kalar alfarma. Ta zabi guda biyu cikin hikima, tana tambayar farashi cikin yaren Yarbanci da nutsuwa. Mai sayar da kayan ya yi murmushi, yana yabawa yadda ta iya harshen, sannan ya bata farashi mai sauki.

Bayan ta gama sayayyarta, ta koma motar, amma zuciyarta tana sanar da ita cewa akwai wata hanya mai tsawo da dole ta bi. Daga nan ta yanke shawarar ci gaba da tafiya ta hanyar da ta saba a da. Tana cikin tafiya, sai ta tsaya a wani wuri da ake tsayawa domin shiga Bus.

Sannan ta samu bus mai dauke da mutane na ciki da waje. Tana shiga, ta zabi zama a cikin dan kyakkyawan wuri, tana lumshe idanuwa kamar mai tunani mai zurfi. Wannan tafiyar mai nisan gaske ta kai su kusan awanni hudu kafin su isa wani gari a gefen birni, cike da gajiya.

Tana sauka daga bus din, ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Ta bude jakar ta, ta dauko snacks da drinks da ta hada tun daga otal din. Bayan ta dan ci, sai ta duba agogonta, ganin cewa lokaci na wucewa sosai. A wannan gefen gari, babu motocin alfarma kamar yadda ta saba gani, sai mashina kawai ake amfani da su.

Wani matashi mai mashin ya karaso gare ta, yana tambaya cikin yaren mutanen garin

"Madam, ina zaki?"

Ta tsaya tana tunani, sannan ta bayyana masa garin da take son zuwa. Sai kuwa ya ɗan kalle ta da mamaki, yana cewa

"Madam, garin da zakije, wanda ake sallah ko wanda ba'a sallah?"

Ta ɗan yi shiru kafin ta amsa cikin sirri

"Wanda ba'a sallah."

Matashin ya gyara mashin dinsa sannan ya ce

"Toh, farashin shi dubu goma ne."

Ba tare da wata gardama ba, ta amince da farashin, Ta hau kan mashin, suna tafiya a cikin duhun dare mai ɗan kauri, iska tana kadawa a fuskar ta.

Bayan tafiya mai nisan gaske a kan mashin cikin duhu da iska mai sanyi tana busawa, sun iso wani wuri da ya fara nuna alamun bambanci daga sauran garuruwan da suka ratsa. Garin yana da wata irin yanayi mai ban tsoro titunan ƙasa ne, cike da laka da ƙazanta. Gidaje masu fasali na gargajiya suna kewaye da dutse da ciyawa mai tsawo, kuma akwai hayaki mai ƙamshi mai nauyi yana tashi daga wani yanki na tsakiyar garin.

Kafin su shiga cikin garin sosai, mai mashin din ya tsaya, yana kallon Ayshatu da idanun da ke nuna rashin jin daɗi.

"Madam, ki kula sosai da wannan wuri. Babu wani imani a cikin wannan gari. Matsafa ne ke nan."

Ayshatu ta ja numfashi mai nauyi, tana jin wani irin bugun zuciya ya sauya. Amma ta ƙara rike kanta da kima. Ta ciro wani ɗan kuɗi daga cikin jakar ta, ta miƙa masa tare da cewa

"Nagode. Zan ci gaba daga nan."

Mai mashin din ya yi mata kallon tausayi, sannan ya juya mashin dinsa da sauri ya bar wajen. Bayan tafiyarsa, sai ta tsayar da numfashi tare da kame kanta, tana kara tabbatarwa cewa dole ne ta yi wannan tafiya domin amfanin rayuwarta.

Garin ya kasance cikin tsananin shiru, sai fitar hayaki daga tsakar unguwa da wasu ƙananan yara su biyu suna wucewa suna jera wakar da ke ɗauke da kalmomi masu tsoro

"Ba mai rai, ba mai gaskiya, cikin duhu muke, mu bauta wa jini."

Ayshatu ta ɗan tsayar da tafiyarta, zuciyarta na bugawa da sauri. Lokacin da ta isa tsakiyar garin, ta hangi wata tsohuwa tana zuba wasu irin ganyayyaki a kan wata ƙaramar wuta, tana zazzaga wasu kalamai a yaren da ba a fahimta. Kallo guda da ta yi mata, sai ta ga idanunta na zaro kamar na maciji.

Wani mutum mai kyan jiki ya matso kusa da ita, yana magana da murya mai taushi amma mai ban tsoro

"Me kike nema a wannan gari, matar mai kudi?"

Ta ɗan tsaya tana tunanin yadda ya gane ta. Tana iya jin fitar turaren Creed daga jikinta, wanda ya yi tsami da ɗan gumi saboda gajiyar tafiya. Ta kame kanta, tana cewa

"Ina neman Baba Asabe."

Mutumin ya yi murmushi mai cike da mugunta, yana nuna mata wani gida a gefen kasuwar duhu, yana cewa

"A can ne."

Ta ɗan runtse idanu, tana jin zuciyarta na tsananta bugawa. Amma duk da haka, ta ƙara ƙarfin hali, tana tafiya a hankali zuwa gidan. Gidan yana da tsohuwar kofa mai ƙarfe, akwai hotunan tsafe-tsafe a jikin bango, da wasu alamu na dodanni da aka zana da jini.

Ta ɗaga hannunta, tana neman bugawa, amma kafin ta kai ga dukan ƙofar, sai ta ji murya daga ciki

"Shigo, Ayshatu. Tuni na san kin iso."

Zuciyarta ta buga da karfi, amma ta tura ƙofar ta shiga cikin gidan mai duhu. Wata irin murya mai ƙarfi ta karade dakin

"Yau shekara biyar kenan, Ayshatu. Me ya dawo da ke garin nan?"

Cikin jin zafi a zuciyarta, ta ce:

"Burukana sun cika, kuma ina son na daidaita abin da ya dusashe tun lokacin da na baro nan."

Tsohuwar da ke zaune cikin duhun ɗaki ta fito, tana da jajayen idanun da suka bayyana cikin duhun. Ta yi murmushi mai cike da mugunta, tana cewa

"Ai nasan za ki dawo. Kuma na san dalilin dawowarki kin zo neman ƙarfin da aka sake miki. Amma fa, wannan karon akwai sharadi."

Ayshatu ta yi shiru, tana jin yadda maganar ke ratsa zuciyarta. Tsohuwar ta yi dariya mai sauti mai cike da tsoro:

"Kin san sharadin kenan sai kin sadaukar da wani abu na kusa dake kafin a dawo miki da wannan ƙarfin Mulkin mijinki."

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA ASHIRIN DA DAYA

Ayshatu ta tsaya cikin tsananin tashin hankali, zuciyarta na bugawa kamar ta tsage. Cikin duhun dakin, tsohuwar ta cigaba da kallon ta da jajayen idanunta masu cike da mugunta. Wuta mai ƙyalli tana ci gaba da kuna a tsakiyar dakin, tana fitar da hayaƙi mai ƙamshi mai nauyi.

Tsohuwar ta matso kusa da Ayshatu, tana murmushi da wani irin yanayi na tsoro, tace

"Nasan komai game da ke, Ayshatu. Na san duk abinda yake faruwa akan sabuwar amaryar mijinki kike nan ko? Ai tuni sun gama aikinsu. Sun yanka sun sadaukar da jini, sun mallake zuciyar As'ad. Aikinsu mai ƙarfi ne sosai - sai sadaukarwa mai ƙarfi kafin a kwace shi daga hannunsu."

Ayshatu ta ji wani irin sanyi ya ratsa cikin ƙashinta. Cikin rawar murya, ta ce

"Ko nawa ne zan bayar! Amma banda abunda zan sadaukar yanzu bana haihuwa, ban da wanda zan bayar. Ina son mijina har abada, bana son wata soyayya ta shiga tsakaninmu."

Tsohuwar ta ɗan yi dariya mai sanyi, tana jinjina kai

"Ayshatu. Amma duk wani iko da aka yi akan mijinki sai dai sadaukarwa -yanka na jini ko kuma wani abu mai muhimmanci gare ki. Kuma mafi sauki a gare ki Shine ki bada sadaukarwar mahaifarki!"

Ayshatu ta yi shiru, tana ji kamar an danna mata dutse a ƙirji. Tsohuwar ta matsa kusa sosai, tana cewa

"Sadaukar da mahaifarki zai tabbatar da cewa duk wata soyayya da aka mallaka wa mijinki ta ƙare. Kinji? Aikinsa kuwa, sai munyi kwanaki bakwai munayi, a nan cikin gidan nan. Bazakiyi sallah, babu ambaton Allah, babu tsarki. Har sai mun kammala, sannan zaki ga yadda zan fitar da wannan sabuwar amaryar da kafafuwanta - mijinki kuma zai koma gare ki da cikakkiyar soyayyarsa."

Ayshatu ta sake kallon tsohuwar, tana jin yadda tsoron da ke ranta ya fara canzawa zuwa wani irin natsuwa. Ta ja numfashi mai nauyi, sannan tayi murmushi mai cike da kauna da ƙarfi

"Indai wannan ne, ai bana jin matsala. Zanyi duk abin da kika bukata - domin As'ad yana da matukar muhimmanci a gare ni. Ban damu ba sadaukar da komai ma zan iya idan hakan ne zai sa ya dawo gare ni."

Tsohuwar ta yi dariya mai tsawo, wuta na ƙara buguwa cikin dakin. Ta tallafi hannun Ayshatu da natsuwa, tana cewa

"Ai na san cewa kin shirya. Ki zauna nan, zamu fara gobe. Amma ki sani, babu mai fita daga wannan gidan har sai an kammala aikin. Zaki sha wahala, amma idan kika tsallake wannan gwagwarmaya, duk wata mace da ta kuskura ta shiga tsakanin ki da mijinki zan halakar da ita!"

Ayshatu ta ɗan lumshe idanuwa, tana jin wani irin ƙarfin zuciya na shigarta. Cikin zuciyarta, ta san cewa wannan matakin da ta ɗauka ya wuce hankali, amma soyayyar da take yi wa As'ad ta sa ta yarda da wannan hadaya.

******

Tafiya suke cikin tsananin izza da kasaita, suna sauka daga motar Rolls-Royce Cullinan mai launin toka mai kyalli, direban ya buɗe ƙofa da girmamawa. As'ad ya fito cikin farar babbar riga ta Shadda hula mai adon azurfa, takalmin fata na Tom Ford, yana tafiya cikin izza da natsuwa. Amaryarsa, Haneefah, tana gefensa cikin shiga ta alfarma riga da zani na Lace mai launin ruwan madara da Alkyabba baƙa ajiƙinta.

Sun shiga cikin falon fadar, As'ad ya durƙusa cikin tsananin girmamawa ga mahaifinsa, ya tsuguna tare da rusunawa kamar yadda ake yi wa mai martaba. Cikin ladabi da murya mai laushi ya ce

"Assalamu Alaikum wa rahmatullahi ya Mai Martaba, ubanmu kuma sarkinmu, Allah ya ƙara maka girma da daukaka."

Mai Martaba ya yi murmushi mai natsuwa, yana amsa cikin farin ciki

"Wa'alaikumus salam As'ad, ka tashi. Na ganka cikin kwanciyar hankali. Amma yanzu zaka koma birnin tarayya da amaryarka? Na zata ka tsaya a nan saboda kasuwancin ka na gida."

As'ad ya tashi cikin kamewa da izza, yana magana cikin natsuwa

"Hakane, Mai Martaba. Amma akwai taruka na kasuwanci da dole na halarta a Abuja, tare da wasu manyan kamfanoni masu zuba jari. Kuma na yanke shawarar tafiya da Haneefah domin cigaba da sabuwar rayuwar mu. Insha Allah, zan kula da ita kamar yadda aka tsara."

Sarki ya ɗan gyada kai, yana mai fahimtar dabarar As'ad. Yasan cewa As'ad yana da sanin ya kamata kuma yana da ikon tafiyar da kasuwancinsa ko ina. Ya kalli Haneefah, wacce ta durƙusa da girmamawa, ya ce

"Allah ya albarkaci tafiyarku. Haneefah, ki kasance mai biyayya ga mijinki, ki nuna masa kauna da kulawa. Kai kuma As'ad, ka tabbatar da cewa ka kula da ita kamar yadda aka saba a gidan sarauta."

Sun nufi bangaren Hajja, matar sarki ta biyu, wacce ke zaune cikin falo mai yalwa. An kawata falon da kujerun fata masu launin coffe da labulen siliki na Dior. Haneefah ta durƙusa cikin ladabi, tana cewa

"Hajja, mun zo muyi sallama."

Hajja ta yi murmushi mai natsuwa, tana kallon As'ad da Haneefah da kulawa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull