Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 14
Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 14: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 14. "Allah ya kiyaye hanya. Haneefah, ki riƙe…
3,352 words
"Allah ya kiyaye hanya. Haneefah, ki riƙe mijinki da kyau. As'ad, ka kula da amaryarka. Allah ya sa kuyi zaman lafiya." Tafada tana kallon yadda gabadaya hankalin ɗan nata ke ƙan haneefa gaba daya yamakasa magana har suka bar gurinta.
Daga nan suka shiga bangaren Fulany Maryam, wacce take cikin shiga ta alfarma riga mai launin baki. Tana kallon Haneefah da murmushi, tana cewa
"Haneefah, kisani zamantakewar aure tana bukatar hankali. Ki kula da magungunan da na baki, kada ki yi sakaci. Ki tabbatar cewa kin bi duk umarnina don ki samu zama mai nagarta a gidan mijinki."
Haneefah ta amsa cikin biyayya
"Mama, insha Allah zan bi duk umarninki. Zanyi yadda kika ce."
Sun fita cikin tsari da izza, suna tafiya zuwa filin jirgin sama a cikin motar Mercedes-Maybach S650 mai launin kore. Jirgin masarauta - Bombardier Global 7500 Private Jet yana jiran su. Suna shiga, aka gaishe su cikin kulawa, sannan suka zauna a cikin kujerun fata masu laushi, yayin da masu hidima suka kawo kayan sha na alfarma.
As'ad ya kalli Haneefah yana cewa
"A nan Abuja ne zamu ci gaba da rayuwa, zan tabbatar da cewa komai ya kasance cikin tsari da alatu kamar yadda aka saba. Ki kasance mai biyayya kamar yadda kike yanzu."
Haneefah ta yi murmushi mai kyau, tana jin zuciyarta na farin ciki. Jirgin ya tashi daga Zaria cikin nutsuwa, yana nufin birnin tarayya Abuja, inda sabon zamani na soyayya da iko zai cigaba.
Jirgin masarauta ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International Airport cikin nutsuwa da tsari. A waje kuwa, tawagar motoci na alfarma sun tanada, babu abin da aka gani sai jerin motocin Mercedes G-Wagon guda biyar masu launin baƙi mai kyalli, da kuma wani babban Range Rover Autobiography a tsakiya.
Haneefah ta fito daga cikin jirgin, tana kallon motoci da tawagar da suka taho don tarbarsu. Cikin tsananin mamaki da ruduwa, ta yi shiru tana nazari. Duk da cewa ta san As'ad yana da kudi fiye da sauran 'yan uwansa, sai da wannan al'amarin ya bata mamaki sosai. Cikin zuciyarta, tana tunani
"Ashe As'ad yana da kudi fiye da yadda nake tunani! Na dade ina jin labarinsa, amma yau na tabbatar!"
Daya daga cikin direbobi cikin rigunan manyan dogarai ya buɗe ƙofar motar a girmamawa, yana cewa
"Barka da zuwa, Hajiya Haneefah. Muna murna da zuwanku."
Ta shiga motar cikin kamewa da izza, tana jin tamkar ta isa wani wuri mai alfarma. As'ad kuwa yana magana da wani daga cikin masu tsaro kafin ya dawo ya shiga motar tare da ita. Haneefah ta kalli fuskarsa tana murmushi, tana jin kamar ta cimma mafarkinta.
Tafiyar ba ta yi nisa ba kafin su isa gidan wani katafaren gida mai tsawo da aka zagaye da babban ganuwa mai launin fari.A kofa, akwai tsararrun dakunan masu gadi masu sanye da kayan tsaro na alfarma, suna tsaye cikin izza.
Bayan motoci sun kutsa cikin farfajiyar gidan, an buɗe ƙofar babbar falon da alama mai kuɗi ne ya gina - ko'ina zinariya da ƙamshi na turaren Creed Royal Oud ya mamaye. Harabar gidan cike take da fulawowi masu kala-kala da fure-furen alfarma.
As'ad ya fita daga motar cikin kamewa, yana duban fuskarta yana cewa
"Maraba da zuwa gidan ki, Haneefah."
Ta yi murmushi amma har yanzu kanta a ɗaure yake. Da yake ita ta taso daga gidan kudi amma wannan gida ya fi komai da ta taɓa gani. Tsan-tsan kauyanci ya bayyana a fuskarta duk da cewa tana ƙoƙarin ɓoye.
As'ad ya juya yana kallon daya daga cikin dogarawan dake tsaye a kofar wani babban sashe mai launin toka da zinariya.
"Ku tabbatar an kaita bangaren ta. A nan ne zata zauna."
Ta dan matsa kusa da shi tana cewa
"Kana nufin na shiga bangaren ka ne ko?"
Wani daga cikin masu tsaron gidan ya tsaya, ya ce da ladabi
"Hajiya, a gidan sarauta, sai miji ya amince kafin amarya ta shiga turakarsa. Anan mulki da tsari na gado ne."
Haneefah ta ɗan yi tsaki cikin ranta, tana jin wani iri. Duk da cewa ta san tsarin sarauta yana da tsauri, bata zaci haka ba. Dole ta bi ka'ida kafin ta shiga dakin mijinta.
Suka shiga wani katafaren bangare mai yalwa wanda aka tanada don ta. Dakunanta ya cika da kayan alfarma gado mai babbar murfin mudubi, fitila mai kyalli na krista, da manyan madubai na Louis Vuitton. Ta tsaya tana kallon ko'ina, tana mamakin yadda dakin yake da kyau fiye da tunaninta.
Lokacin da ta dube ta taga daga baranda, sai ta hangi wani bangare na gidan da aka yi da alamar tsari da tsabta. Wata dogara ta leƙo cikin ladabi tana cewa
"Hajiya, wannan bangaren na Uwargida Aysha ne."
Ta dan yi tsaki cikin zuciyarta, tana tunanin yadda zata samu hanyar cire wannan mata daga gidan.
Ta yi wanka sannan ta shafa turaren asiri na musamman da Fulany Maryam ta bata wanda aka ce yana kashe duk wata soyayya ta daban da zata shiga tsakanin ta da mijinta.
"Hajiya, muna yi miki barka da zuwa. Mune masuyi miki hidima daga yanzu."
Ta yi murmushi mai dauke da izza, tana kiran wayar As'ad, amma bai dauka ba. Zuciyarta na kara tsananta da gajiya, tana jin cewa dole ne ta tabbatar da cewa babu wata mace da zata kuskura ta shiga tsakanin su.
*****
As'ad ya shiga bangarensa, zuciyarsa cike da wani irin yanayi na rashin nutsuwa. Duk da yadda dakin yake a tsare tsaf tsaf da kamshin turaren Creed Royal Oud mai cike da sanyin zuciya bai ji kwanciyar hankali ba.
A hankali ya cire rigarsa, ya shiga wanka don kwantar da hankalinsa. Yayin da ruwan ke malala a jikinsa, yana jin tamkar wani nauyi ya ragu daga jikinsa. Da ya gama, ya sanya jallabiya mai launin toka mai taushi, ya feshe jikinsa da turare na Tom Ford Oud Wood.
Ya kwanta a gado, yana jin yana bukatar hutawa,Atake bacci mai nauyi ya dauke shi ba tare da ya shirya ba. Bai farka ba sai wajen karfe hudu, yashiga mamaki yadda ya yi bacci har ya wuce lokacin sallah. Shi da bai saba barin sallah a jam'i ba, amma yau sallar ya kasance a dakinsa.
Da zarar ya gama sallah, sai wani yanayi na rashin nutsuwa ya sake kamashi. Bai iya jurewa ba, sai ya sa takalmin fata mai sauki, ya fito zuwa bangaren Haneefah.
Tunda ya kusanto bangaren, masu aikin da aka tanadar mata suna gaishe shi da girmamawa, suna daga kai cikin ladabi. Yana shiga, ya hango ta daga cikin dakin nata mai kyau, tana zaune a gaban babban madubi mai haske, tana shafa jambaki mai ja a leɓenta.
Ta dan yi murmushi tana kallonsa ta madubi, sannan ta juya kanta gefe kamar mai jin haushi. As'ad ya ɗan yi murmushi yana kallon yadda take haɗa fuska da tsare jikinta cikin shigar abaya mai launin ruwan madara, da gyale mai kyalli na zinariya.
Ya matso kusa da ita cikin salo, yana cewa da murya mai laushi
"Haneefah, nadanyi bacci ne Ki yi hakuri."
Ta ɗan yamutsa fuska tana tsaki a hankali, tana cewa
"Ni kam ba matsala, ai dama haka kake. Kaga yadda ka barni Ni ɗaya Tun safe?"
Ya ja numfashi cikin sanyi, sannan ya durƙusa a gabanta, ya ɗauki hannunta cikin natsuwa.
"Ki yi hakuri. Ban yi nufin takura ki ba. Ki gafarce ni."
Tana jin murya mai laushi daga bakinsa, sai tsananin so ya mamaye zuciyarta. Ta ɗan yi murmushi, ta ce
"Yanzu na yafe maka, amma fa ka yi min alkawari cewa ba za ka sake ba."
As'ad ya kalle ta, yana ganin yadda kyanta ke ƙara bayyana a ƙarƙashin hasken fitila. Bai jira amsar ta ba, ya matso kusa da ita, yana kamo hannunta da salo, ya ja ta ta zauna a kan cinyarsa.
Ta ɗan yi dariya mai laushi, tana ƙara matse jikinta a jikin sa. As'ad ya rungume ta, yana jin yadda numfashinta ke tsananta. Haneefah ta sa hannunta a wuyansa, tana zagaye masa gashinsa cikin natsuwa.
Ya dube ta da ido mai cike da soyayya, yana cewa da murya mai laushi
"Kin san kina da kyau, ko?"
Ta lumshe idanu, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa. Ta matsa da fuskarta kusa da shi, tana jin kamshin turaren sa yana narkar da zuciyarta. Hannunta ya gangaro zuwa ƙirjinsa, tana shafar jikinsa da laushi, tana jin yadda sanyin fatar sa ke tsuma zuciyarta.
A hankali ya sa hannu a cikin gashinta mai laushi, yana ɗan ja da salo, sannan ya sumbaci goshinta cikin tsananin nutsuwa. Tana jin yadda hakan ya shiga jikinta, ta rungume shi sosai, tana jin tamkar ta narkar da kanta cikin jikin sa.
Ya ɗaga fuskarta da hannu biyu, yana kallon idanunta masu kyalli, sannan ya ce cikin murmushi
"Kin san ke ce farin cikina? Babu wata mace da zata iya shiga tsakanina da ke."
Ta yi murmushi mai cike da jin dadi, tana lumshe idanu, sannan ta kai bakinta zuwa nasa, suna jin yadda zuciyoyinsu ke bugu da sauri.
Ya sauke numfashi mai nauyi, yana jin wani irin farin ciki na musamman ya lullube shi.
"Ni fa, Haneefah, ban taba jin irin wannan soyayya ba. Kina da wani irin salo da ke sa na kasa jurewa," ya furta da gaske.
Hankalin As'ad gaba daya ya fita daga hayyacinsa, yana jin yadda Haneefah ke sarrafa shi da salo mai dadi da soyayya.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ASHIRIN DA BIYU.
Arewabook @nanadiso10
Kusan mako biyu kenan babu wanda ke iya samun As'ad. Tun lokacin da ya koma Abuja tare da Haneefah, babu wani labari daga wurinsa. Abin mamaki shi ne, ko Mai Martaba Sarki ya kira wayarsa, ba ya amsawa. As'ad, wanda aka sani da biyayya da mutuntawa, yanzu tamkar ya bar duniya, ya koma bangaren Haneefah kacokan.
Hajja tana zaune cikin falonta mai yalwa, cikin damuwa da tunani. Ta kishinƙide cikin riga mai launin ruwan toka, tana fuskantar Abba, kanin As'ad, wanda ke tsaye a gefenta, cike da damuwa.
"Hajja, wallahi na kira shi sau da dama, amma ba ya ɗauka. Har P.A dinsa ma na kira, ya ce yanzu As'ad ba ya sauraron kiran kowa sai dai abinda Madam Haneefah ta fada."
Hajja ta sauke numfashi mai nauyi, tana jin yadda zuciyarta ke kuna. Ta girgiza kai cikin takaici
"Abba, akwai babbar matsala akan wannan lamari. Ni kam na kasa gane abin da ke faruwa. Ashe Fulany Maryam ta ci nasara akan As'ad? Na ce tun farko kada ku yi wasa da addu'a. Yanzu da alama ta mallake shi, ba kawai zuciyarsa ba, har da hankalinsa gaba ɗaya."
Abba ya tsaya yana nazari, yana jin yadda wannan magana ke tayar masa da hankali. Yana kallon yadda Haneefah ta yi nasarar canza As'ad cikin lokaci kadan.
"Hajja," Abba ya yi ƙasa da murya, "Mamy ta je gidan As'ad a Abuja domin ganinsa, amma aka ce mata ba za ta shiga ba saboda Madam Haneefah bata bada izini ba. Ta dawo gida cike da takaici. Wallahi, na fara jin tsoro, Hajja."
Hajja ta rike kai tana jin yadda lamarin ke kara dagulewa. Ta sauke numfashi mai nauyi, tana jin zafi a zuciyarta. Ta kalli Abba da ido cike da damuwa
Na roƙi Mai Martaba amma Sarki yace kada a takura masa tunda zaman lafiya suke yi."
"Zaman lafiya?" Abba ya ja numfashi cikin takaici,
"Hajja, wallahi wannan ba zaman lafiya ba ne. Fulany Maryam ta yi nasara. Ba ki ji ba? Jikarta da take a Asubuti ta rasu, amma ko ajikinta ba ta je ba. Idan mace ta iya haka, me zai hana ta kwace zuciyar As'ad gaba ɗaya?"
"Wallahi kuwa," Hajja ta amsa tana girgiza kai,
"ina cikin tsananin damuwa. Na san As'ad da kasuwanci da aiki tukuru, amma yanzu bai kira ni ba, bai nemi shawara ba, ba ya ko amsa waya. Wannan ai ba halinsa bane."
Abba ya rage murya, yana kallon yadda Hajja ke nuna tsananin damuwa
"Hajja, ko dai ayi masa ruƙiya ne? Ni kam na fara jin tsoron Haneefah."
Hajja ta zura ido cikin tunani, ta ja numfashi da kyar
"Ruƙiya kuma? amma fa tayaya za a yi masa ita idan Haneefah ce ke iko da shi gaba ɗaya? Wallahi, ba ni da wani iko a yanzu. Za mu cigaba da addu'a, Abba. Na san cewa babu wani abu da ya fi addu’a ƙarfi. Amma a wannan lokaci, ku ma ku tsananta addu'a a ko da yaushe. Kada ku yi sakaci. Domin idan da gaske Fulany Maryam ta yi nasara, to kuwa As'ad zai iya rasa dukiyarsa da hankalinsa gaba ɗaya."
Abba ya amsa cikin jin ƙwarin guiwa
"Toh, Hajja. Zamu yi duk mai yiwuwa. Allah ya bamu damar ceto shi daga wannan kunci."
Hajja ta kalli Abba da idanu masu cike da damuwa, sannan ta ce
"Allah ya sa haka. Yanzu dai zan tsananta addu’a, ko Allah ya warware wannan asiri da aka yi masa."
******
Fulany Maryam tana zaune a falonta tana hutawa sai ga wayarta tana kara. Ta duba sunan mai kira, ta ga Haneefah ce. Ta ja tsaki, sannan ta dauki wayar cikin bacin rai
"Dan ubanki! Ina ce kwanciya da namiji na turaki? Na ce, kwanciya da saduwa na turaki! Sha sha sha! Ke kuwa wacce irin macce ce wacce batasan me ke mata ciwo ba! Kin zuba masa maganin a abinci kuwa?"
Haneefah ta tsaya daga gyaran kanta a madubi, ta turo baki kamar wata yarinya tace
"Mama, wallahi na manta ne."
Fulany Maryam ta sake jan tsaki
"Lallai kin manta! Yanzu kina son ya dawo hayyacinsa ya kore ki kenan? Kin san wannan aure na ikon asiri ne. Ko kallo wallahi baki ishesa ba idan babu magani. Ke kuma sai ki tsaya soyayya? Babu abinda ya dame ni da soyayya!"
Haneefah ta sauke numfashi mai nauyi, ta yi kasa da murya
"Mama, zan gyara. Wallahi, ba zan sake sakaci ba."
"To ki tabbatar da haka! Kada ki sake sakaci. Idan ba haka ba, wallahi zaki rasa komai. Ba soyayya ake ba, iko da mulki ake yi. Da an barki da soyayya, da tuni kin koma gida kina kuka."
"Na gane Mama, zan kula sosai," Haneefah ta amsa cikin ladabi, sannan ta kashe wayar.
Bayan ta kashe wayar, Haneefah ta mike da sauri, zuciyarta na harbawa. Ta nufi wardrobe dinta, ta bude drawer, ta dauki maganin sannan ta nufi dining. Ta bude abincin da ta shirya masa, ta zuba maganin cikin miyar, sannan ta gyara teburin cikin tsari.
Bayan ta gama, ta shiga wanka, ta feshe jikinta da turaren Gucci Bloom, sannan ta zabi wani leshi mai launin ruwan madara mai laushi wanda ya matseta sosai.
***
As'ad ya shigo bangaren nata cikin gajiya, yana jin kansa yana sara masa. Duk da haka, ya yi murmushi da kyar lokacin da ya ga yadda ta nannade kanta da gyale mai kyau.
"Sannu da zuwa, Ya As'ad," ta furta cikin shagwaba, tana matsowa kusa da shi. "Na shirya maka abinci na musamman."
Ya zauna a kan kujerar falo, yana kallonta da kyar. Haneefah ta zuba masa abinci cikin kulawa, tana masa shagwaba, tana taba hannunsa a hankali.
Yana ci, wani irin dadi da sanyi yana ratsa jikinsa. Amma daga bisani ya fara jin nauyi da sara-saran kai. Ya dubi Haneefah da alamar tambaya
"Kaina na ciwo... Bari na je na kwanta can na huta."
Haneefah ta dan ja hannunsa tana murmushi
"Ya As'ad, ka huta a nan mana. Banson naganka nisa dani.."
Ya girgiza kai da kyar
"Babu komai... kawai kaina ne ke ciwo sosai."
Duk yadda ta so ya tsaya, sai ya dage cewa zai koma bangarensa. Ya bar dakin yana jin kamar kansa zai tsage. Haneefah ta dan tsaki cikin takaici, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da karfi.
Bayan ya fita, sai ta kira P.A dinsa
"Kawo min takardun gidansa na Abuja da ya mallaka mata . Ajiye su nan." Tafada tana binsa da harara..
P.A din ya kawo takardun cikin natsuwa, ya miƙa mata, sannan ya fita. Haneefah ta duba takardun cikin natsuwa, ta nannade su a cikin wata jaka ta boye su a cikin drawer.
Yana kwance a daki, wayarsa ta fara kara. P.A din ya kawo masa wayar yace
"Ranka yadade hajja Nason magana dakai tace Na nema mata izini yafaɗa yana dan miƙa masa wayar tasa.
Da kyar ya iya daga wayar, yana jin muryar Hajja cikin damuwa
"As'ad, me ke faruwa da kai ne? Na kira baka dauka. Ka dage da addu’a, kaji? Ga kuma maganin nan da na turo, ka sha yanzu."
"To, Hajja," ya amsa da rauni, yana jin yadda kansa ke sara masa.
P.A din ya zuba maganin a cikin ruwa, ya miƙa masa, sannan As'ad ya sha. Bayan ya gama, bacci mai nauyi ya dauke shi.
Bayan bacci mai nauyi, As'ad ya farka da tari mai karfi, yana jin yadda hayaki ke cika dakin. Ya rike kansa, yana jin amai na taso masa.
Sautin karatun Al-Qur’ani ya fara tashi daga pop speaker. As'ad ya rike kansa, yana jin yadda wannan karatu ke ratsa zuciyarsa. Bai ga remote din ba, kuma ya rasa yadda zai kashe sautin.
"Me ke faruwa da ni?" Ya furta cikin rawar murya.
Ya kira P.A dinsa Amma Baya kusa kwatakwata wayar tashi ma akashe take
"Wannan abu ya yi yawa," ya furta da kyar, yana jin zuciyarsa tana tafarfasa.
*****
Baba Asabe tana zaune a tsakiyar dakin tsafe-tsafe, wuta tana ci a tsakiyar ɗakin, hayaki mai kauri na tashi sama yana cike da ɗakin. Hotunan tsafe-tsafe sun zagaye bangon, yayin da ƙamshi mai ɗaci ke ratsa hancin Ayshatu. Ta tsaya a gaban Baba Asabe, tana jin zuciyarta na bugawa da tsanani.
Baba Asabe ta daga murya da ƙarfi, tana cewa
"Yau kwanaki uku kenan da kamala aikinmu. Aysha, kin yi nasara! Sadaukarwa ta yi aiki! Zaki kasance sama da duk wata mace. As'ad Mallakin ki ne babu aure da wata mace. Iyayensa ma ba zasu kara yi masa maganar aure ba. Mulkin gidan As'ad yana hannunki."
Ayshatu ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, amma duk da haka, wani abu na damunta. Baba Asabe ta lura da yanayinta, ta ce
"Amma fa, Aysha, na gano wata cakwakiya. Ba mu iya magance ta ba."
Ayshatu ta rike hannunta cikin damuwa
"Baba Asabe, wace cakwakiya ce wannan?"
Baba Asabe ta yi dariya mai mugunta:
"Ba wata matsala mai girma ba ce. Amma fa akwai ɗan cikas. Idan har kina son As'ad sosai, zaki yi biyayya ga umarni. Wannan layar zata tabbatar da nasararki."
Ta zaro wata layar daga cikin kwando, ta mika mata
"Idan kin shiga bangaren As'ad, ki jefa layar a kasa. Haka kuma, idan zaki shiga bangaren amaryar, ki jefa ta kusa da sashjnts. Da zarar kin yi hakan, zamansu ya kare!"
Ayshatu ta dauki layar, tana jin tsoro
"Idan aka gani fa, Baba Asabe?"
Baba Asabe ta dara
"Ki kwantar da hankali. Duk lokacin da kika ajiye layar, zata bace kamar iska."
Ayshatu ta yi shiru, zuciyarta cike da fargaba. Baba Asabe ta ci gaba
"Ki tabbata kin yi yanka ranar Lahadi da Laraba. Kada ki Sallah da Asubahi ko La’asar. Idan kika saba, duk abinda kika yi zai lalace."
Ayshatu ta gyada kai, tana jin nauyin alhakin da ta ɗauka. Amma a zuciyarta, ta sha alwashin yin komai don ta mallaki As'ad.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ASHIRIN DA UKU
Arewabook @nanadiso10
Kullum cikin kuka nake, zuciyata cike da baƙin ciki da gajiya. Yanzu haka, ba ni jin daɗin komai a rayuwa. Wani lokacin ina ji kamar mutuwa ce kadai mafita. In bi mamata in huta da wannan wahala da azabar da nake ciki kullum.
Na zama kamar baiwa a gidanmu. Aiki kawai nake kamar wadda ba ta da wani amfani sai gyara da kwashe-kwashe. Momy na nuna min tsana sosai fiye da yadda zuciya zata iya ɗauka.
Mun gama jarabawar WAEC, yau kusan makonni uku kenan. Amma rayuwa ta ƙara tsananta. Abba kullum cikin zargi da tuhumata yake, ko motsi kawai na yi, sai Momy ta ga laifi a cikinsa.
A cikin waɗannan makonnin, na zama kamar jaka, babu kima. Na rasa komai tun da Abba ya kwace wayata. Wayar ce kaɗai nake amfani da ita don in ɗan ji daɗi a lokacin da muke jiran sakamakon jarabawar. Yanzu komai ya lalace.