Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 15
Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 15: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 15. Gaba ɗaya na cika da damuwa, ba kudi, ba…
3,049 words
Gaba ɗaya na cika da damuwa, ba kudi, ba walwala. Abokiyata Fatima ce kadai take ban 'yar tallafi ta bani kuɗin makaranta da sauransu. Amma yanzu itama ta tafi ƙasar waje gurin yayarta. Na zauna ni kaɗai, hawaye na gangarowa ba tare da ya tsaya ba...
Yaya Billy Kuwa Tsuntsuwar ƙiyayya da take ɗawainiya da zuciyar ta a kaina ta kai matakin da kalmomi ba za su iya warwarewa ba. Sau da dama na gane ta na ƙoƙarin zubamin wani abu cikin shayi ko lemo, amma Allah ya tsare ni. Duk lokacin da na lura da wani abu ba daidai ba, sai kawai na daina sha cikin hikima. Na gane cewa a hannunta babu amincewa, zuciyarta cike take da wata irin ƙiyayya mai zafi.
Ranar Juma’ar nan, ta zo da wani sabon sharri. Tace wai na satar mata dubu ɗari. Kafin a ce kwabo, gida ya rikide hayaniya ta cika ko ina! Aka nemi kuɗin nan har ƙasa, aka rasa. Duk da nasan ƙarya take, hakan bai hana Abba zafafa fushinsa akaina ba. Ya zarge ni da sata. Na tsaya gefe, zuciyata na rawar jiki, na rasa kalmar kare kaina daga abin da ban aikata ba.
Rayuwata ta cushe da ƙunci. Bana da ko sisin kwabo da zan iya siyan pant ko mai da zan shafawa jikina. Ranar da na nemi Momy tabani kudi, sai ta kalleni da raini, ta ce: “Je gurin ‘yan bariki, su ne zasu baki.” Wannan magana ta fasa zuciyata ƙiririƙi. Wace irin uwa ce ke fadi wa ‘yarta haka?
Abba kuwa sai ya mara mata baya. Ya ce tunda na fara sata, to ko naira biyar ba zai sake bani ba. Na shanye ƙuncina. Na fi kowa jin zafin yadda ya yarda da duk wata magana da ta fito daga bakin Momy. Shi kuwa bai san Momy ba kamar yadda na santa mace ce da ta kware wajen ƙirƙira da tsara sharri.
A cikin wannan duhu da zuciyata ke ciki, akwai fitila guda ɗaya da ke haskaka Shamsiyya, makociyarmu. Ita kadai ce take nuna min dan tausayawa. Watarana tana taimaka min da aikace-aikace, tana bani kwarin gwiwa. Ita ce kadai ta tabbatar min cewa har yanzu akwai wanda zuciyarsa ke da laushi a duniyar nan.
*****
Ina zaune yanzu haka cikin ɗaki, nayi tagumi kai na lulluɓe da zullumi. Gajiyata ta zarce ta jiki har cikin ƙashi na nake jin nauyi. Na gama tuka tuwo da rana, na gyara falo, na wanke kayan girki, amma har yanzu babu wani abu da ya sanya zuciyata farin ciki. Na yi iya ƙoƙarina, amma kamar ruwa ne nake shanya a dutse.
Ba komai nake nema ba ɗan nishadi kaɗan ne kawai. Ko fim ɗin Korea da na saba kallo, wanda ke saka ni dariya, ya ɗan mantar da ni da damuwa. Amma yanzu, ko ₦100 da zan biya na kalla bani da shi.
Rayuwata ta dame ni. Gidan da nake ciki kamar gidan da aka kulle albarkacin zuciya. Ina aiki kamar baiwa, amma kamar ina hasken rana a idon makaho. Na rasa wani da zan bude masa zuciyata na faɗa masa haƙiƙanin abin da ke ci min rai, abin da ke rarrafe a cikin dare yana hana ni barci.
Na tuna da Fatima. Da na saurare ta, da na rungumi salon da ta bi Na kula samari don ɗan kuɗi. Watakila da yanzu ina da ɗan abu da zan biya matsalata da shi. Amma ban iya haka ba. Na tsaya da mutunci.
Yanzu ma wani kaikayi ke damuna, wani irin zafi kamar ana cizon wuta ne a gabana. Amma bana da kuɗin shaver, ko man cream, balle in iya zuwa asibiti. Na gwada shiga ɗakin Momy jiya na zaci zan ɗauki ɗan abu, amma gashi ita ke kallona kamar baiwa da aka aje a gaba marar daraja, marar murya.
Na miƙe a hankali daga inda nake zaune, na ɗauki laptop dina, sannan na fice zuwa harabar gidanmu. Iska mai laushi na busawa fuskata, tana ɗan shafa gajiyata da salama. Idona ya sauka a kan Musa, mai aikin gidanmu, yana share ƙasa a ƙasan bishiyar mangwaro. Na nufe shi da fara’a mai launin ɗaci.
“Ina wuni Musa,” na ce masa da ƙanƙanin murya, kamar wadda ke boye wani sirri a zuciya. “Don Allah, idan zaka iya, ka taimaka ka turomin wasu fina-finan Korea masu kyau. Amma dan Allah, kada kowa ya sani. Ni da kai ne kawai.”
Musa ya tsaya, ya ɗago da murmushi mai sanyi, ya ce, “Haba Hajiya Ramlah, ba matsala kwata-kwata. Abokina ne mai turawa, ai ni ma fina-finai kawai nake karɓa, ba sai kin bada ko sisi ba.”
Na ji wata ƙara mai sanyi ta zuba a zuciyata. Na miƙa masa laptop ɗin da hannayena biyu, cikin ladabi da godiya.
Na murmusa, zuciyata ta ɗan lafa. “Nagode sosai,” na faɗa a nutse, sannan na juya na koma cikin gida, kamar wata baiwar da aka samu nata ƙaramin nishaɗin da zai dan shafe gajiyar zuciya.
A yau ba zan ji kunya ba, na faɗa wa kaina. Ko 10,000 ce, zan tambayi Momy. Komai za ta ce, ko yaya za ta yi, in har ba zan mutu ba, zan fuskance ta.
Na ɗaura ɗankwali da hanzari, Na hau saman bene kamar wadda zuciyarta ke harbawa da fatan samun ƙanƙanin jin ƙai.
Tun kafin na karasa palon, idanuwanta ta zuba min. Tana zaune kan kujera kamar sarauniyar da aka gaji da mulkinta, tana kallon tashar da babu sauti.
Lafiya? Me kike nema da rana tsaka zaki hau min sama haka?
Na tsugunna a gabanta kamar wadda ake shirin yanke wa hukunci.
“Momy…” Na daɗe kafin na iya ci gaba. Muryata na rawa kamar tana kokarin fita ba tare da izini ba. “Dan Allah, ko 10k ce kibani. Akwai kayan gyara da nake so nasiya. Wallahi gaba ɗaya jikina wari nake ji. Ga gashi...”
Sai na ji saukar wani abu mai zafi. Hannunta ya buge min baki kamar ana yanka tunani a idanuwa. Na lumshe ido da sauri, hawaye suka taru amma suka tsaya gefe da gefe.
Ubanki ya bani kudi nace? Bazan bayar ba! Ina mazan da kike bi? Je ki su baki mana! Ni bana son damuwa fa Ramlah. Kada kiga ina yi wa Bilkisu komai, ita cikakkiyar ‘yata ce. Ke kuwa? Ke ‘yar kishiya ce. Kishiya dai dai da aƙalla? Ki tashi ki farka, kin ji? Wani sai kin bi hanya irin ta Fatima sai kuɗi da ake nema cikin sharri!”
Tana magana, zuciyata na fashewa a ciki kamar madubi mai tsufa da aka jefa a ƙasa. Kowace kalma kamar tabarya ce aka zuba min a rai.
Tashi ki bani guri! Wata shegiya! Sai kiba kikeyi kin sha ne har kin manta me kika zo nema? Ko maganin ƙarin kiba kika kara siya?
Zan iya jure yunwa, zan iya jure gajiya. Amma wannan kalmomi? Su ne suka fi komai fasani.
Na daure fuska cikin kwanciyar hankali da hawaye ke bijiro min daga zuciya ba daga ido ba. Na ce
“Mama… A’a..” Na sauka da ƙasa da murya, na durƙusa na juya kamar wadda ke ficewa daga duniyar da ba ta ƙara yi mata amfani ba.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ASHIRIN DA HUDU
Arewabook @nanadiso10
Tsaye yake a gaban madubi mai fadi wanda aka shigo da shi daga Italiya. Madubin yana ɗaukar hotonsa Fuskarsa cike da kwarjini, idanuwansa masu haske da zurfin hankali na kallon kansa da nutsuwa.
A jikinsa rigar siliki ce ta musamman, farar fata mai laushi, alamar LV a gefe, da turaren oud daga Dubai da ke zubda ƙamshi a cikin iska.
Tsaye yake yana kallon kansa, sannan ya sauke numfashi a hankali. Ya ɗaura hannu a goshinsa, yana jin ciwon kan da ke damunsa tun jiya ya rage, amma nauyin da ke zuciyarsa bai sauka ba.
“Ya Allah, ka bani nutsuwa,” ya faɗa a hankali, yana mai rusunawa da yin istigfari.
Ya mike, ya ɗauki wayarsa daga mirrored table. Ya shiga lambobin wayarsa, ya kira Ayshatu. Sau ɗaya. Sau biyu. Har sau hudu. Shiru.
Ya dafe goshi. Wani irin bugun zuciya ya taso masa.
“Why aren’t you picking up, Ayshatu?”
Ya jingina da bango, yana kallon sararin samaniya ta cikin tagar gilashi. Hankalinsa yana juyawa. Ya fitar da numfashi mai nauyi, sannan ya kira diyarsa, Aminatu.
Tana ɗagawa cikin sauri da ladabi.
“Assalamu Alaikum, Daddy.”
“Wa alaikumus salam. Yaya gida? You and Abubakar, hope everyone is okay?”
“Alhamdulillah dady, we're all fine. Yaya kai, Dady? Your head?”
“Still heavy. I’ve been trying to reach your mother, but she hasn’t picked up.”
Aminatu ta yi shiru na sakanni kafin tace
“Wallahi Dady, rabona da ita kusan kwana goma. Tace min tana Paris. Ni ma nayi ƙoƙarin kiranta amma bata sake ɗauka ba.”
“Paris?” ya maimaita da mamaki.
“She didn’t say anything to me.” “Tace zata kirani daga baya. Amma har yanzu bata kira ba.”
As’ad ya jingina da kujera ya dafe kansa a hankali. Zuciyarsa cike da tambaya Ina Ayshatu ta tsaya?.
“It’s alright. I’ll try again. Send my regards to Abubakar.”
“I will Dady. Please don’t stress yourself too much.”
“Thank you, sweetheart. Take care.”
Ya kashe wayar, yana jin sanyi ya ratsa jikinsa.
Cikin daƙiƙu kaɗan bayan kammala tattaunawa da diyarsa, Ya danna bell din kofar. Bai ce komai ba PA ɗinsa ne, Mustapha, wanda ke aiki da shi fiye da shekara goma, yana da Amana da sirri sosai da shi.
“Come in,” As’ad ya furta cikin nutsuwa.
Mustapha ya buɗe ƙofar cikin ladabi, yana sanye da farin suit da takalma masu sheƙi. Ya shiga, yana ɗan sunkuyar da kai. “Sir, good morning. Are you available now? You requested to see me urgently.”
As’ad ya ɗaga kai daga littafin da ke gabansa, yana kallon Mustapha da nutsuwa. “Yes, Mustapha. Do I have any meetings today?”
Mustapha ya ɗauko small tablet daga hannunsa, ya duba calendar dashboard ɗin As’ad. “Yes sir. You have four scheduled meetings today one with the Turkish investor at 10AM, a Zoom board update at 11:30, Nigerian Royal Council engagement by 2PM, and a dinner strategy with the EU delegation at 6.”
As’ad ya gyara zama. “That’s a full plate. Alright, ganinan fitowa in few minutes. Make sure the team is ready, the car set, and my private suite at the downtown tower ready for the Turkish guy.”
“Yes sir. Everything is already in motion.”
As’ad ya miƙe tsaye daga kujerarsa ya nufi mirrored hallway wanda ke kaiwa dressing chamber dinsa. Tufafin da ke rataye a cikin ɗakin kayan shiryawa Armani, Tom Ford, da YSL.
Ya zabi baƙar suit mai launin toka a jikin collar, ya ɗaura cufflinks ɗinsa masu logo na family crest ɗin su. Yana gama shiryawa, ya danna intercom
“Mustapha, let’s go.”
“Yes sir,” aka amsa nan take.
Ya fito daga ɗakin cikin ƙamshi na musamman na Oud Wood, yana tafiya kamar sarkin zamani. Ko wanda bai san shi ba idan ya ganshi a haka, sai ya kalli cikakken namiji mai daraja da kamala. Bodyguards biyu suka buɗe masa ƙofa, suka rakashi har zuwa motar Maybach da ke jiransa.
Yana zama, PA ɗinsa da direba suka shiga sannan suka wuce cikin tsari.
*******
Taron ya cigaba da tafiya cikin tsari, kalmomin da ke fitowa daga bakin As’ad na ɗauke da hikima, bayanin kasuwanci, da jagoranci mai zurfi. A matsayin babban attajiri da shugaban kamfani mai haɗin guiwa da ƙasashe sama da ashirin, ya san yadda ake gudanar da taro da ƙwarewa kallon kowa yana kansa, maganarsa ana rubutawa.
Yayin da yake sauraron bayanin Oğuzhan kan yanda za a kafa data-driven smart energy grids, zuciyarsa na tafiya da kallon window da ke nuna masa hasken rana yana saukowa a kan ginin villa dinsa da ke can nesa. Duk da cewa yana gab da yanke shawarar dala biliyan, zuciyarsa na bugewa da tambayoyi “Ayshatu… me kike yi a Paris har yanzu? Kina lafiya? Me yasa ba kya kira? Kuma Haneefa, me yasa take ƙoƙarin shigowa bangarena?”
“Sir? Sir...?” Muryar Mr. Oğuzhan ta dawo da shi daga tafarkin zuciya.
“Yes, I’m here,” ya ce da kwarewa, yana ɗaga ido. “I like your pitch. I’ll have my legal and finance team review this thoroughly and we’ll schedule a signing week after next. Mustapha, make the arrangements.”
“Yes sir,” PA ɗinsa ya amsa da girmamawa, yana zazzage bayanai cikin iPad ɗinsa.
Daga nan, suka tsaya don dan hutu. As’ad ya ja numfashi, ya tashi zuwa wani keɓaɓɓen balcony. Wuri ne mai fuskantar babbar hanyar, ya na kallon motoci da gine-gine masu ɗaukaka.
Ya jingina da katanga, ya ciro wayarsa, ya sake danna lambar Ayshatu.
Tuut... tuuut... Still, no response.
“Subhanallah...” ya furta, yana lumshe ido, yana jin cewa akwai abu mai zurfi da ke gudana. A cikin zuciyarsa ya ɗaura niyya “I will find out what’s going on. I’ll go to Paris myself, but I’ll finish these business duties first.”
A lokaci guda, Mustapha ya ƙaraso.
“Sir,” ya ce da girmamawa, “Your next Zoom conference with the EU delegate is in 20 minutes.”
As’ad ya juyo da murmushi, ya gyara suit ɗinsa.
“Very well. Let’s make it quick and sharp.”
Amma a yayin da suke komawa ciki, ya buɗe Text, ya aika sako ga Haneefa
“We’ll talk soon. I’ve just been under pressure. I see your calls. Be patient.”
*****
Haneefa ta fito daga ɗakin wanka cikin farin doguwar riga mai laushi. Fuskarta na ɗauke da kwalliya, jikinta na ƙamshi da turare Masu dadi. Ta kalli kanta a madubi, ta ga yadda take cikin kyau sosai. Amma duk da wannan kyau, zuciyarta cike take da damuwa da bakin ciki.
Tun jiya mijinta As’ad bai shigo bangarenta ba. Bai kira ta ba. Bai aika mata da sako ba. Wannan abu ya ɗaga mata hankali.
Ta tafi bangarensa har sau uku, tana fatan ko zai fito ya ganta. Amma duk lokacin da ta je, masu gadin ƙofar suna gaya mata cewa ba za ta iya shiga ba.
“Hajiya kiyi hakuri, amma ba’a barin kowa ya shiga bangaren oga sai da izini. Wannan shine doka,” daya daga cikin masu tsaro ya ce mata cikin ladabi.
Wannan maganar ta ci mata rai. “To ni fa matar shi ce? Me yasa zan bukaci izini kafin in ga mijina?” ta tambaya cikin da damuwa.
Amma duk da haka, ba su bar ta ta shiga ba. Daga karshe sai dai ta juya da zuciya mai nauyi, ta koma bangarenta.
Tana shiga ɗaki, ta cire mayafinta ta wurgar, ta ɗauki wayarta. Ta kira Fulani Maryam.
“Mama,” ta fara da kuka, “tun jiya As’ad bai zo bangarena ba. Na najei har sau uku suka ce ba zan shiga ba. Wallahi bazan iya rabuwa da shi ba.”
Fulani Maryam ta ce , “Ke dai ki nutsu. Ba na gaya miki ba ki kula da magungunan da na ba ki? Ko dai baki bashi sosai ba?”
“Wallahi mama duk na bashi. Amma dai wulakanci ne kawai nake fuskanta.”
“Matsalar As’ad tuni zan maganinta. Idan kin tabbatar ya sha magungunan, to ki bar komai a hannuna. Ki nutsu kawai,” Fulany Maryam ta ce da kwarin gwiwa.
Haneefa ta ajiye wayarta, ta zauna kan gado. Duk da cewa ɗakin nata na cike da kayan alatu kujerun , labule masu ƙyau, ga kamshi mai daɗi amma babu farin ciki a zuciyarta. Dukiya ba ta kwantar mata da hankali ita tun asalinta shiyasa bata iya zaman auren.
Ta nufi bar counter din ɗakin, ta ɗauki kankana, habbatussauda, madara, kantu da zuma ta hada hadin da ke ƙara sha’awa. Tasha a hankali tana fatan zai ratsata
Gashi har yanzu tana cikin tsananin sha’awa da kishi. Tana tunanin As’ad. “Da ace yana nan kusa dani. Da ace zai riko hannuna... ya kalle ni a ido... ya ce min, ‘Haneefa na, I’m here.’”
Tana cikin wannan tunani, idonta ya rufe. Bacci ya dauketa.
Nana hadiza
09030569336
**************
*IDO A DUHU*
*NA*
*BILLY S FARI* 💎
Arewabook:-billysfari
Paid book N500 naira only
5044109936
Bilkisu Sani Kaura
Shaidar biya
07040402435
Page 1
Idanuwansa ya ɗago ya zuba akan Kyakkyawan matashin dake tsaye acikin paloun riƙe da wuƙa a hannunsa duk jini, fuskar nan tasa a haɗe babu alamun tsoro ko kuma shiga tashin hankali na riskarsa da akayi cikin wannan yanayi balle kuma nadama, a gefensa kuma wata budurwa ce duƙe tasa hannayenta ta toshe bakinta dasu tana kuka, kukan da gaba-daya kana kallon ta zaka fahimci yadda ya sauya mata kamanni ta hanyar sauya kalar fatar fuskarta izuwa ja, yayin da launin idanuwanta dake farare tas suka yi jajir suna cigaba da tsiyayar da ƙwalla. A gaban su kuma babbar macece ta rungume wani matashi ajikinta dake kwance cikin jini ko motsi bayayi tana kuka tana girgiza sa haɗe da sabbatun ya tashi. Ganin da tayi tabbas bazai tashi ba ya sa ta miƙewa cikin wani irin fushi da zafin rai ta nufo wajen saurayin dake tsaye riƙe da wuƙar da kana gani kasan da ita akayi amfani wajen illata wanda ke kwance cikin jinin babu lumfashi a jikinsa, tana zuwa ta ɗauke sa kyakkyawan mari har guda biyu saboda tabbacin da take dashi akan ko shakka babu shine ya yi wannan aika aikan, cikin zaro idanuwa da ƙaraji take cewa "Kai ɗan gidan uban waye? Me ye ya kawo ka cikin gidan nan? Waye ya aiko ka aikata masa haka? Me yarona ya yi maka ne?". Ta jero masa tambayoyin tana shaƙo wuyan rigar sa kafin ta fashe da wani irin kuka tana zubewa ƙasa, saurayin kuwa kasa amsa mata yayi sai ma ƙasa da ya yi da kansa don har lokacin babu alamun nadamar abinda ya faru ko tsoro a tattare dashi, banda zallar masifa da jin kai babu abinda ke cikin idanuwa da suka yi jajir tamkar an watsa barkono.
Kukan da matar keyi ya maido da mutumen cikin hayyacinsa yana faɗin. "Innalillahi wainna ilaihirrajiun". Kalmar daya iya faɗa kenan haɗe da ciro wayarsa, bugu ɗaya ya yiwa wata lamba aka ɗaga, cikin wata irin murya dake nuni da cike yake da damuwa yace. "Commissioner ina so ka turo mani da yaranka anan gidana, Please ranka shi daɗe". A ta ɗayan ɓangaren commissioner of Police ya amsa masa da, "Yanzun nan amma yallaɓai ina fatan dai lafiya ko?" "Ba lafiya ba.." nan ya kwashe duk abinda ke faruwa da suka isko ya sanar dashi yana jin idanuwansa na kokarin kawo ƙwalla yana ji duniyar nayi masa wani irin juyi, gaba-daya ya gama ruɗewar da bai san me zai yi ba banda ya kira hukuma.