Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 18
Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 18: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 18. Yau ba mu da islamiyya, haka kawai na…
3,373 words
Yau ba mu da islamiyya, haka kawai na tsinci kaina a zaune a farfajiyar gidanmu ina sauraron rediyon da Musa ya kunna. Shirin "Indaranka" nake sauraro, wanda yanzu ya zama tamkar abokina mai debe mini kewa, musamman da yanzu nake cikin rashin walwala saboda rashin kudi da rashin yadda zan samu Korean films da na saba kallo a computer dina. Har sau uku Musa yana turomin, amma yanzu naji kunya na sake zuwa na roƙe shi ya ƙara turawa.
Ina cikin wannan tunanin, sai ga Mumy ta fito daga cikin gida, cikin wani haɗaɗɗen lace mai launin shuɗi da fari wanda ya matuƙar yi mata kyau. Gaskiya, in banda ƙyashi, Mumy ba ƙaramar kyakkyawa ba ce, musamman idan ta shiga irin waɗannan kayan da suke fidda ainihin kyau da kamalarta. Ta iso gabana tana kallona da ɗan murmushi kadan.
"Ke, Ramlah, ni zan fita zuwa bikin gidan Alhaji Wakili. Ki tabbata kin ƙara gyara gidan nan sosai kafin na dawo. Sai wajen ƙarfe tara na dare zan dawo. Kuma ki bar girkin yau, sauran shinkafar da ke tukunya ku ci ita da masu gadi."
Cikin girmamawa na amsa mata, "To, Allah ya kiyaye hanya Mumy. Sai kin dawo lafiya. Yaya Billy ma Allah ya kiyaye."
Yaya Billy tana kallona ta watsamin wata muguwar harara, ko amsa sallamar ba ta yi ba. Ta ɗauke kai kamar ban wanzu ba, suka shiga mota, suka ja suka fice.
Wani mugun daɗi ne ya ziyarci zuciyata, na shiga cikin gida da sauri kamar wanda aka ce masa an raba kuɗi. Na tafi kai tsaye saman gidan, ɗakin Mumy na nufa, zuciyata tana bugawa saboda tashin hankali da fargaba.
Na buɗe ɗakin a hankali, turaren alfarma da ƙamshi ya karɓe ni nan take. Na nufi inda ta aje turarukanta, na ɗauki kwalabe na tsiyaya cikin wata ƙaramin leda, zuciyata na bugawa da sauri saboda tsoron a kama ni. Na duba cikin ɗakin ko zan samu kuɗi, ban samu ko sisi ba. Sai da na juya zan fita, sai idanuna suka kai ga wardrobe ɗinta wanda yake buɗe kaɗan.
Cikin hankali na matsa kusa da wardrobe ɗin, zuciyata na cigaba da tsananta bugawa. Sai kawai na hango wasu sababbin kuɗi 'yan dubu-dubu masu yawa sosai. Take wani sanyi ya ratsa jikina, naji wani irin farin ciki mai gauraye da tsoro yana ziyartar zuciyata.
Hannu na rawa, jikina na ɗan karkarwa, na tsamo guda goma sha biyar. Wallahi idan ka ga yawan kuɗin nan zai fi dubu ɗari biyu! Na tabbata babu yadda za ayi Mumy ta lura. Na lulluɓa kuɗin cikin ledar da na ɗauko na saka turarukan, sannan na zuba ɗan maclean guda biyu ciki don na ɓoye sirrina.
Cikin sassarfa da taka tsan-tsan na fito daga ɗakin, na kulle ƙofa yadda babu wanda zai gane cewa wani ya shiga. Na sauka ƙasa da ƙafafu masu nauyi da zuciya mai nauyi amma cike da farin ciki na shiga ɗakina. Nan na adana kuɗin ƙarƙashin kayan jikina, na ɗan yi ajiyar zuciya sannan na kwanta a kan gado ina kallon saman rufi, zuciyata tana faman tunani.
Wallahi babu wanda zai fahimci irin radadin da zuciyata take ji saboda halin da nake ciki, sai wanda ya gani da idanunsa. Na sani wannan abu ne mara kyau, amma kuma ban da wata mafita da ta wuce wannan a yanzu.
Ina tsaye a harabar gidanmu cikin ɗan nisa daga ƙofar gida, sai ga Musa ya nufo ni cikin sauri. Ya tsaya a gabana yana huci kamar wanda ya zo da saƙo mai matuƙar muhimmanci.
“Ramlah…,” ya kira sunana da wata murya mai ɗauke da damuwa, “ga wata baiwar Allah a waje tana nemanki. Wai tana cewa danAllah ki fito.”
Na ɗan runtsa ido, zuciyata ta buga. “Wacece?” na tambaye shi, ina ƙoƙarin fahimtar me ke faruwa.
Musa ya ɗan sunkuyar da kansa, sannan yace, “Tace wai tana kama da abbanki...”
Baki na na ɗan buɗe, amma ban ce komai ba. Na ɗauki hijjab dina na zura a hankali, zuciyata cike da tambayoyi da shakku. Ina fita daga ƙofar gidan, idona ya sauka kan wata mota mai launin toka da ta ke a bakin titi. Na leƙa cikin motar a hankali…
Sai ga Umman Khalil...
Zaune take, idonta jajir kamar wacce ta shafe sa'o’i tana kuka. Fuskar ta kumbura, ta cika da damuwa. Na matso da takaici da fargaba, zuciyata na bugawa da karfi.
“Umma… lafiya?” na tambaya cikin murya mai sanyi, amma da karfin tashin hankali.
Ta buɗe kofa tana cewa, “Ramlah danAllah ki shigo. Mu tafi wajen Khalil...”
Zuciyata ta ɗaukaka kamar za ta tsinke. Kafafuna suka yi sanyi. Naji kamar ana janyo zuciyata da igiyar baƙin labari. Babu shiri na shige cikin motar. Driver ya ja motar, numfashina na rawa, zuciyata na doki da fargaba me ya faru da Khalil?
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ASHIRIN DA TARA
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
A fadar Mai Martaba, hasken fitilun lantarki sun kawata falon zauren masarauta, suna sheƙi bisa ƙayatattun shimfiɗun da aka tanada musamman ga manyan masu fada-a-ji. Masu hidimar fada suna tsaye cikin girmamawa, yayin da manyan matan gidan sarauta suka haɗu bisa ga alfarma da ƙasaita.
Fulani Maryam (Mahaifiya ga haneefah) uwargidan Mai Martaba, tana zaune cikin shiga ta musamman mai bayyana matsayinta a gidan sarauta, tana lumshe idanu cikin wata irin annashuwa da farin ciki, Hajja ma da sauran matan Nasa suna zaune cikin shiga ta alfarma.
Cikin wannan yanayi ne Haneefah ta shigo zauren, kuka da hawayenta suka mamaye hankalin kowa da ke cikin zauren. Ta zo da sanyin jiki, tana tafiya cikin rawar kafa har zuwa gaban Mai Martaba Sarkin . A hankali ta zube bisa guiwowinta, ta fashe da kuka mai ban tausayi.
Gaba ɗaya idanun fada suka dawo kanta. Zuciyar Mai Martaba ta tsananta bugawa da zafin fushi. Muryarsa ta fito cikin ƙasaita da izzar sarauta.
"Menene ya faru, Haneefah? Wane abu ne ya sameki har zaki shigo mini fada da kuka irin haka?"
Cikin rawar murya da shesshekar kuka, Haneefah ta ce,
"Allah yakara maka lafiya… As’ad... ba shi da lafiya! Ya kasa cika haqqinsa na aure. Gaba ɗaya ya zame min wani abu daban. Ni wallahi na gaji da zama da wanda ba ya iya sauke haqqin aurena. Ya sake ni na dawo gida. Wallahi bazan koma masa ba."
Muryarta ta ƙare cikin kuka mai cike da tausayi, tana ɓoye fuskarta cikin tafukan hannuwanta.
Wannan magana ta girgiza zauren. Duk wanda ke cikin fadar ya shiga al'ajabi da razana.
Cikin fushi da tashin hankali Mai Martaba ya ɗaga murya yace da babban hadiminsa,
"Wambai! Ka aika wa As'ad. Ina son ganinsa a gabana da sassafe ya bayyana!"
Wambai ya amsa cikin ladabi,
"Ranka ya daɗe! an gama."
Fulani Maryam, zuciyarta na rawa da farin ciki, amma tana kokarin ɓoye murmushinta domin kar ya bayyana fili. A cikin zuciyarta tana cewa,
"Allah ya kawo mini ƙarshen wannan yaron aiki yaci."
Tana ɗan ƙarewa Hajja Sa'adatu, Matar Mai Martaba kuma mahaifiyar As’ad, kallon gefe. Tabbas wannan abu ya girgiza zuciyar Hajja, domin tuni hawaye sun taru a idanunta. Ta ɗauko mayafinta ta share kwallarta da sanyi, muryarta na raɗaɗi cikin zuciyarta tana cewa,
"Allah ka jiƙan zuciyar ɗana. Ya ubangiji ka kawo masa sauƙi."
Ƴan uwa da sauran matan Mai Martaba suna gefe suna raɗa-ɗi tsakanin su, wasu da al’ajabin faruwar lamarin, wasu kuma cike da rashin jin daɗin wannan abu da ke neman ɗauke martabar gidan masarautar.
Mai Martaba ya juya ya dubi Haneefah cikin yanayi na tausayi da izza, yace,
"Ki kwantar da hankalinki, Haneefah. Duk wanda ya ɓata miki rai, babu shakka zai gane kurensa. Fadana ba wurin wulakanta jinina ba ne."
Haneefah ta ɗago kanta cikin shaukin kuka, tana duban sarki cikin soyayya da godiya, amma zuciyarta ta riga ta gama yanke hukunci. Auren ta da As’ad ya gama zama tarihi a zuciyarta.
Cikin wannan yanayi ne dukkan wanda ke cikin fadar suka ji sanyin fargabar abinda zai biyo baya idan gari ya waye.
**********
Yau dai ranar As'ad ce ta kasance mai cike da ƙalubale da aiki tun daga safe har zuwa lokacin da rana ta yi zawali.
Fitattun fitilun zinariya na office ɗinsa ne suka haska ko'ina, suna ƙara bayyana ɗaukakar dukiyar da Allah ya mallaka masa. Kujerarsa ta fata mai launi irin fari da duhun ruwan kasa tana zagaye da kyawawan teburori masu ɗauke da litattafai da takardu masu muhimmanci.
A zaune yake a kujerar mulkinsa, cikin wata irin yanayi na tsananin damuwa da tunanin da yake ƙoƙarin samun mafita. Kwana biyu kenan yake fama da wani irin azababben ciwon kai wanda ya hana shi sukuni sosai. Amma babu abinda ke damunsa fiye da yadda zuciyarsa ta sauya gaba ɗaya tun bayan dawowar Ayshatu.
Ya rasa dalilin da yasa soyayyarsa ga Haneefah ta fara mutuwa sannu a hankali. Yana zaune zai yi tunani, zuciyarsa ta fara tambayarsa
"As'ad wai me yasa har ka aure ta? Me kake tunani lokacin da ka amince da wannan yarinyar da yanzu ta zame maka ƙalubale a zuciyarka?"
Sai kuma wani sashe na zuciyarsa ya raya masa wani abu daban.
"Amma fa, Haneefah ta iya sarrafa namiji sosai. Ba kamar Ayshatu ba, wacce aikinta kawai shi ne kwanciya a yi mata romancing. Haneefah mace ce cikakkiya mai zafin nama, mai iya sarrafa namiji ta kowanne ɓangare."
Wannan tunanin na Haneefah ya sa tsigar jikinsa miƙewa cikin wani yanayi mai ƙarfi. Amma sai wani mugun raɗaɗi ya sake tunasar dashi matsalarsa ta rashin lafiyar da gabansa ke fama da shi. Nan take yanayin jikinsa ya sauya, zuciyarsa ta ɗau zafi sosai.
"Ya zama dole in nemi likita cikin satin nan har ƙasar Turkey. Dole na duba lafiyar nan," ya faɗa da zuciya cike da ƙudiri.
Wayarsa ta shiga ƙara cikin ladabi da nutsuwa. Ya ɗaga wayar yana faɗin, "Assalamu alaikum."
Cikin girmamawa, hadimi daga fadar masarauta ya sanar masa cewa, "Mai Martaba yana bukatar ganinka da sassafe gobe cikin gaggawa."
"To, na ji. Za a same ni," ya ce cikin sanyin murya yana sauke numfashi.
Cikin zuciyarsa sai ya raya, "Kenan Haneefah ta kai ƙarar nan zuwa fada? Ashe ta gama tsinke igiyar zamanmu kenan?"
Nan take ya kira P.A ɗinsa yace masa, "Ka shirya tafiya nan da ƙarfe takwas na dare. Ina so komai ya zama shirye."
Da isa gidansa, As'ad bai tsaya ko'ina ba sai kai tsaye zuwa bangaren Ayshatu, wanda aka kawata da kayan ado na zamani, dukiyarsa ta bayyana ta ko'ina cikin ɗakin. Ayshatu tana zaune kan kujerar alfarma, tana waya cikin yanayin ƙasaita, kafa ɗaya kan ɗaya tana wasa da igiyoyin gyalen jikinta.
Ganin As'ad ya shigo yasa ta yanke wayar cikin sauri, ta taso cikin ɗan kissa da ladabi, ta rungume shi cikin wani ɗan sanyi da sassanyar murya tana cewa, "Sannu da zuwa, Habibie. Na jima ina jiran dawowarka."
As'ad ya yi murmushi kaɗan yana dubanta da tausasawa, "Ayshatu, yaya gidan yau?"
"Lafiya ƙalau, Alhamdulillah." ta amsa masa cikin wata irin ƙayatacciyar murya mai cike da jan hankali.
Ya ɗan lumshe ido cikin ɗan gajiya yace mata, "Ina da kiran gaggawa daga fada. Mai Martaba yana nema na yanzu. Ko za ki iya shirya wa mu tafi tare?"
Ayshatu ta ɗan yi murmushi cikin salo da jan hankali tace, "A'a Habibie, yau kam jikina ba ƙwari sosai. Har yanzu ban huta ba. Amma ka je dai, ka gaida min Mai Martaba sosai, Allah ya kiyaye mini kai."
Ya ɗan murmusa ya ɗaga kai, ya fita cikin sanyi da girmamawa.
Amma yana fita, Ayshatu ta koma zaune cikin wata irin muguwar dariya ta mugunta da ƙissa. Dukiyar gidan da ƙayatattun kayan ado da fitilun zinariya suka haska fuskarta mai cike da murna. Tuni direbanta ya sanar da ita cewa Haneefah ta bar gidan, kuma wannan abu ya zame mata babban farin ciki mara misaltuwa.
"Ai wallahi babu kai babu wata diya mace a duniyar nan, As'ad. Yanzu na gama cin nasarar mallake zuciyarka gaba ɗaya." Ta ce cikin yanayin kissa da cikar buri, zuciyarta cike da alfahari da gamsuwa.
*****
Hajja zaune take a saman wata babbar kujera ta zinariya mai shimfidar tattausan bargon alharini. Fuskar ta cikin damuwa sosai, idanunta sun yi jajir saboda zafin hawaye da ke neman cinyeta. Kanta ya sunkuye tana ta share kwallar da take fita, zuciyarta na cigaba da raɗaɗi kamar ana watsa mata garwashin wuta.
Fiddausi dake zaune kusa da ita, cikin tsananin bacin rai ta sake kallon mahaifiyar tata ta ce cikin yanayi mai kaifi,
"Hajja wai ba kuka za ki yi masa ba? Kin manta irin abinda kika yi mini lokacin da matsalar mijina ta taso? Wannan abu da kika yi maraba da shi ne, kika goyi bayana . To yanzu me ya canza da kika shiga damuwa haka?"
Hajja ta ɗago da idanuwan da suka yi jajir saboda kuka, tana kallon Fiddausi da wani irin yanayi na rauni da takaici. Baki na rawa tace,
"Ba za ki gane ba Fiddausi. Wallahi ba za ki fahimci irin tozarci da wannan yarinyar ta jawo mana ba. Ba za ki iya fahimtar yadda zuciyata ke raɗaɗi yanzu ba. Wannan magana ta rage wa As'ad daraja, girmansa ya sauka, mutuncinsa ya karye! Kuma wallahi zuciyata bata yarda cewa Haneefah gaskiya take fada ba. Wannan makircin Fulani Maryam ne! Ina sane da yadda take!"
Fiddausi ta girgiza kai cikin takaici tana cewa,
"To ai ni na san wannan. Wallahi ni ba zan yi kaffara ba! Kin san wannan matar nan tasa mai suna Ayshatu? Wallahi malamai take bi tana hana masa zama da matansa. Wannan matsalar ba daga As'ad ba ce, daga wannan matar ce! Ku dai kalle ta fa da kyau, baku ganin yanayinta?"
Hajja ta ɗan dago hannu tana jan numfashi cikin rawar murya tace,
"Ke Fiddausi ki yi shiru mana! Ai matar mutum kabarinsa ce. Duk yadda kika ga mutum da matarsa, to, Allah ya tsara hakan. Idan akwai matsala to daga Ubangiji ce. Amma wallahi matan As'ad ba masu zama bane, na riga na san haka tun farkon faruwar wannan lamarin."
Fiddausi ta ɗan yi shiru, sai kuma ta ce cikin yanayin sanyin murya da tausayi,
"To Hajja na yi shiru, amma gaskiya ki daina kuka, ki koma ga addu'a domin ita kadai ce mafita. Kukan ba zai magance komai ba. Yanzu lokaci ne na addu'a da neman taimakon Ubangiji."
Hajja ta sake gyara mayafinta, zuciyarta na cike da damuwa, hawaye kuma na cigaba da bin kuncinta a hankali cikin zafin zuciya.
***
A wannan lokacin kuma, a wani ɓangaren daban na garin, As'ad yana cikin wani yanayi na tsananin kunci da damuwa. Duk da cewa ciwon kai yana yi masa azaba, amma zuciyarsa ce ta fi jin raɗaɗi saboda wannan mummunar magana da Haneefah ta kai fada.
Zuciyarsa ta ɗaure tamkar an yi masa ɗaure da igiyar azaba, yana ganin yadda wannan abu zai yadu cikin gidan sarauta, za a zagaya da zancen ko'ina. Wannan ba ƙaramin tozarci bane ga mutum mai daraja irin tasa. Duk dukiya da izzar da yake ji, sai ya kasa jure wannan tozarci da aka masa.
Ya zauna a gefen gadon alfarma mai shimfida ta musamman, idanunsa suka cika da hawayen zafi. Ya lumshe ido yana ambaton sunan Allah, zuciyarsa ta cika da raɗaɗin takaici,
"Ya Allah... Wannan tozarci ne fa da aka yi mini haka? Ta yaya zan iya kallon fuskar Hajja bayan wannan abun kunyar da aka yi mini? Ta yaya zan sake tsayawa cikin jama'a?"
Da wannan tunanin yaji tsigar jikinsa na tashi saboda tsananin ɓacin rai. A gaggauce ya mike ya shiga cikin bandaki wanda aka kawata shi da fitilu masu ƙyalli da madubai Ya yi wanka cikin hanzari, ya shirya cikin wasu kayan alfarma masu kyau da ɗaukar ido.
Da ya fito daga ɗakin nasa kai tsaye motarsa Mercedes Benz ta alfarma ce mai launin baƙi ta fisgi hanya zuwa filin jirgin saman da jirginsa ke jira domin ɗaukarsa. A cikin yanayi na damuwa da tashin hankali suka isa garin da za su sauka.
Ko da suka isa babban otel ɗin da aka kama masa, mai ɗauke da ɗakuna masu ƙyalli da alfarma, duk wannan bai hana zuciyarsa raɗaɗi ba. Duk gajiyar da ta yi masa yawa a jikinsa, amma bacci ya ƙi zuwa gare shi. Ya juya gefe gefe yana jin zuciyarsa na tafarfasa cikin damuwa.
Ya sake ɗago idanunsa da suka yi jajir da zafin damuwa ya kalli halittar gabansa wadda take kwance ba tare da wani motsi ba. Ya ji wani azababben raɗaɗi yana cizon zuciyarsa, cikin wata irin damuwa da takaici ya lumshe idanunsa yana furta,
"Ya Allah, ka kawo mini mafita daga wannan jarrabawar da ka jarrabce ni da ita. Wannan abu ya fi ƙarfin zuciyata da tunanina."
Sai dai ko yaushe ya rufe idonsa wannan mummunar magana ce take cigaba da yawo cikin zuciyarsa da tunaninsa, tana ƙara masa raɗaɗin da ya gagara zama cikin ransa.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA TALATIN
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Da ƙyar As'ad ya samu bacci ya ɗauke shi, amma kafin gari ya waye sai ya farka, idonsa na cigaba da raɗaɗin da damuwa ta haifar masa. Da asubah ya tashi ya yi sallah cikin wata irin zuciya mai nauyi, daga nan ya zauna yana ambaton Ubangiji da addu'ar neman mafita.
Bayan ya gama addu'o'insa, sai ya ɗauki wayarsa cikin sanyin jiki ya kira Hajja. Duk da cewa zuciyarsa tana cike da kunya da nauyin wannan magana, bai iya hana kansa neman ta ba, saboda yasan tana cikin damuwa sosai hajja uwa ce wacce take mutukar son yaranta kasancewarta ita ba jinin sarauta ba Allah yayi ne dai ta auri sarkin.
Kusan sau uku wayar tana ƙara amma babu amsa, sai daga baya Hajja ta ɗaga murya a sanyaye cikin tsananin raunin zuciya tace,
"Assalamu Alaikum, As'ad."
Sai da muryarsa ta ɗan yi rawa kafin yace,
"Wa'alaikumus salam Hajja. Ina kwana? Ina fata lafiya lau."
Hajja tayi ajiyar zuciya sosai, ta share kwallar da ta fara zubo mata tace cikin nutsuwa,
"As'ad, ba lafiya ba ce ka sani. Wannan abu da ya faru yana neman girgiza mana mutunci da martaba. Wallahi baƙin ciki na ya fi ƙarfin abinda zan iya bayyana maka."
As'ad ya lumshe ido cikin rauni yana jin zuciyarsa ta ƙara damuwa.
"Ki yi hakuri Hajja. Allah ya sani ba da sanina bane wannan abu ya faru, kuma wallahi Na gwada magunguna kala kala amma munkasa ganin matsalar a likitance ance kalou nake amma zanfita asatin nan naga wani babban likitan ina cikin wani irin hali da ba zan iya bayyana miki ba."
Hajja ta ɗan yi shiru kafin ta ce da shi cikin hikima da nutsuwa,
"As'ad, ka san kai ɗan gidan sarauta ne. Kuma haka Ubangiji yake jarrabar bayinsa na ƙwarai. Ka daure zuciyarka, ka karbi ƙaddara, amma ka yi ƙoƙari ka nemo hanyar magance matsalarka cikin sirri da hikima. Kuma kar ka manta addu'a ce mafita ga komai."
Cikin jin daɗin wannan magana ya gyada kai kamar tana ganinsa, yace,
"Insha Allah Hajja, zan yi ƙoƙari. Na gode da wannan kalmar karfin guiwa."
Ta sake cewa da shi cikin kulawa,
"Ina maka addu'a dare da rana, Allah ya fito maka da gaskiya kuma ya ɗaukaka maka darajarka. Kada ka bari wannan abu ya karya maka zuciya ko kuma martabarka."
Cikin raɗaɗin zuciya yace,
"Na gode Hajja. Allah ya saka da alheri."
Ya kashe wayar zuciyarsa ta ɗan yi sassauci, amma kuma nauyin damuwa bai sauka ba.
*****
Dagarin Allah yawaye, As’ad ya sakko kasan hotel din inda motar alfarma ta fada ta zo ta ɗauke shi kai tsaye zuwa fadar mai martaba. Zuciyarsa tana cigaba da buguwa cikin damuwa da fargaba, saboda ba shi da tabbacin yadda mai martaba zai karɓe shi.
Lokacin da aka sanar da isowarsa, Wambai ya shigo da sauri cikin ɗakin mai martaba ya sanar da zuwansa. Mai Martaba ya ɗaga hannu cikin alfarma ya ce,
"A shigo da shi."