Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 19
Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 19: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 19. A hankali As’ad ya shigo cikin fadar,…
3,326 words
A hankali As’ad ya shigo cikin fadar, inda ya samu mai martaba zaune cikin matsayinsa na sarki, sauran manyan fadawa da sarakuna masu martaba suna zaune cikin girmamawa. Ya durƙusa gaban mai martaba cikin ladabi yana cewa,
"Ranka ya daɗe, barka da safiya."
Mai Martaba ya ɗan kalle shi da ido mai cike da iko da izza, sannan ya ce,
"As’ad, kana sane da abin da ya kawo ka nan yau. Wannan magana da ta fito daga bakin matarka, ta girgiza martabar wannan fada kuma ta girgiza martabarka kai kanka."
Cikin sanyin murya, As’ad yace,
"Ranka ya daɗe, wallahi wannan abu ya fi ƙarfin tunanina.” Yafada yana jin wata matsananciyar kunya da kuma tozarta.
Mai Martaba ya ɗan daure fuska yace,
"Ka san dai irin gidan da ka fito, kuma ka san darajar da ke gare ka. Ban yi tsammanin zan taba jin irin wannan magana a cikin dangina ba. Amma saboda na san kai mutum ne mai hankali da nutsuwa, zan ba ka damar ka binciki matsalarka cikin sirri, kafin wannan magana ta fita daga ikonmu gaba daya."
As’ad ya yi numfashi cikin jin sauƙi, yace cikin ladabi,
"Na gode ranka ya daɗe.”
Bayan anyi sallar azahar Mai Martaba Sarkin zaune yake a saman kujerar sa, yana sauraron karar Haneefah da As’ad cikin natsuwa da izza, a gefe kuma manyan fadawa da dattawan gidan sarauta na kallon shari’ar da zuciya ɗaya.
Haneefah ta shiga zauren cikin tsantsar kamala da nutsuwa. Shigar alfarma ta mata ce a jikinta, fuskarta cike da tsantsar ladabi.
Da ta durƙusa cikin ladabi, ta ce cikin muryar da ta cika zauren
“Mai Martaba, ranka ya daɗe. Ni Haneefah, bana iya ci gaba da zaman aure da As’ad.”
Wani ƙaramin surutu ya fara tashi daga gefe, amma Mai Martaba ya ɗaga hannu alamar shiru.
“Me yasa, Haneefah?” ya tambaya cikin tsantsar natsuwa da hikima.
Ta sadda kanta ƙasa, ta ce
“Auren da ba ya cika min buƙatata a matsayin mace bai da daraja a wurina. Ina girmama As’ad, amma gaskiya itace zan faɗa gabansa ba ya aiki. Kuma ni ina buƙatar zaman aure na gaskiya.”
Zaure ya dauki shiru.
As’ad ya durƙusa, bai ce komai ba. Kamar dutse, ya makale a inda yake. Kamar izzar da ke jikinsa ta narke gaba ɗaya.
Mai Martaba ya dafe sandar zinariya, ya ɗan jinjina kai cikin takaici.
“Zancen da ya fito daga bakin mace cikin gaskiya, ba a rufa shi da ƙarya. Idan har haka lamarin yake, kuma ba wata mafita, to…”
Ya juya ya kalli As’ad,
"Ka saketa cikin mutunci. Kuma na baka izinin a ɗaura maka aure da mace mai nutsuwa da hikima wadda zata kula da kai da darajar gidan sarauta."
As’ad ya kasa ɗaga kai. Cikin sanyi da radadi, ya furta:
"Na saketa."
*****
Cikin sanyin dare mai cike da sanyi da hasken farin wata, motar As’ad ta fice daga farfajiyar fadar sarki cikin wata irin hanzari. Duk da ƙanƙanin wannan tafiyar, ya ji kamar ya shafe shekaru masu yawa yana barin wurin. Ba haka ya so ba, ba haka ya yi tunani ba, amma shi fa mutum ne, ba shi da iko akan ƙaddarar Ubangiji.
Gaba ɗaya fuskarsa ta sauya daga As’ad ɗan gidan sarauta zuwa As’ad wanda aka ɗora masa tozarci mai zafin gaske. Kamar wanda aka ɗaure wa igiyar kunya da takaici, zuciyarsa tana azabtar da shi, tana ƙara masa raɗaɗin jin cewa ya rasa abin da ya fi kowane abu daraja ga namiji girman mutunci.
Direbansa ya kai kallonsa a hankali cikin madubin mota, sai dai kuma bai iya tambayar komai ba, domin ganin yadda zuciyar Yarima As’ad ta matse cikin mayuwancin hali.
Lokacin da suka iso hotel , ko tsaya gaisawa da masu hidima bai yi ba kai tsaye ɗakinsa ya nufa, yana jin kansa kamar an ɗaure masa nauyin da bai taɓa jin makamancinsa ba. Bai cire tufafinsa ba, bai yi wanka ba, ya zauna bakin gadonsa cikin tashin hankali, idanunsa suka cika taf da hawaye masu dumi.
“Ya Allah, wannan wane irin abu ne ya same ni haka?” ya furta cikin sanyin murya mai cike da raɗaɗin zuciya. “Ni As’ad, an kira ni mara kuzari, rago, wanda mace ba ta bukata?”
Ya lumshe idanunsa, zuciyarsa ta yi masa zafi sosai har yake jin kamar tana ƙuna. Tunawa da yadda Haneefah ta zubar masa da mutunci a gaban Mai Martaba da manyan fada ya ƙara cizon zuciyarsa. Ya rasa yadda zai iya haɗa ido da kowa a cikin gidan sarautar nan, musamman mahaifiyarsa Hajja Sa’adatu.
“Babu wata uwa da za ta so jin cewa an kira ɗanta da marar amfani, wanda ba shi da wani ƙarfi ko kuzari,” ya sake faɗa wa kansa cikin tashin hankali, yana jin numfashinsa na fita da ƙyar saboda ƙuncin zuciya.
Gaba ɗaya ya kasa kwanciya, bacci ya ƙaurace masa, kuma duk lokacin da ya lumshe ido, sai maganganun Haneefah suke dawo masa suna zagaye masa cikin kai kamar faifan rediyo. Ba zai iya jure wannan tozarci ba, ba zai iya zama ya zuba ido ba. Sai kawai ya ɗaga waya cikin hanzari, ya kira PA ɗinsa yana umarnin cewa
“Ka shirya komawa gida, bana son ko da kwana ɗaya ya riske ni a wannan gari. “
PA ɗin nasa ya yi ƙoƙarin yi masa magana, amma muryar As’ad ta fito da tsananin damuwa da ƙarfin zuciya
“Ban buƙatar tambaya, kawai ka tabbatar jirgin ya shirya kafin gari ya waye.”
A cikin wani ɗan lokaci kaɗan, komai ya shiryu domin tafiyar Yarima As’ad. Da sassafe, jirgin As’ad ya bar filin jirgi yana mai ɗauke da zuciya mai cike da damuwa da nauyin kunya.
Yana zaune cikin jirgin, idanunsa sun yi jajir da rashin bacci, zuciyarsa ta ƙara cika da raɗaɗin da ya hana shi nutsuwa.
Hawayen da suka taru cikin idanunsa suka fara gangarowa kan fuskarsa a hankali. Bai yi tunanin ranar da zai shiga irin wannan halin ba. Sai dai babu yadda zai yi, domin haka Ubangiji ya tsara masa ƙaddararsa.
******
A wannan lokacin kuma, gidan sarautar ya zama tamkar an kunna wutar gulma wacce ke bazuwa da hanzari a dukkan lungu da saƙo na fada. Ba wani abin da ake magana sai tozarci da abinda ya sami Yarima As’ad.
Wasu daga cikin fadawa sun taru suna hirar ƙasa-ƙasa da ƙanana maganganu masu cike da izgilanci duba dashi As’ad baya shiga harkar kowa baya magana da kowa komai nashi daban da yaran sarki shiyasa dayawa aka tsanesa duba kuma da irin dukiyar da Allah yabashi fiye da kowa ciƙinsu.
“Wai ku ji As’ad Ashe wannan girman kan nasa duk na banza ne kawai! Mutum kamar shi ace wai bai iya komai ba wajen mace?” wani daga cikinsu ya ce cikin dariyar ƙasƙanci.
Wata kuma ta ɗauki zancen tana cigaba da faɗin
“Wannan magana ta wuce tunanina. Ai wallahi sai yanzu na gane cewa duk wannan izzar da yake yi mana a fada, babu komai a ciki sai rawar kai kawai. Ashe gabansa ma bai iya tashi ba?”
Wata mai hidima tana zaune tana tsintar wake ta ce cikin sigar zargi
“Ai ina ganin laifin matan nan nasa ne, wato Haneefah. Duk yadda mutum yake ai kamata yayi ta rufe masa sirri. Wannan fa ba karamar magana ba ce, sai ga shi har gidan sarki ta kai shi!”
Wata kuma mai hikima ta jinjina kai tana cewa cikin sigar nasiha
“Ai gaskiya ba abin dariya ba ne. Wannan magana ta shafi martabar gidan sarautar gaba ɗaya. Amma yanzu an riga an yi, kuma an ji da kunne, an gani da ido. Yarima As’ad dai ya gama shiga tasku a idon duniya.”
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA TALATIN DA DAYA
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Fulani Maryam zaune take cikin ɗakinta mai kyau, tana ta murmushi kamar wadda aka ba labarin da take jira. Ta yi shiru, tana murza tasbaha, amma zuciyarta cike take da farin ciki. Duk wanda ya kalleta, sai ya san tana jin daɗi “Alhamdulillah. Yau burina yacika As’ad ya ɗanɗana abinda na daɗe ina jira.” takarasa faɗa tana kyalkyalewa da dariya. Ta kwanta cikin kujera mai laushi, ta lumshe idonta tana faɗin “Mutumin da ya raina ni, wanda ya wulakanta diyata, gashi yanzu duniya na masa dariya. Lokacin da haneefah tafara nunawa tana kaunarsa yace Allah yakiyaye ya haɗa zuri'a da maryamu uwarsa kuma ta mulkeni yanzu kuma da karfin iko na Nasa ya aureta nakuma yi Amfani da'ita sunansa yaɓaci ɓaci na har abada tabbas wannan iitace nasara. Kuma wace ta karya shi? Haneefah Diyata. Ashe mace na iya fasa gini da magana guda!”
Ta yi dariya mai ɗan ƙara, “Duk kuɗinsa, duk mulkinsa, ba su iya kare shi daga mace ba! Yanzu As’ad ya zama abin dariya!” Sai ta juya ta duba hasken fitila a ɗakin, ta ce “Na fi jin daɗi ne saboda mahaifiyarsa Hajja tana cikin damuwa. Ai jin daɗin nasara shi ne lokacin da wanda ya ƙyashi ke kuka, ke kuma kina dariya.”
********
Tunda Sarauniya Amina matar sarki ta farko ta shigo zauren fadarta, dariya kawai take ta yi, irin wacce ke bayyana ƙosasshiyar zuciya da shirin badala. Ta kalli baiwarta da idon umarni “Ki bamu guri.”
Baiwar ta ja da baya cikin ladabi, ita kuwa Sarauniya ta zauna bisa kujera mai madaurin sarauta, ta ɗauki wayarta ta kira Ayshatu wacce take ɗaukart kamar ’ya’yanta dan itace sanadi har tasamu ta auri As'ad ita tashige mata gaba tana tunanin ta wannan hanyar ce zata mulkeshi sai gashi data auresa batama samun ikon ganinsa kamar yadda taso shiyasa ta dora mata tsanar duniya duk da batasan tana mata kiyayya ba kuma itace wacce take zuga sarki akan a aura As'ad mata. Ayshatu ta ɗauki kiran, Sarauniya Amina ta fara magana cikin nuna mamaki da zazzafar dariya “Garin yaya kika yi wannan sakarci da har za a samu damar zagin mijinki? Kin san irin abinda Haneefah ta ce kuwa?”
Ayshatu ta ɗan runtsa ido, cikin nutsuwa ta ce “Lafiya kuwa? Me ke faruwa? Me haneefah tace akan habibie??”
Sarauniya ta amsa da muryar da take hade da dariyar raini “Haneefah tace mijinki ba shi da ƙarfin biyan mace bukata! Kin ji kalmar nan da kunnuwanki?”
Ayshatu kuwa bata bari a zubar mata da mutunci ba. Cikin natsuwa, amma da ɗsn dariya, ta ce “Ai wannan ce matsalarsu. Ni da haka nake son abuna . Na fi son zaman lafiya da kwanciyar hankali, ranki ya daɗe. Abuna ya jima yana min dadi ba tare da damuwa ba.”
Sarauniya Amina ta ɗaga gira, mamaki da baƙin ciki yacika mata rai tabbas tasan halin ayshatu zatayi abunda yafi haka ma makirace ta karshe sannan shu’uma ce sosai sai tacigaba da kallon wayar kamar tana nazarin Ayshatu sai kuma tace “To shiyasa ashe baki ci gaba da haihuwa ba kenan? Duba shekarunki da lafiyarki, amma yara biyu kacal?”
Ayshatu tace “Yara biyu da Allah ya bani sun ishe ni. Banson hayaniyar yara da yawa kin san halina. Ni zaman lafiya da kwanciyar hankali nake so. Dan su ne ginshikin farin ciki na.”
Ganin kar tayi mata fitsara yasanyata Sukayi sallama cikin ladabi, Ayshatu ta kashe kiran. Amma da zarar an katse, sai Sarauniya Amina ta fashe da dariya mai ƙarfi dab ita kaɗai tasan abunda ke ciƙin zuciyarta.
“Babu As’ad, babu mulki har abada! Na nisanta shi da iyayensa yanzu kuwa zai zama cikakken wulakantacce, In shaa Allahu! Har hauka ma sai yayi!” Sai ta fashe da dariya, wacce ke cike da alamar mugunta da makirci.
************
Da sallama mai rauni ta turo ƙofar babban ɗakin, Jamila ta shigo da wani irin ɓacin rai da harararta kaɗai za ta iya cin zuciya. Dakin ya yi shiru, sai bushewar numfashinta da gigin zuciyarta suka cika sararin wajen.
"Ke Haneefah! Wannan aikin da kika yi kina ganin daidai ne? Wannan mutumin da ya daga ki sama, wanda ya dora ki akan turbar rayuwa, wanda ya cire ki daga duhu ya miki hidimar aure ya sanyaki amakaranta tun kina karama har yafiddake waje? yanzu shine kika jefa cikin kunya da tozarci?"
Jamila ta taka zuwa gaban Haneefah, tana duba ta kamar wadda take so ta fahimci dalilin da yasa ’yar uwarta ta aikata abin da zuciyarta ta kasa ɗauka.
"Ko da kuwa gaskiya ne, shin bazaki rufa masa asiri ba?Wannan shine sakayyar alherinsa?"
Anty Jamila ce, ɗiyar Fulani Maryam macce mai tsananin bin doka da tsari. A gidan su, mutane suna kiranta "Malama", saboda tsantsar kamun kai da tsoron Allahnta. Da wani bai san asali ba, zai rantse ba ’yar Fulany Maryam bace.
Haneefah, da idanu sun cika da hawaye masu nauyin zuciya, ta ce da ita ƙasa-ƙasa,
"Yaya Jamila, ba sharri nake ba... gaskiya ce kawai nake faɗa. Kinsani gaba, sai masifa kike. Amma wallahi, ban masa
ƙarya ba."
"Zaki rufe min baki ko sai na miki illar da ba za ki manta ba? Mama ke goyon bayanki, kina iskancin da kikaga dama. Sai dole kinyi masa sharri kamin ki rabu da shi? Kin manta ke aurenki biyar yanzu? Wannan na shida ne, wallahi na rantse, ba da son ransa ya aure ki ba. Kuma ki rubuta ki ajiye sai kinyi danasani wallahi."
Fulani Maryam ta shigo cikin kwanciyar hankali, amma idonta ya cika da baccin rai
"Jamila, tashi ki bar min ɓangaren. Ba za ki ci mutuncin yarinya a idonna ba. Kin manta ita fa ‘yar uwarki ce. Idan har ta yi kuskure, ai ba haka ake gyara ba. Wani banza marar kishin ‘yan uwansa ne kike fushi akansa?"
Jamila ta kalli mahaifiyarta da kai a ƙasa, ta dan furta cikin wata murya mai rauni,
"Allah ya baki hakuri Mama. Sai an jima."
******
Tunda jirgin alfarma ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe, Abuja, komai ya kasance a cikin tsari na musamman. Motocin convoy ɗin mai girma As'ad manyan *Mercedes Maybach* da *Range Rover Autobiography* sun ɗauke shi kai tsaye zuwa katafaren gidansa dake Maitama. Ana buɗe masa kofar motar, ya fito da launin gilashinsa mai *designer cut*, yana dafe kansa kamar wanda ke ƙarƙashin nauyin wata zuciya da ke tafasa.
Jikinsa na ɗauke da wani irin zazzabi mai sanyi da dumi a lokaci guda nau’in da ba jiki ke yi ba, amma zuciya. Ba ya magana, ba ya kallon kowa. Kai tsaye ya wuce ɗakin wanka nasa na alfarma, inda ke da jacuzzi mai ɗaukar mutane uku, ruwayen *essential oils* da *aromatherapy* sun cika ɗakin da ɗan kamshi mai ɗaukar hankali haɗin vanilla da sandalwood.
Ya cire kaya cikin kasala, jikinsa na rawa a hankali. Ruwa na dumi ya fara zagaye jikinsa kamar yana shan numfashi na sabuwar duniya. Amma hankalinsa baya nan yana nesa. Kalmar da ta daki zuciyarsa kamar takobi mai kaifi ita ce
**“Haneefah ba za ta iya zama da nakasasshen namiji ba.”**
Zuciyarsa ta rikice. Jijiyoyin kansa sun kumbura kamar ana busa iska a cikinsu. Ya lumshe ido, ya saka kansa cikin ruwan jacuzzi kamar yana buƙatar ruwa ya ɗauke masa tunani. Ya fitar da wani gajeren numfashi mai nauyi, ya ɗauki wayar dake gefensa iPhone 15 Pro Max, ya dannata ba tare da tunani ba. Sai kawai ya furta, cikin murya mai rauni, amma cike da buƙata
**"I need you... kusa da ni, Aishatu."**
Ya kashe wayar. Bai jira martani ba. Hannunsa yana riƙe da kansa kamar yana ƙoƙarin hana jijiyoyin zuciyarsa fashewa. Jacuzzi ɗin mai hasken milk na ci gaba da motsa ruwan da ke masa lulluɓi. Domin daɗin jiki, babu; daɗin rai kuwa? Ya ɓace tuni.
Tunda ta buɗe ƙofar bandakin alfarma, iska mai ɗauke da ɗan kamshin sandalwood da vanilla ya bugi hancinta. Idanunta suka sauka a kansa yana cikin ruwan jacuzzi, da fuska mai cike da raɗaɗin zuciya. Jijiyoyin kansa sun tashi, idanuwansa jajir, har suka yi ƙyalli kamar za su kawo ruwa ba don zafi ba, sai don zuciyar da ke tara abu mai nauyi.
Ya ɗaga hannunsa da kasala ya yi mata alamar ta ƙaraso. Cikin numfashi mai nauyi, ta kalle shi da murya da bai fito ba amma zuciyarta ta furta *“Kai kadai ka isa ka fasa garin zuciyata.”*
Cikin natsuwa da tsari, ta soma cire rigar jikinta tana kallonsa kai tsaye kamar tana turawa zuciyarsa saƙon da kalma ba za ta iya faɗi ba. Ta rage kayan jikinta har sai da ta bar *lace bra* da pant ɗinta masu launin shudi mai siriri. Tsantsar tsarinta da jin daɗin jikinta suka haɗu da halin alfarma da ya ratsa dakin.
Ta tako a hankali, kowane mataki kamar kiɗa ne a kunnensa. Muryarta ba ta motsi, amma hannayenta sun riga sun isa ga shi. Tana kallonsa da idanu cike da kauna da zafi kamar soyayya tana tafasa a zuciyarta.
Ta shiga cikin jacuzzi ɗin kamar wacce ke shigowa wata sabuwar duniya. Ruwan mai dumi ya hau jikinta, ya haɗu da jin sanyi na tsantsar kusanci. Ta shiga rungume shi daga baya, jikinta yana lulluɓe da nashi. Hannunta na sannu-sannu yana bin kirjinsa har zuwa bisa wuyansa, tana furta masa da wani ƙasƙantar murya mai daɗi
**"Na rasa kaina cikin ka... Ina juyawa a jikinka ka sassauta abunda kakeji habibie."**
Shi ma ya rungume ta kamar yana so ya shigar da ita cikin zuciyarsa. Ya matso da bakinsa zuwa kunnen nata, yana raɗa mata wasu kalmomi masu ɗumi
**"Ke kadai ce mafita a gare ni... kuma kema kin sani."**
Numfashinsu ya haɗu, zafin ruwan da suka shiga ya zama kamar zafin da ke fita daga jikinsu *soyayya mai cike da radadi da narkarwa.* Jacuzzi ɗin ya koma shiru, sai su biyu ke can, sun haddace jikin juna, ba tare da wata magana mai yawa ba. Amma zuciyoyinsu na yin ihu cikin kauna mai nauyi, cike da so da buƙata.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA TALATIN DA BIYU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
A hankali ya rungume ta, jikinsa yana rawa cikin sanyi da zafin zazzabi. Idanuwansa wadanda a da suke da farin kwarjini yanzu sun koma jajir, cike da gajiya da raɗaɗin zuciya. Kirjinsa na dukan sannu-sannu kamar ana karanta waka mai ciwon rai a ciki.
Aishatu ta zuba masa ido cikin rawar murya da fargaba ta ce
“Habibie... ya kamata a kira likita. Jikinka zafi sosai... kamar wuta ke tafasa a jikin ka."
Ta dafa kirjinsa da hannunta, tana shafa shi a hankali. Amma kafin ta ƙara magana, zuciyarta ta karye. Hawaye suka gangaro daga idanunta kamar ruwan sama da ba zai tsaya ba. Ta kifa kanta a kirjinsa, tana rungume shi da ƙarfi kamar tana son ta rufe shi da numfashinta.
"Habibie... zuciyata zafi take yi idan na ganka haka. Yaushe rabon da na ga damuwa ya ɗaure maka fuska? Wannan ba kai bane... ba shine Habibiena da ya saba dariya ba.”
Ya lumshe idanu, ya ɗaga hannunsa da rauni ya ajiye a kan laɓɓanta. Muryarsa na fita kamar daga zurfin numfashi mai nauyi
“Shhhh... Aishatu. You're my only hope... Wallahi ke kaɗai na mallaka. Amma... kema kin san ba zaki iya zama da nakasasshen namiji ba, ko? Kema zaki gudu, ki barni kamar sauran kowa, ko?”
Idanuwansa sun rine jajir tamkar wuta a cikin tabo. Zuciyarsa cike da tsoro da rashin tabbaci.
Aishatu ta dafa fuskarsa da hannayenta biyu. Ta dinga girgiza kanta a hankali, idonta cikin nashi, hawaye na zuba.
“Habibie, ba zan gudu ba! Saboda jikinka, rauninka ba zai kore ni ba. Kai ne soyayyata, ba siffarka ba. Ka manta? A cikin idanuwan nan na fara ganin duniya. Kuma in har duniya zata zama ba kai, to ni ban buƙatar ta.”
"Zuciyarka ce rayuwata, numfashinka nawa ne. Ba zan bar ka ba ko da kowa ya bar ka.”
Ya fara lumshe ido, numfashinsa na sauka daidai-daidai.