Kenza eBookz

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 20

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 20

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 20: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 20. Ta jingina goshinta da nashi, tana shafa…

3,345 words

Ta jingina goshinta da nashi, tana shafa kansa da yatsunta kamar tana rarrashi jariri. Sannan ta ce cikin ƙasa da murya amma da girmar ƙauna "Zan kasance a nan a koda yaushe, a cikin damuwarka, a cikin zafinka, a cikin rauninka. Ka ɗaukeni a matsayin rabin jikinka. In kaciwo, nima zanciwo. In ka narke, nima zan narke tare da kai.”

Idanun As’ad na kallon Aishatu yayin da take furta kalmomi masu taɓa rai. Idanunsa sun cika da wani irin haske mai launin tausayi da yarda, kamar rana da take bayyana bayan ruwan sama mai tsanani.

Ya kasa magana. Hannunsa ya dafe gefen fuskarta cikin rauni, ya furta a hankali

"Aishatu... ni da gaske na rasa kaina “

Sai ya lumshe ido, yana sauke ajiyar zuciya mai nauyi, zuciyarsa tana narkewa kamar kankara a rana. Aishatu ta sumbaci goshinsa cikin natsuwa, ta sake rungumesa tana shafa bayansa da laushi. Ta zauna a bayansa, jikinta na rufe nashi, kamar tana so ta karɓi duk wani zafin da ke jikinsa.

Bayan sun fito daga bandakin wanda aka kawata da *Italian Carrara marble*, ruwan sanyi na feshin *aromatherapy* na ci gaba da tafasa a sama. Aishatu ta taka zuwa *smart console panel* ta danna maballin kiran gaggawa, sannan ta ce da murya mai natsuwa

“Call Dr. Malik. Emergency.”

Cikin mintuna, *family doctor* Ya shiga ɗakin , ya duba As’ad, sannan ya masa allura mai hanzari daga *Dubai medical supply*. Cikin natsuwa ya ce

“He needs deep rest. His vitals are overstretched. Emotionally... he’s exhausted.”

Aishatu ta kalle shi tana girgiza kai. Ta dawo kusa da As’ad, ta zauna kan *Loro Piana cashmere chaise lounge*, ta riƙe hannunsa. Tana kallonsa kamar wata mai yin addu’a ga zuciyar da take ƙauna

"Habibie... just breathe. I’m here. I’m not leaving."

As’ad ya lulluɓe da * blanket* mai laushi, sannan bacci ya fara kwasarsa cikin sanyi. Aishatu ta zauna gefensa.

"Huta. Zan tsaya a nan har zuciyarka ta dawo daidai.”

Bayan rana ta fadi, Aishatu ta nufi babban kicin na gidan wanda ke da kayan zamani Tana sanye da *Chanel loungewear*, ta shirya masa abinci cikin faranti Ta shirya masa Saffron-infused couscous,Chargrilled salmon with truffle butter,Mint-cucumber detox water.A dining table ɗin ta aje abincin.

Bayan sallar Azahar da La’asar da ya yi a cikin masallacin cikin gidan da ke gefen gabar ruwa, As’ad ya fito cikin *tailored silk thawb*, yana takowa cikin nutsuwa zuwa falon da aka cika da alatu da kamshi.

Ya zauna, yana kallonta da murmushi mai gajiya da godiya.

"Aishatu… yau na fara jin zan iya rayuwa da kyau saboda ke."

Ta karaso, ta zauna gefensa, tana kallonsa da idon da ke bayyana *"ni nake da kai gaba ɗaya."* Sai ta ce “Jikinka da gajiya... Ka barni na taimaka maka ka ji sauƙi.”

A hankali, ta taimaka masa cire rigarsa, tana shafa masa kafadarsa da *organic eucalyptus oil* daga Australia. Tana masa tausa a hankali daga kafaɗa har wuyansa, tana furta masa da murmushi "Na sadaukar da ƙaunata domin tsarkake jikinka da ruhi. Wannan jikin naka, zai dawo lafiyar da ya dace, saboda ka cancanta da mafi alheri.”

As’ad ya lumshe ido, yana riƙe hannunta da tsananin shauƙi. Yana jin wani irin sanyi cikin ransa ba saboda magani ba, amma saboda ƙaunar mace guda ɗaya.

Ya riko hannunta yana aza mata rikitattun idanuwansa da har yanzu suke cikin wata kalar yace "karki rabu dani... har abada."

"Ina tare dakai har abada. Kai ne komai na."

Sai ya jingina jikinsa a nata, cikin launin daddadɗen dusk light.

*******

Da sassafe hasken rana mai sanyi ya ratsa gilashin *floor-to-ceiling window* na ɗakin As’ad, yana yawo a jikin *pure silk curtain* mai launin ƙasa. Sautin kiɗan *slow jazz instrumental* na *Bose ceiling system* yana ci gaba da kaɗawa a hankali.

As’ad ya bude idanu da ɗan rauni, numfashinsa yana fitowa a hankali. Har yanzu jikinsa babu ƙwari, ciwon da ya ɗan ji jiya bai warware ba sosai. Bai yi ƙoƙarin tashi ba, domin jikinsa ya fi ƙarfin zuciyarsa.

Aishatu, wacce tuni ta farka, tana sanye da *Chanel sleepwear*, ta matsa kusa da shi cikin siririyar murya mai taɓa zuciya, ta dafa ƙafarsa.

“Habibie… ka kwanta, bari na taimaka maka.”

Cikin tsantsar kulawa da natsuwa, ta kama hannunsa, ta ɗan sumbace shi, sannan ta fara rage masa kayan jikinsa — *custom tailored silk pyjamas* ɗinsa mai ɗinki daga *Savile Row*. Ta rike shi har zuwa cikin *marble bath suite*, ɗakin wanka na alfarma wanda ke cike da *Aromatherapy Associates oils*, ruwan zafi mai sanyi da kamshi na lavender da chamomile.

Yana shiga cikin ruwan, Aishatu ta zauna a gefensa, tana ɗura masa ruwa a baya da hannu, tana furta kalmomin da ke narkar da zuciyarsa

“Karka manta, ni ina tare dakai a duk inda kake, da duk yadda kake. Wannan ciwon naka ba ya taɓa ƙaunata, sai dai ya ƙara mini kishin jin dadinka.”

As’ad ya jingina a wuyanta. Ajiyar zuciyarsa ta fita a hankali. A lokacin da ya gama wanka, Aishatu ta ɗauko tawul mai laushi daga *Villeroy & Boch*, ta goge masa jiki, sannan ta taimaka masa ya koma bedroom.

Yana zaune a gefen *6ft Italian velvet bed*, Aishatu ta zube a ƙasa cikin salo, ta ɗauko *scented therapeutic balm*, ta fara shafawa a kafarsa, zuwa cinyarsa da kafaɗa. Hannunta na yawo a hankali, idonta cikin nasa.

Cikin wani irin zazzafan raɗaɗi na zuciya, As’ad ya ce

“Aishatu… ina jin sha’awarki kamar hauka, amma jikina ya ƙi tashi. Gaban ma bai motsa ba.”

Aishatu ta riko hannunsa da laushi, ta lumshe ido, sannan da nutsuwa ta ce

“Calm down, Habibie. Please naga alamun haka atattare dakai tunda Kace zakaje ka ga doctor ko? Karka damu da wannan. Komai zai zama labari.

Bayan shiru na ɗan lokaci, As’ad ya kama hannunta yana kissing a hankali

"Tomorrow… we fly out to Paris. Na shirya private jet ɗin mu. Na yi booking a The Peninsula. Zamu huta, acan ina son yakasance just me and you."

Aishatu ta langabe kanta a ƙirjinsa, tana murmushi da ido cike da shauƙi. Ta ce

Wani murna ne ya lullubeta tasan wannan abun da tayimasq bakaramun dukiya zataka kara samu dashi ba dan shi mutum ne mai son akula dashi sosai wannan tafiya tayimata dadi tasan tunda yace Su huta To yana nufin ayyukansa zasu koma can.

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA TALATIN DA UKU

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Tun cikin motar nake kallon yadda Maman Khalil ke kuka kukan da ke fita daga zuciya, wanda ba'a iya ɓoyewa. Hannunta na goge idanu, amma hawaye na ci gaba da zuba. Ganin haka sai damuwa ta sake lullube ni. Zuciyata ta dinga bugawa da ƙarfi.

Na kalleta cikin firgici, amma sai na ɗauke kaina. Tambayoyi masu nauyi suka fara zagaye cikin zuciyata

“Shin Khalil ne ya mutu? Ko Abba ya aiwatar da barazanar da ya yi masa?”

A wannan lokacin, bani da wanda zan tambaya. Bani da wanda zai bani amsa. Sai dai zuciyata na karanta mummunan abu.

Mun tsaya a gaban wani katafaren private hospital mai kyau da tsafta. Tsakar gidan cike da furanni masu kamshi, kofar shiga tana ɗauke da sunan "Al-Ameen Specialist Centre."

Maman Khalil ta juyo gare ni da ido cike da raɗaɗi, ta ce

“Ramlah... fito.”

Na sauka daga motar jikina duk a mace, numfashina ya rikice. Muka danyi tafiya kaɗan cikin asibitin har muka ƙarasa wani ɗaki da aka kawata cikin salo fale-fale masu tsabta.

Da muka buɗe ƙofa muka shiga, sai ga maza biyu tsaye fuskokinsu babu annuri ko murmushi. Gefe guda kuma akwai wasu mata gufa biyu, kowacce tana sanye da mayafi, fuskokinsu sun kumbura da kuka. Kallon da suka juyo suka yi min ya cika da harara, kamar ni ce sanadin damuwar da suke ciki.

Na danne zuciyata, zuciya na harbawa da sauri. A gefe na ga wani labule, an yaye shi a hankali.

Idanuwana suka sauka kan wani mutum da ya kwanta ba tare da motsi ba Khalil ne!

Na dafe ƙirjina cikin firgici, na furta “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un...”

Na matso kusa da gadon, idanuwa na cike da hawaye. Khalil ya rame sosai, fatar jikinsa ta sauya launi. Fuskar sa ta cika da fari mai duhu, alamun rashin lafiya mai tsanani. Baya motsi sosai, sai murya ɗaya-ɗaya da ke fita daga bakinsa cikin surutu.

Na ji yana faɗin "Ramlah... idan kika haifa min baby, ki saka sunan mamarki... ki sakawa mamanki..." Hawaye suka kwace min da ƙarfi. Na saki wani irin kuka mai tsanani kuka da ya fito daga zuciya, wanda ko ban furta kalma ba, sai zuciya ta bayyana.

"Khalil! Kai ne haka? Na san ba ka cancanci wannan ba! Allah ya kawo maka sauƙi... Allah ya baka lafiya..."

Dakin ya cika da kuka. Yayansa da Mamansa duk suka fara hawaye, suna karanta addu’a.

Ko motsawa bai yi sosai .Dakin ya koma shiru. Sai sautin kuka da karanta istighfari ke tashi daga ko'ina. Na girgiza kaina cikin baƙin ciki, zuciyata kamar an caka mata ƙusa mai zafi. A wannan lokaci, na fi kowa jin ƙunci. Na fi kowa jin nauyin wannan halin da muke ciki.

Kamar ina mafarki... amma wallahi, ba mafarki ba ne wannan gaskiya ce, Khalil ne yake kwance babu lafiya dik wanda yagansa Sai yayi masa kuka.

Daga gefe na jiyo yayarsa da masifa, tana kuka tana fadin

"Ramlah! Wane irin asiri kika yiwa Khalil?!”

Na juyo da ido cike da damuwa, zuciyata na harbawa kamar zata tsinke. Ita kuma ta ci gaba da masifa cikin kuka mai nauyi.

"Wacce irin soyayya ce haka? Tun ranar da mahaifinki ya raba ku, sai ya rikice! Ya zama kamar mahaukaci. Shaye-shaye ne kawai ke damunsa! Ki dubi yadda ya rame! Kina kallo kina kallon yadda yake lalacewa!"

Zuciyata ta karɓi kalmarta kamar an jefa mata ƙaya. Na kasa motsi daga inda nake. Sai wani kuka ya ƙwace min, na zube a kasa da ƙarfi ina rera kuka mai ciwo.

Na kalle shi Khalil. Ya rame, ya bushe, kamar ba shi ba. Fuskarsa duk ta sauya, idanunsa sun rame, numfashinsa ba daidai ba. Na juyo na kalli Maman Khalil, fuskarta cike da hawaye. Kamar rai zai fita. Samarin yayyansa ma kuka suke tamkar yara.

A hankali na matso kusa da gadon, jikina na rawa. Na kama hannunsa cikin tausayawa, murya na rawa nace "Khalil… dan Allah ka tashi."

Sai muka ji kamar daga can ƙasa yana ƙoƙarin magana. Muryarsa da rauni sosai

"Ramlah ce?... Mama, Ramlah ce?"

A hankali ya buɗe idanunsa, yana kallona. Idanuwansa sun cika da ƙauna, hawaye da raɗaɗi. Ya ce da murya mai narkewa

"Ramlah... dan Allah ki aure ni. Ki gaya wa Abba kina sona. Kina kaunata ko?"

Cikin wani irin shauk’i da tausayi, kuka ya ƙwace min. Na kasa magana Sai dai na lumshe ido sannan nace da murya mai laushi

"Ka bar shan komai. Kada ka ɓata rayuwarka. Ina tare da kai... kullum."

Sai ya motsa kamar yana ƙoƙarin tashi, amma jikinsa ya gaza. Sai yayansa ya shigo da sauri, ya dagashi a hankali ya sa masa filo a bayansa. Na ji yana faɗa wa su Mama

"Su bamu wuri."

Kowa ya fice. Dakin yayi shiru. Sai ƙamshi da karancin numfashin Khalil ke tashi.

Ya kalleni da ido masu raɗaɗi. Yace "Ramlah… kin san halin da nake ciki? Abba yace wallahi har abada ba zan auri ki ba. Wai wai zan lalata miki rayuwa."

Ya juyo da ido gare ni, yana fitar da numfashi a hankali "Amma ke kina sona ko?"

Na daga kai, idona cike da hawaye.

Ya lumshe ido cikin salama, sannan ya ce da wata kalma da ta tsayar min da numfashi

"Ke ce rayuwata. Idan na rasa ki… kamar na rasa numfashina ne."

Na lumshe ido, zuciyata na bugawa da karfi. Na kasa magana. Zuciyata kamar an shake ta da igiya. Kamar numfashina yana tafiya da kowane kalmar da Khalil ke faɗi.

Ya juyo yana kallona. Fuskar sa ba annuri, amma kalmarsa mai daɗi da ciwo a lokaci guda.

"Ramlah..." ya kira sunana da wata murya mai taushi kamar numfashin ƙarshe.

Na ɗaga kai, idanuna cikin nashi, sai yace

"Idan na mutu Ramlah... idan Allah ya ɗauke ni..."

Ya tsaya. Numfashinsa ya dan yanke. Sai ya ɗora hannu bisa fuskata a hankali.

"Ki saka sunana a zuciyar ki har abada. Koda kin auri wani, ki rikeni a cikin zuciyarki."

Hawaye suka fara zuba daga idona nace “Kadaina faɗin haka Baza mutu ba.”

Yakara faɗin "Idan kika haifi yara... ki fadi musu labarina. Kice musu akwai wani saurayi da ya ƙaunaci maman su kamar numfashinsa... amma ba su da rabo."

Na fashe da kuka. Kuka mai tsanani wanda sai da ya girgiza duk jikina.

"Khalil ka daina faɗin haka... ka daina..." na ce cikin rawar murya.

Amma ya cigaba.

"Ramlah... ki yi min addu’a idan na mutu. Koda duk duniya ta manta dani... kada ke ki manta."

Ya sauke numfashi, yana kallo na, sannan ya furta da ƙarfi kadan

"Ni dai ina son ki Ramlah. Kuma idan na mutu... kauna ta bani daraja. Ki ce min... soyayya ta bata tafi a banza ba."

Hawaye suka ci gaba da gangarowa daga idanuwansa. Sai ya ce

Na saka kaina a ƙasa, na fashe da kuka. Na ji kamar ana warware zuciyata ne a hankali. Kamar zan fita hayyaci na.

Wani irin tari ya taso masa kwatsam, har sai da na firgita. Yayi ƙarfi sosai, kamar zai fitar masa da zuciya. Hankalin kowa ya tashi.

Cikin mintuna kaɗan likita ya shigo da sauri. Amma maimakon fara dubashi, sai faɗa ya fara

"Me ya sa ba a ba shi abinci ba tukuna? Ta yaya ake tunanin mutum zai sha magani ba tare da komai a cikinsa ba?"

Mama ta daure fuska, cikin muryar damuwa tace

"Ai likita ba cin abincin yake yi ba. Koda ya ci, sai yamaida. Duk wani abu da ya ci, sai ya dawo da shi."

Likita ya jinjina kai yana girgiza, sannan yace

"Dole ne a daure a ba shi yanzu. Abincin ya fi magani muhimmanci a wannan lokaci."

Na juyo ina kallon Mama. Na ce da ita a hankali

"Mama, dan Allah ki bani abincin. Zan ba shi da kaina."

Ta dubeni na ɗan lokaci, sai ta ɗaga kai cikin natsuwa tace

"To Ramlah, nagode. Ga abincin nan."

Ta miƙo min farantin, na karɓa a hankali, zuciyata cike da tausayi. Na nufi gadon da yake kwance, na zauna a kusa da shi, ina kallon fuskarsa.

Wallahi idan ka gan shi a yanzu, sai ka sa kuka. Shi da yake namiji ne mai ƙarfi da kuzari, yanzu ko jingina da kai ba zai iya ba.

Na ce a hankali

"Khalil, ka buɗe baki ka ci. Dan Allah..."

Ya ɗan juyo yana kallona da idanunsa masu cike da rauni. Sai ya buɗe bakinsa kaɗan. Na fara ba shi a hankali kamar yaro. Duk abincin ya cinye da ikon Allah. Bai ce komai ba, amma idanuwansa sun faɗi komai.

Na kalli agogo. Lokaci yana kusa da ƙarfe bakwai na dare.

Nurse ta shigo, ta yi masa allura. Kafin minti talatin ya cika, bacci mai nauyi ya ɗaukesa. Na sauke numfashi, na tashi na juyo na kalli Mama.

Na ce da ita cikin ladabi

"Mama, zanje gida yanzu."

Tayi shiru kamar bata jini ba. Sai da na maimaita sannan tace da dan sanyi

"To Ramlah, ga driver a waje zai kai ki."

Naji kamar kalamanta sun buge zuciyata, amma nayi shiru. Na miƙe da ladabi, na fita daga ɗakin.

Yayyensa mata suna zaune, amma babu ko ɗaya da ta kalle ni. Babu wacce ta ce min sai anjima bayan nayi musu sallama babu wacce ta yi magana. Sai zuciyata ta sake nauyi.

Na daure, na sauka har waje. Driver na jira na, na shiga mota cikin shiru. Har muka bar asibitin, babu wanda yayi magana..

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA TALATIN DA HUDU

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Bayan na fita daga asibitin, zuciyata kamar an daura min dutse. Kowanne mataki da nake ɗauka, kamar nauyi nake ja.

Tunani na Khalil.

Tunani na Mama.

Tunani na yayyensa da suka ƙi kallona.

Tunani... akan me yasa rayuwa ke canzawa a hakan?

Na kai hannu na bisa kaina, na dafe, sai hawaye suka gangaro a hankali. Duk da ina ƙoƙarin ɓoyewa, sai da wasu biyu suka zubo har ƙasan habata.

Na share su da sauri, amma zuciyata na bugawa kamar ana dukan ƙofa a cikinta. Wani irin damuwa ne da kalmomi ba za su iya bayyana ba.

Sai da muka hau hanya zuwa gida, zuciyata ta fara bugawa da ƙarfi. Na kalli agogon motar, naga ƙarfe tara saura. Magriba ma ban yi ba, balle isha’i. Na dafe kirjina. Na sauke ajiyar zuciya. Nasan halin Mumy... kuma wallahi, yau sai ta kusan karyani.

Ban san irin karyar da zan gaya mata ba. Sai kawai na saka kaina a jikin tagar mota, na hau kuka cikin shiru. Ban ce wa driver komai ba, shi ma shiru yayi kamar ya fahimci damuwata.

Da muka ƙarasa kofar gida, sai driver ɗin ya fito ya buɗe min ƙofa. Na sauka a hankali, jikina babu ƙwari. Na nufi kofar get ɗin, nayi knocking. Masu gadi suka buɗe min.

Na shiga cikin gidan a hankali, zuciyata kamar zata fasa ƙirjina.

Na tura ƙofar palo... idona ya haɗu da nata.

Mumy na zagaye a tsakiyar palon, tana tafiya kamar wadda ke jira. Da ta ganni, ta tsaya cak. Ta zubamin ido. Na ce cikin sanyin murya:

"Mumy sannu da gida..."

Bata ce uffan ba, kawai ta taso da sauri tuuah!

Mari biyu a jere! Sai da na durƙusa a ƙasa saboda ƙarfinsu. Idanuna suka cika da hawaye, zuciyata kuma kamar zata fashi.

Tace da wata murya mai cike da ƙiyayya

"Gidan uban wa kika je? Wai tun da mahaifinki yayi tafiya kin koma yawon banza! Ko Islamiyya sai ƙarfe tara zaki dawo? Ke karuwa ce! Shegiya... yar iska kamar uwarki. Inaga zaki fara bin hanya irin tata ko?"

Cikin firgita da tashin hankali, na kalleta... ban iya magana ba. Na ɗan buɗe baki ina son na fadi wani bayani sai kawai _praah!_ Sai da ta ƙara min duka tana zagina da maganganu masu zafi.

"Wai dubiya kika je? Ko dubiyar hotel? Sai dai ki jira uban naki ya dawo... wallahi sai na gaya masa komai!"

Na daure, na girgiza kai cikin hawaye. Nace da ita cikin rawar murya

“Mumy wallahi... Allah ya sani asubuti naje dubiya.”

"Allah sai na i gaya masa Idan ubanki ya dawo, sai ki gaya masa! Dallah ki tashi kije kitchen ki dafa jallop din taliya. Ga bereziyata can kije ki wanke. Kazama kawai!"

Na ɗan dakata, nace

"Mumy... bari nayi sallah, please."

"Sallar uwarki! Dallah shige ki yi min abincina kafin na karya ki. Ke fa banza ce, kazama! Wuce kije kitchen!"

Na juya da jiki mai nauyi, zuciyata cike da raɗaɗi da ɓacin rai. Na shige cikin daki ina kuka, amma na ce zan daure... Allah na nan, kuma zai kawo min mafita.

Cikin tsananin damuwa na dora mata jallop ɗin taliya a kan sin ɗin kitchen. Na sauke numfashi inayin shiru kamar mai jiran sakon da bai zo ba. Daga nan na ɗauro alwala a hankali, zuciyata tana tafasa da tunani, hankalina yana can wajen Khalil.

Na tsaya yin salla a kitchen saboda tsoro ya hana ni shiga ɗaki. Gabaki ɗaya tunanina ya tattaru ne a kansa. Kai! Duniya abun tsoro ce...

Ni da kaina ban taɓa tunanin akwai irin soyayyar da Khalil ke yi min ba soyayyar da nake jin kamar zan narke saboda nauyinta da gaske.

Ban gama komai ba sai wajen ƙarfe goma da rabi. Na tashi na ɗakko bra da pant na Mumy, na wanke su da kyau, na shanya. Da kyar na tafi dakina.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull