Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 21
Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 21: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 21. Da na shiga, gabana ya ƙara ɗaukar zafi.…
3,357 words
Da na shiga, gabana ya ƙara ɗaukar zafi. Kurajen dake min ƙunci sun dan lafa, amma susar su sai gaba take da karfi. Wallahi ina jin zafi, amma ina jimrewa, domin tsarki da ruwan gishiri yana bani sauƙi ko da kuwa yana ƙona jikina.
Sai na haɗa ruwan zafi da gishiri, na wanke gabana da niyyar samun sauƙi. Amma ba zan iya faɗa wa Mumy ba nasan idan na buɗe baki ta ce, “To ba yawon banza ne ke kawo hakan ba?” Tunda yanzu, kalmarta ɗaya ne “Karuwanci.”
Wani zafaffen hawaye ya gangaro kan fuskata. Wallahi maraicin uwa radadi ne. Radadin da idan kana ciki, baka da mafita sai Allah.
Wani lokaci ina mamaki... me nayi wa Mumy haka? Ita ce Mumy ɗina da a da take sona har fiye da kowa. Ita ce ke kawo min abinda nake so, kullum tana tare da ni. Amma yanzu ita ce babbar makiyata.
Na fashe da kuka... kuka mai ciwo daga can ƙasan zuciyata. Har cikin ƙashi nake jin dumin wannan kukan.
Ahaka na tashi, na nufi daddumata Na hau yin sallah, na yi nafila cikin kwanciyar zuciya, ina maimaita
"Ya Allah, Ka ba Khalil lafiya... Ka ba ni hakuri da kwanciyar hankali... Ka ba ni mafita daga wannan rayuwa..."
Zuciyata tana kuka... idanuna ma haka... amma zuciyata ta fi kukan da ya fito da ido.
**********
Cikin kwanakin nan, damuwa ta mamaye rayuwata. Wallahi ko kofar gida bana fitowa, sai dai na zauna a daki na shiga kuka. Tun ranar da na kai karfe tara a waje, Mumy ta kira Abba, ta gayamasa. Shi kuma nan take ya bukaci a bamu waya. Faɗa ya shiga yi min cikin ɓacin rai, ya hana ni fita har zuwa Islamiyya. Wannan yasa hankalina ya ƙara tashi.
Yanzu haka, bayan na gama duk aikin gida, ban da wani abin yi. Sai kawai na kwanta ina kishingiɗe, zuciyata cike da nauyi. A cikin bacci na, na fara mafarki mai firgitarwa. Wata baƙar mace ce ke bina da wuƙa tana ƙoƙarin kashe ni. Ina ta gudu, amma kamar ƙafafuna sun ƙulle. Sai kuma wani bak’in halitta ya rikeni yana neman sha jinina.
Ban san yadda akayi ba, sai kawai na farka cikin razana. Na tarar da Mumy na kwarara min ruwa a fuska tana masifa. Cikin tsoro na kalleta, na rasa ma bakin magana.
Ta ce, “Ban ce miki yau Abba zai dawo ba? Bazaki tashi ki masa girki ba? Kina nan kina surutai cikin bacci kamar mai aljanu!”
Na yi shiru, ban ce komai ba. Sai da ta fita sannan na soma karanta addu’o’i. Na tashi jikina ba kwari, amma na daura alwala na shiga kitchen domin fara girki.
Ina tsakiyar girkin ne sai na ji sallamar ƙannin Abba naji wani sanyi ya shige ni. Anty Luba ce da wasu daga cikin dangin Abba. Tuni na san za ta taimaka min in samu damar ganin Khalil, tunda ta fi kowa sanin irin halin da muke ciki, kuma ita mutuniyar Mumy ce.
Na fito da fara’a na gaishe su. Kowacce ta zuba min ido tana cewa, “Ramlah ce? Kai! Kinyi kyau, kin yi kiba sosai!”
Mumy da sauri ta ce, “Ai maganin kiba ta fara sha sai kibar ke shigarta.”
Anty Luba ta yi dariya, ta ce, “A’a Mumy, ai Ramlah daman jiƙin kiba ne da'ita, kuma kina kula da'ita sosai shiyasa.”
Na kai musu abinci da ruwa da lemo, sannan na koma ciki nayi wanka. Su Hafsa kannen Abba ba sa sona tun asali ma dan ba su son mahaifiyata. Shiyasa ni ma bana kulasu tsakanina dasu gaisuwa.
Na fito daga bandaki sai naga Anty Luba tana salla. Na tsaya, ina kallonta komai nata dagwas dagwas abunta da zarar ta idar sai ta janyo ni kusa da ita. Ta kalli fuskata tana murmushi, tace "Ramlah, mashaa Allah! Kin yi kyau. Wallahi kin koma kama da mamanki. Mamanki fa kamar balarabiya ce. Ko ince, itace kam da Kakarki Mama. Kawai haske zasu nuna miki. Allah ya jikinta."
Na ce: "Ameen." Sai ta kalleni sosai, tace
"Ramlah me ke faruwa tsakaninki da Zainab ne? Na lura komai naki sai ta gwasale. dazu Har zaginki naga datayi.
Baki na na buɗe nace
"Wallahi yanzu ba ta ƙaunata ko kaɗan. Ba kamar da ba."
Ta girgiza kai, tana murmushi mai tausayi.
"To ai na sani. Kiyi hakuri, Ramlah. Wannan itace taki kaddarar ki karɓeta da zuciya ɗaya. Ko da Abba ya hana Khalil aurenki, wallahi ni ba ji daɗi ba ace mutum tun kana ƙarami yake sonka kuma anyi masa alkawarinki sai yanzu a hanasa. Duk da nasan zugar momy ce. Amma kinga fa yadda ya koma yanzu..."
Wani zafaffen hawaye ne ya zubo min, nace
"Anty Luba, dan Allah ki taimaka min ki kai ni naga Khalil. Wallahi kullum cikin tunaninsa nake."
"Kar ki damu, abinda ya kawoni kenan. Hajiyarsu ta aiko ni. Nazo domin mu shirya, muje tare.
Ko da zata fita, ta tambayi Mumy
"Mumyn Ramlah, ina Bilkisu take ne?"
Mumy tace
"Ai tafara zuwa aiki."
Anty Luba ta ce "Kai, mashaa Allah! To kinga zanje kasuwa wa zai rakani ya rike mun ledoji?"
Sai Mumy ta ce
"Ga Ramlah nan, uban me take yi da bazata rakaki ba?"
Anty Luba tace
"Nagode. Ramlah, sa hijjab dinki, ki rakani kasuwa."
Na amsa da murmushi, na shige ciki na ɗauko hijjab. Doya da kwan da nayi na zuba a flask, fura na kuma na zuba acikin jug nasa fridge.
Na kalli Mumy, nace
"Mumy, sai mun dawo."
Su anty Hafsa ma na yi musu sallama, suka amsa amma daga ciki.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA TALATIN DA BIYAR
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Tunda muka fara tafiya, Anty Luba ke ta tayani hira iri-iri. Hira mai daɗi, cike da fahimta da kulawa. Har tana cewa tana jin dai Abbana zai tura ni waje domin ci gaba da karatu. Nikam sai na kalli fuskarta na yi murmushin dole. A Zuciyata tamkar in ce mata "Anty, ai mumy ta hana abba turani” Amma sai na haɗiye abun na yi shiru, na maida kallona waje.
Da muka karasa asibitin, muka shiga. A yau, dukkan ‘yan uwan Abba suna nan. Kowannensu da wata irin fuskata bakin ciki, tamkar ana karanta matsalolin zuciyarsu daga cikin idanuwansu. Suka amsa gaisuwata, amma ba don suna so ba kallonsu ya nuna cewa zuciyarsu ba tare da ni take ba. Suna kallona kamar ni na janyo ciwon da Khalil ke fama da shi.
Na tura kofar dakin Khalil da sannu a hankali, zuciyata cike da fargaba. Na shigo da sallama. Hajiyarsa na zaune a gefen gado, ta rame sosai. Fuskarta ta kumbura, idanuwanta sun kumbura alamar kuka.
Shi kuwa Khalil... Subhanallah.
Khalil da na sani, mai kuzari, mai dariya da annuri... yanzu yana kwance kamar gawa. Sa Numfashinsa kawai kake ji. Fuskarsa tayi duhu, idanunsa sun rufta, kamar bashi da rai, sai numfashi me wahala da ke fitowa daga bakinsa.
Cikin wannan lokacin ne yayarsa ta juyo da masifa
"Amma Ramlah, anya kina da zuciya kuwa? Kin ga yadda yaron nan ya rame saboda ke? Kwanaki uku kenan yana kiran sunanki, kullum sai ‘Ramlah... Ramlah…” ko yana bacci ma sai ya ambace ki. Amma kikasa zuwa ki dubasa ?
Na cika da kunya da damuwa. Hawaye suka fara gangarowa daga idanuna. Da kyar na samu damar cewa
"Anty... wallahi ba rashin kulawa bane. Babu halin fita ne, wallahi kullum ina yi masa addu’a, kuma da yardar Allah zai samu sauƙi."
Ta kalle ni, ta harare ni. Amma ni ban mayar da komai ba. Na karasa gefen gadon na tsaya ina kallonsa. Sannan na durƙusa a kasa, na dafa hannunsa a hankali. Sai.. kukan da ya fito daga bakina kuka ne daga zuciya, kuka da ke dauke da ciwo da ƙauna da tausayawa.
Kawai naji an damƙi hannuna. Da ƙarfi ya damƙe shi, kamar wanda ke kokarin kama mafita daga rami mai zurfi. Muryarsa na rawa, me cike da ciwo da ƙunci
"Wallahi babu inda zakije... Ramlah ki tsaya... kar ki tafi ki barni... don Allah ki tsaya..."
Idanuwansa a rufe, amma hawaye suna kwarara daga su kamar wanda ke kuka a mafarki. Hajiyarsa ta dafa kafadarsa tana cewa
"Khalil... ka bude idonka, ga Ramlah nan fa... itace ta zo."
Cikin yanayi na tausayi, da rauni mai tsanani, ya buɗe idanunsa a hankali. Sai ya zuba min su idanuwansa sun bushe, sun kumbura. Ya dafe cikinsa kamar yana jin ciwo. Muryarsa na fita da ƙyar kamar ana hura iska
"Ramlah... kina nan ko? Don Allah... kar ki ƙi ni. Ki tsaya... Amma kada ki ƙyale ni ki barni cikin wannan duhun da nake ciki..."
Zuciyata tayi wani irin nauyi. Kuka na cigaba da saukowa cikin tsantsar raɗadi.
Na kallesa nace
"Khalil... wallahi ina tare da kai. Wallahi bana ƙin ka. Ka daina yi wa kanka haka... Don Allah... ka ci abinci..."
Hajiyarsa ta tafara magana ciƙin damuwa
"Ramlatu, babu abinda yake yi sai ambaton sunanki. Dazun ma har da kuka yake cewa, ‘Ramlah ta gudu ta barni… Ramlah ta manta dani.’ Wallahi dai kin ga yadda ya rame... kamar an busar da shi."
Na lumshe idanuwa, na dafe kirji. Sai na ce cikin wani irin zazzafan hawaye
"Khalil... idan baka ci abinci ba.... ya kake so in ji? Ka ci abinci Khalil... don Allah..."
Ya dafe hannuna, hawaye na sauka daga idonsa. Muryarsa na rawa kamar wanda zai bar duniya
"Idan na mutu Ramlah... ki saka sunana a zuciyarki. Idan kin haifi yaro... ki sa masa sunana. Kada ki manta da ni... Kada ki hana yaronki sanina... Ki yi min addu’a ko da na daina kasancewa a kusa da ke."
Na fashe da kuka mai ƙarfi. Kuka da ban taɓa yi ba. Na durƙusa a gaban gadon, na jingina kaina a saman hannunsa, zuciyata na tafasa da zafi.
Cikin kuka da girgiza, sai ya damƙi hannuna kamar wanda ke neman mafita daga bala’i. Ya ɗan motsa jikinsa kamar yana ƙoƙarin tashi, amma sai ya saki ajiyar zuciya mai raɗaɗi alamun ciwon ya hana shi ƙarfi.
Kukansa ya ƙara karfi. Dakin ya cika da sautin kukan da ke tafasa zuciya. Nima ban iya jurewa ba, sai na fashe da kuka, zuciyata kamar za ta fashe da zafi.
A hankali, cikin murya da rauni, ya juya yana kiran Hajiyarsa
"Hajiya... danAllah ki riƙe Ramlah... ki ɓoyemin ita... ki auramun ita... hajiya ki tsaremin ita kamar rai na...!"
Hajiyarsa ta dafe kirji, kuka ya ƙwace mata. Kamar ba ita ba, ta fita daga dakin tana goge hawaye da hannunta. Ban taɓa ganinta cikin irin wannan yanayi ba.
Khalil kuwa ya shiga magana, kalmomi masu sosa zuciya, kalmomin da duk mai rai dole hawaye zai zubo masa. Ya ce:
"Ramlata... Ramlah danAllah... ki so ni... ki ƙaunace ni kamar yadda nake ƙaunarki... Kiyi min rai Ramlah... ke nake da ke... ke kadai...!"
Yayi shiru na ɗan lokaci, sannan muryarsa mai raɗaɗi ta dawo
"Wallahi ko da duniya zata ƙi ki... ko da dukan dangina zasu ki ki... ni ba zan taɓa ƙin ki ba... Ramlah... ke ce rayuwata."
Cikin rawar baki da hawaye, na dafa ƙirjina da hannuna biyu. Zuciyata kamar za ta fashe. Naji tamkar kalmominsa suna ratsani kamar ƙusa. Kuka yaƙi tsayawa a bakina, sai motsin zuciya, da dukan kirji kamar ana harbina da ƙaho.
Na buɗe baki cikin rawar murya, nace
"Khalil... ina tare da kai... wallahi bana ƙin ka. Zan tsaya maka... zan so ka... zan zama tare da kai har karshen rayuwarka… da yardar Allah!"
Yayi ajiyar zuciya mai nauyi, sannan ya runtse idanunsa. Daga gefensa, na cigaba da kallonsa ina share hawaye, zuciyata na tafasa da ƙauna da tausayinsa.
Tunda Hajiyar Khalil ta bar ɗakin, sai ta ciro wayarta tana kuka tana girgiza kai, ta kira Abba. Cikin rawar murya da raɗaɗin zuciya ta ce
“Don Allah Malam... ka dubi zumunci... ka duba yadda Khalil yake. Ka yarda ya auri Ramlah. Wallahi yaron nan zai mutu!”
Sai naji muryar Abba a gefe.
“Zan roƙe ki da ki bar wannan maganar. Na riga na zartar da hukunci babu Khalil, babu Ramlah, har abada. Ku je ku samo masa wata, amma ba ita ba!”
Sai kukan Hajiyar ya ƙara fitowa. Ta hau masifa, zuciyarta a cunkushe, tana faɗi
“Wallahi Allah, kai ba dan uwa ba ne. Ka raina zumunci. Ka manta ni ƴar uwarka ce! Abinda kayi min, Allah zai sakamin da zuriyarka. Wallahi sai ka ga sakamakon abinda kayi min, Malam!”
Anty Luba da ke gefenta sai ta karɓi wayar da sauri, tana kuka itama, tana kwantar mata da hankali
“Hajiya ki yi haƙuri, don Allah. Wannan ba kalmar da ya kamata mu faɗa ba. Yaya Malam ba haka yake ba, wataƙila zafin zuciya ne ke sa shi haka. Ki dan sauke rai hajiya...
Sai Hajiyar ta riƙe kanta da hannu biyu, hawaye na gangarowa daga idonta. Tana kallon Luba da wani irin ɓacin rai ta ce
“Luba... me zanyi? Kalli ɗana! Kalli yadda yaron da na haifa da jikina ya koma kamar mahaukaci saboda wata yarinya. Wallahi ko zan rasu sai Ramlah ta zama matarsa. dole sai da waliyyi? To, na riga na mallake auren nan!”**
Ta fashe da wani irin kuka mai tsanani, tana girgiza kai, kamar wacce ta rasa komai a rayuwa.
Luba ta matsa kusa da ita tana shafa bayanta tana cewa
“Ki kwantar da hankali hajiya. Komai zaiyi sauki Muna tare da ke. Allah zai kawo sauƙi.”
Bayan wasu 'yan mintuna, sai ga nurse ta shigo. Tayi masa allura, tana kallonsa da tausayawa. Anty Luba ta juya ta kalleni da murmushin tausayi a fuskarta tace
“Ramlah, tashi mu tafi gida. Kalli fa, har takwas ya wuce.”
Na zuba mata ido cikin shiru, zuciyata na wani irin karyewa. Na kalli Khalil dake kwance kamar wanda ba rai a jikinsa, sai hawaye suka gangaro saman fuskata. Cikin murya mai rauni nace
"Anty Luba... dan Allah, ki barni na kwana da shi. Zuciyata babu dadi wallahi. Idan yafarka bai ganni ba, zai kara shiga damuwa.”
Hajiya ma ta saka baki, tana share hawayenta tace
“Luba, ki bar ta dai. Tana da gaskiya. Zuciyar yaron nan tana a hannun yarinyar nan.”
Sai Anty Luba ta girgiza kai, tace
“Ramlatu, kinason ki jawo min masifa ne? Kinsan abbanki da yaji haka zai iya kulleni... ki rufamun rufamun asiri... don Allah muje.”
Na juya na kalli Anty Luba cike da kuka, hawaye na gangarowa kamar ruwan sama. Na riƙe hannunta nace
“Anty... zuciyata zafi takeyi. Wallahi bazan iya tafiya ba. Ki barni anan... ko abban kuwa yankani zai yi, zan dauka.”
Ta zubamin ido, idonta cike da damuwa. Ta fita daga ɗakin ba tare da ta ce komai ba. Na zauna gefe ina kallon fuskarsa, ina hawaye.
Bayan ƴan mintuna sai ta dawo, murmushi a gefen leɓenta, tace
“Ramlatu... ki taimaka ki tashi muje. Gobe sai ki dawo. Abbanki ma ya kira, yace ina diyarsa?”
Sai na fashe da kuka sosai, nace
“Anty... bazan je ba. Wallahi bazan iya barin shi haka ba...”
Dakyar... dakyar na miƙe, na fito daga ɗakin ina jiyo zuciyata na fasa kamar za ta ɓalle. Cikin kuka da ciwon rai na fice daga asibitin.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA TALATIN DA SHIDA
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
A cikin dare mai sanyi da kwanciyar hankali, jirgin Turkish Airlines ya sauka a Istanbul Airport (IST) daya daga cikin mafi girma da ƙayatarwa a duniya. Fitilun filin jirgin na walkiya kamar taurari a sararin samaniya, yayin da fasinjoji ke fita da gajiya da annashuwa bayan doguwar tafiya.
Ayshatu ta fito daga cikin jirgi cikin pajamas na silk mai launin baby blue, wanda ke lullube jikinta da annuri. Gashinta yana ta lilo, tafiyarta cike da natsuwa da ɗokin ganin Habibie. A hannunta akwai LV rolling suitcase, kuma fuskarta na ɗauke da kwalliya mai laushi, kamar wacce bata yi kokarin yin ado ba.
A wajen karɓar fasinjoji, wani customized black Range Rover Vogue Autobiography ya tsaya a VIP entrance na airport din, gaban masaukin ‘yan kwangila da masu tsananin kudi. Direban cikin uniform na musamman ya fito da hanzari, ya bude ƙofar baya.
As’ad yafito fito cikin white linen shirt, Zara jeans da Tom Ford shades. Cikakken kamshin Creed Aventus yana ratsawa da iska. Ya tsaya yana jiran zuwanta da irin murmushin da ke narkar da zuciya wanda idan ya sauka a zuciyar mace, yana canza mata tunani gaba ɗaya.
Da ta iso, ta kalli shi sai da zuciyarta tayi wani sanyi Kamar yadda aka saba, ya mika mata hannu, cikin natsuwa. Ta kama hannunsa, ta dan yi murmushi cikin kwarewar mace mai so.
“You look tired, Aysha,” ya ce da laushin murya, suna nufar motar.
Ta dan lumshe ido, sai ta ce da sautin da ba kowa ke jin irinsa ba:
“No, Habibie… indai ina tare da kai, I don't feel tired at all.”
Yayi dariya kadan, yana matsa hannunta cikin nasa. Sun shiga motar a hankali, sai direba ya rufe ƙofa, sannan suka tashi cikin natsuwa daga filin jirgi, hanyar su zuwa cikin zuciyar garin Istanbul.
A cikin motar, music mai laushi na Lo-fi chill + Turkish oud fusion yana tashi. AC na busar da iska mai ɗauke da ƙamshi irin na masculine leather da vanilla. Ayshatu ta jingina da kafadarsa, tana shakar ƙamshinsa kamar wacce ke neman shakar salama daga duniya.
As’ad ya juyo ya kalleta. “Do you know you’re the most beautiful thing that ever happened to me?”
Ta murmusa, ba tare da juyowa ba, ta ce: “I do. Because you remind me every day.”
Motar Range Rover ta doshi cikin layin bakin teku na Beşiktaş, inda fitilun tituna ke haskakawa cikin salo. A gefe ɗaya, ruwa ne mai sanyi na Bosphorus yana kadawa a hankali, tamkar yana maraba da zuwansu.
A gaban wani katafaren gini da ke haskaka kamar zinariya cikin duhu, motar ta tsaya. Wannan ba wani gini bane face Çırağan Palace Kempinski, tsohon fadar sarki da aka sauya zuwa hotel ɗin da masu kudin duniya ke sauka. Ginin yana d'auke da ginshiƙai na marmara, balconies masu zane irin na Ottoman, da lambuna masu cike da flowers na exotic species.
Direban ya zagayo cikin hanzari, ya buɗe ƙofar. Asad ya fito da nutsuwa cikakken crown prince. Ayshatu ta fito bayan sa, rolling suitcase ɗinta na taka tiles ɗin da suka fi zinariya kyau. Da zarar suka fito, wasu staff biyu cikin uniform ɗin hotel ɗin suka rusuna da murmushi.
"Welcome to Çırağan Palace, Mr. and Mrs. Kamilu. Your Imperial Suite is prepared and waiting."
Ayshatu ta kalli Habibie da murmushi. Sai ya kama hannunta, suka nufi cikin hotel din.Fuskarta na dauke da jin daɗi da shauƙi ba wai saboda girman hotel ba, amma saboda wanda take tare da shi.
Reception na cikin wani babban gini mai chandeliers da ke sheƙi kamar lu'u-lu'u, da carpet mai launin zinariya. A bango akwai zane-zanen Ottoman da ke bayyana tarihi da girman kai. Ma'aikaciya ta miƙa musu cold towel da fresh mint drink.
Elevator ya ɗauke su zuwa saman ginin Imperial Bosphorus Suite. A lokacin da ƙofar dakin ta buɗu, idanun Ayshatu suka cika da mamaki da bege.
Gadon king size ne, da zanen satin ja da gold. Daga cikin dakin akwai glass wall da ke fuskantar ruwan Bosphorus, wanda ke yawo kamar zinariya mai motsi. A gefe ɗaya kuma, jacuzzi ce cikin dan karamin bangon.
Ta bude akwatinta cikin kwarewa, ta fitar da kayan tsafta da kuma towel ɗinsa. Shi kuma yana kallonta kamar zai ci gaba da kallon ta har abada. Tana motsi da salo, tana fitar da sleeping dress dinta net ne, mai launin purple da lace na musamman.
Ta juya, ta kalleshi cikin ido, sannan da murmushi mai salo ta ce:
“Habibie… can we?”
Ya matso kusa da ita, yana murmushi da raɗaɗin murya
“Why not? You’re my only peace in this crazy world.”