Kenza eBookz

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 2

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 2

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 2: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 2. Mumy ta matso kusa da shi da sauri, cikin…

3,359 words

Mumy ta matso kusa da shi da sauri, cikin hikimar kissa tace masa:

"Abban Ramlah, ka yi hakuri da ita, yarinya ce fa. Ko da yake ni ban ji daɗin maganarta ba, amma kasan dole mu riƙa yi mata haƙuri. Amma da ka bari idan ta dawo sai ka yi mata nasiha a hankali, kada zuciyarka ta ɓaci sosai, ni kaina na san ba halinta ba ne."

Abba ya ja tsaki yana girgiza kai cikin takaici, zuciyarsa cike da ɓacin rai. "Zan nuna mata wannan halin ba zai yiwu ba a gidana. Ina ƙoƙarin ganin komai yana tafiya daidai, amma ita kuma sai ta ce ba zata iya aikin ba. Wani irin abu ne wannan?"

Mumy tana tsaye tana murmushi a zuciyarta, ta san cewa wannan labarin da ta kirkira zai ɗora min aiki da yawa da kuma faɗa. Amma daga waje ta cigaba da nuna kamar tana tausaya mini tana kare min martaba.

Ni kuwa ina can a makaranta ban san cewa akwai wani babban matsala da ke jirana a gida ba.

Na dawo daga makaranta cike da farin ciki, babu abin da ke raina sai in je gida in huta. Ban san cewa wani babban abin mamaki ne yake jirana ba a gidan yau.

Ina shigowa cikin gidan na tarar da Abba tsaye a falon gidanmu, fuskar nan tasa babu walwala ko kaɗan. Nan take gabana ya faɗi, zuciyata kuma ta fara bugawa da sauri.

"Sannu da gida Abba," na faɗa cikin sanyin murya, amma kafin in gama gaisuwar ya ɗaga min hannu cikin ɓacin rai ya ce,

"Ramlah, wannan wani irin halin banza kika ɗauko ne wai? Yaushe kika girma har zaki ce kin gaji da aikin gida? Shi aikin gidan nan wani nauyi ne a gare ki har ba zaki iya ba?"

Na ji numfashina ya ɗauke, kalmomin nan sun shige ni sosai. Na dubi gefena sai na ga Mumy tsaye tana nuna kamar tana tausayina, har tana riƙe da kafadata.

"Abban Ramlah, ka yi hakuri mana, yarinyar nan fa ƙarama ce. Ba zata iya komai ita kaɗai ba," Mumy tace cikin murya mai sanyi kamar mai tausayawa.

"Ban yarda ba! Ai wannan raini ne da rashin tarbiyya. Wani aikin ne ma Ramlah take da shi sai karatu da aikin gidan nan? To, wallahi ki gyara halinki. Ba zan lamunci wannan halin ba a cikin gidana!" Abba ya sake faɗa cikin muryar faɗa.

Hawaye suka fara zubowa daga idona, na kasa magana. Ina ji a raina cewa Mumy ce ta tsara wannan ƙarya domin ta ɗora min aiki da yawa.

A wannan lokacin ne sai ga babban yayana, Abbas ya shigo gidan yana sallama.

"Assalamu alaikum! Me ke faruwa ne, Abba?" Abbas ya tambaya cikin damuwa ganin yadda Abba ya fusata, ni kuma ina kuka.

"Abbas, duba wannan yarinyar taka! Wai tace ta gaji da aikin gida, ba zata iya ba," Abba ya sake maimaita maganar cikin ɓacin rai.

Abbas ya matso kusa da ni cikin tausayawa, ya ɗaura hannunsa akan kafadata yana cewa,

"Abba ka yi hakuri. Ai Ramlah ƙarama ce sosai, wannan aikin gidan gaskiya yayi mata yawa. Mumy, ki nema mata wata mai aiki mana, ina auta ina wannan aikin mai yawa haka?"

Nan take Mumy ta girgiza kai cikin ƙissa tace,

"Ai wallahi Abbas na bada cigiyar mai aiki sosai, amma har yanzu ba a samu ba. Kuma Baba Zuwaira ba ta da lafiya ne shiyasa ta daina zuwa yanzu."

Abbas ya dubi Abba cikin nutsuwa yace,

"Abba ka yi hakuri da ita. Ka daina yi mata faɗa haka. Ni da kaina zan taimaka a nema wata mai aiki daga yanzu. Ki yi hakuri Ramlah, kin ji?"

Ya ɗan bubbuga kafadata cikin rarrashi, nan take naji zuciyata ta ɗan yi sanyi kaɗan. Na ji kamar na samu wanda zai kare ni a wannan lokacin da babu mai jin ƙorafina.

Na share hawayena a hankali, ina godewa Allah da ya bani yaya mai tausayi kamar Abbas.

Ina tsaye, hawaye na bin fuskata a hankali, zuciyata cike da baƙin ciki da takaici. Sai kawai naji Abba ya yi min wata irin tsawa mai tsoratarwa da girgiza zuciyata.

"Ke Ramlah! Ki hanzarta ki cire uniform ɗinki yanzu ki gyara gidan nan tass! Idan da mahaifiyarki ce da rai ai nasan ba za ta taɓa barin gidanta haka ba!"

Wannan kalma ta shiga cikin zuciyata har ta ƙona ni. Numfashina ya ɗauke na tsaya cak kamar an dasa ni a wurin. Amma kafin in ce komai, Yaya Abbas ya yi sauri ya tare shi yana cewa,

"Haba Abba! Wannan magana tayi tsauri. Ka yi mata faɗa, amma ba haka ba."

Mumy ta yi saurin katse zancen da ta ga yana neman rikicewa tace,

"Tsakani da Allah, Abban Ramlah, menene ma dalilin wannan magana? Ai Ramlah cikakkiyar 'yata ce. Kowa ya san haka, kuma tana ƙoƙarin iyawarta."

Ni dai ban iya cewa komai ba. Cikin sanyin jiki na juya na fita zuwa ɗakina, na cire uniform ɗina na sanya wata tsohuwar riga. Sai na ɗauki bokiti da abin goge-goge na fara aikin share gidan.

Wallahi idan kuka ga yadda kicin ɗinmu ya koma sai kun tausayamin. Amma haka na dage ina sharewa, ina wankewa, har na tabbatar ko'ina yayi fes kamar yadda nake so kullum. Na yi wannan aikin cikin gajiya da damuwa.

Ina gamawa wata irin yunwa ce ta bugi cikina. Na nufi wajen dining, amma da na isa sai na tarar babu abinci kwata-kwata. Nan da nan zuciyata ta sake cika da takaici. Na koma sama wajen Mumy domin na yi mata sannu da hutawa.

"Mumy, sannu da hutawa. Don Allah ina abincina?" Na tambayeta cikin sanyin murya.

Tace min, "Ban duba dining ba ne? Ai na aje abincin can."

Na ce mata, "Babu komai a dining, Mumy."

Sai tayi murmushi kadan tace, "Oh, Abbas kenan! Ashe ya kwashe duk abincin nan, ban sani ba wallahi."

A cikin ranta kuwa daman ta san cewa babu abin da ta bar min, kuma ta riga ta yanke shawarar cewa ba zan ci ba.

Sai kawai ta sake ce min, "Amma bari na dafa miki indomie ko taliyar da kike so."

Abba wanda ke gefe yana sauraronmu, sai ya dubi Mumy da faɗa yace, "Ita ba za ta dafa ba sai ke uwarta?

Ina jin wannan kalma daga bakin Abba, zuciyata ta ƙara cika da baƙin ciki. Na koma kicin a hankali, amma da na shiga ciki sai kawai na fashe da kuka mai tsanani. Kuka na takaici, kuka na rashin uwa, kuka na rashin gata.

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA UKU

A cikin wani katafaren gida da ke tsakiyar babban birni, gidan da gini guda ya fi kwatankwacin wani ƙauye, wani mutum ne ya fito daga cikin toilet ɗinsa na alfarma. Bango na marmara ne mai sheƙi, bene na zinariya da fari mai haske, tagogi na gilashi masu ɗaukar hasken rana, da madubai masu bayyana komai da kyan gani.

Shi ne As’ad Babangida, ɗan sarkin Zubairu. Mutum ne mai kamala da mazantaka, cikakken jarumi mai ƙasaita. Shekarunsa kusan hamsin a duniya, amma kyawunsa da lafiyarsa na jikin samari ne. Jikinsa yana da lura da kulawa, fatarsa na sheƙi, ga murya mai ɗaukar hankali, da tabbas a cikin tafiyarsa.

A lokacin da ya fito daga wanka yana ta share fuska da tawul ɗin fata mai launin zinariya, mutum na iya gane cewa wannan bawan Allah ya taso a cikin ni’ima da arziki. Daga nan ya nufi babban ɗakinsa na kaya, wanda ke cike da rigunan Alƙebulan da turaren Dubai, agogo masu daraja, da takalma daga turai.

Ya zura jalabiyya mai nauyin zinariya, sannan ya ɗauki wayarsa mai tsada daga saman table din katako na Itacen India. Wayar ta haska logon kamfanin sa na SILIFAS Group, kamfani da ke sarrafa kayan ado, gidajen alfarma da ƙera turaren maza.

Kamfanin Silifas ɗin nasa yana daya daga cikin manyan kamfanoni da ke jan hankalin masu kuɗi a fadin ƙasar. Duk wani namiji da ya ƙoshi, to ya san turaren Silifas. Ya kuma san cewa daga hannu ko albarkacin As’ad Babangida ne – mutum mai kima, mai iyaka da daraja.

Ya tafi ya zauna a babban kujerar falo, inda masu taimakonsa suka shigo da takardu da wayoyi da zai duba. Ya duba agogo.

Hadimansa biyu suka shigo cikin natsuwa, kowanne sanye da shadda da rawani, suka durƙusa da girmamawa.

"Ranka ya daɗe, kamfanin silifas ɗinka na Legas sun ce sun kammala sabbin kaya da kake jiran shigo da su," in ji ɗaya daga cikinsu.

As’ad ya ɗaga hannu alamar ya fahimta, ba sai ya ce komai ba. A wajen As’ad, magana ba sai mai yawa ba isa na ciki ne, da kallo da numfashi.

Ya ɗauki wayarsa mai lamba biyu ta musamman, wanda aka tsara da suna "AB-Exclusive", wata nau'in waya ce da ake yiwa mutane 'yan takama.

Yana dubawa, ya ga sakon daga kamfanin mai mai a Sokoto, suna neman haɗin gwiwa da wani daga cikin kamfanonin gine-gine mallakinsa – AB Construction & Prestige Estate.

As’ad ya lumshe ido. Wannan ba sabon abu bane a gare shi. Ko da yake ya gaji dukiya daga mahaifinsa, shi ya ninka ta sau goma bisa gogewa kasuwanci.

Bayan ya gama karanta saƙon, sai ya miƙe tsaye. Jikinsa yana sheƙi da lafiya, da karfi. Kallon da zaka masa ya isa ka fahimci cewa yana daga cikin manyan mutanen da kasa kiji dasu.

ƙofar babban falo, wani dattijo mai murya da ɗan kaifi yana jira shi.

"Ranka ya daɗe, Masarautar Rano sun ce za su zo gobe da safe neman haɗin gwiwa akan gina sabuwar cibiyar kasuwanci da banki a yankin su."

As’ad ya tsaya, ya ɗan lumshe ido sannan ya ce da muryarsa mai sanyi amma mai ɗauke da izza

"Ku amsa musu. Ku shirya tsare-tsaren da ya dace. In na ce zan shiga abu, to tilas ya ɗauki martaba."

Dattijon ya rusuna, ya amsa da “To, ranka ya daɗe,” sannan ya juya da sauri.

Bayan As’ad Babangida ya kammala ganawa da masu shigowa , sai ga Sarauniyar gidan Hajiya Aisha ta bayyana cikin natsuwa da kamun kai. Ta shigo da sallama mai nauyin izza, wadda ta cika dakin da kwarjini. A jikinta ado ne na sarauta, tufafi masu kyan gani, da turare mai ɗaukar zuciya. Kallon da ta masa ya bayyana girmamawa da kauna, kirarin da ta kwarara kuwa sai da ya sa zuciyarsa ta narke.

Shi kuwa yana zaune a babban kujerarsa da kamanni irin na manyan maza. Ya kalleta yana murmushi mai nauyi, wanda ba kowa ke samu ba. Hannunsa ya daga a alamar izini, ya nuna mata kujera kusa da shi.

Ta ƙaraso kamar sarauniya, ta zauna da girmamawa, ta ɗan latsa ƙasa da tafin hannunta kafin ta furta da nutsuwa

“Ranka ya daɗe, dama ina so in ji batun tafiyarmu gobe. Yaran sun ce har yanzu baka basu amsa ba.”

As’ad ya ɗan yi shiru, yana kallon gabansa, kamar mai tunanin manyan al’amura. Daga bisani ya ce cikin murya mai ƙarfi da nutsuwa

“Akwai tafiya.”

Aisha ta saki addu’ar albarka a gare shi, da harshen mace mai sanin girman mijinta. Ta ce

“Dama Bilkisu ce zata je gida gobe. Nace mata ta jira, mu tafi tare. Tana son ganawa da iyayenta.”

Ya ɗan jinjina kai cikin karfin hali, ya ce

“Tashirya. Da safe zan shiga garin, in ga mai martaba. Sai mu tafi tare.”

Ta sunkuyar da kai cikin girmamawa, ta ce

“Na gode, ranka ya daɗe.”

Ta miƙe da kyau, ta fita.

Shekaru kusan 45 kenan da As’ad Babangida yake cikin aure. Matar sa ta farko ta rasu tun da wuri, ta bar masa ɗa guda ɗaya mai suna Umar. Umar yanzu gaba ɗaya rayuwarsa yana yi ne a Dubai tare da iyalansa. Yana da kyau, yana da natsuwa, amma ya fi son zaman can fiye da dawowa gida.

Bayan mutuwar matarsa ta farko, As’ad ya sake aure. Wannan matar kuwa ita ce Hajiya Aisha, mace kyakkyawa, mai aji, da nutsuwa. Yanzu haka tana da shekaru 37 a duniya, kuma tana da yara guda uku ‘yan mata biyu. Daya daga cikin ‘yan matan ta rigaya an daura mata aure. Ita kuma ɗayar tana nan a gabanta, suna kiranta da Nawal.

Nawal yarinya ce ta musamman sangartacciya ce da gata. Kyawu, tarbiyya da jin daɗin rayuwa duk suna tare da ita. Kusan ba ka fiye ganinta a Najeriya ba, saboda tana cika zama ne a Dubai tare da yayanta Can ne ta fi so, can ne ke faranta mata rai.

Hajiya Aisha, matar As’ad ta biyu, ce uwar gida. Ita ce mace mai hankali, mai cike da izza da daraja. Yar gayu ce ta gaske, wadda duk ta shiga za ka girmama ta. Bayan aurenta, As’ad ya sake auren wasu mata har guda biyar, amma abun mamaki babu ko ɗaya da ta taɓa haihuwa.

Ba sa jure zama da shi. Yana yiwuwa su zauna wata shida ko shekara daya, sai kowacce da kanta ta nemi saki. Wannan lamari ne da ya ba kowa mamaki, har ya sa As’ad ya fasa neman karin aure, duk da cewa zuciyarsa na da buƙata.

Wata rana yarinyar da ya aura a ƙarshe mai suna Maryam, ta zauna da shi, ta ce

"Ka ji tsoron ɗaukar hakkin yaran da ba su ji ba, ba su gani ba. Dan Allah ka zauna da matarka…"

Kafin ma ta gama, maganar ta tsaya masa a zuciya. Wannan kalma ɗaya ta sauya masa tunani. Ya fasa tunanin karin aure gaba ɗaya.

Sai dai har yanzu babu wanda ya gane dalilin da yasa ba matarsa ɗaya da ta daɗe da shi. Wasu na cewa halinsa ne mutum ne mai ra’ayin kansa da tsaurin hali. Ko da yake, mutum ne mai ibada da addu’a sosai, amma idan ya ce abu, sai Allah ne kaɗai zai iya sa ya canza.

Aisha kuwa, duk da cewar ta fi kowacce mace samun daraja a gidan, akwai abu ɗaya da ta kasa samu daga As’ad mulkinsa. Duk yadda ta ƙoƙarta ta mallake shi, ta janyo hankalinsa, ko da ta hanyar ƙauna ne ko magana mai taushi, As’ad bai sauka a karkashinta ba.

Sai dai ita Hajiya Aisha ta san inda zata taka. Ta san yadda ake tafiyar da namiji mai taurin kai. Da hankali da haƙuri, da kishi, da maganar mace mai wayo, ta kasance ita ke riƙe da gidan da komai ke gudana kamar yadda take so.

Rayuwar cikin gidan As’ad Babangida cike take da sirrika da ruɗani, amma a tsakiyarta, ita ce ta fi kowa shahara. Ita ce matar da ta fi iya jure halinsa. Ita ce ginshiƙin gidan.

Daga babban shashen mijinta, Hajiya Aisha ta nufi nata sashen wani ɓangare na gidan da ke nuna sarauta da jin daɗin rayuwa. Falo ne mai girma, cike da kayan alatu daga ƙasashen waje, fitilun gilashi suna haskawa cikin shudi da zinariya, sannu a hankali AC ke busar iska mai ɗanɗano da ɗumi.

Ta shigo tana tafiya da kwarjini kamar sarauniyar gida, sai kamshin turarenta ya cika wajen. Ta tarar da Nawal zaune a kan kujera tana danna wayarta, ana mata tausa da mai ruwan sanyi. Daga gefenta kuma Bilkisu ke kallo – Korean film ke tashi a giant screen ɗin plasma TV, wanda ke manne da bangon da aka lulluɓe da fatun fata.

Ta tsaya tana kallonsu, sannan da muryarta mai natsuwa da iko ta ce

“Bilkisu, ki shirya. Inji Habibie, gobe da safe zai shiga garin, zai tafi dake.”

Bilkisu ta kalleta cikin girmamawa, sannan ta ce

“To, mamah.”

Nawal kuwa ta ɗan turo baki, ta kalli ‘yar uwarta da ƙuruciyar shagwaɓa.

“Yanzu sis, kina nufin ba zaki bimu ba? Please mana…”

Bilkisu ta ɗan murmusa, ta ce cikin taushi

“Ki yi haƙuri sis, next time. I really want to see my parents.”

Hajiya Aisha dai ba ta ce komai ba. Sai zuciyarta ta ji wata ɗigon bakin ciki, musamman da jin cewa Habibie zai tafi tare da Bilkisu. Anya kuwa zata fasa tafiyarta ta Paris da ta shirya makonni? Sai kuma ta sake ta. Wata dariya ta suɓuce mata tana fadin cikin zuciya:

“Itama ai ba zata fara ba. Tasan wacece ni.”

Ta juya da fara’arta mai ɗaukar hankali, ta bar su cikin dakin, sai kamshin turarenta da sautin takalminta suka rage.

Bayan ta bar falon da 'ya'yan suke, Hajiya Aisha ta shiga ɗaya daga cikin dakunan nata na sirri wuri ne na musamman da ba kowa ke da damar shiga ba. Daki ne mai fadi, an kawata shi da madubai masu haske, fitilun kwali, da kwalabe masu launi na kayan mata daga ƙasashen waje.

Ta nufi wajen da take ajiye kayan mata na gyaran jiki, tsumi, turare da hadin gargajiya. Tana tafiya a hankali, tana tsiyaya a zuciyarta. Daya daga cikin kwanukan matsinta ta ɗauko, ta dora shi gabanta a kan faifan , sannan ta zauna, ta kwantar da hankalinta.

Cikin nutsuwa da kwarewa, ta shiga shan hadin tsumi, tana shafawa jikinta da tsari da salo irin na mata masu gata. Wannan ba shan kaya bane, wannan kula da martaba ce.

Tana kallon fuskarta a madubi, ta dan yi ajiyar zuciya. Bata jin dadin yadda take mu'amala da Habibie kwanan nan. Ko da yake tana da daraja a idanunsa, amma yana yawan kau da kai daga kusa da ita. Tana jin magungunan da take amfani da su, da hadin da take turawa jikinta, kamar suna ƙara nisantar da shi ba tare da dalili ba.

Shin ko ya gaji da ni? Ko akwai wata can da ke jawo masa hankali? Zuciyarta ta tambaya, amma ta goge tambayar da murmushin mace mai karfin zuciya. Ta dora turaren kwalliya a gefe, ta furta a hankali

“Ba zan ja da wata ba, sai dai ta gaji da kallo. Ni ƙadaice matarsa.”

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA HUDU

Idan zan gaya muku irin wahalar da nasha cikin ‘yan kwanakin nan, wallahi sai kun tausaya min. Aiki ne kawai nake yi babu hutu.

Gashi kuma momy ta sanar da yaya Abbas cewa kada ya kawo yar aiki. Ta ce wai ta bayar da cigiyar mai aiki.. Na sani, ba da gaske take ba.

Abin mamaki kuwa, duk sanda na dawo daga makaranta sai in tarar da gidan a hargitse. Da fari na dauka ko baƙi ke zuwa, amma daga baya na gane da gangan ake ɓata gidan domin in gyara.

Momy ta canza. A da kulawa da ƙauna take nuna min. Amma yanzu sai ta taga Abba kafin ta nunamun kaunar. Hakan yana cutar da ni sosai, amma bana cewa komai. Sai zuciyata ke kuka.

Duk rana da na dawo daga boko, zan fara gyaran gida. Bayan haka in dafa girki, in fita islamiya. Da daddare bayan magariba nake dawowa gida. Duk da gajiya, sai na hau wanke-wanke da sauran ayyukan da ba za a rasa ba.

Ina tuna lokacin da momy ke cike da ƙauna a kaina. Tana sona kamar ni kaɗai nake da ita a duniya. Amma yanzu? Idan na ga yadda take wulakantani, sai hawaye ya cika min ido. Na sha kuka a sirrance cikin makon nan.

Wata rana na dawo daga makaranta, na same ta a falo. Na tunkare ta a hankali nace, “Momy turarena ya kare, jikina ma ya soma wari...”

Sai kawai ta juya ta ce, “Ai ke yanzu kina ɗaukar kanki sa’ar kowa ko? Ga ki kwaila ce amma kina jin kanki kamar cikakkiyar budurwa.”

Kamar an zuba min ruwan sanyi haka na tsaya. Na kasa motsi. Na shiga shock. Duk da haka, na saki baki nace, “Ki yafe min idan nayi kuskure.” Na koma dakina cikin ɗaci.

Washegari kuwa abincin dare aka ci, amma ba a kirani ba. Na yi shiru, har na je na ce mata“Momy ba a kirani ba...”

Ta kalle ni da wani irin kallo tace, “Ke ai kin san kitchen din. Koni zan girka miki?”

Na durƙusa na bata hakuri. Na ce ko laifi nayi mata, ta yafe min. Amma sai ta wuce gona da iri, ta juyo tace

“Ki kama kanki a nan gidan! Gidan mijina ne, ba naki ba. Kuma idan kika ce zaki yi min magana gaban Abba, sai na saɓa miki da gangan.”

Yanzu haka muna tsakiyar jarrabawa a makaranta. Allah ne shaida, kawai rubutu nake yi, ba don nayi karantu sosai ba. Yaushe zan samu lokacin karatu ne, jikina gaba ɗaya gajiya ne gajiya da bautar Momee.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull