Kenza eBookz

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 3

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 3

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 3: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 3. Da ace tana da sauƙin kai , da ba za ta bar…

3,360 words

Da ace tana da sauƙin kai , da ba za ta bar ni ba har na zama mai wanke mata pant da bra dinta da kaina. Amma yanzu kuma sai naji wai tana gaya wa Abba cewa ciwon hannu ne ke hana ta wankewa. Ashe dai ni ce zan ci gaba da wanke mata komai.

A wannan satin, sai gashi naji Mumy na waya da Yaya Billy. Har kusan makonni biyu kenan ba ta dawo gida ba. Da farko ban san dalili ba, sai dai da safe sai naji Mumy tana cewa a waya

"Ai Dady As’ad ne ya ɗaga tafiyar, sai gobe zasuzo tare.”

Mumy tana ƙarfafa ya Billy

"Ki dai ci kwalliya sosai. Ki cakare, kin ji?"

Araina nace, ai ba sai an faɗa wa Yaya Billy tayi kwalliya ba. Ko yaushe haka take kamar aljana wadda bata taba gajiya ba. Shafe-shafen fuska da hoda,jambaki.

Amma fa, bana fahimtar dalilin da ya sa Mumy take hura mata wuta haka – sai na kauda kai, na cigaba da sabgogina. Allah ne kaɗai yasan bana jin daɗin jin zata dawo. Wallahi har cikin raina bana sha’awar ganin ta koma cikin gidan nan.

Na san idan ta dawo, azaba ce zata karu gareni. Na yi shekaru ina mata aiki kamar yar aikinta daga ɗebo mata ruwa, share daki, gyara kayanta, hatta jakar kwalliyarta idan ta fita, ni ke ɗauka. A gabanta, bani da wani daraja, kuma ba abinda nake yi ya gamsar da ita. Amma fa duk da wannan halin nata komai auta komai auta.

Yau Juma’a. Saboda haka, da wuri muka tashi daga makaranta, kuma bamu da islamiyya. Tun safe na tashi na gyara gidan, na shirya cikin kayan makaranta. Na je na gaida Abba, ya amsa da murmushi yana addu’a kamar yadda kullum yake yi. Bayan ya kare nasiha, na ɗauki jakata muka huce makaranta.

Kasancewar jarabawa muke yi, da zaran mun shiga ajin ake farawa. Bayan mun gama, muka fita waje. Kawayena suka fara hira kala-kala. A yawanci zancen samari suke yi ni dai shiru nake.

Sai Fatima, kawata, ta matsa kusa dani tana dariya. Tana riƙe da wani kwali. Tana cewa, “Kalli wannan.” Na kalle shi an rubuta a jikin kwalin Dwell Weight Gain Capsule. Na ɗago mata kai da tambaya a idona.

Sai tace, “Jiya nasiya. Magani ne na ƙara kiba. Ramlah, kema ki karɓa ki fara sha. Bakiga yanmatan ajin nan ba? Kowacce da nonowa da hips. Suna yi mana wani irin gayu. Amma mu kamar muciya...”

Na yi dariya, amma zuciyata cike da tunani. Gaskiya ne, ramar nan ta dameni sosai. Ina son in ga jiki na ya ɗan cika. Ko dan in daina zama abin dariya a idon wasu.

Na karɓa daga hannunta, ina tambayarta yadda ake sha. Ta bani bayani da fara’a. Na ji daɗi sosai. Na saka a jakata, muka tashi muka kama hanyar gida.

Kwana uku kenan da na fara shan maganin ƙara kiba. Babu wanda ya sani a gida. Ko Fatima da ta bani maganin, bata tambaye ni ko na fara ba. Na yanke shawarar sai na fara ganin canji a jikina tukunna zan sanar da'ita.

A cikin waɗannan kwanaki uku, abinda na fi lura da shi shi ne yadda yunwa ta ƙi barina. Kullum cikin ci nake. Da safe, da rana, da dare sai na ci abinci kamar jaka.

Har ita kanta momy ta fara zargina.

Ranar Laraba da rana, bayan na ci shinkafa da miya da gasasshen kifi, na ɗauki garin kunu da aka rage jiya, na zuba a kofi, na zuba sugar sosai, na sha gaba ɗaya. Sai na tashi na ɗauko biskit guda biyu na ci.

Momy tana zaune a falo tana kallon labarai. Ta kalleni da mamaki, tace

“Ramlah lafiya kuwa? Kwana uku kenan kina ta cin abinci kamar wadda ake tura. Ko mai sabon ciki ?”

Na ɗan yi dariya da ƙyar nace

“A’a momy, kawai yunwa ce fa. Nima ban san me yake damuna ba, amma ina jin ci kawai.”

Ta zuba min ido kamar tana nazarina. Amma ta kame. Sai tace

“Kar ki je kina janyo ciwon ciki da kanki fa.”

Na girgiza kai kawai, na bar falon. A zuciyata nace:Da sun san me ke faruwa da ni... ai da za su tsaya mamaki.

Kuma duk da yunwar da nake ji da abincin da nake ci, har yanzu bana jin canji sosai. Amma zuciyata cike take da fatan Ko da zai ɗauki sati biyu, in dai zan cika kamar sauran ‘yan mata, ni wallahi zan dage.

Na lula sosai gurin shan maganin. Kullum da safe, da dare, sai na ɗauka in sha, kamar maganin ciwon zuciya. Ranar Juma’ar nan, da na farka, na je gaban madubi sai naga fuskata ta kumbura. Kamar ba fuskata ba ce. Hankalina ya ɗan tashi, amma saboda yarinta da son ganin canji, sai kawai naji dadi.

Na matsa na kalli kirjina... ko su suma sun soma cika? Na dan bubbuga saman rigata da jin daɗi. A zuciyata nace, Yanzu dai na fara zama mace.

Sai na ɗauki maganin, na sha, na kuma sha afa ban daukeshi daga ƙan gadona ba.

Da safe na shirya cikin rigar makaranta, na je na gaida Abba. Ya dube ni sosai sannan yace

“Ramlah, lafiya fuskarki ta kumbura haka?”

Momy ma ta ɗaga kai da sauri tace, “Wai me ke damunki ne? Idan kin dawo daga makaranta zamu je asibiti.”

Na ce musu, “Ba komai, kawai yunwa ne jiya ban ci abinci da kyau ba.” Sai na yi sallama na tafi.

Ban san cewa yau ce ranar da komai zai fallasu ba.

Momy na shiga dakina don duba wani abu, sai idonta ya sauka a jikin kwalin maganin. Tayi saurin ɗagowa ta karanta. Da farko ta fara karantawa da siririyar murya, amma tana kai ƙarshe sai hawayenta suka zubo. Ta fito da maganin hannunta tana fadin

“Abba... ka duba wannan. Ka karanta ka gani da idanunka.”

Abba ya karɓa, ya karanta shiru. Bayan ‘yan dakiku sai ya kalli momy da murya mai nauyi yace

“Na wanene wannan? Waye ke shan wannan maganin?”

Momy ta share hawayenta tace, “Daga dakinta na samo. Ashe ita ce take shan shi. Ita ce take kumbura. Tana shirin janyo mana bala’i!”

Abba ya sauke ajiyar zuciya, yana girgiza kai.

Abba na zaune, kwalin maganin a hannunsa. Ya na kallon rubutun da ke jikinsa, fuskar sa cike da alamar damuwa. Momy kuwa bata bari ya gama karantawa ba, ta fara zuba kalamai:

“Abba, wallahi ban gane Ramlah yanzu ba. Kwana biyu kenan tana canzawa a idona, har na soma tsoro. Fuskar ta ta kumbura, jikinta yana sauyawa, ita kuma kamar ba ta lura da kanta ba.”

Abba ya ɗan ɗago kai da mamaki, bai ce komai ba.

“Sai abin ya taɓa lafiyarta kenan tukunna za’a dau mataki?”

Ta matso kusa da shi, ta zauna da girmamawa, amma tana kuka. Tana cewa

“Wannan maganin da na gani a dakinta fa? Idan wani abu ya faru da ita fa? Ashe ni za a ce na cutar da ita.”

Ta sake girgiza kai tana cewa, “Wannan capsule ɗin fa? Magunguna masu kara kiba ne da ke jawo cancer da cututtuka masu haɗari. Yanzu ace ita yarinya karama tana sha... kuma a gidana?”

Sai ta lumshe ido, hawaye na bin kuncinta

“Abba... da gaske nake... wallahi ni fa na rasa abin cewa. Da ace wani abu ya same ta, me za a ce? Ashe idan tayi rashin lafiya gobe, ba zan zama abin zargi ba? Kai kanka zaka iya cewa ina kallonta amma ban hanata ba Alhali bansan halin datake ciki ba.”

Abba ya shiru, ya sauke ajiyar zuciya. Sai ya ce a hankali, “Allah ya kyauta…”

Ba karamin zafi Abba ya ji ba, amma ba ya nuna komai a fili. Sai dai yana kallon Momy da kwalin maganin a hannunsa, kamar yana jiran jin karin zuga daga gare ta. Ita kuma, kamar ta jima da jiran wannan dama.

Ranar, kuwa Momy ta kama girki da kanta. Ta gyara falo, ta canza labule, ta zuba turaren wuta. Komai ta shirya kamar ba ita bace ta tayar da bala’i da safe. Abba kuma da zarar ya gama Abunda yakeyi ya fice kasuwa shiru kamar ba komai ya faru ba.

Ni kuwa a makaranta, sai wani jin daɗi nake ji a jikina. Ganin fuskata ta cika, jikina ya ɗan cika, sai naji kamar nayi nasara. Nida Fatima muna ta dariya, tana cewa

“Wallahi Ramlah, ki gani fa yanzu. In muka gama wannan kwalin, zamu sayi wani daban sai mu zama kamar ‘yan Instagram.”

Na kyaleta da dariya. A zuciyata nace “Kowa yasan me yake nema, ai da kyau ake bi ana shiga gaban mutane.”

Yayin da muka tashi daga makaranta, muka fito, muka same Malam Idi direban mota. Ya zuba min ido yace

“Auta wannan kumburin naki... anya ba sanyi baniba?”

Na fashe da dariya nace, “Ko ɗaya Malam Idi, kiba ce fa, ina jin dadin jikina yanzu.”

Shi ma ya kyalkyale da dariya yace, “Allah ya kara lafiya.”

Na dawo daga makaranta da yamma cikin gajiya, amma zuciyata cike da farinciki. Sai kallo nake yi wa jikina a madubi, ina murmushi. Na ji kamar wata sabuwar ni’ima ce ta sauka a kaina.

Na ci abinci fiye da yadda nake ci na haɗa da kek da kunun tsamiya. Bayan isha’i, na kwanta jikina cike da nauyi, amma zuciyata na motsi da daɗin canji.

Ban san lokacin da na lumshe ido na fada bacci ba. Sai kawai na ji azaba kamar wuta ta faɗo min a baya!

Wata irin zafi ce ta farka da ni daga barci!

ZAAFFF!!!

Na yi ƙara, na buɗe ido cikin firgici. Idanuwana suka sauka a kan Abba. Tsaye yake da bulala a hannu, fuskarsa ta cika da fushi.

“Ke Ramlah! Ashe guba kike sha kina boye mana?! Ashe kina neman mutuwa da kanki, a cikin gidana?”

Na ce da murya mai rawa

“Abba dan Allah… wallahi ban….”

ZAAFFF!!! ZAAFF!!! ZAAFFF!!!

Ya sake zane ni ba tare da sauraro ba. Wata bulalar ta doki gefen ƙirjina, wata ta shige min a bayana. Na zube a ƙasa ina kukan da ban taba yi ba a rayuwata.

“Sai kace ba ‘ya ba! Sai kace na samo ki daga titi! Wato kina neman kiba har da shan magungunan banza da za su kashe ki kafin ki kai shekara ashirin?!”

Na durƙusa da gwiwoyina, jikina na rawa, zuciyata kamar zata bar jikina. Na rarrafa zuwa gefe, amma kafin na isa gado sai na sake jin

ZAAFF!!!

"Abba don Allah!" Na ƙwalla. "Wallahi ban san me nake yi ba!"

Amma fushinsa bai daina ba.

"Kin girma da wauta! Kin raina ilimi da tarbiyya! Sai kin illata kanki dan uwanki?!"

Na fara haki da gumi, numfashina yana rikicewa. Har na soma jin kamar zuciyata zata tsaya.

“Wallahi yau sai kin sani,” ya ce yana rarrafe a kaina da bulala.

Na yi ta jijjiga kaina, ina kuka, ina kokarin kare jikina da hannaye. Amma bulala sai karfi take karɓa.

A can sama, a ɗakin Momy, tana jin komai. Amma shiru tayi. Maimakon ta sauko ko ta ce ya yi hakuri, sai dadi ya rufe zuciyarta. Ta ma juya gefen gado, tana cewa a ranta

“Ai sai an koya mata hankali. Tana ganin zata yi min fintinkau? Tasaka dariya.”

Ta rufe kunnen ta da bargo, ta lumshe ido da jin daɗin azabar da Ramlah ke sha.

Ni kuwa, na dawo can ƙasa cikin ɗaki, hawaye sun goge fuskar da na ji kwana uku tana cika. Jikina duk yana rawa. Zuciyata na dukan da ban taba ji ba.

Abba ya zube bulalar ƙasa a ƙarshe, yana haki kamar mai gudu. Ya dubeni da idon da bai daɗe da zafin bulala ba, amma har yanzu cike da takaici.

Abba ya tsaya bakin ƙofa, ya juyo ya kalle ni. Idonsa ya dan lafa daga fushi, amma yana dauke da alamar zafi a zuciyarsa. Ya numfasa da ƙarfi, kamar yana kokarin danne fushin da bai ƙare ba.

“Ramlah,” ya kira sunana da murya mai nauyi, “zauna ki saurare ni da kunnuwan ki biyu.”

Na gyara zama a ƙasa, jikina yana rawa, hawaye kamar ruwan sama. Amma zuciyata tana buƙatar jin kalmarsa fiye da bulala.

Abba ya tako zuwa gabana. Ya zauna a gefen gadon, yana kallona kai tsaye.

“Kiba? Kina shan guba domin ki cika jiki? Ashe hakan ya fi miki muhimmanci fiye da lafiya?”

Na durƙusa na ce da kuka

“Abba dan Allah... kayi hakuri. Wallahi na yi kuskure.”

Ya ɗan dafe kansa, ya girgiza shi, sannan yace

“Maganin da kika sha kin san yana illata hanta? Kin san yana iya lalata ƙoda? Kin san yana iya jawo ciwon da ba zaki warke ba? Kin san akwai mata da suka mutu sabodashi?”

Na sa hannuna a baki, kukan ya ƙara tashi. Abba ya dafa kafaɗata, yace

“Rayuwa ba ado ba ce kawai, Ramlah. Kyau yana da rana, amma lafiyar ki... ita ce ke da daraja fiye da komai.”

Ya cigaba cikin natsuwa

“Akwai masu kiba da basu da hankali. Akwai masu kyau da babu tarbiyya. Amma idan mace tana da ilimi, tausayi da kima ko tana da ƙiba ko a'a – kowa zai girmamata.”

Na kalle shi cikin hawaye. Na ce da murya mai rauni

“Na gane Abba. Ka yafe min. Wallahi zan daina. Zan tuba.”

Ya dafa gashina yace

“Na yafe miki, amma ki yafewa kanki. Ki zama sabuwa daga yau. Ki bar kowane abu da zai cutar da rayuwarki.”

Na rungume ƙafarsa da kuka, nace

“Na tuba Abba. Na gode. Na gode da ka tsawatar min. Allah ya saka da alheri.”

Abba ya miƙe, ya ɗauki kwalin maganin daga inda ya jefar. Yana kallonsa da haƙuri yace

“Yanzu zan zubar da wannan. Sannan gobe da safe, za mu je asibiti. A duba ki. A tabbatar komai lafiya.”

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA BIYAR

Washegari, idanuna da fuskata sun kumbura, fuskata cike da hawaye. Ina tsaye gaban madubi ina kallon kaina, zuciyata cike da nadama da tsoro. Na fashe da kuka, saboda abinda ya fi bani tsoro shine yadda aka ce maganin da na sha yana da illa.

Bayan sallar asubah, sai ga Abba ya shigo dakina. Da ya gan ni, ya tsaya na ɗan lokaci yana kallona, sannan ya juya gefe yana share hawaye.

Abba ne fa wannan! Mahaifina da nake da tabbacin yana matuƙar ƙaunata, duk da komai nayi.

"Abba, ina kwana, na ce cikin murya mai rauni."

Sai da ya ja numfashi, kamar mai ƙoƙarin hana zuciya fashewa, sannan ya ce

"Kije ki Nemi abinda zakici. Anjima kadan zamu je asibiti."

Ya faɗi haka cikin wani irin yanayi da ya cika mini zuciya da wani sabon kuka, sannan ya fice daga dakin ba tare da ya ƙara juyowa ba.

Ina kallon bayansa har ya bace, sai ga Mumy ta shigo. Ta tsaya tana kallona na dan lokaci, kiris ya rage ta kwashe da dariya saboda yadda na koma, amma sai ta daure fuska, ta sunne kanta kasa tana faɗin

"Innalillahi wa inna ilaihirraji’un! Abban Ramlah, me ka yi wa ‘yar mu haka?".

Nan take ta fashe da kuka kamar ba ita ce da can ke kokarin dariya ba.

Cikin ruɗani da rashin sanin abinda zan yi, nima na ƙara fashewa da kuka. Na ce

" Mumy, dan Allah kuyi hakuri. Wallahi bansan maganin yana da illa ba. Fatima Habib ce ta bani. Tace min in sha saboda yadda mutane ke cemin wai ni ba mace bace. Kowanne lokaci sai su ce karmashashiya ce ni. Wani lokaci suce kwaila ce ni. Wannan magana na ci mini rai sosai."

Na share hawayena da gefen zanena sannan na ƙara cewa

"A cikin aji kowa baya kulani. Sai suce wai ban da komai a jikina. Shi yasa da Fatima ta bani maganin, na sha... Dan Allah ku yafemin. Bazan ƙara ba."

Mumy ta zuba min ido kamar wacce aka tsaya da ita cak. Idanunta suka cika da hawaye, ta san Abba yana jinmu a waje, shi yasa bata ƙara ce komai ba. Ta juyo gare ni cikin tausayi da sanyin murya.

" Allah ya kare min ke, auta. Allah ya tsare ki daga cutar da za ta same ki. Kinji? Ki daina sauraron maganganun mutane. Ke kyakykyawa ce, kin fi Billy da su Abbas kyau a gidan nan. Kawai dai baki yi kama da mamarki ba sosai. Amma mamarki cikakkiyar Balarabiyar Jordan ce. Kin taba ganin yadda Mama take, kakarki?."

Na girgiza kai cikin kuka.

"To, mamarki ta fi kyau. Kuma kibar da kike so tana zuwa a hankali. Ai ke kinada jiki, ba kya kallon Billy? Ita ma tana da kiba. Ki kwanta ki huta, bari na hada miki breakfast."

Ta juyo ta fice daga dakin, ni kuma na kwanta ina jin zuciyata na sanyi.

Abba bai ce komai ba, sai kawai ya juya ya fice daga dakin. Ashe dakinsa ya wuce kai tsaye, ya zauna yana kallon bango tamkar mai nazarin wata matsala mai nauyi. Cikin nutsuwa ya ɗauki wayarsa, ya kira Yaya Usman.

Yaya Usman ɗan fari ne a gidanmu, kuma yanzu haka yana wata ƙasa yana ci gaba da karatun wani muhimmin kwas. Likita ne kwararre, cikakken masani a fannin lafiya.

Abba na ɗaukar wayar, cikin wata irin damuwa ya ce “Usman, kana lapya?”

“Lafiya lau Abba. Ya Lafiyar gida dai?”

“Ba lafia ba. Auta ta sha wani magani wai na karin kiba. Ashe kuma yana da illa.”

“Subhanallah! Ta sha da yawa ne?”

“A’a. Kamar sau ɗaya kawai. Amma yanzu muka ji wasu na cewa yana da illa.”

“To, Alhamdulillah. Idan sau ɗaya ne kawai, to babu komai insha Allah. Amma fa ku kaita asibiti a duba lafiyarta. Ka kwantar da hankali kuma ka daina fushi da ita. Gaskiya fa yaran yanzu sai addu'a da hakuri.”

Yaya Usman ya ɗan yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya ƙara da cewa

“Ka san Auta fa bata da wani laifi. Idan ka ganta da kawayenta zaka gane ita ce karama. Amma tunda ta fara zama yammata, tana jin kamar dole ne ta canza. Haka yaran zamani suke, suna son su yi girma fiye da shekarunsu.”

Abba ya dan sosa kai, yana fadin

“Au, Usman… Auta ce yammata? Yarinya shekara goma sha biyar?”

Yaya Usman ya kyalkyale da dariya.

“Haba Abba! Auta fa shekararta goma sha takwas ne. Wallahi ba sha biyar ba. Kada ka rage mata shekaru, fa! Ai ma yanzu ita ‘yar shekara sha takwas ce cikakkiya.”

Abba ya dan ɗaga gira, yana mamakin abin.

“Banson karya, Usman. Ta ina tayi sha bakwai?”

Yaya Usman ya murmusa, sannan ya ce

“To Abba, ai ko mamarta marigayiya, tafi shekaru goma sha biyar da rasuwa. Kaga kenan shekarunta sun jima suna tafiya. Ka karbi gaskiya kawai.”

A lokacin, Abba ya jinjina kai, yana murmushi cikin sigar fahimta. Sai ya dafa kansa kamar wanda ya dawo daga rudani, yana sauke ajiyar zuciya.

Yaya Usman kuwa ya ƙara kwantar masa da hankali sosai, ya tabbatar masa cewa komai zai daidaita, kuma zai taimaka wajen ganin an bi lafiyar Auta da kulawa.

Wajen ƙarfe goma na safe muka bar gida muka nufi babban asibiti da Abba. Na zauna a kusa da shi a motarsa, amma ba tare da na ce komai ba. Idanuna na kallon titi ne, zuciyata na cike da fargaba.

Bayan dan lokaci, muka isa asibiti. Likita ya karɓe ni da kulawa, ya fara duba lafiyata, sannan ya tambaye ni wasu tambayoyi masu mahimmanci. Daga karshe ya bani wani magani guda ɗaya.

Ya jingina da kujerarsa, yana fuskantata, sannan ya ce da murya mai sa nutsuwa

“ Idan da akwai maganin fitar da nono kai tsaye, da turawa su zasu fara amfani da shi. Amma wallahi, duk abin da suke yi surgery ne, kuma shima yana da matsala. Wannan shan magungunan kari ba komai bane face barazana ga lafiyar ku.”

Sai ya ci gaba da bayyana mini illolin amfani da magungunan karin kiba da na breast. Na kasa d’aga kai, sai dai na jingina da kujera ina saurare da ladabi kamar wata karamar daliba.

Ya ce da Abba “Abba, just two days ne zaki ga yarinyarka ta murmure. Kada ka damu, komai zai daidaita.”

Da muka fito daga asibiti, muna cikin mota, sai Abba ya ce “To, Auta, me kike bukata yanzu?”

Nace da sauri kamar wadda aka jima da dakile mata murya “Kayan shafawa da turarena sun ƙare.”

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull