Kenza eBookz

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 4

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 4

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 4: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 4. Abba bai ce uffan ba, sai dai ya nufi…

3,355 words

Abba bai ce uffan ba, sai dai ya nufi babban mall. Da muka isa, ya miko min ATM ɗinsa yana fadin “Sai ki sayi duk abinda kike bukata.” “Na gode sosai, Abba,” na ce, cike da farin ciki.

Na shiga cikin mall ɗin kamar wadda aka kawo talla. Na zabi kayan shafawa kala-kala, turare, mai, har da lip gloss da alawa. Na fito da ledodi har uku kamar wata amarya.

Da muka dawo gida kuwa, Mumy na ganina da kayan sai ta cewa Abba “ mai isa yakaini? Me amfaninta wai? Ai da ita sai takaini” Na dan kalli yadda take harara, sai kawai na wuce cikin dariya a zuciyata. "Ai ba ke nagaya ma bukatata ba, bayan wulakancida kikayimun rannan.”

******

Tsaye yake a tsakiyar babban bandakinsa wani katafaren wuri mai ɗaukar hankali tamkar ɗakin sarki a cikin fadar larabawa. Ruwan dumi na sauka daga sama, yana gangarowa a kan fatarsa mai laushi, yana yawo kamar ruwan zinariya.

Bangon bandakin an lullube shi da fale-falen marmara masu sheƙi, kowanne yana ɗaukar hoto idan ka dube shi. Fitilun bango biyu suna bada haske mai laushi, suna walƙiya kamar kyandirori a cikin zauren tsohuwar kasaitacciyar killa.

Turaren wanka na oudh da amber suna tashi a cikin iska, sun cika bandakin da wani irin ƙamshi mai nauyi da daraja kamshi.

A gefensa, tawul mai launin shudi yana rataye a kan bakin tagar gilashi, wanda ke duba filin shakatawar gidan.

A jikinsa, ruwan dumi yana sauka da salo, yana wanke gajiya, yana haɗuwa da kwantar da zuciya. Zuciyarsa cike take da shiru ba don bashi da magana ba, sai don mutumin da kalmarsa guda na iya murkushe magana dari.

Shi ne As’ad Babangida ɗan sarki, attajiri, kuma maigida. zuciyarsa tana saurarar ihun Fiddausi daga nesa.

Sassan gidan suna girgiza da hargowa. Bai ce uffan ba. Bai motsa da gaggawa ba. Ko shakka bai ji ba yasan ita ce. Fiddausi ce fitinanniya marar kunya, ‘yar sarauta amma marar kima. Shi da ita, tuni suka wuce iyakar jin daɗi a tsakanin juna.

Sai dai yau... yau ba zai bari ta raina masa iyali ba. Yau zai koya mata bambancin jin sarauta da daukar sarauta a matsayin shinge.

Cikin hanzari, As’ad ya gama wanka. Ya fito da zafin sarauta a fuskarsa, ya ɗora hula mai nauyin alfarma, kayan jikinsa na sheƙi. Fitarsa daga ɗakin kamar fitar sarki daga zauren fadar da aka tada saboda rashin da’a.

Da ya sauko ƙasa, gaban gidan ya yi shiru. Kowa na jiran mamaki ko faduwar magana.

Yana kallo daya da Aishatu, matar da ke zaune cikin fushi amma da ladabi. Bai yi mata magana ba a farko, sai dai ya fuskanci Fiddausi kai tsaye, murya a k’asa amma kalmomin sa na da nauyi kamar dutsen guga.

“Fiddausi, matata ba sa’arki bace. Kuma ba za ki yi ta shiga gidana kina raina min gida ba.”

Fiddausi ta fara zaro ido, tana fadin

“Yaya… ni fa... ni ‘yar uwarka ce...”

Amma As’ad ya ɗaga hannu, bai bari ta karasa ba. Ya ce da ƙarfi amma da kwantar da kai irin na masarauta

“Babu wata dangantaka da ke da muhimmanci idan har tana tozarta martabar aurena. In kin ƙi girmama matata, to ke ma ba za ki samu girmamawa a nan ba. A halin yanzu, ki fita daga gidan nan.”

“Yaya... yanzu sai da izininta zan gan ka ne?” Fiddausi ta faɗa da kuka.

As’ad ya daka mata tsawa, murya mai danna zuciya

“Idan kika ƙara magana a nan, ba fitar gida ba za ki yi ba har fitar girmamawa! Wannan gida gidan aure ne, gidan ladabi, ba gurin masifa da zagi ba. Ki fita. Yanzu!”

Kamar wacce aka zuba mata ruwan sanyi, Fiddausi ta juya da kuka. Ta ja motarta, jiki ba ƙwari, ta fice cikin hanzari, tana lumshe ido da hawaye kamar zata tsayar da lokacin.

As’ad kuwa ya juyo ya kalli Aishatu. Bai ce komai ba, sai dai ya ɗora hannunsa a kafaɗarta cikin nuni na goyon baya da girmamawa. Wannan shine mulki ba da ihu ake gina shi ba, da hali ake ɗaukaka shi.

Bata tsaya ko ina ba. Cikin huci da kuka, Fiddausi ta ja motarta da karfi, ta bar harabar gidan As’ad. Idonta na cike da hawaye, zuciyarta na tafarfasa da takaici da kishi. Ba don ta zauna a gida ba, sai don zuciyarta ta ɓaci fiye da yadda ta saba.

Tana isa gidan babbar yayarsu, tayi horn sau biyu kacal a alamar "Ina nan, kuma bana cikin natsuwa."

Babbar yayarsu ta fito da kanta, tana kallonta da tausayi. Fiddausi ta fito daga mota tana kuka, sannan cikin hayaniya ta ce

“Wallahi Ammyn Aliyu, sai na wulakanta Aishatu. Wannan matar tsiya ce! Daman ba zan taba mantawa da yadda ta tozarta Hajjarmu ba. Yanzu yaya As’ad yana so ya raina ni saboda ita? Ni fa ‘yar uwarsa ce! Meye yaga a jikinta har yake sonta haka?! Wallahi ko kadan ba sa'arsa bace ba sai faman kore masa mata datakeyi”

Yayar ta rungume ta a hankali, tana lallabata kamar yaro. Sanin halin Fiddausi yasa bata tanka da gaggawa ba. Ta bari sai da kukan ya lafa, sannan ta ce da saukar murya

“Shikenan, Fiddausi. Ki kwantar da hankalinki. Na kira As’ad din, yace yana hanya. Ki zauna ki sha ruwa.”

Amma Fiddausi ta buga ƙafarta a ƙasa, kamar yarinya, ta ce

“Wallahi sai na rama. Sai ta gane wannan gidan ba nata bane! Sai na koya mata darasi.”

Yayar ta kalleta da ɗan bacin rai a fuskarta, sannan cikin kwantar da murya mai cike da nuni tace

“Ki kula da lafazinki, Fiddausi. Kin san As’ad... yafi wuka kaifi. Kuma ki sani, sarauta ba kishi da ihu ba ce ladabi da natsuwa ne.”

Fiddausi ta dan ɗaga kai da mamaki, amma zuciyarta bata karɓi faɗan ba. Sai ta zauna tana haki, tana ta shan numfashi kamar wacce aka hana mata iska.

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA SHIDA

Ayayin da ya daga narƙakkun idanunsa ya zubasu cikin fuskarta, idanuwansa sun ɗauki launin dusar rana kamar yadda zuciyarsa ta ɗauki zafi mai nauyi. Bacin rai ya bayyana a kowane kwarjinin fuskarsa.

Aishatu ta ɗago kai cike da jin nauyin laifinta, tana jiran hukuncin zuciyarsa kamar wacce ta kusa fuskantar sarƙaƙƙen zargi a gaban alƙalin kotu.

"Aishatu..." ya ambaci sunanta da sautin da ya sa zuciyarta ta tsinke.

"Na fa gaya miki sau nawa ki daina saka abu a gabanki?"

Cikin raɗa mai cike da hawaye tace,

"Dan Allah kayi hakuri Habibie... wallahi ba don komai nake sakawa ba, shekaruna sun ja ne, ina buƙatar gyara... kuma abun yana ƙara ni’ima ne..."

Yana daɗa huci , ya ce da ita

"Ni na taɓa ce miki ina son ki saka wani abu a jikinki? Gabanki ba bola bane Aishatu... kuma ban gaya miki sau ɗaya ba!"

Yana ficewa daga gado ya ɗauki tawul, yana gyara rigarsa cikin fushi. Aishatu kuma ta durƙusa cikin ƙasa tana kuka da neman yafiya.

"Habibie please... banson fushinka. I just want to make you happy... kuma... ni naji bushewa sosai..."

Yayi mata wani kallo na ƙarshe kallon da ya haɗa tausayi da yanke hukunci. Ya shiga bandaki, addu’a na fita daga bakinsa, ya kunna ruwan zafi yana shigewa ƙarƙashin ruwa kamar yana wanke zuciyarsa daga rudanin da take ciki.

A yayin da ruwan ke zuba a jikinsa, zuciyarsa na sake jaddada masa abu guda: "Ina buƙatar aure."

Sanin halinsa da idan ya fito masa bazai saurareta ba, yasa Aishatu miƙewa cikin nutsuwa, ta shige ɗayan bandakin dake cikin tafkeken ɗakin barcin da ke cikin katafaren gidan gidan da ke ɗauke da tarkacen alfarma da kamshin kuɗi a ko'ina.

Bayan ta gama wanka da ruwan zafi, ta tsane jikinta, sannan ta zura rigar wanka mai launin fari, ta fito. Tana fitowa, ta tarar da shi zaune a gefen gadon royal, yana danne-dannen system ɗinsa, agogon Cartier a hannunsa na leƙowa daga rigar barcinsa. Ko kallon gefenta bai yi ba.

Cike da natsuwa da salo, ta karaso ta zauna kusa dashi, zuciyarta cike da fargabar kada laifinta ya cusa hazo a tsakanin su.

Bai kalleta ba, amma cikin sanyi da izza ya ce, “Kiyi kwanciyarki. Gobe flight ɗinku da rana ne. I already booked everything.”

Ta narke murya da sassauci, kamar mai kokarin tunzura zuciyarsa da tausayi, "I’m very sorry Habibie... na yarda nayi kuskure, bazan sake ba wallahi."

Shiru ya ɗauki ɗakin, sautin Ac ɗin dakinsu na tsintuwa kamar yana karanta yanayin zuciyar ma’auratan.

Daga bisani ya dago, idanunsa suka haɗu da nata, cike da bacin rai da takaici, yace, “But sau nawa zan gayamiki Aysha? Duk abinda kike buƙata kisha, ki shafa, na barki. Amma wannan saka abu a gabanki da sunan yana ƙara ni’ima? Kinsan dame ake yin waɗannan abubuwan? Kinsan irin cutar da zai iya janyo miki? Kinsan ciwon da zai iya ɓoye a ciki har sai lokacin da babu magani? Cancer is real fa.”

Tana ƙasa da murya cikin kaskantar da kai ta ce, “Please Habibie… bazan ƙara ba. Kayi hakuri.”

Ya lumshe idanu, ya dafe goshinsa kamar mai tunani mai nauyi, amma bai ce uffan ba.

A haka ya juyo gefe, ya kwanta. Ita kuma ta na cikin rigar wankanta, ta na kallo kamar karamar yarinya da aka yi wa gargaɗi. Tana ba shi haƙuri har baccin dare ya ɗauketa a gefen gadon, cikin dakin da yake dauke da kamshin turaren Oud Royal da murɗaɗɗen labulen siliki.

Zuciyarsa na faman bugawa da juyayi. Kodayake fushi ne ya mamaye sa tun farko, amma yanzu zuciyarsa na karkarwa da tausayi da buƙata. Ba wai buƙatar jiki kadai ba, a’a buƙatar kusanci, tausayinta, da ƙaunar da ke neman dusashewa a tsakanin su.

Ya juya a hankali ya kalleta, tana kwance cikin barci mai nauyi, numfashinta na fita a hankali kamar sautun waƙar dare. Fuskar ta ta haske a ƙarƙashin fitilar bango, idonta rufe cikin natsuwa, leɓenta na ɗan motsi kamar tana ƙoƙarin faɗin wani abu.

A hankali ya matsa kusa da ita. Bai faɗa mata komai ba. Amma zuciyarsa ta cika da salwanta.

Ya ɗora hannunsa a saman kugunta, ya janyo ta a hankali kamar jaririya. Ya rungumota kamar yana ƙoƙarin haɗa zuciyarsa da nata. Jikinsa ya buga da nata, zafin ƙauna ya daki lafiyarsa. Numfashinsa ya fara canzawa, jikinsa ya fara rawar buƙata, amma zuciyarsa ta hana shi bin buƙatar jiki sai dai ya yi shiru yana jin dumin jikinta.

Sai da ta ɗan motsa a barci, sannan ya matseta sosai a ƙirjinsa. Leɓensa ya ɗan sauka a gashinta, sannan a saman goshinta, yana sauke numfashi mai nauyi.

"Aysha... Ina jin ki fiye da yanda zan iya bayyana... Amma me yasa kike cutar da kanki har kin manta da irin wacce kike?"

Ya dora fuskarsa a ƙugunta, yana jin hawaye na taruwa a idanunsa, amma ya hana su zubowa. A wannan lokacin, ba miji da mata suka kwanta ba zuciyoyi biyu ne da ke neman mafita a cikin dakin da ya cika da shiru, da motsin ƙauna, da tambayoyin da babu amsa.

Rana na ɗan kaiwa ƙarfe takwas da rabi na safe lokacin da Aishatu ta sauko daga saman bene cikin shigar da ta haɗa ladabi da salo. Riga ce mai launin ruwan kwai, mai ɗauke da ɗan kamshi na turaren Maison Francis Kurkdjian, wanda ko iska na busa daga gabanta, sai ya bar ƙamshi a ko’ina.

A cikin babban falon gidan dake ratsawa da gilasai masu sheƙi da fitilun kristal, ta shinfida kayan karin kumallo a teburin girma croissant, omelette, lemo na orange sabo, da shayi mai madara. Komai cikin kayan fure masu kwantar da zuciya.

Yana saukowa daga sama cikin shigar white linen da agogon Rolex a hannu, ta tarbe shi da murmushi.

"Good morning Habibie… breakfast is ready."

Bai ce komai ba, amma ya zauna yana kallon girman kwazon da ta yi. Duk da jiya sun yi rigima, yau ta taso cikin salo da nuna kulawa irin wadda bata buƙatar magana.

Yana ci, ita kuma tana zaune kusa da shi, tana jiran ya gama. Bayan ya kammala, ya ɗan share bakinsa da tissue.

Bayan ya gama karin kumallo, Alhaji As’ad ya nufi gidan yayarsa, Mamy, domin da yamma zai tafi garinsu don wata muhimmiyar ganawa da Mai Martaba. Da ya isa, ya tarar da ita tana zaune a falo, abinci kala-kala a kan tebur ba sai an gaya maka ba, za ka gane gidan attajirai ne.

Fiddausi, wacce ke gefe tana zaune kamar tana jiransa, ce ta fara gaidasa da murya a sanyaye. Sai dai bai ma amsa ba, ya karkata ya gaida Mamy da girmamawa. Duk da cewa yayarsa ce, ba ita yake binta ba, amma akwai tarin girmamawa da mutunta juna a tsakaninsu.

Mamy ta kalleshi cike da kulawa, tace "As’ad, dan Allah kayi hakuri da halin Fiddausi. Kasan yarinya ce, tana cikin damuwa da matsalolin aurenta. Ko da ta gayamin matsalarta a waya, ni ce na bata shawarar taje ta same ka."

As’ad ya gyara zama, ya dan yi shiru na ɗan lokaci sannan yace da tsantsar takaici a muryarsa "Fiddausi ce yarinya? Mamy kema zaki biyewa Hajja kuna barin fitsararriya tana aikata abin da taga dama? Bari na gaya miki ko kallon banza kika yi wa matata, wallahi sai na dauki matakin da ba zai birgeki ba. Wannan mugun hali kike ɗauka kamar burgewa ne? Yar sarki ce? Mai kudi? To sai ki sani, kasa ce ƙarshenmu– babu daraja a hakan.

Maganar mijinta kuma, da kin san irin abubuwan da take masa, da kun tofa baki tuni. Ta hada kai da kawayen banza tana tozarta mijinta. Fiddausi ba ta da komai sai raini da wulakanci. Ba ta girmama mijinta, ba ta mutunta shi, balle ta sauke nauyin aure da ke kanta.

Ina gaya muku, mace idan ba ta bin mijinta ba wallahi sallarta da azuminta da hijjabinta, duka wuta ne a gaban Allah. Nagartar mace sharadinta shi ne ta bi mijinta.

Kuma Mamy wai har zagin iyayensa take yi? Wallahi Mamy, wannan ba daidai ba ne. Fiddausi, idan kina ganin abin da kike yi shine daidai, to bismillah ki fice daga gidan. Amma idan kina ganin zaki zauna kina kuntata masa, wanda yake ƙaunarki da gaske, to sai na gaya miki, duniya za ta juyo miki.”

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA BAKWAI

Gaba ɗaya zuciyar Ayshatu cike take da rudani da rashin kwanciyar hankali. Duk da cewa tafiyar za ta ba su damar yawon ƙasashe masu kyau, bata jin daɗin barin Habibie a baya. Kishinta yana ratsa jijiyoyin jikinta kamar wutar lantarki mai ƙarfi domin ita ba ta jin za ta iya yin nesa da shi ko da na ɗan lokaci ne.

A wannan karon, sai ta lura Habibie yana da wasu abubuwa masu matuƙar muhimmanci da ke gabansa abubuwan da suka fi tafiya a wurinsa. Wannan ne ya saka mata wata irin fargaba da ba ta taɓa ji ba a baya. Kullum bayan tafiyarsa, sai wani labari ya riske ta ko dai an daura masa aure, ko kuma an tsayar masa da wata magana. Saboda haka, wannan karon zuciyarta tana kukan shiru tana tsoron sake kasancewa a sahun baya a rayuwarsa.

Amma duk da haka, tana da tabbacin babu wata mace da ta ɗauki gurbi a zuciyarsa irin nata. Saboda haka, kafin tafiyarsu, tana ƙoƙarin bar masa wani ƙamshi wani salo na musamman da zai kasance masa kamar alamar tunawa. Wani abu da duk lokacin da ya ɗan lumshe ido, ya tuna da ita da kyanta, da lafuzanta masu taushi, da ƙaunar da ta dora masa.

An gama tattara kayayyaki tun kafin ƙarfe biyu, direbobi biyu na jiran su a gaban ƙofar manyan motocin da za su wuce su kai su filin jirgi. Komai yana tafiya bisa tsari, kamar yadda ya dace da mutanen da ke rayuwa cikin jin daɗi da martaba.

Karfe biyu da rabi da mintuna arba’in da ɗaya kenan a agogon tagwayenta na Cartier, lokacin da kira ya shigo Habibie ne. Muryarsa mai laushi da nutsuwa ta cika kunnen ta da wani salo da ke sanya mata kuzari ko da ta gaji. Ya shaida mata cewa jirginsu zai tashi da misalin ƙarfe huɗu. Wannan ya sa ta hanzarta komawa dakinta domin gyara jikinta.

Ba ta ɗauki lokaci ba wajen zabar Arabian abaya mai ɗinki irin na Al-Zahra Collections abaya mai dinki irin na Amirat mai launin ja da yadin siliki wanda ya rufe jikinta cikin salo da ladabi. Ta rataya ɗan kunne na Van Cleef & Arpels, sannan ta fesa turaren ta na Oud Royal daga kasa har sama turaren da ke saka kowane numfashi ya kasance kamar wata zallar saƙo na ƙauna.

Gaban madubi ta tsaya tana duba kanta. Fuskar ta cike da annuri, ba saɓani da fatar ta mai santsi. Daga nan ta ɗauki handbag ɗinta na Chanel sannan ta rufe dakin da natsuwa, ta nufi babban bangarensa.

Da ta shiga babban falonsa wanda aka yi wa ado ba ta same shi ba. Ta wuce cikin nutsuwa zuwa ɗakinsa, tana bubbuga ƙofar da taushi sannan ta shiga. Ta saki sallama cikin ladabi yayin da idanunta suka sauka a kansa yana waya, fuskar sa cike da annuri da murmushi. Ba sai an gaya mata ba, ta san da Hajja ce mahaifiyarsa yake waya, domin ita kaɗai ce ke da ikon motsa masa zuciya da dariya haka.

Tsit... lokaci kamar ya tsaya. Wani irin salo na ƙauna da cikar burin zuciya ya lullube Ayshatu, tana kallon Habibie da wani irin shauƙi da ko cikin mafarki ba ta taɓa tunanin za ta iya ji ba. Tana ƙarasowa, ƙamshin turarenta mai kyau na Oud Royal yana gauraye da dumin sutturar ta, Arabian abaya mai ɗinke na sarauta da launin zinariya wanda ke zubewa a jikinta kamar ruwa a kan yashi mai laushi.

Ba tare da wata faɗa ko wani bayani ba, ta faɗa masa jiki. Rungumar da ta fi kowacce magana da kalma, tana nemansa kamar wacce aka ƙwacewa iska. Sai da ya gama sallama da mahaifiyarsa cikin ladabi da annuri, sannan ya ɗauki lokaci yana kallonta idanuwanta cike da hawaye masu nauyin ƙauna.

"Please, Habibie... bana son yin wannan tafiyar... ba tare da kai ba." Ta furta cikin wata irin raɗa mai ƙayatarwa.

Wani murmushi mai ɗauke da jin daɗi da mamakin zurfin soyayyarta ya bayyana a fuskarsa, yana jawo gefen kuncinta da yatsansa mai sanyi da tsabta. Kafin ya kai ga amsa, sai ta kai bakinta cikin nasa ta masa wata mahaukaciyar sumba mai cike da tsananin daɗi da buƙata. Jikinsa ya birkice. Numfashinsa ya ƙara nauyi. Idanunsa suka lumshe da tsantsar jin daɗi.

Yana ƙoƙarin daidaita kansa ne ya kalli Rolex ɗin hannunsa. Mintuna uku suka rage kafin jirgi ya tashi. Yayi ƙoƙarin zare kansa daga cikin wannan narkakkiyar soyayyar, yana ce mata da murya mai cike da kwantar da hankali

"Ki sani Ayshatu, ko cikin aljihun zuciyata zan tafi da ke."

Sai ya kama hannunta, sannan ya ce

"Mu tafi. Zan rakaki filin jirgi da kaina."

Ta zube masa murmushi mai cike da cin nasara da jin ƙauna. Ita dai ta san ta karɓe dukkan tunaninsa. A motar suka wuce motar da aka zana tana masa addu’ar samun lafiya da kariya daga sharri.

Yayin da suke yin sallama a Airport ɗin, Ayshatu ta jinkirta da gangan tana kallon yadda iska ke kaɗawa a rigarsa mai alamar Zegna. Ta kama hannunsa a karo na ƙarshe, ta fesa masa ƙamshinta, sannan da murya mai raɗa ta furta

"Kada ka bar kowa ya raba ni da kai, Habibie... Allah ya tsare ka."

Daga nan ta juya cikin tafiya mai cike da izza da tausayi, zuciyarta cike da fatan cewa ƙaunarta za ta kafa sansani a zuciyarsa har abada.

Ko da ya koma gida, ya yi gaggawar shiga cikin babban ɗakinsa mai ƙamshi da kwanciyar hankali. Wanka yayi da sabulun Arabian oud mai ɗaukar hankali, sannan ya saka riga da wando na tsadaddan yadi kaya masu launin zinariya da shudi, haɗe da takalmansa na Ferragamo. Tufafin da suka haɗu da halittarsa suka ƙara fito da cikakken surarsa ta namiji wanda ya saba da alfarma.

Yayin da ya fito daga ƙaton falonsa, ya tsaya gaban layin motocinsa – G-Wagon, Maybach da kuma Lamborghini mai launin zinariya. Idanunsa suka sauka a kan wata mace dake tsaye a gefe, cikin shigar abaya mai sheƙi, gefenta kuma na ɗauke da ƙaramin bag.

Bilkisu ce.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull