Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 25
Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 25: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 25. Da na koma gida da yamma, gajiya ta…
3,370 words
Da na koma gida da yamma, gajiya ta saukar min sosai kamar jaka da aka jefa. Jikina duk ya dau nauyi, kaina ma ya daina ɗaukar tunani. Na zube a kujera a falo ina sauke ajiyar zuciya. Cikin kankanin lokaci na mike da nauyi na shige ɗaki, nayi wanka da ruwa mai sanyi wanda ya dan kwantar da zafin gajiya a jikina. Na shirya cikin kayan gida masu sauƙi sannan na fito ina neman inda kayan Islamiyya suke.
“Momy, Islamiyya fa?” Na tambaya.
Tace cikin sakin fuska mara kulawa “Abbanki ne ya ce ki je.”
Na gyada kai, ba don na gamsu ba, sai don bana da ƙarfi a halin da nake ciki. Na leƙa cikin kicin babu abinci. Ko ƙamshin miya babu. Sai kwanon cornflakes da ya tsaya min idanuwa. Na haɗa shi da madara, na zauna a hankali na sha kamar wanda ba shi da gata.
Bayan haka na koma ɗaki na kwanta. Na lumshe ido amma kwakwalwata na ci gaba da tunani. Washegari lectures uku ke jirana kuma har yamma zan shafe a makaranta. A raina nace, "Ramlah, sai ki dage. Wannan ba lokacin kasala bane."
Na tashi da asuba da ɗan nauyi a jikina amma zuciyata cike take da ƙaramin ƙarfin guiwa. Bayan sallah na shirya cikin kayan makaranta, na saka hijabi, na ɗauki jakata, sannan na fita. Malam Idi ya iso da mota kamar kullum, na shiga a hankali ba tare da nayi magana ba. Hanya ba ta da hayaniya, sai zuciyata dake ta tattauna da ni.
Ni fa ɗaliba ce a Business Administration, kuma yau GST 102, BUS 101 da BUS 103 ne a jadawali na.
Lecture Na Farko GST 102 Communication Skills. Muka fara da GST. Aji ya cika da ɗalibai. Wasu na ɗaukar hoto, wasu kuma na gyara litattafai. Na zauna a baya kadan, ina mai shirin shan ilimi. Malamin ya shigo da fara’a, ya buɗe lecture din da cewa “Without communication, business cannot survive.” Ya ɗan sa dariya. Daga nan ya shiga bayani mai zurfi akan verbal da non-verbal communication, barriers, da feedback. Na rubuta sosai. Wasu lokuta nakan ji kamar lecture ɗin na magana da raina ne kamar ina karanta rayuwata cikin lecture.
Lecture Na Biyu BUS 101 Principles of Management. Wannan lecture ya rikita min hankali kaɗan. Malam ya shigo da kasala kamar wanda aka taso daga barci, amma sai ya fara magana da kwarjini “A good manager doesn’t control people. He guides them.” Ya koya mana game da planning, organizing, leading da controlling, sannan ya ambaci Henry Fayol. Kamar ana faɗa min yadda zan tsara rayuwata daga yanzu.
Lecture Na Uku BUS 103 Business Mathematics. Ni da lissafi ba abokai bane sosai, amma na shiga da shirin cin karo da kalubale. Lecture din ya rikita mutane da dama, amma na dage. Profit and loss, percentage analysis, da basic statistics ne abin da muka koya. Na rike biro kamar bindiga. Na shaƙe takarda kamar zanyi jayayya da ita.
A yau makaranta cike take da kuzari da nishaɗi. Kowa yana harkar dake gabansa wasu na zuwa café, wasu na ɗaukar hoto a harabar makaranta. Na zauna kusa da sabuwar kawata Maryam, muna tattaunawa akan test ɗin da malam ya ce zai kawo mako mai zuwa. Maryam tana da fara’a. Kamar bata da damuwa. Na dinga kallonta ina tunanin "Shin ni ma zan iya zama haka wata rana?"
Yayin da rana ta fara dusashewa, na fito daga lecture na karshe ina jin gajiya.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ARBA'IN DA UKU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Yau da na dawo daga makaranta, sai naga Abba yana jirana a falo, yana murmushi a hankali. Na kalle shi cikin mamaki da farin ciki, kafin ya ce min“Ga wayarki nan, Ramlah. Samsung ce sabuwa. Yaya Usman ne yace na ba ki.” Bani da abin cewa a lokacin sai murmushi da hawaye da suka cika idona. Wannan ƙaramar kyauta da aka yi min ta ɗaga ni fiye da yadda nake zato. Nace “Abba nagode sosai. Allah ya saka da alheri.” Na karɓi wayar hannu na kama kiran Yaya Usman, har layi an sakamun aciki raina na tsalle da murna. Ya ɗaga cikin natsuwa kamar yadda ya saba. “Ramlah, wannan kankanin abu ne. Ki kula da kanki, ki dage da karatu, ki bar damuwa.” Yaya Usman yana sona sosai. Yafi kowa a gidanmu tausaya min da fahimtar halina. Yayi min wa'azi, kamar kullum, akan hakuri da karatu. Na amsa da zuciyata gaba ɗaya. Ina son hakan, ina godiya da kasancewarsa cikin rayuwata.
Bayan na gama waya, na cire kayan makaranta na, na sa hijabi na shiga kitchen kai tsaye. Na san idan na bari Momy ta rigani, tabbas abincin dare ba zata bani ba. Sai na dage nayi girki, har kamshi ya cika gidan.
Duk da gajiya da lecture na yau, da gajiya ta jiki, zuciyata tana cike da kwanciyar hankali. Wani irin farin ciki nake ji – da sabon waya, da kirki daga yaya Usman, da kuma ganin cewa rayuwa tana sauyawa kadan-kadan.
Da daddare, Abba ya dawo da wani babban leda. Na zo daidai zai shiga ɗaki, ya miƙa min shi “Ga system dinki. Nasan waccan ta dade da lallacewa amma ai wannan tafi.”.
Na kalle shi cike da mamaki. Har yanzu ina mamakin yadda Abba ke kokarin ganin yasani farinciki duk da irin tsaurin da ya nuna min a baya. Na karɓa da godiya, zuciyata cike da ƙaunar iyayena. Na bawa musa tsohuwar system dina yaje ya siyarmun, Kimanin Naira 200,000 aka siye ta.
Na bude Opay dina a hankali, na aika da sakon Musa yaje ya saka kudin cikin asusun sabon account ɗina. Babu wanda ya sani. Wannan sirri ne nawa da Musa.
Da asuba, ina cikin mopping, sai naga wayar Abba a saman kujerarsa. Na ɗauka don in kai masa, sai kuma ido na ya sauka kan sunan da ya fito "Maman Khalil." Zuciyata ta buga. Da sauri na rubuta number din, na ajiye a sabuwar wayata. Bayan nayi shirin makaranta, zuciyata ba ta da natsuwa. Daga bisani, sai na tara ƙarfin hali na kira Maman Khalil. Tayi shiru na ƴan daƙiƙu kafin ta amsa.
“Hello?” Na ce da murya mai sanyi “Mama, Ramlah ce. Yaya Khalil?” Tayi shiru na ɗan lokaci, kafin tace cikin ɗan murmush Yamai jiki ne?” Kawai sai tace “Kalou yake.” Ta katse wayar nan take.
Bayan ta katse wayar da waccan ɗan gajeren amsa “Kalou yake”, zuciyata ta faɗi ƙasa. Kamar ana jefa dutse a cikin ruwan zuciyata. Katsewar nan ta cije ni sosai. Ban fahimta ba ko katina ne ya kare? Ko kuma network ne? Na kasa yarda haka kawai aka datse waya.
Na sake kira.
Bayan saƙon farko na ringing, wani murya ta ɗaga .
Muryar Umman Khalil.
“Ramlatu! Kin kamu da hauka ne?! Me kika sake kiran layin nan?!”
“Wannan rayuwar kice? Ko ta mahaifinki ce? Ku barmin ɗana! Wallahi bana kaunarku, bana kaunar jin sunanki, bana kaunar ganin lambar da ke kirana”
Kaina ya daɗe a kasa, wayar na kunne amma zuciyata na ƙanƙamewa kamar zata tsaya. Ba wai masifa kawai take ba ta caccaka min kalmomi masu zafi da ban taɓa tsammani ba.
“Ina roƙon Allah ya wulakanta ku kamar yadda kuka wulakanta ɗana! Ki guji inda yake! Wallahi karki kuskura ki ƙara neman shi ko kallon inda yake!”
Ban iya magana ba. Har motsi a leɓena na rasa. Kalmarta ta ratsa raina kamar wuta, tana ƙona duk wata fahimta da nake da ita. Har ta katse wayar, har yanzu idona a buɗe yake, wayar a hannu, zuciyata cike da ƙunci, kunya da wata irin azaba da ba a iya fasalta ta.
Na lumshe ido, hawaye suka fara gangarowa. Kamar ruwa ne a cikin ido, amma wuta ne a zuciya. Kalmar "bana kaunarki" ta yi karfi fiye da duka. Na rasa ko na kalle kaina a madubi, ko kuma na share kwalla, ko in kwanta in huta komai ya tsaya. Abin da ya fi zafi, ba wai masifar ba ce amincewa ce da gaskiyar da ta fi komai ciwo Ban da matsayi a zuciyar su.
Ina zaune a gefen gado, ƙafafuna na kankame su a jikina, wayata na kwance a gefe. Kalmar Allah ya wulakanta ku... tana yawo a cikin kunnena. Wannan ba magana bace da ake yi da halin ɗan adam. Wannan addu’a ce da zuciya mai cike da ƙiyayya ta fitar Na dafe zuciyata da hannayena biyu. Na buɗe baki a hankali nace “Ni Ramlah … me nayi haka?”
Na rasa wanda zan gayawa. Ban san inda zan ajiye wannan zafin ba. Ban san yadda zan maida wannan bakincikin ba. Malam Idi? Momy? Yaya Usman? Ba wanda zai fahimta. Zuciyata ce kawai ta san yanda zafin kalmomin nan suka huda ni.
"Kamar ni, ni ce bakin ciki, ni ce sharri."
********
Washegari na tashi da wuri, saboda lecture dina zai fara da asuba kusan. Na shirya cikin hanzari, hijab ɗina mai laushi a kai, wayata a jaka, da na ɗan fesa turaren da ke tuna min da Yaya usman dan shine yabani.
Rayuwar jami’a ba wasa bace. A kullum ina da sabon abu da nake fuskanta ko dai sabon malam, sabon salo, ko kuma matsin lissafi da nake ƙoƙarin fahimta. Wasu lokutan bana iya cin abinci, wasu lokuta kuma nakan ci da ƙyar amma bana ƙin zuwa makaranta. Wani lokaci ma ina jin kamar makarantar ce ke ƙarfafa zuciyata.
Yau lecture ɗin mu zai kai har zuwa ƙarfe shida na yamma. Ajinmu yau ya cika kamar kullum, wasu sun shigo da kwalliya kamar na dinner, wasu kuma suna janye jakar su kamar ‘yan kasuwa. A makaranta babu wanda ke tambayarka damuwarka Na zauna kusa da Maryam. Tana ta sharhi akan group assignment da aka basu a previous class, amma hankalina ya kai ga malam ɗin da ke shigowa cikin ajin. Ya fara da cewa “Duk wanda ba zai iya jure kalubale ba, ba zai iya gina kansa ba.” Na lumshe ido. Kamar ya karanta raina. Wani lokaci nakan ji kamar malamai ba kawai koyar da darasi suke ba suna karanta mana rayuwa ne a cikin kwana-kwana. Mun ci gaba da lectures har zuwa lokacin la’asar. Sai da rana ta fara dushewa sannan muka gama. Na ji jikina ya gaji sosai.
Da na dawo gida, na tarar mun yi baki wasu daga cikin yan uwan Abba ne sun zo. Nayi sallama da ladabi, na gaishe su duka, kowanne da murmushi da tambaya “Ke ce Ramlah? Hmmm, gashi kin girma.”
Na murmusa da ɗan kunya, na amsa “Eh, nice. Barka da zuwa.”
Bayan dan zaman gaisuwa, na shiga ɗaki na yi wanka. Ruwa mai sanyi ya bugi jikina ya kwantar da ragowar gajiya da na dawo da ita daga makaranta. Na canza kaya riga mai laushi da dogon wando, na ɗan shafa man fuska mai ƙamshi.
Na fito kitchen.
“Na san idan na barwa Momy girki yau, babu komai da zan ci.”
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ARBA'IN DA HUDU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Unguwar Neuilly-sur-Seine, Paris.
Yana tsaye ne a cikin kayataccen ɗakinsa mai fadin gaske dake unguwar Neuilly-sur-Seine, wani yanki ne na masu kuɗi da attajirai kudi a gefen birnin Paris, yanki mai zaman kansa da cike da bushes masu launin zinariya, da lambuna masu ƙamshi, da fitilun tituna masu saukar haske kamar na aljanna.
Gidan mallakinsa ne ba haya ba, ba ɗauka ba. Shine ya gina shi da kuɗin ginin kamfaninsa na kasuwanci da kuma zuba jari a kasuwar hannun jari (stock market), da cibiyoyin hada-hadar kadarori da na kasashen waje.
Ko da yake duniya tana kallonsa a matsayin attajiri mai farin jini kuma ɗan sarki daga asalin Najeriya, wanda ya yi fice a duniya, zuciyarsa kuma cike take da jijjiga da damuwa mai nauyi. Sai dai a duk wannan, Ayshatu ce ta fi kusa da shi fiye da kowa. Ita ke kula da lafiyarsa, kulawarsa, damuwarsa ita ce matarsa, masoyi, kuma abokiyar shawara. Ta koyi yadda zata karanta damuwarsa ko da bai ce komai ba.
Ya tsaya a jikin gilashin tagar ɗakin, yana kallon hasken titi da ya shigo cikin siririyar labulen fata. Hasken dare yana yawo a fuskarsa mai haske dake cike da damuwa.
A hankali jikinsa ya motsa, tsigar jikinsa tana kara mikewa, kamar yana jin sanyi amma ba daga jiki ba daga zuciya ce. Ya cije leɓensa da ƙarfi, kamar yana hana kansa faɗar wani abu da zai iya juyar masa da tunani gaba ɗaya.Ba yana da matsala da Ayshatu ba. A'a Ayshatu ta gamsar da shi a kowane fanni. Ta nuna masa ƙauna da amana. Ita ce matar da duk wani namiji zai so a matsayin abokiyar rai.
Amma yana jin wani tsoro na ruhaniya tsoron ko yana shiga hakkinta, ko yana jin daɗin soyayyarta fiye da yadda ya kamata. Yana jin laifi ba don tayi masa komai ba, sai don yana ƙaunarta har da jin tsoron bata mata rai.
Shi ko da yaushe yana tambayarta ko yana gamsar da ita, ko yana mata adalci. Amma ita kullum sai tace “Ka daina tunani haka. Kana gamsar da ni fiye da yadda kake tunani. Ka fi karfin zargi da kanka.” Sai ya dinga jin kamar kalamanta na tausayawa ne tana ƙoƙarin kwantar masa da hankali, amma shi zuciyarsa tana rarrabe masa sakonni.
Karar wayarsa ce ta katse shi daga zurfin tunanin da ya shige.yana kallon Eiffel Tower daga nesa, sai da ya duba taga kafin ya kai hannu kan wayar da ke kara kamar zata katse.Ya dan shafa kansa a hankali, fuskar sa cike da gajiya da tsananin damuwa. Ya ɗaga wayar ya kara a kunnen sa yana murmushin ƙaryar da ya saba yi idan zuciyarsa ta kai ƙololuwar wahala.
“As’ad, dazu ka kira. Ina gurin Mai Martaba ne? Da fatan kuna lafiya?”
Muryar Hajja ce Mahaifiyarsa, Kamar yadda ta saba, ta fara ne da tambaya, amma cikin tambayar akwai zargi, akwai tsawa, akwai kulawa. “Yanzu hakan da ka yi dai-dai ne kenan? Ka bar kasuwancin da ka gina a ƙasarka, ka koma wata ƙasa saboda kawai wani ya maka sharri?”
As’ad ya runtse ido kamar zai hana wani abu shiga tunaninsa. Sai zuciyarsa ta cika da ƙuna, da daci, da raɗaɗi mai haɗuwa da zafin wulakanci. Wani abu kamar nauyin dutsen da ya dade a ƙirjinsa, ya sake latsa zuciyarsa.
Zagin da Haneefah ta jawo masa bai tsaya a cikin gida ba. Ya yadu har wajen, har abokan kasuwanci, har manyan da suke yi masa kallon gwarzo.
Zuciyarsa ta girgiza da ƙarfi lokacin da Hajja ta sake tambaya da murya mai taushi “Kana jina ne ko? Kai kuwa kana da tabbaci wannan abun da take cewa gaskiya ne?” Cikin ƙasa da murya amma da karfin nutsuwa, ya amsa
“Hajja... ba ƙarya take ba. Da gaske take.”
“Kamar yaya yarima? Da gaske kace? Yaya zaka ce haka? Kana jin kanka kuwa? Bakaga likita ba ni ba? As’ad, fa wannan magana ba ce mai sauƙi.”
Yayi shiru. Ya dan sauke numfashi kamar wanda ya rasa wani ɓangare na kansa. Ya dafe goshi da hannun hagu, idonsa yana kallon bene mai sheƙi wanda fitilun ɗakin ke taɓa shi da launin fari. “Duk abinda ya kamata nayi Hajja... nayi. Na ga manyan likitoci a ƙasashe fiye da guda uku. Har India na je makon jiya. Na je UK, na je Germany, amma kowanne likita kalma daya yake faɗa 'Lafiyarka kalau.' Na gwada herbal medicine, amma babu wani sauyi. Wani lokacin ma kamar ciwon yana ƙaruwa ne.”
Yayi maganar yana runtse ido, tamkar yana son jure wani zafi da bai bayyana a jiki ba, amma yana yawo cikin kwararan jijiyoyinsa.
Daga dayan bangaren, Hajja ta karɓi shiru na ɗan lokaci, kafin ta buɗe baki da wata kalma mai nauyi sosai a kunne “Anya ba asiri ne ba As’ad? Ba wani abu aka maka ba ne?”
Kalmar ta tsaya masa kamar sara akan dadduma. Idanunsa sun bude da sauri, zuciyarsa na bugawa da wani sabon yanayi. Bai san yadda zai kare kansa daga wannan tunanin ba saboda har yanzu bai fahimci tushen wannan jinya da ciwon ba.
“Asiri fa kika ce, Hajja? Wannan fa ba asiri bane mutum ya rasa ta inda zai warke. Babu wanda yake bani amsa sai dai ace lafiyata kalou.”
“Nikam bansan me zan ce ba yanzu… sai dai nace kawai ka cigaba da addu'a sosai. Ka dage da azkar, da karatun Alkur’ani. Babu abinda yafi karfin Allah.”
Ya murɗe fuskar sa cikin ciwon da ba a iya fassara shi a cikin kalmomi. A lokacin, shiru ya shige wayar, amma zuciyoyinsu biyu sun cika da nauyin da ba sa iya faɗa.
“To yanzu, idan nasa aka kawo maka rubutun rukiyya ko na malamai... za kasha ?” Hajja ta tambaya, tana ƙoƙarin samu ko da ƙofa ɗaya da za ta shiga ta agaza masa.
“Zan karɓa, Hajja. Amma... bana jin karfin komai. Sai dai a taimaka min da addu'a. Ni da kaina na fara shakkar kaina. Amma idan Allah zai kawo sauƙi daga wannan hanya, zan gwada.”
Ya ƙare da murya mai sanyi. Godiya yayi mata da gaskiya daga zuciyarsa. Sannan suka yi sallama Ya ajiye wayar a hankali, ya jingina a kujerarsa. Hasken fitilar chandelier yana sauka a kansa.
***
Duk wani salo na jaraba, fitina, narkar da zuciya da ramgwadar namiji Ayshatu ta kware. Matar nan ba kowacce irin mace bace. Kyawunta yana ƙayatar da ido tun kafin ka fahimci shigarta, sannan kulawarta na tafiya da zuciyar namiji kamar ruwa a kan tabarma.
A yau, sanye take da wasu hadaddun kaya daga Maison Alaïa, rigar famai launin fari da baƙi, tana taɓa jikinta da santsi kamar ruwan madara. Turarenta mai ɗan ƙamshin oud da vanilla ya ratsa dukkan ɗakin, yana haɗuwa da sanyin iska da ke shigo wa ta tagar Neuilly-sur-Seine.
Ta buɗe ƙofar bedroom ɗinsa da salo kamar yadda ta saba, da nutsuwa, da kwarjini. Ba tare da wata magana ba, ta nufi inda yake zaune, yana daddabe kansa cikin damuwa, fuskar sa cike da zurfin tunani.
Bata zauna a gado ba.
Ta zauna a cinyarsa, ta lulluɓe hannunsa da nata, tana mai aika masa da wani narkakken kallon da ya kashe tunani. Idanunta sun cika da yaren da ba a fassara so, damuwa, da ƙaunar da zata iya narkar da dutse.
"Ayshatu..." ya furta a cikin wata ƙasa da murya, yana kallonta kamar ya rasa mafita, "Ayshatu… da ace lafiyata kalau…”
"Ta buga gefen kirjinsa da sauri, kamar yarinya, muryarta na ɗan huci "ka daina faɗin haka! Nifa mijina yana da lafiya. Wannan maganar naka tana dagula min tunani. Duk lokacin da kace ba ka da lafiya, zuciyata na murɗuwa kamar an sa mata ƙaya.”
Ta matsa kusa, ta sumbace hancinsa da sauƙi, sannan ta aika masa da wani kiss mai dumi da tsantsar ƙauna, har sai da numfashinsa ya dan canza. Amma sai kawai ya furta, cikin wata murya marar zafi
“Ayshatu… ban jin komai. Ban jin wani abu da zan iya nunawa dake cewa ina ƙaunarki da jiki. Ban da ƙarfi. Kuma ba na jin ƙwanƙwasa... ba na jin buƙata. Ina so ace ina jin wani abu, amma babu.”
Ayshatu ta ture kanta a hankali, kamar yarinya da take ƙoƙarin tayar da hankali. Ta shaƙi hancinsa, ta matsa lips ɗinta kusa da kunnensa, tana raɗa
"Ni fa ina jin komai. Ina jin buƙatar ka sosai. Mu yi soyayya, As’ad. Ka sumbace ni, ka rungume ni, ka tabani... kayi duk abinda zai sa ni mantawa da damuwa ta wannan duniyar.”
Numfashinsa ya dan ja da nisa. Sai ya yi ɗan murmushin nan nasa mai tsada wanda kowa a duniya ke kira “signature smile ɗinsa.” Cikin murya mai sanyi da sauƙin tabbas ya ce
"Yanzun nan kuwa? Kin tabbata za ki iya ɗaukata?"
Ayshatu ta girma. Ta zama mace mai ilimi, kudi, nutsuwa, amma hakan bai hana ta zama matar aure mai hankali ba. Duk da shekarunta, bata bar shagwaba ba, bata bar ƙoƙarin nuna ƙauna ba.