Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 26
Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 26: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 26. 🗣️ “Dan kin fara girma ko shekarunki sun…
3,332 words
🗣️ “Dan kin fara girma ko shekarunki sun ja, ba shine zai hanaki yina wa mijinki shagwaba da kauna ba. Ki zauna gaban mijinki kina masa duk wani abu da zai ji kamar bashi da wata a duniya sai ke. Ba a tsufa a gado wallahi!”
🔥 “Ku gyara mata. Ku nishadantu da mazajenku. Kada ku manta mijinki ɗaya ne, amma shi yana iya ƙara guda uku idan bai ji isasshiyar kulawa ba.”
Gida ba kawai wurin zama bane, gida shine fagen yaki da damuwar zuciya kuma mace ce makamin soyayya idan ta san yadda ake amfani da kanta.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ARBA'IN DA BIYAR
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Ayshatu ta zame daga cinyarsa a hankali, ta sauka ta durƙusa a gabansa kamar wata baiwa, Wani irin farin cikin kai ne, mace mai daraja ta iya zubewa a ƙasa domin mijinta? A irin wannan lokaci ne kulawa ke canzawa zuwa ruhi ƙauna ta zama jinya, kuma soyayya ta koma magani. Hannunta a kansa, tana shafewa a hankali kamar tana roƙon ciwo ya fice. Ta ce da ƙasa da murya mai raɗaɗi
“Ka daina jin kamar kai kaɗai ne. Ka daina jin kamar ka kasa. Ni ina nan tare da kai. Idan baka jin ƙarfi, zan kasance ƙarfinka. Idan ba ka jin ƙauna, zan zama ƙaunarka.”
As’ad ya tsareta da idonsa. Ba zai iya misalta irin salonta ba ba mace bace da ke da iyaka. A rayuwarsa duka, babu wadda ta tsaya masa kamar Ayshatu.
Ta miƙe tsaye cikin salo, doguwar rigarta na bin jikinta kamar ruwa. Kafarta ta dan sauƙa da sauƙi, ta nufi gado cikin natsuwa. Ta zauna a tsakiyar gado tana kiran sa da murya mai salo “Zo mana. Kar ka bari ciwon zuciya ya cinye zuciyar ƙauna. Zo ka kwanta. Ko baka da ƙarfi.
As’ad bai iya ƙin ta ba. Wannan ba daga jiki kawai ba ne daga zuciya ce. Ya mike da kyar, ya karaso ya kwanta a gefenta. Bata tsaya jira ba, ta kwanta jikinsa, ta ɗora kanta a kirjinsa, tana jin yadda bugun zuciyarsa. Ta ɗora hannunta a kan hannunsa. Ta sumbace wuyansa da laɓɓa masu dumi.Ta furta da ƙasa da murya, kamar addu’a “Allah ya baka lafiya. Allah ya dawo da komai. Ni ba na buƙatar ƙarfi idan ba kai.”
As’ad ya kalleta cikin idanu. Sai ya furta “Wannan kulawar, Ayshatu… sai dai a ce na same ki da farko. Da ba zan bar kowacce mace ta shiga rayuwata ba. Wallahi ke ce gidan da ba zan so barin sa ba.”
Ayshatu ta kwanta a jikinsa, tana shafa bayansa kamar jariri.
Tana faɗa masa kalmomin da ba kowacce mace ke iya furta wa mijinta ba.
“Ka fi ƙarfin ciwo, ka fi ƙarfin sharri. Ka fi ƙarfin gajiya. Ka fi kowa. Kai ne As’ad ɗina.”
(Kada mace ta bar mijinta ya gaji da rayuwa. Kada ta barshi ya bar fahimtar cewa akwai mata masu nuna kauna.
🗣️ Ki zauna kusa da mijinki, ko ya gaji, ko ya fadi, ko ya ɓaci.
🤲🏽 Ki yi masa addu’a, amma ki dafa hannunsa da dumi, ki rungume shi da ƙauna, ki goge gumin jikinsa da shagwaba.)
(Ba a girma da aure. Ba a tsufa da soyayya.
Ba a yawan shekaru a gado, sai yawan ƙarfin zuciyar mace. Kuma mace ce ta fi kowa sanin jinyar mijinta, idan ta damu.)
(Ayshatu ta san irin kalmomin da As’ad ke bukata, ba don ya faɗa ba, sai don tana jin shi. Tana masa magana kamar zuciyarsa ce ke magana da kanta. Tana sumbatarsa kamar magani ke fita daga laɓɓanta. Kuma wannan daren, daren da wata mata za ta bar miji a duhu, Ayshatu ta canza shi zuwa haske da ƙauna.)
*********
****************
Yau muna da baƙuwa agidan mu kanwar mumyce , Yakaka. Ni da ita fa, tun ina ƙarama, babu wata soyayya tsakaninmu. Tunda ban ma san kiyayya ba, na riga na fara jin ƙiyayyarta. yau da nagama aiki da girki dayake lecture ɗin yamma ce, ban sami damar hutawa ba.
Na fito daga daƙina, jaka a hannu, sanye da abaya wacce na sanya yanzu haka ba ta ɓoyewa halittata ba. Sai wata irin kallon tsana Yakaka ta jefani da shi, Ni da ake kira da kwaila yau nice make sanya breziya har size 39, idan kuga yadda nayi kyau sai kunyi mamaki shiyasa mumy kullum maganarta maganin kiba nakesha.
Na karasa cikin palon Na faɗi wa Mumy zan tafi makaranta. Batace uffan ba. Sai kawai muryar Yakaka ta cika parlour, tana cewa
“Ai na fa gaya miki! Sai ta zama miki ƙadagaren bakin tulo. Gobe sai kiyi kuka da idonki akan wannan diyar Larabawan kauyen da kika ƙi ba kakarta!”
Wannan magana kamar ta fantsama kai tsaye cikin zuciyata, duk da ban ce komai ba. Amma Mumy ta ce da ɗan murya
“Yakaka tana shan abun kara kiba ne fa.”
Yakaka kuwa ta barke da dariya “Ke mahaukaciya ce wallahi! Kin manta yadda mahaifiyarta take? Kin manta yadda mijinki yazama bawanta? Mu da har tausayi muke ji miki, Ai ba sai angagamiki ba wannan yarinyar sai tafi mahaifiyarta kyau wallahi ko tasha magani ko batasha ba”.
A nan ne zuciyata ta soma bugawa tamkar ana buga ganguna. Kafafuna sunyi nauyi. Ban ce musu uffan ba. Na juya kawai, na nufi makaranta. Sai na ga Malam Idi a ƙofar motar, na gaida shi. Haba, ina da lecture amma hankalina bai nan . Maganganunsu Yakaka da Mumy suna yawo a kwakwalwata kamar ƙudaje.
****
Zaki tsaya kina kallonta ne, Zainabu? Yanzu fa tasoni kika yi. Kikace bakin cikin yarinyar nan zai kashe ki, ko? tunda yanzu, ko kin yi kissa, kin shirya makirci, bayan kwana biyu uban ta zai dawo da kulawa gare ta kamar ba a taba ba.
To, banda ke da abunki irin soyayyar da mahaifinta ke nuna mata zaki iya yakar ta da makirci kuwa? Ki gode wa Allah da bai gane ki a wancan lokacin ba. Wannan lokaci ne da za mu sake bude masa ido da kwankwasa zuciyarsa.
Mumy ce ta share hawayenta, ta ce, “Yakaka, masifar da nake ciki ta fi karfin bayani. Kinsan Bilkisu bin maza take yi.” Mumy ta fada cikin kuka mai karfi.
“Ke, banson karya, Bilkisun taki?” Inji Yakaka. “Wallahi gaskiya nake fada. A haka ma na ci ubanta, amma abun bai sauka ba. Aikin ma bata zuwa sha’awarta ce kawai take bi. Yakaka, har shaye-shaye Bilkisu take yi fa. Ni na gani da idona!
Idan mahaifinta ya gane haka, wallahi sai ya raba ta da kowa sannan ya yi mata aure cikin hanzari. Zai iya rabuwa da Bilkisu har abada. Kinsan ta fara haddasa fitina tun lokacin da aka kai ta gidan abokinsa. Shine ta nutsu, amma yanzu abun ya koma kazanta.
Shiyasa nace miki kizo ita wannan yarinyar da na dinga dorawa akan bin mazan da shaye-shayen wallahi bata aikata ba. Bata lalace ba sai tawa. Yakaka, ya zan yi? Dan Allah zuciyata na yi min zafi fiye da yadda zan iya dauka.”
“To yanzu dai, shawara guda ɗaya ce zan baki,” inji Yakaka. “Ki san yadda zakiyi, kiyi wa Bilkisu aure. Ki samo wani babban mutum, a aura mata. Daga nan kuma a shiga malamai, a kulle mata kafafu gaba ɗaya.”
Zainabu ta kalli Yakaka, ta ce “Ramlah fa, Yakaka? Ina son ta haukace da bakin ciki. Bana so ta gama karatun nan nata. Ina so ta mutu da bakin ciki kamar uwarta.”
Yakaka ta yi dariya, sai ta ce, “Wannan kuwa abu ne mai sauƙi, Zainabu. Abu na farko aikin fili. A haɗata da wata larura har ta zama sanadiyar rashin lafiya. Idan da ciwo, ai karatun bazai yuwu ba, ko?”
“Abu na biyu,” inji Yakaka, “ki samo a aura mata Bashari. Indai kina so ta lalace, to wallahi zata lalace. Ki dubi Bashari dan shaye-shaye ne, dan iska ne, dan bangar siyasa ne, sannan kuma azzalumi ne. Babu mutunci, kuma dan fashi ne cikakke. Rayuwa a kauye zai killace ta. Zai mata ciki da ciki, har ta rude. Kinga, babu rabuwa kuma rayuwarta zata rufta tun daga nan.”
Zainabu ta dafe kirjinta cikin jin daɗi, ta ce “Na yarda, Yakaka. To yanzu me za mu fara yi?”
“Wannan ba matsala ba ce,” Yakaka ta amsa. “Ni zan daidaita mahaifinta. Sai dai a ɗan buga kansa sau ɗaya kawai dan kada ya mana cikas.”
Mumy ta fashe da dariya, tana fadin “Allah ya bar min ke, Uwata! Shiyasa nake ƙaunarki.”
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ARBA'IN DA SHIDA
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Gaba ɗaya cikin satin nan, da ƙyar nake yin komai. Kaina yana ciwo, gabadaya jikina ya gaji, wani rashin kuzari ya shige ni, sannan kaikayin gabana bai bari na huta ba. Kuma fa idan na cire pant dina, wani irin wari ne mara daɗi ke tashi wallahi bana wasa bane ba. Haka nake ta mamaki, ko dai kowace mace haka take ji? Ko kuwa ni kaɗai ne nake fuskantar haka? Gaskiya ban gane ba, sai dai nake ta tunani.
Kai yau kuma! Na tashi da safe da ciwon kai, sannan ina da lectures biyu, ciki harda na lissafi. Wannan lissafin kuwa ba ƙaramin daure min kai yake ba. Na gama girki da safe, koko da kosai kawai nayi, na ci kadan sannan na je dakin Abba. Na ce masa, “Abba, kaina na ciwo sosai. Wallahi bana jin daɗin jikina.”
Shi kuwa sai ya ɗauko min Paracetamol ya bani, yace, “To ki sha, zai taimaka.” Na karɓa da godiya, amma a zuciyata nace, “Da ace zai ce na je asibiti ma, ai zai fi.” Amma shikenan, na sha, na shirya, na fice.
Ina fita, na kira Musa, na ba shi kuɗin mota, nace, “Dan Allah ka je ka dubamin Khalil. Kwana biyu kenan ina mafarkin shi. Bana jin daɗi wallahi.” Yace, “To In shaa Allahu, zan je.” muka tafi makaranta.
Abba kullum dubu biyu yake bani, amma gaskiya ba su isheni komai ba. Makarantar mu fa, komai tsada. Ko ruwa ka siya ₦500 ne. Meat pie ma har ₦1,000. Sai dai in yi managing. Wasu lokuta sai na ci abinci sau ɗaya a rana kawai domin kuɗin su isa. Har na fara tara Canjin nawa dan naga ina bukatar gyaran jikina ina kuma bukatar kudin.
Lecture ɗin farko da muka shiga da safe, na zauna ne kawai da jiki a mace. Na kasa mayar da hankali. Ina jin kaina kamar yana zafi sosaj, ba komai ke shigowa cikin kunne na ba. Gaba ɗaya raina ya cunkushe. Ina jin ba daɗi. A class ɗin, sai kallon mutane nake yi wasu manyan mutane da make-up, wasu suna dariya, wasu suna buga TikTok, sai kuma wasu masu nutsuwa suna karatu. Gaskiya jami’a ba irin wacce na zata ba ce. Nan ne zaka ga tarbiyya, nan ne kuma zaka ga lalaci da rashin kunya, har cikin malamai ma ba a rasa irin hakan ba.
Lecture na biyu kuwa, ni da kaina nasan na zauna ne kawai domin kowa yana zaune. Na kasa gane komai. Kaina na ciwo, ciki na yana juyawa. Ko magana ban iya wa. Har mamaki nake yi yanda wasu ke iya daukan waya suna dariya a class, ni kuwa ba zan iya komai ba sai zuba ido.
Bayan lecture muka fita waje. Na tsaya gefen wani shago, na siya ruwa ₦500. Sai na sha kadan, na yayyafa sauran a fuska. Na samu wuri na zauna a ɗakin karatu, na duba diary ɗina, na fara rubuta
"Ya Allah, ka sauƙaƙa min. Ka bani lafiya. Ka cire wannan wari, wannan ciwo da wannan damuwa. Kar ka bar ni a haka, don ban da wanda zan faɗawa."
Har na zauna na rasa mafita. Ina jin kamar in kira Abba in gaya masa komai, amma sai na fasa. Kuny ta lullubeni Zan kira in ce masa, “Abba, gabana yana kaikayi kuma wari yake”??? Ai kamar raina wa mutum hankali ne hakan da kuma kunya ai. Kuma duk lokacin da ka faɗa masa wani abu mai sosa rai, sai ya ce in sanar da mumy.
Kullum na nafi son zama ni kaɗai. Idan lecture ya ƙare, sai dai in je ɗakin karatu ko in yi tafiya ni kaɗai. Wani lokacin kuma ina jin kamar in yi kuka. Amma ina? Ko kuka ba zai canza komai ba.
Yanzu haka, ina tunanin mafita. Kwana biyu kenan ban iya yin karatu da kyau ba. Bacci ma ba kamar yadda na saba ba. Ina mafarkin abubuwa iri-iri. Na rasa damuwar da ke tattare da zuciyata. Har Khalil da na rabu da shi kwana dayawa, yanzu sai mafarkinsa nake.
Wannan makon ma, na kasa kammala assignments. Gobe zamu gabatar da presentation, kuma har yanzu ban gama slides ɗina ba. Sai dai na dinga duban wasu daliban da suke da ƙarfi, sukan zo suna nuna mana cewa komai is easy. Amma ni nasan ba komai ne easy a wajena ba.
A makarantar mu, akwai abubuwan da sukan faru da sai dai mutum ya kalle su da ido, ya ɗauke rai. Amma zuciya tana cike da ƙorafi. Wasu malamai a makarantar, wallahi, Allah ya shirya su. Duk lokacin da suka shiga aji, ba abin da suke nema illa 'yan matan da suka fi kyau ko shigar zamani. Suna latsa ido kamar ba malamai ba. Za su je su tsaya kusa da mace, su fara magana da murmushi, su ce suna yaba mata da ƙoƙari, amma ashe wani abu ne suke nema a bayan kalmomin.
Wani lokaci har suna ɗaukar lambar waya suna cewa “zan taya ki da tutorial”, amma gashi kafin a jima sai su fara neman saduwa da daliba. Idan kin ki, sai su fara ba ki low marks, su hana ki shiga exam ko su ƙi amincewa da assignment ɗinki. Gaskiya wannan ba gaskiya ba ne, kuma haramun ne, amma babu mai magana saboda tsoro.
Wasu daga cikinmu kuwa Allah ya kyauta sai su ce ai dama shi ne hanya. Sai ki ji yarinya na cewa, “Ko na faɗa masa no, sai ya ba ni carry over. Na fi so in bi shi in huta.” Wannan kuma abin tausayi ne, saboda sukan cutar da kansu su yi tunanin suna samun sauƙi, amma ba su san cewa rayuwarsu na ci gaba da lalacewa ba. Da yawa daga cikinsu, ba su da burin kammala karatu da mutunci. Yanzu sai dai shigar jikin yara tops da wando ƙato suna zagaye makaranta kamar gaban mirrors. Wasu suna selfie da cinyoyinsu kawai suke so su nunawa duniya, ba ilimi ba.
Gaskiya rayuwar daliba mata a jami’a da wahala. Idan ba tsari da zuciya da hankali, sai ki lalace. Idan kuma kika tsare kanki, sai ki zama kamar bakya cikin “system.” Kullum sai kowa na cewa ke serious ce ko kuma ke religious ce. Amma sai da irin haka ne ake tsira.
Ni dai na bar kaina cikin tsarewar Allah. Dan yanda nake ji yanzu ciwon kai, wari, kaikayi, da rashin lafiyar da bana fahimta na fi buƙatar kulawa fiye da komai. Sai dai, wata sabuwa fada tsakanina da mumy jiya da dare. Tun safe banjin daɗi ba, amma ina kokarin dafa abinci. Sai mumy ta shigo da masifa, tana cewa “ke bani dankune na dakika daukai.” Na tsaya ina kallonta, ban ce komai ba. Tace “ ni kike wa shiru?” Nace, “Wallahi mumy ba haka bane. Wallahi jikina ke ciwo. Amma ban daukar miki ba Ba” Ta ce, “To ni ƙarya nake yi kenan? Kawai kina so ki rainani!” Nayi ƙoƙarin bada haƙuri, amma ba ta saurare ni ba. Tana zuwa ta zunduma min mari.
Gaba ɗaya na rikice. Idanun nawa suka cika da hawaye. Jiki na babu ƙarfi, zuciyata kuma cike take da raɗaɗi. Nace, “Wallahi Mum, ban da lafiya ne. Kika ma sake kallon jikina zaki ga...”
Amma kafin in ƙare zance, ta zage ni da kalmomi masu zafi. Tace ni ban da tarbiyya, cewa ina neman maza ne, cewa na gaji da karatu sai bariki. Wannan kalaman da marin suka fi duk ciwon da nake ji.
Na koma ɗaki na kulle kaina. Na zauna ina kuka. Kukan da ban iya bayyana shi ba. Nace, “Ya Allah, me na yi? Lafiya nake nema. Ina wurin da ba wanda ke fahimta ta.”
Daren jiya ban iya bacci ba. Na yi ta tunanin rayuwa. Shin haka ake rayuwa ne? Ko ni kaɗai ce nake cikin wannan bala’in? Gaskiya ya isheni.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ARBA'IN DA BAKWAI
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Da safe nayi kokarin tashi duk da jikina na a mace. Har yanzu kaina yana ciwo fiye da jiya. Na sha Paracetamol da safe, amma sai ciwon ke kara karfi kamar ana jujjuya kwano a cikin kwakwalwata. Na kasa cin abinci sosai, sai tea kadan da biskit. Komai a jikina kamar baya cikin hayyacinsa zuciyata na tashi, gabana na faduwa.
Amma yau presentation muke da shi, kuma ban yarda na sake karatu ba. Public Administration muke karantawa, kuma ina cikin group ɗin da za su fara gabatarwa. Na ɗauki takarduna, na zuba su a jaka, nayi addu’a, nayi shiru na jima kafin na fita.
Kafin na fita ne kuma Musa yazo. Bai shigo da fara'a ba kamar yadda ya saba. Ya tsaya a bakin ƙofa kamar wanda aka daka.
“Ina wuni,” yace da sassautaccen murya.
“Lafiya Musa? Ka ga Khalil din?” Na tambaye shi cikin sauri, zuciyata na bugawa kamar an tada karfe.
Yayi shiru. Yana kokarin duba idona, sai ya kauda kai. “Wallahi ba su barni na ganshi ba. Wani babban likita ne yace ba zamu iya ganin marasa lafiya yau ba.”
Na ce, “To lafiya kuwa? Me ya faru? Wane ciwo yake da shi da har ba a bari ana ziyara?”
Yayi karamin numfashi yace, “Na tambayi nurse. Tace kawai ‘da sauki ne’, amma bazata iya bada cikakken bayani ba. Sai dai ta ce yana samun kulawa sosai.”
“Da sauki?” Na maimaita cikin ƙara. “Da sauki amma ba a bar kowa ya ganshi? Me yasa suke boye mana komai?”
Zuciyata tayi raurau, jiki na ya yi sanyi, kaina ya fara juyawa da sauri kamar zan fadi. Sai kawai na kama bango domin kada in sulale a wajen. Musa ya matso yana faɗin inyi a hankali.
“Ki zauna mana.” yace. “Kamar kina jin jiri ne.”
Na kada kai kadan, hawaye na taruwa a idona. “Wallahi Musa idan wani abu ya faru da Khalil, bazan iya jurewa ba. Tun jiya nake mafarkinsa. Yau kuma sai ace ba a bar ka ka gan shi. Wane irin da sauki ne wannan?”
Yayi shiru, bai ce komai ba. Sai kawai ya zauna kusa da ni yana kallona da tausayi.
“Zan tafi makaranta,” na fada da karfi. Presentation ɗin mu yau ne, kuma ni ke da jagoranci.”
Musa ya tsaya yana kallona kamar ba zai yarda ba. Amma na mike tsaye na wanke fuskata da ruwa, na ɗauki hijab ɗina, na fice.
Da muka isa makaranta, zuciyata babu daɗi. Na zauna a cikin ajin da presentation ɗin zai gudana, ina jujjuya takardun da ban ma san me ke ciki ba. Idanuna sun rame, kaina kamar an dora masa dutse. Amma ina iya cewa duk da haka, na tafi da ƙwazo da nutsuwa.
Lecture ɗin ya shigo cikin aji, ya duba lissafin waɗanda ke da gabatarwa. Lokacin da ya kira sunan group ɗinmu, zuciyata ta buga. Sai na mike da ƙarfin hali, na fito gaban class. Na buɗe laptop ɗina, na haɗa projector, na fara magana.