Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 27
Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 27: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 27. Amma ina magana, sai na lura da wani abu…
3,326 words
Amma ina magana, sai na lura da wani abu da ya dame ni fiye da ciwon kai. Lecture ɗin yana kallona kamar zai cinye ni da idanuwa. Kallon da bana so, kallon da ban da buƙata, kallon da ya sa nayi kuskure na karanta “Public Admiration” maimakon “Public Administration.”
Sai na tsaya cak. Na gyara. Na yi murmushi na dole, amma zuciyata cike take da fargaba da jin kunya. Sauran daliban sai dariya suka fara yi kadan kadan. Na ji wata wuta kamar ina tafasa a ciki. Na ci gaba da magana, amma ganin irin kallon lecture ɗin ya fara damuna sosai. Ko dai yana kokarin cutar da ni ne kamar yadda wasu malamai ke yi wa wasu dalibai? Kamar yana daukar hotona da idanuwa.
Sai na kasa jurewa. Na kalli shi a ido. Ya danyi murmushi.
Subhanallah... Wannan murmushin fa na mutumin da yake kallonki ba don aikin ilimi ba, sai don wata sha’awa ko mugun nufi. Kamar na faɗi kalma guda a nan gaban aji “Sir, please stop looking at me like that.”
Amma na ƙyale. Na ci gaba da gabatarwa. Na dage da karfin zuciya, na kare abinda nake da niyyar fada, na zauna. Na kalli kasa, na ji ciwon kai yana kara tsananta.
Bayan na fito daga makaranta, jikina ya ƙara tsananta. Zazzabi ya tashi sosai. Kaina yana ƙara ciwo, jiki na yayi rauni. Na ƙara shigowa cikin gida da ƙyar, amma na ji muryar Mumy a palour tana fada kamar kullum.
“Ina gaya miki Billy! Wallahi sai dai ki fitar min da tsayayye a Samarin naki. Idan ba haka ba, sai dai ki fitar da kanki daga gidan nan! Kina neman ki jawo min bala’i! Mara tarbiyya kawai!”
Na tsaya a ƙofar palour, zuciyata na bugawa. Sai Billy ta tashi ta bar palon ba tare da ta ce komai ba. Ni kuma na yi sallama, na shigo cikin gida a hankali.
Mumy ko kallona bata yi ba. Kamar bata ganni ba kamar ba sallama nake ba. Na wuce cikin ɗakina. Na kwanta ina jin jiki na kamar ana hura masa wuta. Na rasa ina zan saka kaina. Dakyar nayi girkin dare ina Sallar isha’i na kwanta kwana biyu ko adduar bana iyayi saboda zazzabin dare dake rufeni.
Washegari da wuri nake da lecture dan haka da wuri na fita, Ina gama lecture na ƙarshe da rana, jikina kamar ba nawa ba. Kaina na sarawa sosai, idanuna na juyawa, ƙafafuna na rawa. Komai yana tafiya da ƙyar. Jikina yayi rauni fiye da yadda nake tsammani. Na dan tsaya gefe a bakin titi ina satar numfashi, sai na ga chemist a can nesa kadan. Na tattara ƙarfin da ya rage min, na nufi wajen.
“Yaya lafiya?” Cewar mai chemist din bayan na shigo da wata irin kwana da take nuna ba lafiya nake ba.
“Zazzabi ne, ciwon kai, da ciwon jiki.” Na fada cikin sanyin murya.
Ta duba min wasu magunguna, ta duba farashinsu sannan ta ce, “₦8,000 ne gaba daya.”
Na tsaya da baki a buɗe. ₦10,000 ne kacal ke hannuna –kudin da nake ajiyewa don wani abu da nake so nayi na kaina, abu mai muhimmanci. Amma yanzu lafiya ta fi. Ba zan iya hakura da magani ba.
Na dube ta, na ce “To ki bani.” Na ciro kudi na ba ta, na karbi magungunan, na fita da wata irin karyewar zuciya.
Ina shiga gida da magunguna a jaka, jikina a mace, sai Mumy tace daga saman bene.
“Ramlah ki shirya da sauri. Za mu gidan ‘yan uwan Abba. An yi rasuwa.”
Sai da gabana ya buga. Zuciyata ta fara faduwa. Na daina motsi tsawon dakika biyu. Mutuwa kuma? Ko dai... Khalil?
Na ɗan taka kadan, na ce a hankali, “Waye ya rasu?”
Ta juyo tana daure fuska tace, “Kakar su Abba ce. Wacce take zaune can kusa da su.”
Na sauke ajiyar zuciya, “Allah ya jikanta.”
Nayi shiru, na shiga ɗaki a hankali, na canza kaya. Hijab na dogo na saka, na fesa turare, Ina fitowa sai muka hadu da Bilkisu a waje
Na nufi gaban mota kamar yadda na saba. Nayi niyyar buɗe ƙofa na zauna. Sai kawai na ji tsawa daga Bilkisu “Ke gidan ubanki ne ke kadai? Ko motar ubanki ce? Wuce can, ki shiga baya!” Na tsaya, na kalle ta cikin mamaki da haushi. Amma na tuna tafiya ce ta gaisuwa. Na kasa cewa komai. Na juya na bude ƙofar baya, na zauna. Har sai da hawaye suka taru a idona amma na danne su.
Mun isa gidan cikin natsuwa. An sa kujeru a farfajiya. Muka zauna. Ana ta shigowa da ficewa, ana karɓar gaisuwa.
Ni kuma na zauna a gefen Mumy, cikin nutsuwa. Magungunan da na sha sun fara rage radadi, amma ba su kawar da gajiyata ba. Duk da haka, na zauna cikin ladabi da kamun kai. Na rufe bakina, na sunkuyar da kai. Amma a lokacin ne wasu suka fara gulma daga gefena. Wata dattijuwa daga cikin ‘yan uwan Abba ta fara magana da wata a kunnenta, amma duk inajinsu.
“To Ramlah ce dai kinganta kamar yar labarawa ko dayake balarabiyar ce tunda uwarta haka take. dayake tafara zuwa makaranta mai shigen tsada da kudi fa. Amma naga kamar ba ta damu da Khalil ba. Yaron har yanzu yana jinya, amma ki kalleta ko ajiƙinta ko adan yatsanta ahaka kamar ta Allah sai munafurci.”
Wata tayi dariya ta ce, “Ai ni nasan dai babu yanda za ayi su yi aure. Dama ita ce ta rikita Malam dinnan. Tace wai Khalil bai dace da ita ba. Dan taga tanada kyau.”
Suka sa dariya. Wani daga cikinsu ya ce, “To dan tanada kyau sai tafara raina mutane?.”
Na sunkuyar da kai. Na ƙura ido cikin tabarma. Na ma rasa wane hawaye ne nake kokarin dannewa. Gaskiya ba su san ciwon zuciya na ba. Maganar su ta fi zafin maganin da na sha dazu.
Suna ci gaba da zance. “Ai idan ba masu kudi ba wannan yarinyar bata auren dangi tabbijan bakuganta ba kamar ita tayi kanta?.”
Na ci gaba dayin shiru. Ko kallonsu ban yi. Ban ma motsa ba. Na ce a raina, “Na haƙura. Zan yi shiru, zan barwa Allah.Ina zaune, Bilkisu tana gefe tana kallona da idon ƙiyayya. Har da girgiza kai tana dan gunguni. Idan na duba, sai ta kau da kai kamar ba ni take kallo ba. Amma nasan zuciyarta kamar wuta take yanzu ni ce kowa ke magana akai haushina take ji. Bilkisu ta dade tana jin cewa rayuwata bata dace da jin daɗi ba.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ARBA'IN DA TAKWAS
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Muna zaune a gefe, nayi shiru kamar ba ni ba. Na dafe kaina saboda ciwo yana ƙara girma. Duk da magungunan da na sha da safe, kamar ba su aiki. Idanuna suna sauka da wahala, zuciyata kuma cike take da abubuwa da yawa. Har yanzu nake jin kalaman gulmar da suka yi a kusa da ni, suna yawo cikin kunne na kamar amsa.
Yaya za a ce gidan mutuwa ya koma gidan gulma? Gidan da za a tuna da mutuwa da addu’a ya koma wurin cin zarafi da wulakanci?
Wannan tambaya ce kawai da zuciyata ke maimaitawa. Sai kuma naji muryar maza suna shigowa harabar gidan sunata gaida mutane suna gaisuwa..
Alhaji Munzali ne kawun su Abba, babban mutum a cikin ‘yan uwan Abba. Idan ya shigo, kowa yana nutsuwa, domin mutum ne mai daraja. Amma yau kam, fuskar sa ta bayyana damuwa. Kamar wanda ya jima da kuka.
Yana shigowa, sai kawai ya kalli mutanen gidan. Kowa yayi shiru. Sai ya ce da murya mai rauni “Khalil ya rasu. Allah yayi masa rasuwa yanzu.”
Wani dumi ne ya zube min a kai. Wani sanyi mai ƙara daka zuciya ya ratsa gabadaya jikina. Kamar wata iska ta buga ni daga baya. Komai ya tsaya. Kamar rayuwa ta daina tafiya. Na rasa numfashi. Ina kallon Alhaji Munzali, baki na a buɗe, zuciyata na harbawa da ƙarfi. Na buɗe baki ina so in ce wani abu amma babu muryar da zata fito. Idona ya raina gani. Idanuna sun jike, sun rikice. Na ji kamar zan fashe. “Khalil?” Na furta a hankali.
Sai kawai niyi wani ƙara da karfi “A’a! Khalil bai mutu ba! Don Allah kuce karya ne!” Kowa ya juya kaina. Kafin wani ya iya tashi na saki ihu mai karfi.Na kamo hijabi na na fizge, na durƙusa kasa, sannan na fadi a kasa kamar an sare itace,Na suma. A gaban kowa.
Mutane suka fara kururuwa. Wata ta kama hannuna, wata ta duba idanuna. “Ta fita hayyacinta!” wani yace. “Da sauri a kira mota, a kaita asibiti!” Alhaji Munzali ya dakko waya da sauri ya kira Abba. “Ku zo da mota! Ramlah ta faɗi bata motsi.”
Yaya Billy da Mumy da wasu daga cikin dangin gidan suka tsorata. Kamar abin ya fi yadda suka zata. Mumy ta kasa cewa komai, idonta ya ƙafe a kaina..
Lokacin da na fadi a gidan gaisuwa, ban kuma san kaina ba. Na fadi a kasa tamkar wadda aka cire rai. Kamar wani iska ya kwashe ni, ya tafi da zuciyata zuwa wani wuri nesa. Komai duhu. Komai shiru. Ina cikin wata irin ƙasa da ba na iya kiran ta duniya ba.
Gaba daya jikina ya mutu. Na shiga doguwar suma. Likitoci suna ta kokarin dawo da ni hayyacina. A gaggauce aka kaini asibiti cikin mota, aka shigar da ni zuwa gaggawa (emergency ward). Na kwanta a gadon asibiti, hannaye na kwance, numfashina a hankali. Kamar numfashin wanda ke cikin mafarki, ba tare da mafarkin yana da dadi ba.
Likita ya dubi nurse yace, “Ta shiga doguwar suma. Amma har yanzu zuciyarta na bugawa. Jikinta na da rauni sosai.”
Bayan kusan awa biyu, na fara motsawa kadan. Na buɗe ido a hankali. Ina duba sama. Idona na yawo, amma zuciyata a cike take da wani irin zafi da na kasa fassarawa Sai na saki wani irin ihun da ya girgiza dakin
“Khalil! Khalil! Don Allah kar ka barni! Ka dawo! Khalil!” Na sanya kuka. Na fara jijjiga jikina kamar ina yaki da wani abu da ba a gani. Nurse ta rike ni da sauri, ta kira likita, ta kira family dina da ke bakin asibiti. Abba da Mumy suka shigo. Na dago kai na ina kuka, na ce, “Yace min zai dawo. Me ya sa bai dawo ba? Don Allah ku gaya min ba gaskiya bane…” Na sake faɗi. Likita ya duba ni, ya ce da nurse “Ta rasa jini. Blood pressure dinta ya sauka ƙasa sosai. Sai an sanya mata jini cikin gaggawa.” Nurse tace, “To yanzu sai mu fara gwajin wanda ya dace da jinin nata. A gaggauce aka fara duba wanda jinin sa zai dace da nawa. Ina kwance a gado, ina cikin ciwo da rashin hayyacina, amma jiki na yana kokarin faduwa gaba daya. Wata nurse ta zo ta dubi Abba “Dan Allah malam, akwai wani daga cikin ‘yan uwa da za mu iya amfani da jinin sa? Idan babu, za mu je asubuti mu siya.” Abba ya ce, “Ku fara gwada jinina dana kanina .” Aka fara da su. Sakamako ya fito bai dace ba. Aka gwada na wani daga cikin dangin abba suma bai dace ba. Har ana tunanin sai an je asibitin gwamnati don a samo jini cikin gaggawa.
Sai likita ya ce, “Mu kira Dr Hari shima babban likitane Da aka duba nasa, sai aka ga jinin sa ne ya dace da na Ramlah.
Cikin sauri aka saka mata allurar kariya, aka cire masa jini, aka soma shiryawa don sanyamin.
Mumy na zaune kusa da gadon asibiti, tana riƙe da hannuna kamar tausayinta ya kai kololuwa. Ita ce ke girgiza kai tana cewa, “Ya Allah ka tausaya wa Ramlah. Zan rasa komai idan na rasa ta.”
A gaban mutane sai tana share hawaye, tana nuna kamar tafi kowa damuwa. Har mutane suna ce mata, “Mumy ki kwantar da hankali. Allah zai bata lafiya.” Sai ta ce, “Ramlah rayuwata ce. Ko ban nuna ba, ina sonta fiye da rai na.” Amma a cikin zuciyarta, ba haka take ji ba nasani. Abba ya ce da ita, “Ki zauna anan da ita, ni zan je ayi jana’izar Khalil.”
Ta ce, “To, Allah ya karɓe sa ya yafe masa ya gafarta masa. Ka je, zan tsaya da ita.” Sai ta mayar da murmushin tausayi ga mutanen da ke kusa. Amma da aka fita, bayan mutane sun bar dakin, sai tace “Yanzu ai rayuwar ki tafara lallacewa ramlah sai kin zamana baki da gata koda na sauro ne sai tasanya dariya. Allah ya ɗauki abin da zai jawo min matsala.”
Sai tayi wani siririn dariya.
Ina kwance Jini yana shigowa jikina a hankali. Amma har yanzu ina cikin doguwar suma. Nurse suna lura dani.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ARBA'IN DA TARA
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Cikin dare na farka da tsananin kuka. Na farka kamar wacce aka tasar da ita daga mafarki mai zafi. Na dinga jijjiga jikina, ina girgiza kai, hawaye suna zuba a idona sosai. Sai na fara magana da karfi “Khalil! Khalil! Don Allah kar ka bar ni! Ka dawo mana! Ka ce min zaka warke…” Na tashi daga gadon da nake kwance, da ƙyar na ɗaga jikina. Jiki a mace, amma zuciyata kamar wuta ake hura mata. Na dinga kokarin fita daga dakin asibiti da ƙarfi, kiran sunan Khalil kamar zan same shi a wani sashi. “KHALIL! KHALIL!!” Na dinga kiran sa cikin murya mai cike da raɗaɗi.
Mumy tana zaune a gefen kujera. Tayi kamar tana bacci, amma na tabbata tana jin kiran da nake yi. Ta motsa, amma ta yi shiru.
Nayi ward din da ƙafa na ina rawar jiki. Ihu na ya firgita ma’aikatan asibitin. Nurse biyu da wani likita suka fito a guje. Daya ya ce, “Rikota! Har yanzu tana cikin shock, zata iya cutar da kanta!”
Suka riƙe ni da ƙarfi, suna kwantar da ni da tausayi. Na dinga fizge-fizge, har suka ɗauko allura suka yi min maganin saboda zazzabin dake jikinai. Har sai da jikina ya yi sanyi, suka dawo da ni dakin.
Nurse ta ɗan tafa kafadar Mumy
“Mumy, ki kula da ita hajiya yanzu duk ihun nan nata bakiji ba saboda Allah data fita babu kowa a ward dinfa?.”
Mumy ta jinjina kai. Sai suka fita suka bar mu. Ina kwance a dakin, ban iya motsawa, amma idona biyu. Ba bacci nake ba.
Mumy ta ɗauka nayi bacci ne. Sai ta sauke numfashi. Ta juyo ta kwanta a kujera, sai na ji ta fara magana “Ni baiwartace da zan tsaya ina gadinta ji wata nurse da maganar banza ai data fita tabi duniya yafi mana, haka kurum
Ta gyara kwanciya. Tana kokarin komawa bacci.
Ni dai ban motsa ba, amma zuciyata ta ji komai.
Da safe, ina kwance ban iya magana. Jikina ya yi rauni, numfashi na yana fitowa a hankali, kamar na wanda ba ya da karfi.
Sai dai har yanzu zuciyata ta kasa yadda cewa Khalil ya mutu.
Wata nurse ta shigo ta duba ni. Tace, “Alhamdulillah, kina samun sauki. Amma har yanzu jiki ba ya da karfi sosai. Sai a ci gaba da lura da ita.”
Bayan lokaci kadan, su Abba suka shigo da wasu daga cikin ‘yan uwa. Sun tsaya a bakin gadon, wasu na cewa “Allah ya taimake ki, Ramlah.” Wasu na shafa kafada, wasu na kallona da tausayi. Amma babu wanda ya san yanda nake ji.
Ban ce komai ba. Ina jin kamar wata hasara ce ta cika zuciyata har tana hana ni magana. Sai dai hawaye ne kawai suke kwaranya daga idona, koda ba na kuka da murya.
Sai ga Yaya Mujittapha, dan uwan Khalil na jini, wanda yayi karatun addini sosai, yana da nutsuwa da mutunci. Yana zuwa ya tsaya a gefen gadon. Ya kama hannuna a hankali.
Shima idanunsa cike da hawaye. Bai ce komai ba na wani lokaci. Sai ya daure, ya ce Ramlah… Khalil ya gaya min wani abu kafin ya rasu. Yace idan wani abu ya faru da shi, ki sani cewa ba ki da laifi. Ki yi masa addua. Kada ki zubar da hawayen da bai cancanta ba. Ki ci gaba da rayuwarki. Ki gina kanki. Kiyi masa addu’a.”
Na fashe da kuka. Na saki hannunsa, na dafe kaina “Khalil! Khalil!! Me yasa ka tafi?” “Kaina! Kaina!!” Na hau ihu, na zame da ƙarfi, jikina ya fara rawa. Ya Mujittapha ya firgita, ya ce “Nurse! Nurse!” ya fita da gudu ya kira su Abba da Nurse.
Nurse ta shigo a guje, Abba ya biyo bayanta da wasu daga gidan. Suka kama ni. Na shiga fizge-fizge, sai dai a ƙarshe suka danne ni, suka sake yi min allura. Jikina ya lafa. Idona ya lumshe. Numfashi ya koma a hankali.
Yayin da ake zaman makokin Khalil a gida, ni kuma a nan asibiti nake kwance. Ina kwance cikin rauni da zafin zazzabi. Cikin damuwa da rashin kuzari. Cikin raunukan da ba likita zai gane ba, sai zuciya mai fahimtar zafin rasa masoyi. Cikin wani salo mai ban tsoro, na kasance wacce ba ta da ƙarfi a jiki da zuciya. Ranar da aka tafi da shi, ni ban je ba. Ban gan shi ba. Ban ga jana'izarsa ba. Amma na ji kamar raina yana tare da gawarsa.
Yau da asuba, zazzabi ya taso min sosai. Na tashi da kyar na yi sallar asuba, jikina duk yana rawa. Na ɗora hannu a ƙirjina, ina jin bugun zuciyata da ƙarfi. Baya ga zafin rashin lafiya, bayanin jana’izar da akayi min jiya yana ci gaba da dawowa a zuciyata kamar fim.
Nurse ta shigo da allura a hannu, tana murmushi kadan kamar tana tausayina. Ta duba zafin jikina ta ce “Zazzabin ki yana da yawa. Amma da sannu zaki warke. Ki ƙarfafa zuciya.” Na kada kai kawai. Na kasa magana. Idona sun kumbura da kuka da rashin bacci. Daga nan ta fita Kusan mintuna talatin da nurse ta fita, sai na ji ana bude ƙofar dakin. Sai ga Maman Khalil da wasu ‘yan uwanta mata biyu. Suka shigo ba tare da sallama ba, ba tare da murmushi ko rahama ba. Kamar masu aikin bibiya suka shigo.
Na juyo na kallesu. Cikin ciwo, na ɗan daga kai kawai. Ina son na ce da su “Sannu da zuwa,” amma babu muryar da zata fito.
Sai Maman Khalil ta tsaya a gabana, ta dubeni da idon da ya cika da tsana, sai ta ce da karfi: “Ke ba kya jin tsoron Allah ne? Da kika kashe min ɗa! Kin tsaya kika hana shi kwanciyar hankali har Allah ya karɓi amanarsa!”
Na buɗe baki da mamaki. Kamar mafarki nake. Na sauke idona kasa, hawaye suka zubo daga idanuna. Wata daga cikin su ta ce “Allah zai saka mana! Rayuwa ba zata bar ki lafiya ba. Zaki ɗanɗani kunci.yanzu kuma sai ki ɗanɗani sakamako.”
Na kara juyar da idona gefe. Na ma rasa inda zan kalle su. Wani abu a zuciyata yana ce min “Toh ni fa ban yi komai ba…”
Amma ban iya kare kaina ba. Babu karfi, babu lafiyar jiki, kuma babu wanda zai tsaya min.
Suka ci gaba da maganganun su . Sun yi tsawon lokaci suna zagina, suna fadin abubuwan da suka firgita zuciyata. Wasu daga cikinsu suna cewa “Ai ita ce ta jawo wa ɗanmu cutar da ta kashe shi.”
“Ta raina mu, yanzu zata ga abinda rayuwa ke nufi.: “Zan tabbatar ba zata cigaba da karatu ba...” Daga karshe, suka juya suka fita. Ba su tsaya ko don su dubi yanayina na ciwo ba. Ba su yi addu’a ba.