Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 29
Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 29: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 29. Ayshatu ta ci gaba da cewa “Na zaɓi…
3,374 words
Ayshatu ta ci gaba da cewa “Na zaɓi mijina lokacin da yake da ƙarfi. Kuma yanzu da yake cikin rauni, sai in gudu? Kin manta ke da ni matan musulmi ne. Miji ba wai kamar yadi bane da idan ya ƙyama, a canza ba. Miji kalma ce ta amana. Kuma ni da amana nake zaune da shi kinfi kowa sanin As'ad yafi karfina Allah ne yabani shi kuma har dake acikin masu irin wannan kalamin?.”
Anty ta sunkuyar da kai.
Ayshatu ta ce “Wanda yake bani lafiya a zuciyata, wanda yake bani kwanciyar hankali a gida, ya fi wanda zai bani daɗin minti goma, ya barni da zubar da mutunci. Ki bar wannan magana,anty, Bazata canza ni ba.”
Sosai ranta yaɓaci Gabadaya bakin ciki ya cikata karshema tace anty zanfita akwai masu jirana please.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA HAMSIN DA BIYU.
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Gidan ya yi shiru. Fitilar cikin falon ta haskaka lafazin zaman masu daraja. Fitilun bangarori sun kashe kansu kamar sun san ana shirin fita. Ayshatu ta tsaya a gaban madubi tana kallon kanta. Sanye take da abaya mai sheƙin da launin baki, gashinta a zube, Takalmanta sun jitu da kayan jikinta Jimmy Choo heels, baki masu ɗan ɗanƙo. Hannunta na ɗauke da clutch bag daga Louis Vuitton daidai da ɗan ƙamshi na Maison Francis Kurkdjian da ke tashi.Idonta yana nuna cewa akwai abubuwan da ta riga ta ɗauka a zuciya soyayya, ƙoƙari, rashin fahimta, da gaskiyar zuciya.Tana kallon kanta, sai ta faɗi a hankali “Kada ki manta da ke. Kada ki manta da soyayyarki, da kima ki. Ko duniya tana magana, ke ki tsaya daram.”
Ta ɗauki wayarta da jakar hannu, ta fita. A kofar gidan, Rolls-Royce Ghost mai sheƙi ta tsaya, direba Pascal ya fito ya buɗe mata ƙofa
Cikin motar, an kunna AC mai kamshin vanilla, fitilar cikin ta launin ruwan hoda, kuma komai sanyi da tsabta.
Ayshatu ta zauna a baya, ta jingina da kujera. Direban ya dubeta ta madubi.“Madam, café ɗin da ke Avenue Montaigne, ko?”
Ta ɗaga kai a hankali. “Eh. Wanda ke kallon fountain ɗin nan. Ina so na sha ruwa mai sanyi... cikin natsuwa.”
Motar ta soma tafiya, tana sauƙin jiki, kamar ba a tuka ta ba.
Tana tafiya, Aysha ta lumshe ido. Tana tunani. Tana jin numfashinta. Tana jin duniyar na yawo amma tana buƙatar kwanciyar hankali.
A café, ma’aikatan waje sun shirya, masu bude ƙofa, masu sa hannu akan kujera.
Wata mata mai fata fari da tabari a fuska ta buɗe ƙofa da girmamawa. “Madam Aysha. Welcome.”
Aysha ta sauka a hankali. Tafiyarta ba ta da sauri, amma tana da nauyin kima. Café ɗin yana kallon wata fountain da ke fesa ruwa da salo, tsuntsaye suna shawagi a sararin sama, iska tana busawa da sanyi.
Aysha ta zauna. Ta buɗe menu, amma idonta bai karanta ba. Ta kalli Fatima ta mika mata
Fatimq ta ɗora kofi a bakin tebur, tana kallon Ayshatu. “Ina kallonki fa Aysha. Ki dai gaya min gaskiya.”
Ayshatu ta ɗan murmusa. “Me kuma?” Ayshatu ta ɗan lumshe ido. “Ban fahimceki ba.”
Fatima ta matso da kujerarta. “Kinamun ƙarya dai. Ki ce min kina tare da miji, amma miji wanda baya iya biya miki bukata? Haba Aysha. Da wayewarki da hankalinki da kyanki??
Ayshatu ta juyo da mamaki. “Fatima, me kike nufi da ‘biyan bukata’?”
Fatima ta saki dariya mai zafi. “Oh? Wato har yanzu ba zaki yarda ba? Ki daina ɓoye damuwarki. Ke mace ce! Sha’awa fa ba laifi bane. Kuma ki sani duk kalaman soyayya ba za su rage sha’awarki ba. Duk da kudi, duk da lambu da kayan Alfarma... ai mace ba fata kawai take so ba, tana buƙatar kulawa ta jiki.”
Ayshatu ta ɗan dago kai, fuskarta ta canza.
Fatima ta ci gaba:
“Yanzu ki fada min gaskiya taya za ki zauna da namiji wanda kullum gantale yake, wanda babu motsi, amma kullum kalaman soyayya yake jera miki? Ke fa ba budurwa ba ce, Wallahi da nice ke da tuni na duba gabana. Maza nan sun cika, babu lokacin jira.”
Ayshatu ta zuba mata ido. Idonta ya yi ja.
“Fatima… ki saurare ni.”
Ta matso da kujera gaba, ta furta cikin sanyi da karfi a lokaci guda
“Kin san me nake da shi da baki da shi? Ni ina da abin da ku baza ku gani ba zuciya mai kyau Kauna ta gaskiya. Fahimta. Karɓa. Tausayi. Kuma da duk abinda kika lissafa sha’awa, jiki, motsi –babu wanda ya fi waɗannan daraja a soyayya.”
Fatima ta dan ja bakinta gefe. “Zuciya dai bata cire kishirwa ba.”
Ayshatu ta dafe kirjinta. “Amma zata hana mace zama tamkar rakumi mara ruwa. Ni fa bana son abun sosai yarana fa biyu shekarar mu nawa yanzu? Nazama shi yazama ni Ina sonsa saboda yana kula da ni a lokacin da maza da dama ke wulakanta mace idan ta ce ‘ban ji daɗi ba’. Yana sauraren kuka na. Yana tuna lokacin da nake fara karatu. Yana tuna ranar da muka haihu. Me zai hana in kasance da mutum wanda ya ba ni komai face ɗaya lafiya, wanda kuma yana kokarin dawo da ita?”
Fatima ta ɗan sauke murya. “Toh, ina nufin fa… ki lura da kanki.”
Ayshatu ta ce, “Ina lura. Kuma na gane ba kowane abu kike samu a gado ba. Wasu abun sai ka nema a gwiwa, cikin addu’a da hakuri. Shi yasa ni bazan canza wannan soyayya da duk masoya ‘tsala-tsala’ ba.”
Fatima ta ɗan sunkuyar da kai. “Ki yafe ni, Aysha. Kawai na damu da ke.”
Ayshatu ta ce da murmushi mai zafi, “Idan kina damuwa da ni, ki tsaya a gefe kina duba yadda ƙauna ke ƙarfafa wanda duk duniya ta ce ‘ya kasa’.”
Fatima ta ɗan ɗaga kai, idonta cike da tunani. Ita daman baƙin cike takeyiwa kawartata so takeyi takashe auren dan duk ciƙinsu tafi kowa samu da wadata.
*****
Yana zaune a cikin wani shahararren café da ke tsakiyar Casablanca. Gaban sa akwai ƙaramin kofin Moroccan tea, tururin shayin na tashi yana haɗuwa da kamshin mint.
Cikin shigar farar riga da wando ruwan toka, yana ta danna wayarsa da yatsu masu tsabta.
Ya gama kira da Mai Martaba, wanda ya masa magana “bana jin daɗin jinkirin ka. Kana buƙatar dawowa. Cikin satin nan ka bayyana a gabanmu. Ina buƙatar ganinka da kaina.” ya sunkuyar da kai. “Na'am, ranka ya daɗe. Zan shirya, insha Allah.”
Ya ajiye wayar. Zuciyarsa bata da nutsuwa. Ba don kira daga Mai Martaba ba. Kafin ya iya miƙewa daga kujera, sai wayarsa ta sake ɗaukan karar kiran Ayshatu.
Ya kalli sunan Habibiyata Sai murmushi ya bayyana a leɓensa, ya dan latsa “accept”.
“Assalamu alaikum, Aysha.” “Wa alaikum salam, Habibie. Na gaji da ganin hoton ka inason ganinka kusa dani.”
Murmushin da mai tsada yayi yace “Ina jinki, masoyiyata.” “Nace ko zaka iya kara ganin likitanka a nan Morocco. Ka san fa bana jin daɗin yadda ka ke yawan shiga damuwa yanzu.” Yayi dariya mai taushi.
“Aysha, likitoci nawa kike so nagani? Gaskiya magunguna sun ishe ni. Kowanne likita yana bani kalma daya. Ki manta da wannan.”
Aysha ta dan yi shiru. Sannan ta ce da hankali “Habibie, ba a gajiya da neman lafiya. Koda ana da kwanciyar hankali, mutum yafi jin daɗin samun tabbatacciyar lafiya. Ka kara ƙoƙari mana, ka sake ganin wani.”
Shiru ya shiga cikin muryarsa. Ya dago idonsa daga kofin shayi, ya duba sararin sama, kamar yana karanta abinda ya kasa faɗa.
Sai ya ce da sanyi mai sosa rai “Toh, Aysha. Zanje nagani gobe… Tunda kema kin gaji da namiji da baya miki komai Kin gaji dani ne, ko Aysha? Kin gaji da rashin amfanina? Kin gaji da zama da mutum wanda ba zai iya biyan ki ba a matsayin miji?”
Kalamarsa ta tsaya a kunne kamar ruwa da aka zuba a cikin toka. Aysha tayi shiru. Kamar kalmar ta daki zuciyarta.
Ta buɗe baki a hankali. “Habibie… Ban ce na gaji da kai ba. Na ce… ka ƙara ƙoƙari, domin ina son ganin ka da ƙoshin lafiya.
Sosai ya sauke ajiyar zuciya. Murya ta fara canza launi. “Na san baki ce haka ba. Amma bana jin kaina yadda nake. Wani lokaci nakan ce a zuciyata Me yasa mace mai kyau, mai tsafta, mai haƙuri kamar Aysha zata zauna da ni har yanzu?”
Aysha ta ce da kwantar da murya“Ka fi gabanka daraja. Ka fi karfin jikinka. Ka fi karfin lafiyar da ta ƙi tsaya maka. Ni ina sonka saboda zuciyarka, kulawarka, fahimtarka. Ba saboda... gamsuwa ba. Na riga na daina buƙatar hakan tun ranar da na fahimci kai da ciwonka na buƙatar ƙauna fiye da komai.”
Sosai ya saki numfashi mai zafi. Ya zauna. Hannunsa na rawar jiki.
“Ina jin kamar na kasa zama namiji. Kuma kina ci gaba da nuna min cewa ni har yanzu ina da daraja… hakan yana min ciwo, Aysha.”
Ayshatu ta ce da sauri, “ Wai Habibie shekara nawa kana gamsar dani? Shekaru ma yakamata nace ni yanzu da girma yafara kamani bari ni in fada maka kai daraja ce a wurina. Kai mijina ne, uba ne ga yarana, aboki ne, garkuwa ce. Idan babu karfi, akwai ƙarfi a zuciyarka.”
A can bangaren Morocco, Sosai ya lumshe ido. Ya kama kansa da hannu daya.
A cikin duk shirin tafiya, da kasuwanci, da kira daga masu daraja wannan kalmar Aysha ce ta fi komai nauyi.
“Zan je. Zan je gobe. Ba don magani kawai ba. Don ke.”
*******************************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA HAMSIN DA UKU.
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Washegari bayan hirarsa da Ayshatu, Sosai Yashiga damuwa ya zauna cikin shiru a ɗakin hotel ɗinsa mai matakin “presidential suite” a Casablanca.Girman ɗakin bai dame shi ba. Tagogin gilashi sun buɗe zuwa ga teku, hasken rana yana shiga cikin ɗakin a hankali, amma duk da haka, zuciyarsa cike take da kalmomin Ayshatu
“Kai daraja ce a wurina…”
“Ni bana sonka saboda jikinka…”
Wannan kalmomi suna yawo a cikin kansa. Sun damesa ba don sun ci masa rai ba, amma don sun faɗi gaskiyar da ya daɗe yana ƙoƙarin guje wa. Sai ya ɗauki waya. Ya kira direbansa.
“please, ka kai ni Centre Hospitalier Universitaire.” Wannan asibiti ne mafi girma a Casablanca, inda manyan likitoci ke duba matsalolin da suka shafi hormones da lafiyar maza.
A VIP lobby ya zauna, cikin farar rigar linen da wando mai sauƙi. Likita Faouzi ya fito daga ofis. Dattijo ne mai kamala da nutsuwa.
“Yashiga?” ya ce da murmushi. “Please, shigo ciki.” ya shiga. Ofishin ya cika da kamshi da tsabta. Likitan ya zauna yana kallon takardun da aka aiko masa tun tuni. Ya fara da cewa, “Na duba gwaje-gwajenka. Matsalar da kake da ita ana kiranta androgenic decline raguwa ce ta testosterone da karancin jinin da ke kai kuzari.”
Sosai ya lumshe ido, ya ce da murya mai rauni, “To, likita… akwai mafita kuwa?”
“Eh,” Dr. Faouzi ya ce. “Amma tana ɗaukar lokaci. Maganin hormones ne, da sauya salon rayuwa, da kuma goyon bayan zuciya. Kana buƙatar hutu. Kana buƙatar ƙarfin gwiwa. Kuma kana buƙatar ka yarda cewa har yanzu kana da daraja.” ya sauke ajiyar zuciya.
“Ina tsoron kada in rasa jin kaina kamar da,” ya faɗa.
*****
Da dare…
Ya kira Ayshatu daga dakin hotel ɗinsa. Tana kwance a gado, rigar barci a jikinta, tana murmushi da ganin sunan wayarsa.
“Ka yi kuka ne?” ta tambaya da dariya kaɗan.
“Ban kuka ba,” ya ce, yana murmushi. “Amma na kusa hakan.”
“Likitan fa?”
“Yace akwai mafita. Amma sai da hakuri. Da magani. Da taimakon mace mai ƙauna.”
Aysha ta dafe zuciyarta. “Ni zan kasance tare da kai, Kullum. Ko daga nesa.”
Yace, “In na dawo, zamu tafi hutu. Ba Maldives ba. Ba Paris ba. Sai inda zuciyarmu za ta huta.” “Zuciyata tana tare da kai,” ta ce.
*********
PARIS
Zaune take a cikin ɗakin salon penthouse a kusa da Eiffel Tower. Glass na kofar balcony a buɗe, iska mai sanyi tana shiga cikin ɗakin a hankali. A gabanta, teburin shayi ne mai tsabta, akwai cup guda, sai tiren croissant da bata taɓa ba. Zuciyarta cike take da tunani kala-kala. A waje ana ta motsi motoci suna wucewa da sauri, mutane suna kallon shaguna, amma Ayshatu ba ta jin komai sai ƙaran zuciyarta.
Ta ɗauki cup ɗin shayi ta sha sip ɗaya. Sanyi da ɗan ɗaci ya cika bakinta, kamar yadda maganar Fatima kawarta ta cika zuciyarta.
“Wai yanzu ke Aysha, haka zaki zauna? Miji baya biya miki bukata, ba da jiki ba, ba da kulawa ba... Kuma kina jurewa haka? Kinada kyau, kinada kudi, ga maza nan da zasu iya yayemiki sha’awa. Be wise mana.”
Ayshatu ta haɗe gira. Kalaman Fatima suna yawo a kanta kamar an kunna speaker a kunne. Ta san Fatima ba muguwa bace. Tana faɗar gaskiyar da yawancin mutane ke tunani, amma basu faɗa ba. Amma kalmomin nata suna ƙara zafi saboda akwai ɗan gaskiya a ciki.
“Kinada right. Kinada iko. Kinada kyau da kudi. Kuma mijin me? Kalaman soyayya da hawayen da ba su da amfani.”
Ta ajiye cup ɗin shayin, ta ja numfashi. Tana zaune a kujera, kafa daya a kan ɗayan, tana kallon hoton Eiffel Tower daga cikin gilashi.
Wayarta ta ɗauka. Tana jin komai dai dai tana da komai, amma tana jin ba komai a cikinta.
Ta shiga Instagram.
Scrolling take, tana kallon hoton wasu ma’aurata suna dariya a gaban wani wuri mai kyau haka kawai ta danji wata irin gasa a zuciyarta. Sai ta shiga shafin wani guy mai kyau wanda take yawan gani a Explore.
Guy din yana sanye da kaya masu kyau, gashi mai tsabta, lafiyayyen jiki. Sabon hotonsa na bakin teku ya ja hankalinta sosai.
“Handsome guy,” ta ce a zuciyarta, tana dannawa like.
Sannan ta shiga DM, ta sanya "Hot man 🔥"
Ta fita daga shafin, tana dan murmushi kaɗan. Ba dariya bane, murmushin wace ta san me take yi, amma har yanzu tana jin nauyin zuciyarta. “Sosai As'ad yana sona. Amma yanzu fa, ya zama wani irin mutum mai tausayin kansa da kalaman da basa motsa jiki. Kalaman soyayya da hawaye? Me zasu canja?” Ta ɗauki jakarta Gucci, ta ajiye a kusa da kujerar window. Tana son fita, amma ba inda take so ta je. Paris na motsi a waje, amma zuciyarta na cikewa da shakku.
Ta girgiza kai. Wannan kalmomi suna da daɗi, amma “Ni kuma fa? Shin ina da haƙƙin jin daɗi? Ko dole ne in zauna ina jiran shi ya murmure ne?” Ta tashi, ta nufi mirrow. Tana kallon fuskarta, wacce take cike da kyau, amma idanunta cike da fargaba. Tana son a ce ta daure, amma zuciyarta na faɗin abu biyu “Jira.” Da kuma “Bari.” A waje, iska ta fara ƙaruwa. Clouds sun rufe hasken rana. Tana ji kamar Paris ma na jin abinda ke cikinta. Ta koma ta zauna. Ta ɗauki wayarta, ta shiga chat ɗin As’ad, ta duba message dinsa na karshe “Ina fatan kin ci abinci. Ina jin ki kullum.” Ta rubuta “Na ci.”
Sannan ta ɗora da“Kana tunanin wannan ya isa?” Ta ajiye wayar, bata danna send ba.
Ta rufe ido. Idanuwanta sun cika da hawaye, amma ba sa gangarowa. Sai zuciyarta take rawa. “Akwai lokacin da soyayya ke gina mace. Amma akwai lokacin da zata iya karyata ta. Na san bana mugunta, amma ni mace ce. Ina da jiki. Ina da zuciya. Kuma ina da burina.” Sai ta danyi shiru. Kamar tana sauraron zuciyarta tana yanke shawara. A hankali, ta sake buɗe wayar. Sai ta koma message ɗin da bata tura ba... ta share shi.
*************
MOROCCO
A Morocco, cikin wani katafaren ginin da aka lulluɓe da gilashi mai kyalli, zaune suke a babban ofis wanda aka tanadar don tarurrukan manyan attajirai.
Abokan As’ad kusan goma ne, kowa sanye da kaya masu alfarma, wasu cikin suit, wasu cikin babban riga na gida, dukkan su masu kamfanoni, kadarori, da sunaye a cikin manyan jaridu na duniya.
Sun zauna cikin ɗakin taro mai sanyi, yana ɗauke da kujera na fata, gilashi da coffee tables masu tsari. A tsakiyar tebur akwai kayan ciye-ciye na musamman daga Marakeshalmond-stuffed dates, saffron tea, da pistachio rolls.
Hira ta kaure. Sai dariya take tashi lokaci-lokaci. Abubuwan da ke gudana sun shafi mata.
Wani daga cikin su Alhaji Muqaddam mai shagunan zinariya a Istanbul, ya ce yana dariya "Wallahi mace sai godiya idan tanada matsala. A gida sai koke-koke. Kai! Shi yasa na karo aure kawai. Kamar famfo ne in ɗaya ta ƙafe, ɗaya tana aiki."
Daga can, wani ya ce "Kai, ba kai kaɗai ba. Wato matata kamar gwamnati ce. Yanzu nake shirin tura ta Ghana kawai ta huta a can." Dukansu suka sa dariya.
As’ad kuwa yana zaune a gefe guda, yana dannawa wayarsa. Sai dai ya ɗago kai lokacin da Alhaji Salisbury, abokin kasuwancinsa, ya tabo kafadarsa. "Kai, Young Billionaire! Ka yi shiru ma. Kowa yana tofa albarkacin bakinsa akan mata, kai ka ƙi cewa komai."
Dukkan su suka dubi As’ad. Ya ɗago kansa, yana sanye da kayan Versace, wristwatch ɗin Cartier yana sheƙi a hannunsa. Sai yayi murmushi irin nasa mai taushi da ƙima. "Me zan ce? Ni ban da korafi." Wani daga cikin su ya ce "Kai ba korafi? " As’ad ya sosa gemunsa, sannan yace "I have the best wife in this world. Wallahi idan zan roƙi Allah, sai in ce ya ƙashe mu tare. Mutashi tare, rayuwa tare. Ayshatu is the best woman I ever met."
Suka kalli juna. Wasu sun yi dariya, wasu suka girgiza kai da mamaki.
Wani ya ce "Kai abokina, wacce irin giya kauna ka sha haka? Matar da aka baka ba mai martaba ne yabaka ba? Kai fa har yanzu baka gane menene soyayya ba!"
As’ad ya dan lumshe ido, yana murmushi kamar wanda ya gama addu’a. "Kuna kallon ita mace ce da kyau da hankali. Amma wallahi Ayshatu itace salama ta. Da ita nake samun natsuwa. Ba sai na ce komai ba, zata ji abinda zuciyata ke so. Ina ganinta kamar wata zuma ce da Allah ya ajiye a duniya saboda ni."
Salisbury ya kwantar da kai. "Kai As’ad, ni dai kam sai na ce Allah ya tsare wannan soyayya. Saboda kalamanka ba na kasuwa ba ne. Na zuciya ne."
As’ad ya gyara zama. "Ina da komai kadarori, jirgi, har kamfanin crypto. Amma wallahi ban jin daɗin komai idan Aysha ba ta cikin farin ciki. Idan ta yi dariya, ina jin kamar kasuwanci ya ci riba kashi dari. Idan ta yi shiru, duk ginin da na tara, sai ya zama duhu."
Daya daga cikin su ya ce da mamaki "Kana nufin da gaske, baka taɓa tunanin wata mace ba bayan ta?" As’ad ya dan yi shiru. Sannan ya ce "Ina za ka kai zuciyar da tuni ka bar a hannun wani? Ko da mace ta fi ta kyau, ta fi ta jiki, ta fi ta ilimi ba zata iya gina abinda muka gina ba. Aysha ba matar gado bace. Ita matar rayuwa ce." Salisbury ya ce, “Kai, kai da ka zama Sheikh Romeo.”
Suka sake dariya, amma wasu daga ciki sai suka saki jiki da tunani. "Ni dai Allah ya bani irin zaman lafiyar da ka ke da ita," wani daga cikinsu ya faɗa a hankali.
As’ad ya ɗauki wayarsa, ya kalli hoton Aysha wanda suka ɗauka tare a lokacin da suke tafiya Spain. Tana sanye da farin hijabi, tana murmushi. Wannan hoton ke masa kwanciyar hankali fiye da signature din banki.Ya ajiye wayar, ya sha ɗan saffron tea ɗinsa.Sannan yace cikin nutsuwa "Ba laifi bane mace ta buƙaci soyayya. Amma laifi ne mu manta cewa su ma mutane ne. Idan mutum yana so a girmama kasuwancinsa, ya fara da girmama macensa. Saboda mace da bata farin ciki ba zata yarda ta rike gidanka ba." Dukkan su suka yi shiru. Wannan kalaman ba na kowane attajiri bane. Kalaman mutumin da ya gano sirrin rayuwa ne.
*******************************