Kenza eBookz

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 30

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 30

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 30: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 30. Nana hadiza

3,354 words

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA HAMSIN DA HUDU

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Na dauki sati biyu ina jinya a asibiti. Ciwon ya kama ni sosai har sai da aka ƙara saka min jini. Likitoci sun yi min gwaje-gwaje da yawa domin su gano abin da ke damuna. Sun kara bani wasu magunguna masu ƙarfi, suka ce in huta sosai. Amma duk da haka, jikina na kara ramewa. Na rasa ƙwari. Ciwon kai da gajiya sun zame min tamkar abokan zama.

Mumy kam, bata ji daɗin hakan ba. Kullum cikin masifa take cewa ta gaji da wannan jinyar. Bata damu da halin da nake ciki ba. Duk lokacin da ta zo asibiti, sai ta yamutsa fuska, ta ce, "Ke ba kya gajiya da kwance ne? Me yasa ba za ki warke ki dawo gida ki yi aiki ba?"

Nakan juya gefe kawai, ban ce komai ba. Ban san me yasa ta ke ganin kamar ciwon nan da nake yi da wasa ne.

Yanzu kwana biyu kenan da aka sallame ni daga asibiti. Amma har yanzu jikina babu ƙwari. Ina jin gajiya ko da ban yi komai ba. Duk jikina kamar an daddage shi. Da na hau gado, sai na kasa tashi da wuri. Nakan kwanta har rana tana fitowa.

Ranar da muka dawo gida, Abba ya ce wa mumy, "Yakamata Billy ta dinga gyara gida, ko kuma ku samo yar aiki."

Mumy ta amsa da cewa,

"To, ai Billy taje gidan ya Abbas ne. Can take yanzu."

Bayan kwana biyu, Abba bai ga Billy ba. Yacewa mumy me isa baya ganin bilkisu ina tashiga mumy takara cemasa ai tana gidan yaya abbas ne shiyasa bai ganta ba har yanzu. Sai yakira ya abbas ya rufeshi da faɗs akan ya tabbatar Bilkisu tadawo sai yace masa ai bama tazo gidan ba nan ne fa yadinga faɗa yakirata yace maza taxo ko datazo sai tayi masa karya tace masa ai tana gidan anty luba ne ai kuwa yadinga faɗa,

"Ke ki fidda miji. Auren zanyi miki idan bazaki iya samowa ba Ni zan samo miki miji."

Wannan abu ya yaɓakantawa mumy rai sosai.

Na shiga cikin dakina na kwanta. Ban da ƙarfi balle in ce zan fita ko in yi aiki. Ciwon kai bai bar ni ba, jikina kuma sai zufa yake kamar wanda ya sha gudu.

Da sassafe, ina cikin bacci, sai na ji wani abu mai sanyi ya zubo min a kai. Na farka da firgita. Na ga mumy ce ta zubamin ruwan sanyi daga cikin fridge. Na ɗaga kai cikin mamaki na ce,

"Mumy me nayi?"

Ta ce,

"Tashi ki gyara gida! Ina gaji da kallon ki kawai kina kwance naga kin warke kokuma jakar uwarki ce ni da zan dinga yimiki girki da aiki?"

Na ce mata,

"Kaina ciwo yake yi... Wallahi bazan iya ba."

Sai ta hau masifa. Tana cewa ni ban da amfani. Tana zagi na, tana cewa ni ba zan taɓa zama abin kirki ba. Na tsayar da hawaye na da ƙyar, amma zuciyata tana kuka sosai. Wani lokacin nakan tambayi kaina Shin me nayi wa mumy? Me ya sa take ƙin na haka?

Daman munada lecture da safe. Na san ba ni da ƙwari, amma na fi son na fita fiye da na zauna a gidan da za a ci min mutunci.

Sai Maryam, kawata ta, ta zo ta zauna kusa da ni. Ta kalle ni da kulawa ta ce,

"Ke lafiya? Kin rame fa. Yajikin naki nazo gidanku ai masu gadi sukacemun kina asubuti kuma mamanku na can kinganki kuwa kamar ba ke ba."

Na so in fashe da kuka, amma na ɗan daure. Na ce mata,

"Zan faɗa miki... Amma ba yanzu ba."

Ta dafa kafadata ta ce,

"Ni ina tare da ke, ko me ke damunki. Kar kiyi kasa da addu'a ramlah Allah yana jinmu yana ganin komai."

Na juya gefe, hawayena gangarowa a hankali. Wannan kalaman nata sun shige min zuciya.. A wannan lokacin na fara jin sauƙi kadan. Ko da kuwa jikina yana rauni, amma zuciyata ta samu sauƙi saboda akwai wanda ya damu da halin da nake ciki.

******

Washegari da safe, na farka da ƙarfin jiki. Bayan jinyar da na sha a asibiti, yau ce rana ta farko da na tashi ina jin natsuwa da ƙarfi kadan. Na shirya na ɗebo jakata, na saka hijabi, na fita makaranta da sauri. Gobe za mu fara exam, kuma yau muna da lecture na “Public Policy” daya daga cikin muhimman darussa da muke dashi a cikin Public Administration.

A hanya, zuciyata tana tafasa da tunani. Na sha wahala a gida. Amma makaranta ce kadai wurin da nake jin kwanciyar hankali. A can ba mumy, ba masifa, ba faɗa.

Da na isa makaranta, na samu Maryam a wajen da muka saba zama ƙarƙashin bishiyar mangwaro kusa da theater 2. Tuni tana karatu. Na zauna a kusa da ita, ta ce,

“Ramlah yau kin yi kyau. Yau jikin na ki ya samu lafiya kenan?”

Na murmusa kadan. Na ce,

“Eh, jiya na dan huta sosai. Gobe fa exam... dole in dage.”

Maryam ta bude littafinta, ta ce,

“To, yau zan koya miki summary ɗin ‘Decision Making Models’ da malam ya koyar lokacin da baki zo ba.”

Na kafe ido ina saurare. Ta fara bayani kamar malama. Ta ce

“Kin san akwai Rational Model, Incremental Model, da Garbage Can Model. Wannan su ake amfani da su wajen yanke shawara a ofisoshin gwamnati ko ma'aikatu.”

Na rubuta a cikin not dina, ina jin dadin yadda karatun ke shiga min sauƙi. Karatun Public Administration ba sauƙi ba ne, amma idan kina da wanda ke taimaka miki kamar Maryam, sai ki ji kamar komai yana yiwuwa.

Malam Lawal ya shigo da class ɗin “Administrative Theories”. Ya fara magana cikin salo mai natsuwa. Ya ce:

“Za mu fara da Theory of Bureaucracy na Max Weber. Kowa ya buɗe shafi na 45.”

Na buɗe shafina. Duk abin da yake faɗa, ina rubutawa. Sai na lura da wani sabon nutsuwa a raina. Duk da ciwon da na sha da halin gida, yanzu ina jin kamar na dawo cikin duniya. Na dawo Ramlah da nake so mai burin ta zama mace mai ƙarfi a gwamnati.

Bayan lecture, muka fita waje da Maryam. Tana dariya tana cewa

“Ramlah, idan kika zama Permanent Secretary sai ki tuna da ni!”

Na ce,

“In dai kika ci gaba da koya min haka, sai na sa ki Chief of Staff!”

Mu kayi dariya sosai. A irin wannan dariyar nake jin dadi araina. A hostel, na zauna da littafina. Ina nazarin abinda muka yi a rana

Public Choice Theory,Bureaucratic Politics

Fiscal Federalism, Na daina jin rauni. Ina ji a zuciyata cewa wannan karatu na da ma’ana. Ina so in gama in samu aiki a ma'aikatar kula da jin dadin al'umma. In taimaka wa matasa, in bude shafi sabo a rayuwar mutane masu rauni kamar yadda ni nake ji yanzu.

Da daddare, na lumshe idona. Na yi addu’a. Na ce “Ya Allah, ka bani lafiya da ƙarfi. Ka taimaka min in gama karatu, in canza rayuwata. Ka bani damar zama abin alfahari.”

Idan nace bana cikin damuwa ko tunanin Khalil, wallahi nayi karya. Kusan kullum sai ya fado min a rai. Ina kwance nake ji kamar yana kirana da murmushin sa. Sau da dama nakan so in tashi in tafi gidan su kawai in ga babansa in ce, inyi masa gaisuwa" Amma duk lokacin da nayi niyar zuwa sai tsoron wulakanci ya rufe ni kada Maman khalil ta koroni.

Na san mamansa ba za ta iya yi min dariya ba. Yanuwansa kuwa? Ina jin kamar ba zan iya jure kallonsu ba. Allah sarki Khalil. Masoyi na kirki. Yayi mini abubuwa da ba zan iya mantawa da su ba. Amma yanzu... komai ya zama tahiri. Soyayyar da ta cika zuciyata, yanzu ta zama ciwo. Kullum idan na tuna da shi, sai na ji wani abu kamar bargo mai sanyi ya rufe ni... amma da ƙaya.

Yau lecture ɗin da muka yi ya matuƙar gajiyar da ni. Ina isa gida na tarar da hayaniya. Kafin in karasa parlour, sai na hango Abba yana tsaye Yana faɗa da karfi, fuskarsa cike da fushi. Yana yi wa Yaya Bilkisu masifa sosai.

Yana cewa "Ki fidda miji Bilkisu! Bazaki cigaba da yawo a ba! Na gaya miki sau nawa? Wallahi ba zan sake jurewa ba. Nace ki zo office dina kiyi aiki aa! Sai yawon banza kike! Ko to, bazan yarda ba!"

A cikin zafin zuciya, ya ɗaga hannu ya mareta. Na tsaya cak! Bilkisu ta zube tana kuka. Mumy tana gefensa, tana ƙoƙarin kwantar masa da hankali.

"Don Allah... ka yi hakuri. Ta dai shiga mawuyacin hali ne. Ka ba ta dama," in ji Mumy tana tsaye

Ni kuma, ba ni da abin cewa. Na kalli Bilkisu tana kuka, sai zuciyata ta cika.nashige dakina nakwata kawai nasan wannan fadan da akayi mata mumy zataso ni akayiwa Sai gashi halin yaya Billy yanata fitowa ana gani.

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA HAMSIN DA BIYAR

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Yau wata rana ce mai sanyi a cikin birnin Paris. Iskar garin tana busowa da ƙamshi mai daɗi daga Jardin des Tuileries, kyakkyawan lambu da ke tsakiyar birnin. Rana na haskakawa, amma sanyi yana ratsawa da laushi mai sanyaya zuciya.

A cikin wani katafaren gida mai hawa huɗu da ke kusa da Champs-Élysées, wata mata ta tashi daga barci a cikin gado lallausa Ita ce Ayshatu mace mai shekaru 34, mai fata kamar madara, cikakkiyar mace mai kudi, kyau, da sirrin rayuwa. Tana cikin fitattun matan da kafafen sada zumunta ke magana a kansu.

Da ta buɗe idanunta, ba bacci ne ya isheta ba, sai wani irin nauyin zuciya da ba ta iya fassara. Duk da komai na duniya tana da shi, akwai abinda zuciyarta ke nema, kuma wannan abun ba komai bane face namiji. Namiji wanda zai cika wannan giɓin da dukiya ba ta iya rufe wa.

“Sha’awata yanzu tafi yadda take lokacin da nake ‘yar shekara ashirin da bakwai,” ta faɗa da ƙasa da murya, tana kallon hasken da ke ratsowa daga Eiffel Tower. “Sun fa ce mace tafi buƙatar namiji daga shekara talatin... yanzu na fahimta.”

Tsaki ta ja, ta tashi daga gado. A yau tana da alƙawari a wani spa mai daraja da ke cikin Avenue Montaigne L’Institut Dior Spa. An shirya mata gyaran jiki da wankin kai da turaren sinadaran ƙasashen waje.

Tana cikin motarta mai tuki da kanta (Maybach na zamani), zuciyarta cike take da tunani. Duk da ita ce Ayshatu, wadda duniya ke kallo, akwai wani abu da babu wanda ke iya ganinsa sai ita kadai tasan indai dacen Miji ne to tabbas tayi amma kuma itama tana bukatar lafiyayyen namiji mai kuzari.

A isarta spa, aka tarbe. A can aka yi mata cikakken wankan jiki da gyara da sinadaran da ke fitowa daga itatuwa na musamman daga Côte d’Azur, da man lavender daga Provence. Ƙamshin jikinta sai annuri da salo.

Da ta dawo gida, ta zauna a cikin wani falo mai ƙayatarwa da ke fuskantar lambun Versailles. Zuciyarta ta fi yin nauyi. Tana kallon wayarta, tana jiran sakon wani saurayi da suka fara magana kwanan nan Farouk Ibrahim, ɗan kasuwa ne daga Nigeria da ke zaune a London. Muryarsa tana da daɗin ji, fuskarsa cike da kamewa da natsuwa, kuma yana da cikakken kamala.

Amma bai amsa saƙonta na ƙarshe ba. Tun kwana biyu ke nan.

Ta shige Instagram, tana kallon hoton da ya wallafa jiya yana tsaye a wani taron kasuwanci a Dubai. Bai ce komai gareta ba. Tsaki ta ja. Tana jin wani damuwa yana shiga jikinta, duk da gidan yana ɗumi da jin daɗi.

“Shin ni ce ban isa ba?” Ta tambayi kanta.

Wani lokaci tana mamakin yadda maza ke jin cewa mace mai dukiya ba na buƙatar soyayya bace. A ganinsu, dukiya ce zata maye gurbin kulawa da motsin rai. Amma a gaskiya, ba komai ke maye gurbin kulawa ba.

*****

Washegari

Ayshatu tana zaune a wani shahararren café a Champs-Élysées, inda take zuwa idan tana buƙatar nutsuwa da tunani mai zurfi.

A gabanta, caramel macchiato da ɗan muffin ne, amma ba ta taɓa su ba. Wayarta a hannunta, amma idonta baya kansu. Idanuwanta suna bin mutanen da ke wucewa sanye da kayayyakin alatu bags, perfumes, da agogo murmushi na gamsuwa a fuskarsu, soyayya na bayyana a kwayar idanunsu.

Zuciyarta tana ta faɗuwa kamar wata mai buguwar ƙwaƙwalwa.

Kamar daga sama, saƙo ya shigo ta Instagram. Sunan mai aikowa Alhaji Muqaddam.

Sunan da ta gani a cikin hirar As’ad da attajirai a Morocco. Ta san da shi, suna kusanci sosai da As'ad wani lokacin ma yana neman kaya sosai gurin As'ad din ko wata alfarma tunda duk cikinsu yafi kowa fice da dukiya. amma bai taɓa aiko mata da saƙo ba sai yanzu.

“Salam Aysha. Kyauwunki da kamewarki na da daraja fiye da abinda Paris kaɗai ke iya gani. Zan kasance a birnin gobe don taron kasuwanci. Kin shirya dinner da ni? Just dinnerba tilas ba. Kina da haƙƙin ƙin amincewa.”

Ta kalli hotonsa mutum ne da ke da ƙima da murya mai zurfi. Kwalarsa tana nuna alamar jarumta da kwarewa. A bio dinsa yasanya CEO, International Gold Merchant | Private Collector | Uba ga ‘ya’ya huɗu.

Hannunta ya yi sanyi. Ta kalli wayar. Zuciyarta ta ce “As’ad yana can da kalamai masu daɗi. Amma ke kina nan kin rasa kulawa. Wannan ba zina bane talk only. Dinner only.”

A hankali ta rubuta “Waalayk salam, na gode da kalmomin ki gareni, Insha Allah zan samu lokaci gobe da yamma.” Ta dannawa send.

Ta lumshe ido, ta ɗauki numfashi mai tsayi. Ta san ba komai bane amma wani abu a zuciyarta yana ta yi mata kururuwa “Ki tuna wanda ya tsaya a Morocco, cikin attajirai, amma bai ambaci kowa ba sai ke. Wanda yake mutuwar kaunarki da kulawa dake menene As'ad ya rageki dashi?.”

Washegari Da Daddare

Wurin dinner ɗin ya kasance a Le Jules Verne, wani luxury rooftop restaurant da ke kan Eiffel Tower. Wurin da ke cike da haske mai natsuwa.

Alhaji Muqaddam ya zo cikin kaya masu daraja, fuska cike da annuri da halin jarumta. Ayshatu ta bayyana cikin doguwar riga mai ɗaukar ido, ba shigar banza ba, da mutunci da ƙima.

Ya miƙe yana mata sannu da zuwa da ladabi, amma tare da yabata da ke iya tada hankali.

“Masha Allah. Gaskiya kina da kwarjini da kamewa. Ki zauna.”

An kawo musu sparkling juice da kayan ciye-ciye masu daɗin ƙamshi. Hira ta tashi cikin natsuwa da girmamawa.

Ya tambaye ta game da kasuwanci, karatu, da yara Amma daga bisani, sai ya fara karkata hirar “A ganina, yana da wuya mace mai daraja kamar ke ta jure jinkirin kulawa. Ina fata As’ad na fahimtar irin lu’ulu’u da yake da shi.”

Ayshatu ta yi murmushi mai sanyin zuciya. “Na yarda yana da kalubale, amma ina tare da shi.”

Muqaddam ya ce “Na fahimta. Amma a matsayina na wanda ya jure aure fiye da shekaru ashirin, na san cewa mace tana buƙatar kulawa da nuna darajarta, ba kawai jiran lokaci ko alƙawari ba.”

Ya ɗago idanunsa cikin nata, cikin natsuwa mai nauyi. “Ki yarda in sa ki dariya. Ki bar zuciyarki ta huta. Ko na ɗan lokaci.”

Ayshatu tayi shiru. Kalaman nasa kamar ana zuba zuma ne a kunnen mutum mai yunwa. Amma cikin zuciyarta, wata murya mai tsarki tana ce mata “idan kika yarda da dariya ɗaya, zaki rasa gaskiya goma.”

Ta ɗauki wayarta don kawar da damuwar da ke cike da zuciyarta. Sakon As’ad ya shigo

“Ina fata kin ci abinci. Ina jin kamar zuciyata tana Paris a wannan daren.”

Idanunta suka cika da hawaye.

Ta kalli Muqaddam, wanda ke kallon ta da fahimta, amma cikin shakku. Ya ce

“Zan iya zama aboki. Ko fiye da hakan, in kika yarda.”

Ayshatu ta lumshe ido. Ta ce “Kai mutum ne mai kirki. Amma zuciyata yanzu ba ta da wuri.”

Ta miƙe, ta ɗauki jakarta. “Na gode da gayyata. Amma zan koma gida.”

Muqaddam ya tsaya kallon ta, har ta fita. Sai ya girgiza kai, yana cewa da kansa “Toh, wannan ce matar da As’ad ke faɗi da yabonta a kowanne lokaci.” wani kalar murmushi yayi.

Marrakech, Morocco

The Royal Mandarin Hall

Wani babban taron kasuwanci ne na shekara-shekara, inda manyan attajirai daga ko’ina cikin duniya ke taruwa. Wurin ya cika da hasken kristal, ƙamshi mai daɗi, da sautin kiɗan jazz da ke fitowa daga saxophone.

As’ad ya shigo cikin wani shigar Farar babban riga da bakar hula, da turaren Tom Ford Oud Wood mai ƙamshi. Girmansa da nutsuwarsa sun sha bamban da sauran masu kwarjini a wurin. Kamar yadda aka saba, mutane da dama sun tsaya suna gaisawa da shi, amma idonsa baya can.

Zuciyarsa na can Paris, a wajen Ayshatu. Kwanaki sun dan ja, kuma daga kalamanta na ƙarshe, yasan tana buƙatarsa. Wannan shine dalilinsa na zuwa taron cikin hanzari ya kammala komai ya koma gareta.

Bayan gabatar da jawabinsa mai cike da hikima da hangen nesa, As’ad ya koma gefe yana gaisawa da wasu manyan mutane. Sai Alhaji Muqaddam ya karaso, yana sanye da riga fara shima. Ya ɗan leƙa gefen As’ad cikin natsuwa, yana murmushi da kwaikwayon As'ad "Mutumina, wai menene sirrin? Zamanku da Ayshatu... na lura kamar kabata yarda dari bisa dari. Me kake mata haka da bata shakka?"

As’ad ya kalli Muqaddam da murmushi mai nuni da cikakkiyar fahimta. Ya ɗan girgiza kai yana ɗora gilashinsa na shayi akan teburin kusa. "Abokina... bazaka gane ba. Shiyasa kullum nake muku faɗa akan bin matan da ba su da tushe. Biyan buƙata kawai babu amfani. Mace ɗaya ce zata baka abinda kake nema zuciya, kulawa, girmamawa... da soyayya ta gaskiya."

Muqaddam ya yi shiru. Babu abinda ya faɗa. Amma cikin ransa wata murya tana bugawa da ƙarfi.

Yana tuna dinner ɗin da yayi da Ayshatu. Kamar yana sake jin yadda ta janye jikinta da nutsuwa, duk da ƙoƙarinsa.

Yana kuma tuna yadda ta tsaya akan kaunar As’ad ba tare da faɗi wani abu mai zafi ba. Wannan kwanciyar hankali da ƙwarin zuciya ne ke damunsa.

“Ta yaya zan iya juya zuciyar mace kamar Ayshatu? Me As’ad ke yi da ya sa har zuciyarta ta tsaya masa? Yasan dai bai isa ya yaƙeta da kudi ba dan As'ad yakai matsayin Multimillionaire yanzu kuma baya wasanda kyautata mata yasan wannan.”

Alhaji Muqaddam ya kama gindin kujerar da ke kusa da shi, yana sauke numfashi. Idanunsa na bin yadda As’ad ke shan shayi cikin kwanciyar hankali, yana amsa kira daga wani director na bankin duniya.

Wannan ba kawai kishi bane wannan haushin wata mace ya ƙiyi wacce jawo masa hankali, duk da komai da yake da shi. Zuciyarsa ta riga ta kasa zama. Sai ya furta da zuciya “Wallahi sai na dandaneta. Sai na kwanta da'ita kamar yadda kayi sai na mai data abar hutawa ta nakasa kamoka akudi amma a yanzu sai nashiga gonarka nayi yabanya. Alhaji Muqaddam yafaɗa yana sauke ajiyar zuciya.

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA HAMSIN DA SHIDA

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Kwanakin nan, sanyi ne ya lullube garin. Kamar dai duniya tana motsa murya da tausayin masu ɓoyayyen ciwo.

A hankali nake takawa a harabar jami'a, ƙafafuna na ji tamkar suna ɗauke da dutse. Jikina gaba ɗaya na nauyi, amma zuciyata ce ke ƙoƙarin tura ni gaba. Da zazzabin da ke ɗaure ni, sai dai har yanzu ban kaɗaita da dawowa makaranta ba muna cikin lokaci mai muhimmanci wato jarabawa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull