Kenza eBookz

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 33

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 33

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 33: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 33. Wallahi ba zan taɓa manta ranar ba. Ranar…

3,374 words

Wallahi ba zan taɓa manta ranar ba. Ranar da rayuwata ta karye. Ranar da duk wata ƙaramar fata da nake da ita ta narke kamar ƙanƙara a rana.

Na zauna a gaban mumy, na durƙusa, na rasa abinda zan ce in ba rokon ta da kuka ba. “Mumy… baki ji me Abba ya ce ba? Baki ga abinda yake shirin yi ba? Dan girman Allah, dan zatin Allah, ki taimake ni. Ki tsaya ki saurare ni kada ki bari a auramin Bashari.”

Sai ta yi dariya. Dariyar da har yau take min ƙara a kunnena muguwar dariya, dariyar da bata da tausayawa.“Auren Bashari? Ai babu fashi, Ramlah. Tunda ubanki ya yanke hukunci ko kiyi biyayya, ko ki karɓi tsinuwar iyaye a kanki”

Na share hawayena, sai na fara bayani. Ba na buƙatar hawaye kawai gaskiya na buƙata ta kare ni. “Mumy… na san Bashari tun ina ƙarama. Ranar da Abba ya samosa yana kan hanya, yana shaye-shaye, yana dabanci, ya ɗaukosa gida. Ni ina tsaye. Na gan shi da idona. Na ji muryarsa, na ga yadda yake ruɗewa cikin rikicewa.Abba ne ya sa shi a makaranta. Abba ne ya biya masa kudin karatu. Abba ne ya ɗauke shi a matsayin ɗa. Amma duk da haka bai sauya ba.Nasha jin sunansa a rediyo. Nasha ji suna cewa yansanda na nemansa. Nasha ji an ce ya kashe mutum, amma masu kuɗi suna toshe labari.Na sha jin mutane suna cewa bashida halin zaman aure, bashida tausayi, kuma mutum ne mai tarin boyayyen laifi."

Abba ya turo ƙofa da ƙarfi ya shigo dakin. Na tsugunna a ƙasa ina kuka, na riƙe ƙafar Mumy kamar ƙa’idar rayuwata na rataye da mafita daga bakin ta.

Zuciyata na bugawa da tsoro, da fatan zata tsaya ta saurare ni. Amma bata ce komai ba.

Abba ya tsaya yana kallona da fuska cike da fushi, numfashinsa yana fita da huci. “Wallahi, Ramlah, idan kika ƙara cewa ba za ki auri Bashari ba to ki sani ban yafe miki ba. Ko da kinaso ko bakyaso aure ɗin nanysai nayi miki. to kisani Allah ya isa!” Kalmarsa ta tsaya cikin zuciyata kamar dutsen dutse. Sai na fashe da wani kuka mai zurfi, na matse kafar Mumy da hannuwana biyu. A ƙofar dakin, Yaya Bilkisu ce tsaye – wacce ko da wasa ba ta taɓa ra’ayin ta tsaya min baya. Amma yau… yau ta ce “Abba, amma fa Bashari… haba dai Abba! Bashari fa?” Idanunta sun cika da damuwa, da mamaki. Bilkisu ta tsaya min? Duk da yadda ta tsaneni, sai ta ce gaskiya. “Wannan mutumin dai fa, Abba, mun san shi. Kusan kowa ya san shi mutumin banza ne”

Kafin Abba ya iya cewa komai, na ɗago da fuska cike da hawaye, na ce da shi cikin murya mai rauni “In shaa Allah, Abba… ni mai biyayya ce gareka. In shaa Allah… na amince.” Sai na fashe da sabon kuka, wanda ko zuciya ba zata iya ɗauka ba.Ya kalleni, idonsa ya sauka a kaina, amma ba alamar tausayawa ko jin kai. Sai ya ɗago kansa sama yana furzar da iska mai nauyi da damuwa.

Yaya Bilkisu ta ɗan matsa gaba, ta juya ga Mumy cikin ɓacin rai “Haba Mumy! Wannan shi kike goyon baya? That illiterate, that drug man? amma wannan zalunci ne. Duk da haushinta nake ji, amma wallahi babu adalci a wannan aure.”

Mumy ta ɗago kai da ƙyar, ta buga hannu a ƙasa, sannan ta ce da masifa: “Ku yi shiru! Ku bar ni da 'yata! Wannan aure za a yi ko da me. Ai tunda ita ba ta da hankali, dole mu tsare ta.”

Ni kuwa a ciki, bani da ƙarfi, bani da dama. Abba ya tsine, Mumy ta tabbatar, Yaya Bilkisu ta faɗi gaskiya amma babu wanda ya tsayar da komai. “To ni fa fa?”

“Ni ce aka yankewa hukunci ba tare da tambayata ba.”

“Ni ce za a tura auren nan ba da so ba.

Mumy na fita daga dakin falo, kai tsaye ta nufi nata dakin kamar wadda ta samu lamban cin nasara. Fuskarta cike da murna, keta dariya kamar an kashe mata abokin gaba. “Na gama da ke Ramlah. Wallahi sai kin fuskanci yadda ake wulaƙanci da gaskiya.”

Tana shiga daki, ta zube a gadonta, ta ɗauki wayarta cikin sauri. Ta kira Y'akaka aunty dinta da suke hadin baki wajen gulma da tsare sirrin su. “Y'akaka! Aiki ya kammala wallahi. AURE Ramlah! Hahaha! Aure da Bashari fa!”

“Ni yanzu zan huta da kwallon mangwaro wato yarinyar nan mai girman kai. Zan huta da annobar gida wato Ramlah!”

Murmushi mai cike da mugunta ne ya bayyana a fuskarta. Idonta ya dau sheki kamar na maciji mai jin nasara. “Kuma danake gaya miki... Abbansu ya kira Bashari ya kuma amsa da gamsuwa. Wallahi a gobe za'a daura auren.Kayan daki fa? Ina! Ni ba zan tsaya yi mata kaya ba zandai cillata da kayan jikinta da na tufafinta. Ai daban ne daita, sansanin dabar tasu ce zata.

Y'akaka tana dariya a waya, tana faɗin“Lallai yau kin cinye ta Mumy. Wannan ai ba dafa ba ne wannan dafa da gishiri ne har da yaji!”

Mumy ta ce “Wallahi ko auren ta yi ko ba ta yi ba ni dai na yanke hulda da ɗiyar kishiya Zan tabbatar ta yi nadama har gaban kabari.”

___

Na shiga dakina da ƙafa mai rauni, na jingina da ƙofa na sulale ƙasa kamar jarirai da aka cire wa mafita. Na fashe da kuka. Kukan da bai da salo. Kukan da ba a iya tsayarwa. Kuka mai ciwo fiye da duka. Na riƙe kirjina. Na ce da kaina “Me nayi wa duniya? Me yasa iyayena suka fi ƙaunar cutata akan su kare ni?” Na miƙa hannu na ɗauki wayata, da fatan zan samu wanda zai ji ni, wanda zai ji zafin da nake ciki wanda zai tsayar da wannan auren da nake tsoro kamar mutuwa. Na shiga layin wayar Yaya Usman, na gwada kiransa sau ɗaya bai shiga ba. Sau biyu… har uku… still not reachable,Wayar tayi shiru kamar babu duniya a kanta. Sai na ji kamar an ƙara dora dutse a zuciyata. “Ya Allah, wa zan kira yanzu? Wa zai saurare ni?” Sai na ɗan goge hawayena da yatsa, na duba lambobin wayata.

Na hango Khalil. Khalil ya mutu wayoo Allah na Amma a wannan lokacin… sai na ce “Inama da shi za a haɗani… inama da shi ne Na sanya kuka. Kuka mai sanyi, mai fasa zuciya, mai rikita kai. Kuka da ko bango da ɗaki sun kasa jure wa. “Inama… inama… inama shi ne. Inama zan iya guduwa tare da shi… inama kana raye khalil.” Kuka nake yi kamar mara lafiya mai buƙatar taimako.

Ina jin numfashina na rikicewa. Zuciyata na sarawa. Kaina na juyawa. Sai na tashi da ƙyar, na ɗauki magunguna paracetamol da aspirin, ko zai saukar da wannan ciwon zuciya da jiki. Na sha su da ruwa. Ban ci komai ba tun safe amma bana iya tunanin ci.

Kafin dare yayi sosai, na fara jin zazzabi ya mamaye jikina. Ya fara rawa, sai zafi da dumi ke ɗaukar kaina gaba ɗaya.

Fuskata ta fara yin ja, idanuna sun kumbura da kuka. “Ya Allah… ka duba halin da na shiga. Ka fitar da ni daga nan cikin rahamarka.” Babu wanda ya shigo dakina. Babu wanda ya tambaye ni. Babu wanda ya lura da irin halin da zuciyata ke ciki.

"Inama Allah... Inama ace mahaifiyata bata mutuba..." Wannan kalmar ce kawai nake iya furtawa a cikin zuciyata cikin dare, cikin zafi, cikin rashin mafita. Wallahi da mahaifiyata bata mutuba ba, da bana kiranta “Mumy”.

Wannan Mumy da nake kira uwa bata da tausayi. Bata da zuciyar da zata ji kuka na.

Da ace uwata mai rahma ce har yanzu tana raye… Da ba zan kasance cikin wannan hali ba na wahala, na matsin lamba, da aure da bana so. Da zan zauna a jikinta in fadi damuwata, ta shafa kaina, ta ce “Zan kare ki.”

Da ba zan sha zazzabi a daki ni kaɗai ba, sai turaren kamshi da dumin lullubi daga hannunta, Kullum nake addu’a “Ya Allah, ko mafarki ne, ka bar ni in ganta.” “Ka bar ni in rungumeta sau daya.” “Ka bar ni in ce mata Ina sonki, na rasa ki, ki dawo mana.” Na fashe Da kuka..

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA SITTIN DA BIYU.

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Da ƙyar na lulluɓa jikina da bargo, na matse idona da karfi kamar hakan zai tilasta zuciyata ta kwanta. Amma bacci bai zo ba. Sai firgici, rawar sanyi, da tunani mai nauyi. Na kasa gane me yasa duniya ta juya mani haka me yasa rayuwa ta koma kamar mafarki mai daci? Na sauke ajiyar zuciya. Har da magani na sha domin natsuwa, amma har cikin baccin ma, zuciyata tana kuka.

Washegari da sassafe, na farka da karar murya da tafiya da takalma a cikin gidan. Na leƙa ƙofar dakina sailing vna hango palon gidan ya cika da dangi, musamman ‘yan uwan Abba maza da matasa da dattawa. Muryar Mumy ce na fara ji tana fadin “Anty Luba, zo mu hada kayan Ramlah lokaci ba ya tsaya wa.” Suna shigowa dakina da ledoji da jaka. Anty Luba ta riƙe wata buhu ‘bakko’ ba ma akwati ba. Sun fara zubawa cikin sauri kamar wasu ‘yan haya. Na zauna a gefe, idona na bin su, amma zuciyata na zubar da hawaye kamar kogi. Ban ce musu komai ba. Har suka gama. Daga bisani sai na mike na shiga wanka amma ba dan na shirya aure ba, sai dan ina jin zafi a jiki da zafi a zuciya.

Bayan na fito daga wanka, na tafi gaishe da kannen Abba da ke zaune a falo. Sai na ci karo da Uncle Hamza, yana kallona da kallo mai cike da damuwa. “Ban ji daɗin zabin da kika yi ba, Ramlah. A gidana ma akwai Abubakar da Mubarak, baki zabesu ba, sai Bashari?” Na ji duk wata magana ta makale a makogwarona. Ban iya cewa komai ba

saboda na tuna da kalmar Abba “Idan kin ƙara cewa ba za ki auri Bashari ba, sai na tsine miki. Ban yafe ba!” Sai na sauke numfashi, na ce da rauni “Indai hakan ne farin cikin Abbana, to nima farin cikina ne.” Uncle Hamza ya kurbi kalmomin nan da wata irin fushi da tausayi. Ya dubi Abba da ƙarfi, ya ce “Haba yaya malam! Wallahi kun tilasta wa yarinya. Wannan ba aure ba ne azaba ce!” Abba ya kalle shi, bai ce komai ba. Na tashi da ƙyar, na juya na Na koma dakina amma da na shiga, ban gane shi ba.Naturar da Mumy da Anty Luba sun kwashe komai.

Kayana a cikin buhun “bakko”, ba ma akwati. Kamar matar da ake korar aure. “Wannan Anty Luba ce? Ita ce wadda kullum take nunamin soyayya? Ita ce da murmushi take ce min ‘ki tsaya da karatu Ramlah’?

Ita ce yanzu ko kallona batayi ba?”

Tana gefen Mumy, tana murna kamar suna shirin mika min tikitin hijira zuwa rayuwar azaba,Na zauna a gefe.

Anty Luba ta dawo dakina, ta zauna a gefena kamar wadda zata bani shawara. Amma sai tace “Ashe rabonki da Bashari ne ba Khalil ba? Ashe Khalil ya ƙare kenan, yanzu rabonki ya kashe shi kenan?” Na dan kalli fuskarta, ba da ƙiyayya ba, ba da mamaki ba amma da daddawan zuciya da ba ta da mafita.

Na murmusa kadan, na ce “Allah ya yi. Shine mijina. Anty, ki yi mana addu’a.”Ta dan buɗe baki, ta ce “Allah ya bada zaman lafiya.”

Na san ba addu’a bace a zuciyarta duka maganganu ne na wulaƙanci da cin mutunci.

Ina zaune a cikin ɗakina shiru kamar kabari. Sun tafi da komai. Sun tafi da kayana, da ƙuruciyata, da burina. Sai ragowar ƙamshin turarena da yake shawagi cikin iska, kamar tunawa da wata ni’imar da ta shuɗe.

Nike nan… Ina kallon bango. Bango da ya zama shaidu a cikin kuka da firgici.

Kamar mafarki, sai ga Yaya Bilkisu ta shigo. Fuskar ta cike da mamaki, da bacin rai, da wata guntuwar tausayina da ban zata ba daga gareta.Ta zauna a kusa da ni, tana kallona da damuwa. Sai tace "Ke Ramlah, baki da hankali ne? Zaki yarda su yi miki auren dole?"

Ta matse hancinta, ta girgiza kai da takaici. Sai ta ci gaba "Wallahi ko videos ma Mumy ta sanya ta saka aka tura miko sannan ta kunna kina shiga bandaki dataji karar motar Abba, ina kallonta! Wannan Bashari kike yarda da shi? Wannan ɗan daba? Wannan mashayi? Wannan mai makami? Kinsan yadda kike da kyawu kamar 'suffer matan manya, kina da daraja, kina da ilimi amma yanzu kike barin su jefa ki cikin wuta da rai da ido? Ramlah, na rantse miki ki gudu! Ki bar gidan nan! Ki je family house, ko wajen su kakarki. Kada ki yarda da wannan mugun auren."

Na kalleta. Kuka ya turnuke ni. Hawaye ba su tsaya ba. Sai na ce da muryar da bata da ƙarfi "Ya Billy... nagode da shawararki. Wallahi ina jin kalamanki a zuciyata. Amma ba zan iya guduwa ba.Na amince. Na amince da auren. Na amince da hukuncin da Abba ya yanke saboda banason tsinuwar mahaifina ta hau kaina. Ko da kuwa wannan aure ne da zai yanka naman jikina da ruwan wuta.Koda kuwa raina ba zai samu salama ba, zan daure. Koda na rasa farin ciki, zan yi aure domin biyayya." Na fadi haka ina fashewa da kuka.Yaya Bilkisu ta kura min ido. Bata ce uffan ba. Sai daga ƙarshe ta tashi tana girgiza kai da masifa. Ta ce "To ai sai ki ɗauka da kanki. Wallahi ba za ki ce ban gaya miki ba Ki gama da kanki. Amma wallahi kin zalunci kanki, kin sallami burinki." Ta fita, ta barni cikin dakin da ya cika da shiru.

---

Wajen ƙarfe goma sha biyu na rana, rana na haskaka sararin sama da kyan fitilarta, duk da cewa a cikin zuciyata tamkar ƙirin dare ne duhu, ba haske. Mutane sun yawaita a gidanmu, sai hayaniyar gaisuwa da dariya ke tashi.

Kamar almara, Bashari ya iso. Ba shi kaɗai ba, tare da kawunsa guda biyu mutane masu fuskokin ƙasa da dariya mai ɗaci.

Suka shigo falon cikin takun izza, jikinsu sanye da hadadden shadda 'Getzner' mai launin zinariya da rawaya. Tufafin nasu sun sha guga, suttura masu sheƙi da ƙamshi. Sun shiga cikin falon da nutsuwa, suka tsugunna cikin mutunci. “Assalamu alaikum.” Sai gaisuwa ta biyo baya canji-cinji na "Lale-lale, maraba da zuwa", kamar waɗanda ke murnar abun da ke faruwa.

An karanta fatiha.

An daura aure.

Auren da ban ji soyayya ba a cikinsa, auren da naji kamar ana rufe ni a cikin akwati ba tare da iska ba.

Bashari ya zauna da ƙarfin zuciya, yana cewa “Na karɓi auren Ramlah diyarki a kan sadaki naira dubu hamsin, na amince da sharuɗɗan aure.” Sauran mutane suka amsa da “Allah ya amsa. Allah ya bada zaman lafiya.”

Amma cikin zuciyata:

Shin ni fa? Me nake ji? Wani abu ne mai nauyi na danna kirjina, kamar zuciyata ta tsaya amma ba ta mutu ba.

Abba ya ɗago da murmushi mai ɗauke da girman kai. Ya kalli Bashari, ya ce da shi a fili “Kai fa kana da sana’a ko? Kana da abin yi?”

Bashari ya gyara zama, ya kada kai “Eh Abba, ni ina sana’ar tukin mota da siyar da kayan itace. Kuma ina da gida a can ƙauyenmu.” Sai Abba ya ja dogon numfashi, ya sa hannu cikin aljihunsa, ya fitar da wani envelope mai kauri. Ya mika wa Bashari yana fadin “To, ga wannan. Naira Miliyan Biyar ne. Wannan shine kudin kayan dakinta. Ka je kasiya, ka bata duk abinda mace ke buƙata. Na barmaka Ramlah halak malak.” Daga nan ya ɗago hannunsa sama, ya fadi “Allah ya baku zaman lafiya. Allah ya sa wannan aure ya zama albarka gareku.” Bashari ya durƙusa da girmamawa. Fuskarsa cike da godiya, idonsa da hawaye “Na gode sosai Abba. Wallahi wannan alfarma da nayi mafarki ban taɓa tsammanin zan gani da ido ba. Zan kula da Ramlah fiye da komai. Allah ya saka da alkhairi.” Ya ɗago ya kalli Mumy, yana kallonta kamar uwa “Mumy, na gode sosai. Allah ya saka da lada. Kin bani diyar ki, ni kuwa zan riketa amana.” Mumy tayi murmushi “Kai ɗan kowa ne. Kai yanzu namu ne gaba ɗaya.”

Na ji kamar ana rufe ni a ƙofar mafita. Ina kallon fuskoki na murmushi amma ba wanda ya leƙa cikin zuciyata.

Bayan daura aure, mutane na ci gaba da gaisuwa da godiya. Na zauna a cikin daki amma na ji kamar zan huta ne da kwana a tsakar rana, ba da miji ba. Ban san da wani farin ciki ba, sai da wasu hawaye ne ke cin karo da ni a ƙasan zuciyata. Auren da bai da tushe a so, ya fara a tsaye da addua da miliyoyi amma ba da albarkar zuciyata ba.

Ina zaune a ƙasa, durƙushe da jiki mai rauni, cikin ɗaki da ya zame min kabari tun da aka fara maganar aure. Sai ga Abba ya shigo. Muryarsa mai sanyi ta shiga kunnuwana cikin sallama “Assalamu alaikum, Ramlahtu.” Na ɗago kai a hankali, idanuna cike da hawaye da azaba. Sai ya matso kusa dani, ya zauna a gefen katifa sannan ya miƙo min wasu takardun kudi. “Ga sadakinki,” ya ce.

Na kalle shi. Hannu na rawa. Ban kai ga karɓa ba, sai ya ɗan daka min tsawa wani irin raɗaɗi ne ya tsinka zuciyata. Da rawar jiki, na karɓi kudin kamar na karɓi takardun da suka goge ni daga littafin rayuwa ta. “Alhamdulillah,” Abba ya ce, yana mai sauke ajiyar zuciya. “Yau na sauke nauyin dake kaina. Kitashi ki je, ki bi mijinki. Ina roƙon Allah ya baku zaman lafiya.” Sai ya dan dakata, yana kallona da idon da ke cike da ƙarfi da tsawa, ya ƙara “Kisani idan har kika bijire wa aure, to tabbas ban yafemiki ba. Ki yi masa biyayya, kinji ko?”Cikin kuka mai nauyi na amsa “Na ji, Abba. Kuma zan yi yadda ka ce.” A gefe, Kawu Hamza ya ɗan girgiza kai da takaici, ya ce “Haba Yaya Malam! Wannan aure fa babu tsari, babu kamu, babu yini, babu lefe. Wannan fa faɗuwar kima ce!” Kafin ya kai ƙarshe, Abba ya ce da murya mai zafi “Hamza! Duk abinda ka lissafa, akwai wanda Allah ya ce sune sharudan aure? Ka fita sabgar nan kafin in bata maka rai, tunda naga kai da kanka ba ka da hankali.”

Dakin ya cika da shiru. Fuskar Kawu Hamza ta canza, ya hadiye mamakinsa ya juya ba tare da ya ƙara magana ba. “Ke kuma,” Abba ya ce, yana kallona da karfi. “Mike! Ki je, mijinki na jiranki.”

Na miƙe da kyar, jiki a sanyi, na zura hijabina. Kamar gawar da aka shiryawa jana’iza ba amarya ba.

Na fito waje. Sai ga Mumy ta fito daga ɗaki, tana kuka mai kama da murmushi. Ta riko hannuna, ta ce “Ramlah… Na yafemiki. Allah ya sanya wannan aure ya zama sillar farin cikinki, Insha Allahu. Zamuzo miki ziyarar gida idan kun nutsu. Ki bi mijinki. Ki riƙe zaman aure da hakuri. Kibisa, kinji?”

Ban iya ce mata komai ba. Sai wani sabon kuka ya kubuce min.

Anty Luba ce ta zo, tana riko da hannuna. Tana fitar dani waje, zuciyata kamar za ta faso ƙirji. Na dago idona…

Gabana ya yanke. Kafafuna sun tsaya. Na ga Bashari.

Wani katoton namiji ne, mai dogon jiki da baƙin fata. Fuskarsa cike da gyambo da alamomin shaye-shaye da rikicewa. Bakin sa ya kone da sigari. Yana ta faman juyar da leɓe kamar mai fama da jaraba. A fuskar sa akwai yanka-yanka, kamar wanda yasha fada ko karan wuƙa.

Idanunsa kuwa? Kamar na dabba. Ba su cike da tausayi ba, balle kwarjini.

Wani irin rawa ne ya kama jikina. Hannuna ya saki. “Wannan shi ne mijina? Wannan dan daba? Wannan shi ne aka mallaka ni gare shi?”

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA SITTIN DA UKU.

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull