Kenza eBookz

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 36

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 36

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 36: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 36. Bajimawa sai ga Uwani ta shigo. Tun daga…

3,344 words

Bajimawa sai ga Uwani ta shigo. Tun daga ƙofa take dariya tana faɗin “Au har kin tashi! Ai yau ranar Lahadi, yau ce ranar cin kasuwar mu. Da idon ki biyu da kin ga yadda ake fafatawa, sai dai ai yanzu ne kika zo. Kuma nasan kema zaki fara sanaar nan kinga sai mu dinga shiga tare.” Na kalleta, na ɗan murmusa. Nace “Sannu da zuwa.” Ban rufe baki ba, sai na ji wata murya daga waje “Kee! Fito, mutafi!” Na juya. Muryar Bashari ce. Na mike a hankali “Sai anjima. Nagode sosai.” Uwani ta bini da idanu, kamar tana son ta ce wani abu, amma bata ce komai ba. Na fita waje. Wallahi, da na ganshi, kuka ya kusa kufcewa a bakina. Sigari biyu a bakinsa, yana wasa da hayaƙi kamar rakumi mai ciwon makogwaro. Da ƙyar na iya cewa “Sannu da zuwa.” Ya wani kalleni ya ce da murya mai cike da firgici “Ke fa baki san ki nemi mijinki ba ko? Dazu nazo kina bacci Ni ina can ina fama da wahala, ke kina nan kina bacci abunki Shige muje mana!”

Da muka iso karamin gidan Bashari yasanya aka gyara gidan ya sha gyara sosai. An shafe bangon da fenti mai kyau wanda ya ɗan kawata karamun gidan hakan yasa naji ɗan saukin zuciyata

Ko’ina tsaf! Kitchen din ma an kawo kayan bukata sai dai kurfoti yasiyo ba gas ba, Sai dai ko a haka, komai an tanada. Har da ashana da mai duk abinda mata ke buƙata don yin girki. Cikin ɗakinmu kuwa, Bashari ya sa gado da wardrobe, ba laifi. A falon kuma, kujera ɗaya ce kawai, amma hakan ma yayi. Bayan ya gama nuna min gidan, sai yace

“Gashi nan. Ki san yadda zakiyi da sauran kayanki.” Na gyara murya nace, “To.”

Na zage na gyara ko’ina. Kayana ma na shiryasu a cikin wardrobe. Ashe Mumy ta sanyamun wayata da laptop dina cikin kayan. Duk abubuwana tasamun hakan yasa naji wani ɗan sanyi a zuciyata.

Bayan gyaran na haɗa kurfoti. Duk da ban iya kunnawa ba duba da gas muke amfani dashi sai nayi kokari na dafa taliya. Na soya mai, babu yaji, sai na ɗora Maggi a gefe kusa da flask. Ina kokarin gyaran gurin, sai na ji muryarsa daga ciki yana faɗin “Ke! Zo ki cire mun kayan jikina!”

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA SITTIN DA TAKWAS.

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Gaba ɗaya na tsaya wuri guda kamar wacce aka soka da sanda. Ji nake zuciyata na bugu sosai Sai na jiyo muryarsa cikin masifa. “Ke! Ki zo ki cire mun kaya mana, ko sai na karya miki ƙugu!” Muryarsa kamar ana hura wuta. Ya ɗaga kai ya kalleni ido jajur,, hayakin sigari biyu yana fitowa daga hancinsa. Fuskar nan tasa kamar bai taɓa dariya ba, sai zaro idanuwan sa yakeyi. “Ke! Dallah malama! Bansan rainin hankali ba! Me kike kallo a Jikina? Idan baki zo ba, wallahi sai na fasa miki baki!” Na karaso da sauri, jikina yana rawa zuciyata cike da tsoro, na ce “Don Allah kayi hakuri... ba zan iya ba...” Cikin wani irin mugun sauri, ya daga hannu ya hankadani. Na faɗi kamar buhun shinkafa. Na ji kamar na soke a bayana, amma ko kuka ban iya yi ba saboda girman zafin da nake ji a zuciyata ya fi na jikina. “Kin ci sa’a! Ina da aikin da nake yi yanzu. Da sai na koya miki hankali.. Ware!

Ya fice da takun daba, wato irin wanda ke taka ƙasa kamar yana murza abu Duniya ta ta tsaya. Ni kuma na zauna a ƙasa, na fashe da kuka, cikin sanyi da kunci. “ Wannan ne wanda iyayena suka zaɓa min? Wannan ne mijin aure? Ya Allah.. Na share hawaye. Na mike. Ba don na so ba, don kawai ba zan ƙyale rayuwa ta cinye ni haka nan ba. Na shiga bandaki shi ma yanzu ya zama kamar na wani gidan masu hali. Bashari ya gyara gidan sosai masai, tiles, ko’ina na sheƙi kamar ba kazamun gidan danazo natarar ba.

Na zauna , ba don inason cin abinci ba sai don yunwa ta matsamin. Ciwon ƙai ya dan lafa, amma zuciyata bata daina nauyi ba. Gidan yayishiru, babu ƙarar komai. Ba wutar lantarki. Garin yafara duhu alamun dare yafarayi akayi sallah nayi Magariba. Ina zaune kawai.

Na so in kira gida. Na gaisa da iyayena. Duk da yadda suka tilasta auren nan, zuciyata ta kasa tsanarsu. Iyayena ne. Na rasa damar jin muryarsu. Wayoyina duka suna a kashe.

Na jawo littafina na makaranta. Na buɗe, na soma karantawa. Ban san abinda nake karantawa ba, amma ina son in manta da kaina. In bar wannan duniya da nake ciki na dan lokaci. Amma kafin ma na gama sakin numfashi, sai na ji karar motsi. Da farko naɗan tsorata. Sai kuma kamar tafiyar mutum. Sai bugun ƙyaure ya biyo baya.

“Taf! Taf! Taf!”

Na miƙe da sauri, zuciyata na dukan ƙirjina “Wanene?” na tambaya cikin rauni da tsoro.

Sai muryar mace ta amsa a hankali, “Ni ce... makociyarki.”

Na buɗe ƙofar da dan jimami. Wata dattijuwa ce, baiwar Allah mai kyau da natsuwa. Na ce, “Sannu da zuwa.”

Ta tsaya daga bakin ƙofa tace, “Ina fatan komai lafiya?”

Na yi murmushi, nace, “Lafiya kalau.”

“To mu shiga ciki mu gaisa,” tace tana murmushi mai taushi.

Na yi shiru, sai na juya na shigar da ita. Ta zauna a kujerar falon. Ta fara yawo da ido tana kallon ko’ina. Nace, “Ina wuni Baba.”

“Lafiya lau, ƴata. Nasan baki san ni ba. Ni ce makociyarki. Gidan nan na kusa ne. Kodayake mijinki ya fada cewa kar mu shigo gidan, amma ni nace ai ba laifi mu gaisa.”

Na ce, “Nagode sosai. Ina da ruwan pure water . Bari na kawo miki .”

Na mika mata. Tayi godiya sosai ta karɓa. Sai ta kalle ni sosai. Ta ce “Wallahi nayi mamaki da gaske. Allah ya bawa Bashari sa’a. Yarinya kamar ke? Tsaf. Kina da kamala, kunya, da tarbiyya. Amma... soyayya ce ta hada ku?”

Na dan kauda kai. Sai nace da ita, “A’a, iyayena ne suka zabe min shi.”

Tayi ajiyar zuciya. Ta girgiza kai.

“To, kin ji. Wannan rayuwar akwai aiki a ciki. Da kike gani haka, mijinki yana da halaye biyu akwai kyauta da ibada, amma akwai ɗabi’un da babu kyau a faɗi da baki. Shaye-shaye da zafin rai. Kiyi hakuri, ki dage da addu’a. Allah ne kadai mafita.”

Na kalli dattijuwar. Murya ta sanyi amma tana ƙunshe da gaskiya. Sai ta ci gaba da cewa “Shawara ɗaya zan baki. Idan kina son zaman ku ya daɗe, to kar ki yawaita fita. Kar ki yawan shige-shige. Shi ba ya so, kuma ba ya son makwabta su riƙa zuwa. Ki kula da kanki, da aure ki mayar da hankali. Ki dage da addu’a, karatun Al-Qur’ani, da neman tsari a wajen Allah.”

Na kalli dattijuwar, zuciyata cike da tunani. Nace, “Wannan wane ƙauye ne Baba?”

Ta ce, “Sunansa Majiya.”

Na ce, “Nagode sosai.”

“Kinji dai? Duk wanda yayi biyayya ga iyayensa, Allah baya tozarci. In shaa Allahu zan dinga leƙowa in gani ko lafiya. Allah ya baku zaman lafiya. Ki zama mace mai haƙuri da addu’a.”

Na yi mata godiya. Ta fice tana addu’a. Na zauna cikin shiru. Na miƙe na kulle ƙofa. Na zauna a kan kujerar da ta baro. Sai na ce a raina, "Allah, ka sa wannan dattijuwa ta zama ƙofa ta rahama gare ni.

Tun kafin ya shigo, na riga na shirya masa abinci da ruwan pure water da karamin flask na ruwan mai zafi. Ko da zuciyata cike take da baƙin ciki, na dage nayi komai da kyau saboda kada a samu wata matsala. Na shirya komai a saman darduma a tsakiyar falon.

Na ji takun sawunsa kafin ya buɗe ƙofa. Yana taka ƙasa kamar yaro da ba ya jin magana, yana ɗaga kafafu kamar wanda yake rawa. Kafin na hango fuskar sa, wani wari ya ratsa hancina wari Yana shigowa, baiyi sallama ba nace masa“Ina wuni,” sai hararata da idanuwansa jajaye kamar na karnuka da suka sha tsumi. Ya rataye sigari a bakin sa yana hura hayaki a hankali, yana kallona kai tsaye kamar yana cin wani abu da ido.

“Ina abincin?” ya faɗa.

Na nuna masa darduma da abincin da na tanada, ina ɗan sunkuyar da kai. Ya zauna da wani irin diris, sai ya kai hannu ya buɗe flask, ya soma ci. Amma ba cin abinci kawai yake ba, yana kallona sosai, kamar wanda baitaɓa ganina ba.

Yana zuba abincin a baki, yana hura hayakin sigari, yana zuba min ido. Wani lokaci yana sumbatu da bakin sa, yana cewa “Hmm… kin girma sosai. “

Na sunkuyar da kaina Amma jikina ya fara rawa.

“Ke, tashi ki zo nan! Ko kin manta ni mijinki ne?”

Yana gama rabin abinci, sai ya ajiye. Ya miƙe tsaye a hankali kamar biri. Ya nufo inda nake zaune. Kafin nace komai, sai ya durƙusa a gabana, yana kallon fuskata da wani irin kallon daba.

“Ke, ki duba ni. Ko na canza?”

“A’a,” na ce cikin sanyi da ɗan razana.

Sai ya ƙara matsowa kusa. Ya jawo rigarsa da gumi ya cika ta ya soma cire ta, yana cewa

“Bari na dan huce… kinga yau rana tayi zafi...”

Wani sabon wari ya cikamun hancina. Na dan ja baya, amma ya ƙara matsowa. Ya kamo kaina da hannu ɗaya.

Na soma karkarwa. Na ji idanuna sun cika da hawaye. Sai ya matso sosai, bakin sa a kusa da kunnuwana, sai naji ya ce “Rage zafi kawai fa zanyi shine kike Haka?”

Kafin na iya cewa komai, sai ya bude baƙinsa yana kokarin sumbatata Wani irin wari ya gangaro daga bakinsa wari mai cike da sigari, miya, da ƙazanta. Na ji zuciyata ta murɗa. Sai naji kamar amai zai fito. Na rufe baki da sauri, na ɗan ja gefe, zuciyata na bugawa.

Ya jawoni da ƙarfi kamar wata jaka. Na ji ƙafafuna suna rawa.

“Kinsan fa tun da muka iso garin nan ban samu dama ba. Kin ci abinci lafiya, ko? To yanzu ni ma sai na ci naki.”

Wani abu ya tsaya a makogwarona

Idanuwana sun ciko da hawaye, zuciyata ta kulle. Na matsa baya da kyar, na ɗaga hannuna nace “Don Allah, kayi hakuri... bani da lafiya.”

“Ai haka nake so,” ya faɗa da wata murya kamar an haɗa ƙarfin rakumi. Yana faɗar haka, sai ya damƙe ni da hannu biyu, ya rungume ni kamar zai shanye ni. Jikinsa cike da zufa da wani ɗan banzan ɗoyi. Idanunsa sun cika da wani mugun nufi, kamar ba mutum bane, kamar wani dabba mai yunwar nama. “Ki daina nuna sanyi! Kin fahimta? Ke matata ce! Kuma yau ba zan yi hakuri ba!”

Na fara kamewa, zuciyata tana huci kamar wutar hura. Na ɗaga hannu zan turesa, amma ya riƙe ni da ƙarfi, yana kokarin zare rigata. Sai na ji kamar zan haɗiye kaina. Na ji hawaye sun cika idona, zuciyata ta shige ƙasa.

“Don Allah, ka daina... Bashari don Allah...”

Yana dariya a hankali, irin dariyar dabbanci.

“Don Allah?ina da hakki a jikinki, kuma yau ba zan bar ki ba!” Ya cusa kansa a wuyana, yana hura numfashin sa a fuskata. Warin bakinsa ya shiga cikin hancin na.

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA SITTIN DA TARA

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Wayar sa ce ta fara ƙara sosai Alamu a ana nemansa da gaggawa. Yana cikin kokarin raba ni da kayana kenan, sai ya hankadeni gefe da ƙarfin da ban zata ba. Na faɗi saman gado, jikina yana kakkarwa. Ya ɗauki wayar cike da fushi da masifa, sai huci yakeyi.

“Helo? wanene ne kuma cikin daren nan!? Da yawarka oga menene!?”

Na ƙara matsawa gefe, ina kokarin bin sa da ido cikin tsoro. Amma kafin in fahimta me ke faruwa, sai naji cikin wayar ana cewa “Kai! Ganinan! Wallahi, sai na sassare musu jiki! Kai kai... karka ce zaka gudu yanzu! Ai sai na wanke jinin su da hannu na!”

Zuciyata ta buga. Maganganunsa sun narke cikin kunnuwana kamar ƙasa da ruwa. Na soma jijjiga kai a hankali. “Sassare jiki”? “Jini”? Me ke faruwa haka? Bashari ya dungura kafarsa, ya shige cikin daki kamar iska. Sai naji karar buɗe akwati ko drawa. Na ɗaga kai, kuma nan fa na gan shi da wata sharbebiyar wuka a hannunsa sabuwa, mai tsini da kauri, tana sheƙi da hasken fitilar da ta rage kaɗan tana flasha.

Bai kalli inda nake ba. Bai ma ce da ni komai ba. Yana tafe yana ihu, yana faɗin

“Wallahi yau sai na sha jininsa! Sai na koya musu darasi! An raina ni ne!?” Ƙarar ƙafafunsa da na wukar sun cika gidan Ina zaune a gefen gado, jikina yana rawa. Na kasa miƙewa, na kasa kuka. Hannuna biyu na sa su goge fuskata, amma hawaye na fita a idanuwa na “ Wayyo Allah na… wannan wane irin mutumi ne? Wannan wa ne kuka bani,”

Tawani bangaren kuma sai na ji daɗi. Allah ya taimake ni. Wannan kazamin mutumin bai samu damar yi min komai ba. Na miƙe na rufe ƙofar ɗakin da kyau. Na dafe zuciyata, na sauke ajiyar zuciya.

“Allah na, kai ka kare ni. Kai kadai ne garkuwata.”

Na nufi inda Qur’ani na yake. Na ɗauko shi, na zauna. Na buɗe a hankali, na soma karantawa. Na karanta da niyyar roƙon kariya, da nutsuwa, ina jin shi ne abinda zai kwantar min da hankali.

Na ji zuciyata ta fara sanyi. Na lumshe ido, Bayan na gama, na ajiye Qur’anin a gefe, na gyara gadon da kyau. Na kwanta a jikin gado, na jawo zanina, na rufe jikina.

Cikin kwanciyar hankali na soma karanta addu’ar bacci “Bismillahi Allahumma ahya wa bismillahi amut…”

Na lumshe ido, a hankali naji bacci yana zuwa. Barci ya ɗaukeni cikin kwanciyar hankali da natsuwa.

Na farka da asuba, na yi sallah cikin natsuwa. Na karanta azkar kadan, na kwanta na sake komawa bacci. Lokacin da na sake farkawa, rana ta fara haskawa. Na tashi na gyara ɗaki, na share. Zuciyata dai ta fara samun sauki fiye da jiya.

Sai dai... kafin in kai ga hada breakfast ko tunanin mene ne, sai kawai na ji ƙarar ƙofar gida an bubbuga da ƙarfi.

Taf! Taf! Taf!

Na ƙaraso kofar da sauri, na bude Bashari neyashigo. Amma ba yadda nake tsammani ba Jikinsa duk ya baci da jini, rigarsa ta yage, fuskar sa ta kumbura. Hannunsa yana rike da gefen ciki ana iya cewa an sassareshi da wuka. Na firgita. “Innalillahi…me ya faru?” Bai amsa tambayata ba. Ya kalleni da ido na bacin rai. Idanunsa sun yi jajir, jikin sa yana bari. Amma ko da yake yana jin rauni, maganar da ya fara da ita ba na neman taimako ba bace… “Ina giyata!?” Na tsaya na zuba masa ido. “Giyarka fa? Wace giya?” Ya zaro ido. Yana nuna ni da yatsa. “Kar ki raina min hankali! Ban ɓoye miki inda na ajiye kwalban giya ta ba!? Tunda na fita nake shan jini da sara na dawo na kasa samun abinda zai narke ni! Kin ɗauka zan mutu ne? Ke kika ɓoye min giya!”

Na ɗan ja baya. “Wallahi ban taɓa giyarka ba. Ni fa ban san ma inda kake ɓoyewa ba banma san yadda take ba...” Nafaɗa jikina na mugun ɓari.

Bai saurare ni ba. Ya fincikoni daga bayansa

“Ni fa ba mutum bane da zaki raina! Ke matar aure ce amma kina wasa da zuciyar ɗan daba!? Wallahi sai kin gane wa kika aura yau!”

Ya jawoni Yashiga duka kamar an aiko masa ni yayi mun hukunci mari kusan 5 yayimun. Na yi ƙoƙarin guduwa, amma ya rikeni da hannu guda, sauran hannun yana buguna min wani igiya kamar tana warware min fata. Ina ihu ina kuka. “Don Allah kayi hakuri!…” “Ina giyata!” yana ta maimaitawa kamar mahaukaci Na share hawaye ina girgiza kai, amma shi ba hankali gare shi ba. Ya zane ni a baya, a hannu, a kafa. Na zube ƙasa da kuka.

“Ya Allah! Ya Allah! Ni ban ɗauka ba wallahi…!” Sai da ya gaji. Ya hankaɗani gefen bango Ya juyo ya zube a kujera, yana huci kamar dabba. Jinin raunin sa yana zuba, amma har yanzu bai damu ba. Wani yanki na zuciyata ya ce, yau nashiga uku yaje yayi shaye shayensa… Na tsaya ina hawaye. Cikin zuciyata nace “Ya Ubangiji, idan mutuwa ce tafimun alkhairi ka yanke ta cikin salama. Amma idan rayuwa ce, ka fitar da ni daga hannun wannan mugun mutum.”

Ina kwance a gefen daki, jikina cike da ciwo, bayana yana ƙuna kamar an hura wuta. Bulalar da Bashari ya yi min tana yawo a jikina. Idanuna sun kumbura da kuka. Sai na ji karar ƙofa da ƙarfi an bubbuga.

“Ramlah! Ramlah! Ki buɗe ƙofa! Na ji ihunki!”

Na mike da kyar, na kalli Bashari da yake zube a kujerar daki jini yana zuba daga gefen sa, amma idonsa cike da masifa. Na ce da muryar kuka “Baba ce... Baba ta leƙo...”

Kafin in isa ƙofa, sai ga Baba ta turo ƙofar da kanta ta shigo. Da alama ba zata tsaya kallo ba, tunda taji ihu daga wajen. Da ta shigo, sai ta tsaya a tsakiyar falon. Ta kalli ni da idanunta masu rahama, sannan ta kalli Bashari “Kai Bashari! Me kake yi haka!? Wannan ai ba auren mutunci bane! Yarimya mai tarbiya haka amma kuma ka zane ta? Wannan fa rashin hankali ne! Wallahi akwai Allah!”

Kafin Baba ta kai ƙasa da maganarta, sai Bashari ya tashi da wuka daga gefe, ya nuna mata hannu da fuska cike da barazana “Ke tsohuwa! Wacece ke da zaki shigo min gida kina magana kamar ke ce uwarta!? Ke baki da aikin da ya wuce shiga rayuwar mutane? Ko dai ke ce kika ɓoye min giya!?”

Na razana. Baba ma ta firgita, amma bata matsa ba. Tace “Ni? Kai Bashari, ni da shekaru na, zaka ce ni ce na ɓoye maka giya? Ai wallahi da kanada tarbiyya da tsoron Allah, da baka sha giya ba!” Sai ya zabura kamar zai bugeta “Wallahi idan baki fice daga gidana yanzu ba, sai na ci mutuncinki!”

Baba ta zuba masa ido. Tana ganin hakan, sai ta ja baya a hankali. Amma kafin ta fita, ta juyo tace “Ramlah! Ki saurare ni.Ki natsu ki cigaba da addu’a. Ta fice cikin zafin rai, tana girgiza kai. Ni kuma na tsaya a tsakiyar ɗaki, zuciyata na dukan ban san me zan yi ba. Sai Bashari ya kalle ni ya ce da dariyar raini “Ke idan ba ku fita daga harkata ba, sai na koya muku darasi na gaba da ba zaku manta ba!”

Duk Yadda jikina yakai gurin radadi da zafi kallon yamkan cikinsa nakeyi amma shi ko ajiƙinsa karshe Ma sai ya dakko taba yashiga zuƙa yana cillarwa. Wallahi shaye shaye masifa ne ɗan natabbatar yasha wata ƙwayar ce ta bugar dashi haka na tashi dakyar nashiga doramana abunda zamuci.

*****************

Nana hadizaƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA SABA'IN

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

PARIS

Ayshatu na kwance luf a gefen jikin mijinta, As’ad. Tana tsakankanin cinyoyinsa, yana wasa da gashin kanta cikin natsuwa. Hannunsa yana shafa kuncinta a hankali, “Ayshatu…” ya furta sunanta cikin kasalalliyar murya mai daɗi, kamar kida ce ke fita daga leɓunsa.

“Na gode da kasancewarki tawa. Kin fi komai daraja a rayuwata.”

“Ina sonki Ayshatu...

Ayshatu tayi dariya cikin shagwaba, tana lumshe ido. Ta shafa masa kirjinsa da yatsunta masu laushi

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull