Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 38
Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 38: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 38. Sun rungume juna cike da ƙauna kafin ya…
3,363 words
Sun rungume juna cike da ƙauna kafin ya fice, yana shafa kanta. “Take care of the house. Don’t forget to drink your chamomile tea before bed.”
Ayshatu ta bishi har bakin ƙofa, Ba tace komai ba, kawai ta tsaya tana kallonsa, idanunta cike da hawaye.
Yana buɗe ƙofa, ya sake juyowa ya dawo ya rungumeta, yana sumbatar goshinta. "Ki kula da kanki."
Sai da motarsa ta ɓace daga gani kafin Ayshatu ta saki ajiyar zuciya ta saka sai kawai ta fashe da dariya tana faɗin, “Sannu da tafiya, Habibien duniya. Amma Alhaji Muqaddam ya fi ka komai.. Tana shiga daki, ta canza kaya, ta nufi wardrobe ɗinta ta zaro Goyard bag guda biyu da kuma Chanel tote ta cika da kayan da zata bukata.
Ta ɗauki wayarta, ta kira Muqaddam, tana murmushi.
“Baby, I’m coming over. I miss your scent already.”
Muqaddam ya amsa da “The house is yours. Gidan yana jiranki.”
A cikin mintuna talatin, wani Mercedes Benz S-Class mai number plate “M-QDM 1” ya zo ya ɗauketa. Driver nata ya bude mata kofa, tayi settling cikin leather seat mai sanyi da kamshin Italian interior.
Ayshatu ta fice daga gidan As’ad cikin halin da ko tsuntsu bai ji, balle mutum. Amma zuciyarta ta cika da sha’awar wani… yayin da wanda ya fi ƙaunarta ke jiranta a Naija, cikin amana da soyayya. Alhaji Muqaddam yana falo, cikin dogon wando da riga mai kyan gaske, yana karanta wani kasuwanci a system. Ganin Ayshatu sai ya miƙe yana fadin:
"Baby... You came."
Tana ƙarasowa ta faɗs jikinsa kamar wata marainiya da aka manta da ita. "I missed you," ta ce da sanyi a muryarta.
"Ina nan yanzu. And you won’t have to be lonely again," ya faɗa yana ja da ita har cikin Luxury Living Room, inda komai ke sheƙi da tsari na manyan masu kudi.
********
Washegari da safe, garin Paris ya kasance cikin sanyin hasken safiya da iska mai ɗauke da ƙamshin barin hunturu. A wajen da ba kowa ke zuwa ba Private Terminal na Bourget Airport wani jet mai launin white pearl da fari ya tsaya yana jiransu.
As’ad na sanye da farin Zegna Agnona senator, da takalman Louis Vuitton masu ƙyalli. Hannunsa ɗauke da iPad ɗin business schedule, sai agogon Cartier da ke haskawa. Umar, ɗansa, yana bayansa cikin black Dolce & Gabbana suit sharp and commanding.
Suna tahowa cikin natsuwa, matakin kowane ƙafarsu yana nuna power. Ma’aikatan filin jirgin da ke kula da VIP suna tsaye daga gefe suna rusunawa da gaisuwa “Welcome Your Excellency, Mr. As’ad Babangida. Your jet is ready.”
Yayi murmushin manyan mutane, yana girgiza kai cikin salo. Umar ya kalle shi yace “Dad, even after all these years, I still get chills seeing how much respect you command.”
“Zuciyar mai nutsuwa ba ta ƙasƙantar da kai, Umar,” As’ad ya faɗa, yana taka gangar tafiya zuwa jirginsu.
Wurin zama cikin jirgin ya kasance mai alfarma ce da kowa ke mafarkinta cream leather seats, gold plated trims, da furen blue hydrangeas masu ƙamshi. Ana shan espresso daga Versace gold mugs, da nutsar da kansu a cikin taskar business updates da Umar ya shirya.
As’ad ya ɗan danna remote, plasma screen ta kunna, showing the flight path to Nigeria. Yace "Gobe zamu isa fadar Sarki kai tsaye. Kayi magana da Palace manager din?" "Yes dad, every royal protocol is set. Sarki yana jiranmu kamar yadda ya saba. Kai fa har yanzu kaine fitilar gidan nan.”
As’ad ya lumshe ido, yana maimaita zikirin da ya saba kafin tafiya. Jirgin ya ɗaga.
ABUJA PRIVATE AIRPORT TERMINAL
Saukar jirgin ya kasance cikin tsari da ƙima. Gidan jirgin masu kudi na Abuja an rufe shi gaba ɗaya don karɓar As’ad Babangida. Black Rolls Royce Cullinan, Bentley Mulsanne, da Maybach S600 Guard suka jeru a gaban red carpet.
Royal drummers na masarauta suna busa kaɗe-kaɗen masu daraja, yan tsakar gida na Sarauta suna tsaye cikin rigunan masarauta da rawani. Gaban kowanne motar akwai furen farin lilies da tambarin gidan sarauta.
Sarki ya aiko da babban Dan Majen Fada domin ya jagoranci tarba. “Fadar Sarki tana farin ciki da dawowarku, Ranku ya daɗe. Masarauta ta buɗe ƙofa gareku.”
Umar ya kalli mahaifinsa, yayi murmushi yace
"Dad, this is home. You’re a born royal, no matter how far you go."
Motar As’ad ta fice daga tashar jirgin, tana bi ta cikin tsararren convoy. Titi ya kasance a rufe, 'yan sanda da guards na Fadar Sarki na yi musu rakiya. Mutane na gefen hanya na rusunawa suna gaisuwa, wasu na ɗaukar hotuna daga nesa.
Wanda bai san ko waye As’ad ba, daga wannan tarba sai ya fahimci ba kowane attajiri ne yake da alaka da masarauta ba.
Gidan Sarki ya kasance ƙatuwar fada da tarihi. Babban kofar shiga ana yaye ta da rubutun Larabci, ƙasa na murjani, sannan tagogi na stained glass. Da zarar suka shiga "Masarauta ta buɗe hannunta ga ɗanta. Barka da zuwa, Alhaji As’ad Babangida ɗan sarki kuma Attajirin kasarmu,” cewar Sarki, yana miƙa hannu da murmushi mai cike da ƙwazo da soyayya.
“Godiya nake, ya Mai Martaba. Wannan gida ne na alfarma da albarka.”
As’ad ya rusuna da ƙwantar da murya irin ta masu hali. Daga nesa, mahaifinsa ya kalli Umar yace: “ Muna maraba da umaru Farouk Jikan Babangida” Umar yazo yarissina yana masa gaisuwa ta girmamawa “Wannan ɗa ne na daraja, wanda kowa ke alfahari da shi.” Sarki yafaɗa yana murmushi.
********
A cikin ɗaki mai yalwa da tsari irin na sarauta, Haneefa tana kwance saman lafiyayyen katifarta, zuciyarta cike da shiru. Duk da zaman sarauta, amma rayuwarta na cike da sake-saken tunani, musamman tun bayan rabuwarta da As’ad.
Tana cikin wannan tunanin ne sai aka buga ƙofar da karfi, ƙofar ta buɗe. Wata daga cikin ‘yan munafurcin masarauta, mai suna Gwaggo Lanti, ta turo kai cikin ɗakin tana sanye da alkyabba mai sheƙi “Haneefa… Ai wallahi Allah ya ƙaddara! Kin ga tsohon mijinki As’ad? Ashe dama mace zata rasa rabo irin naki har ta bar namiji irin As’ad?”
Ta tsaya tana kallon Haneefa da murmushi mai cike da ƙyashi, sannan ta cigaba “Gashi can yazo da ɗansa Umar ɗan Dubai fa! Yasha gayu, ga kyau! Ni dai gaskiya nayi bakin ciki da rabuwarku, amma yanzu kin ci amanar kanki da kanki.”
Kafin Haneefa ta iya cewa komai, sai Zainu, yayarta ta shigo cikin ɗakin tana dafe da hannu “Ai kema kinsan Haneefa ta cuci kanta. A yanzu da zata ci gaba da gina rayuwa da As’ad sai ta zabi ta bige da faɗa, da gardama, sai gata ta rasa komai. Ke kika lalata rayuwarki da hannunki.”
Haneefa ta ɗaga ido tana kallon su, ba tare da tace komai ba. Tayi shiru amma idanunta sun cika da hawaye da bata bari sun zubo ba.
Ta daure murmushinta cikin haƙuri, ta ce a hankali “Zainu… Ina kika ganshi?”
Zainu ta tabe baki, ta ce “Ina? Ashe ba kuji ba? Yanzu yanzu ya shiga fada tare da Umar. Na gansu da idona. Kuma ba karya zance ba… duk wani abun da kika rasa na rayuwa yana hannunsa yanzu.”
Cikin sauri Haneefa ta miƙe. Zuciyarta ta buga ba dan wata sha’awa ba, sai dan wani kishi na zuciya, wani murɗi na cikin rai.
Ta sa gyale a kai, ba tare da ta saurari ƙarin zuga daga Zainu da Gwaggo Lanti ba, sai ta fice da sauri, takalmin ta na sheƙi da karan ƙasa.Tana ficewa suka bita da ido.
Gwaggo Lanti tace“To ai fa ba da an kalli baya ake gina gobe ba. Amma dai muryarta na nuna har yanzu tana da ruwa a zuciya.”
Zainu ta murmusa “Ko kuma da gaske take so ta dawo, sai dai... yanzu wallahi yafi karfinta.”
*****************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA SABA'IN DA UKU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Yau garin mun tashi da hadari.
Gajimare ya turnike sararin sama, iska na kaɗawa da ƙarfi Abin ya ƙara cusa damuwa cikin zuciyata.
Kusan kwana uku kenan Bashari bai dawo ba.
Kafin ya tafi, ya ce min akwai wani 'aiki' da zai yi. Amma tafiyarsa ta zamar min wata 'yar walwala a zuciya. Domin wallahi... tsoron Bashari nake ji. Bai fi kwanaki biyu ba cikin dare sai ya ɗauki makami ya fita kamar ɗan fashi. Idan ya dawo kuma yayi shaye-shayensa,
Idan ya ɗan sha, sai ya hau ni da duka kamar jakarsa!
Zan kasance ina kuka, ina kukan da ba ya tsayawa, amma sai ya ɗora. Ba ni da ƙarfi, ba ni da gata. Tun da farko ban gane ba, har sai da Babah ta ce min “Ke yarinya, idan kika ji Bashari ya dawo cikin dare, to ki ruga, ki buya! Wallahi ba a hayyacinsa yake ba!”
Danaji karar ƙafarsa nake guduwa. Har na zama kamar berar gidan da ke tserewa don ta rayu. Na daina sanin kwanciyar hankali. Rayuwa na... ta zama kunci da fargaba.Idan dare yayi, ba zan iya bacci ba. Idan rana ta fito, zuciyata na bugawa. Ina tsoron kada na ga Bashari ya shigowa.
A nan kauye babu wanda zai ce masa komai. Kowa na tsoronsa. Ɗan daba ne, kuma ba kowa ne ke son jefa kansa cikin rikici da shi ba. Koda yake yana da mahaifi da uwa, sai ka rantse bai da wata alaka da su. Gidansu baya shiga. Iyaye na kauyen nan ma ba su so ‘ya’yansu suyi hulɗa da shi.
Kusan sati guda kenan ba mu samun huta. Allah ya taimake ni da wata ƙaramar torchlight da Bashari ya sayo min, ita nake amfani da ita wajen haska gida idan dare yayi. Sai dai duk da torchlight da system da wayata da na samu daga gida, babu wutar lantarki ko ɗigo. Gidan ya dinga ɗim, na zauna cikin duhu ina haska kaina kamar wata baƙuwar bakar fitila.
Ganin hadari ya haɗu da iska ke kadawa sai na kwashi shanyar kayana da na ɗora a jikin ƙugiya, Kurfuto da na dafa abincj kuma na ajiye su cikin kitchen , ina gyarawa, sai na hango Habu jikan Babah yana kokarin shigowa cikin gidan.
Habu ɗan ƙarami ne, yana da shekara goma sha ɗaya, Shi ke taimaka min yanzu idan ina buƙatar ɗan taimako a gida. Babarsa da farko bata yarda na riƙe shi ba saboda tsoron Bashari. Sai dai yaron mai kwadayi ne, tun da na fara bashi abinci sau ɗaya, sai ya fara zuwa kullum. Ni kuma ina tausaya masa, saboda kullum kamar bai ci komai ba.
A yau ma, yana shigowa cikin kitchen ɗin sai ya tsaya yana kallona. Na kalle shi na ce,
“Habu, ga abincinka nan. Ganin hadari ya fara haɗuwa, ka ɗauka ka wuce gida kafin ruwa ya fara sauka.”
Sai ya sosa ƙeya, ya ce da fara’a,
“Tohm, nagode Antin Birni. Allah ya saka da alheri.”
Ya ɗauki abincin cikin farinciki, sannan ya juya da sauri ya fice, yana ɗan rera waka kamar yaron da aka bai wa gwal.
Na bishi da kallo, zuciyata cike da tausayi da kauna. Yaron nan ya fi mutane da yawa tausayi da ƙauna, duk da karancin shekarunsa.
Sai iska ta kara tasowa. Wani guguwa ya kwashe ƙofofin kitchen ɗin, ina tashi zan rufe kofofi sai wani faɗuwa naji a bayana. Torchlight dina ya faɗi ƙasa ya mutu. Na sunkuya na ɗaga shi, na busa. Na kunna shi a hankali yana ɗan haske kadan.
Nace cikin kaina, "Allah dai ka kare ni daga dukkan sharri a gidan nan."
Daga nan na koma ɗaki. Na zauna kan tabarma da aka shimfiɗa tun safe. Wato duk bayanin da zan muku game da Bashari, wallahi bazaku taɓa fahimtarsa ba ko kaɗan. Sai dai in fa kun ganshi da idonku. Wannan mutumin ko in ce, wannan halittar ba wai ɗan daba bane kai tsaye, cikakken aljani ne cikin mutane. Idan nace muku babu wata makociya da ke shigomun, kuna iya ɗauka kamar ƙarya nake yi, ko? To wallahi da gaske nake yi saboda kowa a kauyen nan yana tsoronsa, balle ni da nake da aure da shi.
Babah ce kaɗai ke shigowa wajena ita ma ba yanda take so take shigowa ba, dan har ita ma ba a kyale ta.
Da dare yayi, bayan sallar isha’i, na zauna ina lazumi a tsakar ɗaki. Na sanya hijjabina, na jingina a bango, ina karanta “Hasbunallahu wa ni’imal wakil” kamar yadda Babah ta koya min. Ta ce idan ina karanta hakan, komai tsorona zai ragu. Kuma Allah zai tsare ni.
Kamar kullum, sai nayi kwanciyata kan kujerar tsakar ɗakin. Ina kokarin tashi na rufe ƙofar ɗaki, kawai naji an banko ƙofa da ƙarfi! Ji nayi kamar zuciyata ta tsaya! A firgice na mike, nayi kokarin guduwa zuwa ɗaki kawai sai na hango shi...
Kamar an cilloshi. Fuskar nan tasa cike da yanka-yanka, wasu wurare har sun kumbura. Jikinsa duk ya baci da jini. Wata kalar wari ne mai cike da tsami da shan jini ya doki hancina. Ina kallonsa kamar wanda ba mutum bane. Ba a cikin hayyacinsa yake ba.
Na sauke ajiyar zuciya, na yi saurin ja baya, amma ya riga ni ya fizgo hijjabina ya rufeni da duka. Ba wata tambaya, ba wata magana duka kawai! “Ke karuwa ce! Yar iska ce! Ke! Dama haka kike? Kin boye cikin shege a cikinki!” haka yake yimin ihu yana caccaka mini duka, yana tura ni bango da ƙarfi kamar jaka.
Na hau ihu, "Wallahi ban aikata komai ba!" amma wannan ba zai hana shi ci gaba da wulakanta ni ba.
Ya kamo ƙuguna, ya buge ni da bango, sai ya ce: “Ni ba dan iska bane! Amma ke sai yanzu nasan ke karuwa ce!”
Duk da kokarina na guduwa, babu hanyar tserewa. Kawai sai muka ji an banko ƙofar gida da ƙarfi. Wani saurayi ya shigo da gudu Aliyu Awilo, babban ɗan daban gari, wanda shi da Bashari suke tafe.
Ina zaune a ƙasa, jiki a sarke, sai kawai na ji shi yana fadin
“Haba oga! Haba aljanin dare! Wannan maccen ka ke bugawa haka?!”
Kafin Bashari ya ankara, Aliyu ya zaro wata allura daga aljihunsa ya soka masa a hannun hagu. Bashari yayi wani irin ƙara kamar zaki, sai kuma ya fara dushewa a hankali kamar bishiyar da ruwa ya tsinke. Ya rufta a ƙasa yana nishi kamar mara lafiya, yana karyar baki har bacci ya ɗaukesa.
Ina zaune gefen bango, jiki a sarke, hannu na rawa. Na kasa motsi, zuciyata na bugawa kamar za ta fashe. Sai Babah ta shigo cikin tashin hankali tana sanye da mayafi, ta hango ni a ƙasa tana fadin.
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Ya ubangiji! Wannan mutumin wata rana zai kasheki wallahi! Ramlah ki tashi mu tafi!”
Ta karaso ta tsalleke jikin Bashari, ta rungume ni kamar yarta . Amma ni nakasa jikina yayi sanyi, hawaye na gangarowa
Babah ta girgiza ni tana kuka
“Allah yasa bai bugeki da wuya ba Ramlah... Allah yasa...”
Na ƙara rungume ta. Na rusa kuka kamar ƙaramin yaro. A cikin zuciyata ina fadin
“Ya Allah, me nayi da na cancanci irin wannan azabar?”
*****************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA SABA'IN DA HUDU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Baccin ya ɗaukeni ne cikin ciwo da gajiya, amma da safe na tashi da duka jikina yana rawa da zafin zazzabi. Bashari kuwa ban gan shi ba a gidan. Da ƙyar nayi sallar asuba, na dora farar shinkafa ba tare da yaji ba kawai Maggi na sa domin babu ƙarfin da zan iya dafa komai mai nauyi.
Ina jin bude ƙofa da ƙarfin gaske, sai na ruga da gudu na shige ɗaki. Ashe Bashari ne, sai yasa dariya yana cewa,
“Wato na zama abun tsoro gareki ko?”
Kafin na ma ce uffan, naji Aliyu ya karɓa da magana mai zafi “Ai da gaskiyarta da ta zauna kana shigowa ka halakata da duka a wofi” Bashari ya saki wata ballagazar dariya yana faɗin “Kai Aliyu, ka daina shirme! Kana jin abin da ta ce? Ta ce fa Ramlah cikakkiyar karuwace ce mai bin maza. Kada na sake nayi wasa da ita! Gaskiyar Mumy ce, zan koya mata hankali...”
Cike da firgici da baƙin ciki, na dafe kirjina ina furta “Innalillahi... Mumy?”
Idanuwana suka cika da hawaye, zuciyata ta shiga wani irin radadi da ya fi ƙarfin jiki. Wane irin sharri ne wannan? Nayi auren ma bazata kyaleni ba yanzu kuma sharrin karuwanci tayimun.
Daga can naji muryar Aliyu awilo yana kwarara wa Bashari ihu yana fadin “Kai Oga! Kana ganin wannan sharrin gaskiya ne? Ka manta yadda kishiyar Babanka ta yaudare ka a baya? Ka manta yadda ta jefa ka cikin halaka? Wannan mumy take ko wa wallahi karya takeyi shegiya munafukar tsuhuwa”
“Kai ka kalli Ramlah tayima kama da ƴan bariki? Na tabbatar maka idan yar bariki ci yo tabbas wallahi saita gudu lokacin da akace za'a aura maka ita amma ka kalli yadda tayi biyayya kuma gana ganin yar bariki haka? Kasan irin yan iskan matan nan fa idan ka rasa da hannu ka rasa da kafa! Allah ya baka wannan yarinyar mai kamun kai, amma ka tsaya kana sauraron gulmar tsohuwar guzuma!”
Sai naji Bashari yayi shiru, daga nan sai yace
“Kaga fa Aliyu, wannan tsohuwar guzuma zata canza min kwakwalwa ne. Amma ai nasan irin matan bariki, basa jin magana balle ita wannan yarinyar ƴar aljanna.”
Aliyu ya goge hanci da bayansa yana cewa “To sai ka gama bugun kwakwalwarka ne? Dan Allah Oga, wannan yarinyar fa ta amince dakai lokacin da duniya gaba ɗaya ke gudunka. Ta tsaya maka lokacin da kowa ya kaurace maka. Wlh Ramlah ba mace bace da za’a watsar da ita kamar pepsi a titi! Nagaya maka ka riketa hannu bibbiyu wallahi. Ka bawa makiya mamaki Oga, ka riƙe ta da hannu biyu. Ka share sharri, ka goge abin da ya baci. Wallahi matarka irin 'yan Aljanna ce!”
A gefe na, zuciyata na karɓar kalmomin Aliyu da wani sanyi. Duk da shi dan daba ne, yana iya fadar gaskiya cikin dukan irin salon titin da ya saba. Amma Bashari, sai na kasa gane inda zuciyarsa ke karkata.
Na saka ƙeya daga daki ina sauraron su cike da tausayi. Shin kalmomin Aliyu zasu canza tunanin Bashari? Ko kuwa sharri da gulmar Mumy sun riga sun yi zurfi a zuciyarsa?
Na saka kai a ƙeya ina leƙen su daga kofar daki. Zuciyata na bugawa kamar ana harbi da sandar tsinke. Na kasa gane me nake ji tsoro ne? Mamaki? Ko wani sabon abu da har yanzu ban saba jin sa ba?
“Wallahi Oga, idan ka bar wannan yarinyar ta fita daga rayuwarka, sai dai ka rasa nutsuwa har tsawon rayuwarka.” Cewar Aliyu, yana mai kaɗa ƙafafunsa cikin sandar girman kai irin ta 'yan daba.
“Kai ka duba fa! Wata rana zaka dawo daga sararka ko nace shaye shaye ka tarar da dakin ka na ƙamshi, ta dafa maka abinci da tufafi a wanke. Waye ya yi maka haka a rayuwarka? Sai fa Ramlah.”
Bashari ya ƙwanta a kasan gurin, ya ciro sigari daga aljihunsa ya cizge. Ya ɗauko lighter ya kunna, sai ƙamshin hayaƙi ya cika filin gurin “Dama kasan me? Rayuwa tana da rikice-rikice. Amma gaskiya na fara gajiya da wannan sharri. Kullum sai Mumy ta kirani ta zagi yarinyar nan me tatare mata ne.”
Aliyu ya yi dariya yana cewa,
“Haka ake so! Wannan ne Bashari ɗan titi! Kada wani ya juya maka kwakwalwa kamar waina a tukunyar gawayi.”
Ya matso kusa da shi yana daga hannu
“Oga, ka dawo nefa! Wannan shine gangster Bashari na gaske. Wanda idan ya so mace, to sai dai Allah ya ɗauki rayuwarta.”
Na girgiza kai da hawaye a idona. Ina sauraron su, ina jin yadda su ke magana da salo irin na titi da layin masu shaye-shaye, amma duk da haka kalmomin Aliyu sun taɓa zuciyata.
Sai na ji muryar Bashari, a hankali, kamar mai tunani.
“Zan kirata... In ta fito, zan ce mata... Tayi hakuri ko?.”