Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 41
Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 41: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 41. A hankali ya mike daga kan gadon,…
3,269 words
A hankali ya mike daga kan gadon, murmushi a fuskarsa, idanuwansa jajaye kamar wanda ya shafe daren cikin mafarkin da ba su zo da mafita ba. Cikin wata murya mai sanyi da kasala, ya ce,
“Ƴar kwalisa… bazan taɓa takuramiki ba har sai kin amince dani da kanki. Kuma wallahi sigarin da nasha kara ɗaya ne, saboda naji kamar zan sake komawa.”
Ya dafa bango, yana kallona da idon da ke magana da kansa.
“Ke fa kina gudun ɗan shaye-shaye ko? Kina tsoron ace mijinki ɗan daba ne, wanda ba zai iya zama uba ba? Haka ne? Na fahimta. Kowa yana ƙin kazamar rayuwa.”
Yayi dariya mai ciwo, yana ƙoƙarin ɓoye raunin da ke cikin zuciyarsa.
“To amma ki sani... iyayena su ne suka fara kashe ni tun ina ɗan shekara huɗu. Ba wai da wuka ba, da kalmomi ne. Da rashin kulawa. Da barina cikin ruwan sanyi, da barina cikin yunwa da duka da tozarci. Rayuwata ta yi tsami kafin na san daɗin zuma.”
Ya lumshe idonsa, kamar yana ƙoƙarin fitar da wani abu daga zuciyarsa.
“Wallahi ban taɓa kashe rai ba. Amma nayi sara, nayi suka, nayi fada. Na yarda an cuce ki da aka baki ni a matsayin miji. Wallahi basu kyautawa nutsatsiyar yarinya kamar ke ba. Ki gafarce ni... yanzu bari na kwanta a palour. Ki kwanta lafiya.”
Yayi gaba cikin natsuwa, ya fita daga dakin kamar wanda ke gudun kallon tausayi.
Na tsaya ina kallon ƙofar da ya rufe, hawaye suka cika min ido. Me yasa nake jin tausayinsa? Me yasa wani ɓangare na ke cewa zai iya sauyawa? Me yasa naji kamar na taɓa jin zafin da ya ji, ko kuwa ni ce nake mayar da tausayi ya rinjayi hankali?
Na sunkuyar da kai, na runtse idona.
“Allah Ka shige min gaba,” nace a ranta.
Sai na tashi, na gyara gadon da ya zauna akai, na zuba ido zuwa ƙofar da ya fita ta. Ba tare da wani tunani ba, sai na zare hijabi na Nayo alwala, na shimfiɗa zani, na tada sallah.
Ina addu'a da hawaye. Na ce
“Ya Allah... idan har wannan mutumin yana da rabona, Ka shiryar da shi... Ka bani jarumtar jure masa... Idan kuma ba ni ka yi masa ba, to Ka raba mu cikin sauƙi da albarka.”
Ina idar da sallah, na kwanta. Amma zuciyata bata huta ba. Tunanin Bashari ne ya mamaye ni.
Shi kuma... yana kwance a palour, rufe da bargo mai tsufa, yana kallon rufin dakin kamar yana ganin mafita daga cikin lalatacciyar rayuwarsa.
A hankali na mike, na leƙa palour. Na gan shi kwance a ƙasa, ya lullube jikinsa da tsohon bargo. Idonsa a lumshe, numfashinsa ya daidaita kamar wanda ke cikin mafarkin da bai san yadda zai farka ba. Wani abu ya taso a zuciyata… tausayinsa ya cika ni. Wannan ba kawai mijina bane wannan mutumin ne da duniya ta rinjaya, ta zubar da shi kamar ɓargo mai datti.
Na taka a hankali zuwa gare shi. Sai na tsuguna gefensa, na dora hannuna akan kafadarsa cikin sanyi.
“Bashari…” na kirashi da sassanyar murya.
Ya bude idanu a hankali. Idonsa cike da dariya da ƙauna da mamaki.
“ƴar kwalisa...” ya faɗa da murya mai rauni.
“Ina so ka sani… bana ƙin ka. Abin da nake gudu shine abinda kake aikatawa. Shaye-shaye ne ke hana rayuwar ka daidaita. Amma kai Bashari... kana da zuciyar mutum.”
Ya lumshe ido.
“Kin gane ni fiye da kowa. Amma kin sani Ramlah, bana tunanin zan iya tsayawa na canza idan babu wanda ke tare da ni. Ni da kaina ba zan iya ba. Amma idan ke… idan har ke zakiyi min rufa, wataƙila zan iya canzawa.”
Na dafa kafadarsa, na ce da kishi mai sanyi a zuciya
“Zan taimaka maka. Amma ka taimaka wa kanka ma. Ka farka daga wannan baccin rayuwa.”
Yayi shiru yana kallona.
Sai ya kamo hannuna a hankali, kamar zai rasa ni, yace
“Ina jin ki sosai Ramlah. Da farko nayi tunanin kin tsani ni, amma yanzu naga kin fi kowa fahimtata. Wallahi zan canza. Bana so ki zubda hawaye saboda ni.”
Wani irin numfashi ya fito daga zuciyata. Sai kawai naji hawaye sun zubo a idona. Na ce cikin kuka
“Ina fatan Allah zai taimake mu. Domin ban san yadda zamu iya ba tare da shi ba.”
Sai ya tashi zaune, ya kamo hannuna biyu.
“Mu yarda da Allah. Mu tafi tare cikin sabuwar hanya.”
Na gyada masa kai.
******
Cikin kwana biyu sai rigima ta kaure a ƙauye.
Wasu 'yan daba daga kauyen makwabta sun shigo sun buge wani dattijo, wai saboda ya tsallake hanyar su a kasuwa. Gaba ɗaya jama’ar garin suka rude.
Na fito na tsaya bakin ƙofa ina kallon hayaniyar da ke tashi. Sai ga su Aliyu da wasu 'yan daba guda biyu suka nufi gidanmu da masifa. Na ja baya cikin tsoro.
“Bashari... ka bamu shawara jiya! Yanzu fa su suna jin kana tare da mu!”
Na jiyo Aliyu yana ihu.
Bashari ya fito rike da farin riga a hannu yana fadin,
“Dallah ku rufemun baki Ina kokarin gyara rayuwata. Banason tashin hankali yanzu. Ku tafi.”
Sai Aliyu yayi dariya mai ban tsoro, “Kaji Bashari! Wanda muke ɗauka uban yan daba! Kamar yadda muka zaburarka lokacin da babu kowa, to yanzu ba mu buƙatarka.”
Kafin su juya, sai daya daga cikinsu ya buge kofar gidanmu da sanda. Ina tsaye gefe da kwanon shara a hannu, numfashina na karanci, zuciyata na bugawa da karfi.
Bashari ya tsaya cak, yana kallon kofar. Na leƙa gefe na ce masa,
“Dan Allah kada ka yarda su jawo ka baya. Ka tuna da maganar mu. Ka tuna da yadda kake son canzawa...”
Sai ya juya ya kalle ni.
Wallahi kallon da ya yi min a lokacin, ya bayyana cewa zuciyarsa na cikin ruɗani. Amma sai ya dafe kansa da hannaye biyu, ya rufe ido ya furta,
“Allahu Akbar… Ya Allah Ka ba ni ƙarfin zuciya.”
Na matso na riƙe hannunsa cikin sanyi, nace
“Zaka iya, Bashari. Ka tuna da abinda kake faɗa min.”
Sai ya sauke ajiyar zuciya, ya ce
“Ramlah… idan har zan tsira daga wannan hali, Sai na dage, sai na zama wani.”
Bayan kowa ya watse, sai muka zauna a cikin dakinmu. Ya juyo yana kallona.
“Na gode da kika tsaya tare da ni.”
Na girgiza kai nace
“Ni dai ina so ka canza. Ka zama wanda zaka iya tsayawa da kansa.”
Sai ya kama hannuna, yace
“Ni kuma ina so ki zama matar da zata nuna min cewa har mazan da aka watsar da su za su iya komawa mutane.”
Na lumshe ido cikin shiru. Amma zuciyata sai bugawa take da sabuwar ƙauna, sabuwar fatan rayuwa.
Kwana biyu kenan Bashari na yawan zuwa birni. Ranar Laraba da daddare, nayi mana danwake da daddawa sai kawai na ji “Assalamu alaikum” daga ƙofar gida. Ashe Bashari ne. Ada shigowarsa ba sallama, amma yau sai da murya mai nutsuwa ya shigo da sallama, hannunsa ɗauke da ledoji na kayan miya.
Na kalle shi cikin mamaki da murmushi, nace
“Sannu da zuwa Bashari.”
Yayi murmushi, yana cewa,
“Ƴar kwalisa ta... nayi missing dinki wallahi.”
Yayi kamar zai rungume ni, nima na rungume shi a hankali kamar yadda na saba da shi yanzu. Sai yace
“Kinsan yanzu idan zan kwanta, sai nayi wanka. Na saba da tsafta saboda ke.”
Na murmusa nace
“Lallai kayi kyau.”
Sai yayi dariya ya ce
“Na gaji da zama kamar kura. Yanzu na samu mai rarrashi, mai gyara.”
Na karɓi kayan miya daga hannunsa na kai cikin kitchen. Yana zaune yana kallona da murmushi mai taɓa zuciya, har na dawo da abincinsa. Yana ci yana hirar kirki da ni ba irin hirar dan daba ba. Sai naji yana fadin
“Kamin na manta, ga wasu takardu nan.”
Na karɓa na dubasu, takardu biyu ne. Na kalleshi cikin tambaya
“Takardun me ne ne wannan?”
Sai yayi shiru kadan sannan yace
“Lokacin da zan aure ki, mahaifinki ya bani 5 million. Ya ce inyi miki jere ko kuma wani abu da zai amfaneki.
Ni kuma nace tunda ina Sanaa sosai, kuma shagunana biyu ne a birni, da kudin da nake samu da kuma ƙwazon da nake da shi, sai nayi amfani da wannan kudin na saya miki ƙaramar gida a birni.”
Na ɗaga kaina cike da mamaki ina kallonsa, sai yace
“Wannan takardar mallakar gidan ne. Gidan ki ne Ramlah. Ba hayar da za ki biya ba, sai dai ki dinga karbar haya idan kina so. Harkar gidan yana kawo kusan 1 million a shekara.”
Nayi shiru, zuciyata na bugawa, idona na cika da hawaye.
Bansan lokacin da nace masa
“Kana nufin wannan gida nawa ne? Wallahi Bashari ka bani abin da zuciyata bata taɓa tsammani ba. Allah ya saka maka da alheri.”
Ya girgiza kai yana murmushi, ya ce
“Ƴar kwalisa... wannan duk saboda ke. Daga ranar da kika ce min in gyara rayuwata, na fara hangen wani haske a cikin duhu na. Ina jin ki da zuciya.”
Na ɗan sunkuyar da kaina ina jin wani sanyi a jiki. Kalaman Bashari sun fara karade ni da wani irin soyayya da ba daga baki ke zuwa ba, daga can cikin zuciya take fitowa.
Yana kallona yana dariya yace
“Kada kiyi kuka fa. Ki murmushi. Ameen da addu’arki... Allah ya saka.”
Na daga kai na kalleshi da idanu masu sheƙi da hawaye nace masa
“Allah ya saka da alheri. Na gode.”
Ya kai hannu ya share hawayena da yatsansa, yana kallona da wani kallo da ba na daba ba, ba na barkatai ba, amma na mutumin da ke ƙoƙarin zama mafi alheri.
Cikin baccina naji ana kiran sunana cikin sanyi da murya mai rauni, kamar daga zuciya. Na ɗago idanuwana da dan tsoro, zuciyata na bugawa. Idanuna suka sauka a kan Bashari, tsaye yana kallona da idanu masu launin dare danun da suka saba da duhu, amma yau sai suke kamar suna nema su haskaka cikin duhun da ke ransa.
Sai yace cikin murya mai laushi
"Ƴar kwalisa... dan Allah in rungumeki? Wallahi bazan miki komai ba.
Nayi wanka, nayi brush, bansha taba ba... ban sha giya ba. Kawai... runguma nake nema daga gareki.
*****************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA TAMANIN
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Gabadaya hankalina ya tashi. Ban gane ko mafarki nake ba, ko kuwa wani abu mai girma ne ke shirin faruwa. Jiƙinsa yana rawa, idanuwansa kuwa sun canza launi daga irin yadda na saba ganinsu zuwa wani, kalar gaba daya jiƙinsa rawa yakeyi.
Ban iya cewa komai ba. Kawai sai na ji ya rungume ni da ƙarfi, kamar wanda zai fasa ni saboda yadda zuciyarsa ke bugawa. Na ji numfashinsa masu zafi, masu nauyi suna saukowa a wuyana da kafadata, suna tafiya cikin fata ta tamkar wuta. Wani shock ya ratsa ni tun daga kaina har ƙafata. Na kasa motsi. Na kasa magana. Amma zuciyata na harbawa da wani irin yanayi da ban taɓa sanin yana cikina ba. Wani abu ne daban, ban sanshi ba ban taɓa jinsa ba sai yau tsigar Jikina tashiga Amsawa sosai Yanayin da har kwallah sai da naji ta cikamun idanuwa na.
Kafin na gama mamaki, sai na ji bakinsa a fuskata. Sumbatar da ba zan iya kwatanta ta da kowacce ba. Ba sumbatar da za ka iya ce "so kawai" ba a’a, sumbatar da ta shige hanu, ta shige ido, ta shige zuciya. Ta tsaya a tunani kamar ana ƙoƙarin rubuta wani sabon labari a jikina. Sumbatar da ta motsa wani irin kuka daga cikin raina kuka mai nauyin gaskiya da tsoro da soyayya da ƙauna. Sai na fashe da kuka. Kuka mai sauti, mai daci, amma kuma mai natsuwa.
Yayi shiru. Sai na ji ya dakata. Amma yana ta harhada kalmomi da bakin da ke rawar jiki.
“Na bari… na bari… amma ina so, dan Allah.”
Ya faɗa da wata irin murya mai nutsuwa, irin wadda ko a mafarki bai taɓa yi min da ita ba. Muryar da ta gama karya rigar zuciyata.
Na dago kaina na kalleshi. Idanunsa har yanzu suna da wannan yanayin da na gani a da, amma yanzu suna cike da hawaye hawaye da ke zawarci ba da karfi ba. Ya kama hannuna. Hannunsa yana rawa sosai, amma kuma yana da dumi.
“Me kake nufi?” Na tambaya a hankali, kamar wata murya daga cikin ni'imar da ke yawo a jiki na.
Ya kalle ni, sannan ya saki wani irin numfashi. “Na tsaya. Na tsaya saboda ban san ko zan iya dawowa ba idan na ci gaba. Amma bazan iya ɓoye ba ina jin ki fiye da yadda ya kamata. Ba ina son ki ne kawai ba. Ina jin kamar idan ban ce miki ba, zan mutu gaba daya jikina ya saƙe ƴar kwalisa muradinki yakeyi.”
Na rasa me zan ce. Kalmomin sa sun shige kaina, sun shiga zuciyata kamar wani ƙarfi da ke zuga wuta. Na ji kamar ni ma na shiga wani hali. Ba son rai ba. Ba wahala ba. Ba jin daɗi kawai ba. Wani abu daban ne cikakken ɓacewa a cikin wani wanda ya karanta jikin ka fiye da ka karanta kanka.
Ya matsa kusa, yana kallon kaina, kamar yana jiran izini daga wata duniya. Idanunsa sun dawo kamar yadda na saba daidai, masu haske, masu ban tausayi. Yana fadin
“Kiyi min afuwa idan na wuce gona da iri. Amma bana neman gafara ne saboda kuskure, bana neman yafiya saboda jin haushin kai ba bani da haushi, bani da hujja, sai dai gaskiya. Ina so ki sani cewa tun ranar da na fara kallon ki da zuciyata…”
Wani irin sanyi da dumi suka gauraya a kirjina. Na kasa hana hawaye zuba. Kuka na ya dawo, amma wannan karon kuka ne na fahimta. Na fahimci kaina, na fahimce shi.
Ya ɗora kaina a kirjinsa. Numfashin sa har yanzu yana nan sama masa mai nauyi. Amma wannan karon na ji dumin sa kamar garkuwa. Na ji kamar a cikin duminsa akwai amsa ga tambayoyin da na taɓa yi wa kaina ba tare da furta su ba.
Muka zauna haka na wani lokaci, babu wanda ya ce komai. Sai jikinmu ke magana, sai numfashinmu ke musayar zance. Sai zuciyoyinmu ke faɗin kalmomin da bakunanmu suka kasa furtawa.
“Idan kika ce min mu tsaya anan, zan tsaya,” ya ce cikin sanyi. “Amma idan kika ce min mu ci gaba, ba zan taɓa ja da baya ba. Zan tsaya tare da ke har karshe.”
Sai na dafe hannunsa, na ce
“Ka tsaya.”
Bansan lokacin da bacci ya dauke ni ba, amma kafin hakan, sauke ajiyar zuciya kawai nake, ina jin motsinsa a jikina. Numfashinsa mai zafi da nauyi yana bugawa gefen wuyana kamar yana karantar zuciyata ne, yana sauke wani salo da ke tayar min da dukkan tsigar jikina. Sai dai haka bacci ya saceni, cikin nutsuwa, zuciya cike da mamaki da tausayi.
Da safe farkawa nayi a hankali, idanuna sun fara bude ido ne akan shi. Na hangoshi zaune a gefen gado, yana karatun Alkur’ani. Wannan abu ya bani mamaki sosai, har na tashi nayi alwala nayi sallah. Bayan na dawo, na karasa kujerar da yake zaune a kai, nace da shi da fara’a, “Ina kwana?”
Ya juyo da murmushi mai cike da nutsuwa, sai ya sumbaceni kadan sannan yace, “Zan fita yanzu, ƴar kwalisa. Zan tafi birni. Ki rubuto min abubuwan da kike bukata, zan siyo miki inna dawo.”
Na tsaya da mamaki ina kallonsa, sai na dauki takarda da biro na rubuta masa jerin abubuwan da nake so. Na mikamasa, sannan na dafa kafadarsa nace, “Allah ya dawo da kai lafiya.”
Ya juya yana saka takalmansa, sai nace masa da tausasawa, “Yaya Bashari, dan Allah kadaina tafiyar nan ashagiɗe.”
Ya tsaya ya juyo, kallon tausayi ya saukar min da shi, sannan yace da wata murya mai natsuwa, “Sai a hankali ƴar kwalisa. Zan rage, insha Allah. Ki kara hakuri, kinji? Yar albarka .”
Sai ya juya ya fita, yana cewa “Bari naje, yau bana son kwana a can, yau nakeson dawowa.” Na bi bayansa da addu’a, “Allah ya kiyaye hanya.”
Bayan ya fita...
Na dauki tsintsiya, na gyara gidan tsaf. Na dora ruwa, nayi shayi, nasha da ragowar bread din da ya kawo jiya. Ina gamawa wayata ta fara ringing. Maryam ce, na daga da fara’a. Mun sha hira sosai, tana cewa
“Wallahi Ramlah, duk mijin da Allah ya bani yanzu, hannu biyu zan rikeshi. Mazan nan yanzu ba su san darajar aure ba, son lalata kawai suke. Kin ga dama Allah yayi ki da miji kamar Bashari da ke kokarin canzawa ki rikesa da gaske.”
Na yi dariya, na ce mata, “Ai hakane Maryam, komai sai da hakuri.”
Bayan mun gaisa sosai, sai mukayi sallama. Nace bari in kira Mumy ko zata daga. Na sake kira, sai naga blocked. Hatta wayar Abba ba a daga. Wannan abu ya sosa min rai sosai, sai na daure zuciya naceTo ba komai, Allah ya fi komai. Zan ci gaba da hakuri da addu’a. Lokaci zai nuna komai.”
Na ajiye wayar a gefe, na shafa fuska da ruwa, zuciyata cike da tausayi da fatan alheri.
Daga can sai naji an buga ƙyaurena. A firgice na tashi, na nufi ƙofar. Da na buɗe, sai ga Babah ce tsaye da farar hijabinta, tana kallona da wayam.
Nace mata, “Sannu da zuwa Babah,” tana shigowa cikin ɗaki na kawo mata ruwa, muka gaisa da dan sakin fuska, koda kuwa na lura da kallon bincike a idanunta.
Sai tace min, “Ramlatu, naji kwana biyu Bashari bai buge ki ba. Kamar ma baya gidan?.”
Na dan tsaya, zuciyata ta bugawa da ƙarfi. Mamakin tambayarta ya girgiza ni, amma da kyar na danne kuma na ƙirƙiro murmushin karya nace,
“In shaa Allahu Babah, ai yanzu ya shiryu. Wallahi har shaye-shaye ya bari, yana kokarin gyara kansa.”
Sai ta gyara zama tana fadin, “Inji uban wa? Dan shaye-shaye yana daina wa? Shi ne yazo yayi miki karya kin amince? To ai karya yake miki .”
Mamaki ya sake kamani. Baki na na kasa rufewa, na kasa amsawa kai tsaye.
*****************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA TAMANIN DA DAYA
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Ke yarinya ce, ba lallai ki fahimci abinda nake nufi ba yanzu, amma bari na faɗa miki gaskiya, wayagamiki dan shaye-shaye ba abokin amana ne, makaryata ne, ko da ya ce ya daina, kada ki gaskata shi, domin babu wani shiryuwar gaske da suke yi, kalmomin Babah kenan, matar da kullum ke shigowa cikin gidana da sallama da nasiha, tana bani hakuri, tana ce min in dage da addu’a saboda mijina zai sauya, itace yau a zaune take kallona tana furta kalmomin da suka fi kowane zafi a gare ni, ita ce yau take fadar zancen da zai iya fasa min zuciya da hawaye saboda kawai nace mata Bashari yafara shiryuwa Nakasa rike takaicin dake zuciyata nace mata"Babah, wallahi Bashari ya daina shaye-shaye,” daga nan kuma sai zuciyarta ta canza, sai magana ta koma daga fatan alheri zuwa zargi, daga tausayi zuwa gaba, daga kulawa zuwa cin mutunci, kai wannan duniya ba a gane mai kaunar mutum, wallahi tamkar a mafarki nake, ban san yadda zan fassara wannan sauyi daga mutum ɗaya ba, sai kawai na ji wani zafi a zuciyata, kamar ana watsamin garwashi, nayi shiru ina kallonta.