Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 42
Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 42: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 42. Sai ta ce “To banda abunki yarinya, ni ba…
3,349 words
Sai ta ce “To banda abunki yarinya, ni ba ni ce nake gaya miki kullum ki dage da addu’a ba? Na ce maki zai canza ? To me yasa yanzu kike kokarin kare shi? Wannan ai ba addu’a bace, wannan ruɗi ne,” ni kuwa na kasa rike bakina, sai nace mata da damuwa, “Babah, dan Allah ki fahimce ni, me yasa a duk lokacin da aka nuna alamun canji sai a fara masa zargi? Kin fa san yadda Bashari ya ke da halin rashin mutunci, amma yanzu yana ƙoƙari, kin dai sha ganinsa yana zama da Qur’ani yana karatu ko? To me yasa sai kike ganin duk wannan wasa ne?” amma ina, kamar ta ƙi jin kowace kalma tawa, kamar kalmomi na na fita ne daga kunnen da ba ya ji, ta kalle ni da fuska ba yabo ba fallasa tace
“Ni na gaya miki gaskiya, ba zai yiwu ba Habu ya sake shigowa wannan gidan, Na tsorata kar Bashari ya koya masa shaye-shaye. ni bana so habu ya koya halaye marasa kyau daga wajen ɗan daba, ki dinga aikinki da kanki, ki dinga girki da kanki, abinci kuma ai ba zai rasa ba agurina, tun kafin ki zo ni ke basa,” sai naji zuciyata ta karye gaba ɗaya, ba don komai ba, sai domin irin yadda kalamanta suka juyamin komai, matar da ke bani hakuri kullum, tana gaya min in dage da addu’a, yau ita ce ke min kallon wadda ke kare ɗan daba, sai kawai nayi murmushi cike da takaici nace da kwantar da murya
“Ai hakan da kika yi Babah nagode, Allah ya saka da alkhairi, Habu kuwa Allah ya rayashi,” tana kallona da idon da babu wata alamar juyayi sai ta juya da sallama Ta daka tsaki kadan, tace:“To madallah sai anjima”.
Tana barin gidan zuciyata kamar zata fashe, sai naji duniya tayi min kama da wata matsatsiyar ƙasa da nake tsaye a cikinta, na juya na shiga daki ina jin kamar na fashe da kuka, amma sai na runtse idanuwa na, na kalli sama cikin zuciya nace “Ya Allah, kai kadai ka san abin da ke cikin raina, kai ka fi kowa sanin zuciyar wanda ke ƙoƙarin sauyawa, idan da gaske Bashari yana neman gyara, ka ba shi ikon hakan, idan kuma da zambo ya ke, kai kadai ne shari’a, ka hukunta shi bisa gaskiya,” daga nan na sauke numfashi, na zauna ina tunani, me yasa ake jin tsoron canjin mutum? Me yasa mutane basa yarda da sabon shafi? Me yasa ake cigaba da ƙyamar mutum duk da cewa yana neman barin duhu? Zuciyata cike take da tambayoyi, amma babu wanda zai bani amsarsu sai Allah.
Ina cikin zurfin tunani da nauyin zuciya, wayata tayi kara. Numba ce ban sanshi ba, amma saboda yadda zuciyata ke bugawa, sai na daga. Amma kafin na iya cewa komai, naji muryarsa “ƴar kwalisa...”
Na danne wani abu mai nauyi a ƙirjina, nace da sanyi, “Baka yi sallama ba.” Sai naji yace, “Afuwan tawa... ya gidan?” Amma saboda takaicin da nake ciki, musamman kalaman Babah da suka tsaya a zuciyata, sai kawai na kashe wayar kai tsaye.
Ina jefar da wayar gefe, sai wani kuka ya kufce min kamar wanda aka yanka da wuka. Ko shakka babu, kalaman Babah sun fara ratsa zuciyata sun fara barazana ga irin tunanin da nake dashi game da Bashari.
Ina zaune, zuciyata cike da ɓacin rai da ruɗani, na duba wayata ya kirani fiye da sau ashirin. Amma duk da haka, ban ɗaga ba. Ba don bana son jin muryarsa ba, sai dai bana bukatar jin wannan muryar tashi yanzu muryar da take neman rushe ƙoƙarin da zuciyata ke yi don ta fahimta.
Wani irin bakin ciki ne ya taso min tamkar toka a wuyana ya toshe zuciyata ya hana ni numfashi. Bansan sanda na ɗauki mayafi ba, jikina kamar ba nawa ba. Kai tsaye na nufi gidan Uwani, aminiyar Malam Zakari, domin in nemi nutsuwa, ko sauƙin zuciya. Amma a maimakon haka, na tsinci kaina cikin wani sabon rikici.
Na yi sallama ina shigowa, muka gaisa. Tana ta murmushi irin na wayo, can sai ta kalle ni da idon tuhuma tace
“Ƴar birni, me ke haɗaki da munafukar matar gefen gidanku?”
Na zaro ido cike da mamaki, nace, “Wacece? Babah? Kakar Habu?”
Ta gyada kai tana dariyar gulma.
“Eh ita mana. Tsohuwar hegiya ce ai. Ni dama nace wa Malam, wallahi ita ba ‘yar kirki bace. Wai fa tana yawo da ke a kauyen nan, wai kuna saka mata jika a ɗaki kuna kunna masa sigari... Ke kuma kina kallon haka kina murmushi.”
Na ji wani zafi ya ratsa ni, na kasa magana. Jikina ya dau rawa. Nace cikin muryar da ba ta da ƙarfi
“Ban gane ba Uwani… ta baya kuma? Meye hakan?”
Ta kalle ni tana wani sauke numfashi na gulma tace
“Ta baya mana… wato bashari yana bin Habu ta hanyar da bata dace ba.”
Nayi sallati cikin firgita.
“Innalillahi wa inna ilayhi raji’un! Wallahi Karya ma take yi wa Bashari. Wannan wacce irin mummunar zuciya ce haka?”
Uwani ta kara gyara zama tace
“Ai wannan kadan kika gani. Babah fa ba karamar fitina bace. Itace aminiyar matar uban Bashari. Dukkanin auren da yake yi su ke zuga matansa su rabu da shi. Sun kasance silar ɓarnatar da rayuwarsa. Ita kanta shaidaniya.”
Na rasa mai zan ce. Hankalina ya tashi kwarai. Nace a hankali
“Wallahi Bashari ba haka yake b. Kuma tsakanin Habu da Bashari babu komai gaisuwa ce kawai.”
Uwani ta tabe baki cikin raini tace ai haja tace “Ke ma ai karuwace... da haka kika auri ɗan daba. Iyaye naki sun yi miki baki. Ai in ba haka ba, ba za su aura miki shi ba.”
Kamar wuta aka kunna a zuciyata. Idanuna suka cika da hawaye. Cikin jimami da ɓacin rai na mike tsaye, ban ma yi sallama ba na fita cikin zafin zuciya da girgiza kai, kamar wata wacce aka karyar da zuciyarta.
Na dawo gida kafin magariba. Cikin damuwa da faɗuwar gaba, kasa girki nayi. Sai da na dan tattara ƙarfina sannan na dafa shinkafa fara kawai ba domin ina so ba, sai don kada ciki ya ɗaureni.
Bayan nayi sallah, na koma ɗaki. Na zauna ina dannar waya, amma babu isasshen caji da zai ba ni damar kiran kowa. Sai dai kawai na kunna game don in ɗan kwantar da hankali, kodayake tunani ya ƙi barin zuciyata.
*****************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA TAMANIN DA BIYU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Ina zaune a ɗaki, zuciyata cike da nauyi. Tunani na yawo ba tare da natsuwa ba. Cikin wannan shiru sai kawai na ji an tura kofa. Na ji murya yana sallama da cewa, "Assalamu Alaikum."
Ban ce komai ba. Sai na ji yana kirana, "Ƴar kwalisa… Ƴar kwalisa kina ina? Ina kika shiga? Fito mana."
Na ƙi magana. Raina ya ɓaci, na kasa ma kallonsa. Na ji ya ajiye kayan da ya shigo da su, sannan ya shigo cikin ɗakin ya tsaya yana kallona. Ya ce da mamaki, "Lafiya? Ina ta sallama baki amsa ba?"
Na ce da ƙasa da murya, "Ban ji ba ne shiyasa."
Bai sake cewa komai ba. Sai ya cire rigarsa, ya ɗauki tawul ya shiga bandaki. Bayan lokaci kaɗan ya fito, ya fesa turare ba irin wanda na sani ba. Ya tada sallah, ya yi cikin natsuwa, har ya gama. Ni kuma ko motsi ban yi ba, ina zaune kamar gunki.
Ya fita daga dakin. Bai dade da fita ba, sai ya dawo. Na ji yana waya yana cewa, "Aliyu ku bar su. Nifa yanzu na bar dabi'ar nan. Abin da na yi a baya Allah ya gafartamun. Ka daina binsu danAllah."
Sai ya yi tsaki ya kashe wayar.
Ya kalle ni da ido mai rauni. Ya zauna ya ce
"Ƴar kwalisa… laifin me nayi? Ki yafe min. Halina ba nan take ake gyara ba. Zaki ga zan gyaru. Na dade cikin munanan halaye. Ki cigaba da taimaka min dan Allah."
Nan da nan hawaye suka gangaro daga idona. Ba haushinsa nake ji ba, haushin maganganun da Babah ta fada ne.
Na ji ya zo ya rungume ni. Yana bani hakuri.
Sai ya tambaye ni, "Me ke faruwa? Wani ya taɓa ki ne?"
Ya ce da murya mai ƙarfi, "Magana nake miki!" Fuskar sa ta nuna fushi. Jikina ya fara rawa. Na ce da shi cikin kuka:
"Babah ce. Ga abinda ta fada…"
Bai bari na karasa ba, ya fizgeni daga jikinsa, ya miƙe cikin fushi. Na miƙe shima cikin hanzari nace, "To kenan baka sauya halinka ba kenan? Ita fa tace bazaka taba canzawa ba!"
Ya shiga ɗaki yana neman wani abu. Na biyo shi da kuka, na rungume shi daga bayansa. Na ce
"DanAllah kayi hakuri. Ka saurare ni."
Ya tsaya, ya dafe hannuna yana sauke numfashi. Ya ce
"Me nayi wa Babah da zata min haka? Wallahi ban ƙara shan komai ba. Wannan makon ma na ware kaina daga abokai. Addu'a nake yi. Ina roƙon Allah ya kare ki dani. Amma ki barni na ɗauki mataki a kanta."
Na shafa fuskarsa nace, "Kayi hakuri. Koma me tayi, kanta tayi wa. Allah yana gani. Allah yana kallon komai."
A hankali jikinsa ya lafa. Ya kalleni cikin ido. Sai ya ce da murya mai sanyi
"Bani abinci."
Na ce, "Da me nayi?"
Sai ya ce da dan murmushi, "Na siyo kaza da kayan marmari. A waje kayan suke. Ki dakko mana." Na ce masa, “To.” Sannan na mike na fita daga ɗakin. A hankali na tafi na ɗauko abincin da ya ajiye kazar da kayan marmari da ya siyo. Na dawo na aje a gabansa.
Yayi murmushi yana ce min, “Matso kusa dani ki zauna.”
Na zauna a hankali a gefensa, zuciyata tana bugawa da raɗaɗin ƙaunar da ke ƙara samuwa tsakaninmu. Yana cin kazar cikin natsuwa, sai ya ɗago ya kalle ni da ido cike da tsantsar buƙatar kulawa.
“Ƴar kwalisa, danAllah ki dinga dan nunamin kulawa… kinji?” ya faɗa cikin muryar da ba za ta gaza motsa zuciya ba.
Na ɗan saki murmushi, nace masa, “To.”
Sai ya ɗebo abinci da cokali, ya ce, “Bude bakinki.”
“To kinji,” na ce ina dariya kadan, na ɗan rufe fuska da tafin hannuna, kamar wata yarinya mai jin kunya.
“Kitaimaka mana,” ya faɗa yana kallona da idanunsa masu dumi. “Wallahi, idan na ga murmushin nan a fuskarki, wani irin dadi nake ji a zuciyata… Ƴar kwalisa.”
Haka ya cigaba da bani abincin. Shi kuwa bai ci ba. Idonsa yana kaina, hannunsa yana ciyar da ni. Sai da na fara jin nauyin bacci.
Na yi wata hamma mai nauyi, sai ya ce, “To fa, sai munyi brush ko?”
Na ce da dariya mai rauni, “To… Amma kai fa baka ci abincin ba.”
Yayi murmushi yana kallona, “Kallonki da nayi da yadda kike ci… wallahi hakan ya isheni. Na koshi da kallonki kawai. Allah ya baki albarka matata. Allah ya baki Aljanna. Kuma ya saka ki fara sona da zuciya ɗaya.”
Na lumshe idanu cikin jin daɗin kalamansa. Na saki murmushi, na gyara wurin da nake zaune, sannan nace masa, “Sai da safe.”
Na tashi na nufi ɗaki cikin nutsuwa. Na shiga na kwanta a kan gado, cikin shiru. Shi kuma ya cigaba da zama a kan kujera, inda yake kwana kullum.
A cikin duhun ɗakin, sai kalamansa ke yawo a kunne na kamar ana karanta su kai tsaye cikin zuciyata. Na juya a gefen gado, na lumshe idanu da murmushi, zuciyata cike da sabuwar fatan soyayya.
Ko minti goma banyi da kwanciya ba, bacci ya fara mamaye jikina. Idona ya lumshe, zuciyata na sauke numfashi cikin shiru. Cikin wannan natsuwa, sai na ji muryarsa a hankali yana cewa:
“Ƴar kwalisa... danAllah... na kwana a gadon yau?”
Na buɗe idona a hankali. Bansan me zan ce ba. Na rasa ko mafarki nake yi ne, domin wannan ba irin Bashari bane da na saba gani. Muryarsa cike da ladabi da nutsuwa.
Na daga masa kai a hankali. A gaskiya... nima jiya na ji daɗin kwanciya a jikinsa. Daɗin da ya sha bamban da komai da na taɓa ji. Mafarkai na na mugaye da ke yawan addabar zuciyata har dare, duk basu zo ba. Wata nutsuwa ce ta sauka.
Yana kallona da idanunsa masu taushi, ya ƙarasa ya kwanta a gefe. Sai ya ce cikin rauni, “Zan iya rungumeki? Babu abinda zan miki… Wallahi.”
Baki na ya buɗu kamar zan ce wani abu, amma kalmomi sun makale a maƙogwaro. Idona ya faɗa cikin nasa, sai kawai na juya a hankali.
Yana ƙarasowa kusa dani, ya sa hannunsa ya ja ni a hankali zuwa jikinsa. Zuciyata ta fara dukan kamar ana bugunta da ƙwanƙwasa. Amma ba saboda tsoro ba saboda wani sabon yanayi da ban saba ba.
Ya janyo ni gaba ɗaya cikin jikinsa. Numfashinsa na bugun bayan wuyana. Hannunsa ya zauna a kafadata, yana shafewa a hankali. Wata sanyi mai dumi ya lullube jikina gaba ɗaya.
Amma sai na ji… hannunsa ya gangara. Ya sauka a kirjina. A nan ne na ji wani mugun shock ya kama jikina. Na kasa motsi. Idona na lumshe da ƙarfi. Kwakwalwata kamar za ta tashi sama, zuciyata na harbawa da karfi.
Bansan me ke faruwa da jikina ba. Amma na san wannan ba tsoro bane. Wannan wani yanayi ne mai cike da daɗi... da jin daɗin kasancewa kusa da wanda kake so, koda ba ka furta hakan ba.
“Na ƙosa ki fara sona,” ya faɗa da wata murya mai raɗa.
Ban ce komai ba. Amma numfashina ya nuna masa komai. Hannunsa ya ɗan matsa ya kama hannuna. Sai ya riƙe shi a kirjinsa. “Kiji yadda zuciyata ke bugawa saboda ke.”
Na lumshe idona da hawaye masu ɗumi. Kamar wata damuwa ce ta narkewa cikin zafin kulawarsa.
Sai ya ce, “Zan iya kwana da ke haka... babu wani abu... sai numfashinmu kawai?”
Na gyada kai. Ya matse ni a jikinsa. Na ji kamar wannan gabar jikinsa ce mafakata. A can ne nake so in kwana… kuma in tashi.
Washegari da safe ban farka da wuri ba. Sallar asubah ta shude kamar iska. Idanuwana sun kasa buɗewa, zuciyata cike da dumin daren jiya. Sai da safe sosai har kusan goma na farka da cikakken numfashi mai nauyi. Na mirgina daga gefen gado cikin natsuwa, na ɗan shafa filon da har yanzu yana ɗauke da kamshin jikinsa. Wani sanyi ya ziyarci zuciyata.
Na miƙe da gajiya, amma cikin nishaɗi. Na kalli dakin, sai naga tsaf. Gidan duk an gyara, carpet ya sha tsinke, kitchen tsaf kamar ana jiran baki. Wanke-wanke babu ko leda guda, komai daidai. Ashe Bashari ya gyara gida kafin ya fita...
Ina cikin shan shayi a ƙanƙanin cup, sai Uwani ta shigo kamar wadda aka biyo da labari.
“Ke dai kin kwana lafiya Ramlah,” ta faɗa tana kallona da murmushi mai cike da sirri. “Kin san me ya faru kuwa?”
Na kalleta da kallon tambaya, amma ban ce komai ba. Na ɗauko mata cup na zuba mata shayi. Tana karɓa, tana cewa
“Rigima babba ta kaure yau da safe. Ke kin san filin da ke bayan gidan su Bashari? Ashe wai uban Bashari da shi suke rikici. Bashari ya fita waje da makami fa! Dakyar aka raba su.”
Na ɗan juya kai, zuciyata ta fara bugawa. “Makami?” na maimaita a hankali.
“Eh mana,” Uwani ta ce tana gyara zama. “Wallahi matar uban Bashari ke zuga shi. Ke dai ki tsaya Allah ne yasan abinda ke tsakanin su.”
Na saki wani sassanyan ajiyar zuciya. Ban ce komai ba. Na ci gaba da shan shayina a hankali, na zuba mata nata cup. Ta sha, ta mike ta tafi.
Na san halinta ba zata taɓa tafiya ba indai ba labarin Bashari na bata ba. Wannan karon dai sai ta hakura.
Bayan ta fita, sai na ga wayar Bashari a gefe kusa da gado. Na ɗauka da murna kamar na ɗauki wata kyauta. Cikin nutsuwa na duba contact list. Na saka number Abba a ciki, zuciyata cike da burin jin muryar wanda ke da daraja a idonsa.
Sai da ya kusa kira na hudu kafin aka ɗaga. Muryata na ɗan rawa, nace, “Abba, ina kwana? Ramlah ce.”
Na ji dariyarsa a gefe, mai dumi. “Auta! Yanzu saboda Allah ke bazaki kirani ba ki gaidani?”
Na saki murmushi cikin jin kunya. “in nakira bana samunka shiyasa…”
“Lafiya ko? Badai wani abu ba?” ya tambaya cikin damuwa. “Yayanki Usman yazo nan, muna nemanku, ba a samu ba. Ashe Bashari ya sauya wayar.”
Na ce, “Lafiya lau. Ina Yaya Abbas? Ina Billy? Ina mummy? agaidasu”
“Zasu ji. Ramlatu, ki rike mijinki da kyau. Ki yi masa biyayya. Wallahi bana so wani abu ya raba ku, sai dai mutuwa.”
Sai na lumshe ido. Wani zafi ya ratsa zuciyata kalaman da suka nuna amincewa da Bashari fiye da yadda mutane suka saba dubansa. Shi da mutane ke ganin dan daba ne, dan maye... Abba na masa kallon cikakken namiji.
“Zan yi iya kokari na, Abba,” na ce a hankali, hawaye yana makale a gefen idona.
“Allah ya baku zaman lafiya,” ya faɗa kafin muka ajiye wayar.
Bayan ‘yan mintuna, na ji ƙofa ta buɗe. Bashari ya dawo. Amma da zarar ya shigo, sai na fahimci cewa ba shi da walwala. Fuskar sa a murtuke, kamar wanda aka takura masa da duniya gaba ɗaya.
Bai ce komai ba. Bai kalle ni ba. Ya cire rigarsa ya shiga bandaki. Bayan ya fito da jiki mai danshi, sai ya zauna a kujerar daki, yana fesa turare kamar wanda ba ya cikin hayyacinsa.
Bansan me ke damunsa ba. Amma na san… akwai abu mai nauyi da ke cin zuciyarsa. Ko sannu da dawowa bai amsamun ba
Na zauna a gefe ina kallonsa, zuciyata cike da tausayi. Wane irin ciwon zuciya ne haka ke yawo da shi? Ina so in tambaya. Ina so in matsa kusa. Amma shiru nayi.
Kalaman Abba suka dawo mini a kunne “Ramlatu, ayiwa miji biyayya dai. Ayita hakuri.”
Sai na lumshe ido na ce a zuciyata Zan yi. Amma ya kamata shima
*****************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA TAMANIN DA UKU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Cikin wani shahararren wurin shakatawa mai suna Shangri-La Rooftop Lounge, dake tsakiyar birnin Paris, wanda ke ɗauke da kyakkyawan daki mai kallon Eiffel Tower, Ayshatu ke zaune cikin rangwamen soyayya da wani mutum mai muhimmin matsayi da kowa ke jin tsoronsa Alhaji Muqaddam.
Ayshatu ta sa wata Versace short dress fara, da ba ta rufe gwiwarta ba. Gaban kirjinta a bude, sai glass da mask masu Fendi design suka kammala kyawun fuskar da ta zubo gashinta a baya.
Alhaji Muqaddam, sanye da Gucci shirt budaddiya da short wando mai sauƙin launi, yana sanye da Rolex Oyster Perpetual Platinum a hannunsa, ya kafe ta da wani irin kallo da ke narke zuciya.
"Kwana biyu da bakizo ba din nan, naji kamar nayi madness, Ayshatu," ya faɗa da murya mai sanyi, yana tsunduma cikin idonta. "I love you so much wallahi..."
Ayshatu ta sauke murmushi mai cike da nishaɗi. "Ka sani dai cewa bani da ikon boyewa. Yanzu ma na lallabashi ne, yana can wajen Prince babansa, zai ɗauki lokaci kafin ya dawo. I'm missing your touch nima yanzu idan ya taɓani, ban jin wani abu…"
Alhaji Muqaddam ya bushe da dariya, yana rungumarta da damƙa, ya ce
“Wannan ai ba sabon labari bane. Ragon namiji ne shi, kullum sai rigimar maganin ƙarfi yake. Kuma... wallahi idan kin ce ‘I love you’ gareshi , inajin kamar ana tsaga min zuciya da reza saboda bana son wani yayi miki kusanci ko magana babu yadda zanyi da as'ad.”
Ayshatu ta zaro ido, tayi masa tsaki. "Wallahi na gaji dashi but bazan taba iya rabuwa dashi ba …"