Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 44
Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 44: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 44. Nan take aka kawo masa fruit goran ayaba,…
3,366 words
Nan take aka kawo masa fruit goran ayaba, apple, da watermelon cikin kwanon azurfa. Ya ɗan ɗauki apple ɗaya, yana yanka a hankali da wuƙa, ba tare da magana ba har sai da Hajja ta soma “As’ad, yau da wuri kake? Na zata aikin gwamnatin ka ta shanye ka kamar kullum.”
Yayi murmushi kaɗan, yana ɗan goge gefen baki da tissue “Na tafi da wuri ne domin na zo mu tattauna kadan akan shirin rabon hannayen jari na sabon kamfanin da zamu bude.” Hajja ta gyara zama. “Wannan kamfanin sabo kenan, ko?” “Eh Hajja,” ya ce cikin natsuwa, yana kai apple bakinsa. “Kamfanin zai mayar da hankali kan kayan masarufi da kaya daga ƙasashen waje. Mun samo masarrafan da zasu rage mana wahala da dogaro da import. Muna kokarin kafa masana’anta a cikin gida.”
Hajja ta ɗaga kai, cike da sha’awa “To Allah ya yarda yasa albarka. Amma kayi hattara, kasuwa yanzu bata da sauƙi. Mafi yawa ‘yan kasuwa suna fakewa da kamfanoni ne suna wasa da kudin gwamnati ko bashin al’umma.”
As’ad ya gyara zama, yana fuskantar Hajja da girmamawa“Mun dauko manyan consultants daga Singapore da UK. An tsara tsarin biyan albashi da kula da ma’aikata sosai. Kuma a wannan karon, muna bude rabon shares ga manyan ‘yan kasuwa a nan domin su ma su mallaki kaso a ciki.”
Firdausi ta dago kai a hankali kamar wacce zata ce wani abu, amma tana jin idanunsa na kallonta, sai ta koma gefe. Tayi shiru, tana juyawa a cikin ranta kamar komai yana tafiya cikin natsuwa ne amma zuciyarta tana ƙona saboda tsanar ayshatu dake cikin zuciyarta har yanzu.
Hajja ta gyada kai, tace da jin daɗi “Wannan kyakkyawan tsari ne. Amma kada ka manta... kudi da iko sukan jawo wa mutum abokan gaba. Ka kiyaye marasa kishi, da makiyan nasara.”
As’ad ya kalli mahaifiyarsa da kwarjini, yace “Na dauki dukkan matakan tsaro. Kuma na hada da ƙananan hannun jari domin matasa su ma su samu dama. Insha Allah wannan zai taimaka wajen rage zaman banza da rashin aikin yi.”
Hajja ta yi murmushi cike da alfahari. Firdausi kuwa ta lumshe idanu tana zubda huci a hankali. Ta san cewa da wannan irin cigaban da As’ad yake yi shiyasa duk ƴan uwansa basa kaunarsa ko kadan.
Motoci biyu suka tsaya a harabar fadan Range Rover SV da Mercedes Maybach. Kafin kowa ya farga, sai ga Aminatu, babbar 'yar As’ad, ta fito daga motar. Cikin kayan modest fashion na Dubai, tana sanye da abaya na Elie Saab da hijab mai launin zinariya, hannunta ɗauke da ledoji na Versace da Prada.
A bayanta sai Nawal, yarinya kyakkyawa, siririya da kamala, tana sanye da doguwar riga daga Chanel, glass na Gucci, da jaka mai tambarin Hermès. Ta fito daga motar a nutse, amma idanunta suna nemowa tana neman mahaifinta da zuciya.
“DADDY!!” suka faɗa duka a lokaci guda.
As’ad ya ajiye iPad ɗinsa, ya miƙe da annuri yana rungumar su duka. “Welcome home, my angels,” ya faɗa yana murmusawa.
“We missed you, Daddy!” Nawal ta ce, tana langwaɓar da kanta akan ƙirjinsa.
Aminatu ta ce da dariya: “Dubai was amazing... but there’s no place like home.”
Daga nan suka wuce wajen Hajja, suka rusuna da girmamawa.
“Grandmaaaa!” suka faɗa a tare suna rungumar ta.
Hajja ta ɗaga hannu tana samusu albarka “Allah ya dawo daku lafiya. Naji daɗin ganin ku sosai.”
“Where’s Anty fiddau?” Nawal ta tambaya, tana lumshe idanu.
Firdausi ta fito daga ɗaki, tana sanye da shigar gida. Nawal ta rungumeta da murmushi. “Nice to see you, aunty Firdausi.”
“Yauwa baby. Kinyi kyau sosai.”
Ma’aikata suka fara shigo da abinci jollof rice, seafood pasta, lamb chops, cakes na alfarma, fresh juice, da ice cream. Kowa ya zauna yana ci da raha.
Amma sai Nawal tayi shiru, ba ta ɗauki spoon ba. Idanunta suka cika da hawaye, sannan ta ce a hankali:
“Daddy…” As’ad ya kalleta da damuwa. “Yes, love?”
Ta ɗago idanunta cike da kuka. “Maamah… … she doesn’t call me. She never checks on me. Even when I was sick, she didn’t know.”
Zuciyar As’ad ta tsinke. Ya miƙa hannu ya janyo ta ya rungume. “Sweetheart… I’m so sorry. I promise I’ll talk to her. She loves you. Maybe she’s just... caught up with life.” “But I don’t want her money. I want her.” Sai ta fashe da kuka sosai.
Aminatu ta dafa kafaɗarta “We love you, sis. You’re not alone.” Firdausi ma ta ce “Ayshatu is missing out on a gem. But you’re home now. And we will make you happy.”
As’ad ya kalli duka ’ya’yansa yana shafar kai, zuciyarsa na kuka a ciki. Yana rantsuwa a ransa cewa zai gyara komai idan har har yanzu akwai mafita tsakanin yaransa da mahaifiyarsu.
Wannan abin yana damunsa sosai.
Ita ce ta haifi yaran, amma yanzu ko a jikinta ba su ke ba. Ko kiran waya ba ta yi musu. Ko tambayarsu halin da suke ciki babu. Duk wata alaka da mahaifiya ta dace ta kasance da ‘ya’yanta, bata nuna komai ba.
As’ad ya rasa yadda zai yi da wannan hali nata.
Ya dafe kansa yana kallon Aminatu da Nawal da ƙauna.
“Allah ne kadai ya bani ‘ya’ya nagari,” ya faɗa a zuciyarsa.
“Ni ne uba kuma ni nake maye gurbin uwa.”
Yaran suna girma cikin soyayyarsa da kulawarsa.
Tun Aminatu tana ƙuruciya ya kula da ita da kyau har ya aurar da ita a cikin girmamawa.
Yanzu kuma ga Nawal, itama yana shirye-shiryen aurar da ita da hannunsa cikin martaba da daraja.
Yana kallon yadda Ayshatu ta kau da kai gaba ɗaya, zuciyarsa na masa zafi. Ita ce ta haife su, amma shi ne ya rungume su kamar shi ne ya haife su.
"Ya za a ce uwarsu bata damu da su kwata-kwata?"
*****************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA TAMANIN DA SHIDA
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Kukan uban me kikeyi tun dazu?" Gimbiya Maryam ta fado cikin ɗakin Haneefah, tana turo ƙofar da ƙarfi, fuskar ta cike da fushi, muryarta na dukan bango da ƙasa.
Haneefah, dake kwance kan gado tana kuka, ta dago idanunta da suka kumbura. Murya na rawa tace,
"Mama dan Allah in roƙe ki alfarma, dan Allah Mama kar ki ce a'a. Wallahi ina son mijina. Ban san yadda akayi na rabu da Yaya As’ad ba. Mama, gaba ɗaya kaina baya gane komai. Idan na kwanta mafarkinsa nake yi, idan na farka shi nake gani. Ni ina sonsa... ko da gaban nasa baya aiki."
Gimbiya Maryam ta nisa da karfi, ta tunkare ta da tsananin ɓacin rai. Ta jawo wuyanta cikin huci.
"Ke ba ki da hankali Haneefah? Makiyin nawa kike so? Daman ba na gaya miki ba? Na haɗa miki wannan aure ne da wata manufa, domin darajar gidanmu. Kuma yanzu na kashe auren! Me za ki yi da nakasasshen namiji da ba zai amfane ki da komai ba?"
Haneefah ta fashe da kuka, muryarta ta shake.
"Mama dan Allah ki saurare ni. Wallahi Allah ina kaunar sa. Gaba ɗaya hankalina ya tashi akansa. Mama, nasan ke zaki iya mallaka min shi. Dan Allah ki taimaka..."
A take, Gimbiya Maryam ta daga hannu ta kifa mata mari mai ƙarfi da karar da ta amsa.
"Dan ubanki! Na ƙara jin wannan sunan daga bakinki wallahi sai na salwantaki! Mahaukaciya wacce ba ta san inda ciwon ta yake ba! Kin ce da gaban nasa baya aiki, amma har yanzu kina binsa kamar wauta. Wacce 'yar hajja ce? Kalla yanzu zai buɗe mata wani kamfani! To wallahi, Allah ke da As’ad har ki mutu! Ballagaza kawai!"
Ta juyo da murya mai cike da ƙyama da raini, sannan ta bar ɗakin tana bubbuga ƙafafu. Haneefah ta bita da idanuwanta da suka ɓaci da hawaye, zuciyarta kamar zata fashe da ciwo. Ta fadi a ƙasa tana kuka kamar ƙaramar yarinya, tana faɗin
"Wallahi ina sonsa... wallahi As’ad…”
Dakin ya sake yin shiru bayan fushin Gimbiya Maryam ya fice. Haneefah na kwance a ƙasa, ta baje cikin kuka da hawaye, zuciyarta tana fuskantar tashin hankali da raɗaɗi. Dukan kalmomin da mahaifiyarta ta faɗa suna mata kara a zuciya “nakashasshe”, “zuriyar hajja”, “ballagaza”.
Sai ta dafe ƙirjinta tana ambaton sunansa a hankali
"As’ad... wallahi kai ka mallake ni. Kuma ban san me ya shiga tsakanina da ke ba. Amma zuciyata ba zata iya manta da kai ba.”
***
Zafin jikinsa kamar ana ƙonawa da wuta. Kwana biyu kenan, As’ad ba ya iya komai da kyau zazzabi ya rike shi gaba ɗaya, jikin sa kamar yana bijirewa. Ko motsi yayi, sai yaji kamar ana murɗe ƙashin sa. Ya zauna akan kujera, yana dafe goshinsa da gumi mai yawa.
A gefe, Hajja ta zuba masa ido cike da tausayi da lura.Tace
“As’ad... ko zakaje ka huta ne a can waje ko a dakinka na private? Jikinka fa bana gane shi.”
Ya kalleta cikin kasala, muryarsa a raunane.
“Hajja... jikina babu dadi kwana biyu. Ina jin kamar wani nauyi ne yana damuna a zuciya...”
Hajja ta zauna a gefe, ta ɗauko tasbihinta tana jujjuya yatsunta.
“To sai ka dage da azkar As’ad. Ina fatan dai kana yinsu kullum?”
Sai yayi shiru yana lumshe ido, baice komai ba sai ya ɗaga kansa da alamun eh. Amma ba shakka yana ramewa.
Azkar suna taimakawa wajen kwantar da zuciya, samun kariya daga sharrin aljanu da mutane, kuma suna ɗaukaka darajar mutum wajen Allah. Azkar suna kawo nutsuwa a ran mutum da kwanciyar hankali, suna hana mugun abu shiga rayuwa, sannan suna sanya haske a fuska da zuciya.
Can daga sama, Nawal ce ta sakko daga bene cikin gudu. Riga ce ta designers body fit tana sanye da hular da tazo da ita, tana tafe da ƙamshi mai daɗin gaske. Tana sauka, tace da turanci cikin wata muryar baby girl masu wayewa
“Dady... Dady... Kaga na kira Mamaah fa. It’s been ringing but she’s not picking up. Is she okay?”
As’ad ya buɗe idanunsa kadan, ya kallota, yayi murmushin ƙarya.
“Sorry baby... Babu komai. Kije ki kwanta yanzu. Gobe zan kirata sai ku yi waya kinji?”
Tayi ƙasa da kai.
“Okay dady…” ta faɗa da karamin murya sannan ta juya ta fita cikin nutsuwa.
As’ad ya lumshe idonsa. Zuciyarsa na tafarfasa. “Ayshatu... har yara na na damuwa dake, amma ke... baki ma damu da su ba.”
Yaji wani zafi ya ratsa zuciyarsa. Wannan ba cutar jiki kadai bace.
Hajja ta kallesa tana murza tasbihinta. Ta dan matso kusa, ta dafa kafadarsa a hankali cikin salo irin na manya masu hikima.
"As’ad," ta fara cikin natsuwa, "kai mai kudi ne, kana da iko, kana da daraja. Amma ka sani, duniya ba da dukiya kawai take juyawa ba wallahi akwai wasu abubuwan da su suka fi duk zinariya.
Ka san menene? Lafiya, natsuwa, da kariya daga makiya."
As’ad ya lumshe ido, yana sauraren kalamanta kamar karatu a zuciya.
"Kowa yana son samun arziki kamar naka," Hajja ta ci gaba, "amma ba kowa ke ganin abinda ke faruwa a bayan fage ba. Wannan zazzabi da rashin jin daɗi da kake fama da shi yanzu, ba lallai ne cutar jiki ba wata rana ana iya zama ana kallonka da hasada.
Wasu na iya yin kallo guda su shuka sharri. Amma akwai sirrin kariya guda ɗaya: Shifa, azkar, da karatun Al-Qur’ani da niyyar tsari."
Ta nisa, sannan ta kalleshi da idanu masu gaskiya.
"As’ad, kana buƙatar shifa. Karatun Ruqya. Ka dage da addu’o’in asuba da yamma. Ka rika karanta Ayatul Kursiyyu bayan kowacce sallah. Ka daure da istighfar a rana fiye da sau 100. Wallahi, za ka sha mamakin sauyin da zaka ji. Sai a gobe ma kace min kina jin kamar an ɗauke maka kaya daga kafada."
As’ad ya buɗe idanunsa a hankali.
"Hajja, ina saurarenki. Kuma ina ganin gaskiya a cikin zancinki. Amma me yasa yanzu?"
Ta dan murmushi, tace
"Domin ka isa. Kuma makiyanka suna kallonka fiye da yadda abokanka ke maka fatan alheri. Ka tuna lokacin da wani ɗan sarauta daga jihar Bauchi ya fadi kasuwanci? Me yasa? Saboda ya manta da addu'a. Saboda ya bar shifa.
Amma kana da lokaci. Ka koma ga Allah, ka dage. Kuma ka rike magidanta na gaskiya wallahi As’ad, dukiyar ka zata ninka. Zuciyar ka zata huce. Kuma abinda ka rasa zai dawo maka da karimci fiye da duka duniya."
As’ad ya zuba mata ido, ya dafe zuciyarsa.
"Hajja... wannan ba shawara bace, wannan ceto ne. Na fahimta. Na yarda. Kuma daga yau, ba zan ƙara barin kaina haka ba.”
Bayan As’ad ya yiwa Hajja sallama da “sai da safe”, ya fice daga shashenta cikin nutsuwa. A hankali, shashenta ya koma shiru, sai ƙamshin turaren humra da ƙarar tasbihi na tashi a gefe.
Amma shiru bai daɗe ba...
“Wallahi Hajja, wannan Ayshatu dai... ai kina ganin halinta, ko?” Cewar Firdausi, tana matsowa kusa da Hajja, ta kafe ta da idon tambaya da na gulma.
Hajja ta kalleta a hankali. Bataso maganar, amma Firdausi bata barin mutane da shiru.
“Firdausi,” ta ce cikin kasala da ɗan gajiya, “karma ki karasa.”
Firdausi ta ɗan lumshe ido kamar tana sauke numfashi, sai kuma tace:
“Au... Gwaleni kikayi kenan Hajja? To shikenan, nayi shiru.” Sai ta juya da kafada kamar mai jan rigima cikin fara’a.
Hajja ta rufe tasbihinta, ta ajiye a gefe, ta gyara zaman ta.
“Ki saurareni Firdausi. Karki zamo mai sa ido akan abinda ba bai dameki ba. Idan har kinason zaman lafiya da kowa, gulma da sa’ido ki rage. Kuma ki tuna, gulmar da ke farawa da niyyar magana, kan ƙare da laifi.”
Firdausi ta dafe kirjinta cikin girmamawa.
“To Hajja, ai ba wani gulma bane fa”
“Shiru,” Hajja ta dakatar da ita cikin nutsuwa. “Ki shiga daki ki kwanta, kafin na ɓatamiki rai.”
Firdausi ta sunkuyar da kai kamar wata yarinya da aka faɗawa magana.
“Good night Hajja,” ta ce da lallausan murya, tana juyawa zuwa dakinta kamar wata yar bulala.
As’ad ya shiga cikin ɗakinsa na musamman da ke cike da ƙamshi mai nutsuwa da ƙawata na musamman daga Turkiyya da Morocco. Wannan ɗaki haɗadde, an tanade shi don hutu da shakatawa. Amma yau, ya canza. Yau ɗakin ya zama masallaci na sirri wuri na natsuwa da komawa ga Allah.
Ya shimfiɗa alwala cikin nutsuwa. Ya ɗauki Al-Qur’ani, ya buɗe suratul Baqarah ya fara karantawa a hankali. Muryarsa mai nutsuwa tana karanta ayoyi cikin ladabi. Idanunsa suna rufe, zuciyarsa tana tafiya da kowanne aya da fassarar sa. Ya maimaita Ayatul Kursiyyu sau da dama.
“Lā ikrāha fī ad-dīn…” ya karanta da zuciya mai nauyi.
Can wani lokaci, ya kalli ƙasa. Ya jinjina kansa
“Na bari duniya ta shagaltar da ni, na manta da wanda ya bani duniya. Amma yanzu… zan dawo.”
Zuciyarsa ta fara samun natsuwa kamar ruwan sanyi yana bi masa ƙirji. Zazzabin da yake fama da shi, sai ya fara raguwa kamar ruwa yana fita daga jikinsa.
Ya yi murmushi. Ya ɗaga wayarsa, ya kira Firdausi. Ita ke kula da harkokin sarauta da tsare-tsare yanzu.
“Firdausi,” ya ce cikin natsuwa, “Ina son a shirya ganawa ta musamman da sarakunan kasuwanci da masu ruwa da tsaki na cikin gida. Ina son mu haɗu domin kafa wani babban gidauniyar taimakon yara marasa gata.”
Firdausi tayi shiru, sannan tace da murmushi
“Wannan babban ra’ayi ne yaya As’ad. Allah ya saka da alheri.”
Daga nan sai ya aika da saƙo zuwa Aminatu da Nawal yana son su kasance da shi gobe wajen buɗe kamfani da ɗaukar nauyin yara 500 cikin gidauniyar.
*****************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA TAMANIN DA BAKWAI
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
A cikin kwanaki biyu da suka gabata, zazzabi ya rufe ni tamkar wuta. Sai gumi sai ciwon da har ƙashi na ke ji kamar ana murɗa su da sandan ƙarfe. Gaba ɗaya jikina ya zama kamar ba nawa ba. Na kasa motsawa. Ko buɗe ido sai na ji kamar ana ɗibo dutse daga idanuwa. Ban iya magana sosai ba, kuma numfashina yana fita da ƙyar.
Shi kuwa Bashari... wanda ni na sani da taurin kai da ɗabi’un banza, sai na ga wani sabon salo a tare da shi. Kamar ba shi ba. Cikin dare da rana, yana gefena. Ko ina kwance a tabarmar ɗakin nan na ƙauyen mu, sai ya zauna gefena yana shafa gashina da tawul mai ɗumi. Yana ɗibar ruwa a ƙoƙon kasko yana sawa a cikin kasko sannan ya matso da tawul, yana dinga goge min jiki da shi.
"Ramlah... Allah yabaki lafiyaji. Na fi so ni nayi ciwo akan ki." Yana faɗin hakan yana sharar hawayen da suka cika idanunsa. ban taɓa tunanin rana za ta zo da zai zauna yana kuka saboda ni ba.
"Wallahi Allah Ramlah, da ina da iko sai na dauki ciwon nan na sa shi a .. wallahi ba zan iya kallonki kina wahala ba," ya ce yana riƙe hannuna da ya riga ya lalace da zazzaɓi.
****
Ranar Lahadi ce. Tun da na farka jikina yaƙiyin daɗi. Ina jin nauyi a ƙirjina, ciwon kai da zafin jiki. Bashari ya shigo ɗakin, yana kallona da damuwa, ya taɓa goshi na, sai ya ce, “Ramlah, zafin jikin nan fa yayi yawa hankalina yafara tashi gaskiya.”
Nace, “Zan samu lafiya, insha Allah.”
Ya ɗan juya ya ce, “Yau fa na shirya muje birni mu ga likita, amma bari mu fara zuwa wani kauye nake jin akwai wani dattijo mai magani da ake ce wa Malam Jinjiri. Naji yana bada magani sosai.”
Ya taimaka min na saka hijabi. Na ji ya rungumeni kamar zai hana iska ta busa jikina. Ya fitar da ni har mota, ya rufo gidan, ya buɗe akwalar mota ya ɗebo bargo ya shimfiɗa a ciki, sannan ya tallafani na shiga na kwanta.
Ƴan kauyen mu kuwa sai kallon mu su ke yi, wasu na cewa, “Allah ya ba lafiya,” wasu kuma sai gulma kawai ke bakinsu. Amma Bashari bai damu ba, sai ya ja mota muka tafi.
Mun yi tafiyar sama da awa guda, muka isa wani ƙaramun kauye da ake kira Tungar Rago. Kayan ginin gidajen kauyen duk da bulo ne. Muka wuce wani babban gidan tsakuwa da bishiyoyi masu inuwa a gabansa. A can muka hango wani dattijo fari sol yana zaune gindin bishiya da almajirai kusan goma ke zagaye da shi suna latsa allo.
Bashari ya gaisa da su, cikin ladabi. Malamin ya amsa da fara’a, yana kallon mota yace, “Ina marar lafiya?”
Bashari ya taimaka min na fito, na taɓa ƙasa da kafata. Cikin girmamawa ya ce, “Ku shigo ciki maraba.” Muka shiga wani soro wanda ke da faɗi da furen ciyayi a gefe. Bai da wani ado face carbi guda da robar ruwa a gefe.
Ya nuna min kujerar ƙasa. Na zauna. Yana kallona da ido kamar mai karanta zuciya, sai ya ce, “ƴata, nunamun tafin hannunki.”
Na buɗe tafin hannuna na nuna masa, ya lumshe ido. Daga baya sai ya buɗe idonsa ya ce “An yi miki asiri, yarinya. Ba cuta ba ce ta halitta ke damunki, wani abu ne akasa miki ya shige miki kuma anyi amfani da takalminki ne, kuma suna son su sha jinin jikinki ko dayake ma sun sha sha zance. Amma addu’ar da kike yawan yi, musamman lokacin dare, ta hana su samun dama. Asirin su yana ƙonewa da addu’arki.”
Na saki baki ina kallonsa. Bashari ya dafe kai, yana cewa, “Innalillahi… Ashe ba ciwon birni ba ne?”
Malam ya ce, “Ba likita zai magance wannan ba. Sai dai Allah ki dage da addu’a, da yardar Allah zakiga abun mamaki.”
Ya ɗauko wata roba daga wani leda, ya ce, “Ga maganin ruwa nan. Ki dinga wanka da shi sau biyu a rana. Na safe da na dare. Ki cigaba da addu’ar da kike yi. Ki yawaita Ayatul Kursiyyu, Suratul Falaq, da Suratul Naas.”
Bashari ya karɓa da godiya. Na saki ajiyar zuciya. Wani irin sanyi na ji ya ratsa zuciyata. A cikin zuciyata nace, “Allah kai ne mai mafita ta..”