Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 45
Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 45: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 45. Malam ya ƙara da cewa, “Ki guji ƙin yarda…
3,370 words
Malam ya ƙara da cewa, “Ki guji ƙin yarda da kaddara, ki dinga yawan istighfari, kuma ki bar fargaba. Da izinin Allah, wannan ciwo zai wuce.”
Mukayi masa godiya . Bashari ya ciro kuɗi ya mika masa, amma sai ya ɗan yi dariya ya ce, “Ni bana karɓar kuɗi. Allah ne ke biyan alkhairi.”
Sai da muka fito daga soron, na tsaya na kalli bishiyar da muka hango shi a ƙarƙashinta.
Bashari ya kama hannuna, ya ce, “muje ko?”.
Da muka dawo gida daga kauye, har yanzu jikina bai gama dawo daidai ba. Amma kuma zuciyata cike take da natsuwa da ƙaunar mijina. Ashe kulawa tana warkar da zuciya fiye da magani.
Bashari bai bar komai a hannuna ba. Shi da kansa yayi girki. Na zauna ina kallonsa daga gefe, yana tsiyaya mai a cikin tukunyar miya, yana jujjuya girki kamar tsohon chef. Sai ya dan kalle ni lokaci zuwa lokaci yana dariya, yana ce min, "Ke dai ki zauna ki huta. Ni zan yi miki komai yau."
Bayan ya gama girkin, ya gyara falo da ɗakinmu. Ya ɗauko kayana, har da nasa, ya zuba cikin bokiti ya shiga wanke su. Breziyata ma bai barta ba har ita ya wanke. Na kalle shi cike da mamaki da jin daɗi, zuciyata ta harbawa naji kamar an yayimun damuwata. Wani lokaci in na kalli irin halinsa na baya, sai na kasa yarda da wanda nake gani a yau. Ashe kulawa na da wani salo mai motsa zuciya.
Na ce masa da sassaukar murya, "DanAllah.. Nakasa faɗar sunansa, inason in watsa ruwa."
Sai ya kalle ni, ya ce, "To amma sai ni na taimaka miki. Karki ce zaki iya da kanki."
Na ce, "Kai dai barni, zan iya."
Sai ya ce, "Sam, Sam! A'a Ramlah. Ki bar ni. Na fi kowa sanin halin da kike ciki yanzu."
Haka ya ɗauko ruwan wanka ya kaimun bandaki. Ya ɗauke ni da ƙyar ya kai har ciki ya dakko kujera ya ce, “Zauna a nan ki watsa ruwa ” Ya tsaya har na gama wankan, sannan ya sake rungumata a hankali ya dawo dani daki.
Na kwanta ƙasa da gado. Shi kuma ya ɗebo abincin da ya dafa da kansa. Ya zo kusa dani ya ce, “Bude baki ki ci. Kin san dai bazan barki da yunwa ba.”
Na buɗe baki ina kallonsa kamar wata ƙaramar yarinya. Ya fara bani da cokali, yana kallona da murmushi. Sai na ce da shi, “Kai fa baka ci ba?”
Sai ya ce, “Na koshi da kallonki. Bakin nan naki, yadda kike motsa shi lokacin da kike ci, wallahi nafi jin daɗi fiye da komai.”
Na ƙasa kai ina jin kunya, na ce, “Ni ma na koshi.”
Sai ya ɗaure fuska, ya ce, “Na san karya kike. Amma kin ga fa sai na sa kin ci.” Ya ɗauko cokali, ya sake bani. Na ɗan buɗe baki da dariya, zuciyata cike da jin daɗi da ƙauna.
Bayan mun gama cin abinci, ya ɗauke kwanon, ya share gabanmu tsaf. Sai ya dawo kusa da ni, ya zauna yana shafamin gashina a hankali. Ya ce, “Ramlah, Allah ya albarkace ki. Ni bazan taɓa bari wani abu ya sake ɓata miki rai ba. Ki dinga addu’a, Allah yana ji.”
Bashari na zaune gefena yana kallona da idanuwansa masu ja. Ya ɗauko maganin rubutu daga jaka, ya buɗe a hankali. Sai ya ce da ni, “Ramlah… yanzu zan fara shafa miki wannan rubutun ajikinki. Yana da matuƙar muhimmanci, malam ya ce da safe kafin rana ta fito. Amma kada ki ji komai… bazan kalleki ba, ki yarda da ni.”
Na kalle shi da ido mai cike da kunya, na ce da sanyi, “Bashari… wallahi ina jin kunya sosai.”
Sai ya ɗan murmusa, ya ɗora hannunsa kan kafaɗata, ya ce, “Ke fa matar aure ce. Kuma ni mijinki ne. Ai duk wani abu dake jikinki halal ne a gareni. Amma ki daina tsoro. Babu kallon banza, babu ƙetare gona.”
Na lumshe idona ina jin kamar wata sabuwa a jikina. Na dinga takure jikina da hannu, zuciyata na bugawa da ƙarfi.
Sai ya ɗebo ruwan rubutun cikin hannun sa ya fara shafawa daga hannu har zuwa kafa. A hankali, yana karanta wasu addu’o’i a hankali cikin raɗa. Na ɗan buɗe ido, na ganshi yana kallon kasa, yana aikinsa da nutsuwa kamar wanda baima san ina kallonsa ba.
Yana zuwa tsakiyar kirjina, sai ya dan tsaya yana jan numfashi. Na kalle shi da ido mai tambaya, shi kuma ya ce cikin ladabi, “Ki yarda da ni. Bazan taba cutar da ke ba. Wannan rubutun fa sai na shafa miki, amma ki yarda da zuciyata.”
Cikin sanyin murya nace, “To... amma ka dinga rufe idonka… wallahi ina jin nauyi sosai.”
Sai ya ce, “Na rufe zuciyata da kunya fiye da ke. Amma Allah na gani, ki yarda da ni.”
A hankali ya matsa gaba, ya ɗan shafi gefen nonona da hannunsa mai ɗumi. Wani irin shauƙi ne ya tsinkeni. Na rufe nonon da tafin hannuna, fuskata na kunce kamar zan fashe da kuka. Amma ba saboda zafi ba… saboda yadda nake jin jikina yana amsa wa, zuciyata na sauke numfashi mai sanyi.
Na ce da ƙasa da murya, “Bashari…”
Sai ya ce, “Shhh… Na gama. Ki huta yanzu.”
*****************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA TAMANIN DA TAKWAS
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Cikin dare, gaba ɗaya na kasa bacci. Na dinga jin jikina kamar ana zuba min garwashi. Wani marayan kuka na fara yi na kasa tsaida kaina. Da ƙarfi na shiga kuka, cikin azaba da ɓacin rai.
“Wayyo Allah... kaina... kaina!”
“Basharii...!”
Na fadi da karfi kamar wacce aka wurgar da ita. Kafin in ankara, sai na ga Bashari ya shigo da gudu daga falo. Ya rikeni da tsananin damuwa.
“Ƴar kwalisa! Lafiya? Menene? Kaina kaina?”
Wannan ne kaɗai abin da na iya furtawa.
Abin mamaki, sai na ji Bashari ya fara kiran sunayen Allah da girmamawa. Wannan ne karon farko da na san cewa ya iya addu’a. Ya fara karanta ayoyin Alkur’ani cikin sanyi da tausayi, yana cewa
“Ƴar kwalisa, zaki warke insha Allah. Kinji?”
Ya ci gaba da raira mun ruƙya a hankali. Daga baya na fara jin azabar da ke ƙona min kai tana raguwa. Na lumshe ido a hankali, zuciyata ta fara samun nutsuwa. Ba da jimawa ba, sai bacci ya dauke ni a jikinsa yana rungumeni kamar wanda baya son ya sake ni.
Bani da masaniyar yadda dare ya wuce, sai da na farka da safe. Da kyar na samu na mike na tashi, na shiga bandaki nayi alwala sannan nayi sallar asuba.
Jikina a lokacin yana da zazzabi sosai, ga gajiya da rauni a sosai. Amma abun mamaki duk motsin da nayi, Bashari yana tare da ni. Ko dai ya rike ni, ko yana saka hannu yana dafa ni da tausayi. Hankalinsa ya tashi sosai. Ya sanya min hannu, ya karanta ruƙya a jikina, sannan ya ce
“Zan dinga yi miki ruƙya kullum ƴar kwalisa. Sai kin warke gaba ɗaya.”
Bayan ya gama, na koma na kwanta. Bacci ya kwashe ni har zuwa bayan la’asar. Na farka da jin wani irin nishadi da ƙarfi a jikina kamar ba ni ba. Ina tashi na ji komai ya lafa azaba, zazzabi, ciwon kai... duk sun bace kamar da sihiri. “Alhamdulillah...”
Na fada cikin jindadi da godiya.
Amma banga bashari ba sai hango flask din shayi da bread nayi agefe da Alama ya dafa yafita Na sha, sannan na tashi na haɗa ƙurfoti, na dora ruwan zafi, na yi wanka. Na canza kaya sannan nayi sallah. Cikin kwanciyar hankali, bacci ya sake dauke ni.
Na farka da misalin ƙarfe biyar na yamma. Na juya da sauri domin ban ji motsin Bashari ba har yanzu bai dawo ba. Wayata kuwa ba kuɗi balle in kira shi, kuma na duba naga shima bai kirani ba. Hakan ya saka ni cikin wani irin damuwa.
Na yanke shawarar fita can gabanmu domin sayen kayan miya. Na dawo na dafa mana tuwo, sannan na sake gyara gidan gaba ɗaya. Da yamma, bayan sallar isha’i, sai bacci ya sake kwashe ni cikin nutsuwa.
Wajen ƙarfe goma na dare kenan, sai na ji ana kwankwasa ƙofa da ƙarfi. Cikin ɗan firgita, na miƙe na zura mayafi. Na buɗe ƙofar da sauri, sai kawai na ji hannu ya rungume ni da ƙarfi. “Ƴar kwalisa… yanzu tun safe na aiko Uwani baki buɗe mata ba? Jikinki ne ko wani abu? Haba Ramlah.”
Fuskar sa cike da damuwa, idanunsa sun nuna gajiya da ƙauna. Na kasa magana. Sai hawaye suka fara gangarowa daga idona. Na juya da sauri na koma ciki, zuciyata na rawa kamar garwashin wuta.
Ya shigo da ledoji hannunsa, ya rufe ƙofar, sannan ya bi ni ciki. Ya zauna gefena, yana kallona “Ƴar kwalisa, me nayi miki ne? Me yasa kika ƙi gaya min abinda ke damunki? Wallahi hankalina ya tashi.”
Cikin sanyin murya nace, “Bashari… I don’t know what to say. Na ji haushin yadda ka tafi ba tare da ka faɗa ba. Kuma kamar baka damu da lafiyata ba.”
“Ki yafe ni,” ya ce yana shafar gefen fuskata da hannunsa mai dumi. “Na fita ne domin neman likita, naga jikin naki har da asuba da zafi. Na siyo miki magani. Na ga ko ruwa sai da kyar kike sha.”
Na zube a jikinsa da kuka, sai na ji kamar duniya ta daina nauyi. Ya ɗora hannunsa a bayana yana bubbuga a hankali, yana faɗin
“Na san bani da daraja a idon mutane, amma wallahi har gaban Allah ina sonki Ramlah. Soyayya ce ke sa ni tsayuwa a kanki.”
Ya ɗaga fuskata da yatsunsa, ya sosa gira da ɗan murmushi mai laushi. Sai ya ce “Kinyi kyau sosai duk da kukan nan, amma zaki yi kyau fiye da haka idan kika murmusa min yanzu.”
Na ƙanƙame leɓe na da kunya, amma sai na saki ɗan murmushi mai rauni. Ya kai fuska kusa da tawa, ya sumbaci goshina a hankali, sannan ya ce “Ƴar kwalisa... Ki sani wallahi na canza. Ba zan kuma barin ki kina kuka ba. Ina son ki fiye da yadda nake son kaina.”
Na ji jikina ya saki. Na kwantar da kaina a kirjinsa, ina jin bugun zuciyarsa yana rawa.
“Idan na riga na gaji da duniya, sai kawai na tuna dake... sai zuciyata ta lafa,” ya ce cikin sanyin murya. “Bari na shigo da kayan.”
Ya fice, ya ɗauko su daga waje. Da ya dawo, sai ya cire kayansa cikin natsuwa, ya wuce bandaki. Bayan wasu mintuna ya fito da gajeran wando da vest kawai a jikinsa. Sai kamshi mai daɗi ya biyo bayansa turarensa na musamman.
Ya zauna yana buɗe ledar kayan abinci. Na ga fruit ne, yoghurt, kaji soyayya, da kuma kwalbar magani. Wani kaya guda ɗaya ya ware gefe, bai buɗe ba. Sai ya miƙe zuwa kicin ya yayyanka fruit ɗin cikin bowl da kyau, ya dawo ya ce “Ƴar kwalisa, sauko nan.”
Ya miƙo min yoghurt ɗin tare da faɗin “Ki sha. na san yau ba ki iya cin abinci ba na lura ma kamar bakyason tuwo shiyasa nasiyo miki su cabbagesai kiyi shinkafarku ta birni har man salad nasiyo da kwai. Maza ki sakko Kuma ba zaki ce min baki da yunwa ba.”
Turarensa ya cike ɗakin, yana birkita min hankali. Na karɓa cikin jin daɗi, na sha yoghurt ɗin har na gama. Yana kallona yana murmushi, sai ya miƙo min farantin kaji.
“Karɓi wannan kazarma. Ki cinye yanzu. Ban son wannan ramar da kike yi. Ina son ki cikakke kamar da.”
Sai da ya tabbatar na ci sosai, sannan nima na zubo masa tuwon da nayi, ya zauna ya ci da jin daɗi . Yana ci yana kallona da murmushi, sannan yace: “Na sha maganina yanzu.”
Na gyada masa kai da murmushi na ce “To. Allah ya kara lafiya.”
Bayan mun gama cin abinci, ina zaune a gefe ina kallonsa yana gyara wurin da muka zauna. Idona yana lumshewa kadan-kadan, alamun bacci na zuwa, sai kawai na ga ya ɗago wata leda daga cikin kayan da ya shigo da su.
Ya buɗe ledar nan a hankali, sannan ya fara fidda abubuwa ɗaya bayan ɗaya
Atamfa guda biyar, kowacce na zamani ne, sabbin salo masu kyau da launuka masu ɗaukar ido,Lace ɗaya mai laushi da kyan gaske, Shadda tana sheƙi,Kayan kwalliya da mayafai masu kyau masu ɗaukar hankali.
Ya juya ya miƙo min kayan yana murmushi, sai yace da wata murya mai sanyi “Ga su nan ƴar kwalisa, kingansu kuwa? Wallahi kadan ne, amma tsada ne dasu gani nayi dana siyo miki kanana gwara na dakko manyan kadan. Matata mai tsada ce, dole ta saka kayan da suka dace da ita.”
Na ɗan ware ido ina kallon kayan. Ganin super da gizna cikin kayan ya sa zuciyata ta cika da farin ciki Cikin natsuwa da farinciki nace masa “Na gode sosai, Bashari. Allah ya saka da alheri, ya kara maka lafiya.”
Ya ɗan ɗaga gira yana dariya da nutsuwa, ya ce “Bakomai ƴar kwalisa. Gobe da asuba zan fita zuwa birni. Akwai aiki da nake ƙoƙarin kammalawa. Ki tayani da addu’a kawai.”
Na ce masa da fara’a “Allah ya taya ka riko, ya dawo da kai lafiya.”
A hankali na lumshe ido, bacci na kokarin ɗauka. Sai na ji muryarsa a hankali “Tashi mu kwanta.”
Na bi shi zuwa ɗakin. Mun kwanta ne, amma ba kamar yadda ya saba ba yau bai rungume ni ba. Na lumshe ido ina jin kamar wani abu ya canza. Sai na ja jikina a hankali, na matsa kusa da shi, na jingina a gefensa kamar jaririya.
Sai kawai ya juya, yana kallona da idonsa masu cike da kulawa, yace da murya mai nutsuwa “Menene ƴar kwalisa? Kina lafiya?”
Na lumshe ido nace masa “Bakomai... bacci kawai nake ji.”
Sai ya ɗan murmusa ya rungume ni a hankali. Muryarsa na fita kamar rada a kunne na “Ƴar kwalisa... kina son wani abu ne?”
Numfashinsa yana bugawa da dumi a fuskata, sannan sai naji jikina ya saki gaba ɗaya. Yadda ya rungume ni da dumi da taushi sai na ji kamar duniya gaba ɗaya ta narke a zuciyata. Bacci ya ɗaukeni cikin wannan kwanciyar hankali, a jikinsa inajin wani kalar dadi.
*****************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA TAMANIN DA TARA
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Washegari da asuba, na farka cikin natsuwa. A hankali na tashi, na nufi bandaki nayi alwala, sannan na dawo nayi sallah. Bayan na idar, sai na juya ina kallon Bashari yana zaune a kan daddumarsa cikin nutsuwa, yana lazumi. Fuskar sa cike da annuri da natsuwa kamar wanda ke cikin wata sabuwar rayuwa.
Na ce masa "Ina kwana… Bashari, wai kayi Islamiya ne?"
Ya juyo yana murmushi, sannan ya amsa cikin ladabi "Na dan yi kadan ƴar kwalisa, amma ban kai ga haddar Qur’ani ba. Duk da haka, ina da ilimin addini sosai. Wallahi, na saba da zuwa Islamiyya a baya, har na kai ga fahimtar darussa da yawa."
Ya ja numfashi, sannan ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. "Ƴar kwalisa, gaskiya ina jin tsananin bakin cikin dabi’u na da suka wuce. Har gobe, ba na jin daɗin yadda rayuwata ta taɓe. Na rasa iyayen gida da yawa saboda halayya na. Amma da taimakon Allah, nayi ƙoƙari na gyara komai.”
Ya ci gaba da bayani da murya mai raɗa
“Aliyu, na dawo da shi wajen iyayensa munje muka roƙi gafara, suka yafe masa. Haka sauran biyun ma, na basu jari, na saka su makaranta, sannan na nemi gafarar iyayensu. Yanzu, Alhamdulillah, suna tare da iyayensu cikin salama.”
Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyata. Amma cikin wannan sanyi, akwai ɗan wani zafi da ya sosa min rai ganin cewa Bashari ya gyara dangantakarsu da iyayensu, amma ni… ba ni da kowa. Sai na lumshe ido na ɗan ɗago kai, ina kare masa kallo.
Ya cigaba da cewa “Kinsan inada gadon mahaifiyata gona guda huɗu ne. Na samu nasu rabon, na sayar da guda biyu, nayi jari da su. Na kama sana’a a birni tun kafin na zama haka, Wallahi ƴar kwalisa, ba kudin aikin daba nake amfani da su ba, sai dai nayi shaye shaye dasu. Amma cikin ikon Allah, ban taɓa amfani da su wajen kasuwanci ba. Inada baffa yayan mahaifiyata shine yake taimaka min, yana ba ni shawara kuma yana saka ni a hanya ta kwarai bangaren kasuwar yanzu ma haka shago daya nawa shine aciki tun da daɗewa.”
Na juya masa ido cike da tausayi da kuma yabo. Na ce da shi “Allah ya ƙara shiryar da kai, Bashari. Allah ya yafe maka. Ya kuma saka maka da lada akan kokarinka da wahalar da ka sha wajen gyara rayuwarka.”
Ya murmusa da jin daɗin kalaman da na furta. Nan na mike na ce “Bari na ɗan haɗa maka dumame.”
Na nufi kitchen cikin sauri, na haɗa masa dumamen tuwo da miyar . Bayan ya ci, muka zauna muka yi sallar safe tare. Sai na tsinci kaina ina jin wani irin farin ciki da kwanciyar hankali cikin zuciyata. Bayan sallar, ya kama hanya zuwa birni kamar yadda ya saba.Ya juya ya fita. Amma kafin ya buɗe ƙofa, sai ya sake waiwayowa ya ce “Kin manta da wani abu?”
Na girgiza kai cikin mamaki, sai yace “ kiss kafin in tafi... domin in tuna da ke a hanya.”
Ya dawo ya sumbace ni a goshi, sannan ya fice. Na tsaya a ƙofa ina kallonsa har ya ɓace cikin duhun safiya.
Tun daga lokacin da Bashari ya fita, zuciyata ta kasa samun kwanciyar hankali. Na zauna na miƙe, na koma na kwanta amma ina! Kamar zuciyata tana tambaya, tana yawo kamar tana neman abu da bata gani ba. Daga ƙarshe, na yanke shawarar cewa ba zan zauna haka ba. Na saka hijjab dina, na nufi gidan Uwani.
Da na shiga, muka gaisa da salam. Uwani ta ce “Matar Bashari kece?” Na dan yi murmushi nace “Eh, ni ce.” Ta dan yi dariya, tace“Ai jiya nazo har ƙofar gidanku ina ta bugawa amma baki buɗe ba.” Nace mata “Wallahi banji ba, ina can ina bacci sosai..” Ta kalleni da tausayawa tace“Yaya jiki yanzu?” Nace “Alhamdulillah, naji sauƙi sosai. Allah ya kara lafiya.” Sai kawai ta gyara zama tace“To Allah ya ƙara lafiya. Amma ai in gaya miki gaskiya, ana ta gulmarki fa.” Na dan ɗaga gira, nace “Gulma kuma? Uwani, wace irin gulma?”
Ta ce “Ana cewa ke kika hana Bashari dabbanci, ai yanzu wai Bashari ya daina dana Wai kamar ki kika chanza shi.” sai kawai na dan saki murmushi nace“To Uwani, Allah dai ya shiryesu. Aikin gulma ai ba ya hana hasken gaskiya.” Uwani ta ce“Gaskiya kam. Amma ya kamata ki dinga kula da abinda kike ji a gari.” Na ce mata “Haka ne. Amma Uwani, ba wannan bane dalilin zuwana.” Ta ɗago kai tace:
“To me ne?” Na ce “Ina son ki raka ni gidan su Bashari. Ina da magana da wasu can.”
Sai tayi dariya tace: “Ke ƴar nan, me zai haɗaki da waɗancan marasa mutuncin?”
Na dan danne dariya nace “Ba komai, kawai inason ki kaini.” Ta kalle ni, tayi shiru na ɗan lokaci, sannan tace “To shikenan. Bari na ɗauko mayafi.”
Bayan mun fita daga gidan Uwani, muka nufi hanyar gidan Baban Bashari cikin natsuwa. Rana tana dukanmu, iska tana kadawa a hankali. Uwani tana tafe da ni, tana dan tambayata “Ramlah, me kike so ki faɗa musu ne?” Na ce “Uwani, kawai dai naje na gaishe su ne da kuma dan magana da maigidan nasu.” Uwani ta gyara mayafinta tana cewa “Haka ne, amma fa ki daure zuciyarki. Mutanen can ba mutane bane.”
Da muka isa ƙofar gidan, sai muka shiga harabar gidan. Matarsa Baban Bashari ce ta fito da hannu a haɓa. Tana kallon mu da tsanani. Kafin mu kai gaisuwa sai ta fara magana cikin tsiwa “Ina zaku? Ina kuka dosa?”