Kenza eBookz

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 46

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 46

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 46: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 46. Uwani ta ce “Sannu dai, mun zo ne dan…

3,336 words

Uwani ta ce “Sannu dai, mun zo ne dan gaisuwa da Baba.”

Sai matar nan ta harare mu, ta ce “To kuji tsoron Allah. Gaisuwa kuma? Kuje ku same shi can gindin bishiya yana shan iska. Kada ki ƙara zuwarmin gida kinji? Ku shigar mun gida kawai. Wayasani ko ke mayya ce.”

Cikin ƙyasa da rashin kunya ta juyar da kai ta koma ciki. Ni kuma da Uwani muka tsaya muna kallon juna. Uwani ta ce “Na fa gaya miki, Ramlah. Ki ga irin sharrin da mutane ke ɗauke da shi. Ba komai. Mu tafi can inda take cewa.”

Na ɗan lumshe ido, zuciyata cike da nauyi, sannan muka juya muka nufi gindin bishiyar da tace Baba yake. Cikin zuciyata kuwa, na ƙuduri niyyar cewa idan mutunci ya gagara a gaisuwa, to shiru ma gaisuwa ce.

Ko da muka iso bakin bishiyar, shi kuma yana zaune gindin bishiyar mangwaro yana shan rake, ya ware kafafu yana kallon wucewar mutane kamar wanda babu abin da ke damunsa.

Uwani ta juyo ta kalle ni, sai tace “Ramlah, sai kin dawo. Kada ya tozartani, ni kuma kinga tafiyata ba mutunci ne dashi ba.”

Nace mata da ladabi “Na gode Uwani. Allah ya saka da alheri.”

Na karasa na tsaya, sannan da sallama nace “Sannu Baba... ina kwana?”

Ya ɗago kai yana kallona daga sama har ƙasa.

Yace da wata irin murya mai tsauri “Lafiya kalau. Banganki ba.” Na samu guri a ƙasa kusa da shi na zauna a hankali, sannan nace “Eh... bazaka ganini ba, ni ce matar Bashari.”

Cikin mamaki da haushi, sai ya watsa min harara, ya ce “Ke? Ke fa kika ce ke matar Bashari ce? To banson wasa. Wani mahaukacin uba ne zai yarda da ɗansa ya aurawa ɗan iska irin sa? Ke da kallo ɗaya ma sai naji haushi! Yaushe Bashari ya zama mutum har zai samu matar arziki? Wallahi ke ba matar ɗana bace, ki tashi ki bar wurina kafin na maka ihu.”

Sai na lumshe ido, na dafe ƙirjina da hannu daya, sannan nace da nutsuwa da ƙasaitacciyar murya “Baba, ka saurare ni. Idan ka ce ka kore ni, zan tafi. Amma ka saurari kalmomi na kafin nan. Na fahimta cewa kana jin haushin Bashari. Na fahimta cewa kana kallon sa a matsayin wani abu mara amfani. Amma, Baba... ni ce matarsa. Kuma tun da nake da shi, ban ga illa daga hannunsa ba. Wallahi yana ƙoƙarin canzawa.”

Na ɗan ja numfashi, sannan na ci gaba “Baba... kai uba ne. Ka sani, Allah zai tambaye ka akan ɗanka. Idan kai ka yanke masa hukunci, wa zai gyara shi? Idan kai mahaifinsa ka ƙi yarda da shi, wa zai yarda da shi? Hadisin Annabi ya ce “Ku taimaki ɗan uwanku mai zalunci da wanda ake zalunta.” Aka ce masa, ya Rasulullah, ya taimake mai zalunta? Sai ya ce “Iya taimako shine ka hana shi zaluncin.”

Na ciro alƙur’ani da ke cikin jakarta, na nuna masa “Baba, cikin wannan Littafi ne Allah ya ce “Wa man ‘afaa wa aslaha fa ajruhu ‘alal laah” Wanda ya yafe kuma ya gyara, to ladansa yana wurin Allah.”

*****************

Nana hadiza

09030569336

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA CASA'IN

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

Na gyara zama a hankali, na ɗan saki numfashi, sannan nace da sautin muryar da ta cika da ladabi “Baba... da yardar Allah na zo ne ba wai dan na ɓata maka rai ba. Na zo ne dan na bude maka zuciya ta. Dan Allah Baba, ka yafe min idan wani abu ya ɓata maka rai game da zuwana.”

Ya harare ni da idonsa, sai ya tura rake a baki yana taunawa, sannan yace “Ina jinki. Ki fadi abinda ya kawo ki.”

Na gyara zama sosai, nace “Baba... Ni ce Ramlah, matar Bashari. Ni mace ce, amma zuciyata cike take da raɗaɗi da tunani. Baba... meyasa zamu haifi yaro, amma mu barshi cikin duhu? Meyasa uba zai raina ɗansa, ya wulakanta shi, ya ɗauke shi kamar ba jini ɗaya suke da shi ba?”

Ya ɗan yatsina fuska, yana kallona da alamar bacin rai, amma ban damu ba. Na ci gaba “Baba, idan mutum bai taimaki dansa ba, wa kake zato zai taimakeshi? Alhali Allah yana cewa a cikin Alkur’ani ‘Yā ayyuhallazīna āmanū, qū anfusakum wa ahlīkum nāran...’

(Ya ku waɗanda suka yi imani, ku ceci kanku da iyalanku daga wuta.) Baba, mecece rayuwa idan ba ta da soyayya da kulawa daga iyaye? Bashari bai zabi haihuwar kansa ba. Amma ya taso cikin wulakanci da ƙyama daga gida. Ya girma cikin rashin kulawa. Daga ƙarshe sai rayuwa ta jefa shi cikin duhu, cikin mugunta, cikin shaye-shaye da daba. Amma Baba... yanzu ya canza.”

Na sauke ajiyar zuciya, hawaye na gangaro min daga ido, nace “Baba, wannan yaron da ka haifa wanda kake raina... shine yake bani ruwa na sha, yana dafamin abinci, yana duba jikina idan na kamu da zazzabi. Shine ya daukeni daga kasa ya gina ni. Amma shine kuma kake cewa dan iska ne. Baba, idan mutum yana da kuskure, sai a gyara shi ba a yashe shi ba.”

Na ɗan jima ina kallon fuskarsa. Na lura ya rage tsawonsa. Na ci gaba cikin karfin hali “Manzon Allah ﷺ yace:

‘Kowane ɗanku na da hakki akan ku, ku basu tarbiyya da adalci.’

Kai kake da hakki akansa Baba. Idan ka guje shi, wa zai karɓe shi?”

Na share hawayena da gefen mayafina, sannan nace “Baba... Dan Allah ka saka Bashari a ranka. Ya sauya. Yana ƙoƙari. Yana karanta Alkur’ani yanzu. Yana taimaka min da gaskiya da kulawa. Kuma wallahi Baba, a yanzu ni ce nake gani kamar ni na fi kowa sa’ar miji. Duk da yana da laifi a baya, amma yana ƙoƙarin canzawa. Idan ka cigaba da ƙin amincewa da shi, zai iya dawowa baya. Kuma idan hakan ta faru, sannu a hankali duniya zata yi masa kisan gilla. Amma idan kai da kanka ka rungume shi, wallahi zai ci gaba da gyara rayuwarsa.”

Na lumshe ido, na sauke ajiyar zuciya, sannan nace“Wannan ne ya kawo ni Baba. Na gode da ka saurare ni. Ni ban zo dan in ɓata maka rai ba. Na zo dan zuciyata ba zata iya jure rashin kulawar uba ga ɗansa ba.”

Ya tsaya shiru yana kallona, rakin da yake taunawa ya tsaya, sai yaja numfashi da ƙarfi, baice komai ba. Sai na miƙe a hankali, nace “Na gode Baba. Idan Allah ya yarda, in Allah ya kaimu, zan sake dawowa.”

Na juya na bar shi da tunani.

Da na juya zan bar wuri, sai kawai na ji muryarsa daga baya tana kiran sunana “Ke... dawo nan...!” Na tsaya cak, na juyo a hankali, zuciyata cike da tsoro da rashin tabbaci. Ya nuna min gefensa da hannu, yace “Zo ki zauna nan.”

Na ƙarasa cikin ladabi, na zauna a hankali kamar ɗiya mace a gaban ubanta.

Ya kalli idona kai-tsaye, yace da wata irin murya mai nauyi “Da gaske ke ce matar Bashari?”

Na ɗan sunkuyar da kai, sai na ce a hankali“Eh... Baba. Ni ce.”

Ya gyara zama, ya sauke ajiyar zuciya, sannan yace “Na ji duk kalamanki. Wallahi sun shige ni. Kuma kafin ma kisameni, wani abokina ya kirani jiya ya fadamin maganganu da suka sa ni tunani sosai. Yace min ‘Kai malam... baka tsoron Allah ne? Yaronka yana can yana fama da rayuwa, kai kana zaune ka juya masa baya. A'a malam... hakan ba daidai bane.’”

Sai ya kalli gefe kamar yana tuna abubuwan da suka faru a baya, sannan ya ce “Kina ganin ni ne na fara gujewa ɗana? Wallahi ba haka bane. Bashari ne ya fara guduna... sama da shekara ashirin ina ƙoƙarin jawo shi amma baya zuwa. Yana kallona kamar bashi da uba. Sai naga kamar shima ya zaɓi rayuwarsa ni kuma na zaɓi tawa.”

Ya lumshe ido na ƴan daƙiƙu, sannan ya ce “Kwarai kuwa, ina da sakaci. Ina da rashin kyautatawa. Na biye wa matata a rayuwa, nayi son zuciya. Na yi kuskure da yawa. Amma yanzu... yanzu na gane komai. Da na kalle ki kawai naga nutsuwarki, ladabinki, da yadda kika tsaya gaban mutum kamar ni kiyi wa’azi na tabbatar Allah ya karbi addu’ata.”

Ya kalle ni da ido cike da tausayi da gamsuwa “Na dade ina rokon Allah ya kawo wani abu ko wani mutum da zai zama sanadiyyar canjin ɗana. Kuma yanzu na yarda... ke ce wannan mutumin.”

Sai ya daga hannunsa sama, yana fadin “Saboda haka... daga yau, na yafe masa. Duniya da Lahira. Kuma ina rokon Allah ya yi masa albarka. Ya tsarkake shi daga kurakurensa, ya gyara masa gaba. Na yafe masa gaba ɗaya.” Na share hawaye da gefen mayafina, zuciyata cike da daɗi da farin ciki.

Ya ɗan lumshe ido, sannan yace “Yaya sunanki?” Na ce: “Sunana Ramlah.”

Sai ya ce “To Ramlah... Allah ya yi miki albarka. Allah ya bar ki a matsayin farin cikin ɗana. Allah ya tsare ku gaba ɗaya. Na gode sosai... kinji.” Na ce “Nagode Baba, Allah ya saka da alheri.” Na miƙe da ladabi, na masa sallama, zuciyata cike da farin ciki da sanyi. Sai na tafi gida ina jin kamar an sauke dutse daga zuciyata.

Bayan na dawo gida daga wajen Baba, na zauna ina jin numfashina kamar ana daddafe shi. Wayata da na bari a daki na ɗauka, sai na ga an kirani sau biyu. Da na duba, sai naga Maryam ce. Nayi mata flashing ta ɗauka nan take muka gaisa.

Cikin farin ciki tace “Ramlah, labari mai daɗi! An cire strike, makarantarmu zata koma aiki nan da week guda.”

Zuciyata sai da ta buga sau biyu. Cikin wata murya mai nauyi nace “To Maryam... Allah ya kaimu.”

Tace da zolaya “Hmm... Ramlah ko dai ciki ne dake?”

Nayi dariya cikin rauni nace “Ko ɗaya Maryam, ba ciki bane.”

Tace tana dariya “Wallahi kin ji daɗinki, Ramlah. Dama ni nayi auren nan. Wallahi kowane ma zan aura.”

Nace da kashedi cikin lallashi “Aa Maryam, kidaina cewa haka. Ki dage da addu’a, Allah zai ba ki nagari.”

Tace cikin gamsuwa “Hmm... Ramlah, bazaki gane ba. Yanzu mazan kadan ne suke son aure da gaske. Yawanci sai iskanci suke so. Amma ni, in Allah ya yarda, zan auri na gari.”

Nace “Allah ya baki wanda zai rike ki da gaskiya da tsoron Allah.” Tace“Amin. Naso nazo gidanki wallahi, amma bari sai na dawo city. Yanzu ina nan garinmu.”

Nace “To Allah ya kaimu lafiya.”

Na kashe wayar. Sai na zube a kujerar gefen gado, na zuba ido sama. “Ramlah, kina son karatu. Amma kin rasa mafita… kina da mijin aure, amma kuma burinki na ilimi bai mutu ba.” Nayi ajiyar zuciya. Sai na tashi na shiga kitchen na dauko jallop ɗin shinkafa da ragowar naman da Bashari ya siyo jiya. Na jera cikin karamin flask, na kira wani yaro nace yakaiwa habu na bashi.”

Na dawo cikin gida, na rufe ƙofa. Na ɗauki hijab dina, na gabatar da sallar la’asar, sannan na zauna na shiga yin azkar da addu’o’i na zuciya. Na rika maimaita “Hasbunallahu wa ni’imal wakil...” har sau 450. Bayan na gama, na zauna ina jin sauƙi a zuciyata. Sai na ɗan kunna game a waya, amma har yanzu tunani bai barni ba. Sai naji kamar in kira Mama, amma zuciyata ta fasa ni da kuka. Na fashe da kuka sosai, hawaye na zuba Ban san dalili ba amma zuciyata na cike da ƙunci, ƙauna, da fatan ina ma nima mamata tanada rai.

Yayin da nake kokarin kwanciya akan katifata, sai na ji ana bugun ƙofa da ƙarfi sosai!

Na farka da karfi kamar wanda aka tsoma cikin ruwa. Na miƙe da sauri, zuciyata sai bugawa take kamar ana busa gangar yaki. Na saka mayafi a gaggauce, na nufi ƙofar cikin ruɗani...

Na buɗe ƙofa da niyyar karɓar bako ko maraba da ɗan uwa, amma sai gani na yi da Babah tsohuwar kakar Habu tana riƙe da kwano a hannu. Kafin in ankara, sai ta jefa kwanon a gaban ƙafata da ƙarfi, har ya bugu da ƙasa ya yi ƙara. Tana cikin fushi tana faɗin

*****************

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA CASA'IN DA DAYA

Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!

Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!

Domin biyan kuɗi:

Acc Name: Bilkisu Sani Kaura

Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:

09030569336 ko 07040402435

Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a

Arewabook @nanadiso10

https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********

"Na gaya miki muna yunwa ne, munafukar yarinya! Uban me yasa kika kai wa jikata abinci? Ko kina so ki ƙara janshi ku dinga iskanci da mijinki?"

Zuciyata ta kaɗu. Amma ban bari ta fashe ba. Na lumshe idona, na sauke ajiyar zuciya. Sai na ɗago kai na ce cikin ƙwantar da murya, kodayake zuciyata na cike da daci "Babah... menene laifina idan na kai wa yaro abinci? Ai kaiwa ɗan jiran kauna, sadaka ce. Alkhairi ne ya haɗani da jikanki, ba sharri ba.”

Kafin na ƙarasa, sai na ga ta cire mayafinta, ta shiga zagina. Tana ƙara hayaniya tana ihu kamar wacce aka cije "Ke! Ke har kinada miji? Kujifa! Wannan ɗan iskan ɗan luwadi mai bin mata da shaye-shaye shine mijin naki? Wayesan abin da kikayiwa iyayenki suka baki wannan basharin? Wayesan ko ciki yayi miki?!"

Na tsaya na kalleta ido cikin ido. Mamaki ya cikani. Wani irin ciwo da ɓacin rai ya ratsa zuciyata. Ashe haka masifa zata fito daga mutum da ba a zata ba? Ashe haka ake jefa mutunci da kima cikin ƙasa?

Na dafe ƙirji, na sake nisa. Sai kuma na ɗaga murya cikin nutsuwa da ƙarfi "Babah... Toh shikenan. Yanzu zagin mijina ya zama dariya? Gaskiya na gane ke ba abokiyar addu’a bace ke abokiyar ɓata zuciya ce. Ashe bakin ciki ne ya hana ki huta da cewa na samu sauƙi da zaman lafiya? Ashe addu’ar da kika shigowa da ita karya ce kawai da kike ɓoye sharri a ciki? Na kawo abinci abinci, Babah. Abinci wanda ke kawar da yunwa, wanda zai ciyar da maraici. Wannan ne ya sa kika fito da rana kika tsine min, kika tsine wa mijina, kika tsine wa iyayena? Ashe ke baki da rabo a cikin kalmar rahama?"

Mutanen unguwa sun fara taruwa. Wasu na kallonta cikin ban tausayi, wasu kuma suna juyawa saboda ƙyamar kalmominta. Sai na ce da murya mai ƙarfi "Ni ba zan faɗa zagi ba. Ba zan rama ɓatanci da ɓatanci ba. Amma Babah, ki sani Allah yana sauraron kowa. Kuma Allah yana bibiyar maganar kowa. Kalmomin da kika faɗi yau zasu dawo gare ki, ko a nan duniya, ko a lahira.Idan kika ce dan Bashari ya tuba karya yake yi. To ina shaidarki? Ke kika zauna da shi? Ko dai dai yadda kike janye jikan ki da sharri, haka kike musu da mijina ba tare da shaidar gaskiya ba?" Na daidaita mayafina, na ci gaba da magana da ƙwazo "Babah... kin ce ciki nake da shi? Shine iyayena suka bani shi bakya jin kunyar gaban Allah da mutane?. Me yasa ke kike sa kalmar nan a bakinki? Me nayi miki? Dan haushin bashari ya shiryu "Ina rokon Allah ya yafe miki. Amma daga yau, kada ki kuskura ki sake shigowa gidan nan da kalmomin da ba na alkhairi ba. Zaki iya zagi, amma ba zaki iya karya ni ba. Zaki iya ƙoƙarin ɓata sunana, amma mutuncina ba zai fadi ba domin Allah ne ke rike da shi, ba mutum ba. Kinyi kaɗan da kika ce mijina ɗan iska ne. Kinyi ƙasa da kika ce ni ‘yar iska ce. Amma sai na gaya miki ni mace ce da ta fiye da ɗaukar zagi da haƙuri. Amma idan kalmominki ba su daina ba, wallahi zan roƙi Allah ya hukunta duk wanda ke cutata da wanda nake ƙauna." Na juyo cikin nutsuwa, na ce "To Babah, idan kin gama zaki iya komawa gida. Ki ɗauki ɓacin ranki. Amma daga yau ƙofata zata rufe ne da zaman lafiya da addu'a, ba da fushi da fitina ba."

Na rufe ƙofa a hankali, na durƙusa, na ɗaga hannuwana sama cikin shiru "Ya Allah, ka ƙara min haƙuri. Ka tsare min mutuncina. Ka kare mijina daga bakin da ke ɓata masa suna. Ka sanya zuciyata ta samu salama da kwanciyar hankali..."

Duk da irin zagin da Babah ta mana, har cikin zuciyata ina jin kalmarta kamar ana karkada su da reza a kunnuwana. Amma ban ce komai ba, kawai na shige ɗaki cikin shiru, zuciyata na kunci da zullumi. Na ɗauki alwala, na yi sallah, na tsaya gab da Allah, ina kuka cikin roƙon shiriya da natsuwa.

Waje-wajen karfe 11 na dare, bacci ya fara kwashe ni, amma bugun ƙofa ya tasar da ni. Cikin kasala na miƙe na buɗe ƙofa. Sai kawai na hango Bashari da laida a hannu, yana kallona da idanuwansa da suke cike da ƙauna da kulawa. Ya rungume ni, yana faɗin "Na yi kewarki, ƴar kwalisa. Da na ganki haka, sai naji zuciyata ta karye. Ko jikin ne?"

Na danne zuciyata da nake ji kamar ta fashe da kuka, nace "Babu komai..." Ya kalli fuskata da mamaki. "To me yasa baki min dariya ba yau, ƴar albarka?" Na murmusa da ƙyar, na ce "Sannu da zuwa." Na karɓi ledar, na shiga ciki, na aje, shi kuma ya shiga wanka. Bayan kamar awa ɗaya, ya dawo, na zuba masa abinci. Ya ci amma baice komai ba. Ni ma ban ce masa uffan ba Can kuma sai naji yace "Kina tunanin zan bar zagin da Babah ta miki haka kawai?" Na zaro ido, ina kallonsa. Ashe labari ya iso gare shi. Na ce "Bakomai Bashari... ka barshi kawai..." Kafin in ƙarasa, sai hawaye ya gangaro daga idona. Na kasa daurewa. Na fashe da kuka.

Yayi saurin ajiyewa cokalin, ya tashi, ya je ya wanke hannunsa. Ya dawo, ya zauna kusa dani. Ya jawoni jikinsa, jikinsa na kamshi da turaren da na saba jin yana sosa min zuciya.

Yace "Yar kwalisa... bana son ganin hawaye a idonki. Ki kwantar da hankalinki. Aikin banza ce. Zagin da ta miki sai da naji yana fashe min kirji. Amma kin fahimta yanzu, ba kowanne mai dariya dake masoyinki bane."

Na gyada masa kai, da ƙyar na iya magana. Cikin sanyin murya na ce "Na yafe mata, Bashari... amma kalamanta sun daki zuciyata." Yayi shiru na ɗan lokaci. Sai kuma na ce da murya mai kaifi "Abu ɗaya nake so kayi..." Na kallesa, idanuna cike da hawaye "Me ne ne hakan?" Ya kame. Yayi shiru da ɗan lokaci, sai kuma na ce da murya mai laushi "Dan Allah, kayi hakuri da mahaifinka. Ka shirya da shi. Ni fa bana son ka rayu da ƙiyayya. Allah ne ke jarabtarka da su. Idan ka shiryawa mahaifinka, Allah zai ƙara maka daraja da nutsuwa." Cikin minti ɗaya idon Bashari ya sauya launi. Yayi shiru, ya janye jikinsa daga nawa, ya tura ni ɗan gefe, yana kallona kamar wanda aka faɗa masa aljani na jikinsa. Na juyo na kalleshi sosai, cikin murmushi da kauna na matsa kusa dashi "Na san ka ji rauni. Amma ka bari Allah ya saka maka. Ka yafe musu. Idan kai ba ka saka alkhairi a cikin alkhairi ba, wa zai yi? Ka shirya da mahaifinka, don nima zanyi farin ciki, na ga gidanmu yana cike da zaman lafiya da albarka."

Sai kawai ya zare ido ya kalle ni, ya rungume ni da ƙarfi sosai kamar yana son saka zuciyata cikin nashi. Ya ce cikin wani muryar kuka "Wallahi na rasa yadda zanyi dake. Ina jin ki fiye da kaina. Amma duk lokacin da kika roƙi abu, sai naji zuciyata na sarƙa... saboda ina ƙaunarki. Idan hakan zai faranta miki rai, zan koma gida, zan ba mahaifina hakuri."

Bashari…Na kira sunansa a hankali, kamar wata ƙaramar murya da ke so ta sulale daga cikin zuciya. Ya lumshe ido, yana jiyo ni. Na ɗan ɗago kaina, ina kallon fuskarsa da hasken fitila ke haskawa daga gefe.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull