Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 47
Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 47: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 47. Na ƙara matsowa jikinsa, na ɗora kaina a…
3,364 words
Na ƙara matsowa jikinsa, na ɗora kaina a kirjin sa kamar wata yarinya da take so ta sa masoyinta ya natsu, ya fahimci komai daga bugun zuciyata. Bansan yadda nake jin kaina ba, amma zuciyata tana cike da wani abu mai nauyi, kuma sai ya fita ne zan iya sauke shi.
Na ɗago kaina a hankali, na kalle shi da ido cike da damuwa da ƙauna. Na kama tafin hannunsa na saka cikin nane, ina shafawa a hankali kamar wacce ke lallashin ɗanta da zuciya guda.
"Bashari...", na kira sunansa da siririyar murya, "ka sani kuwa cewa idan akwai wani wanda zai fi dacewa da ƙaunarka bayan ni... to mahaifinka ne."
Ya kalle ni da mamaki, kamar wanda kalmomi suka bige shi da kasko. Na sauke numfashi da taushi na cigaba "Ban san abunda ya faru tsakaninku ba sosai, amma ina tunanin cewa idan har Allah ya zaba maka shi a matsayin uba, to akwai dalili. Kuma Allah ya riga ya umurta mu mu kyautata musu." Na ɗan shige jikinsa, ina shafa wuyansa da yatsuna a hankali kamar wacce ke rarrashi. "Kaji irin wannan ayar, Bashari... Allah yace: 'Wa qadha Rabbuka alla ta’budu illa iyyah, wa bil-walidayni ihsana…' (Isra’i: 23), ma’ana Ubangijinka ya umurce ka kada ka bauta wa kowa sai Shi, kuma ka kyautata wa iyayenka."
"Wallahi Bashari, hakan yana cike da darasi da fa’ida. Allah bai ce kayi su daidai ba, ya ce ka kyautata musu." Na janyo hannunsa, na dora a fuskata ina dan dariya. "Ko da mahaifinka ya maka wani abu mara daɗi, ka kyautata masa saboda kai namiji ne mai daraja. Kuma ina son mijina ya zama nagari har cikin halayen sa." Na tsaya ɗan shiru na kalli fuskarsa, sai na ɗora "Ka sani, Manzon Allah (SAW) ya ce: 'Uban naka shine tsakiyar ƙofa daga cikin ƙofofin Aljanna. Idan kana so ka kiyaye, ka kiyaye; idan kuma kana so ka lalata, ka lalata.'" "Kai ne masoyina... amma masoyina da ba ya daraja uba, wallahi wani bangare na zuciyata ba zai natsu ba."
Na ɗan motsa jikina zuwa kusa da shi, ina shafa ƙirjinsa da kauna. "Bashari, zan so na ga ranar da zaka riƙe mahaifinka da hannu, ka ce masa 'Baba na yafe Ni zan kasance a bayanka, zan farka da kai da safe in ga ka ce masa 'Ina kwana Baba', da dare ka ce masa 'Allah ya tsare ka Baba'. Wannan itace soyayyar da nake mafarkin gani a cikin mijina." Na shaƙi ƙamshinsa, na ƙara shige jikinsa sosai, numfashina yana gauraye da nasa, sai na rada masa "Idan kana sona da gaske, Bashari... to faranta ran mahaifinka. Ni kuma zan kara zaburce maka da addu’a da kauna... har sai ka zama gwarzon mijin da nake mafarki.”
Ina cikin rungumarsa, har yanzu hannu na na sanye a kan kirjinsa ina jin dukan zuciyarsa kamar ana buga tambarin “na yarda da ke” a cikin jinin sa. Kallon da yake min tamkar wanda zuciyarsa ta sake sabuwar bude, kamar ya sake ganina da wani idon daban na ƙauna, na girmamawa, na nutsuwa.
Yayi ajiyar zuciya mai nauyi, yana fidda wani salo na daɗi da kwantar da hankali da har saina lumshe ido. Sai naji ya kamo fuskata da hannayensa masu ɗumi, yana kallona tamkar ya rasa furuci. “Ƴar kwalisa... wallahi naji kamar zuciyata an shayar da zuma... Wannan kalamanki sun motsa wani abu da ban taɓa jin irinsa ba.”
Ya kankameni sosai cikin ƙauna, yana shafa bayana da siririyar yatsarsa, kamar yana ƙoƙarin rubuta sunana a kowane tsoka dake jikina. Sai ya rada min a kunnena da wata murya mai raɗaɗi "Zan je... zan je Ramlah... Zan je nasamesa. Zan ce masa, 'Baba ka yafe min, na dawo matsayin ɗa da ka haifa, ba ɗa da zuciya ba.' Kuma wallahi, babu wanda ya motsa ni irin yadda kika motsa ni yanzu."
Yayi min kiss a gefen kumatu da laushi, sannan ya furta "Kece kyautar Allah yabani da ban cancanta ba, amma ya bani. Zan faranta miki… zan nuna miki cewa akwai soyayyar da zata iya gyara namiji, kuma ke kika kawo min hakan.”
Na dan matsa jikina kusa dashi har bugun zuciyarsa ke busa kunnuwana. Na ɗora yatsana a leɓensa na ƙasa ina jan shi a hankali, na shafa gemunsa da ɗan murɗa kai, sai na ce “Zan so inji kalmar nan daga bakin ka… cewar zaka faranta ran mahaifinka saboda ni.”
Yayi dariya mai laushi, kamar wanda aka taɓa wani ɓangare mai taushi a zuciyarsa, sai ya kama hannuna, yana shafa shi a hankali kamar yana tsarkake shi da zuciyarsa, sannan ya ce "Wallahi Ramlah, inajin so na kaunarki har tsoka ta … Kuma zan yi komai da ke sa ki farin ciki. Gobe zan je in gaishe da Baba. Ince masa na tuba.
Ya jawoni har cinyata ta zauna a kansa, sai na ji hannunsa yana shigowa bayana yana shafa saman kugu na da salo, yana sake rada
“Kuma saboda ke... zan kasance mafi kyau, mafi cancanta, mafi daraja... in da ke ke gefena kamar haka.”
Sai na sake narke masa a jiki, inajin laushin sa a kowanne numfashi, jikina na amsawa da girgiza da sauyin zafin da ƙauna ke haifarwa daɗi mai ƙona zuciya cikin nishadi.
Na kasa rike numfashina lokacin da Naji ya zura hannunsa cikin rigata, yatsunsa na lilo cikin sanyin fata kamar yana karanta sirrina. Ya kai hannunsa zuwa kirjina, yana shafa shi cikin yanayi mai cike da natsuwa amma da karfi da kwazo, har zuciyata ta fara bugawa fiye da kima. Na dan tashi da sauri, amma kafin na iya ficewa gaba daya, ya jawoni jikinsa, bakinsa ya sauka a kan nawa sanyi da zafi suna karawa juna karfi.
“Dan Allah ka daina,” na furta cikin kuka mai sanyi, zuciyata na tafasa da rudani da tsoro. Amma muryarsa ta fito da sanyi amma kuma da cikakken iko.
“Babu abinda zan miki… taɓawa ce kawai,” ya ce, idonsa na kallona da wata irin murya da take haduwa da laushi da tsauri.
Jikina na rawa, kamar na rasa ikon kaina. A karshe dai na mike, na tsere zuwa bandaki, inda na yi tsarki da alwalaina bukatar nutsuwa, wani abu mai tsarki da zai mayar da ni cikin kwanciyar hankali. Bayan haka, na koma na kwanta, jikina har yanzu cike da rawar tsoro da rudani.
Ina jin motsinsa daga dakin wanka, kafin daga bisani ya tada sallah da natsuwa. Ban san lokacin da bacci ya kwashe ni ba. Amma zuciyata bata kwanta ba.
*****************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA CASA'IN DA BIYU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Washegari...
Tun kafin na farka, Bashari ya fita. Shi mutum ne da baya son takurawa kowa, musamman idan yana bacci. Ko da yaushe yana ce min
“Ƴar kwalisa, bana son tashin ki daga bacci. In Allah ya kaimu lafiya, zan dawo kafin ki farka.” Wannan halayensa ne ke sa na ƙara son shi kullum. Da na buɗe idona, zuciyata cike da natsuwa da farin ciki. Na tashi hankali kwance, na fara gyara gida kamar yadda na saba. Na wanke pant ɗina da bra ɗita, na shimfiɗa zanin gadonmu da kyau, sannan na fesa turaren da Bashari ke sawa mai ɗaukar hankali da ƙamshi mai dadi.
Yau kuma, wata irin sha’awar wainar fulawa ce ta taso min. Tunanina yana can kan yadda zanyi masa wainar ga wani missing din bashari da nakeyi ji nake duk wani iri wani mugun sabo nayi Dashi da nakejin wani mugun nishadi aduk lokacin dana gansa kusa dani.
Na shiga kitchen da natsuwa, na ɗauko kayan fulawa, na sa ruwa, na jajjaga albasa da ɗan barkono, na dora mai, sannan na shiga soyawa. Yayin da wainar ke yanda a cikin kasko, zuciyata na yawo a cikin soyayya da ƙaunar mijina.
Na san yana daɗa ƙaunata saboda kulawa, kamar yadda ni ma ina ƙaunarsa saboda ƙoƙarinsa da halayensa masu laushi. Kukawar da yake bani sai naji kamar ba'a taɓa bani irinta ba acikin rayuwata Ina cikin suya a wajen kitchen din, ƙamshin wainar fulawa yana cika gurin, sai na ji an turo ƙofa da salo. Uwani ce ta shigo tare da ita da wata. Muka gaisa da murmushi, na ɗauko musu tabarma suka zauna. Matar ta karɓi ɗaya daga cikin suyar da nake yi, tana ɗan ci da murmushi. Haka muka ci gaba da hira, uwani na fadin“Wallahi kin kyauta. Wannan wainar fa kamar ana soya ta a gidajen masu kuɗi.”
Na murmusa, nace “Ai saboda me Baza'a soya acan ba?.”
Yayin da muke hira, sai Uwani ta soma zagin Babah akan abin da ta yi mini jiya. Na dakatar da ita cikin ladabi “Ki bar ta Uwani, ai ya huce. Allah ya kiyaye gaba. Ni na yafemata.”
Sai Uwani ta ce “To shikenan. Dama yanzu nake son gaya miki wani labari. Wannan yarinyar dai diyar yayata ce. Tana fama da matsanancin sanyi ajiki. Hatta gabanta har wani wari da doyi ke fita, sai ki ce wata cuta.”
Idanuna suka kalleta zuciyata ta dan duka. Saboda wannan matsalar itace nake fama da ita nima tun kamin aure Na ce da ita cikin dan damuwa “To Uwani... ya maganin? Ya yi mata magani kuwa?” Sai Uwani ta ɗan murmusa ta ce “Kai matar Bashari! Maganin kuwa? Ai mai maganin da taje wajensa yanada magunguna masu kyau sosai. Cikin kwana biyu kacal sai da nake ta mamaki. Kurajen suka bushe, wari ya daina, ita kanta tana cewa bata taɓa jin jikinta yana da ɗanɗano kamar yanzu ba!”
Nace da sauri “DanAllah Uwani, idan kina da jerin magungunan, ki nuna min. Wallahi ni kaina ina da irin wannan matsalar. Kuma tun farko ban san inda zan nema ba.”
Sai Uwani ta ce “Ke bari in huta tukunna, daga baya zanje gurin shi , zan kawo miki kayan maganin da ya haɗa mata da sunayensu da yadda ake amfani da su.”
Na lumshe ido ina murmushi. Na ji kamar wata kafa ce aka cire daga zuciyata.“Allah ya saka da alheri Uwani. Wallahi wannan maganar naji dadinta Uwani ta kalli yarinyar, ta ce "Lantana, ko kin rike magungunan?"
Lantana ta dan murmusa, ta matsa kusa da ni cikin natsuwa, tana kallona da tausayi. Sai ta ce da murya mai sanyi
"Matar Bashari, bari na gaya miki hadin maganin da malam ya bani. Na sha shi tsawon kwanaki bakwai, wallahi ko wari bai saura ba. Na zaro ido ina sauraron ta da kulawa. Ta cigaba"Ga yadda ake hadawa:"
1. Ganyen magarya a tafasa da ruwa, ana zauna acikinsa safe da yamma. Yana kashe cututtuka masu wari a gaba da fatar jiki.
2. Kaninfari, na’a-na’a da habbatus-sauda a niƙa su gari a ajiye. Duk rana sai a ɗebo karamin cokali a zuba cikin ruwa mai dumi, a zauna a kai ko a shafa a gaba bayan wanka.
3. Zuma da garin kaninfari – a haɗa cokali biyu na zuma da cokali daya na garin cloves, ana shan karamin cokali safe da dare. Yana gyara ni’ima da ƙamshin jiki.
Lantana ta kammala tana kallona da murmushi "Ki fara da wannan hadin, matar Bashari. Wallahi, za ki ji bambanci cikin kwanaki kaɗan. Sai ki ci gaba da addu’a da tsafta." Na kama hannunta da godiya, zuciyata cike da fatan samun sauƙi. Uwani ta ce "Shi yasa nace ki saurari wannan yarinyar. Tayi ta fama, amma yanzu kam Sai sauki take samu. Kema zaki samu insha Allah.”
Ta murmusa, ta ce "Bakomai matar Bashari. Allah ya baki lafiya, ya baki lafiya ta jiki da ta zuciya." Suka tashi tare da Uwani suka yi min sallama suka tafi. Ni kuma na ja mayafina na nufi karamar kasuwar kauyen Allah ya taimakeni masu kasuwar yamma suna cj Yayin da nake tafiya, ina lura da yadda mutane ke kallona sai kace na fito daga wani waje na daban. Gani-gani kamar kallon tsana suke min, amma ban damu ba. Na sani abinda nake nema ya fi muhimmanci.
Na shiga kasuwa cikin nutsuwa, na siya duka abubuwan da Lantana ta ce a hada ganyen magarya, kaninfari, na’a-na’a, habbatus-sauda, zuma, da sauran kayan hadin. Nayi gaggawar dawowa gida.
Da na isa, ban bata lokaci ba. Na dora ruwan da za a tafasa, kamar yadda ta ce. Sai na fara shirin yin tururuka da ganyen magarya da sauran kayan hadi.
Na shirya wanda za a sha, kamar yadda aka koya min. Na hada, na fara sha daidai lokacin da rana ta fara faduwa. Na ce a zuciyata
"Yau ne ranar farko, insha Allah zan ga canji.”
Bayan sallar magariba, sai kawai na ji ana bugun ƙofa. Na tashi cikin gaggawa, na je na buɗe. Mamaki ya kama ni ganin Baban Bashari ne tsaye a ƙofar. Cikin murna da girmamawa, na ce
"Baba sannu da zuwa, maraba da zuwa. Mushiga ciki dan Allah."
Sai ya ce
"A’a, nan ma ya isa."
Nace masa da lallashi
"Baba, dan Allah mushiga. Ba abin tsayawa a waje bane."
Ya dan yi murmushi, ya zuba ido ga mutane dake kallon mu, sannan ya amince ya shigo har cikin palonmu. Na kawo masa ruwa da abinci, ya zauna ya ci cikin nutsuwa.
Bayan ya gama, sai ya ce
"Sannu diyar kirki. Allah ya saka da alheri. Tabbas kin haihu. Wallahi da safe sai ga Bashari a gabana, Kuka har ya kwace min. Ya bani Murtala talatin (₦30,000), yace in rike har gobe. Nagode wallahi, Allah yayi miki albarka."
Kafin ya gama maganar, sai ga sallamar Bashari daga ƙofa. Na karɓi ledar hannunsa kaza da kwai ne ciki. Amma da ya hango baban nasa, sai na ga yayi turus ya tsaya cak. Na ce masa cikin murmushi
"Bashari, Baba yazo. Wallahi naji dadin ganin ku tare."
Abin mamaki, Bashari ya durƙusa har ƙasa, yana gaishe da mahaifinsa da cikakken girmamawa. Baban kuwa sai murmushi kawai yakeyi, yana fadin
"Kai… tsakanin ɗa da uba sai Allah. Allah ya amsa."
Bashari yace "In cire mai kaza ɗaya da kwai goma daga cikin wannan."
Na ce "To ," na cire masa, na sanya a leda.
Ya dinga godiya yana cewe"Allah ya saka da alheri. Allah ya albarkace ku."
Ya mike zai tafi, nacewa Bashari "Yaraka Baba har gida mana."
Bashari ya amsa da girmamawa, suka fita tare suna hira. Na leƙa ta window, ina kallon yadda mutane ke mamaki da ganin sabuwar alaka ta farfadowa tsakanin uba da ɗansa. Gaskiya, Allah ne kadai mai juyar da al’amura.
Ni kuma da na rufe ƙofa, sai na yi sauri na shiga wanka na tsarkake jikina. Bayan na fito, na shafa turare mai daɗi, na gyara kaina sosai. Cikin dan lokaci, sai ga Bashari ya dawo, shi ma yayi wanka, ya zauna yana cin abincin da na dafa masa.
Bayan ya gama, sai ya matsa kusa da ni, ya ce"Ƴar kwalisata..." ya faɗa yana dora kansa a cinyata cikin laushi.
Ni kuma na shiga shafa fuskarsa a hankali, ina kallon sa da kauna. Sai ya ce"Kin san dai inata sintirin birni kwanakin nan ko? Amma wallahi akwai wani abu da nakeyi ne mai muhimmanci. Kina so ki koma birni?"
Na kalleshi da mamaki, nace
"Me ya sa zaka ce haka? Nifa ban raina inda nake ba."
Ya yi murmushi yana dariya, ya ce
"Ai ba sai kin faɗa ba. Kin yi sadaukarwa sosai. Matata ce wacce tayi rayuwa a birni, cikin jin daɗi, a gidan masu kuɗi, amma an kawoki nan ƙauye. Kin zauna lafiya da haƙuri. Ban san me zan saka miki da shi ba sai dai na roƙa miki Aljannah duniya da lahira."
Na ce masa da tausasawa
"Dan Allah Bashari, kada ka takura wa kanka. Wallahi ban taɓa cewa bana so nan ba, kuma ba na yin ƙorafi. Kabarmu a haka"
Yayi nisa cikin tunani, sannan ya tashi zaune, yana cewa
"Ai na gama komai. Na siyo wani ƙaramin gida, ya fi wannan girma. Yana da ɗakuna guda huɗu, bandaki biyu da kuma kitchen. Nayi gyara sosai. Shine nake yawan fita, dan aikin gyaransa nake duba. Kin ga idan Allah ya bamu haihuwa, wannan gidan yayi mana kaɗan ƴar kwalisa."
Ya kama hannuna a hankali ya ce
"Kuma ina so ki cigaba da makarantarki. Shi yasa gobe, mota zata zo ta fara kwashe kayanmu. Mu kuma sai mu dauki hanya bayan la’asar, ko kin yadda?"
Ban iya cewa komai ba. Sai kawai na rungume shi da ƙarfi cikin tsananin jin daɗi da kauna. Sai ya ce da murmushi
"Tashi muje mu kwanta, gobe zan siyar da itacena da wuri in fita."
*****************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA CASA'IN DA UKU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Na kwanta akan gadon cikin natsuwa, fuskata cike da gajiyar rana. Na juya jikina gefe ɗaya, zuciyata na dukan a hankali. Sai kawai na lumshe ido, addu’a a zuciya “Ya Allah, ka bani nutsuwa, ka yaye mini damuwa. Ka ƙarfafa zuciyata da jiki.” Bacci yana kokarin daukana. Amma kafin na nutsa sosai, naji kamar an ɗaga bargon da ke kaina a hankali. Cikin zafin nama naji wani jiki mai dumi ya rungume ni daga baya. Numfashinsa na bugun wuyana, hannunsa na tafiya a sannu akan cikina. Nayi ƙoƙarin juya kaina, sai kawai na ci karo da idanunsa.
Yana kallo na kamar wani masoyin da ya rasa nutsuwa. “Ƴar Aljannata… jikina yana bukatarki. Dakyar nake daurewa. Sha’awa tana son ta haukatani, shiyasa nadawo da wuri.”
Yayi magana da wata irin murya mai laushi amma mai zafi. Muryar da take motsa ruhi fiye da kalmomi. Kafin na iya cewa komai, ya aza bakinsa bisa nawa. Ya shiga sumbata ba da gaggawa ba ba da hatsaniya ba da kyau da natsuwa kamar yana karanta litattafai akan leɓuna.
Hannunsa ya shiga tafiya akan jikina kamar yana neman hanyarsa ta gida. Ban san lokacin da na saki ƙaramar ajiyar zuciya ba. Sai naji dukan zuciyata ya fara canzawa daga tsoro zuwa shauƙi. Na ce masa a shagwabe
“Ni banida lafiya fa…”
Ya dan lumshe ido, sannan ya murmusa da wata murya da ba ta da ƙarfi sai dai motsa zuciya
“To ai idan nayi magani zan baki.”
Kafin na gama fahimtar kalmarsa, ya zame ni gaba daya daga bargon. Ya shige jikina da qarfi amma cike da taushin ƙauna. Yana sake sumbata, yana sauke wani irin numfashi mai zafi irin wanda ke shigowa da fitar da zuciya. Na fara jin kaina yana dushewa a wani yanayi da ban saba ba.
Na shiga turashi da ƙarfin da ban da shi. Na ce da raɗa “Ni kabari... please...”
Sai kawai ya saki dariyar da ba karfi.
“To idan kika san daɗi kamar na sani... bazaki roƙi in tsaya ba.”
Yayi magana yana kallona da wani irin salon da ke sa zuciyata takan shaƙe. Kamar yadda yatsunsa ke tafiya a jikina, shima zuciyarsa ke tafiya cikin tawa. Sai kawai naji jikina ya kasa hana shi ba dan na yarda ba, sai dan ni kaina ina buƙata.
Yayi wani irin kallo da ba komai ke ciki ba sai so da shauƙi.
“Wallahi duk na zabure… ataimaka mun... in shiga gonata ƙinji...”
Gonarsa? Nayi shiru. Amma jiki ya ci gaba da amsawa. Kasa da zuciya na ya shiga girgiza da wani irin farin ciki mai cike da azaba. Hannunsa ya shiga zame rigata da kyau, yana kallon kowanne inci na fatata kamar an zana ta domin sa kadai.
Na ji wani irin dadi ya mamaye ni tun daga ƙafata har tsakiyar kaina. Na juyo da ƙarfi na rungume shi, kamar na rasa kaina. Na ce Ni banaso cikin wani irin ƙarfi mai rauni
Sai yace “Ni... inaso...”
Yayi murmushi yana kankameni.
“Sai a sabon gidanmu...”
Na shiga jikinsa, ya sauke ni akan gadon, ya shiga lullube ni da soyayya. Sumbatunsa, kalamansa, da lallabansa sun zame min kamar addu’a ba ni da ƙarfin karɓa, sai karɓar so. Kamar rayuwa ta tsaya, sai ni da shi.
Numfashinsa yana bugun kirjina. Hannuwansa suna riƙe jikina kamar wani abu mai daraja. Idanunsa cikin nawa, kamar yana karanta tunanina.