Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 48
Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 48: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 48. “Ƴar Aljannata… Duk kin riketa ni idan na…
3,372 words
“Ƴar Aljannata… Duk kin riketa ni idan na taɓa wannan kirjin naki dadin danaji bazai taɓa misaltuwa ba.”
Ban iya cewa komai ba, sai in tsaya ina jin yadda ya lullube ni da so.
Washegari da sassafe, Bashari ya ce min zai fita saboda yana da wasu muhimman abubuwan da zai kammala. Na ce masa, “Allah ya kiyaye hanya, ya kuma dawo da kai lafiya,” cikin kulawa da addu’a.
Bayan ya fita, sai ga shi ya dawo cikin hanzari. Na ce masa, “Ka manta wani abu ne?” Ina kallonsa na tuna hulata tana kan kujerar falon, nace masa “Gatanan, na aje maka.” Sai ya saki murmushi, ya kafe ni da idanuwansa na soyayya, bai ce komai ba sai ya fita.
Cikin daddafe na cigaba da aikin gida, domin marata na min ciwo sosai ba ƙaramin zafi nakeji ba. Na kasa fahimta ko period dina ne ko wani abu daban, duba da cewa wannan farkon watan ne, ba lokacin al'ada ba.
Ba a jima ba, sai ga Bashari ya dawo. Nace masa, “Zan haɗa kujerun nan ne da kayan kicin?”
Sai ya ce “A'a Ramlah, kada ki damu. Gidan da komai da ke cikinsa zan bar wa mahaifina. Wannan gidan, duka, mallakinsa ne.”
Wani matsanancin farin ciki ne ya lullube ni. Na kalleshi da ido cike da soyayya nace masa, “Da gaske kake? Mungode! Allah ya saka maka da alheri mijina.” Nayi masa kallon da nake da tabbacin ko zuciyar dutse zai ji daɗi.
Sai kawai ya zo kusa dani, ya rungume ni da ƙarfi kamar wani abu zai kwace ni daga gare shi. Yana ajiyar zuciya mai nauyi ya ce
“Ban son rabuwa dake Ramlah… Wallahi ban so. Kowanne lokaci da nake tare da ke, nakan ji kamar wata rana za a raba ni da ke. Kuma hakan na daɗa saka min tsoro.”
Sai na ture shi a hankali nace masa, “Don Allah kayi hakuri, jikina fa wani iri nakeji. Karka dameni da wani abu yanzu.”
Sai yayi dariya yana raɗa min a kunne da wata murya mai sanyi
“… ashe ana sona haka?”
Na kalleshi da murmushi, zuciyata na ɗauke da natsuwa da soyayya, batare da wani shakkar zuciya ba. Sai na zuba masa abincin da nayi, muka zauna muka ci tare yanata kallona nima ina kallonsa.
Bashari ya kalli fuskata cike da natsuwa sannan ya ce,
“Ramlah, ki je ki yi wa su Babah da Uwani sallama. Motar haya zamu hau, na siyar da tawa motar, kuma abokin aikina zai tafi mana da kayanmu tashi.”
Nace masa, “To, bari na saka hijjabina,” cikin sauri na nufi ɗakin. Wallahi dole bawa yaji tsoron Allah idan naga yadda bashari yacanza yake bin dokakin Allah abun har tsoro yake bani da mamaki.
Da na je gidan Babah sai aka ce min ba ta nan, don haka na wuce gidan Uwani. Da na shiga, muka yi gaisuwa cikin annashuwa. Uwani ta dubeni tana murmushi, tace
“Kai Ramlah! Lafiya? Ashe an samu karuwa ne? Naga kin ƙara kiba sosai.”
Sai na fashe da dariya nace, “Zamu koma birni ne, shine nazo sallama.”
Uwani ta kalli ta, tana kama hannuna da kulawa tace
“Kai amaryar Bashari, zan yi kewarki wallahi. Idan na zo birni zan ganki ko?”
Nace mata cikin murmushi da kwanciyar hankali
“Inshaa Allahu Uwani. Allah ya kiyaye hanya. Idan na haihu zan turo muku sakon albishir.”
Ta ce “To shikenan, Allah ya tabbatar da alheri.”
Nace mata “Ameen,” sannan na juya na fice daga gidan, zuciyata cike da farin ciki da Annashuwa
.
Yana cikin daki yana da tasbihi, yana maimaita "Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un... Ya Allah ka karɓi rayuwata cikin alheri, ka sa na tafi da kwanciyar hankali..."
Na tsaya a bakin kofa, zuciyata na wani irin bugawa, kamar akwai sako da raina ke kokarin karantawa amma ban iya furta shi ba. Na kalli fuskarsa, da fuskar mai nutsuwa. Ya daina rigima. Ya daina yawan magana. Yana murmushi da kyar idan nayi masa dariya. Kuma yafi kowa yawan hakuri yanzu.
“Bashari, yaushe zakazo daga birnin idan muka tafi gobe?” na tambaya cikin sanyi.
Ya juyo, ya kalle ni da wata fuska mai annashuwa. Ya ce
“Ni kuma? Ramlah, bazan ƙara dawowa kauyen nan ba, sai dai wani dalili ya dawo da ni.”
Na dan harareshi nace
“Kai? Me kake nufi? Baba fa?”
Sai ya juyo yana kallona da idanu.
“Au… Baba. Wallahi Ramlah, na manta da komai. Kamar duk wannan rayuwar nan babu komai a cikinta sai Allah.”
Na tsaya cak.
Sai ya kara cewa,
“Kidinga yimun Addu'a , ki roki Allah yafeni. Banason tuna rayuwata ta baya banaso ko kadan.”
Bayan ya gama faɗin waɗancan maganganun masu taɓa zuciya, sai ya fito da duk kayanmu ya saka su a cikin bakko, da akwatina a gefe. Ya fice da su ina zaune a bakin ƙofa, ina masa sannu Bai jima da fita ba, sai ga mahaifinsa Baba —ya shigo da sallama. Muka zauna duka a kan kujera. Na gaishe shi cikin ladabi, ya amsa cikin fara’a.
“Yar albarka,” in ji Baba, “Ashe Allah yayi, birni zaku koma?”
Na gyada kai cikin ladabi nace, “Eh Baba, dazu yake sanar dani.”
Baba ya ce, “Masha Allah! Hakan yayi kyau. Bashari, ga amana nan a hannunka yarinyar nan ka riƙeta da hannu bibbiyu, kuma ka kula daita da addu’a da fatan alheri. Don Allah ka kula da ita, ka tsaya mata a komai. Duk wani abu da kayi min tun daga farkon rayuwarka har zuwa yau na yafemaka. Allah yayi maka albarka.”
Nan take muka ji shashshekar Bashari, yana fashewa da kuka kamar yaro.
“Baba, dan Allah ka yafemun. Ban kasance ɗa nagari ba. Amma ina fatan Allah zai karɓi tuba na. Ka yafemun, Baba!”
Sai Baba ya kamo hannunsa yana cewa, “Na yafemaka, Bashari. Allah yayi maka albarka. Ya baka yara nagari. Ke kuma, diyata,” ya juyo gare ni, “Allah ya miki albarka. Ku zauna lafiya. Kuyi hakuri da junanku.”
Bashari ya miƙe yana share hawayensa.
“Ku zo mu tafi,” ya ce, “zan rakaku har wajen mota.”
Sai bashari ya ce, “A’a, dan Allah. Kada ka wahala. Zamu karasa dakanmu baba.”
Bashari ya ciro mukullin gidan ya miƙa masa. “Ga mukullin gidan nan, Baba. Na bar muka Wannan gida ba zai ƙara zama nawa ba.”
Sai kuwa Baba ya fashe da kuka, cikin kukan da ke fitowa daga zurfin rai..
*****************
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA CASA'IN DA HUDU
Wannan littafin kuɗi ne, ba kyauta ba!
Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama!
Domin biyan kuɗi:
Acc Name: Bilkisu Sani Kaura
Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp:
09030569336 ko 07040402435
Masu son vip 👇Sai ku bibiyeni a
Arewabook @nanadiso10
https://www.arewabook,vs.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********
Nashiga ɗaki zan canza kaya. Bashari ya biyo ni cikin nutsuwa ya tsaya yana kallona kamar ba zai ƙara ganina ba. Na juyo daidai lokacin da na cire rigar da ke jikina, yana kallona da wani irin so da tausayi da babu kalma da zata misalta shi. Idanunsa sun cika da abu mai nauyi kamar wutar zuciya da ke cin ƙwalwarsa a hankali.
Batare da ya ce komai ba, sai kawai ya rungume ni da ƙarfi. Ya lumshe idonsa yana maida numfashi cikin kaina. A hankali ya fara sumbatar wuyana... sai kumatuna… sannan kirjina. Gaba ɗaya jikina ya ɗauki rawa, marata ta kulle, zuciyata ta karaya. Na kasa tureshi, sai dai naji wani sabon nau’i na kauna da tsoro sun mamaye raina. Na shige jikinsa kamar ƙananan yara da suka rasa mafita a duniya.
A hankali sai ya saki numfashi, ya zare jikinsa daga nawa, ya ce da wata murya da ta soma rawa “Allah ya yi miki albarka, matata. Bari mu tafi, kinga ƙarfe huɗu har ya wuce. Kada mu yi dare. Hanyar nan ba lafiya ce ba akwai ruwan da zamu tsallake, saboda daya daga cikin hanyoyin an ce wajen masu garkuwa da mutane ne.”
Na gyada masa kai, amma ina jin wani abu yana niyya a ƙasan zuciyata. Mun kulle gidan, muka yi sallama da waɗanda ya kamata. Amma cikin zuciyata… na kasa rabuwa dashi.
Cikin hawayen da suka cika min idanu, na rungume shi sosai. Na fashe da kuka
“Bashari… Wallahi, idan na kalleka yanzu, sai naga kamar ba kai ne ɗan daba ba… kamar ba kai ne wanda na sha kuka a dalilinka ba. Ka canza... da gaske ka canza.”
Ya dafe bayana yana rarrashina da wata murya mai rauni “Ki daina kuka, don Allah. Kada ki sa in kasa tafiya… Ki tuna hanyar nan bata da kyau.”
Sai na shiga jikinsa, na ɗora kaina a kirjinsa. Na ce “Ina ƙaunarka, Bashari… Wallahi, ina jin ka har a jinina. Inace na tsani ka a baya, amma yanzu… na gane cewa babu wanda ke sona kamar yadda kake ƙoƙarin dani.”
Ya ɗago fuskata yana kallona. Idanunsa sun cika da hawaye. Bai ce komai ba, sai ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Na rungume shi sosai. Ramlah "In shaa Allahu, ke yar Aljanna ce Yayi murmushi ya ce "Mu je ko, munada tafiya."
Sai muka hau mashin muka nufi tashar motoci. Can muka iske hayaniya, jama'a na lodi kamar yadda aka saba. Lokaci ne na rana, rana na ɗan dumama. Muka tsaya a gefe, sai Bashari ya ce “Mota uku zamu hau kafin mu isa birni. Ta farko awa ɗaya ce, ta biyu haka, sai ta uku kusan awa uku za mu sha.”
Nace da sallama: "Allah ya kaimu lafiya."
Muka shiga motar. Ni na zauna kusa dashi. Sai ya ce “Sanya kanki a cinyata mana ki huta, kin san baki saba ba kuma jikin naki yana bukatar hutu.”
Nace "To," cikin sanyin murya saboda jin ciwon mara da kasala a jiki. Ina jin kamar tsokata ta daina ƙarfi. Na kwanta, na danne kaina cikin cinyarsa kamar ƙaramin yaro da ya samu kulawa. Na yi bacci sosai. A lokacin da na buɗe idanuwa, naga yana kallona yana murmushi. Nace da ƙanƙanin murya, ina tsokanar sa “Kai Bashari, me kake min kallon fari fari haka? Wallahi sai naga kamar kayi fari… Sai yayi dariya ya ce “Ke kika shafamin farin fa, ina namiji, ina shafe-shafe ƴar kwalisa?” Nace masa cikin shagwaɓa "To ni yunwa nake ji," ina turo baki kamar karamar yarinya.Yan motar sun soma kallon mu kamar muna fim a gaban su. Bashari ya kama dariya. Sai ya ce “Gashi nan,” ya miko min leda. Na buɗe ledar, sai naga gurasa ce mai ɗan ɗumi. Na fara ci cikin jin daɗi, sannan ya bani ruwa na sha. Nace “Kai fa? Ka ci?” Ya ce "Na koshi tuni, ai kin fi buƙata." Nace masa "Kasha ruwa dan Allah." Ya ce: "Na koshi."
Mun cigaba da tafiya har muka isa wurin sauka. Sai muka sauka muka koma jirar wata mota, itama tafiyarta na kusan awa ɗaya kenan. Jikina ya soma yin sanyi saboda yawan bacci da gajiya.
"Bashari, wai ba zaka ci komai ba?" Na tambaye shi cikin murya mai rauni da kulawa. Sai ya ja hancina yana murmushi, yace "Na koshi ƴar kwalisa. Ai da zanci, da kin gani naci. Kinsan bana wasa da abinci. Kinga danwake nan a tasha? Bari na siya miki, kinji?" Na gyada masa kai cikin jin daɗi. Ina tsaye a gefe har ya tafi ya siyo danwake sannan ya dawo, muka yi sallah a cikin tashar cikin nutsuwa.
Bayan sallar, muka sake ɗaukar hanya. Daidai lokacin sallar isha’i ce, motar da muka shiga ta cika sosai mutum goma sha biyar (15) a cikin motar mai wuri bakwai! Sai na jingina kadan, ina kallon Bashari cikin kwanciyar hankali, ina ta masa surutu.
Ya kalli fuskata yana murmushi, sai yace “Ƴar kwalisa, bani ruwan nasha.” Na miƙa masa ruwan, ya sha sannan yace “Wallahi bacci nake ji sosai.” Nace: "To, ka dan kwanta." Sai ya jingina kansa a kafadata, yana kwanciya cikin kwanciyar hankali da natsuwa. Ya lumshe idonsa cikin sanyi, ina jin numfashinsa yana daidaita kamar baccin ƙaramin yaro.
Ni kuwa, saboda rashin damuwa, na buɗe wayata naci gaba da wasa da game ina satar kallonsa lokaci zuwa lokaci. Cikin zuciyata kuwa, ina addu'ar Allah ya kai mu lafiya, ya sa wannan tafiya ta zama albarka garemu duka.
Mun kusa shiga birni ne, bayan doguwar tafiya da muka sha. Lokacin dare ya fara sauka, iska na kadawa a cikin motar, jama’a duk sun gaji wasu na bacci, wasu suna ta kallon hanya da ido na kasala. Ni kuma, na jingina da Bashari, mijina, na lumshe ido ina jin ɗumin jikinsa yana lulluɓeni.
A cikin zuciyata, ina godiya. Godiya ga Allah da ya bani mijin da yanzu na fara ganin alherinsa, mijin da na tsana a baya, amma yanzu ina jin kamar na rasa shi, zuciyata zata tsaya.
Sai dai... rayuwa bata da tabbaci.
Kusan bayan awa guda da fara tafiya, mun kusa shiga cikin babban birnin. Sai na lura cewa direban yana ta gaggawa sosai. Muryar wasu fasinjoji na bayana naji suna faɗin
“Yallabai dan Allah rage gudu, ruwan sama ne fa, titi fa a dame yake...”
Direban dai kamar baisan da shawararsu ba, yana cigaba da bin titin kamar wanda wani abu ke masa tashi. Gabanmu akwai wata karamar gada da ke cike da ruwan da ke tsiyaya saboda kwalbatoci da suka toshe. Motar ke tafiya da gudu sosai har muka kusa shiga gadan, kwatsam sai muka ji ƙarar fashewar tayar baya "BAAAM!”
A yayin da motar ke shigowa cikin wani lankwaso mai hatsari, sai muka ji ƙara mai firgita. Taya ta fashe! Direba ya rasa daidaituwa. Motar ta fara karkarwa da ƙarfi, mutane suka fara ihun “Innalillahi!”
Na buɗe idona, kamar mafarki. Komai ya fara juya. Motar ta karkace gefen hanya sai wata ihu ta fito daga cikin motar. Cikin kankanin lokaci, muka ji motar ta kifa da ƙarfi ta gangara wani babban rami..
Gaba ɗaya jikinmu ya buge. Aka jiyo karar gilashi yana karyewa, karar ƙananan kaya da mutane suna raɗaɗi. Na daina jin motsin jikina.
wata mata ta rungume yaronta tana fadin “Wayyo Allahnaaa! Wayyo Allah ka taimake mu!”
Amma zuciyata bata mutu ba. Cikin hawaye, na kalli Bashari. Jikinsa na zubar da jini. Idonsa a rufe, numfashinsa ya ja sai kuma ya tsaya.
Bashari! Ka tashi! Ka daina wasa dani don Allah... don Allah kada ka barni... Bashari!!” Na dinga kiran sa kamar ƙaramar yarinya.
Na tuna komai da muka yi. Duk surutan da muka sha, duk kalmomin kauna, sai kuma yanzu... yanzu yana kwance a gefena kansa na zubda uban jini kafarsa tashige cikin motar, kamar wanda yake bacci amma zuciyata ta gaya min wannan ba bacci bane...
Sai dai kalaman da ya faɗa min a cikin motar kafin hatsarin sunci gaba da juyawa a cikin zuciyata. "Na tsani rabuwa dake Ramlah... banason mu rabu..." Ashe dama alamar barinsa kenan? Ashe dama zuciyarsa ta karanta wafatin nasa tun kafin ta faru?
Na tuna… Ya ce “Na gama da gidana, kuma na bar muku komai.” Ya ce “Na yafe wa mahaifina, kuma na ɗaura yarana bisa hanya.” Ya ce “Motar gidan zamu sayar. Na shirya.” Ya ce “Wannan tafiyar bazan sake dawowa kauyen ba.” Sai yanzu na fahimta... yana yin ban kwana ne da duniya.
Na fashe da kuka ina jujjuyawa da jini a jiki. Wani dattijo ya karaso yana cewa “innalilahi kuzo nan kuzo..
Na zuba idona kan mashin ɗin da ya tsaya, mutane sun fara taruwa.
“Don Allah ku taimaka mun! Ku ceto mijina! Bashari fa?”
Wasu na ji suna kara da muryar ban tsoro, kamar ana kwala kuka daga ƙarshen duniya.
“Jama'a ku zo! Ku zo ku ciro motar nan gaba ɗaya ta kife! Mutanen ciki kamar sun mutu!”
A nan ne jikina ya kara mutuwa da sanyi. Wani radadi mai ƙayatar da kwanya ya ratsani daga ƙafa har kai. Sai na ji wani zafi mai kama da wuta a gefen kafata. Ashe glass ɗin da ke kusa dani ne ya balla ya shige min gefe, yana zubar da jini a hankali.
Na furzar da kuka mai ƙarfi, har ma na kasa iya ware baki na sake kalma.
“Wayyo Allah... Bashari... na shiga uku...!”
Hawaye suna fita tamkar an kunna fanfo, amma zuciyata bata san inda take ba. Ina cikin wannan halin ne sai na ji murya daga nesa, wata mata na ihu cikin firgici tana fadin “Ga wata tana raye! Ga wata! Kuzo ku taimaka! Ga wata tana motsi wallahi tana raye!”
Mutane sun fara taruwa da sauri, wasu na kiran ‘yan sanda, wasu na kuka, wasu kuma suna ƙoƙarin cire murɗaɗɗen kofar motar.
A jikina kuwa, jini na yanda kamar ruwa ne, yana zuba ba tare da tsayawa ba. Kaina ya daina jurewa gani nake kamar haske yana rufe fuska ta, zuciyata tana karanta kalmar shahada a hankali.
Na kasa kiran sunan Bashari, amma zuciyata na ambatonsa. Idanuwana sun fara rufe kansu, numfashi ya fara yin rauni. Cikin wannan daɗin daɗaɗɗen ciwo, sai na ji wata murya ta ce “Ku ɗauketa yanzu! Tana raye! Allah dai ya ƙaddara rayuwa…”
A hankali, wasu suka ɗago ni, jiki na na malalewa kamar gawa da ta dawo numfashi kadan. Lokaci ɗaya kawai nake jin kukan wata karamar yarinya a cikin zuciyata, kamar muryar haihuwa da ban kai ba“Don Allah... Allah kada ka ɗauke min shi! Bai kamata ya tafi ba yanzu... Ya Allah, dan Annabi ka dawo mun da mijina!”
Cikin ƙara da rudani sai na ji wani tsoho yana ihun ban tausayi yana fadin “Allah yasa kafarta bata karye ba! Tashiga jikin kwanon namijin kusa da ita! Kansa ya fashe! Sai jini! Gaba ɗaya motar ta murɗe jikinsa! Ku kira Murtala! Ku kira shi yanzu! Ku zo ku ceto ita kadai ce da rai a ciki wallahi!”
Na kasa cewa komai. Na kasa motsawa. Jikina yayi sanyi kamar ba ni da rai. Komai ya tsaya. Kamar ba numfashi. Kamar babu fata. Kamar duk abinda na sani a rayuwa ya gushe daga zuciyata.
Ina jikin mutumin da yake gefena idona na ganemun kamar bashari Amma kwakwalwata tadaina aikj sai kawai jini na fita daga kansa kamar rijiya. Wani kallo na yi masa, kansa fashe, idanunsa a rufe, jikinsa yayi sanyi tamkar dutse a cikin dusar ƙanƙara.
Na dube kafata sai na ga glass ya manne, yana barin jini mai zafi. Zafin da nake ji ba wai saboda ciwo bane kawai, amma saboda tsoron da ya lulluɓeni. Ban san ko ina rai na yake ba. Ban san ko ni ɗin ma ina raye ba.
Wannan itace ƙarshen fahimtata kafin komai ya zama duhu. Ban jin numfashi. Ban jin zafi. Sai kawai shiru, sai zuciyata dake bugawa a hankali, tana kwana da fatan ceto daga Allah.
Wannan hatsarin shi ne babban ƙaddarar rayuwar Ramlah. Rayuwar da ta fara ɗaukar salo na soyayya da bege, yanzu ta fara komawa fargaba da hawaye. Ashe kaddarar bata tambaya, kuma bazata sanar da zuwanta ba. Sai dai zuciyar da tayi imani, ta gane cewa komai yana cikin rubutun Allah.
Littafin Ƙaddarar Ramlah (Littafi na 1) ya kasance cike da darussa masu fa’ida, tausayi da kalubale da ke faruwa a rayuwar aure, musamman ga mace da aka aura bisa ƙaddara da ƙarfin iko. Ga cikakken tarin darussa guda goma da ke fitowa daga littafin gaba ɗaya
1. Auren Dole Ba Soyayya Ba Ne
An nuna illar auren dole da yadda hakan ke jefa mace cikin wahala da baƙin ciki.
Iyaye su daina tilasta wa ’ya’ya aure, musamman idan babu fahimta ko amincewa.
2. Cin Zarafi da Shaye-shaye Guba Ne ga Aure
Halayen Bashari sun nuna yadda namiji mai shaye-shaye da tashin hankali ke wargaza aure.
Ya zama darasi ga mata da maza cewa halayyar mutum ta fi kuɗi da kyan fuska muhimmanci a aure.
3. Haƙuri da Addu'a Su Ke Gina Mace Mai Ƙarfi
Ramlah ta rungumi haƙuri da addu’a, duk da halin da take ciki. Wannan ya nuna cewa matar da ke dogara ga Allah ba za ta taɓa faɗuwa ba.
4. Ba Kowane Da Ke Dariya da Kai Ne Masoyi
Babah, wacce ta saba zuwa da dariya da kula, ta fi kowacce cutar Ramlah.
Wannan darasi ne da ke nuna cewa ba duk wanda ke kusa da kai ke maka fatan alheri ba ne.
5. Zuciyar Namiji Zata Iya Sauyawa, Amma Lokaci Yakan Kure
Duk da halin da Bashari ke ciki, daga ƙarshe ya gane kurensa.
Wannan ya nuna cewa canzawa tana yiwuwa, amma wasu lokuta lokacin yakan kure.
6. Soyayya Cikin Ƙunci Tana Iya Tabbata da Girmamawa