Kenza eBookz

Afra ko amrah complete - Chapter 1

Afra ko amrah complete - Chapter 1

Afra ko amrah complete Chapter 1: Afra ko amrah complete Chapter 1. [10:18PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [ 7/8/2016] πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ… ~ AFRAH KO AMRAH~…

4,458 words

[10:18PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [ 7/8/2016] πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ… ~ AFRAH KO AMRAH~ πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…

πŸ…NaπŸ… Bilqis sidibeπŸ’…πŸ»& Billy giro😊

πŸ…1βƒ£πŸ… Zaune yake a office dauke da kyakkyawar yarinya maqale a kafadar sa wacce shekarun ta baza su wuce four to five yrs ba sai bacci take abin ta shikuma yana faman cike ciken wasu takardu.

Gayen ya hadu sosai wanda kallo daya zakayi masa kasan dan hutu ne. Kuma komai na sa a natse yake yinsa.

Wani gaye ne ya shigo office d'in da sallamar sa shekarun sa baza su fi 27yrs ba duk dai en tsara ne kuma da alama en uwan juna ne sbd suna dan da kama. shigowar gayen keda wuya ya ajiye aikin da yake tare da amsa sallamar sa yayinda fuskar sa ke dauke da alamar murmushi.

Wanda ya shigo ne ke cewa "Doctor farhan sae aiki kake ta faman yi da Afrah maqale a kafada,se faman bacci take baza ka ajiye ta ka huta ba" doctor farhan yayi murmushin da ke qara masa kyau yace "fu'ad kenan ai kasan Afrah haka take ko yaushe tana maqale a jikina har dai idan zatayi bacci ba makawa sae kan jikina take samu baccin ya dauke ta. Kuma zancen ajiye ta na huta ko naso hakan idan baccin ta bai yi nisa ba zata farka ne idan taji zan ajiye ta,sauqi na daya Afrah bata da nauyi abin har mamaki yake bani dmn komai tsawon lokacin da nayi dauke da ita bana jin na gaji, idan kaga na ajiye ta ba wai don na gaji bane se don zanyi wani aiki. Fu'ad ya nisa hade da fadin lallai Afrah najin dadin ta,inace dai bata hana ka sake wa da amaryar ka Amrah? Nop ko daya. Yauwa haka nake son ji ace Afrah na bata takura kowa,ya fadi haka ne tare da d'ora ledar sweet kan desk yace ga sweet na saya ma sweet Afrah ita kadai bada Amarya ba dmn bana son a sakawa Afrah rani, idan amarya na buqata angonta ya saya mata,farhan yayi murmushi yace "bazan siya ba kuma sae ta sha na Afrah,kai ita ma zata fara sha kafin Afrah. Fu'ad yace "cab bazan yarda da haka ba Afrah dai zata fara sha" ya fadi haka ne tare da kiran sunan Afrah kusan sau uku bata motsa ba. Farhan yayi murmushi yace "tank God da yasa yau en jin basa kusa da ka tayar min da ita,kamar ya en jin basa kusa? Kai fu'ad kar ka ce min baka san Afrah bata ji ba she is deaf,au haba meyasa idan aka mata magana take dagawa mutum kai alamar taji?eh tana ji wani lokacin amma rashin jin ta yafi yawa kuma d'aga kan da take, ka fahim ce ta da kyau idan kana magana bakin ka take kallo ta hakan ne take samu ta baka amsar abinda kace, ikon Allah to kace tana ji wani lokaci, kenan har da magana tana yi a wannan lokaci? Bata iya magana kawai dai bakin ta na motsi kamar tace wani abu se ta kasa,amma idan tana kuka ka rantse da Allah tana ji,kukan tsaf yake fita kamar ba na deaf ba haka ma dariyar ta. Fu'ad yace Allah sarki to baza ka kaita a duba ta ba,,fu'ad ai kasan bazan bar Afrah haka kawai ba, abun ne ya faskara amma ko yaushe cikin shan magani take,kamar Amrah.

Ka ce dai blind & deaf kake fama da su a gidan ka...kai! waye blind?ai ka fini sani, au dama cin mutunci ne ya kawo ka a office dina,wane cin mutunci ai gaskiya na fada Amrah bata gani sae da glass,to shine zaka kirata blind,bazan kirata blind ba kuwa tunda da zarar ta cire glass bata ganin komai,....wa ya gaya ma Amrah kam tana ganin shadow,....ahaf shadow din da ko ta gan shi kwata kwata bata fahimtar na mene ne,to na dai ji koma yaya ne ina sonta a hakan,ai an san kana son ta a hΓ kan tunda ka aure ta,ya fadi haka ne tare da miqe wa tsaye yace "ni zan tafi na san patient na can na faman jira na,idan kaje a gaida amarya, farhan ya gyada masa kai yace inshaAllah zata ji sannan fu'ad ya fita.

Fitar fu'ad keda wuya Afrah ta fara motsawa a hankali. Farhan ya maida ta kan cinyar sa, tayi saurin sauka tare da jawo hannun sa tana nuna masa toilet hakan yasa farhan ya fahimci fitsari take ji. Ya tallabeta cak yakai ta toilet tayi fitsari suka fito. Ya dora ta kan cinyar sa tare da jawo food flask,ya zuba mata abinci ya shiga bata a hankali har taci ta qoshi ya bata ruwa tasha hade da zaro tissue ya goge mata dan qaramin bakinta. Ya lotsa en yatsun sa kan kumatun ta se kawai naga tayi murmushin da ya bayyanar da dimple in ta,sannan ita ma ta kai hannu ta lotsa en yatsun ta a nasa kumatun shima yayi murmushin da haqoran sa farare tas suka bayyana. Mayar da Ita yayi kan desk suna fuskantar juna ya dauko ledar sweet ya miqa mata tare da fadin uncle fu'ad ne ya ce a baki, Shiru ta mishi tana kallon shi sbd bata fahimci me yace ba, sake maimata maganar yayi yayinda ta tsure bakin sa da kallo,a nan ta fahimci me yake cewa,yayinda ya dauko dayan sweet yana bude mata.

Cike da murmushin jin dadi irin nasu na yara ta kai hannu ta kar6i sweet din da farhan ya bude mata ya miqa mata ta kar6a. Ta hade tafukan hannyen ta alamar thank u sannan ta saka sweet din a bakin ta se shillo take da en qafafuwanta,farhan ya kai hannu ya gyara mata tsorayen kalabar ta da ke reto kan fuskar ta.

Da dare guraren qarfe tara farhan ne da Afrah a kwance kan bed cikin shirin su na bacci suna game da waya Afrah se qyalqyatar dariya ta ke......uncle!uncle!! kiran yana fitowa cikin murya mai dadin sauraro.

Farhan naga ya tashi a natse ya nufi toilet ya same ta riqe da towel bata riga ta daura ba ta dai kare qirjinta da shi,sae faman lalabe take.

Towel ya kar6a ya daura mata sannan ya tattara sumar ta da ta jiqe shar kaf da ruwa ya mayar a baya ya shiga dube dube a toilet din bai ga abinda yake nema ba, ya jawo dan qaramin towel tare da jawota jikin sa,ya shiga tsane mata gashin kanta da ya gama ne ya dauko ta cak se kan bed kafin yake kai duban sa kan mirror ya hango eye glass din ta,yace "Amrah me yasa kika shiga toilet ba glass a idonki? Oily eyes din ta ta dago tana kallon inda take sa ran fuskar sa ce, in kaga hakan zakayi zaton tana gani sbd yanda ta saka qwayar idonta a cikin nashi wanda ni billy & Futha munyi mamakin kallon amma shi farhan da alama ya saba ganin haka shiyasa bai yi mamaki ba ko kadan tace"uncle ina so ne na fara koyon yanda zan riqa zuwa wani gun ba sae da glass ba,yace no ki daina haka ina tsoron ya zama had'ari wata rana,ta gyada kanta kafin farhan ke tashi ya dauko mata eye glass ya saka mata.

Tace "tank u" sannan ta tashi tana tafiya cikin dabara, farhan sae kallon qafafun ta yake cike da tausayi.

Gaban mirror taje ta shafe jikinta da turarukka masu qamshin dadi. Sannan ta nufi wardrobe yayinda Afrah ta mirgino kan jikin farhan tayi pillow da cinyar sa tare da miqa masa wayar sa. Gashin kanta ya shiga shafawa a hankali sbd ya fahimci bacci take ji.

Koda Amrah ta gama shirin baccin ta har Afrah tayi bacci, qaraso wa tayi ta zauna a dayan gefen sa tare da d'ora kanta a kafadar sa, farhan ya shafo gashin kanta ya kalle ta cike da kulawa yace"ya jikin naki?duqar da kanta tayi dauke da alamar jin kunya tana wasa da zoben hannunta kafin take cewa "naji sauqi"

πŸ…2βƒ£πŸ… Murmushi yayi wanda ya qara masa kyau sbd yanayin yanda Amrah keyi idan taji kunya yana birge shi sosai, shafo gefen fuskar ta yayi kafin yake dora Afrah kan kafadar sa da tuni baccin ta yayi nisa yaje a hankali ya shimfide ta kan d'an maidaidaicin gadon ta. sae da ya jima yana tofe ta da addu'o'i kafin yake barin gurin. Amrah kuwa ba abinda take face kallon sa wanda ako yaushe bata gajiya wa da hakan. Ba ita ta daina kallon sa ba sai da yazo gab da ita ya zauna tare da jawo ta jikin sa hade da lakuto hancin ta yace wannan kallon fa sae kace yau ne farkon haduwar mu. Bata ce dashi komai ba face lumshe idon ta da tayi hade da d'an guntun murmushi,farhan kuwa ya kashe musu wutar dakin suka kwanta sae bacci.

Da jijjihi kukan Afrah ne ya tashe su. Farhan ne yayi saurin saukowa kan bed ya qarasa inda take ya dauke ta cikin hanzari ya nufi toilet da ita domin tayi fitsari sbd yasan ba abinda take ma kuka face fitsari sbd Afrah ta kasance yarinya wacce duk yadda take jin fitsari bata yin shi kan bed sai dai ta ajiye ma mutum kuka. Bayan sun fito ne yayi zaune da ita kan bed,yayinda ta lafe kan jikinsa bacci na sake fizgar ta kadan kadan har ya fizge ta gabadaya. Nan farhan ya shimfide ta wanda sai Allah Allah yake kar ta farka sbd so yake yaje masallaci lokacin sallah yayi.

Sai guraren qarfe tara Afrah ta farka daga bacci,lokacin farhan ya fito daga wanka kenan yana taje gashin kansa, saurin kallon Afrah yayi wacce ke kuka irin nasu na yara idan sun tashi daga bacci ganin idon ta a rufe yasa ya sauke ajiyar zuciya sbd yasan idan a bude suke da ta qyalla ido a kan shi ba makawa shine zai mata wanka gashi sauri yake sosai yana so ya hallarci meeting din da za a yi da qarfe goma, kallon Amrah yayi wacce shigowar ta dakin kenan da alama daga kitchen ta fito sbd dauke take da trayn abinci,kallon da farhan ya mata ne yasa ta fahim ci me yake nufi nan ta ajiya tarayn da ke hannun ta ta nufi Afrah cikin sauri ta dauke ta, kafin Afrah ta bude idon ta har sun shiga toilet.

Koda suka fito basu sami farhan a dakin ba ya fita. Amrah takai dubanta gun break fast din da ta ajiye nan ta fahimci farhan ya dibi nashi kasancewar ba plate daya a cikin plates din ta ajiye. Nan ta shafa ma Afrah Vaseline ta shirya ta cikin kayan sanyi kasancewar sanyin da ake sosai.

A 6anfaren farhan kuwa falo yaje ya zauna kan dining yana break fast sauri sauri. Sai da ya kammala sannan ya koma gurin su amrah ya samu afrah kwance jikin pillow sai tsutsar babban yatsan ta take Amrah na riqe da plate din abinci sai faman lallashin ta take kan ta tashi taci abinci,amma mirsisi taqi tashi gashi tana jin yunwa sosai,ita ala dole farhan kadai ke bata abinci ta kar6a. A hankali farhan ya qarasa gurin su ya zauna,Amrah ta ce "uncle nayi nayi taci abinci amma taqi"yace "dama nayi tunanin haka shiyasa naje na gaggauta yin nawa braek fast domin na samu na bata kafin lokaci ya qure min" Yana gama fadar haka ya jawota kusa da shi ya shiga ciyar da ita har sai da ya tabbatar cikin ta ya cika. Sannan ya bata ruwa ya tashi ya jawo suit din sa blue black in colour kallar wandon sa yayinda rigar sa ta ciki ta kasance milk haka talkalman da ke qafafunsa milk ne agogon hannun sa ma haka,briefcase din sa ya dauka hade da makullin mota,tare da fadin ni zan fita. Nan Amrah ta tashi tare da daukar Afrah da niyar su raka shi farhan yace "a'a kuyi zaman Ku bana so taga shiga ta mota dmn na tabbatar kuka zata min sai naje da ita gashi bazai yiyu na shiga da ita taron meeting din da zamuyi sbd gabadaya likitawan state ne za a hadu wanda bansan iya tsawon lokacin da zamu dauka ba bare naje da ita na bayar a riqa min ita gun nurses,kuma gashi yau sanyi ake sosai hakan yasa nake so tayi zaman ta a gida" Ya fadi haka ne tare da kallon agogon da ke hannun sa yaga 9:40am sannan ya maida duban shi gun afrah da ke kallon shi da alama so ta ke ya dauke ta, bye bye kawai ya mata ya kama hanyar fita daga dakin wanda har ya bude qofar dakin ya jiyo sautin kukan ta,tsayawa yayi cak cike da damuwa sbd ko kadan baya son jin kukan ta musamman ma idan ya tuna cewa ita marainiyace kuma amana ce a gare shi. Jiki sa6ule yaje ya kar6e ta yace bara na kai ta gun gwaggwo naga ko zata yarda ta zauna.

Nan ya fito ya nufi dayan 6angaren da muke sa ran nan ne 6angaren gwaggwor da ya ambata.

Da sallamar shi ya shiga ya same ta tana Karin kumallo ya russuna cike da ladabi ya gaishe ta sannan ya fadi buqatar shi na son Afrah ta zauna gurin ta har ya dawo. Ba musu gwagwo ta miqa hannu domin ta kar6i Afrah,ai kuwa ta maqale kafada tana mai qara manne masa alamar baza ta je ba. Gwaggwo tace dama shiru kawai nayi amma nasan baza ta yarda ta zauna ba kuma in banda abinka kai da kake zuwa da ita kullum yau kuma me ya kawo zancen baza ka je da ita ba?cike da damuwa ya nisa yace gwaggwo nima ba haka naso ba zuwan ne da ita ba zai yiyu ba kasancewar meeting din da zamuyi wanda tun jiya na sanar da ke irin di'n bin taron da za'ayi.....haka ne fa gaskiyar ka. Nan ta kar6i Afrah wanda da qyar aka samu taje da kuka da komai har da su murmurje. Farhan kuwa ya fita cike da rashin jin dadi har ya naji kamar da zai yiyu da ya fasa zuwa meeting d'in.

Futha Luv & Billy giro

πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ… [10:18PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [ 7/10/2016] πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ… AFRAH KO AMRAH πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…

Na Bilqis sidibeπŸ’…πŸ» & Billy giro😊

πŸ…3βƒ£πŸ… Tunda ya fita gidan bashi ya dawo daga gurin meeting d'in ba sai bayan sallar la'asar.

Shigowar sa keda wuya bai zarce koina ba sai 6angaren gwaggwo, da shigar sa dakin yayi tsaye cike da murmushi yana kallon Afrah kwance sae bacci take ga sweet a gefen ta zube saura kuwa duk ta watse su a tsakiyar dakin kamar yadda tsorayen kalabar ta suka barbaje akan bed.

K'arasawa yayi daga ciki ya zauna tare da gaida gwaggwo dake zaune kan sallaya tana lazimi yace "gwaggwo haka er reonon taki ta 6ata miki daki da sweets?sae da gwaggwo ta shafa addu'a tare da yaye hijabin jikinta tace"hm!ai yau ni qaramar hauka tamin sae fada take dani cikin gwallanniyar su ta kurame,farhan yayi murmushi mai hade da dariya sannan ya kalli Afrah shidai haka kawai baya son yaji an kirata a kurma duk da yasan eh kurma ce,gwaggwo taci gaba da cewa "a cikin gwalaniyar ne take dauko duk abinda ta samu tayi ta jifa da shi nayi rarrashi har na gaji haka ma Amrah tazo ta bata alawa tayi ta rarrashi amma duk d'aya wai mamaci ya karye. Ita da kanta ta gaji da murmujen ta a nan bakin qofa har bacci ya kwashe ta shine na dauke ta na d'ora kan gado tare da alawar da na fara tsincewa ban samu na qarasa ba naji kiran sallah shine na ajiye aikin tukun idan na qarasa sallah.

Farhan ya nisa yace "ina ce dai bata jiwa kanta ciwo garin murmuje ba kuma bata miki 6arna ba?Aa ko d'aya bana tunanin haka,nan ya tashi tare da fadin to zanje na da'n huta na dawo na dauke ta,gwaggwo tace "to Allah hutar da gajiya" yace "Amin"kafin yake fita daga dakin.

Yana isa 6angaren su ya tarar da Amrah daure da towel gaban mirror tana taje gashin kanta. Ya jima a tsaye bata san da shi ba sai daga baya ne ta hango shi ta jikin mirror sakar masa lallausan murmushi tayi yayinda ya russuna a hankali ya rungumo ta tare da dora kansa a kafadar ta yana mai shaqar qamshin turaren da ke fita a jikinta, yace "my Amrah na gaji sosai"shafo sajen fuskar shi tayi tace "sorry my uncle"ta fad'i haka ne yayinda yake miqar da ita tsaye yace "muje ina son naci abinci"nan ta cire masa suit hade da fadin bari kayi wanka tukun ko...a gajiye ya kalle ta yace"ba kya da tausayi ko my Amrah sbd ke kinci kin qoshi shine ni sai nayi wanka ko zanci",,um um uncle ba haka bane ba,, haka ne man gashi har cikin ki ya tasa alamar kinci ki qoshi"ya fadi haka ne yayinda yake shafa cikin ta ya tafi har izuwa qirjinta cike da jin kunya ta cusa fuskar ta a qirijin sa ba tare da ta jaye hannun sa da yake yawo dashi kan qirjin ta ba, tace "Allah uncle ina tausayin ka kasan ulcer nake fama da ita ko naso na jira ka bazan sami damar hakan ba" Bai ce da ita komai ba sae aikinsa da yake na shafar jikinta wanda komai yana yinsa ne a natse a haka ne har yake qoqarin zame mata towel bata hana shi ba duk da masifar kunyar abinda yake mata da take ji sbd har yanzu bata sake dashi gabadaya ba kuma idan ta hanashi tasan bata masa adalci ba sbd tasan turarukkan da ta shafa qamshinsu ba xai barshi a iya kallonta kad'ai ba. Suna cikin haka ne tayi saurin jaye jikinta daga nashi tare da daura towel d'in ta da farhan ya fara zamewa hakan yasa farhan ya d'ago a hankali yana kallon ta, ganin tana kallon qofar d'akin yasa shima ya maida duban sa a gun. Afrah ya gani a tsaye riqe da sweet a hannun ta sae dai fuskar ta dauke take da fishi,murmushi yayi wanda ya nuna cike yake da farin cikin ganin Afrah. qarasawa yayi gurin ta ganin bata da alamar qarasowa, yaje ya durqusa tare da kama kunnen sa afrah kuwa kauda fuskar ta tayi gefe ta turo baki tare da maqale kafad'a wai bazata haqura ba,kamar qaramin yaro ya nuna kansa yace "nine baza kiyi ma haquri ba"kallon sa kawai tayi sannan ta kalli amrah da ke tsaye tana kallon su nan ta bar shi durqushe ta tafi gurin amrah tare da miqa mata sweet din da ke hannun ta Amrah ta kar6a ta bude mata sweet d'in sannan ta dauke ta,farhan ne ya qaraso gurin su yana cire buttons din rigarshi yaje gefen gado ya zauna tare da jawo stool di'n da kulolin abinci ke kai, Amrah ce ta zuba masa abinci shi kuma sae kallon Afrah yake da ke shan sweet tana kallon shi wanda ya fahimci so take ya d'auke ta nan ya miqa hannu ya kar6e ta ya dora ta kan cinyar sa yana mai fadin an daina fishi da uncle? tsure bakin sa kawai tayi da kallo ta lafe a jikin sa tana mai wasa da buttons d'in rigar sa.

πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ… [10:19PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [7/11/2016] πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ… ~ AFRAH KO AMRAH ~ πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…

Na Billy giro😊 &Bilqis sidibeπŸ’…πŸ»

πŸ…4βƒ£πŸ… Cike da kulawa farhan ke kallon Afrah da ke wasa da buttons d'in rigar shi wanda ya fahimci akwai yunwa a tattare da ita, cire sweet d'in da ke bakin ta yayi ya zaro tissue ya goge mata bakin ta, ya zaunar da ita ta yanda zai ji dad'in ciyar da ita. Sai da ya fara cin abincin sbd yaji idan ba wata matsala ta yaji haka, kasancewar Afrah bata son yaji ko kadan, ya kuwa ji abinci dai dai ba wata matsala kuma dama yayi tunanin haka bcs bai ta6a jin wata matsala a abincin Amrah ba ko yanzu ya d'and'ana ne sbd yasan d'an adam ajizi ne ya kan yi kuskure wata rana. A hankali ya shiga fara bata abincin yayinda take bud'e d'an qaramin bakin ta tana kar6a haka shima yake bud'e d'an madaidaicin bakin sa tana saka mishi,domin Afrah yarinya ce wacce duk abinda farhan ya mata ta kan so ita ma ta mishi haka, duk da cewa yanda take bashi abinci akwai shiririta amma haka farhan ke biye mata wanda wani lokaci idan taje saka mishi spoon yakan d'an karkace abincin ya zuba amma sai dai yayi murmushi yasa tissue ya share ya kuma dai dai ta mata spoon d'in ta yanda zata saka mishi a baki ba tare da abinci ya zuba ba. Haka suka ci gaba da cin abincin su cike da sha'awa da burge duk wanda ke kallon su. Bayan sun kammala cin abinci ne ya dauke ta yaje ya mata wanka ya dunqulo ta cikin towel ya kwantar kan bed sannan ya fice toilet domin yayi nasa wanka. Koda ya fito har Amrah ta shirya ma Afrah cikin kayan da suka yi matuqar daukar ta sai zuba qamshi take.

Bayan wasu kwanaki farhan ne dauke da Afrah a kafadar sa dayan hannunsa kuma kaya ne niqiqi. Amrah da ke kwance kan 3 seater ta zo cikin hanzari ta kar6i kayan da ke hannunsa suka shiga daga ciki, Amrah na ajiye kayan Afrah ta shiga bubbud'e su cike da murna tana gwalanniyar su ta kurame tana nunawa Amrah kayan d'aya bayan d'aya, nan Amrah ta shiga kar6ar kayan tana dubawa, school bag ce da littafai da kuma sweets,choculate,biscuit,da school basket sannan da kuma lunch box,da ta gama gani ne ta shiga tambayar ta tana mai mata maganar kurame da hannu yayinda Afrah ke bata amsa.

Bayan ta gama tambayar ta ne ta maida dubanta gun farhan da ke jingine kan sofa idanuwansa a lumshe tace"uncle Afrah tace wae gobe zaka fara kai ta school?a hankali ya bud'e idon shi tare da gyara kwanciyar sa yace eh by tomorrow inshaAllah zata fara zuwa school"to ni zancen tawa school fa? shiru yayi kamar ba zai ce da ita komai ba can ya nisa tare da fad'in "kar ki damu idan lokacin WAEC da NECO yayi zaki je kiyi amma baza ki koma da zuwa school ba, ba ta ce da shi komai ba, ba wai don bata ji dad'i ba sai don ita ma haka yafi mata,jin shiru yasa ya tashi zaune tare da yaye hular da ke kansa ya kalle ta da kyau yace"yadai Amrahna baki so hakan ba ne?girgiza kanta tayi hade da fad'in "ai ni uncle haka ma da kayi yafi min"ok dauko min ruwa nasha kinji. Nan ta tashi ta dauko masa ruwa had'e da lemu mai sanyi.

Da dare guraren qarfe goma sha biyu kowanen su bacci yake abinsa cike da kwanciyar hankali.

A hankali farhan yake bude idon shi sbd yanda yaji jikinsa kamar wanda aka d'ad'd'aure, gabadaya yaji sa a tamke ga kuma yawan motsi da yake ji a d'akin yunqurawar da zai yi ne yaga tabbas kuwa a d'aure yake har ma ba ta yanda za'ayi ya iya wani qwaqqwaran motsi,kallon d'aurin da aka masa yake cike da tsananin mamaki shin ta yaya hakan ta faru,waya masa haka ⁉ Idon sa yakai kan gadon Afrah wayam ba kowa ya kuma kalli gefen sa ba Amrah sosai hankalin sa ya qara tashi kan yayi wani yunquri yaji kukan Afrah an fito da ita a dayan daki aka shigo da ita d'akin da yake tare da kunna wutar dakin, Afrah na ganin shi ta fara kuka sosai tana zille zille tare da miqo hannunta tana so farhan ya cece ta, su kuwa sai janta suke zasu bar d'akin da ita,yayinda farhan ke yunqurin ya kunce kansa amma ya kasΓ  gashi kad'an ya rage su fita da ita hakan yasa ya fad'o kan bed yana son yaja jikinsa da sauri yaje ya kar6o Afrah, amma hakan ya gagare shi sbd hannayen sa a baya suke kuma a daure haka ma qafafuwansa a daure suke, da qarfin tsiya ya yunqura hade da wani irin nishi yayinda aka kashe wutar dakin wanda yayi dai dai da tashin qarar bindiga.........kamar had'in baki farhan da Afrah suka tashi firgigit daga bacci wanda hakan ya nuna kowanen su ya tashi daga mummunan mafarki,a rikice farhan ya kai dubansa kan gadon Afrah kamar yadda ita ma Afrah take kallon nasu gadon, Da gudu ta sauko kan gadon ta nufo gurin shi tare da fad'awa kan jikinsa, jikinta sae qyarma yake shi kuwa farhan jikinsa ne yaji ya mutu ya qara matse Afrah a qirjin sa ya shiga shafa sumar kanta a hankali sae dai tunani ne fal a ransa yayinda yake tuna fuskokin mutanen da ya gani a cikin mafarki tabbas a zahiri yasan wad'annan fuskokin, kuma yasan mugun nufin su a kanshi, shiyasa ya shiga fargaba sosai kar mafarkin sa ya zamo gaskiya"saukar hawaye yake ji kad'an kad'an a qirjin sa tare da jin sautin kuka, wanda shine ya dawo dashi daga duniyar tunanin da yake ya kalli Afrah da ke lafe a qirjin sa hawaye na ta faman zarya a kumatun ta, tana kuma fitar da sautin kuka a hankali, sannu a hankali farhan yakai hannu yana share mata hawaye yana kuma tunanin shin ita kuma Afrah wane irin mafarki ne ya firgita ta har take yin kuka. Gashi bai iya maganar kurame ba bare ya tambaye ta, Amrah ce ta iya kuma bacci take. Lallashin ta kawai ya shiga yi ta hanyar bubbuga bayan ta, har ya samu tayi shiru ta kuma qara lafewa a qirjin sa alamar tayi bacci.

Futha luvπŸ’…πŸ»&Billy giro😊

πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ… [10:19PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [ 7/12/2016] πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ… ~AFRAH KO AMRAH ~ πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…πŸ…

Na Billy giro😊&Bilqis SidibeπŸ’…πŸ»

πŸ…5βƒ£πŸ… Domin sae ajiyar zuciyar ta ke fita a hankali, cike da kulawa farhan ke ci gaba da kallon er fuskar ta mai kyau wacce d'igon hawaye ke kan eyelashes d'inta, yasa yatsan sa ya share mata tare da kwantar da ita a tsakiyar su, cike da shagwa6a ta farka tana fad'in"uhm uhm"tayi saurin shigewa jikin sa kamar wacce ke jin tsoro har dai yanda ta cusa fuskar ta a qirjin sa ta qudundune guri d'aya. Addu'a ya shiga yi mata lokaci mai tsawo, sannan ya kalli matar sa Amrah wacce har yanzu bacci take gashin kanta duk ya barbarje a kan pillow har ma ya d'an rufe mata fuska, bai yi yunqurin gyara mata ba sea surar jikinta da yake bi da kallo yana cikin haka ne yaji wani irin fad'uwar gaba wanda ya sa shi saurin daina kallon ta ya tashi a hankali yana mai karanto addu'a yaje gab da ita ya yaye mata gashin kanta da ya rufe mata fuska kafin yake zuwa toilet ya d'oro arwala yazo ya saka jallabiya kasancewar d'an guntun wando ne kad'ai a jikin sa. Sae da ya shimfid'a carpet sannan ya kabbarta sallah.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull