Afra ko amrah complete - Chapter 35
Afra ko amrah complete Chapter 35: Afra ko amrah complete Chapter 35. Farhan ne ya dawo daga aiki a gajiya Afrah taje ta tarbe shi ya kar6i suhail da…
2,592 words
Farhan ne ya dawo daga aiki a gajiya Afrah taje ta tarbe shi ya kar6i suhail da suhailat ita kuma ta kar6i jakar hannun shi,suka haura sama zuwa d'akinshi. Da taimakon ta ya rage kayan jikinsa ya fad'a wanka, kayan wasa ta zuba akan gadon da Farhan ya ajiye su snn ta tafi downstairs ta d'auko mai abincin sa sbd tasan yanda ya shigo a gajiye ba zai iya sake sauka ba.
Barin yaran tayi suna ci gaba da wasar su ita kuma taje zuwa nema ma Farhan kayan sawa masu sauqi. Yana fitowa ya kalli yaran sae wasa suke da abubuwan wasan su ita ma Afrah tayi tsaye tana kallon su sae dai kmr wani tunani takeyi ,Farhan ya qaraso inda take ya juyar da ita ta baya ya rungume suka ba yaran bai yakai bakinshi dai dai wuyanta kmr wanda zai mata kiss yace"tunanin me kike kina kallon yara? Ba komai nima haka kawai na ganni a tsaye kmr mai tunani kuma gsky ba abinda nake tunani,ni kuma na d'auka tausayin su ne kika fara idan kika fara karatu, dmn suna samun kulawar ki ba kad'an ba, idan kika fara zuwa school abin zai rage sosai ,to sae suyi haquri ai gwaggo na nan kuma da na sami time zan dawo ne na shayar dasu,ya juyo da ita yana kallonta yace"ko zaki bari idan sun shekara sae ki fara karatun? kai tsaye taji qwallah sun cika mata ido tana kallonshi ,had'e bakinsu kawai taga yayi, tayi tayi ta qwaci kanta ta kasa , yayi saurin sakinta sbd towel d'insa dake qoqarin zamewa ya kalli yanda ranta yayi mugun 6aci ya sake jawota yana qoqarin had'e bakinsu ta fixge kanta da qarfi tana fad'in"wai meye hk dan Allah! yara fa na kallon mu,sake riqota yayi yana kallonta yace"Afrah yau ni kike ma tsawa? Da sauri ta sadda kanta qasa tace cikin muryar kuka ni uncle ka gaya min kawai idan baka son nayi karatun nan sai na haqura,Afrah kinsan nafi kowa son kiyi karatu yaran ne kawai suka bani tausayi amma kar ki damu zaki fara karatun nan bada jimawa ba inshaAllah ,gyad'a masa kai tayi snn taje kan qirjinsa ta kwantar da kanta kmr yanda ya buqata ,sun d'an jima a haka ,ya d'agota yace"bari nasa kaya naci abinci sae muje 6angaren gwaggo tace tana son tayi magana damu.....yes!Allah yasa plan d'in mu ne yayi, hm Allah yasa hln ke kinga ta fara shiga damuwa kan canza mata da mukayi?bazan iya ganewa ba tunda da mun gaisa nake tafiyata kawai dai nasan baza ta rasa shiga damuwa ba duk da cewa still suhail da suhailat gurinta suke yini shan mamma kad'ai ke kawo su ,ko yanzu an maida su kenan ka dawo basu ko sha mamman ba ,ya kalli yaransa yace"to je ki basu mamman kinga har suhail ya fara ta6a kunnen sa alamar bacci yake son yayi. Nan taje tana breast feeding d'insu shi kuma ya shirya yayi zaune yana cin abinci.
Koda suka je 6angaren gwaggo suka dawo ba qaramin murna sukayi ba musamman Afrah da har tsalle take tana rawa sae kace wacce aka yiwa bushara da gidan aljanna ,tace"uncle ai yau nasan ba qaramin murna Abban uncle fu'ad zai yi ba idan yaji gwaggo ta amince zata yi aure,gsky kam na tabbatar har zowa sae yayi amma fa bazan gaya mai ba sae anji daga bakin Abban Amrah duk da a gurin shi bana tunanin akwai matsala but jekiyi magana da Amrah sae ta fara tuntu6ar Abban nata muji,ai na tura mata text ynz zata shigo 6angaren mu ,yauwa naji door bell inaga ita ce.
Ta sauka downstairs tayi sauri ta bud'e qofa ta qanqame Amrah dake tsaye ,Amrah ta qarasa shigowa suka zauna ta kira Abbanta tana gama wayar ta kalli Afrah tace"Abba baya gari yana Abuja amma yau zai dawo yanzu uncle nake son na kira ko zai barni naje gida yau, ke Amrah wa zai barki ki fita kina biqi ,mtsw meye a ciki kuma ai bazan bari gwaggo ta sani ba idan uncle yazo anjima da dare sae na roqe shi ya kaini,kina ganin xai barki ?inshaAllah.
Da dare Amrah ce zaune da fu'ad a cikin mota yace"ya baki zo min da Najeeb ba ?bacci yake ,bai sake cewa komai ba sae fira da ya sake janta da ita a cikin firar su ne tace"pls uncle ina son ka kaini gun Abba yanzu "kallonta yayi yace"gida yanzu why? Nidai dan Allah kawai ka kaini zan ganshi ne,matsowa yayi kusa da ita tayi saurin jaye fuskarta ganin abinda yake shirin yi ,tace"kace wani abu ba wnn ba"jinginawa yayi a jikin seat yace"kina ganin Najib ba zai tashi ba har mu dawo? Najib ya riga ya shiga bacci sae kuma cikin dare idan ya farka shan mamma,ajiyar zuciya ya sauke snn yaja motar suka tafi.
Bayan wata hud'u da faruwar haka abubuwa da dama sun faru dmn anyi auren gwaggo da Abban Amrah sae dai a nan gidan yake zowa kafin ya kammala gyara wani gida da ya saye dake gab da gidan sbd baya son d'auke gwaggo kusa da su farhan sae akayi sa'a maqwabcin su farhan yasa gidansa a kasuwa sbd zasu bar garin gabad'aya dmn ba mazauni garin bane shine sae Abban Amrah ya sayi gidan,duk da gidan mai kyau ne amma yafi so ya qara tsara gidan yanda yake so. Amrah kuwa tuni ta koma gidan mijinta haka kuma a cikin watan nan sun fara zuwa school sae dai sae Amrah tazo gida ta ajiye Najib nan gurin gwaggo tare da su suhail da suhailat.
yau weekend hakan yasa Afrah da Farhan suke zaune gida suna hutawa sae shan fruits suke suna kallo, su suhail da suhailat sae wasa suke da motar su ta wasa . Afrah tace"ni kuwa uncle gidan nan da Abban Amrah ke gyara banga illarsa ba da har naga yasa an rushe katangar da ke tsakanin mu dasu,wai fa duk don mu yake yi so yake ya bud'e qofar da zata riqa sada mu da gwaggo cikin sauqi ba sae mun zagaya ba, kai amma fa ya kyauta mana, to shi 6angaren gwaggo idan suka tare a nasu gidan rufe shi kawai za'ayi? Eh to za'a rufe qofar da ke sada mu da ita sae a zuba en haya a ciki, en haya kuma uncle? Eh amma ba irin en hayan da kike tunani ba wani shahararren d'an kasuwa ne matashi da kasuwancin sa ya bunqasa a nan garin shine yake so ya tare nan garin shida matarsa da d'ansu qwaya d'aya ,bare kinsan yanayin gida yanayin wanda zai dauki hayar shi ba wai haya duk haya bace,kuma kinga gwaggo yanzu ta samu wata hanya da kud'i masu tsoka zasu riqa shigo mata duk shekara ,haka kuma keda Amrah nake son a raba muku dukiyar ku ta gado sae na samar miki hanyar da zaki riqa juya kud'in ta hanyar business ,um um nidai uncle idan an rava kabar nawa a hannunka kawai na bar ma halak malak, sam hakan bai zai yiyu ba Afrah ,meyasa ? Sae kace Farhan d'in mahaukata... As how uncle, calm down mana Afrah, ina son kiyi business ne shiyasa ,nifa uncle harkar business d'in nan bazan iya ba, to shikenan akwai wani tunani da nayi zamu had'a kud'i mu gina asibiti nida fu'ad idan zaku iya keda Amrah sae mu had'a hannu mu duka hud'u sae mu gina babbar asibiti idan Allah ya nuna mana kun kammala karatun ku sae mu koma can da aiki damu har ku, ko ya kika gani ?gaskiya haka yayi uncle muyi aiki tare da mazajenmu .
Two weeks later tafe suke sun fito da gidan su Amrah sae fira suke abinsu cikin mota, hankalin Farhan ne ya d'auku har ya tashi kad'e wata mata yayi saurin jan birki Allah ya taimake shi bai kad'e matar ba ya fito dmn ya bata haquri cikin tsananin mamaki yake kallon fuskar matar bakinsa na rawa ya samu da qyar yace"mama dama kina raye! Matar tayi saqwarqwatai tana kallon shi ko zata tuna inda ta san shi Farhan yace"mama baza ki san fuskata ba sbd lokacin ba kya gani akasin yanzu da aka miki eyeglass ,mama nine Farhan mijin er ki marigayiya Amrah ,kuka ta fashe dashi tace"Allah sarki kaine ashe kaima kana raye aka ce min har da kai ka mutu "ganin kukanta zai tara musu mutane yace"mama muje na kai ki gida sae muyi magana a can.
Bayan sunje gidan yake cewa "mama waya snr da ke cewa har ni na mutu? Mai gida na ne da ya tafi dani , ya gaya min labarin da yaji a gari cewa en fashi sun shiga gidan ku har ma an kashe ka kaida Amrah, ba qaramar nadama yayi ba dajin mutuwar Amrah haka nima ba irin kukanda banyi ba dmn kasan ita kad'ai ce 'ya a gareni haka kuma a lokacin qafata tayi tsanani shiyasa maigidana ya d'auke ni yaje dani qauyen su dmn amin magani ,snn kuma shi yayi d'auwainiya dani har aka min madubin ido na fara gani, amma har ko yaushe ina mai jin baqin cikin yanda ya rabani da Amrah ba tare da yasan halinda zata shiga ba, dmn ba don ka ceceta ba da ban san halin da zata shiga ciki ba,wanda duk zamn da tayi a gidanku kafin ka aureta har zuwa lokaçiñ da ka aureta maigidana ya bani lbr don kawai ya samu na kwantar da hnklina har yana min alqawarin idan naji sauqi zai kaini gurinta ashe ba rabon mu qara ganin juna bane haqiqa Allah baya barin wani don wani ,na yafe miki Amrah na yafe miki duniya da lafira, daga haka tayi ta kuka cikin kukan take cewa don Allah d'an nan nasan baza ka rasa hotonta ba idan ka sami lokaci ka kawo min ko zan riqa ganin fuskar 'yata, ta qarashe maganar cikin wani irin kuka mai ban tausayi. Sosai Farhan kejin kuka amma haka ya dake ya ciro kud'i masu yawa a aljihunsa ya ajiye mata yace"ga wnn mu zamu tafi sae gobe inshaAllah zan shigo na kawo miki hoton , nan tayi ta yimai godiya har suka fita.
Har suka isa gida Farhan bai qara cewa komai ba. Da dare Afrah tayi shirin bacci taje d'akin Farhan ta same shi sae kallon photon marigayiya Amrah yake qwallah cike tap a idonsa. Zama tayi ta kar6i photon ta ajiye snn ta kwantar da kansa a qirjinta tana shafa sumar kanshi a hankali yayinda qwallah ke silalowa a hankali kan kumatunta, har suna d'iga kan fuskar Farhan, yayi saurin d'agowa yana kallonta yace"no Afrah ki daina kuka kinji nima na daina,nan ta sake maida shi kan qirjinta kmr wani d'an yaro tana ci gaba da shafar sumar kanshi.
Washe gari ne ya tafi ya kaiwa Maman Amrah photo kmr yanda ta buqata ,dashi da gwaggo ma yaje sbd ya bata labarin had'uwar da sukayi ta jiya.
Some yrs a go .
Farhan ne ya shigo d'akin Afrah ya same ta kan gado ta jingina bayanta da pillow tare da miqe qafafunta sae chat take da Amrah yaje yayi pillow da cinyoyinta yana kallon fuskarta ta ajiye wayar tace"yadai uncle? zancen asibitin mu ne da aka yi kusan kammalawa amma har yanzu bamu tanadi sunan da zamuyi mata ba, kai ko dai uncle bayan ance sunayen mu ,mu hud'u za'a had'a da kuma na yaran mu, to ai bai yi ba yayi kad'an sbd kinga nida fu'ad F keda Amrah A suhail da suhailat S sae Najib kinga idan aka had'a ba zai bada wani abu ba face FASN hope get it, kinga abu mai sauqi kafin a kammala gini ku sanbad'o muna wasu yaran..... Cabd'i sae mun kammala karatu tukun, ba wani yau d'in nan a yanzu ki shiryi kar6ar babyna ,nan yakai hannu ya xuge mata zip d'in riga ,Afrah ta saki dariya ta tashi ta fita dagudu ta bar shi sae dariya yake .
Bayan wata d'aya da faruwar haka ne. Fu'ad da Amrah sunzo musu yini suna zaune kan dining su duka hud'u zasu fara cin abinci. Suhail da suhailat n Naheeb kuma suna gun gwaggo.
Afrah na bud'e warmers qamshin abincin ya daki hancin Amrah ta rufe hancinta ta tafi da gudu sae toilet d'inda ke nan downstairs tayi amai har ta gode Allah ,fu'ad da ya bita shi ya taimaka mata ta wanke bakinta suka fito. Kan su qaraso Afrah ta kalli Amrah ta fashe da dariya tace"ba dai ciki ba muna last yr da batun kammala school,wayyo Allahna har kin ban tausayi ,takai har qasa tana dariya tana ta6a ciki tana nuna Amarah tace"wayyo Allah cikina wai ke ya ma akayi kika bari kika sami ciki kuma a shekarar mu ta qarshe,ta sake kwashewa da dariya tace" kai amma har kin ban tausayi ga renon ciki ga karatu Allah sarki baiwar Allah.....suhailat ce ta shigo da gudu ta sami Afrah nan durqushe sae kwasar dariya take tana nuna Amrah wacce ranta yayi mugun 6aci ta kalli fu'ad cike da qwallah a idonta dmn ganin take laifinsa ne. Suhailat ta katse Afrah da cewa" mommy kinji wani turare mai qamshi da gwaggo ta siyo a lokacinda kuka je makka..... Ture ta Afrah tayi da sauri sbd wani irin abu taji lokacinda turaren ya daki hancinta, ta daka mata tsawa tace"6ace min da gani da wnn qamshin turaren naki! cikin fushi suhailat ta fita,inda har ran Farhan ya soma 6aci yaga Afrah ta tashi da gudu tana yunqurin amai sae toilet , tayi amai fiye da na Amrah ta,ta fito wahale rungume a jikin Farhan sae numfashi take fitarwa ta samu da qyar tace" uncle nidai ba ciki ne dani ba ko? Kmr mai rad'a yaje saitin kunnenta yace"ciki ne mana Afrah ke baki lura da yanayin jikin ki bane a kwanakin nan?a tsorace cikin d'aga murya tace"ciki fa kace uncle....zama d'aya su duka ukku suka kwashe da dariya har Farhan d'in dake rungume da ita sbd ba qaramin dariya ta bashi ba yanda tayi tambayar. Dariya suke sosai musamman Amrah ,Afrah kuwa kuka ta fashe dashi tana qoqarin haurawa sama da gudu, Amrah ta riqota tana share mata hawaye tace"bassu kawai na tabbatar da gayya suka mana cikakkan nan don kawai sunan asibiti ya fito, wata dariyar Farhan da fu'ad suka sake kwashewa da ita sbd yanda Amrah tayi maganar shaye da toka ko kunyar maganar ma bata ji ba,sae da sukayi dariya mai isar su har su Afrah da Amrah suka fashe da kuka dmn ganin suke kamar shikenan sun 6ata musu tsarin karatunsu,hakan yasa kowanen su yaja matar sa zuwa rarrashi da qyar suka samu suka shawo kan matan nasu cikin nuna musu cewa cikin fa daga Allah ne kuma in Allah ya yarda zasu kammala karatun su lami lafiya.
Bayan shekara d'aya har da watanni. Alhmdlh su Afrah sun kammala karatun su lami lafiya kuma result Almdlh yayi kyau ba kad'an ba, inda tuni suka haife abinda ke cikinsu yayinda Allah ya azurta Afrah da haifuwar d'a namiji da suke kira *Sameer* Amrah kuwa ta sami en biyunta duka mata wato *Najwa & Najma*
Kuma har sun bud'e asibitir su mai suna *FASAN SPECIALIST HOSPITAL* da tayi matuqar kar6uwa gun mutane sbd qwararrin likitawan da aka zuba a ciki.
TAMAT BIHAMDILLAH! WE DEDICATED THIS NOVEL TO ALL OUR FANS! LUV U ALL😍
NI BILLY GIRO KECE MUKU SAI MUN HAD'U A LITTAFINA NA GABA MAI SUNA *BAZAN BAR SHI BA!*
NI KUMA BILQIS SIDIBE WATO (FUTUHATUL~KHAIR) KE CE MUKU AFTER KAWATA KISHIYATA DA NAKE YI YANZU ZAKU JINI A LITTAFINA NA GABA MAI SUNA *GIMBIYA BILQEES*
🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅