Kenza eBookz

Afra ko amrah complete - Chapter 34

Afra ko amrah complete - Chapter 34

Afra ko amrah complete Chapter 34: Afra ko amrah complete Chapter 34. Washe gari har qarfe goma Afrah bacci take ita da yaranta . Gwaggo ta shigo ta ajiye…

4,441 words

Washe gari har qarfe goma Afrah bacci take ita da yaranta . Gwaggo ta shigo ta ajiye kayan da ke hannunta snn ta kar6o wasu dake hannun Raheema dake tsaye a bakin qofa ta shiga dasu ta ajiye tace da Farhan dake kar6ar kyn yana ajiyewa"wai tashin ta suke tatayi da dare ne ? Sau d'aya ne kawai dai yaran akwai bacci but ita Afrah she deserve it bcs tunda muka dawo daga asibiti bata samu tayi bacci ba sae dare, to nikam zan yiwa yara wanka sbd kar a fara shigowa barka yara ba wanka, haka ne kam gwaggo.

Wankan da akeyiwa yara suna kuka shi ya tashi Afrah ta tashi a hankali ta zauna snn tayi wa gwaggo ina kwana da gajiyar aiki ,gwaggo tace"lafiya lau ya jikin naki ba wata matsala ko?Alhlmdlh ba komai,to Farhan da ka had'a mata ruwan zafi tayi wanka......um um bana so ni zan had'a abuna da kaina, gwaggo tace"ke ruwan zafi kike had'awa ko abu da kama....uhm uhm gwaggo da zafi yake had'a min,to so kike ki koma tsofuwa ki raku6e zama d'aya jiki bai sami gashin kirki ba,to ai ba dole sae ruwan zafi ba ko magani nasha zan bi normal ,to naji dai jeki kinga har Farhan tuni ya shiga bayi yana had'a ruwan ,kamar tayi kuka ta tashi ta tu6e ta fad'a bayi, Farhan dake cikin bathroom d'in ya kalleta da kulawa ya riqo hannuwnta yana magana cikin rarrashi yace"pls Afrah kiyi wankan qwarai kinji,idan bakiyi wankan kirki ba zan duba ki ne dmn zan gane na kuma maida ke na miki wankan da kaina, to uncle ciwo fa ka sani, jurewa zakiyi my Afrah kuma ki dirza jikin ki sosai kinji, then dan Allah kar kice zaki qara sirka ruwan ,inshaAllah uncle zanyi yanda kamin jiya sbd naji dad'in wankan daga baya, that's gud my dear Afrah kinga amfanin wanka mai kyau kenan,uhm amma uncle zan d'anyi ihu ko zanji damar zafi,murmushi yayi yace" kiyi ihun bada yawa ba amma"

Bayan ta fito ta shirya aka bata yaran ta shayar dasu sbd kukan da suke,cikin kulawa gwaggo tasa ta gaba tayi break fast .

Haka taci gaba da samun kulawa sosai gun gwaggo har rnr suna tazo akayi biki shagali yara suka ci sunan *Suhail da suhailat*

Ana gama biki da bayan magrib Amrah ta koma gida sbd wani irin zazza6i da ya taso mata ,fu'ad ya shiga damuwa ba kad'an ba don komai bata iya yi sae da taimakon sa ne ma ta samu tayi wanka ,ya tasa ta gaba taci abinci ba don taso ba, ko ruwa bata samu tasha ba bacci yayi awon gaba da ita nan ya dubata ya gano ba komai bane face d'inbin gajiyar aiki da kuma zama da yunwa.

Ba ita ta farka ba sae guraren qarfe goma taje bathroom tayi arwala ta fito ta sami fu'ad zaune ya taso ya riqo hannyenta yana murzawa as usual yace"ba dai zazza6in bane ko, naji jikin naki ba zafi ynz? Eh bashi bane tashi nayi dmn nayi sallah kasan banyi isha'i ba,kallon cikinta yayi da ya fara fitowa yayi murmushin jin dad'i tare da kai hannu ya shafo cikin,Amrah bata ce komai ba sae hannunsa take kallo dake yawo kan cikinta, oops sorry kar na 6ata miki time je kiyi sallar. Hannunta ta xare a hnkli cikin nashi snn ta wuce.

6angaren su Afrah kuwa. Afrah ta fito daga bathroom ta sami Farhan ya shigo d'akinta bcs dama a d'akinta take , bacci ne yake kawo mata kullum. Kallon sa take yana ma Suhail da Suhalait addu'a dake kwañce cikin d'an gadon su suna bacci ,taje a hankali ta rungumoshi ta baya ya juyo ya d'aga ta cak suka je kan bed ya kai hannu ya rage hasken d'akin snn ya kwanta Afrah na kan qirjinsa yana shafa bayanta har tayi bacci snn shima yayi bacci.

Sannu sannu lokaci keta tafiya yanzu har cikin Amrah ya shiga wata tara.

6angaren gwaggo suke ita da Afrah suna fira sbd yau tazo yini gida Suhail da suhailat na hannun Raheema sae wasa take musu gashi sun qara qiba sunyi matuqar qara kyau abin ba'a cewa komai sae kace 'ya'ayan larabawa. Afrah ta kalli cikin Amrah tace"ke kam kin huta cikin ki ba hayaniya dai dai ke ba kamar ni ba da har fita na daina yi kan girmansa "hm Afrah kenan ke cikin en biyu ne dake fa ni kuma da gani d'a d'aya ne.....wayr Amrah ta shiga ringing kallon wayr kawai tayi ta basar bayan sak taga sunan da ke yawo akai wato switat. Afrah tace"ban gane uncle fu'ad na kiranki ba kin wani kauda fuska"bari kedai yau da safe fad'a mukayi.... Oh no why?wai shi ba zai barni na dawo gida haifuwa ba a can zan zauna na rasa wa yake son ya kula dani can d'in,ke ko Amrah baki sani ba ko zai nemo wata mai kula dake....Ba wani shi kawai lokacin haifuwar ki ne ya birge shi ganin kinyi zamanki a 6angaren ku , taya ma zai had'ani dake keda gida d'aya kuke da gwaggo ni kuma ba ko anguwa d'aya ba kuma ba wani d'an uwa da muke da a anguwar, Kuma sam ba hujja bace ma yace wai bazan dawo gida haihuwa ba,Afrah ta nisa kan tace komai suka ji sallamar yaro ana kiran Amrah,Afrah tace"ce masa gata nan zuwa snn tace"bawan Allah nasan duk yaji ba dad'i shine har ya biyoki, Amrah dai komai bata ce ba ta nemi hijab ta tafi tunda ta hango motar shi ta qara d'aure fuskar nan tamau taje ta shiga motar ta rufe ba tare da tace dashi uffan ba asali ma ko kallon gefensa bata yi ba, as usual ya riqo hannunta zai fara murza ta fizge hannun ta rungume duka hannayenta biyu a qirjinta, komai kasa ce mata yayi sae kallonta yake can yace"Amrah baki fahimce ni bane bana jin dad'i idan kika tafi kika barni but i dnt mean to hurt u....u mean to hurt me uncle bcs cikin fad'a kake min magana har kana daka min tsawa bayan ni cikin rarrashi nake ma magana, ta qarashe maganar cike da son tayi kuka, hkn yasa fu'ad ya qara shiga damuwa yace"kiyi haquri raina ne ya 6aci ganin kinqi ki fahimce ne shine ma yñz nazo na qara fhmtar dake ni mai iya kula dake ne ba sai kinzo gida ba.... Wato ma ba zuwa kayi kace ka amince ba , sae kawai ta fashe da kuka tana qoqarin fita daga motar yayi saurin jawota jikinsa sae zille mai take, bata iya qwatar kanta ba sbd yanda ya matse ta a qirjinsa hkn yasa ta ci gaba da kuka a jikinsa ,fu'ad ya rufe idanunsa yana jin kukanta kmr wata azaba ce ake mai yace"dear na amince ,wlh na amince idan kin haifu zan maida ke gida"ta d'ago tana kallonshi ta sake komawa kan jikinsa tace"thank u uncle i thank u so much "daga hk suka yi shiru long time fu'ad ya d'ago ta yace"sae kuma me kike son na miki dear? Ba komai ,d'an bakinta yake kallo kmr ya had'e da nashi ,tace"uncle zan koma daga ciki fitsari nake ji"yace"ok zan zo d'aukar ki ,kamanta da mota ta nazo, ban manta ba zan dai zo, to sae kazo, nan ta wuce sae kallonta yake cike da so da qauña har ta 6ace ma ganin sa snn ya furzadda iskan bakinshi a hnkli yaja motar shi ya tafi.

Washe gari Afrah ce cikin kwalliyar ta mai kyau sae zuba qamshi take tayi tsaye tana kallon Farhan da yaran sa kmr masu gasar ado sae wasa yake musu Afrah nata dariya dmn wasar tasu daban dariya take yanda yaran ke qyalqyatar dariya suna rigengeniya gun hawa jikin Farhan sbd duk wanda ya fara hawa shi/ita farhan ke fara d'auka yayita cilla shi/ta sama yana mai/mata wasa. da murmushinta ta hau gadon ta zauna Farhan ya tashi daga kwancen da yake tare da riqo yaransa yana kallon ta tace"hm Suhail da Suhailat fa sunyi saurin wayo ji fa yanda suke wasar nan wai ba wanda keson a rigashi, to Afrah meye abin mamaki yaran nan fa sunyi 4 to 5 months kuma kullum fa idan ina gida wasa muke yi dasu ,haka ne kuma. tashi zatayi yayi saurin riqota ya d'ora mata kiss gefen kunce yace"ina zuwa byn kinsan time d'in wasan yarane? shafo kiss d'in tayi tana murmushi tace"bakaji wayata tana ringing ba ita zan d'auko,tana tashi suhailat ta aza kuka wai ta d'auketa tace"yi haquri Suhailat waya zanyi,Farhan ya d'auketa ganin taqi shiru yace"yi haquri mana Suhailan daddy mommy zata yi waya ne bari ta dawo kinji, ba musu tayi shiru ta kwanta kan jikinsa tana wasa da Suhail da shima yake kan jikin Farhan. Sae ga Afrah cikin murna ta qanqame Farhan tace"wayyo dad'i! uncle Amrah ta haifu ta sami baby boy"

*Billy giro😊&Futha luv* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:23PM, 11/30/2016] Billy Geeero: *[11/30/2016]* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*

*Futuhatulkhair.WordPress.com*

*```🏅95🏅```* Cikin farin ciki sosai yace"mashaAllah tana asibiti ko ansallamo ta? No a gida fa ta haifu, shine nake son nayi sauri naje kafin a maida ta na samu na tsara mata kayan da zata zo dasu. Ok to muje a snr da gwaggo . Nan suka je 6angaren gwaggo dai dai ta gama waya kenan sae murna take tace"Afrah sae ki gaggauta zuwa sbd tace tana son kije yanzu, ni yanzu bari naje nayi sauri a had'a mata abincinda zata ci kafin ku dawo, hahaha yau su Amrah za'a sha d'aci da zaman ruwan zafi,uhm ai ita kinsan ba irinki bace ,Aa gwaggo ai kinsan ita ma bata son shuwaka amma jin qiris yaja mata yau, farhan yace"muje nidai da wannan srtn naki . To bani yaran a bawa Raheema, ni da yarana zan tafi, kenan ni zan mana driven? Eh ni wasa zanyi da yarana ,murmushi tayi ta girgiza kai shidai yaransa yaransa.

Suna shiga mota suhailat ta ajiye kuka sae taje gun Afrah, Afrah tace"kai me yake damunki ne yau ga Abbanki kice sae ni zan d'auke ki bayan kinga driven zanyi" ki kar6e ta may be yunwa take ji....haba uncle kaima kasan ba dai yunwa ba ,kasan ita wani lokaci rigima ne da ita ba kamar suhail ba da ko mamma bai damu dashi ba idan yana hannunka . Ta kalli suhailat tace"kima daina kuka kina taro min hannu ni ba kar6ar ki zanyi ba, nan ta mird'a key zuwa tada mota Farhan yace"Aa gaskiya ki kar6eta sae ni na jamu,ta wani turo baki tana kallon suhailat dake taro mata hannu tana gwalanniya Afrah tace"yanyanyan kedai na kar6e ki ko? Suhailat ta fashe da dariya Afrah tace"dariya ma na baki to zo muje nan ta kar6e ta,Farhan ya fita d'auke da suhail ya zauna driver seat ita kuma ta zauna inda ya tashi ta rufe gambun mota tana fad'in "kawo suhail ko dashi zakayi driven? Eh mana baki ga har seat belt nasa mana ba, but uncle kasan suhail da wasa da ta6e ta6e ,bacci yake ji ai ko suhailat bacci ne yasata rigimar nan gashi har tayi kwanciyar ta a jikin ki alamar zata yi bacci, ok to muje .

Suna isa gidan fu'ad ya tarbe su da murna ya kar6i suhail a hannun Farhan da tuni yayi bacci kamar yadda suhailat tayi bacci. Yace"wai kai Farhan ina ka ajiye phone d'inka nayi kira har na gaji na snr dakai an haifi mai kama dani ,au haba ?wlh sak ni yaron ya d'auko har bakina baya rufuwa kan murna,to Allah ya raya mana su akan sunna, sae dai phone d'ina fa ka tuna min kmr na manta ta a bathroom bcs zan shiga wanka aka kirani na shiga da ita kuma vibrate kawai take,, eyyah that's y.

suna shiga Afrah ta shimfed'e suhailat ta kai hannu da bisimillah ta d'auki jaririn Amrah mai kyau dashi kmr ubansa ,murmushi tayi tace"wlcm to d world of Islam Allah ya raya mana kai akan sunna, fu'ad da ya shigo yace"amin"tare da shimfid'e suhail kusa da suhailat ya kar6i jariri kan cewa zai kaiwa Farhan ya ganshi dai dai Amrah ta fito bathroom d'aure da towel yace"dear kinyi wankan yanda ya dace ko sai nazo?nayi shine abinda tace snn ya fita Afrah tace"su Anti Amrah dai an zama babba yau anji qiris .....wlh kmr kin sani naji qiris.... Au da wahala kenan ,bari kedai tunda muka dawo na fara jin naquda nayi shiru ban snr dashi ba , yaga na kasa yin bacci kuma sae fira yake min bana iya bashi amsar kirki sae kawai ya tsaya yana qare min kallo inda cikin en mintina ya fahimtar dashi naquda nake yace"na tashi muje asibiti nace masa bacci nkeji sbd kedai wani irin bacci nake jin yana fizgata ,sae kuwa nayi bacci abuna amma yana tashi na sllr asuba sae naqudar ta taso gabad'aya baji ba gani har ya had'a mana kayan zuwa asibiti se na haifu abuna .......huh!sannunki,hm ni ko godiya ban ma uncle ba, name kenan?ke ko har sae na fad'a na haifu a gida ai kinsan shi zai yi wahalar gyran wuri da yiwa baby boy wanka sauqina d'aya ba wata qazanta tass na haifo yaron , kankana da rake sunyi aiki dmn kinsan nasha su kmr hauka kuma kinsan wankin ciki suke had'a da tamarind juice da na mayar kmr ruwan shana,to anti tamarind sae jikin ki ya 6aci kina tsaye, cab!nifa na shirya kaina tun a bayi tufafi kawai zan sa.

Tana gama shiri wayarta ta shiga ringing koda ta duba Abbanta ne bayan sun gama waya, ta ajiye wayar tana murmushi tace"Abba kenan yanzu fa business ya ha66aka har ko waya yake yana magana da mutane"Afrah tace"ai ni naga alamar business d'inda yake ya ha66aka sosai wnn tsadaddiyar motar da naga yana shiga, hm kedai bari wlh Alhmdlh Abba ya gode Allah wasa wasa fa ya fara business d'in nan cikin qanqanin lokaci Allah ya ha66aka abun inda yanzu har Abba zai koma gida ya taradda mutane a bakin qofar gidansa suna neman jiran taimako.....wai don Allah? Wlh kinsan fa Abba kalar manya ne tun baya da komai zaka d'auka ko hamshaqin mai kud'i ne sbd yanayin halittar jikinsa lumui lumui ,to bare yanzu da kud'i ke d'an shigo masa kuma yana shiga babbar mota ai dole ya taradda mutane a qofar gidan sa,Afrah tace"kai amma Alhmdlh amma dai ya daina zuwa asibiti ko don naga zuwanda nayi kusan sau biyu ban ganshi ba? Kai tun ya daina aiki asibiti dmn business d'in nan fa bazai barshi ba sbd yanzu masu kud'i sae siyan kayan gini suke suna ta gina gidaje suna bayarwa haya inda tuni har ya biya banki kud'in su da ya ciyo bashi yaja jari,,hmm kinsan uncle ko kad'an bai ji dad'in bashin nan da Abbanki yaci ba,Aa gaskiya ni banga laifin Abbana ba ,wai shi uncle sae yace komai Abba keso ya tambaye shi zai bashi a kyauta shi kuma Abba baya son haka shiyasa yaje banki ya ciyo bashi ba tare da uncle d'inki ya sani ba,ni yanzu abu d'aya ke damuna da Abba shine tun ba yau ba nake son yayi aure kullum sae yace min yaji zai yi sae kuma naji shiru kmr an shuka dusa ko kwanakin baya ina albishir d'inda nace bazan gaya miki ba? Eh, yauwa to cemin yayi zai yi aure amma wai yanzu kwanaki da na tuntu6e shi kinsan me yace? um um sae kin fad'a ,wai bai ma fara nema ba at all bai ma san taya zai tunkari mace ba,dmn ganin yake duk maccen da ya snr da ita matsalar shi ta rashin haifuwa baza ta yarda ta aure shi ba kmr yadda yasha gwagwarmaya a baya, haka ne fa but kinsan tunanin da ya fad'o min kai tsaye shine y not Abbanki da gwaggo su had'a kansu su auri juna tunda dukkansu basa haifuwa......ke Afrah!...um um to meye a ciki ko so kike Abbanki yayita zama ba aure ne har azo a fara masa wani banzan tunani can dmn kinsan yanda Abbanki yayi kud'i kuma yake da kwarjinin da duk wanda yaji cewa bai da aure sae ya kwana da mamaki,kamar yanda duk wanda yaji gwaggo bata da aure sae ya fita da tsegumi a gidan, dmn da Abbanki har gwaggo ba mai kalar tsufa a tare dashi sbd kyawon jiki da Allah yayi musu kuma sam ba mutunci bane ace cikin su ba mai aure dole kuwa abun ya zamo abin tsegumi, kuma naga akai akai suna yawan waya da junansu suna gaisawa ,Amrah ta sauke numfashi tace "nifa kinsan gwaggo ko maganar aure bata so a mata sbd yanda take matuqar son mijinta marigayi da har ko yaushe ta tuno da mutuwar sa sae ta zubar da qwallah,haka ne fa kin kashe min jiki dmn uncle ba irin nacinda bai mata ba amma taqi tayi aure ko Abban uncle fu'ad da yake yaya a gurinta yayi nashi ya gaji ya daina ya zuba mata ido shiyasa ma baki cika jin tana maganar sa ba sbd fushi yake da ita,amma in Allah ya yarda sae na zamo silar auren gwaggo da Abbanki inshaAllah ,tayaya Afrah? Kedai bari uncle zan fara tuntun6a tukun komai ake ciki zaki sani, to Allah ya tabbatar da Alhairi, Amin.

Knocking suka ji bayan sun bada izinin shigowa fu'ad ya shigo d'auke da jaririn sa a kafad'a yace"ku fito muje"kallon juna sukayi ita da Afrah tace"uncle bamu shirya ko kayanda zan tafi dasu ba fa ,to me kukeyi tun snn...koda yake ai ba sai na tambaya ba nsn da kun had'u bakuda aiki sae srt ,amma yanzu kam don Allah ku ajiye srt a had'a kayan nan na maida ke gida mom ta matsa sae kirana take nayi na maida ki gun gwaggo ki samu kulawar da ta dace, to uncle inshAllah 30 mnt sun isa kaji, to shikenan , ya fad'i haka ne kafin yake fita.

Koda 3omnt yayi har sun kammala shirya komai sae gashi ya sake shigowa baby boy na kuka ya tashi daga bacci dmn tunda aka haifeshi fu'ad ya mai wanka bai ko sha mamma ba yayi bacci shine sae yanzu ya farka yana kukan yunwa. Fu'ad ya jawo hannun Amrah ya zaunar da ita tare da miqa mata baby boy yace"oya ciro mamma ki bashi yasha .....pls uncle bari muje gida mana.... What!yarona najin yunwa kice sae anje gida keda mom ne inta jiki dmn ina cikin waya da ita yaron ya tashi yana kuka shine tace a kawo shi kuma yanzu zata kira taji in ya fara sha, don haka yi sauri kar ta kira ta ji bai fara shaba ta min fad'a. Kmr tace wani abu sae kuma ta fasa ta shiga bawa yaron mamma ta yanda ba a ganin mamman sosai sbd d'aga rgr ta tayi ta qasa ba ciro mamman tayi ta saman rigar ba. Duk irin zafin ciwon da take ji haka ta jure bata nuna ba sbd tsn fu'ad zai iya shiga damuwa ne idan ya fahimci tana jin ciwo. Wayar fu'ad ce tayi qara ya d'aga yace"mom eh ya fara sha ok to gata" nan ya d'ora waya kan kunnen Amrah inda cikin ladabi take waya da mahaifiyar tashi kamar suna kusa . Bayan sun gama fu'ad ya kar6i wayar ya tashi yace"zan dawo na kar6i yarona idan ya gama sha" kafin ya fita ne Afrah tace"pls uncle fu'ad idan zaka dawo d'aukar baby boy kace da uncle yazo dan Allah ya d'auka min d'ayan yaran nan sbd bacci suke bazan iya d'aukarsu su duka ba kuma ga kaya ,yace"ok to ku bani kayan ma na fara ragewa.

Ya d'auki kayan ya fita dasu.

Tafe suke su Amrah cikin motar su haka ma su Afrah . Suhailat dake bacci kan jikinta ce ta tashi sae kuka take tana son mamma dmn sae tura hannunta take qoqarin yi cikin rgr Afrah,Afrah ta d'aga ta sama tana fad'in"sorry habibtee suhailateee!Farhan yace"ba wani Habibtee ki bawa yarinya mamma tasha kafin ta tayar da suhail ya hana min driven cikin dad'i "nifa bana son shayawar a mota sae mun isa gida tukun ,idan kuwa ta tada suhail zan baki shine suyi ta miki rigima kin san dai halinsu, naji ba komai zan iya dasu ai ,ta qarashe maganar cikin dariya dmn tasan har kuka take idan suka tasa ta gaba suna mata rigima. Shima Farhan dariya yayi yace"to wa nasha kamawa a d'aki yara kuka ita kuka ba mai kama wani ? Oho wata qil mafarki kayi......waini waini kaina ga cikin ku ban huta ba kun fito ma ban huta ba, Farhan ne yayi maganar cikin qwaiqwaiyon murya irinta ta Afrah idan tana kuka yara sun tasa ta a gaba" Dariya kawai tayi ta ci gaba da yiwa suhailat wasa har suka isa.

Sosai gwaggo ke kula da Amrah da yaronta kamar yanda ya dace,haka ma ko yaushe Fu'ad na zuwa ya kawo ma Amrah da yaron su ziyara. ranar suna yaro yaci sunan *Najeeb* akayi biki bidiri har umman fu'ad ba'a bari a baya ba dmn sae da taxo.

Bayan kwana 2 da biki. Afrah ce kwance ita da Farhan suna fira suhail da suhailat na kan d'an gadon su suna bacci Afrah ta birgino a hankali kan jikin Farhan tace"uncle wata shawara nake son muyi"da kulawa yace"tame kenan ?wai gani nayi me zai hana gwaggo da Abban Amrah su had'a kansu suyi aure tunda ba mai haifuwa a cikin su"shiru yayi yana nazairi tace"uncle ko basu dace bane?sunyi matuqar dacewa my Afrah, ba don komai ba sae don kinga Abban Amrah duk wanda ya kalle shi ba zai ta6a tunanin yasan wani abu talauci ba a hakan ne ma lokacin da ya fara min aiki a asibiti wasu suka d'auka ko mahaifina ne kemin sharar office har abun ya zama tsegumi sosai ga wad'an da basu san cewa iyayena basa raye ba hakan yasa nace ya bari na bashi kud'i yaja jari yayi wata sana'ar yace shi sam yafi son aikinda na d'ora shi akai kuma taimakon da nakeyiwa Amrah ya isa ya gode min, nayi nayi dashi yaqi se cewa yayi indai en tsegumi ne na rabu dasu sa gaji su bari. Haka kuma Abban Amrah mutun ne mai yawan ibadah kamar gwaggo hakan yasa nake tunanin sun dace duk da cewa gwaggo kalar matar manya ce amma ai Alhmdlh tunda shima haka yake kuma gashi yanzu ya kama sana'a mai kawo kud'i nan take ko kuma nace sana'ar ta kar6e shi,sai dai gwaggo ce matsala dmn baza ta amince ba kinsani, but ka dai lalla6ata kuma duk sallah mu riqa addu'a Allah yasa ta amince, to shikenan Allah ya shiga ciki ya kuma sa Alhairi ne,Amin.

Washe gari farhan ne ya shigo d'akin Afrah ya samu tana shirya ma yara, suna ganin shi suka tafi jikinshi kallon yaran kawai yayi ya d'an riqa hannunsu yana shafa bayan su ba kullum da in sunzo jikin sa ba zai d'auke su da murna yana d'aga su sama suna dariya, hkn yasa Afrah ta fahmci akwai damuwa a tare da shi ,jiki sanyaye Afrah ta zauna kusa dashi ta ta6a jikinsa ya kalleta yace"yadai ?uncle baka da lafiya ne? Lfyta lau gwaggo ce tamin fad'a kar na qara mata maganar aure idan har ba so nake koda za'a wayi gari ta bar mana gidan ba, ba kuma zamu qara ganin ta ba. Wani irin abu Afrah taji da ya qara sa jiknta yayi sanyi tace"shikenan uncle dan Allah kar qara ce mata komai ,tayi hanzari zata bar gurin sbd kukanda ke qoqarin zo mata,Farhan yayi saurin jawota jikin sa sae dai bai hanata kukan ba taci gaba dayin abinta kan qirjinsa can ya d'ago ta yace"duba suhail da suhailat yanda suke kallon ki ita suhailat har da wani le6ace baki kmr zata yi kuka, mamaki ya kama Afrah had'e da dariya tace"wlh uncle na gaya ma yaran nan sunyi saurin wayo jifa kuka zatayi ganin inayi kuma nayi dariya ita ma tayi dariya,barikallah kin sa ma yarana ido ke baki san yara nada wani abu ba duk abinda suka ga anayi suma qoqarin yinshi suke koda basu san mene ne ba, duk da haka dai uncle suhailat tafi sona ba kamar suhail ba ,Afrah kenan mace ce tafi tausayin uwa kuma kina nuna musu banbanci ba kamar yanda nake musu ba kin fiye kula suhailat ko mamma ita kike fara ba kafin shi wanka ma haka idan kuka suke kinga damar ki d'auki suhailat kice Raheema tazo ta d'auki suhail ,hkn da kike yana qona min rai ba kad'an ba kuma ba abune mai kyau ba wnn dmn raba kan 'ya'yanki kike shirin yi baki sani ba, kmr tayi kuka tace"uncle nifa ba ina yin haka bane don nafi son suhailat sae don ganin ita mace ce tana da rauni kuma idan tana kuka ba lallai bane ta yarda taje gun wani sanin kanka ne suhail ya fita haquri kuma duk wanda ya tara masa hannu zai je, amma kayi haquri zan gyara inshaAllah dmn nafison su taso kansu a had'e . Farhan yace "to Allah ya had'a mana kawunan su tace"amin"snn ta koma jikinsa ta lafe tana tunanin hali irin na gwaggo, farhan yace "baki gama shirya yaran ba fa kinsa musu waduna ba riga, to basu bane suna ganin ka suka qi tsayi,oya suhail zo a qarasa shiri ko, ba musu yaje dmn hanunwanta da ta tara tana kallon shi ya bashi damar kiran sa take ,tana d'aukar shi suhailat ta ajiye kuka ita ma a d'auketa Afrah tayi murmushi tace"uncle see ur dota kaga son kai irin nata ko ta nuna suhaila da yatsa tace"kin barin son kai to sae na gama shirya shi ko zan d'auke ki,kuka ta ajiye taje jikin Farhan kmr taji me Afrah ke fad'i, Farhan yayi murmushi ya d'auketa ya cira ta sama yana cewa "suhailan mama bakida gaskiya ai ba ke kadai ce 'ya ba kuma kin sani. Daga haka yayita cira ta sama yana mata wasa sae dariya take, suhail na gani ya bar jikin Afrah dake qoqarin sa masa hannayen riga ya tafi sae sauri yake yana qyalqyaltar dariya har yaje gun Farhan, Afrah tace"ji kuma ba mai son yaga ana yiwa d'an uwansa wani abu ba a mai ba"Farhan yayi dariya ya qarasa saka ma suhail riga snn ya kar6i ta suhailat ya sa mata.

Yau kusan sati d'aya Afrah da Farhan sun sauyawa gwaggo kmr had'in baki da d'ayansu ya shiga 6angarenta gaisuwa kawai ke had'asu su fito ba wani sakin fuska bare zancen zama ayi fira ,duk da Amrah na gidan ba wani zama Afrah keyi ba take komawa 6angareñta. hkn ba qaramin rashin dad'i yayiwa gwaggo ba duk da tasan dalilin da yasa suke mata hakan.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull