Kenza eBookz

Afra ko amrah complete - Chapter 33

Afra ko amrah complete - Chapter 33

Afra ko amrah complete Chapter 33: Afra ko amrah complete Chapter 33. Washe gari Farhan ya tashi Afrah tayi sallah tana tashi zaune tace"pls uncle kayi…

4,481 words

Washe gari Farhan ya tashi Afrah tayi sallah tana tashi zaune tace"pls uncle kayi haquri ystday night naje canza kaya ne shine koda na dawo har kayi bacci"ba komai Afrah shine abinda yace snn ya fita.

Ta d'anyi mamakin ganin baiyi fushi da ita ba ta dai basar taje zuwa bathroom.

Koda ya dawo tana kan sallaya tana addu'a bayan ta tofa tayi mishi ina kwana ya amsa ba yabo ba fallasa ,ya d'auko qur'ani taje kusa dashi ta zauna tace"yauwa uncle saukar da mukeyi a sati sati kaga munyi missing 3weeks ba muyi ba na d'auko nawa qur'ani mu fara ta satin nan? A natse ya kalleta yace"meyasa ba ruwanki da damuwa ta Afrah?qwalla ne suka ciko mata ido tayi saurin duqar da kanta yaci gaba da cewa"na fahimci rayuwarki ko shekara nayi ban neme ki ba ba ruwanki harkar gabanki kawai kike ,ba haka ake rayuwar aure ba Afrah ki gyara kinji. Daga haka yayi shiru yana kallonta sae hawaye take yace"meye na kuka kuma ko baki ji dad'in magana ta bane?girgiza kanta tayi tace"ba haka bane nasan na shiga haqqin ka da yawa pls kayi haquri uncle,ya jawota jikin sa yace is ok ki daina kuka ba komai ya wuce bari mu karanta ko sura d'aya ce sae ki bani abuna ko? Murmushi jin kunya tayi tare da gyad'a masa kai. Shima murmushi yayi snn suka fara karatun.

Sha biyun rana suka farka daga nannauyan baccin da sukayi sae miqa suke Afrah ta rungumo Farhan a hnkli tace"uncle muje muyi wanka kar zuhur ta same mu dmn qila d'aya tayi, sha biyu ne yanzu bansan dai wane tunani gwaggo zata yi ba yau bamu je mun gaisheta ba da safe kmr yanda muka sava ko yaushe ,nifa uncle a d'azun har knocking naji...yaushe? shiru ta mishi tare da kauda kanta gefe hkn yasa ya gano time d'inda take nufi, yayi murmushi yace"to ya akayi baki snr dani ba ko ba kya iya magana a wnn lokacin? Tashi tayi tare da bedsheets a jikinta tace"nidai ban iya yanda ka iyaba kuma ma ai gara ni har naji knocking d'in,yayi miki kyau akwai rnr da zan kama ki ne ai,dariya kawai tayi ta shige bathroom ya bita sukayi wanka suka fito sun gama shiri kenan suka ji knocking Afrah taje ta bud'e ,Raheema mai aikin gwaggo ce a tsaye riqe da kula ta gaida Afrah snn ta miqa mata kular tare da fad'in"gashi gwaggo tace a kawo snn tace ko lafiya taji ku shiru yau? Kice mata lafiya lau bacci mukayi amma gamu nan shigowa.

Koda ta shiga ciki ta bud'e kular tace"kai gwaggo na sona wlh abinda nake so shine tamin mayemayen shinkafa da ganyen sure,ta rufe kular ta kalli Farhan tace"uncle muje muci don ni yunwa nake ji sosai bazan iya jira har ayi sallah ba,yace"nima yunwar nakeji nan suka je downstairs kan dining suka ci. Bayan sunyi sallah ne suka je 6angaren gwaggo suka gaishe ta tare da yi mata godiya kan abincin da ta aika musu.

3weeks later Afrah ce keta roqon Farhan kan yaje da ita asibiti bazata yi rashin ji ba ta samu da qyar ya amince suka tafi. Tafe suke cikin asibiti suka had'u da matar da Afrah ta ta6a tsarawa d'auke da cikinta da har ya soma fitowa Afrah tace"lah Anti kin gane ni? Matar tace"ai bazan manta ki ba,kodan hasashenki da ya zamo gaskiya a gare ni ba qaramin farin ciki nayi ba na kuma gode Allah sosai dmn ya bani abinda na jima ina nema, ta kawo qarshen zancenta kenan idonta ya fad'a kan cikin Afrah tace"ikon Allah ciki ne nake gani a tare dake ko kuwa? Mugun kunya Afrah taji tayi saurin zuwa bayan Farhan ta 6uya ,mtr tace barkalla wnn cikin da gani tun lokacin had'uwar mu kina d'auke dashi wato kenan da auren ki er yarinya dake abin gwanin sha'awa ,matrka ce kenan doctor? Farhan yace"eh matata ce, to Allah ya baku zamn lafiya da zuri'a d'ayiba Farhan yace "amin mungode" Tayiwa Afrah sae anjima ta wuce.

Bayan sunje office Farhan ya kalli Afrah da ta wani sha toka cike da son tayi kuka, yace"me akayi kuma? Ba kai bane kafin mu fito na tambaye ka ana gane cikina ya fito kace min a'a,amma Afrah ai kinsan da wasa nake miki inace kinga yanda cikin nan ya qara girma zama d'aya ba sae kin tamvaya ba ma kinsan dole a ganshi, to ba qatoton hijabi na saka ba kuma rgr jikina mai 6oyon ciki ce fa,ni bazan ma qara fita ba daga yau, ta qarashe maganar cikin kuka ta tashi ta tafi daga ciki gurin hutawa ta kwanta tun tana kuka har tayi bacci. Har ya gama aikin sa Afrah bacci take. Yaje ya sameta ya durqusa kusa da ita yana kiran sunan ta yace"tashi muje gida "ta tashi tace "ni bazan fita ba sae kowa ya watse ,tashi muje na baki briefcase ki riqa sae ki kare cikin ki da ita ta yanda baza a gane ba, ba musu ta tashi suka fito suna zowa parking space suka had'u da fu'ad shi da Amrah wacce kallo d'aya zakayi mata kasan bata da lafiya dmn wani irin haske tayi da rama, da mamaki Afrah tace"Amrah lfyr ki kuwa, duqar da kanta tayi ta kalli fu'ad ta gefen ido, murmushi yayi ya kauda idonsa sbd ya gano me kallon ke nufi, Afrah tace"Amrah ina magana dake kin min shiru ,ba komai d'an zazza6i nayi amma naji sauqi, shine Amrah duk wyr da muke yi baki gaya min ba, sorry naga ba wani zazza6i mai qarfi bane, jin abinda tace yasa fu'ad ya kalle ta bai ce komai ba dai dmn ysn bata son tayar da hnklin er uwarta ne amma ta darji ciwo ba kad'an ba ko yau tausayinta yaji sosai ganin bata iya komai ga kuma kad'aici ita kad'ai a gida shine yazo da ita ko abin zai mata sauqi. Jirin dake shirin d'ibar Amrah ne yasa tace"bari muje gida Afrah ma qarasa maganar kinji,can gidan mu ko kuwa? Eh can mukayi dama.

6angaren gwaggo suka tafi gabad'ayan su,fu'ad na gama gaisawa da gwaggo ya tafi, shima Farhan ya tafi 6anfaren su dmn ya samu ya watsa ruwa. Afrah kuwa Abinci suke ci ita da Amrah bayan sun gama ne Afrah ta jata zuwa 6angaren su sbd tana son ta d'an watsa ruwa ita ma. Da mamaki Amrah ke kallon Afrah dake d'aure da towel zata je bathroom tace"kai!barikallah ya naga cikin ki ya girma hk zama d'aya ?hm bari kedai nima na tsorata da girman sa sae wani nauyi da ya qara min shiyasa ko dogon tsayi bana son yi ynx,Amrah tace"ko dai en biyu kika kwaso mana ne? Ko en uku ba, cewar Afrah wacce ranta yayi mugun 6aci ta wuce bathroom ba tare ta sake cewa komai ba. Har ta fito shaye da toka Amrah tace"ke daga kawai na ambaci en biyu sai kawai ki tsiri fushi dani? To ya zaki ce min haka ,yama zan iya haifuwar en biyu idan ba so kike na mutu gurin haifuwa ba mtsw ni ko da wasa kar ki qara ambata min en biyu bana so, idan Allah ya baki ai sae kice ba kya s.......amai ya hanata qarasa mgnr ta tafi da gudu sae bayi, da taimakon Afrah ta wanke bakinta ta fito ta nemi guri ta kwanta sbd jiri ba zai bar ta iya zama ba,da kulawa Afrah ke kallonta tace"Amrah ciki ne dake ko? Shiru Amrah ta mata dmn tasan ciki ne da ita amma kunya take ji a sani shiyasa ta roqi fu'ad kan kar ya snr da kowa. Tace"dake nake magana ?haba Afrah wane irin ciki ni ki barni na huta dan Allah,hm yrinya ko kiso ko kar kiso ciki ne dake ko hasken da kikayi kad'ai ya ishi ya fhmtar, nifa ba ciki bane shawara ce dani don kar kije ki snr da gwaggo nasan halinki, hhhh nayi wnn yarinya indai ciki ne baya 6oyuwa gamu gani dai tunda kince bashi bane.

Yinin rnr kafin Amrah ta koma sae da kowa ya fahimci ciki ne da ita sbd yawan aman da take yi da kuma jirin da ke yawan d'ibar ta, gwaggo baki yaqi rufuwa sae murna take. Afrah kuwa sae tsula ma Amrah tsiya take tana mata dariya.

Tun da labari yaje gun iyayen fu'ad ko yaushe mahaifiyar Fu'ad cikin kiran wyr Amrah take tana tambayar lafiyar jikinta. A qarshen satin sae da taxo daga Abuja takanas don kawai tazo ta duba Amrah wacce Alhmdlh ynz jiki yayi sauqi. Sosai suke shiri da gwaggo shiyasa tayo mata tsarava kala kala ta kawo mata ,bayan wacce ta ba su Afrah ,Amrah kuwa ba'a zancenta dmn har kayan wasan baby ta siyo mata kan tsananin farin cikin zata sami jika gun d'anta qwaya d'aya tal da Allah ya basu.

Sannu sannu rayuwa keta tafiya inda yanzu cikin Afrah watan sa tara cikin da yayi girman wuce misali da duk wanda ya gani sae yayi mata tunanin en uku ne a ciki ba ma biyu ba. Yanzu bata da ikon saukowa downstairs sae da taimakon Farhan gashi tunda cikin ya tsufa wani zafin bala'i ya taso mata da bata jin sanyin Ac zai mata maganin shi ga Farhan ya hanata shan qanqara duk da ba irin kukan da bata yi ba kuwa har tana cewa don bashi ke d'auke da cikin bane, shi kuma ba don komai ya hanata ba sae don gudun kar unborn child d'insa ya kamu da cinyon sanyi sbd shan qanqarar take tmkr Allah ne ya aikota. Yanzu bata da gurin zaman da ya wuce garden kusan ko yaushe tana can bata da wani aiki sae shan fresh air sallah da komai can takeyin abinta sae ta gama shan iskan tane take komawa daga ciki in ta shiga kuma ba wani aikin take yi ba sae kwanciya tayi kallo sbd bata iya aikin komai hatta girki yanzu a 6anggaren gwaggo ake kawo musu abinci ,kuma idan Raheema ta gama aikinda take yiwa gwaggo, gwaggo ta kan izo ta nan 6angaren su Afrah sbd ta riqa taimakawa Afrah da wani abu.

Guraren bayan la'asar gari yayi luf kmr za'ayi ruwa Afrah ta matsu ta fito taje garden shan iska dmn tasan yanda yanayin garin yayi iskan yau zai fi na kullum dad'i. Farhan ya fito daga gurin wanka cikin sauri yace"sorry yau na shiga time d'in fitar ki zuwa garden ko? Gasky kam na matsu banje ba sae jiran fitowar ka nake ,ko mai bai tsaya shafawa ba ya nemo jallabiya ya saka yaje ya kamata ta tashi tace"waih!uncle nauyi"kallonta yake da kulawa yace"sannu kinji"ta gyad'a masa kai cikin shagwa6a tace"Allah babyn nan naka nida shine in ya fito ya wahaldani ba kad'an ba wlh duk na tashi tsaye sae naji kmr na fasa ihu don nauyi, cike da tausayinta yake ta mata sannu yayinda suka fara tafiya har suka fito gun staircase Afrah tace"plz uncle kafin mu fara sauka a bari na d'an zauna na huta, bari na d'auke ki..... cab! wlh a'a inada nauyi kbr shi Allah ma ya biyaka don kana qoqari dani ba kad'an ba, murmushi kawai yayi yaje zuwa d'aukar ta tayi sauri zata zauna sbd har ga Allah bata son ya d'auke ta ya wahala,wani irin ihu ta saki kafin takai zaune tace"na shiga uku uncle zan mutu bayana da cikina zasu tsage ah!wayyo uncle zan mutu wlh! dan Allah ka taimake ni uncle!duk Farhan ya rikice yana kallon Afrah dake durqushe tana ihu sae fmn yarfi take da hannu. Cikin rud'u ya d'auketa ya kaita downstairs ya ajiye ya tafi 6angaren gwaggo ya snr da ita dmn ya fahimci haifuwa ce tazo mata kai tsaye.

Bai jira gwaggo ba ya dawo ya d'auki Afrah ya saka a mota gwaggo na isowa suka wuce asibiti. iya wahala Afrah tasha har ana tunanin yi mata aiki sbd jikinta kwata kwata ba qarfi bata iya yunqurin haifuwa ,Allah da ikonsa har ana gav da yankata ta suntu6o 'ya'yanta guda biyu boy en girl da sukayi bala'in kama da Farhan tu6ul tu6ul dasu jawur kmr a qwanta jini ya fito. Byn sun koma gida rungume take a jikin Farhan tana kallon 'ya'yan da ta haifa da idanuwanta da suka qabe kan kuka,Farhan ya kai hannu ya d'auki yaran ya rungume su qam a qirjinsa yana mai gode Allah da ya bashi jinsi biyu at d same time.

*Billy giro 😊&Futha Luv💅🏻* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:23PM, 11/30/2016] Billy Geeero: *[11/27/2016]* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*

*Futuhatulkhair.WordPress.com*

*```🏅93🏅```* Ya ajiye yaran yana kallon Afrah da ke qoqarin kwanciya, yace"Afrah tashi ki d'anci wani abu tukun kafin yaran nan su farka su buqaci mamma. Fasa kwanciyar tayi ta zauna ya jawo stool tare da ware ledar da ke saman shi, naman rago ne gasasshe mai kyau da shiga rai, ya d'auko tsoka d'aya yakai a bakinta, bata bud'e bakin ba sae jinginawa tayi a jikin sa tace"uncle ni tea nake son na sha, ba musu ya had'a mata tea mai kauri ya bata tasha. Sae ga gwaggo ta shigo d'auke da kula ta ajiye tace"ka qoqarta ta cinye abinda ke ciki kaf har romuwar"yace"inshaAllah gwaggo snn ta fita. Farfesun nmn rago ne da aka had'a shi da ganyen shuwaka. Ya zuba mata ya fara bata kenan ta wani 6ata fuska yace"mene ne ba dad'i? d'iba tayi ta sa mai a baki yaci yace"wai shuwaka ?tace" eh mana shine har gwaggo ke fad'in na cinye duka gsky ni bazan iya shan farfesun nan ba, amma Afrah ni dad'in sa naji ba wani d'aci sosai, to uncle ai kasan ko ya d'aci yake bana son sa ,haquri zakiyi Afrah shuwaka abu ce da take da matuqar amfani a jiki musamman ga wacce ta haifu,kiyi haquri kisha kinji,maqale kafad'a tayi tace"gaskiya uncle bazan iya sha ba, lallashin ta ya shiga yi taqi kan dole ya shiga bata sae kuka take tana ci har sae da tayi rabi snn ya barta yakai hannu yana share mata hawaye cikin fushi take son barin jikin shi ya riqo kumatunta Yace"kar kiyi fushi mana, bari na rage miki d'acin kallonsa take yana matso fuskar a hankali har ya had'e bakinsu can ya zare yana kallon yaran sa da suka tashi daga bacci ,ya maida dubansa gareta yace"na qara rage miki d'acin? ta sadda kanta qasa tace"Aa d'acin ya rage sae ma d'an wani zaqi da nake ji,, yace"to kinga yaran mu sun tashi suna buqatar su sha mamma, ni ai fushi nake yi dasu tunda suka wahalarda ni sae dai susha madara ba dai mammana ba, cikin shagwa6a take maganar yace"yarana ne fa Afrah ki basu ko don ni, murmushi tayi tare da nuna shi tace"don kai? Ya gyad'a mata kai yana kallon cikin idonta tace"to zan basu amma ka fita kunyar ka nake ji"kai Afrah ni kike kunya yau? Allah da gaske nake uncle. Ya tashi tare da fad'in "ok feed them well n secure"

Yana fita ta d'auki mace cikin so da kulawa take kallonta ta samu da qyar ta iya fara bata sbd ciwon da take ji haka dai ta jure ta ci gaba da bata, ta gama bata ta d'auko namiji zata bashi kenan taji za'a shigo tayi saurin mayadda mammanta ta gyara rigar ta, Amrah wacce ta shigo tace"ke nice fa huta da 6oyon mamma "Afrah dai bata ce komai ba har Amrah taje ta zauna kusa da ita ta d'auki baby girl tana kallo cike da sha'awa tace"wow barikalla snn ta kalli Afrah tace"sannu kinji kinsha fama"ta kalli baby boy dake jikin Afrah tace"ki bashi mamma mana kinga kuka yake qoqarin yi, Afrah tace"ke nifa kunya nakeji na shayar a gaban kowa don ko uncle na kasa shayarwa a gaban shi"to wai me? Wlh wai kunya nakeji yau nice uwa ina shayarwa sae kace a mafarki, hm Afrah kenan daga kawai Allah ya kaiki gaba abin kiyi feeling as kin zama babba,au haba to daga yau Anti Afrah sama da qasa, ta riqe kunnenta tace "bari ma na miki hud'ubar da ban miki ba, kar inji kar in gani aure ba abin wasa bane ki bi mijinki sau da qafa,yi nayi bari na bari,kuma shi zamn aure dole sae da haquri dmn duk nan da kika ganmu da haquri mukeyin zaman aure amma fa idan ya 6ata miki rai ki nuna masa 6acin ranki, uncle kike kira masa amma da ya 6ata miki rai ce masa kai fu'ad! dan yasan ranki ya 6aci dgske ehe!dariya Amrah tayi tace"Allah ya shirye ki" gaskiya na fad'a miki fa namiji idan baka nuna 6acin ranka zai maida ke bora duk abinda ya kwaso sae saman kanki,to Anti Afrah naji sae kace ke kiran sunan uncle d'in naki kike idan ya 6ata miki rai, dariya tayi tace"ai kinsan tun tashi na ko da wasa bana kiran sunan uncle dmn sunan babba ne a gurina ina girmama sunan ba kad'an ba,Amrah tace"to ki dai shayadda yaron mutane kinga har ya fara kuka,nifa dagaske bazan iya shayar dashi kina kallo ba sae dai na juya miki baya, ke kunya ne dake hln,na dai ji ko banda ita yau ina jinta. nan ta juya bayanta ta shiga shayar da yaron har sae da ya qoshi inda cikin wash da komai aka kammala bashi, Amrah ta shinfid'e baby girl ta kar6i baby boy sae ga gwaggo ta shigo d'auke da flask d'in kunu ta ajiye ta kalli Amrah tace"ke kin manta da fu'ad ne da kika barshi yana zaman jiran ki kai masa yara? gwaggo na samu tana shayadda su ne shiyasa sae ynz ta gama,to d'auke su ki kaimai shi kad'ai ne a falo bansan inda Farhan ya shiga ba ya barshi zaune shi kad'ai.

Kafin ta qaraso gurin shi yayi sauri yaje ya kar6i d'aya snn sukaje suka zauna ya kalli baby boy d'inda ke hannun shi yace"nima zaki haifo min mai kama dani, kinga Afrah ta haifo masu kama da Farhan,murmushi jin kunya tayi tace"ni duk ma na tsorata da jin yanda Afrah ta wahala gurin haifuwa sae tausayin kaina nake ji" kar ki damu kowa da irin haifuwar sa sae kiga kina bacci kin haifo min d'ana tashin ki kawai zanyi na nuna miki mai kama dani,dariya tayi tace"wlh da ana haifuwa haka da na fi kowa farin ciki,wai ina uncle ya tafi ya barka? Baqinsa zai shigo dasu tashi ki koma daga ciki bcs nan zai shigo dasu, ok to na bar yaran ko na koma dasu ?bar su mana ai su aka zo gani, ok bye, yace"bye dear"

koda Amrah ta koma d'akin sae ihun Afrah taji ta fito daga bathroom d'aure da towel gwaggo na biye da ita Afrah tace"gwaggo fa nayi wanka da dawowar mu,gwaggo tace ai na gaya miki kin d'auraye jiki ne kawai don na tabbatar bada ruwan zafin kirki kikayi wankan ba,to gwaggo wlh ruwan zafin da kika had'a min zafi ne dasu sosai. Farhan ne ya shigo ya same su yace"gwaggo je zuwa aikin ki nasan yanda zanyi da ita. Byn gwaggo ta fita yace"Afrah gaya min gaskiya tsakanin ki da Allah da ruwan zafin da ke gasa jiki kikayi wanka d'azun? Cike da son tayi kuka tace"Aa but.... Shiiii!ba sai kin d'ora da wata magana ba muje bathroom, nan yaja hanunta sae kuka take har suka shiga. Jiki sanyaye Amrah ta zauna sbd tausayin er uwar ta, bayan ta wahala gun haifuwa kuma rad'ad'in haifuwa na tare da ita ace ta shiga ruwan zafi. Fu'ad ne ya shigo d'auke da yara ya ajiye su kan bed yana kallon Amrah da tayi suku suku, ya zauna tare da riqo hannunta yana murzawa a hankali yace"dear what happen? Kan tace komai tayi saurin qanqame shi cike da jin zafin ihun Afrah da taji ,fu'ad ya d'ago fuskarta a hankali yana kallon idonta da suka cika tap da qwalla, yace"mene ne na kuka dear ?kana nufin baka ji ihun Afrah ba?naji amma nsn tana tare da Farhan kuma ihun da tayi ba zai wuce raki irin naku na mata ba ,ba wani don kawai abin baya faruwa daku shine komai mukayi kuce raki ne damu ba kwa ko jin tausayin mu, snn ko banza Afrah bata son ruwan zafi duk yanda suke zafin su take ji,qara rungume ta yayi yace"am sorry ai kinji ta rage ihu da alama ya rage mata zafin ruwan,bari na tafi ma kafin su fito,sae da yayi pecking nata snn ya tafi.

Afrah ta riga Farhan fitowa tana zuwa ta fad'a kan bed tana kuka mara sauti. Da damuwa ya fito yana kallonta yace"sorry Afrah tashi ki shirya kanki kinsan ba zai yu ki zauna haka ba yanzu jikin ki zai iya 6aci" Cikin shagwa6a ta fizge hannunta da ya riqo da niyyar tada ta zaune tace"ni ka rabu dani"ya kalli Amrah yace"fu'ad fa ko ya koma gida ,Aa yanzu ya fita kuma na maji kafin ya qarasa fita yana waya da uncle JB kan zasu shigo shida maman shi da matar shi nasn zai jira zuwan su,"ok tom"shine abinda yace ya tashi yana mai kallon Afrah ya fita.

Yana fita Afrah ta tashi ta shirya.

Guraren qarfe goma na dare Afrah ce zaune kan bed can nesa ta had'e kai da guiwo ga yara kwance a gefenta sae sharar baccin su suke. Farhan ya fito daga wanka d'aure da towel a qugunsa ta d'ago tana kallon shi da idanuwanta da suka cika tap da qwallah, Yaje gab da ita ya zauna yace"poppy luv wa ya ta6a min ke? ba gwaggo bace bayan ta tasa ni gaba na cinye farfesun en ciki mai had'e da ganyen shuwaka wai kuma shine tace kunnun da ta kawo d'azun a flask na tabbatar kafin safe ba komai, kisha ko kad'an ne ba sae kin shanye ba kinji,ta wani yamutse fuska tana kallon shi tace"uncle da ganyen shuwaka fa aka yi shi"eh amma zan sa miki madara a ciki sae kiji dad'in sha ko? Maqale kafad'a tayi yace"to so kike gobe da safe gwaggo taga baki sha komai ba taji ba dad'i bayan duk wahalar nan da tayi dake yau? um um bana son gawggo taji ba dad'i,to nasa miki kisha?gyad'a masa kai tayi, ya tashi yaje ya d'ibar mata kunun a cup yasa madara ya motse yazo ya miqa mata yayi zaune had'e da tagumi yana kallon yaransa cike da sha'awa , kur6i d'aya tayi ta 6ata fuska ta d'ago tana kallon shi taga sajen fuskar sa ya kwanta luf sae yayi mata mugun kyau kmr wani balarabe,shafo sajen tayi a hnkli, ya d'ago yana kallonta ta sakar mai murmushi tace"kayi min kyau uncle"

*Billy giro😊&Futha Luv💅🏻* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:23PM, 11/30/2016] Billy Geeero: 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*

*Futuhatulkhair.WordPress.com*

*```🏅94🏅```* Saurin kama cup d'in hanunta yayi ganin kunun zai zuba Afrah tace"sorry"no ai bai zuba ba, ya jawota ya zaunar kan jikinsa ya shiga bata kunun sae sha take tana kallon yaran har ta shanye kunun sbd ba wani yawa ne dashi sosai ba,ya ajiye cup ya zaro tissue ya goge mata bakinta wacce still idonta na kan yaran yace"kema suna baki sha'awa sosai ko?kunya taji ta kauda idonta tace"nifa uncle don sunyi kama da kaine nake kallon su"ba wani kedai 'ya'ya na sha'awa suke baki shine har ba kya son qyaftawa idan kina kallon su"turo baki tayi tace"nida mà ba ruwana dasu sunci arziqin kàmar ku shiyasa ma nake d'an kulasu" to naji dai gaya min meyasa kika ce na miki kyau, nima haka kawai naga yau kamin kyau ,menayi haske na qara ko qiba ko rama? Ammm kayi haske kuma kayi er qiba ,shi kawai?eh, to bari na gaya miki abinda baki sani ba shine basu suka sani nayi kyau ba farin cikin samun 'ya'yana ne,,, dagaske? Yep haka nake idan ina cikin matsanancin farin ciki baki ta6a lura ba?baka ta6a irin farin cikin nan ba taya zan lura, um um kin dai manta rnr da na fara samun ki as my wife, that's our first night nayi farin ciki ba kad'an ba,hm uncle kaidai kafi farin ciki akan yaranka dmn ni banga hk a tare da kai ba a wnn lokacin, taya zaki lura byn rnr guduwa kikayi"ni uncle kunya nake ji a daina zancen nan, naji kwanta kiyi bacci bcs u have to sleep. Ta kwanta ya tashi ya nemo jallabiya ya zuba ya d'auko sallaya tace"uncle ba yanzu xaka yi bacci ba kenan? Taya kike tunanin zan iya bacci yau ai sai dai na duqufa gun godewa ubangijina da ya axurtani da yara har biyu a lokaci d'aya,tayi murmushi tace"that's y i love u but idan ka kai time d'inda ya kamata kayi bacci dan Allah kayi bacci uncle sbd shi Allah har ko yaushe cikiñ gode masa ake baza a ta6a daina gode masa ba dmn yafi da hakan sae dai a kwatanta kawai,, to my Afrah get sleep. Nan ya fara sallah tun tana kallon shi har tayi bacci.

Bacci take mai dad'in gaske da ta jima bata yi irin shi ba, yara suka tashe ta ta tashi taje bayi ta dawo Tayi tsaye tana kallon yanda suke qoqarin ftr da sautin kukan su gashi ko kad'an bata son su tada Farhan. dabara ce ta fad'o mata taje a hnkli ta d'auki yaran sae Allah Allah take kar ta kadasu sbd bata iya d'aukar su su biyu ba wai ita a wautar ta duka su biyu zata runguma a hannunta kmr yanda ake d'aukar jariri d'aya, ba ma ta d'ora kowanen su a d'ayan kafad'ar ta ba ,ai kuwa kai tsaye taji baby girl ta sa6ule a hannunta ta fad'a kan bed sae kawai ta fashe da kuka sosai kan tsoratar da yayi ,firgigit Farhan ya tashi ya d'auki baby girl da sauri snn ya kalli Afrah wacce ta saki ido kan tsoro yace"me yake faruwa ne? Uncle sorry fad'uwa tayi sbd ban iya d'aukar su ba ,to meyasa zaki d'auke su su duka biyu ?kukan su naga yana so ya tashe ka ni kuma bana so dmn nsn baka jima da kwanciya ba shine nayi tunanin naje dasu living room na shayar dàsu, ajiyar zuciya ya sauke yace"my Afrah kar ki soma yin haka daga yau ki riqa zamnki a nn kina shayar dasu idan sun tashe ni ai yarana ne ba komai " Oya kar6e ta ki fara bata a samu tayi shiru, ta ajiye baby boy taje zuwa kar6ar baby girl ya kalli yanda idonta suka ciko da qwallah yace"ko ta samu buguwa a wani guri ne? um um kan bed kawai ta fad'a kuma ban ko d'aga dasu sosai ba dn ko miqewa tsaye ban qarasa yi ba,to ya naga kmr zakiyi kuka? tsoro ne kawai da naji. Ok sorry take her, ta kar6eta ta zauna ta bashi bai tana shayarda ita sae da ta koma bacci snn ta shimfid'ar da ita ta kar6i baby boy da Farhan keta fmn jijjigawa kan kukan da yake. Bayan ta gama ne suka sa yaran a tsakiyar su suka koma bacci.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull