Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 100
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 100: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 100. .........Maanal na kwance…
4,496 words
.........Maanal na kwance barcin wuya ya ɗauketa dan oga da kansa ne ya gama wajigata. Itako sarkin raki tasha kuka har ta godema ALLAH. Sam ta kasa sabawa, gabanta har faɗuwa yake ya nuna buƙatarsa a gareta. Zata biye masa a shan minti amma da anzo fagen fama ta fara kuka da roƙo. Shi ko ya zama kurma ya zama makaho har sai ya samu yanda yake so dan bai san ɗanɗani haukaci ba bai kuma san haƙuri ba. Kwana biyun nan har ƴar rama ta fara. Ko kuma ta gudu sashen Oum sai yata zarya ko Oum ɗin ta korosu sannan. Gaba ɗaya ta ƙagara weekend ɗin nan ta ƙare, idan aka koma aiki ta samu sauƙinsa ai tunda da rana babu dama. Oum data fahimci matsalar Maanal dan ramar da yarinyar ta fara ta fara tsaya mata a rai sai ta shiga haɗa abubuwa, ta kuma amso wasu hannun Hajiya Shuwa. Itama ta fuskanci irin wannan yanayin a hannun Abah, dan shima akwai fitina kamar AA ɗin, kai bama su kaɗai ba kusan duk mazan family ɗin Darma haka suke sai dai wani yafi wani. Gasu kuma ALLAH ya jarabcesu da son zama da mata ɗai-ɗai, shiyasa matan ke jigatuwa a hannunsu kafin su saba.. Kiran da Oum tama Maanal ɗin a waya ne ya farkar da ita, dan AA ya fita shi da Yaya Fawzan shiyyasa sai ita kaɗai. Muryarta kawai Oum ɗin taji ta fahimci mike faruwa. Dan dama tana anan sashen suna hirarsu AA yay kiranta a waya ta kawo masa wai fruits dan shi yana sashen Abah suna meeting shi da su babban Yaya. To daga kai fruits ɗin ne fa ya samu ya matseta a sashen sai da ya sauke damuwarsa sannan yay shirin fita da zasuyi da Yaya Fawzan ɗin. Ita kuma wahala ta hanata tashi dan barci ne ya ɗauketa sama-sama ma taji fitarsa. Cike da tausayi Oum ta girgiza kai, sai kuma ta ce, “Barcin yamma kike Baby?”. Cikin sanyin murya Maanal ta ce, “Eh Oum, amma na ma tashi gani nan zuwa sashen.” “Okay sai kinzo”. Oum ta faɗa tana yanke kiran. Itama Maanal tashi tai ta shiga bayi ta gyara jikinta yanda ya kamata, koda ta fito gashinta ta busar ta shirya cikin atamfa doguwar riga tai sallar la'asar da ake kira sannan ta gyara gadon da suka yamutsa ta fita. Ta nufi sashen Oum motar Momyn Nibras ke shigowa gidan. Maanal bata tsaya ba tai shigewarta, dan yanzu kusan kullum Momyn Nibras ɗin sai tazo gidan. Jiya da yamma har sabuwar rigima suka tafka da Mamy. Wani haɗaɗɗen gashin nama mai ruwa-ruwa Oum ta bama Manaal taci ta ƙoshi, sannan ta bata abubuwa na musamman data haɗasu da kanta kuma ita tasan sirrinsu dan sune take amfani da su. Har sai da Maanal taji kamar zatai amai sannan ta ƙyaleta. Daga haka suka cigaba da hirarsu. Su AA basu dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i. Anan suka yada zango sashen Oum sukai dinner aka ɗora da hira, hirar gaba ɗaya akan yanda bikin Fawzan zata kasance ne dan shi aka fara shirye-shirye, amma suna saka rana a haɗa dana Babban Yaya, sai dai ba'a yanke hukunci ba sai gobe idan ALLAH ya kaimu su Baba Sardauna zasuje Katsina domin ganawa da dangin mahaifin su Ameerah. Koda AA yace Maanal tazo su tafi catai ita anan zata kwana. Shiru kawai yay yana kallon ta, Oum kuma taƙi saka musu baki. Yanda AA ya tsaya yana kallonta mi Yaya Fawzan zai yi inba dariya ba. Harda ƴar waƙarsa ta neman tsokana. Aiko AA ya wuce ya tafi kawai ransa a ɓace. Babban Yaya daya bisa da kallon ƙasan ido ya ɗan murmusa a zuciyarsa. A zahiri kam fuskarsa babu alamar wasa ya kalla Maanal da itama ta kumbura baki ta kwanta a cikin kujera. A dake yace, “Lilly!”. Amsawa tai tare da tashi zaune. “Tashi kibi mijinki kinji, sai da safe”. Ji Maanal tai kamar ta fashe da kuka. Amma bazata iya ma Babban Yaya musu ba. Haka ta miƙe tai musu sallama ta tafi. Babban Yaya ya bita da kallon tausayi. Dan a ransa kawai yaji cewa ga abinda takema gudun. Cike da shaƙiyanci Yaya Fawzan da baya iya shiru shi ya kai bakinsa saitin kunnen Babban Yaya ya ce, “Idan baka saita fitinannen ƙaninka ɗin nan ba watarana ma nan Lilly zata dawo gaba ɗaya dan zugeta sanyi da kaina”. Fillo Babban Yaya ya ɗauka zai buga masa. Da gudu ya tashi ya fice yana dariya da faɗin, “Oum goodnight ”. Oum ta ce, “ALLAH ya tashemu lafiya.” Shima Babban Yaya miƙewa yay ya mata sallama. Oum ta amsa masa da kulawa shima, ta musu addu'a da sanya albarka. Koda ya fito sai yaci karo da Saheeba tsaye a ƙofar sashensu tana jiransa. Tamkar bai ganta ba ya ɗauke kansa. Da sauri tasha gabansa ta durƙusa. Tare da fashewa da kuma tana roƙonsa yayi haƙuri ya yafe mata koma wane laifi ne yake ganin tayi, wlhy bazata sake ba dan ALLAH yayi haƙuri ya barta ta dawo sashenta. A daƙile ya kalleta ya watsar, sai kuma yay wucewarsa batare dako tanka mata yayi ba ya shige ciki ya maida ƙofa ya kulle... Kuka mai tsuma zuciya da ruhi Saheeba ta saki. Wlhy ta gaji da zaman sashen Mamy bazata iya ba. Dan duk daɗin wani waje naka wajen daban ne. Ga Mamy da saka aikin tsiya. Haka zatai zaune saboda ƙafarta ba gama ƙwari tai ba taita sakata Safa da marwa tsakanin upstairs da downstairs. Wai sai tace bata gamsuwa da aikin su Haule ita tai mata da kanta, Nuratu kuwa lafkewa take ita adole bata da lafiya. Gaba ɗaya ta maidata wata ƴar aikinta ma. Ga kewar mijinta da buƙatarsa ya riga ya saba mata da fitinarsa. Ga kewar ƴaƴanta dako kallonta basayi gaba ɗaya sun koma sashen Oum ko tunawa da zamanta a gidan basayi. Ga jiya mamanta tace mata ta sanya ido akan Babban Yaya dan tasan mike faruwa tsakaninsa da ƴar Hajiya Shuwa. Wannan magana ma tafi komai ɗaga mata hankali. Dan a duniyar nan babu abinda ta tsana irin kishiya. Kai itafa ko ƙawarta akama kishiya ta daina ƙawance da ƙawar kenan. Shiyyasa ta shirya zuwa ta bashi haƙuri dan gara ta dawo kusa da mijinta in ma nesa da shi da take ne ya sashi fara kallon wasu matan. Tun ɗazun take dakon fitowarsa daga sashen Oum. Dan ita Nuratu yau taje gida amso musu wasu kayayyaki da mamansu ta aiko da su.. Ta jima a wajen tana kuka. Kafin ta tashi ta koma sashe Mamy. Ta buɗe ɗakin da take zaune ta shiga, waya ta ɗauka tai kiran Mamanta tana mata kuka ta zayyane mata komai daya faru. Ran Maman ya sake ɓaci, amma ta kwantar mata da hankali akan ta ƙyalesa indai sukai amfani da wannan kayan data turo duk wani girman kansa zai saukane. Wannan ya sake Saheeba jin sanyi a ranta, har tai shirin barci ta kwanta....
_______★
A ɓangaren Maanal kuwa koda ta shigo sashen nasu ta samu AA ya haye sama abinsa, har yama kashe wutar ko'ina sai amfani tai da fitilar wayarta. Tana shigowa bedroom ɗin yana fitowa daga bathroom, bathrobe ce a jikinsa alamar wanka yayo. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa dan harga ALLAH yaji haushi. Itama sai ta ɗauke nata tare da ɗan murguɗa baki ta wuce closet tana ƙunƙuni. (Haka kawai sai na zauna ka kashe ni. Sam babu tausayi a al'amarin ka. Yo in haka auren yake banga abin cewa akwai daɗi ba. Tsabar jaraba sam bana son naga mun kasance mu biyu kawai a waje tunda nasan ƙarshen zancen. ALLAH in zan dawo sashen nan gabana gabana har faɗuwa yake yi. Abu dare da safiya, yammaci da rana idan kana gida ma ba hutu.....) Haka dai taketa masifarta a rai idonta har yana cika da ƙwalla. Wai a hakan ma maganin nan na sit bath da Hajiya Shuwa ta bata yana matuƙar taimaka mata ne. Koda ta fito har ya gama nashi shirin yana zaune a cikin sofa ya ɗakko laptop yana kunnawa. Gefe ɗaya takardu ne sai kwalin fresh milk da kofi. Ɗauke kanta tai tayi shirinta. Tana gamawa tai shafa'i da wutri ta haye gado ya kwanta. Idanu AA ya ɗan ɗaga ya kalleta, sai kuma ya cije lips ya cigaba da aikinsa. Tun fa yana aikin da marmari har yaji ina bashi yiwuwa. Tattare komai yay ya ajiye, ya tashi ya kashe fitilar ɗakin ma gaba ɗaya dan dama mara haske sosai ce ke a kunne. Maanal datai barci cike da farin cikin fushin nasa dan tasan ko dai yaya ne ta samu sauƙi kawai ta farka a rikice jin ya nutsata cikin jikinsa. Muryarta na rawa ta buɗe baki zatai magana, ai bai bari a ta gama fita ba ya rufe shi ruff da nashi. Bore taso fara masa ya nuna mata ƙarfin ba ɗaya bane, wayon ma kuma ba ɗaya ba, dan sai da yasan duk hanyar da ya bi wajen lankwasar mata da jiki ta fara amsar saƙonsa. Sai da tafiya taje gaɓar tayar mata da hankali ta sanya masa kuka. Baiko saurareta ba sai da ya samu yanda yake so. Daga ƙarshe ya koma lallashinta da mata wayon daya saba. Sai ga hajjajunku an lafe a jikin AA ana sauke ajiyar zuciya.....
Na gabannin asuba kam da ya zame masa jiki kuka ta saka masa bana wasa ba, dole ya haƙura ya ƙyaleta. Koda ya fita salla kafin su dawo haka ta daure ta tashi ta hau gyaran gidan, harta sakko kitchen ta fara ƙoƙarin haɗa breakfast sai gashi ya shigo. Ƙin yarda tai ta kallesa, a haka ta gaishesa ita a dole tana fushi. Shi sai ma ta bashi dariya. Ya rungumeta yana murmushi da faɗin, “Haba Besty munyi faɗa ne wai?”. Baki ta tura gaba, idannunta na tara ƙwalla ta ce, “Eh munyi, kuma kada ka sake kulani tunda baka tausayi na. Ni wlhy sashen Oum zan koma kafin ka kasheni.” Sosai dariya tazoma AA wuya. Amma ya danne da ƙyar, a ransa ko ayyanawa yake (Inda ana mutuwa Besty da ba'a haifomu ba ai. Kedai kin cika raki ne kawai da tsoro. Sai kuma yanayin jikinki da sai dai nace Alhmdllh) a fili kam rungumeta yay yana lallashi, sai da tace masa ta haƙura sannan ya fara tayata sukai komai a tare, su Inte ta kira a waya suka kwashi abincin zuwa sashen Oum, dan haka take yi, a sashenta take musu breakfast gaba ɗaya, sai akai can sashen Oum, da rana kuma taje can tayi, hakama na dare. Yau da tasan zata koma aiki saita haɗama Oum harda abincin ranar ta, suma tai musu nasu ta na lunch. Tare sukai wanka suka shirya. Kayan farko data ɗakko zata saka AA yace bai yarda ba. Shi da kansa ya zaɓo mata wanda zata saka. Data saka ɗin kuma nan ma ya haɗe fuska wai suma ɗin dai tayi ƙyau. Gudun kar ya ja musu makara ta shiga lallashinsa, da ƙyar ya haƙura suka fito.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖9️⃣8️⃣
______________
.......Sashen Mamy suka fara nufa. Sosai zuciyar Mamy ta wani irin tsargawa. Dan wani irin ƙyau da nutsuwa ta gani a fuskokin yaran. Kodan hankalinta ba a kwance yake ba kwana biyun nan shiyyasa bata luran ba sai yau. Badan kar ace tayi ƙarya ba da tace idannunta kamar suna kallo mata yaron ciki a tare da Maanal. Kai ina abinda ma bazai yiwu ba kenan. Ciki fa, tabbas yarinyar nan akwai ƙaramin ciki a jikinta. Sai maganar wancan cikin ƙaryar ya faɗo mata a rai, a take taga wautarta a wancan lokacin, to yama akai ta zurma da wuri daga ganin yarinyar na amai, yanzu kam gashi babu wani signing na ciwo a tare da ita amma wlhy gaba ɗaya alamomin yarinyar ya mata na mai ciki..... Gaisuwar da suke mata ta katse mata tunaninta. Da ƙyar ta iya amsawa tana tsare AA da shima yay mata wani fresh da shi da ido. Yaron ya ƙara ƙyau da cikar kamala harda ƙiba. Kaida ka ganshi kasan hankalinsa a kwance yake, yana kuma hutawa da kwasar ganima a jikin mace dai-dai gwargwado. A lallai babbar magana. Ina hankalinta ya tafi har haka ita kuwa. Bata da amsar hakan, dan a yanzun ma dai hankalin nata baya a tare da ita har AA da Maanal ɗin suka fice abinsu. Sai Saheeba da itama jikinta ke mazarin abinda ta hango a tattare da Maanal ɗin ta maidota hankalinta ta hanyar faɗin, “Kai amma yarinyar nan fa wlhy kamar mai yaron ciki”. “Taratsatsatsa!!!!!!”. Kake jin sautin tarwatsewar abu a ƙasa. Ba komai bane face kofin shayi da Nuratu ta fito da shi a hannu daga kitchen. Dan ƙamshin turaren AA da tajiyo ne ya sata fitowa da sauri sai furicin Saheeba a kunneta babu kuma AA a falon. Muryarta na rawa ta ce, “Ciki kuma! A jikin wa?”. Saheeba ta ce, “A jikin wa kuwa in ba tsinanniyar yarinyar nan ba Maanal. Wlhy ko rantsuwa nayi babu kaffara wannan yarinyar ciki ne da ita ko Mamy?”. Mamy bata iya ta bama Saheeba amsa ba Nuratu dake hawaye ta ce, “Kenan da gaske wancan cikin bana gaskiya bane yarinyar nan is a virgin?”. Saheeba tace, “Tabbas wancan lokaci mun ruɗa kammu ne kawai yanzu ne yarinyar nan ke ɗauke da ciki na gaske. Maganar budurwa ce kuwa dole shima mu bincika dan akwai ƙamshin gaskiya”. Saheeba ke bayanin amma zuciyar Mamy ce ke duka da ƙarfi, jikin Nuratu kuwa na rawa.....
★★★
Su AA da basu san suna yi ba kuwa tuni sun isa sashen Oum. Itama dai yau kamar hasashen su Saheeban ya buɗe mata idanu akan Manaal ɗin. Dan sai duk kammanin ta suka juye mata na mai yaron ciki. Ko kuwa kwalliyar da tai ne ya canjata zuwa hakan. Duk da bawai Maanal ɗin tayi zane-zane a fuska bane. Hasalima hoda da kwalli sai lips-gloss ne kawai ta saka. Komai dai Oum batace akan hakan ba, sai ma gaisuwa da sukayi, dai-dai kuma nan Babban Yaya da Yaya Fawzan suka shigo suma a tare cikin shirin fita. Manaal ta gaishesu suka gaisa da Oum da AA sannan sukai zaman yin breakfast. Yau dai Fawzan bai tsokani AA ba. Hakan yasa Oum da sauran ƴan uwansa fuskantar ransa a ɓace yake. Sun tabbatar dai bazai wuce shi da Nibras ba, dan haka cikin hikima irin ta iyayen ƙwarai Oum ta shiga yimasa nasiha, ai ko sai gashi kafin su gama su fito harda ɗan murmushinsa. Su dukansu sukan shiga damuwa a duk lokacin da suka ga babu fara'a a fuskar fawzan, ba komai yasa haka ba kuma sai sanin shi mutum ne mai sauƙi da yawan fara'a, akan jima baka ga damuwa a tare da shi ba, dan ko abu ya ɓata masa rai yakan shanye shi ta yanda da wahala a gane masa kai tsaye. AA da kansa ya buɗema Maanal mota ta shiga, sannan ya zagaya ɗayan side ɗin da driver ya buɗe masa shima ya zauna. Yana gama zama ta kwanto jikinsa, kanta a kafaɗarsa ta lumshe idanunsa ɗan barci ne a cikinsu. Kallonta ya ɗanyi, sai kuma a hankali ya kamo hannunta cikin nashi ya riƙe. Ɗayan hannunsa kuma wayarsa yake dannawa yana son yay kiran RK. Tafiyar ƴan mintuna ta kawosu MAWAAD COMPANY. Sai Maanal taji tayi kewar wajen sosai. Yanda take kallon ko'ina yasa AA sakin ɗan murmushi. Ƙasa-ƙasa yace, “Kinyi kewarsa ne?”. “ALLAH sosai ma Besty”. Murmushi ya sake yi, sai kuma ya ɗan taɓe baki ya yunƙura ya fita dan har driver ya buɗe masa. Zagayawa yay ya buɗe ma Maanal, ya duƙo ya riƙo hannunta, ɗayan kuma ya ɗauka handbag ɗinta ya riƙe. Tuni masu shigowa suka tsaya kallon gulma, dan haka kawai suka tsargu da boss ɗin yau tare yake da amarya. Aiko sun gane ma idonsu abinda suke jiran, AA kam da baima san sunayi ba ƙoƙarin gyarama Maanal mayafinta yake yana kallon ta da murmushi, ita kuma tana masa magana a shagwaɓe dan yace mata yau a office ɗinsa zatai aiki ne, ita kuma tana cewa a'a bata yarda ba ita dai nata zata zauna sai tafi yin aiki da ƙyau. Uhhm babbar magana boss na murmushi available. Wannan shine taken gulma yau a Maawad. Lokacin da suke shigowa AS da shima ya iso yanzu suka haɗu a waje na biye dasu sai driver daya kwaso musu kayayyakinsu. Cike da farin ciki da girmamawa kowa kema Maanal barka da dawowa office. Itako tana amsawa kowa da kulawa da fara'a. Hakan kuma sai yayma kowa daɗi dan basuyi zaton haka ba. Jin tarihin alaƙarta da ogansu yasa suka fahimci hotonta ne a ko'ina na companyn, yanda aka ɓoye kamaninta ne yasa basu gane ba. Irinsu Zaharadeen kam kunya ce fal a cikinsu da jin shakkar haɗuwa da Maanal. Yayinda ƴammata masu ɓoyayyar manufa akan boss suke jin kishinta da shakkarta a wani gefen. Dan sun san dai lallai wutsiyar raƙumi tai nesa da ƙasa. Saboda muhimmancita ga boss mai girma ne ƙwarai da gaske da yanzu yake a bayyane gare su. Har cikin elevator hannunta na riƙe cikin nasa, amma kasancewar su AS a tare da su ya kama kansa kamar ba shi ba, itama Maanal ɗin a nutsenta take. Sai da suka fito ne ta saka masa rigimar ita dai office ɗinta zata. Dole ya haƙura ya yarda, amma sai taga ya nufi sama inda nashi yake na ƙarshe shi da AS. Zatai magana ya hanata, sai da suka iso taga AS ya buɗe office ɗin jikin na boss ɗin da ada yake kamar ma'ajiyar wasu muhimman abubuwa yasa Maanal a mamaki. Koda suka shiga sai tai tsaye tana kallon ikon ALLAH, sai kuma ta kalla AA ɗin dake kallonta yana murmushi. “Office ɗin waye?”. “Matar AA Darma mana. Kina tunanin zan barki ki cigaba da zama can ni ina nan? Sannan kema president ce kuma (Chairwoman) a wannan companyn, kina kuma da damar cigaba da kasancewarki a artist dan bazamuyi sakacin rasa gwarzuwarmu ba a wannan fanin. Barka da zuwa sabon office Bestyna”. Rasa ma abin cewa Maanal tayi, sai taji kawai ƙwalla ya cika mata idanu. A hankali ta shige jikin AA ta rungumesa tsama ta wani kalar sakar masa kuka. Shima slowly ya lumshe idanunsa tare da rungumeta yana ɗan murmushi. Saɗaf-saɗaf AS ya lallaɓa ya koma tare da ja musu ƙofar gulma da dariya fal cikinsa. AA cak ya ɗauka Maanal har zuwa office chair ɗinta dake sabuwa fil dan komai na office ɗin sabone irin na office ɗinsa, wancan kuma office ɗin Yaqub aka maida ciki a madadinta. Zama yay a kujerar ya sakata a cinyarsa. Sai da ya ɗiba tissue dake a saman desk ɗin ya share mata hawayen sannan cike da lallashi da soyayya ya ce, “Babyn Oum kwana biyun nan shagwaɓa kike jin yimin da yawa. Komai kuka kina son zama rigimammiya. Minene abin kuka anan, companyn ki ne fa, ko office ɗina kikace na fito na baki ba da gudu zan fito ina faɗin, “An gama Madam ba”. Dariya yanda yay ya bata, sai ta saki murmushi da ɗan ja masa hanci ta ce, “Daka zama mijin tace”.. Murmushi yayi mai ƙyatarwa, tare da sumbatar lips ɗinta ya ce, “Aini mijin kafin tace ne ma. Idan kuma da abinda yafi ma hakan to gaskiya duk ni ne Besty”. Dariya sosai yanzun kam Maanal keyi, shima yana tayata da murmushi. Zata fara masa godiya ya rufe mata baki da nashi. Bata hanashi ba, sai da ta tabbatar ta nuna godiyar tata a haka sannan. Ya rungumeta shima yana sanya mata albarka. Jin yanayinsa na ɗaukar sabon salo cike da wayo ya zame jikinsa ya bar office ɗin zuwa nashi shima. Ita ko ya barta da farin ciki tana faman zagaye office ɗin da kallo komai. Daga ƙarshe tai kiran Ammie a waya tana sanar mata. Ita kanta Ammie sai da taji ƙwalla ya taru mata a ido, dan a rayuwa takan ji matsannacin farin ciki idan taji Maanal a farin ciki. Kodan yarinyar ta wahalu a shekarun baya ne fiye da sauran oho. Bayan ta katse kiran su Didi ta kira suma ta gumtsa musu. Suma suka tayata farin ciki sosai.... Aikin dake a companyn sosai yasa babu zama, kowa aiki yake tuƙuru a tsakanin nan. Ita kanta Maanal yau gaba ɗaya bata huta ba. Sun shiga meeting har sau kusan huɗu kafin break. Sun fito na ƙarshe ne lokacin salla yayi, AA yaja ra'ayinta suka je office ɗinsa sukai alwala. Sannan suka fito zuwa yin salla. Ana idarwa suka dawo, a hanya ne suka haɗu da CFO. Sai tai saurin ɗauke kai kamar bata gansu ba. Murmushi Maanal tayi a ranta tace (ƙyaji da shi dai) a fili kam yitai kamar bata ganta ba. Dan taga dama wani ɗacin rai da take a wajen meeting. Shi kam AA baima ɗauka abinda CFO ɗin keyi a komai ba. Dan yanda ta iya takunta yasa bai wani fahimci take-takenta ba har yanzu. A office ɗinsa sukai zaman cin abincin data shiryo musu sukazo da shi. Suna nishaɗinsu da soyayyarsu. Bayan sun kammala Maanal ɗin ya haɗe komai waje guda ta koma nata office ɗin. Bata wani jima da zama ba suka sake fita yin meeting, sai dai yanzu babu AA yana ganawa da baƙi, AS ne ya zauna a madadinsa. Meeting ɗin ya jasu lokaci mai tsayi kafin su fito. Dan lokacin ma la'asar tayi........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖9️⃣9️⃣
______________
🥱🥱 Nace ba, na fara saida GUMAMA ta yara data manya mai so yayi magana kafin ta ƙare. Dan na sakata a farashi mai RAHUSA da ARHA, karku damu tana ƙamshi yanda ya kamata😆🤌.
Hhhhh Haba hajjaju ya da fara maida murtanin faɗa bayan WASAN bama a farashi ba. Banning number Bilyn Abdull tamkar an kashe MACIJI ne ba'a sare kansa ba wlhy😂. Dan ko mutuwa Bilyn Abdull tai in sha ALLAHU ina ji a raina zan cigaba da zama a zukatan masoyana zasuna min addu'ar kwanciya lafiya a kabari. Karki kuskura kice zakiyi wannan wasan, dan wlhy mamaki zan baki keda ƴan jagaliyar taki. Ke reporting kika sa akayi a WhatsApp ni kuma dare zan raba ina reporting naki ga babban sarki. Kinga maimakon Banning a WhatsApp ke a media ɗin gaba ɗaya ma UBANGIJINA zai yi banning ɗinki, (Wayaga ruwa zai ƙarema ɗan kada, dama kuma da ruwan muka dogara😜😆🤭).
Wannan Bilkisun da kike ganinta ba ƙyalan bace ƙyalle ce, kawai kafin mu sara ne mu sai mun dubi bakin gatari ALLAH wlhy. Ina ƙara baki shawara karki ce zaki saka Game dani akwai damuwa, ubana har ya rasu albarka yake zuba min, uwata kullum sai tace ALLAH yay miki albarka Bilkisu dan dattijuwar ƙwarai ta kullum goshinta na bisa ƙasa tanama UBANGIJI Sujuda. Mijina kam ai duk motsinsa sai ya ce Bilyn Abdull ALLAH yasa ki gama da duniya lafiya, yo an gaya miki a banza nake ɗaɗara shi a littafin🤪, gata yake bani iya gata, tsaro iya tsaro, naci shinkafa na kora da ruwan fanfo ga windows ɗin gidana iska tako ina ko ba'a bamu wutar nepa ba bana damuwa. Idan zai fita yanda nake masa addu'a haka yake min shima kaga shalelen Bilyn sa ALLAH yasa muna jone har a aljanna🤏🥰.
To Ladidi banda kankamba😲 ke wacece da kike tunanin zaki nuna min yatsa ban karya shi ba🤣 ina da waɗan nan ƙafofin murhun uku na haye kansu na zauna matsayin tukunya na dafa duk kalar ruwan dana gadama TSAYAWAR ALLAH kenan. To gaskiya ina baki shawara, kawai dai ki daurewa zuciyarki abar kaza cikin gashinta, dan in akace figeta za'ayi wallahi jikinta zai koma ne kamar na BALBELA. Shegen tsuntsu kenan ƙyau iya ƙyau a waje ciki kam ba'a cewa komai. WAJENJI FARI CIKINKI BAƘI KENAN😂.
Nifa a duniya cakwakiya na birgeni kwarai-kwarai da gaske kun ganni nan, ALLAH birgeni take😆, idan akai wasa ana gama AJIYA A DUHU zan saki sabon Update na zazzafan littafi mai suna Ladidi a harhaɗa🤣, alƙalami ɗan albarka, kun san yafi takobi kaifi, balle na Bilyn Abdull har ƴan a leƙa katanga zanowa yake, gashi baya yafiya dalla-dalla yake cika aikinsa🤫.
Bari dai nayi shiru, tsiyar Mamy ma ta ishi al'ummata, ita kuma Sille ya isheta😂, wayaga AJIYA A DUHU.
Kai idan akace ƴar baka za'ai na rantse akku zan koma muku ALLAH dai ya ƙyauta ba shekarar zazzaga bace ta kama😆, dan wata tabarmar idan aka zazzageta babu mai sake ɗora ɗuwawunsa akai saboda ƙazantar da aka zubar a bisanta.
Kudai kuyita salati ƴan uwa karna zare a maimakon labarin na koma muku tatsuniyar gizo-gizo. Dan labarin ƙoƙi dai baya wuce na gizon Update iya Update 😎.
🤔To Kuma su Haƙilah a dai kiyaye dan mun jima da sanin suna kuma mun san numbers, yanzu komai mai sauƙi ne a buga maka sallama a ƙofar gida daga ƴar jagaliyar media ki jawa kanki ai miki tonon leƙa katanga a gaban Rijalu da matan anguwa, ya barki a gida da tunanin ya killaceki ƙarƙashin igiya uku a kira shi ace kina ofishin ƴan doka. Banu taci ƴan a ara a yafa kenan, bamu san tushe ba amma muna rawar takaɗiɗi akan nera biyar-biyar😂. Tab ɗin wayaga goge hadda, kajawa kanka daga karanta HIKAYIYIN su Bilyn Abdull a tuɓale ƴar igiyar auren😮💨 dama lamarin rijalu yanzu ana basu wuta a sama suna bama Nisa'u a cikin gida, yana ƙaraki gaba wlhy galleliya zai santalo, idan dama kuma kina da abokiyar burmi a cikin gidan shike nan ya samu filin shakatawa, yo kunga laifinsa ne, koni na auri mace ta zama ƴar ARE-ARE (Gayyar SHANU) a media walle na kamata zanen yarbawa zan mata a uwawu😌 kafin na saita miki hanya zuwa gidan tsoho.🥳
To kama kanki wannan kokawar ta GIWAYE ce, ke kunama daga neman suna ko na gwajin harbi karki jama kanki ƙafa ta takeki batare da ansan da ke a cikin ƘURAR YAƘIN ba. Idan kunne yaji jiki ya tsira. 👉🙆👈