Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 99
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 99: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 99. .........Haushi sosai Hajiya…
3,718 words
__________★
Gaba ɗaya Yazeed baya gane komai a yanzu sai umarnin mahaifin matarsa. Ji yake ko wuta yace ya faɗa zai faɗa domin faranta masa. Nazeefa kuwa wata irin soyayya yake nuna mata kamar ya cinyeta. Balle da maganar cikin jikinta ta bayyana. Ita kanta sai abinda tace yayi yake yi. Dan haka take mugun tatsarsa kuɗaɗe, tana daga kwance shike mata tausa shine fita sayo mata abinci, shine mata wanki kai komai daya kamata tama kanta, tai masa matsayin matar gida yanzu shine keyi. Ga itama Sabuwa na zuba nata capacity ɗin a gefe. Sai da suka tabbatar sun gama samunsa a yanda suke so, sannan suka dawo gida Nigeria. Dawowar tasu kuma ta kasance rana ɗaya da dawowar su Ammie da Daddy suma. Sosai Daddy ya zubama Yazeed ido, yaron ya rame yayi duhu daka ganshi kasan baya a cikin hayyacinsa. Ji Ammie tai ƙwalla sun cika mata ido, dan a wannan dambarwar dai shi Yazeed shi aka cuta wlhy, tana ƙaunar Yazeed tana tausayinsa, dan yaron ya taka rawar gani a rayuwarsu suma, kuma in sha ALLAHU ta ɗauki aniyar taimaka masa a wannan gaɓar, bazata so cigaba da ganinsa a wannan yanayin ba. Daddy kam bazaka taɓa fuskantar komai a fuskarsa ba. Amma shima al'amarin Yazeed ɗin na matuƙar damunsa a zuciya. Sai dai ya zuba ido ne dan Hajiya Yaya taji a jikinta. Sai dai tabbas bazai yafe mata ba, dan ta cutar masa da yaro. Ɗansa babba abin sonsa, mai hankali da nutsuwa ga jin ƙan iyaye ta zama sanadin da aka maida masa shi ƙarƙashin ikon mace..
Yaya Yazeed kam sai yaji kunyar ganin Daddy da Ammie, dan ko wancan dawowar har suka sake barin ƙasar bai bari sun haɗu ba duk da gida ɗaya suke kwana suke tashi. A mamakin Nazeefa sai taga yaje yana gaida Daddyn da Ammie. Wannan abu ya mata zafi, fuuu ta wuce sashensu batare data gaida Daddyn ba ita balle ma Ammie da bata saka rai ba. Sai ko Yazeed ya zabura ya biyota yana kira kamar zai faɗi dan sauri. Hawaye suka zuboma Ammie. Daddy kam sai ya ma kauda kansa gefe. Ƙannensa da komai ka faruwa akan idonsu cike da baƙin ciki suka nufi sashen su suka sanar ma Hajiya Yaya. Aiko sai gata ta fito kamar zata tashi sama. Kai tsaye sashen Yazeed ɗin ta nufa, tana tura ƙofar kuwa ta buɗe. Ta wani bugata da iya ƙarfinta ta shiga falon. Turus taja ta tsaya hakama ƴaƴanta da suka biyota ganin Yazeed durƙushe a ƙasa yayi kneeling yana bama Nazeefa da tai wani zaman ƙasaita haƙuri. Itako sai danna waya take tana taunar cingum kamar ma bata san da shi ba. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Sarai Nazeefa taji shigowarsu amma sai ta watsar da su kamar bataji ba, sai ma cike da rashin mutunci ta dakama Yazeed tsawa. “Dalla malam yimin shiru, shashasha kawai dabai san ciwon kansa ba. Kai ko kunya bakaji ba zagam-zagam ka tafi gaida ubanka sai kace wani uban kirki. To wlhy ka jama kanka yau sai kaji a jikinka a gidan nan. Dalla tashi ka mana shara kana ganin waje duk datti”. Jiki Yazeed har rawa yake ya miƙe kuwa. Ko kallon su Hajiya Yaya baiyi ba ya nufi inda suke ajiye kayan shara ya ɗibo...........✍️
Tofa Hajiya Yaya da alama anzo dai-dai wajen🥱.
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖9️⃣6️⃣
______________
.......Muryar Hajiya Yaya na rawa ta ce, “Yazeed!”. Yanzun ma baiko kalleta ba sharar sa ya fara ma. Ta ƙara kiranshi cikin tsawa. Ko gezau baiyi ba. Dariya Nazeefa ta shiga tuntsurawa. Sai kuma ta wani miƙe cike da gadara da raini taje gaban Hajiya Yaya ta tsaya, kallon sama da ƙasa tai mata fuskarta da murmushin ƙularwa ta ce,. “Kima daina wahal da kanki, dan in dutsen arfa zaki hau kiyi ihu bazai taɓa ya jiki ba. Dan yanzu shi ɗin ba naki bane, nawa ne nan, dama kin rainar min shine Hajiya Sadiyya”. Ta kira ainahin sunan Hajiya Yaya. Hannu Hajiya Yaya data gama kaiwa wuya ta ɗaga ta ɗauke fuskar Nazeefa da mari. Marin daya farfaɗo da sauran ƴaƴanta da sukai sumar tsaye tunda akace yayansu yay shara. Gigitaccen ihu Nazeefa ta fasa da kiran sunan Yazeed. Bawan ALLAH tamkar ƙyaftawar ido har yazo inda suke. Yay ƙoƙarin kama Nazeefa yana tambayar miya sameta? Hankaɗashi tai baya ya tafi taga-taga zai faɗi saboda a bazata ta turesan. Ta kallesa hannunta riƙe da kuncinta ɗayan ta nuna Hajiya Yaya da yatsarta manuniya. “Wannan jakar ce ta mareni, kuma wlhy idan baka rama min ba sai na tafi gidanmu yau....” Ai baki ma Nazeefa bata gama rufewa ba Yazeed ya zabura tare da ɗaga hannu zai sauke ma Hajiya Yaya a fuska. Ammie da ihun Nazeefa ya sata nufo sashen saboda sashen su Yazeed ɗin shine kusa da nata, duk tana iya jiyo hayaniyar tasu caraf ta riƙe hannun Yazeed ɗin. ALLAH sarki Hajiya Yaya harta rufe idanu tana jiran saukar marin ɗanta a fuskarta😥. Abinda zai baka mamaki suma sauran yaran kowa ya kasa yunƙurin komai sai idanu kawai suka rufe dan suma su Sabuwa ba ƙyalesu sukai ba😂👍. Kai Ammie ta shiga girgiza masa hawaye cike da idannunta. Muryarta na rawa ta ce, “Karka sake ka taɓa wannan gangancin Yazeed. Komu da muke matan uba bama fatan ALLAH ya jarabceka da aikata hakan a kammu balle ita. Yazeed bakai data haifa ba, ko mu da muke ƙarƙashin miji ɗaya bazamu so taɓa kwatanta haka ba gareta kodan shekarun da ALLAH ya bata a kanmu. Haba Yazeed Mamma ce fa...” ALLAH sarki, a mamakin kowa sai Yazeed ya risinar da kansa a hankali. Itama Ammie sai ta sakar masa hannunsa. Sum-sum ya wuce yabar wajen kansa a ƙasa ya koma ya ɗauka tsintsiyar daya yarda ya cigaba da shararsa. Ko kaɗan ba haka Basariyya dake laɓe jikin window tana leƙe taso ba. Sai taji wani irin haushi da takaicin Ammie ya sake kamata. Cikin ƙus-ƙus tace, ‘Munafuka ta hanamu kallon show. Ai mu irin wannan wasan muke so’. Ko kallon Nazeefa dake cika tana batsewa Ammie batai ba. Sai ma hannun Hajiya Yaya ta kama. Cike da lallashi da kwantar da hankali ta ce, “Yaya kiyi haƙuri muje”. ALLAH sarki rayuwa, Hajiya Yaya ko musu bataima Ammie ba. Ta sake kallon inda taga Hajiya Basariyya dake laɓe tun ɗazun ta janye idanun ta dake cike da hawaye. Suma yaran Ammie tace, “Ku wuce muje”. Suma babu wanda yay musu. Har falo Ammie takai Hajiya Yaya, ta taimaka mata ta zauna sannan ta dubi yaran ta ce, “Ku bani ruwa mai sanyi”. Amrah ce dake hawaye taje ta ɗauka mata. Koda ta kawo Ammie ta buɗe ruwan Hajiya Yaya ta ba, nanma bata musa ba ta amsa ta sha, dan ji take tamkar zuciyarta zata fashe mata a cikin ƙirji. Sosai tasha ruwan, dan ɗan kaɗan ta rage. Kamar dama ruwan take jira tasha kawai ta saki kuka. Yaran duk sunyo kanta a zabure zasuyi magana Ammie tai musu alamar suyi shiru. Duk komawa sukai suka zauna, sai da Hajiya Yaya tai kuka sosai sannan Ammie ta ciri tissue ta bata ta kuma sake bata ruwan tasha. Bayan wasu mintuna ta sake natsawa Ammie ta fuskanceta. “Yaya kuka ba shine mafita ba, na barki kiyisa ne dan ki samu nauyin zuciyarki ya ragu. Kiyi haƙuri idan na shiga hurumin daba nawa ba. Amma Yazeed ba kuka ko biyema yarinyar nan ai rikici al'amarinsu ke buƙata ba. Hasalima ɗauke idanu daga garesu shine yafi alkairi, idan ba haka ba komai zai iya faruwa, saboda Yazeed baya a cikin hayyacinsa gaba ɗaya. Yanzu shi yana a wani matsayine da baya banbance fari da baƙi sai wanda yarinyar nan ta nuna masa kawai. To idan muka ce ta ƙarfin tsiya zamu sakashi ya gane akwai babban matsala, dan maimakon ya gane ɗin sai ya sake rikice mana ne kawai, idanunsa su sake makancewa daga ganinmu. Dan haka dole zamuyi haƙuri da kauda kai na wani ɗan lokaci, mu shanye zafi da radaɗin da muke ji akan wannan sabon yanayin nashi tunda mun san bayin kansa bane. Ita kanta yarinyar mu barta ta rinƙa jin tamakar ta gama samun dukkan nasarar da take buƙata sai mu samu damar gayama ALLAH damuwar ya warware mana ita cikin sauƙi kuma. Amma tankawa da nuna damuwar kai tsaye a yanzu tamkar sake zaburar da ita ne ta cigaba da sabon shiri a kansa, shi kuma dama illar sihiri ɗaura wani aikin akan wani, yakan sa asha wahala sosai kafin a raba mutum da shi. Wannan shine mataki na farko da zai taimaka mana. Mataki na biyu addu'a, Yaya Addu'a Yazeed yake buƙata daga garemu baki ɗaya. Kuma taki ita ce mafi ƙololuwar daraja a gareshi, itace kuma tamkar yankan wuƙa. Kasancewar ta a hakan kuma bazai samu ba sai kin daure kin sanyaya zuciyarki, kin yafe ma Yazeed kurakuransa. Ki rage barci, ki tashi cikin dare ki gayama ALLAH damuwar ki masa kuka ki masa bagiya shi mai ji ne mai gani, kuma shine ke raba abinda duk duniya babu mai kwatantawa. Yaya da zakiji wahalhalun da na fuskanta a rayuwata data zuri'ata da kince wannan na Yazeed ba komai bane ba. Amma wlhy ban taɓa zuwa gaban wani na duƙa nace ya taimakeni da garin magani ba. UBANGIJINA na fuskanta, shi kaɗai na amince zai yaye min damuwar da ƙuncin. Na ajiye maganar barci gefe, na sadaukar da rabin nema na a sadaƙa, na maida harshena da laɓɓana a ambaton UBANGIJI ne a koda yaushe. Na rungumi ƙishirwa da yunwa a kowane yini. Na sakama zuciyata jarumta da tunatar da kaina akwai fa wanda suka fini shiga ƙuncin rayuwar, akwai wanda idan zanga halin da suke a ciki nawa ba komai bane ba. Na dinga tuna ANNABAWAN ALLAH ma an jarabcesu. SAHABBAN MANZON ALLAH sun sha gwagwarmaya da jarabawoyi kala-kala. Amma da sukai haƙuri wace irin riba ce basu samu ba. Ƙarshen dai wahala da faɗi tashin bawa shine ya samu makoma mai ƙyau ta aljanna. To su tun ma suna duniya akama mafiya yawansu albishir da aljannar, sakamakon ayyukansu na alkairi da sadaukarwar yaƙi a bayan MANZON ALLAH. Wannan abubuwan sun ƙarfafani matuƙa, na kuma saka yarana suma suka dage, dan nasan yanda tasirin addu'ar uwa take akan ɗa haka addu'ar yara nada tasiri matuƙa. Dan haka Yaya ki jure, ki gwada ki gani in sha ALLAHU zakiyi dariya nan bada jimawa ba, al'amarin Yazeed zai zama tamkar labari ne. Muma kuma ba zama zamuyi ba in sha ALLAHU. ALLAH ya baki haƙuri ya sanyaya ranki.” ta juya ga yaran suma da duk suka nutsu suna saurarenta. “Kuma ina muku nasiha da ku kauda kanku akan al'amarin Yayanku, komi zaku gani tsakaninsa da matarsa dan ALLAH ku daina zuwa kuna faɗawa mahaifiyarku. Ba wannan Yazeed ke buƙata ba, addu'a yake buƙata, idan ba haka ba maimakon mu tsamoshi a wannan masifar sai dai mu sake bada hanyar sakashi a cikin wani. Kunga dai abinda yaso faruwa. Da taci nasara ya mari mahaifiyarku kunga ya sake shiga wata masifar ne ai ko. Ku kwantar da hankalinku mu haɗu mu tayashi da addu'a, sadaka, komai zai wuce”. Daga haka Ammie ta miƙe abinta. Harta kusa kaiwa ƙofa Amrah dake kuka sosai ta ce, “Ammie!”. Tsayawa Ammie tayi, tare da juyowa tana kallon ta, sai kawai Amrah ta taso da gudu ta rungumeta tana sake fashewa da kuka da faɗin, “Mun gode Ammie, mun gode, in sha ALLAHU ke ƴar aljanna ce. Dama nace ke mai ƙaunarmu ce da zuciya ɗaya amma ba'a fahimtata.....” Murmushi Ammie tayi, tare da ɗagota, cikin katseta ta ce, “Amrah ya isa haka kinji, mu dukanmu in sha ALLAHU ƴan aljanna ne. Kuma ba fahimtarki ne ba'ayi ba. Kowace rayuwa da nata ƙalubale ne kinji”. Amrah zata sake magana Ammie ta hanata, sai ma share mata hawaye datai tas sannan ta maidata ta zaunar ta fice...
★Baki Hajiya Basariyya ta ƙyaɓe. Tare da faɗin, “Kai wannan kilakakkiyar mata anyi munafuka. Ita adole gata ALLAH. Yannn! yannnn! yannnn! Tana wani zabga wa'azi. Sai dai kuma a gayama wasu amma wlhy bamu ba. Ubanwa ye zai yarda wani kin tsaya a addu'a ne da azumi da mima tace. Waye wawa an gama tsaface mana miji, da samarin ƴaƴanmu sun aure ƴaƴanki”. Haka dai ta gama surutanta sai kuma ta gyara yanayinta ta nufi cikin falon Hajiya Yayan a ɗan rikice. Har wani neman yin tuntuɓe take zata faɗi. Tadai dafe kujera tana kaiwa zaune kusa da kujerar da Hajiya Yaya ke zaune. Sudai kallonta suke kawai. Cike da makirci ta fara faɗin, “Mun shiga uku, ina wanka yanzu Jannah ke sanar min abinda ke faruwa. Kai wannan yarinya anyi ibilishiya, ita yanzu dan bata da mutunci sai ta saka Yazeed ya mareki, kai ALLAH wadan naka dai ya lalace. Amma gaskiya dai ya kamata a kira Sabuwa a gaya mata wannan ɗanyan aiki tazo tai mata faɗa dan ba halin arziƙi bane ba. Yanzu haka ƙawayen banza ne suka ɗorata a wannan hanyar mara ɓullewa. Yo mara ɓullewa mana kasa ɗa ya mari suruka ina arziƙi. Ita bata tunanin zata haifa tunda ga cikin nan a gabanta itama za'ai mata wataran. Ai ni yaran nan baku ƙyauta min ba da baku haɗu kun lakaɗama shegiya duka ba, har sauran ƴan uwanku duk basai ku kira ba damu mu haɗu mu ci ubanta ai daɗi gidan yawan kenan dama ko”. Amrah da surutun ke ƙonama zuciya ta ce, “Ai hakan baida amfani Ummi. ALLAH kawai ya shiryeta. Jarabawace watarana sai labari.” Kasare Hajiya Basariyya tai tana kallonta, ta zata wani zai sake magana ta samu point, sai taga kowa bai tanka ba. Hajiya Yaya ma miƙewa tai abinta ta nufi bedroom. Sai suma yaran suka fara miƙewa.. ganin fa zataji kunya sai itama ta miƙe tana faɗin, “To ALLAH dai ya ƙyauta. ALLAH kuma ya kiyaye gaba iyakarta kenan”. Daga haka ta fito tana tsine musu a zuciya. Ganin nan babu nasara sai ta nufi sashen Ammie, Sakina da Waleed kawai ta samu, sukace mata Ammie na sashen Daddy. Nan ma ta fito cike da baƙin ciki, amma sai itama ta nufi sashen Daddy ɗin duk da kuwa ɗazun taje ya korota..........✍️
🤣Itafa Hajiya Basariyya tafi dacewa da haihuwar Saheeba. Kai ALLAH ya rabamu da munafunci gaskiya☹️.
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖9️⃣7️⃣
______________
Chapter notes and social links
.........Haushi sosai Hajiya Turai taji da ganin Maman Saheeba, amma sai ta dake suka gaisa, koda Maman Saheeba ke sanar mata ai sunata kiranta a waya tun ɗazun sai tace ta fita ne yanzu take dawowa. Akwai kayan ta da suka ɓace a airport shine sukaje ake nema ga mai kayan ma har yazo amsa yanzu. Dan tasha jinin jikinta tabbas sunga Sille. Aiko sai cewa Maman Saheeba tai, “Ko shine ma mukaga yana fita yanzu”. “A eh kwarai shine! Shine!”. “Kai wanan kasuwanci naku kuna ƙoƙarin, ai ni wannan mutumin sai ya firgitani”. Cikin murmushin yaƙe Hajiya Turai tace, “To mu da muka kasa a siya ina ruwanmu da s....” maganar ta maƙale saboda shigowar Sille.. Daburcewa Hajiya Turai tayi, haka shima sai ya tsaya turus yana kallon Maman Saheeba, dan ya santa, kai kaf dangin Mamy ma ya sani saboda a biye yake da komai nata tsahon shekaru, sune dai basu sanshi ba sai ita Hajiya Turan. Cikin in ina Hajiya Turai ta ce, “Yauwa ka dawo? Dama nace ko na ɗakko maka wanda ke hannuna kafin wancan su fito?”. Shiru Sille yay bai tanka ba, sai ma zaune da ya kai a cikin kujerar. Hajiya Turai data fahimci mi yake nufi saita kalla Maman Saheeba. “Nana muje ciki, idan na ƙarasa da shi zan shigo”. Miƙewa kuwa tayi zaram dan dama harga ALLAH a tsorace take ita kam. Yo kallon idanun Sille kawai abin firgitarwa ne. Tana shigewa Hajiya Turai ta tabbatar ta shige ɗin ta dawo kusa da shi cike da tashin hankali da lallashi ta ce, “Dan ALLAH kayi haƙuri Baby, wlhy ban san zata zo ba, nima ganinta kawai nai yanzu”. Batare da ko kallon Hajiya Turai ɗin yayi ba a daƙile ya ce, “Ki sallameta yanzu nan ta koma inda ta fito kota kama gabanta, dan ban gama abinda nake ba bazan tafi saboda wata banza ba matsalarku ce”. Ya miƙe abinsa ya wuce bedroom ɗinta yana wani tafiyar rangajin iskanci. Ji Hajiya Turai tai kamar ta sanya kuka, amma tasan dole ne ta sallami Nana kamar yanda ya faɗa dan bazai bar gidan ba kuwa. Mamman Saheeba na a ɗakin da take sauka idan tazo Hajiya Turai ta sameta. Fuskarta ta ƙawata da murmushi tana kallonta. Sai kuma ta ce, “Kinga ko kinzo a dai-dai, dama akwai ticket dana saya yau zan je Kano sai batun kayan nan ya shigo, dole zan canja na tafi Lagos anjima dan wai kayan nacan. Ga mutumin nan bai da kirki ya bani daga yau ne zuwa gobe kayansa kawai ko kuɗinsa. Ni kuma na cinye kuɗin, tare ma zamuje lagos ɗin da shi”. Cikin rashin damuwa Maman Saheeba tace, “Ai kije Lagos ɗinki kawai ki dawo zan zauna abina. Saina kira Nuratu ta tayani zama”. Hajiya Turai ta danne takaicinta ta ce, “Ai bazai yiwu ba Nana, mutumin nan yaje yay bi baya ko yasa azo a cutar daku, shiyyasa ma naji daɗin da Nuratu bata gidan. Baya ji fa cikin Abujan nan kaf tsoransa ake ji, nima tsautsayi wani ministar ne ya taɓa aikosa amsar kaya a wajena shine sanadin da ya fara sayen kayan shima ga shi nan ya zame min alaƙaƙai. Dan haka faka-faka shirya mu wuce airport nima daga can zan wuce.” Sam ba haka Maman Saheeba taso ba, gashi bata son komawa gidan Darma tana kunyar haɗuwa da Abah. Ga al'amarin nan na babban Yaya da ƴar Hajiya Shuwa ya tsaya mata a rai. Ƙin gaisheta da AA yayi, har ma ta shiga motar ta fita bai nuna ya santa ba nan ma ya zafeta. Haka dai ta shirya badan taso ba Hajiya Turai ta ɗauketa suka tafi airport. Suna isowa sai ga kiran Mamy ya sake shigowa Hajiya Turai, kaɗan ya rage taja tsaki ALLAH dai ya kiyaye. Koda ta ɗaga cike da wayancewa taba Mamy haƙuri da tsarata kamar yanda ta tsara Maman Saheeba. Mamy tace “Ba komai, dama wani hoto na tura miki ta WhatsApp dan ALLAH idan ban takuraki ba ɗan duba ki gani yanzu”. Babu musu Hajiya Turai ta shiga WhatsApp ɗin kuwa tana faɗin, “Haba ba komai ai” dai-dai tana buɗe hoton dan bata yanke kiran ba. Ta ce, “Wannan ai Ra'iz ne. Badai zancen first night ɗin yaran nan bane ke neman tada ƙura?”. Mamy da abin ya daketa cikin dauriya ta ce, “Shine kuwa Hajiya Turai, ina son nasan gaskiya kafin Aban su Ajwaad yace zai yi bincike. Kinga dai ƴan uwansa duk suna a gidan nan maganar nan ta fito, wannan shirun nasu kuma na tabbatar akwai wata a ƙasa. Ina Ra'iz yanzu? Ina son naji shin da gaske baima yarinyar nan komai ba a wacan ranar amma ya amsa mana yayi.” “Tab babbar magana. A yanzu Ban san ina Ra'iz yake ba gaskiya. Dan tun bayan aikin nan wata alaƙa bata sake haɗamu ba”. Ji Mamy tai kamar ta zandara ihu. Amma ta danne da ƙyau zuciyarta sai bugawa take. Cike da damuwa ta ce, “Lallai akwai matsala Momyn Nuratu”. “Amma ni sai nake ganin abun duk mai sauƙi ne. Ki zauna da shi Ajwaad ɗin mana. Nima kuma zan bincika inda Ra'iz ɗin yake” “Zama da Ajwaad ba shine mafita ba shiyyasa ma ban masa ko zancen ba har yanzu. Kin san wannan matsiyacin yaron Rafeeq ne ya baza musu zancen yarinyar virgin ce. Ina da tabbacin koshi Ajwaad ɗin babu wanda yay maganar da shi akan hakan har yanzu, alamun akwai abinda suke shiryawa. Nasan su wanene wannan family ɗin Turai, wlhy akwai damuwa. Gashi na saka a bincika min Dr Tofa ɗin ma har yanzu babu wani bayani. Idan nace kuma zanje Kanon da kaina a yanzu akwai damuwa”. “In dai dan wannan ne ki kwantar da hankalinki, daga yau zuwa gobe zansa a bincika mana Dr Tofa ɗin shima”. Mamy ta ɗan ji sanyi a ranta, amma zuciyarta a birkice take fiye da farko. Tana ajiye wayar zufa na keto mata. Gadai Hajiya Turai ta tabbatar mata yaron da suka saka aiki ne akan Maanal. To miya haɗashi da Junaid kuma? Sannan Junaid bai san da zaman jaririn can ba taya za'ai hotunan su su kasance tare a wajen mutum ɗaya? Yau ta shiga uku mike shirin faruwa da ita? Ga batun Abah na ɗaga mata hankali. Kada dai ace abubuwa ne zasu rikice mata a gaɓar da take ganin nasararta zata fara, ƴaƴanta da komai nasu zai dawo tafin hannunta. Mijinta da take ganin ta gama nasarar wawashe zuciyarsa gaba ɗaya zuwa yanzu amma zai suɓuce mata. Wai wanene wannan mai tura mata saƙon? Wanene shi? Miyyasa zai shigo duniyar ta a gaɓar samun nasararta da ribantuwa da wahalhalunta da haƙuri da juriya da tai na shekaru aru-aru. Mafita ɗaya gareta a yanzu ta sanin wanene shi? T kuma yarda su gana kamar yanda ya buƙata, to amma idan ta amince lokaci guda zai ɗauketa shashasha. Bari ta ɗan latsashi na wani lokaci kamar bata damu ba. Kuɗi kuma bai isa ya ci su ba....